L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 40
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 40: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 40. Ba wani ido daya taba hanata furta bacin ranta koda…
3,306 words
Ba wani ido daya taba hanata furta bacin ranta koda kuwa idanun mammina ne.....mamminan dake da girma da kima a rayuwarta,amma a yau da kallo daya da yayi mata ya shafe duk wani tunaninta na abinda ya kamata ta fada masa,na sanya masa iyakoki da tsaidashi daga shiga hurumin da ya shafeta. Da kallo guda daya tak taji ya saka mata wani irin fargaba da rudewar da batasan dalilinta ba.......da wannan kallon guda daya ta daina shaqar kowacce iska saita wannan mayataccen qamshin da har yau bata gaji da neman wanne nau'in turare bane haka?.
A nutse ya miqe,miqewar data sanya idanunta sauka kan qafafunsa duk da yadda take qoqarin yiwa qwayoyin idanunta control. Kai tsaye suka fada kan takalmin dake sanye cikin doguwar qafarsa. Fes take fara sol kamar bai taba taka qasa a duniya ba,yayin da baqin takalmin da aka saqashi da magi daukakar darajar fata ta dace matuqa da gaske da qafar tasa.
Karon farko wani abu ya fusgi hankalinta,ta zubawa takalman idanu sosai sanda yake matsawa baya da baya a hankali yana barin jikin dokin.
Crown half shoe ne na kamfanin Dolce and Gabbana.......irin takalmin sultane sak,takalmin da aka taba bawa sultane din kyautarsa don nuna girmamawa daga sarkin tahoua. A lokacin suna tare da sultane din,tana zaune a farfajiyarsa yana duba kayan,kurkusa lokacin da take a matsayin aminiyar sultane din,ba yanzu da komai ya sauya ba.
Takalmin ya burgeta sosai a sannan,don har sultane yana cewa.
"Inda namiji ce ke da na bar miki shi kadeejatou" Tayi murmushi sosai a sannan,ta kuma dauki wayarta tayi qiyasin adadin kudinsa. Kanta ya kwance sosai da zallar kudin da aka buga mata lissafi da CFA din qasarsu.
Idanunta take ta qoqarin zarewa,ko kuma qaryata asalin takalmin shine a qafarsa. Sam takalmin bai dace da malami ba......takalmine dake bayyana zallar kuma tsantsar mulki da iko ga duk wanda ya mallakeshi,anya ba takalmin sultane dinne ba?,idan har haka ya kasance kenan baya ga shigar sauri da yakewa sultane da dukka al'amuransa har ya fara shiga taskokinsa?. Idan hakane gaba me zai faru?,anya bazai shiga sahun mutanen da suke zuwa a madadin baqi ba amma daga baya su qwace sarauta daga anihin wanda sarautar ke hannunsu ba.
"Da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa" Yayi maganar hankali kwance yana sakin akalar dokin. Blue eyes dinta ta dauke daga saman takalmin tana maidawa kansa,daidai lokacin da ya juya baya,bata iya hangen fuskarsa sai kwanctacciyar baqar sumar da take kwance a qeyarsa zuwa dokin wuyansa kadan,shigen yadda asalin matasan samarin BUZAYE 'yan qabilarta suke.
Wani irin taku da take iya hangen zallar izza a tattare dashi,izzar da har yanzu take qalubalantarsa akan yinta,izzar da takejin bai cancanceta ba.....izzar da take alaqantata da tsananin girman kai ne kawai irin nashi,tare dakai kanshi inda bai baije ba.
Wani abu ya mata tsaye a wuya sanda take jinsa yana magana da hadiman gurin.
"Koda dabba ne sai Allah ya tambayeku yadda kukayi kiwonta kuka kula da damuwarta,kada kuyi tunanin idan akwai zalunci gurin kula dashi Allah bazai muku hisabi akai ba,don haka ku kula" Yadda dukkaninsu suka rusunar dakai cikin girmamawa ya sake tunzurata qwarai. Me yasa yana bare zai shigo masarautarsu ne har ya dinga iko mulki da kuma izza?.....don me sultane zai bar masa riqon babbar masarauta kaman masarautar agadez?,bayan shi din baqone akan komai ma. Hasalima baisan me ake kira da sarauta ba,meye hadinsa da ita?,sunyi hannun riga ta kowacce fuska. A yanzun tsakanin ita dashi batasan waye magajin SULTANE OF AGADEZ ba. Tana hangen wani girmamawa da dukka hadimai ke.masa,har tayi kunnen doki da irin girmamawar da suke mata.
Wannan bacin ran shi ya sanyata yin abinda bata taba yi ba wato kiran bawa da kanta. Yana dab da fita daga gurin yaji sautin kiran,karon farko da shima yaji bayyanar muryarta a fili irin haka,sai yaja numfashi sosai ya fesar dashi yana lumshe idanunsa gami da budesa duka lokaci guda.
Kadan kadan yakejin magananta cikin fada,kalma daya tak ya iya jiyowa.
"Akwai wani dama dana bayar na kowa ma zai iya shigarmin barga da duba dawakaina bayan ku?". Idanunsa ya lumshe a hankali yana maida hankalinsa ga maleek dake tattauna matsalolin daya hanga tattare da dokin,can qasan zuciyarsa kuma tana sake cika da mamakin tsananin girman kan dake damunta. Bai cewa maleek komai ba,har zuwa sanda shi da kansa ya sauya topic din.
Ita kanta batasan dalili guda daya da ya sanya taketa zabga fadan ba. Saita dinga jin kamar ba ita ba,kamar an canzata sanda ta baro bargar tana takowa gami da komawa sassanta. Yanayin girman kansa da izzarsa ke sake bata mata rai. Yana da wani dabi'a data lura da ita,basarwa tare da attitude na I don't care. Komai ma yana nuna bai gabansa bai dameshi ba,abinda take gani a matsayin zallar wulaqanci da kuma girman kai.
wadannan idanun suka sake gilmawa ta tsananin hijabin tunaninta,taja siririn tsaki yana qoqarin kauda tunanin gefe. Abu daya ta sani tabbas koda ba shine mutumin hippodrome ba.....komai nasu yazo da tarin tsananin kamanni,mutumin da har yanzu yaqi barin cikin baccinta,a wannan karon tana jin zata saka kudo ko nawa ne don binkito gaskiyar WAYE SHI?.
"Ranki ya dade.....mammina ta aiko tana son ganinki......"
"Bana sha'awar ganawa da kowa......" Ta amsawa birra a taqaice wadda ta karbo saqon daga hannun yalwa. Ko d'ar bataji ba soma takawa zuwa balcony dinta. Har qasan ranta tana jin wani zafi zafi na mammina.....tana kuma son nuna mata taji radadin da bata taba ji ba a tsahon rayuwarta don ta fahimci cewa ta bata mata da gasken gaske. Ta bata mata martabarta tarihinta da GIRMANTA da taketa fama riritawa,sai takai hannunta a hankali da zummar jawo mayafin kanta dake shirin sauka,nan take hancinta ya shaqi wannan daddan qamshin da duk sanda zata shaqeshi yake haifar mata da faduwar gaba.
Sake kai hannun nata tayi hancinta da sauri,sosai qamshin ya shige mata qofofin hancinta yana ratsawa a hankali yana isa ga kwanyarta dama zuciyarta gaba daya.
Dakatawa tayi da tafiyar a hankali,sunan barratu ta kira,ta qaraso a hanzarce,saita miqa mata hannunta kawai. Ta fahimci me take nufi,ta matso a hankali cikin d'ar d'ar takai hancinta ta shanshana.
"Inaso ki nemo contact na kamfanin YASMEEN.....shine kawai company din daya rage bamu yiwa magana ba akan turaren nan ba haka ne?" Kai ta girgiza cikin girmamawa.
"Haka ne ranki ya dade".
"A siffanta musu shi,ina buqatar wannan qamshin.....indai suna dashi su fadi price din da zasu siyar dashi,ni kuma zam biya ko nawa ne.....idan ma babu,muddin sun shirya samar dashi,su fadi abinda suke buqatar a basu" Ta qarasa maganar tana wucewa ciki ba tare data tsaya ko waiwaye ba.
_Hmmm,nikam akhnan me zakiyi da wannan tsadadden scent da kika qwallafa rai haka a kanshi,anya?🫣🫣....muje dai zuwa_
*MORSA SAFIYYA*
Tun daga farkon sashenta yasan akwai banbamci me tarin yawa a tattare da komai ma,abinda yake bayyana masa akwai wani abu daban da yasha banbam dana sauran sassan gidan. Kowa a nutse,cikin kuma doka da order,kowa kuma cikin tsari yake a tsaye akan nasa aikin. Sam ba maza kusa da mata,hakanan basu kusa da ainihin ginin gidan,kamar yadda ba mata kusa da inda maza suke nasu ayyukan. Surutacciyar shiga dake bayyana nutsuwa kamun kai da kiyaye doka gami da kiyaye dokokin musulunci.
Mewada ne yayi masa jagora cikin tarin girmamawa har zuwa sanda ya isa gurin da morsa safiyya take jiransa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tunda ya doso gurin ta miqe don nuna girmamawa a gareshi,ya sauke dubansa qasa yana jin kaman ta aza masa nauyi. A qa'ida UWA take a gareshi,wani irin yanayi me kama da na nanay dinsa yake hanga sosai tattare da ita. Yadda ta tsaya tana jiran isowarsa da tarin girmamawa. Yadda tayi tsaye fuskarta a washe da wani yanayi da baiyi kama da murmushi ba.....amma yafi murmushi fidda nutsuwa saman fuska gami da nuna halin girma da dattako.
Da cikakkiyar sallama ya qaraso gurin,ta amsa masa tana furta.
"Ga guri ka zauna muhammad" Yadda ta ambaci sunan sai yaji fitar sautinta sak na nanay dinsa. Sai a sannan yake tuna me yasa lokuta da dama idan tayi magana yakejin girman maganarta,idan tayi magana yakejin kamar ya santa a wani guri?.
A nutse ya zauna,itama saita koma ta zauna tana karantarsa a hankali.
"Tubarakarrahman......ma sha Allah" Ta fadi can qasan ranta. Bataga lafin falaak ba data fadaawa wannan character din ba.....wannan nutsuwar.....wannan kamalar......wannan kamun kan.....uwa uba wani kebantaccen kyau da kuma gayu daya sake yiwa kyan ado da sake bayyanashi.
"Na gode sosai da amsa kirana da kayi akan lokaci" Ta fada tana dan duban agogonta a sace. Baiko qara minti guda tak ba daga lokaci da ta sanya na zamansu,abinda ya sake sanya wata kimarsa da darajarsa qaruwa ainun cikin ranta da idanunta.
Miskilin murmushinnan me wahalar fahimta ta saki yana gyara hannun jubah dinsa.
"Babu buqatar godiya,cancanta ya sanya nazo". Ya fadi kansa tsaye fuskarsa a sake yana jin kamar yana gaban nanay. Murmushi tayi kadan daya nuna masa wani digon baqi daga qasan hancinta sak irin nanay dinsa,abinda ya sake saka zuciyarsa harbawa da sake samun tabbaci da gamsuwa,saiya zare idanunsa sanda take fadin.
"Akwai magana me muhimmancin da duk duniya kai daya ya cancanta nayita da kai.....ta daya hannun kuma ALFARMA ce zan roqeka kayimin......wadda alfarmar zata shafi rayuka masu yawan gaske.....rayukan rayayyu harda na matattu". Shi din wani bangarene na tunani.....kuma shi din an haifeshi ne don ya karanta tunani yayi wasa dashi,don haka daga fitar lafazin kadai daga bakinta ya bude masa wani fage ya buda masa kuma wata hanyar me fadin gaske.
"Zan iya gabatar da dukka maganganu na?" A nutse ya daga kanshi.
"Nazo nan ne saboda kinyi kirana,so kiyi dukka maganganunki kai tsaye"
"Na gode" Ta fadi. Sai kuma tayi qasa da idanunta gaba daya zuwa ga barin kallonsa,zuciyarta taji tana mata wani irin nauyi gami da matsewa a qirjinta. Ta sani a yau zata buda maganganun da suke da tsauri a rayuwarta zuwa ga mutumin da yake bare,saidai batasan me yasa ta gaza jinsa a mazaunin bare ba,zuciyarta ta kasa amsar haka,duk sanda zai zama a kusa da ita tamkar dai sultane,tana jinta kamar tana gaban D'ANTA tana jinta tamkar tana gaban hairaan ko falaak ne.
"Akwai maganganun da me yiwuwa basu shafeka ba.....amma ya zama tilas na shaida maka,saboda qila wannan shine zai zama mabudin da zama fahimci muhimmancin ALFARMAR da zaka yi mana,ka kuma fahimci ma'anar neman ALFARMA a tare da kai" Takai qarshen maganar tana maido idanunta akan haisam din da yayi shuru yana saurarenta. Baice komai ba har zuwa yanzun,sai ta fahimci dama ya bata tayi magana yadda takeso kamar yadda ya fadi da farko.
*"Sunana SAFIYYA YUNNUS JALLATA"* Ta fada da wani yanayi da ya tilastawa haisam daga idanunsa ya zubesu fes a kanta.
Shikenan ta tabbata,ta tabbata wannan din Obboleettii Lamaan(twin sister) din nanay dinsa ce......dukkan wani tantama ko kowanto yakau. Jinin nanay dinsa ne zaune a gabansa,jinin da aketa kewa.....jinin dake damfare da zuciyar Nanay dinsa tsahon shekaru,jinin da har yau ba'a dains kewarsa ba......ba'a daina mararinsa ba YUNNUS JALLATA sunan daya sake amsa kuwa cikin kunnuwansa kafin sautin morsa safiyya yaci gaba.
"Yar asalin qasar Ethiopia,saidai bazan iya gaya maka daga ahalin dana fito ba" Ta sake fadi tana girgiza kai a hankali. A nutse ya sake dubanta,yana son tunawa da hango abinda ya sanya wani d'aci cikin amonta da yanayinta harma da cikin idanunta.
"Ba wannan bane me muhimmancin........SAFEENATA" ta furta tana yin qasa da kanta,wanda idan har haisam ya gani daidai hawaye ne suka shammaceta suka sulmiyo mata. Har cikin jininsa yakejin saukar da digar hawayen,wani abu me qarfi ya motsa cikin jikinsa. Duk da batace komai ba amma tunaninsa hasashensa masaniyarsa dama jikinsa gaba daya suna gaya masa sunan MAMMINA/ZAITUNA.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 70*
"KHADEEJA ta zama wani sashe na rayuwa da zuciyata da har yanzu ban fidda ran ganawarmu ba.....duk da mutuwa ta raba tsakaninta da safeena kamar yadda ta rabata dani......mun tashi tamkar 'yan ukkun da ko bacci baya rabamu duk da mun fito daga mabanbantan uwaye......har zuwa sanda qaddara ta fara aurar da khadeeja......sannan tazo ta aurar da safeena ga hannun da bata cancanci rayuwa dashi ba.....bisa tilastawar mahaifinta. Idan nace maka SAFEENA duk cikin mu ukun nan ta fimu haquri zurfin ciki da hangen nesa kada ka qaryata,kada kuma kayi mamaki. Tun kafin ta shiga gidan mijin farkonta take ganin alamomin da suke gaya mata lallai ba za'a zauna lafiya ba daga matarsa ta biyu. Matar da take ganin ta aureshi ba bisa cancanta ba,don kyanta yafi qarfin ajinsa......amma ana kyautata zaton auren mazaje masu kudi bata maidashi a bakin komai ba shi yasa ta shiga gidan. Saidai duk gidan data shiga bata taba yarda a sake auro wata bayan ita,muddin zaka aureta.....saidai ta zama ita daya ce a wajen miji. Ba kasafai ta fiya yadda ta taras ba bare a auro mata,saidai a gidan AJANI gaba daya wannan tsarin nata ya karye. Qabilarsu suna da wani irin hadari,matsafa ne na gaske masu ta'ammali da asiri cikin qabilun Ethiopia........amma duk da haka bata samu nasarar fidda uwar gidan ajani ba,haka ta shiga da wannan haushin,bayan lokaci kadan ko amarci bata gama ci ba ajani ya hangi safeena ya qwallafa rai ya hannun MAHAIFINTA. Tun kafin ta shiga akaso maidata mahaukaciya......gane gane ta dinga yi muraran,amma ko ni bata gayawa ba bare falmaga mahaifiyata data zama itace UWARTA don ita ta riqeta tun tana da watanni a duniya. A haka safeena ta shiga gidan,ta samu tsananin soyayyar mijinta kamar bai taba son wannan matar tasa ba......ta samu wani irin tattali da kulawa da kuma soyayya.......saboda sauqin kanta,tsananin haquri,iya kula da miji miqa wuya da sadaukarwa. Kome ya fada ta zauna,wannna ya sake haukata soyayyarta cikin zuciyar ajani,ya zamana hatta da abokansa ba wanda baisan da zaman safeena ba. Zaman shekara daya kawai sukayi,amma duk wanda yasan ajani yasan safeena a bakinsa,dukkan nutsuwarsa ta duniya itace,zamansa safeena tashinsa safeena. Wannan bai daga hankalin uwar gidansa ba,don sosai safeena ke binta sau da qafa dayi mata biyayya,sannan matarsa ta biyu tafi tsaye mata a wuya,saboda izgilanci.....girman kai gadara da ganin ta isa da take dashi,ba launin wulaqanci da qasqancin da uwargidansa bata gani ba lokacin shigowar ZEENATU gidan......." Sunan data furta din ya sake sanyashi daga idanu ya dubeta. Fuskarta ta fara sauyawa daga wani mataki zuwa wani matakin.....matakin dake sake bashi tabbacin magana ce me nauyi a zuciya da bakinta.
"Shekar daya safeena ta dawo da tsohon ciki gida,da kuma shaidar saki uku lokacin da muke zaman makokin mahaifina.......baiyi arba'in ba safeena ta fara naquda,ta kuma haihu cikin daya daga cikin asibitocin dake daura damu.....saidai wani abun mamaki shine,sama ko qasa aka rasa jaririn da safeena ta haifa. A lokacin tabbas inda mahaifina yana raye,lallai na tabbata zai tsaya yayi shari'a akan case din,amma sai safeena tace abarwa Allah tunda anyi dukkan iya bincike akan neman yaron da yadda akayi ya bace amma ba'a samu komai ba.....ni da falmata da khadeeja dukka mun fusata,muna ganin donme zata fadi haka?,saidai daga bisani ni da falmata muka fahimci wani mummunan aikene na saqo aka yiwa safeena.......yatsa daya na jaririnta aka aiko mata dashi daga inda dukkanmu bamusan ina bane......ana kuma shaida mata cewa muddin taci gaba da tada zancan neman abinda ta haifa nan gaba kadan kanshi za'a aiko mata dashi sukutum da guda. Wani irin mummunan tashin hankali muka shiga,baci ba sha,ga tsoro na bayyanar zancan,don sosai safeena ke kuka da roqonmu nida falmata kada mu fadawa kowa,tanaso yaronta ya rayu don sun bata tabbacin haka,ana tsaka da wannan saiga wani saqon. Gargadinta akeyi da shaidawa mutum biyu da tayi wato ni da falmata......ana kuma umartarmu da mu tattara komai namu nan da kwanaki uku mubar qasar......wannan shine zai bawa jaririnta 'yancin ya rayu,idan ba haka ba kuwa.......tabbas a asubahin kwana na ukun,ta duba randunan ruwa dake bayan masallacin kusa da masarauta ta cire gawar jaririnta,koda wasa kuma muka sake waiwayar qasar ba jaririn kadai ba.....har uwar jaririn za'a rasata. Naso mu tsaya mu tunkari koma waye.....naso mu fuskanci ko waye,saidai banason rasa safeena.....kamar yadda safeena batason rasa jaririnta wannan ya sanya mukayi baton dabon da har yanzu ba'a sake ganinmu......bisa zato da tsammanin mun tserewa matsala......saidai inaa....." Ta fada tana sauke wani numfashi.
"Zeenatu ta biyo mu har zuwa agadez.......ta wacce hanya ce?,ta wanne dalili?......mutuwar ajani........ta kuma biyo sahun babban abokin da ajani baida kamarsa. Zuwan nata ya sanya na fahimci wannan zeenatu da hannunta faruwar wannan abun daya sami safeenata,amma bani da shaida ko tabbacin cewa itadin ta aikata gaba daya. Wata sabuwar babin qaddarar ce ta budewa safeena.......safeena din da sultane muhammad hammud ya soma gani a wani taron bikin al'ada da buzaye ke gabatarwa duk shekara Festival de l’Aïr. Wani irin bikine dake hada manyan mutane da sarakuna. Yada safeena ya qwallafa rai a kanta.....a sannan kuma abinda bamu sani ba zeenatu ta jawo zuciyar sultane,kafin ajani ya aureta da sultane suka fara soyayya,tayi mutuwar sonshi kamar me......amma da ajani ya nuna yana da ra'ayi sai sultane din ya barwa ajani din ita. Abun yazo mata da ciwo,ta haqura ta karbi ajani ne saboda binciken da mahaifin sultane dake raye a sannan yayi. Ya bashi tabbacin zeenatu ba matar aurensa bane.....don a sannan ya samu labarin aure auren data dinga yi. Sultane baya musu wa mahaifinsa,ya sallamawa ajani ita,sai kuma daga baya ta sake dawowa sultane a karo na biyu. Saidai ni na sani.....dawowar zeenatu a karo na biyu yasha banban da niyyarta na farko......bayan soyayya akwai wani lullubabben sirri.......wanda bincike na da Idanun dubana suke bani akwai wani abu da takeson sani na ajani,wanda ga sultane kawai zata samu amsarsa.....". Sosai maganan morsa safiyya ta sauka samam zuciyar haisam,ya lumshe idanunsa a hankali yana daidaita maganganun gami da jinjinawa kaifin basirar morsa safiyya,koda yake duka ahalin tsohon sarki yunnus JALLATA ba wanda yake koma baya gurin JARUMTA da KAIFIN BASIRA. Da gaske ne zaituna kuma zeenatu ta biyo sanin sirrin mafi girma dukiyar ajani da kuma makullin ragowar taskarsa,saidai ya raba qafa kenam?......tana harin mahaifinsa motii aba jifar daya zama amini na biyu a gurinsa......tana kuma harin SULTANE? Sai ya jinjina kansa wani boyayyen murmushi yana subuce masa. Lallai da gaske sai yayi wasa da hankalin matar nan,irin wasan da baa taba mata irinsa ba......saiya sanyata da kanta da kanta ta tonawa kanta ASIRI.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Daga sanda ta sake gane cewa safeena ce matar da sultane ke mutuwar so.....wanda shi kuma ya sota ne ba tare da yasan ma cewar matar abokinsa bace......a sannan ta sake tsananta wani kalar tsana da qiyayya a kanta. Tabi duk wata hanya don raba abun.....ni kuma naqi bata wannan damar ta cimma nasara akan hakan. Daga sanda nima na karanci ta sake shigowa rayuwar SAFEENA ta daga sannna ban sake bacci da idanu biyu ba. Safeena tana da sanyi tana da raunin dana tabbatar cikin ruwan sanyi zeenatu zataci galaba a kanta. Daga qarshe zeenatu ta bari ko ince qaddara tafi qarfinta an daura auren safeena da sultane a matsayin matarsa ta farko......saidai bata bari safeena ta tare ba,har sai daka daura nata auren ta kuma tare a gidan sultane da shekara guda cur......sannan tsananin addu'ar da family din diory hammani suka tsaya akai safeena ta shiga gidansa bayan zeenatu ta tabbatar ta gama kafawa ta tsare,ta kuma amshe sunan UWARGIDA daga hannun safeena"