Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 38

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 38

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 38: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 38. Kamar anyi ruwa an dauke haka kowa a cikinsu ya kasa…

3,358 words

Kamar anyi ruwa an dauke haka kowa a cikinsu ya kasa magana,ya kuma kasa cewa komai,musamman omar da yakejin wani abu yana tsargawa ta cikin jininsa da zuciyarsa. Yana son ya gaya masa labarin sakin akhnan diya ga sultane wanda yayi waliccin aurenta,yana jin kamar nauyin zaiwa zuciyarsa yawa. Ya sani faduwa a wannan aikin wani abune da zai ma haisam din wahalan dauka,sai kuma gashi dukkanin alamu suna nunawa cewa BA'A BANZA AKA HAIFESHI A MATSAYIN YARIMA BA,BA'A BANZA YA FITA DAGA JINI ABBA JIFAR BA.......ba kuma a banza yake dauke da kalar wannan nauyin ba.

Baya ya basu yana fuskantar widow.......bayason ya matsantawa kowa aiki dashi......bayaso suji nauyin idanunsa suyi masa kara,baya kuma so kuma ya shiga hurumin rayuwarsu na matsa musu ci gaba da rayuwa cikin agadez. Daren jiya duka baiyi bacci ba ko sau daya,baccin da har yanzu yakejinsa cikin idanunsa,amma sai yakejin bai samu lokaci da zai kwanta ba.

Ya qarasa qarar da daren jiya ne wajen yin sallah da tarin addu'oin da suka bashi cikakkiyar nutsuwa a yau din. Ya tsaya gaban ubangijin kowa yana damqa amanar kansa da kansa a hannunsa da kuma neman jagoranci daga gareshi. Salon sirrintattun addu'oin daya saba yi a duk sanda wani abu ya cakude masa ko ya shige masa duhu,wanda kuma yake da cikakken alaqa me kyau da Allah,don ko sau daya ubangiji bai taba kunyatashi ba. Yanaji a ransa zaiyi komai da dukka numfashinsa......yana kuma jin zai fuskanci komai da sadaukarwa.

Hannunsa yaji an riqo ta baya,tun kafin ya juyo kuma yasan omar ne,sai ya tsinci omar din yana fadin.

"Ina tare dakai a dukkanin abinda ka shirya zakayi......a iya adadin kwanaki watanni ko shekarun da zaka kwashe a agadez.....har sai mun cimma nasara" Yayi maganar yana dora hannunsa saman na haisam.

Kafin haisam din yace komai abdii ya matso ya aza hannunsa saman na omari dake kan na haisam din,ya kuma sake maimaita abinda omar ya fadi. Ya daga idanunsa da sauri zaiyi magana salawi ya biyo baya,basu barshi yace komai ba har sai da dukkanin wanda ke gurin ya dora hannunsa saman nasa yana masa mubaya'a da dukkan gaskiyarsa da zuciyarsa.

Wani irin abu yaji yana ratsashi,bawai don yafi kowa ba amma Allah ya mallaka masa amincin wadannna mutane dukkaninsu lokaci guda?,sai ya rasa me zaice,ya wara hannuwansa iya yadda zai iya yana rungumesu,zuciyarsa tayi wani rauni,ya rasa da wacce kalma zai nuna girman karbar amincinsu da yayi.

*BAYAN AWA DAYA*

*SULTANE*

Tun bayan kammala wayarsa da mammina yakejin wani irin shuru cikin kansa. Tun bayan da suka gama wayar data isar da saqon da takeson isarwa yakejin komai ya dauke masa wuta. Wani abune da bai taba tunanin zai faru ba,wani abune da iya hasashensa ko lissafin rayuwarsa bai taba qiyasta zai faru ga gudan jininsa ba. SAKI irin wannan wulaqantaccen saki?. Cikin kwanaki uku kacal da daurin auren?. Da wanne idanu zai kalli duniya?,da wanne idanu zai jama'arsa?.

A yanzun da yake zaune gaban ka'aba bayan ya kammala dawafi na musamman da yayi saboda akhnan din.....ya gaza tantance laifin waye?. Laifinta ne bisa bijirewa dukkanin zabin da yayi mata wanda yake da tabbas a kansa?,laifinta ne na rashin daukan zabinsa da muhimmanci ta zabi fifita nata zabin akan nasa?. Ko Laifinsa ne?. Shin laifinsa ne daya barta da zabinta?,laifinsa ne daya kauda kai daga dukkan al'amuranta?,ya kauda kai daga zurfafa bincike akan mutumin data kawo tana so ta aura?.

Idanunsa kan dakin Allah......yayin da zuciyarsa ta cika da wani irin yaqini da kyautatawa Allah zato. Sawun mutane masu yin dawafi ya ragu sosai daga cunkusonsa na al'ada,wannan ya bashi damar ganin ka'aba sosai daga inda yake zaunen.

Idanunsa ya lumshe a hankali na tsahon wasu mintuna,yana son tuna me ya kamata yayi?,yanason tuna me ya kamata ya aiwatar. Kamar an rada masa sunan haisam ya fado a ransa,sai ya fara laluben wayarsa.

Ya tabbatar shi kadai zaiyi magana dashi yaji dadi a ransa,yana kyautata zaton baiji maganar ba tunda bayajin dadi kwana biyun shi yasa bai kirashi ba. Yanajin dadin magana dashi,yana jin nutsuwar magana da haisam sosai,wani lokaci idan yana bayyana damuwarsa a gabansa ko a tare dashi,yakanji irin yanayin nan da d'a yakeji a sanda yake magana da mahaifiyarsa.

*HAISAM*

Idanun omar a kansa sanda yake takowa inda yake zaunen. Cikin wata qaramar rumfa dake ta bayan gidan daura da wani garden dake dauke da wasu nau'ikan shuke shuke dake bada iska me kyau daya banbamta da iskar da gidan yake kadawa.

Yayi relax cikin rocking chair yana lilawa a hankali,idanunsa a lumshe suke abinda yake alamtawa omar cewa ya lula ne duniyar tunani.

Motsin da yaji ya sanyashi bude idanunsa kadan,ganin omar din kuma ya sanyashi bude idanun nasa gaba daya ya tashi ya zauna sosai cikin kujerar.

"Ina maleek ya shiga ne?". Kafada omar ya daga yana neman wajen zama.

" Tun sanda yaga zamu zauna meeting ya fita,kuma har yanzu bai dawo ba......hussam ne yaketa kirana yanaso na hadaka dashi........issue ne na company,order din daya saka daga India ta iso........sannan yace watanni uku suka rage a fidda sabon scents,suna buqatar hankalinka a wajen" Qaramin tsaki haisam din yaja yana shirin komawa cikin kujerar.

"Ka fada masa idan bazai iya handling komai ba ya zauna ya zubawa company din ido" Yana qarasa fada ya maida idanunsa ya lumshe. Murmushi omar ya saki......haisam yana wasa da kasuwancin da Allah yayi.masa wata irin daukaka dashi kansa baiyi zato ba. Yana mamakin yadda yake fifita aikin security services akan kasuwancin da kowacce rana wasu irin mahaukatan kudi suke saukewa a account dinsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kaf kamfanin turaruka dake duniya a yanzu ba wanda yake daukakar nasa da karbuwarsa,amma ya tattara komai ya aza akan hussam.

"Man.....yaron nan fa yana qoqari".

" Kada ma yayi.....namiji ne ai,dama kuma shi namiji ai ba'a sanshi da hutu ba....banda ragonci me ya sani?,company uku kawai amma ya kasa riqesu gaba daya sai qwaya daya?,dayanma komai sai anyi guiding nasa?" Ya fadi yana bude manyan idanunsa da suka rusuna a yau din kan fuskar omar.

Wannan kwarjinin nasu ne ya motsa,ya kuma daki omar din,sai kawai ya kauda idanunsa daga kan haisam din yana lalubar wayarsa don bawa hussam mafita. Shi kansa yasan a yanzu haisam din bazai saurareshi ba.

"Fata dai kawai idan ka kammala branch dinka dake dubai ka nemi wani ka bawa....kada ka hada masa zafi" Yayi maganan yana danna kiran hussam,daidai sanda kiran suitane ke shigowa wayar hasaim,abinda ya sanya omari tashi yana waya da hussam din ya barwa haisam gurin.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Muryar sultane ta bayyana cikin wayar,muryar dake cike da wani irin dattako da kawaici,muryar data saukar da wani irin tausayin sultane din me nauyin gaske a zuciyar haisam.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 66*

"Wa'alaikumussalam warahmatullah,barka da warhaka" Haisam ya amsa masa cikin matuqar girmamawa,girmamawar data daukar da murmushi duk da tarin zafin dake ratsa zuciyar sultane din.

"Barka kade haisam,ina fatan ban shiga huruminka ba kirana kuma bai takuraka ba" Maganan saita masa nauyi,don da gaske zuwa yanzu yana yiwa sultane wani kallo na tausayi,kallo kuma na girmamawa.

"Ina fata yarona yana lafiya".

" Alhamdulillah,ina fatana kana cikin aminci da nutsuwa" Haisam din ya maida masa. Idanunsa ya lumshe,yaja wani numfashi can qasa,tambayar nutsuwarsa da haisam din yayi sai yakejin kamar ya fama masa wani tabo ne dake danqare qasan zuciyarsa.

"Ina cikin aminci,amma nutsuwa tayi nesa da zuciyata haisam". Magana sai ta yiwa haisam wani iri,fargaba kadan taso kama zuciyarsa amma ya daidaita yanayinsa.

"Ina fata kana cikin agadez?" Kai haisam ya jinjina masa kamar yana a gabansa.

"Ina nan ranka ya dade.....ina riqe da amanar al'ummarka"

"Ma sha Allah.....naji dadin hakan" Sultane ya furta a nutse,saidai qasan ransa yana jin nauyin furta maganar da alamu ke sake gaya masa haisam baisan da ita ba. Yanayin shurun sultane bai masa kama da amintaccen shuru ga wanda ya gama magana ba,wannan ya sake sanyashi tattara hankalinsa a kansa.

"Labari ya riskeni a daren nan haisam.....auren akhnan ya qare....mijin data aura kwanaki uku baya ya saketa". Da sauri ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa tana wani irin harbawa. Maganar ta shammaceshi ta kuma zo masa a bazata sosai. Harshensa da zuciyarsa yaji sunyi nauyi,mamaki yana sake cika kwanyarsa.

Wanne irin baqon al'amari ne wannan?,ya akayi baisan da lamarin ba a matsayinsa na waliyyinta?,shi ya kamata sultane yaji daga bakinsa bawai shi yaji daga bakin sultane ba. Wani irin nauyin sultane yaji ya saukar masa,sai yaji gaba daya kaman laifi yana laftuwa a kansa,sai yaji kamar shurun da sultane yayi yana bashi qofa ko dama na kare kansa,sai yaji kaman ya gaza da riqe wannan amanar ta wannan bangaren,sai yaji kamar ya gaza a aikin da sultane ya bashi.

Ta wani fannin kuma haka kawai yaji wani nauyi yana sauka daga qirjinsa......a hankali yakejin wani abu daya tsaya masa a wuya kamar yana narkewa yana wucewa. Alhamdulillah,ya furta qasa qasa,yanajin kamar wata rahama akayi masa bushara da ita,ta wannan bangaren yanajin ya kubuta daga fadawa TARKON mammina data d'ana,ta kuma shirya akan fadawar kowanne mutum daya rabi plan dinta.

"Subhanallah......" Ya furta a fili a hankali,yana saukewa muryar sultane cike da raunin da ba kasafai zaka ji sarakai da irinsa ba.

Ina tsaye daura da dakin Allah haisam.....labarin sai yayimin nauyi da yawa" Kansa ya gyada a hankali,ya sani ko waye mutum dole ya fuskanci irin wannan yanayin,sakin aure ga diyar da yafi so da qauna fiye da komai ba qaramin lamari zai zame masa ba.

"Haka ne.....amma sau da dama wani lokaci gaskiya takan zabi bayyana a muhallin da taga dama"

"Gaskiya ne.....inajin kamar na gaza ne haisam,inaji kamar na kasa,ina jina kamar wani gajiyayyen shugaba......sau da dama shugaba yakanyi tunanin shuru hikima ce......har sai lokaci da wanna shurun ya zama KUSKURE". Yakai qarshen maganan yana tuna adadin lokutan da morsa safiyya ta kwashe tana kwabarsa akan duk wani motsi na akhnan din. Bai taba kallon hakan a matsayin tsana ga akhnan ba,saidai ya sake mata wasu abubuwa ne saboda soyayya,ya sake mata wasu abubuwa ne saboda yana gani da tunanin TSANANI baya tarbiyya.

Tsam haisam ya miqe yana takawa a hankali,yana tsinkayi ma'anoni masu yawa cikin maganganun sultane din,ma'anonin da yake sanya ran su juye watan watarana zuwa fahimtar birnannun abubuwa dake lungu da saqo na masarautarsa.

"Baka gaza ba ranka ya dade.....baka zama gajiyayye ba,shurunka kuma bai zama kuskure ba,kayi dukka iya qoqarinka na kula da komai,na ajiye komai a muhallinsa.....wani lokaci koda ginannen bango dake a tsaye yana iyayin rauni,akwai alaqa qarfafar gini da samun gini me kyau da inganci idan har masu jingina a jikinsa sunyi goyi bayan hakan yaci gaba da tabbatuwa" Maganan ya ajewa sultane wani tunani a ransa,abinda ya sanyashi gyara zamansa sosai,daga inda yake yana sake ganin ka'aba sosai.

"Ka fadamin haisam.....a lokacin da barna ta faru a cikin iyali......wanene?.....sannan kuma ta yaya za'a iya dauko gyaranta tun daga tushe ba tare da gida duka ya samu matsala ba?". Shuru haisam yayi,yana son gane abinda sultane yake fadi.

A zahiri ya fahimta,amma ainihin asalin dalilin tambayar ya shige masa duhu,amma dai koma meye,yana jin zai bashi amsar tambayar daidai da amsartata

"Wani bazai hari tushe da farko ba kai tsaye.....wani zai fara da ganye ne,sanda ganye zai saitu ya gyaru,ko ya kauce daga dogara da ainihin jikin bishiya,dole tushiya ta fidda kanta da kanta". Kai kawai sultane yake jinjinawa,yana jin wata irin gamsuwa a amsar haisam din. Indai haka ne tunanin da yakeyi bai saba ba,indai haka ne mafarkan da yakeyi a kwanakin da bacci ke daukansa a masallacin manzan Allah ya kamata a tabbatar dasu......akwai wani abu a boye.....akwai wani abu a binne da Allah yakeson gwada masa.

Yasha zuwa gurin ba sau daya ba basau biyu ba,amma bai taba kalar mafarkan da yakeyi cikin masallacin ba,kuma duka duka akan mutum biyu kawai,dole a gobe ko jibi ya koma madeena ya samu muhammad dawud.

"Naji dadi da kiran dana maka a yau haisam"

"Nima haka....ina maka fatan sauqaqar al'amuranka,tare da daidaituwar iyalinka".

"Ina maka fatan alkhairi haisam,tare da addu'ar ubangiji ya shiga dukkanin lamuranka baki daya,amincin Allah ya tabbata a gareka"

"Amincin Allah kaima ya tabbata a gareka" Ya amsa yana katse kiran daidai sanda idanunsa ya gane masa omar dake tsaye a gefansa,da alama bai jima da fara wayar ba ya shigo.

"Me yasa ba wanda ya gayamin?" Yayi tambayar kai tsaye ba tare da ya kalli omar na,yana qoqarin cire wayarsa ne kawai daga silent.

"Me yasa sai an gaya maka?" Omar ya maida masa martanin tambayar. A nutse haisam ya daga kansa yana sanya wayarsa da hannunsa duka cikin aljihun trouser dinsa. Dan kafe omar yayi da kallo,yana son gane me yasa omar yace haka?,saidai omar din yaqi bashi dama,yama kauda kanshi ne kawai daga barin kallon idanun haisam,don ya tabbatar ya qyaleshi zai karanta tunaninsa ne fes.

"Saboda nike riqe da al'amuran gidan a halin yanzu......saboda nine waliyyinta" Ya fada da wani irin coolness.

Murmushi omar ya saki shima,yana ajiye wayarsa gefe guda.

"Akwai wani al'amari daban dake tattare da wannan maganar.......amma har yanzu ina ganin baka cancanci sani ba...."

"Omar mana" Ya fada yana tsuke girarsa sosai idanunsa still a kansa. Dukka girarsa biyu omar ya daga,alamun tambayar me kuma nayi?. Numfashi yaja sosai yana harde hannuwansa a qirji

"Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa har sau uku,abinda ya sanya omar daga kansa ya kalleshi. Yayi addu'a sosai gaban Allah,ya yiwa Allah magiya akan ya kawo warwarewar komai,kada Allah ya sanya ya zama silar cutuwar kowanne bawa,gashi tun ba'a je ko ina ba.....wayewar garin yau kawai ya fara ganin warwarewar daya daga cikin abubuwan da bai gamsu kwata kwata da wanzuwarsa a muhallinsa ba.

"Me kakewa hamdala a ciki?"

"Kasan darare nawa na kasa bacci saboda tunanin qulla auren da ban da tabbacin sahihancinsa?....kasan sau nawa na zargi kaina akan bayar da aurenta ga mutumin da bai cancanta ba?".

"Saboda me zaka zargi kanka ne?,bayan baka san wayeshi ba sai daga baya?".

"Amma musulunci ya shardanta yin bincike,me yasa banyi ba?"

"Me yasa mahaifinta baiyi ba shi da yafi ca cancanta yayi hakan?,yayi accepting kawai hankali kwance?"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Amma omar......."

"Haisam......stop blaming your self......ita ta kawoshi tun farko bakai ka kawo mata shi ba.....kayi gyara kawai ta fannin daya ca canta,ka bawa kwanyarka da zuciyarka dama ta fadi maka ra'ayinta.....abinda ya faru ya riga ya faru,gaba ake gyarawa ba baya ba.......Allah ma dai ya sanya bai samu ya shiga gona ba shi angon" Omar yayi maganan yana tsuke girarsa.

Baisan ya zuqi sassanyar iska ba sai da yaji yana fitar da ita a hankali,amma cikin salon miskilancin nan nasa sai kawai ya janye idanunsa daga kan Omar ya juya a hankali yana takawa majestically yana barin gurin...

Da kallo Omar ya bishi,qaramin murmushi yana subuce masa. Yana sane yayi maganan qarshen,yanaso ya tabawa haisam din wani turning point dashi ya gaza tabawa kansa.......yanason bude wani abu da haisam din qarfi da yaji yasa qaton kwado ya datseshi......amma miskilancinsa ya sanya ya hanashi kara ta ko fahimtar komai,saidai duk da haka yadda yabar gurin salin alin ya bawa Omar wani dan qanqanin hope a ranshi.

A ranshi ya yanke ya kamata ya koma cikin gidan,ya kamata ya zamana kusa da komai,don haka kai tsaye ya bawa abdii umarnin shirya komai. Saidai baiko jima ba maher ya qaraso gidan da saqo.

Rubutacciyar wasiqa ce da iya envelope din da wasiqar take ciki kadai zai gaya mata tarin izza sarauta da girmamawar da aka gwadawa shi da aka turawa saqon.

"Abdii.....karbi ka karanta" Yayi maganan sanda yake qoqarin cire agogon hannunsa. Kwanciya yakeso yayi kafin yammacin da zasu koma can gidan. Yanaso yayi wani tunani,yanaso ya fadada nazarinsa.......yanason ta kowacce fuska ya tsara yadda zaiyi wasa da tunanin mammina......yanaso ya sanya mammina ta BAYYANA masha'ar data aikata......ta kuma tone dukkan wani abu mugun aikinka da kanta.....da hannunta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 67*

A nutse yake sauraron saqon,saqo ne daga morsa safiyya na neman ganawa dashi a yau. Saqo ne da aka rubutashi cikin girmamawa da nuna muhimmancin dan adam.

Zuciyarsa yaji tana motsawa,yanayin kalaman matar da yadda take magana kadai yana sake tabbatar masa cewa UWA take a gurinsa. Yanayin maganganunta sak na nanay dinsa,sai ya miqawa abdii hannu,abinda ya alamtawa abdii cewa yanason ya bashi takardar ne,sai ya dora masa takardar yana cewa dasu.

"Ka gaya mata zanzo in sha Allah,kuna iya tafiya,bayan sallar la'asar zamu tafi.....ka fadiwa omar kowa ya duba e-mail dinsa".

"An gama obbo" Abdii ya furta da girmamawa da kuma qauna da yakewa haisam din.

A hankali ya zube idanunsa saman wasiqar. Duk da cewa ta rubutata da yaren hausa ne,amma yanayin zubin rubutun sak na nanay dinsa. Ba qaramin martabawa da girmamawa bace basarake ya zauna ya rubuta maka wasiqa da hannunsa,duk da cewa suna da tarin masu zama su rubuta musu saqon duk da sukeso. Ya sauke idanunsa can qasa gurin sunansa,yanayin data rubuta sunan sak rubutun yaren oromo. Hannu yakai ya shafa kan sunan yana sake zubawa signature dinta idanu,wata irin signature da bayan ya matsanta zurfafa bincike akan ma'anarta sai ya fahimci sunanta ne da sunan nanay dinsa dana safeena cakude guri daya.

Murmushi ya qwace masa saman kyakkyawar fuskar nan ma'abociyar nutsuwa da hasken addini. Ya tuna da nanay dinsa.....wato komai nasu iri daya ne?,daidai da signature dinsu kowacce ta zabi ta tabbatar da sunan junansu akan kowacce alama ta rayuwarta?,duk da an nesantasu da juna?.

Bayajin koda tona asirin mammina shine aikin da zai zame masa na qarshe a rayuwa zai dakata a kansa. A baya ya kwashi watanni uku,cike da matsuwa nason yayi aikinsa ya kammala,amma a yanzu yana jin koda shekara dubu zai wanzu a agadez,koda shekara dubu zaiyi yana jira zai jira din. Bazai gaji ba bazai sare ba,sai ya tabbatar da adalci akan kowa.....saiya shimfida murmushi akan fuskar kowa.

*_INTERMISSION_*

😄😄😄😄

*_Me karatu?......wanne kira kake zaton morsa safiyya ta yiwa haisam?_*

*_Tunaninsu yazo daya tsakanin mammina da morsa safiyya.....saidai manufa ta banbamta_*

*_meye a zuciyar sultane ne?_*

*_MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR (THE SILENT ONE)ya dauki wani alwashi......Ta yaya zaiyi WASA da hankalin wannan BAQAR QADDARAR?_*

"_YANZU SABON SALON WASA ZAI DAUKO......SABON SALON ZUBI......magana ake ta INTELLIGENCE ga kuma EVIL a gefe......MASOYA HUGUMAWA KUZO MUJE ZUWA_💃🏼💃🏼

*MAMMINA*

Haka kawai ta zabi yin shawagi a yau cikin masarautar kamar yadda ta saba a lokuta masu yawa. Irin hakan yana zama wani salo ne a gareta na fahimtar kowa da komai ba tare da yanayinta ya nuna ba. Takanyi noticing yawan adadin baqin dake masarautar ba tare da tayi magana da kowa ba,saidai a yanzun ta sani ba wata baquwar fuska cikin masarautar,don wancan malamin yayi limiting na komai.

Tafisu na biye da ita a hankali sunayin nazarinsu a tare ba tare da wata hira a tsakaninsu. Wannan yanayinne ya sanya kowa ke zaton ba shaquwa ba kuma kyakkyawar mu'amala tsakaninta da tafisu din.

"Ina yaiwata mafarkin Ethiopia......ina yawan afkawa cikin tunaninta koda banso hakan ba,bana jin akwai sauran aminci a nan gurin tafisu,haka zuciyata da jikina suke bani" Murmushi kadan tafisu ta saki tana girgiza kai.

Readers Also Read

More by Huguma