Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 39

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 39

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 39: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 39. "Nafi zaton kwadayin cikar burinki ne yake sakaki a…

3,375 words

"Nafi zaton kwadayin cikar burinki ne yake sakaki a irin wannan yanayin. A nan din uwargijiyata......babu wani abu daya isa ya karya amincin da kike dashi,ba wanda ya isa ya tsallake iyakokin da kika shata......ba wani abu komai girmansa da ya isa ya girgizaki ko ya girgiza darajarki da martabarki. Anya kina da masaniyar irin girma kima da amincin da kike dashi kuwa a zukatan talakawa?". Maganganun tafisu sun shigeta sosai.

"Kin manta cewa ke a yanzun ba halak malak din qasar Ethiopia bace ke?,ke din ba'abzina ce haifaffiya uwa uba da dangi gaba daya?,kin samu wannan shaidar ta hannun mutum mafi girma daraja da kuma aminci irin sultane,kin manta ne?" Tafisu ta sake tuna mata da wani abu daya sake bata relief.

"Kamar isowar tamim nake gani" Tafisu ta furta qasa qasa tana duban gabansu.

"Shine.....gwara daya iso,dama yau ne rana ta qarshe cikin yarjejeniyarmu......mu qarasa can" Mammina ta fadi yana sauya akalarta zuwa wani amintaccen gurin zama daya zama kebantacce garesu kadai da kuma sultane.

Idanunta akan tamim sanda yake takowa da wannan qaqqarfan jikin nasa,tana karantar wani yanayi a tattare dashi da bata saba gani ba.

Cikin girmamawa ya qaraso,ya kuma zube a gabanta kamar yadda ya saba din da tarin girmamawa.

"Bani labarin dukkanin abinda yake tafe dakai.....ba saura jira ko doguwar shimfida" Ta buqata cikin zaquwa da ganin yanayinsa.

Qasa yayi da kansa,yana jin wata fargaba tsakiyar qirjinsa da baisan dalilinta ba.

"Akwai alamun kwancewar wani noti guda daya cikin notikan da muka daure" Kai tsaye ta fahimci inda maganan ta dosa,wani irin abu taji yayi yarrrrr cikin jikinta,tsigar jikinta tayi wani irin zubawa,ta ritsashi da ido sosai.

"Bani bayanin a bude". Zama yayi sosai a qasa yana sake yin qasa da kansa.

"Akwai mutum daya da gilmawarsa ta qaranta cikin hukumar......akwai mutumin da aka dauki wasu satittika da kwanaki ba'a ganshi ba......bacewar motsin daya daga cikin ma'aikata kuwa a wajen yana alamta tafiyarsu izuwa wani muhimmin aiki,bacewar kowa a cikinsu bazai iya zama barazana ba.......amma BACEWARSA shi din babban barazana ne da zai iya tarwatsa KOWA!......An tabbatar min indai shidinne.....to ba shakka SHI KADAI GAYYA NE!!!"

"Dakata!!!!" Mammina ta fada cikin tsawa.

"Daina kurantamin kowanne mutum a gabana,ka manta a gaban wa kake?". Qasa yayi da kansa,haka kawai yana jin wani rashin nutsuwa yana shigarsa.

" A bani tabbacin gurbin da ake tunanin ba kowa da gaske ba kowa din?.....muddin ya sanya qafarsa cikin agadez ne.....muddin ya sanya qafarsa cikin masarautata ne.......saina sanyashi yayi nadamar binciko laifin daya daga cikin mutanena ma ballantana ni da kaina......tabbaci nake buqatar samu da farko tukunna!!.....ka riqe wannan da kyau.....sati daya tak na baku,duk kuwa wahalar da aikin ke dashi,bazan iya jira sama da kwanaki bakwai ba".

"An gama" Tamim ya furta yana miqewa da cikakken karsashin nan nasa yana barin gurin.

Kasa motsawa tayi kwata kwata daga gurin,saita dinga jin wani abu yana shigarta gaba daya me kama da fargaba da razani.

"Bai kamata kiji komai ba,bai kamata ki dinga mantawa da cewa ke ba jinin Ethiopia bace.....bai kamata ki dinga mantawa da al'adar agadez ba game da gwiwar sarki,ke din kina cikin kariyar sultane da alfarmar masarauta HAR ABADA!" . Wadannan kalaman na tafisu su suka suka shiga jikinta da kyau,wadannan kalaman su suka binne tsoron da yaso yayi tasiri a zuciyarta.

*MORSA SAFIYYA*

A nutse take gyara lullubin lafayar dake saman kanta,tana kuma sake duban fuskarta a madubi. Fuskar da wasu lokuta suke tuna mata mutum biyu da har yanzu bata maye gurbinsu ba a rayuwarta duk da tsahon shekarun. SAFEENA DA KHADEEJA.

Motsa qofar da akayi shi ya sanyata waiwayawa. Armelle ce cikin kamalar nan tata.

"Allah ya baki yawan rai,an kammala shirya komai,kuma sunce sheikh yana hanya,amma kuna falaak da hairaan suna buqatar ganinki".

"Ki fadi musu su shigo" Kai armelle ta jinjina ta koma da baya.

A nutse ta koma saman ottoman ta zauna tana fuskantar qofa. Daidai sanda hairaan ke shigowa a gaba falaak na biye da ita a baya,hairaan din riqe da hannun falaak.

Cikin kwanaki qananu falaak din tayi wani fayau da ita,daga jiki har fuska sun nuna ramarta. Sau daya tak momma ta qara ganinta tun wancan ranar,duk da zuciyarta cike take da tausayin autar tata amma ta danne,saboda bata son komai da zai kawo mata cikas a tsarinta da qudurinta har sai ta cimmasa. Ta shirya fuskantar kowa......ta shirya qalubalantar kowa,koda kuwa sultane ne,shi yasa koda nanny batayi maganan komai ba,duk da awannin da suka shafe ita da nanny din suna tattaunawa game da sakin.

"Ina fata ba zuwa kukayi ku batamin lokaci ba" Morsa ta fada tana wani hade rai. Murmurshi kawa hairaan ta saki.

"Inamu ina batawa morsa kuma momma guda rai?....neman afuwa da yafiya kawai mukazo yi" Hairaan ta fadi tana sakin falaak,wadda bata zame ko ina ba sai gaban morsa safiyya.

Sulalewa tayi ta zauna a gabanta tamkar me zaman sallah,muryarta can qasa da wani irin rauni ta soma magana kanta a qasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Momma ki yafemin.....kiyi haquri momma,na gaza ganowa da fahimtar nufinki,duk da cewa nice na miki alqawarin tallafa miki da bada gudunmawata wajen gyara rayuwar yaa biftu,kiyi haquri bisa musun da nayi miki,kiyi haquri kan bata miki ran da nayi.....gaskiya ne da kikace yaa biftu ta fini buqatat sheikh haisam.....da gaske ne momma na yarda da hakan,ni ina iya ganinki,ina iya rabarki naji duminki.....ita kuwa ta rasa hakan,ni ban rasa gatan wanda zai dorani akan hanyar da rayuwata zata inganta ba ta kuma kubuta,amma ita ta rasa wannan.....na SADAUKARWA da yaa biftu sheikh da dukka soyayyar da nake masa,na sadaukar mata momma.....zan kuma goya miki baya ganin komai ya daidaita" Wasu hawaye ne suka taru sosai a idanun morsa safiyya,duk kuma yadda takai ga taresu amma sai hakan ya gagara,don haka ta barsu suka zubo da duminsu gaba daya,suka kuma sauka kan hannuwan falaak dake saman cinyarta,abinda ya sanya falaak din kama hannun morsa din ta saka cikin nata ta runtseshi sosai.

Hannunta ta aza kan falaak a hankali tana dauke hawayen da gefan lafayar jikinta.

"Ba abinda kikayimin falaak,Allah yayi miki albarka.....Allah yayi miki albarka....Allah yayi miki albarka,tabbas ina me yaqini da tabbacin ba zaki tozarta ba,ba shakka Allah sai ya maida miki madadin sheikh haisam,ina miki fatan ya zama a kurkusa ta yadda zuciyarki ba zata cika da kadaici ba,ba kuma zata tagayyara ba,soyayyar da baki hasashen samunta gurin sheik ba alfarmar manzan Allah S A W zaki sameta gurin makwafinsa har sai kinji kamar tayi miki yawa ma,Allah ya cireshi daga zuciyarki kaman yadda yake fidda gashi daga nono,ya mantar dake soyayyarsa ya cikata da qaunar Allah da manzansa dama dukkan wanda zai zama madadinsa" . Qanqame morsa safiyya tayi da kyau,tun daga nan tasan cewa addu'ar UWA ba wasa bace,wani sanyi taji yana ratsa zuciyarta,wata nutsuwa ce taji tana saukar mata,sabanin kwanakin data dauka cikin qunci da jin cewa ba zata iya barwa kowa haisam din ba. Sai hairaan ta matso itama tana cuso kanta a tsakaninsu hawaye fal nata idanun. Morsa safiyya tasan me take nufi,qarin sanya albarka itama take nema,don haka ta saki murmurshi tana shafa kanta itama gami da kwararo mata addu'a. Koda ta kammala bataji ta nutsu ba,hannuwanta ta daga tana yiwa akhnan tata daban,duk da batasan me akeyi bama,amma bata taba daga qafa ba akan mata addu'a,ko ta yiwa yaranta ko batayi musu ba.

(Duk runtsi duk wuya a nemi addu'a da albarkar iyaye,karku yadda kuyi wasa da ita,wata dama ce da idan ta wuce bata dawowa kowa,idan sun rasu ka kyautatawa 'yan uwansu da qawaye da abokansu,hakan zai zama tamkar su ka kyautatawa,haka addini ya koya mana,haka yake a addininance,Wanda suka rasa nasu Allah ya jiqansu da rahama,wadanda kuma suke raye ubangiji ya qara musu lafiya da nisan kwana me amfani).

*HAISAM*

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 68*

*HAISAM*

Qasan ransa yakejin dadi da sassauci na yadda ya samu gidan komai yana tafiya daidai da umarnin da yake bayarwa daga can ainihin gidansa. Wannan girman.....wannan martabar da kowa ke bashi ba abinda ya sauya sai sake qaruwa ma da yayi. Cikin girmamawa da martaba dan adam daya gada daga ainihin jinin OROMIA na asali yake amsa kowa gami da duba matsayar kowa a aiki da yadda kowa ke tsaye akan aikinsa.

Baiyi hanzarin wucewa kai tsaye zuwa sassansa ba,sai ya zabi ya qarasa mintunan da suka rage wajen duban tsaron gidan da sauransu.

Akwai kusan mintuna talatin zuwa arba'in da suka rage kafin cikar lokacin ganawarsa da morsa safiyya din. Yana ankare da lokacin,yana qiyasce yana kuma lissafe. Yana jin wani girmamawa daga qasan zuciyarsa dangane da ita,yana jin bazai qara mata koda minti daya ba cikin mintunan da ya kamata ace sun hadun. Wani girma nata yake ji,yana jinta a matsayin nanay kamar yadda musulunci ya shimfida cewa qanwar uwa itama uwa ce. Qanwar uwar ma irin morsa safiyya din,daya tabbatar rayuwarta na zagaye da wasu tarin qalubale,bai sani ba itama ta sani?,ko bata sani ba?,ta fahimta ko nata fahimta ba.

Maleek yana daga gefansa yake ci gaba da duba gidan,ya maida idanunsa kan maleek a hankali.

"Kowanne gidan sarauta ya banbamta da waninsa,saidai akwai gidan sarautar dake binne da tarin sirrika masu nauyin gaske dake dilmiyar dashi sannu a hankali har zuwa wani mataki" Kai maleek ya jinjin a hankali,duk da hankalinsa ma yayi nisa gurin tunani da fatan inama ace zai samu ganin falaak koda daga nesa ne.

Basu kai ga cewa komai ba muryar ta soma tashi,cikin daga murya da rikici yake fadin.

"Ya tsinke haadi....daya daga cikin dawakan ne......bansan me ya sameshi haka ba.....na kasa sarrafashi" Akayi maganar da yanayin daya ja hankalin haisam. A nutse ya dubi sashen da maganar ke fitowa,bargar dawakai ce dake wani kebantaccen guri a gidan. Yasan da ita,amma baisan mallakar waye ba,bai kuma taba shiga gurin ba duk da yadda yake mararin hawan doki,musamman dadewar da yayi bai hau ba a yanzu.

A jininsa yake,yana jin wani iri idan yaga dawakai ko raquma,wani lokacin har cikin kansa saboda tsananin sabo da rayuwa a cikinsu,suna tuna masa da nasa dawakan daya tabbatar zuwa yanzu sosai sunyi kewarsa suma.

Maleek ya waiwaya a hankali shima yana maida hankalinsa sashen da maganan ke fitowa,sannan a nutse ya dubi haisam.

"Kamar fa akwai matsala.....inajin kamar akwai dokin da ya balle.....ina kyautata zaton loosing control ñasa sukayi". A nutse haisam din ya dubi maleek,sai kuma ya zare dubansa daga kansa yana maidawa qofar shigar bargar,ya fara takawa a hankali yana nufar gurin,abinda ya alamtawa maleek shiga zaiyi,miskilancinnan nasu na cikin jini ne kawai bazai barshi ya furta da baki ba.

*AKHNAN*

Zuwa yanzu idan tace ba komai cikin 'ya'yan hanjinta ta tabbatar batayi qarya ba. Ta manta a daidai wanne lokaci......ta kuma manta wanne abinci ne na qarshe daya shiga cikinta cikin salama.

A wannan yammacinne kawai data gama tabbatarwa gami da amannar ba zata rayu ba tare da abinci ba ta amince ta karbi zazzafan ruwan tea din da birra keta mata nacin ta karba tasha din.

Sanye yake da wata cotton gown ta wani irin tattausan material fari qal wanda aka yiwa adon gold d'aid'aiku a jiki. Hade yake da hularsa da kuma yalwataccen cotton din mayafin da tunda birra ta ware mata kayan batabi ta kansa ba. A yau ko hula bata sanyawa sassalkan gashin kanta ba,ta sakeshi ne kawai yana kwance a bayanta wanda tsahonsa yayi kusa da mazaunanta. Abune me wahalan gaske ka samu gashinta a cukurkude ko a yamutse,ko a yanzun ma da take cikin wani irin mode da batasan sunan da zata bashi ba,gashin a kwance yake a gadon bayanta da wani irin glowing da darkness dake nuna kulawar da yake samu,saidai daga gaban kanta yadan tashi kadan,tashin da bai hana kwantacciyar sumar data kwanta daga goshinta har gefunan kunnuwanta bayyana ba.

Fuskarta tayi wani irin haske,tayi fresh sosai,blue eyes dinta haskensa ya sake fitowa qwarai. Kana iya ganin yadda labbanta suka sake sirancewa,labban da basa rabo da kyakkyawan lip gloss ko lip balm.

Wani irin zurfi tayi a tunani,har yanzu tana jin emptiness dinnan a zuciyarta dama rayuwarta gaba daya,har yanzu zuciyarta ta kasa miqa wuya dari bisa dari akan cewa bada taimakon mammina ta tsinci kanta a hali mafi muni da tozarci a tarihin masarautar agadez dana family dinta ba.

Bata zargin mammina da cutar da ita......amma tana zarginta da gaza maida hankali ta zaba mata CANCANTACCE da zata rayu kalar rayuwar da mamminan tasan ta jima tana mafarki,kalar rayuwar da tasan ta jima tana mararinta,RAYUWAR 'YANCI BA QARQASHIN DOKA KO UMARNIN KOWANNE D'A NAMIJI BA.

"Ranki ya dade......akwai matsala....." Taji muryar bushira daga bayanta,abinda ya sanyata waigowa da sauri tana dubanta,zuciyarta kuma na cike da fata da kuma neman tsarin sake jin wani abu da zai kassara farincikin da taketa tattalin dawowa dashi.

Da idanu ta tambayi bushiran,wani yare da sun jima da saba magana dashi da ita da kuma haddaceshi,don haka ba tare da jinkiri ba ta amsa mata.

"Thunder ne ya tsinke.....yace ko zaki iya wani abu akai?,dukka dabarunsu ya qare". Bata tsaya sauraren sauran maganar bushira ba ta dire cup din dake saman d'an plate din da take zuqar coffee din a gaggauce,ta soma baro harabar dake liqe da dakin hutawar tata tana shigowa ciki da wannan zazzaqar siririyar muryartata take bawa bushiran umarni.

"Bani mayafi". Da hanzari bushiran ta dauko mata tana yafa mata,gami da saita mata lausasan takalmanta.

Bata wani damu da boyon kanta da takeyi na kwana da kwanaki ba,kamar yadda bata damu da gaisuwa da kuma kallon da hadimai keta binta dashi ba. Wasunsu kallo ne na gulma da munafunci,ta fito a yau din bayan kwanakin data shafe ba wanda yaga koda qyallin idanunta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Hankalinta sosai yana kan dokin,doki ne matuqar tsada da sultane ya sanya zunzurutun kudade na qasar dubai ya siyo mata shi,ya siyo mata shine kawai a matsayin kyautar kammala degree dinta,ta kuma fita da kalar sakamakon da sultane din yake buri,harma sama da yadda yake hasashe. Takanas tasa aka dawo dashi agadez tun a wancan abun daya faru a hippodrome,tasa ake bashi kyakkyawar kulawa,sai ta qara saurin tafiyarta wanda duka duka baifi takun tafiyar wata macen tafiya ta al'ada ba......bata soma jin nutsuwa ba sai data kawo bakin gurin ta kuma sanya kai kai tsaye ba tare data tsaya sauraren jawabin hadimin data samu a tsaye bakin gurin ba.

Tun daga nesa idanunta suka sauka a kansu,yana zaune saman bayan thunder din,saidai yayi kaman rub da ciki ya riqeshi da kyau. Sukuwa yake faman yi tare da qoqarin kayar dashi,amma cikin wata irin qwarewa yaqi bashi wannan damar. Magana yake masa da dan qarfin da zaka iya jiyowa tamkar yana magana da dan adam. Da dukka jarumtarsa ya sake rungume gadon bayan thunder din da yayi wata irin haniniya yana daga qafafunsa na gaba,abinda sukasan tabbas idan ba gwanin sarrafa doki ba ba abinda zai hana mutum faduwa qasa war was a gurin.

Idanunta ta lumshe,tana jin wata irin matsananciyar faduwar gaba,tana hango yadda thunder zai watsar dashi ya kuma tattakashi yabi ta kanshi ne kawai. Faduwa a doki wani mummunan abune da bata qaunar kalla,saidai kuma yadda taji gurin ya fara nutsuwa ya sanyata bude idanunta a hankali. Ga mamakinta thunder ya fara nutsuwa,still bai sauka a kansa ba yana ci gaba da shafashi a hankali gami da yin magana qasa qasa dashi,har zuwa sanda ya tsaya cak ya daina bige bigen da yakeyi,sai yayi wani tsallae tana direwa a qasa daga bayan thunder din.

Sosai ya qarewa dokin kallo bayan ya samu nasarar maidashi nutsuwarsa. Ya aza hannunsa gadon bayansa yana sake shafashi a hankali,abinda ya sake bawa dokin nutsuwa sosai,sannan yaja akalarsa zuwa gefe,ya kuma tsugunnar dshi,cikin ladabi yayi biyayya ya tsugunna saman qafafun nasa,sai shima ya tsugunna daga daya side din yana ci gaba da magana dashi,maganan da ba wanda yasan me yake fadi.

Idanunta ta ware sosai,tana jin wani irin kishi yana saukar mata. Don me zai sarrafa mata doki bayan bata da tabbacin iya komai a tare dashi?,meye hadinsa ma da doki?,tunda ba magana ake ta takarda ko bada karatu ba?. Batason yayi mata komai da yayi kama da taimako tallafawa ko dafawa,da wannan tunanin nata ta fara takawa zuwa inda ya tsugunnar da dokin.

Bai lura da ita ba sam,cikin sassanyan sautinnan nasa maras amo yake ci gaba da karantawa thunder wasu ayiyo na qur'ani. Yayi relaxing sosai tamkar me fahimtar ma'anonin ayoyin.

Ta daya bangaren thunder din ta tsugunna,tana qanqance idanunta. Zataso ko sau daya ya kalleta don ta karanta masa a karance cewa din bashi da hurumi akan komai nata,saidai baiyi hakan ba,don baikai qarshen ayar da yake karantawa ba,wadda sautin ya fara shiga zuciyarta a hankali yana saukar da wani yanayi,saita janye dubanta daga kallon mutumin da ko sau daya bai daga idanunshi a kanta ba,ta soma shafa fuskar dokin.

Shafar fuskar tasa ya sanyashi yin wani qaqqarfan yunquri kamar zai tashi,abinda.ya sanyasu dukkaninsu miqewa da hanzari da niyyar riqe akalarsa,lokaci guda.....cikin sakanni guda,abinda yayi sanadiyyar haduwarsu gaban fuskar dokin.

Haduwa hannuwansu sukayi guri guda,kowanne ya janye da wani irin sauri. Lokaci guda dukkaninsu suka daga kai. Idanunsu ne suka gauraya dana juna,wani irin zuzzurfan kallo suka sakarwa junansu,iskar dake kai kawo a gurin tana kada sassanyan qamshin da ya kama jikin kowannensu. Musamman nasa scent din,wannan unique turaren da shi daya ya mallaki irin qamshin a duniya.

Hasken ranar da yayi saura a sassanyan yammacin dake sake hada wani irin nau'in hadari ya haske fuskar nan tata,fuskar data mallaki wata irin kwantacciyar fata kaman da madara take wanka.

A nutse ya janye idanunsa daga kanta yana mamakin samun blue eyes a yankain africa a tattare da wata mace har haka. Launin idanun da suka jima suna bashi mamaki kafin a hankali su juye su soma burgeshi tun daga sanda ya fara mallakar hankalin kansa. Nata idanun sunyi wani irin dacewa da zara zara eye lashes dinta,da kuma gewayayyar fuskarta dake dauke da kwantaccen gashin gaban yalwataccen goshinta.

Wani abu ya taba zuciyarsa,sai ya samu kansa da tuhumar kansa da kansa da ganin baikensa na qare ma fuskarta kallo.ya sunkuya a hankali yana daukar akalar thunder dake zube a qasa,abinda ya sanya akhnan din ja da baya a hankali.

Idanunta ta sake lumshewa tana sake budesu lokaci daya sanda ya sake zaunar da thunder sosai. Ta budesu fes a kansa,ta tsani duk wani mutum da zataji yayi mata kwarjini......ta tsani wani mutum ya fits kwarjini,ba'a taba samu ba tsahon rayuwarta tsakanin mutanen da duk suke kewaye da ita,sai yanxu?,bama kuma akan kowa ba akan wani malami can?.

Iska ta zuqa sosai don daidaita nutsuwarta da hankalinta da takejin kamar tana shirin daburcewa daga sanda kallon cikin idanunsa ya zame mata wani abu na kusa kusa da tayi a yau din. Idanun da cikin mafarkinta kadai take ganin irinsu,......idanun da take tsammanin su ta gani a hippodrome,yau gasu kusa da ita ainun,kusancin da baifi banbamcin d'ani biyar ba. Kwarjinin da take hanga a nesa a kusa ya ninka wannan.......idanun sun zame mata alaqaqai din rayuwa da a yanzun cikin qasa da second ashirin na gaurayar idanunsu waje daya ta soma tunanin anya ba sihiri gareshi ba?.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 69*

Readers Also Read

More by Huguma