Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 41

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 41

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 41: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 41. "Wani irin zama ne da safeena tayi gidan sultane me…

3,289 words

"Wani irin zama ne da safeena tayi gidan sultane me dadi ta bangaren mijinta,saboda samun mafificiyar soyayya daga gurin sultane din kamar yadda ta samu mafificiyarta daga gurin ajani. Wannan ya daga hankalin zeenatu da mafificin tashin hankali......tashin hankalin da ya ninku ne saboda ta gaza gusar da wannna soyayyar. Ta rayu tsakaninta da zeenatu cikin BARAZANA turata zuwa ga tarin matsalolin da batasan kansu ba batasan kuma yadda zata warwaresu ba. Saidai qarfin addu'a da na saka aka tsayawa safeena da ita komai yake zuwa da sauqi,duk da a sannan nima ina gidan nawa auren.

"Ni kadai.....ni da safeena kadai muka karanci baqin matsanancin halin da zeenatu ta shiga lokacin da safeena ta haifi AHMAD......ko kadan ban bari zeenatu tasan akwai wani ciki jikin safeena ba,don jikina yana bani ba zata taba barinsa ya zauna ko a haifeshi ba. Ina da wani hali da bansani ba.....a halittata ce?,ko ina da mutanen boye dake tsartamin abu idan zai faru......inaji a jikina.....raina da zuciyata suna bani,abu qalilanne zai faru banji hakan a jikina ko zuciyata bata rayamin ba. Hatta da sultane dake neman haihuwa sosai a sannan saboda shekarun aurensa daya fara turawa ban bari safeena ta gaya masa ba,saida cikinta ya shiga wata shida,ta kuma roqeshi kada ya bari kowa ya sani,koda 'yar uwarsa nannie saboda kare lafiyar abinda yake cikinta. A sannan zeenatu tana ta fadi tashin yadda zata samu ciki da sultane,a duk duniya a wannan lokacin burinta kenan,kudade take kashewa marasa iyaka waiko zata dauki ciki dashi,saidai ko b'ari bata samu ba bare cikin dan mutum,dan mutum dinma d'a namiji. A sannan ta gama da kowa cikin masarautar,kowa kirkinta yake gani,kowa qaunarta yakeyi,ta kama nannie qam qam ta riqeta,don kusan ita kadaice ta ragewa sultane a wadda suke uwa days uba daya. Bansan me.ya faru ba,bansan ya akayi ba,ko sun manta zeenatu din 'yar Ethiopia dinnan ce da suka hana muhammad hammud aurenta?. Mun wayi gari kowa yana mata kallon cikkiyar ba'abzina,buzuwa musamman data kasance fara sol kamarmu. Sunanta da muka sani na zeenatu ya koma ZAITUNA,yaren Tuareg a bakinta fes.....al'adunsu shigarsu da komai nasu"

"Haihuwar Ahmad ta qarawa safeena kima da martaba a idanun sultane.....wata sabuwar soyayya yake gwada mata wadda bata boyuwa,abinda ya sake daga hankalin zeenatu kenan,saidai da tarin kirsa irin nata da komai Ahmed ya koma kamar D'ANTA ya koma rainonta,ya koma hannunta ma gaba daya. A sannan ba abinda bance da safeena ba,amma tacemin ba zata iya gwadawa sultane zata amshe ahmad ba.....zeenatu bata isa ta masa komai ba sai abinda Allah ya rubuta qaddararsa ce......" Sai ta dakata tana hadiyar wani abu me d'aci a qirjinta.

"Kasan wace safeena?" A nutse haisam ya maida dubansa kan morsa safiyya da kalar cakurkudaddiyar tambayarta.

"Kasan wanne sadaukarwa SAFEENA ta mana nida sultane da bazata taba shafewa a zukatanmu da rayuwarmu ba?" Ta fadi wani irin hawaye me yawan gaske yana ballewa daga idanun morsa safiyya,wanda ko da wasa bata gwada tsaidasu ba. Bai iya amsa mata ba,amma wannan karon bai dauke dubansa daga kan fuskarta ba.

"Sultane ya harbu da ciwon qoda sanda take dab da daukan cikin AKHNAN......dukka qodarsa guda biyu,kuma aka buqaci ayi masa DASHE na qoda......bada saninsa ba safeena ta sadaukar masa da qodarta guda daya,wanda baima sani ba sai bayan ya warke.......". Saita dakata tana yin qasa da kanta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 71*

"Wannan ya sake sanyawa safeena ta zama wata mace da ba kamarta a gurin sultane.......ba jimawa ta samu cikin KHADEEJA wadda taci sunan 'yar uwarmu.....babbar aminiyarmu da duniya bamu da kwatankwacinta. Samuwar cikin ya sake jaddada tashin hankalin zeenatu,don cikin khadeeja yazo da banbamce babance sosai. Ciwo da laulayi sosai safeena takeyi,kamar ba cikin d'iya mace ba,girman cikin da wahalarsa daban yake,har mun fara zaton ko twins ne. Saidai daga baya zeenatu ta koma tayi relax,ta kuma maida komai ba komai ba,ta sake riqe ahmad da kyau. A wani dare da bazan manta ba,na kawowa safeena ziyara muke maganar

"Duk yadda ka dauki rayuwa haka take zuwar maka,idan zeenatu ta riqe ahmad ga wani kyautar Allah zai sake bamu,Allah yana tare dame haquri safiyya,ki koyi haquri,akwai riba sosai a cikinsa,idan mace na haifa khadeeja nakeso a saka mata,ina yawan mafarkin khadeeja,inaji a jikina babu ganawa a tsakaninmu,zuciyata kullum da ciwon son ganinta da kuma ciwon son sake sanya d'ana a ido nake kwana nake tashi,duk sanda Allah ya hada fuskokinku,ki gayawa khadeeja ina qaunarta......ina qaunarta.....ina qaunarta har abada,nayi kewarta.....nayi rashinta,ki gaya mata ban tafi na barta don bana sonta ba,na tafi ne saboda tseratar da ruhin da bamusan gaba me zai zama ba......" Wani irin abune yake sauka saman zuciyar haisam,sanda morsa ke maimaita masa abinda safeena ta fada a sannan......sai yakejin kamar yana zaune a gurin.....kamar a gabansa safeena ke maganar. Wani irin rauni yaji zuciyarsa tayi,yana iya sauraren yadda morsa safiyya taci gaba da magana muryarta na rawa.

"Daga ranar jikina yayi sanyi da safeena,munyi doguwar hira sosai,a sannan na yaye hairaan,tace nabar mata ita,ban musa ba nabar mata hairaan,saidai sanda zan dawo daukar hairaan na tadda wani tashin hankali ne da har yanzu bamu fita a ciki ba.......batan ahmad sama ko qasa,da fara haukar SAFEENA" Ta dakata tana sanya gefan lafayarta tana dauke hawayen idanunta da suka sake yawa kamar ana tunkudosu.

"An rasa ahmad sama ko qasa,a wani dare aka wayi gari babu shi. Ba kalar nema da binciken da ba'a masa ba......a darenma yana kwamce jikin mamarsa,haka kawai kamar tasan hakan zai faru tace a dakinta zai kwana,don tun farkon cikin akhnan har girma daya fara yi bata da lafiya cikakkiya. Wayar gari tayi taga bashi a gefanta,da farko ta dauka kawai cikin gida ya shiga gurin zeenatu,nema da wasa saiya koma na gaske,amma tsahon kwanaki shuru babu shi ba alamarsa. Wani irin tawakkali safeena tayi,saidai kana ganinta kasan abun ya zame mata dafi ne kawai a zuciyarta.

"Wataqila ni kuma tawa qaddarar kenan batan yarana.....wataqila tawa jarrabawar kenan,ya Allah ka bani ikon cinyeta" Ta fadi da wani irin soyewa cikin idanunta. Zeenatu ta fita haukacewa,don saida aka yita karbo mata tofin dangana,sultane yasa aka dinga kiran malamai suna mata wa'azin tawakkali,saidai tana dangana din sannan ne kuma aka wayi gari wani gagarumin hauka ya samu safeena" A hanzarce haisam ya dubi morsa cikin mamaki.

"Hauka tuburan,yanzu yanzu xaku gama magana da ita lafiya lau.....amma da zarar guri ya zamana ba kowa sai ita kadai yanxu zata fara cisgar sumar kanta tana ci da yage jikinta da suturarta,wani abun mamaki indai da mutum a guri lafiya lau zata zauna,amma ko yaya ta kebe sai abinda aka gani.....naga abubuwa da yawa game da ita masu daga hankali da ban tausayi.......amma ban taba ganin abinda ya gigitamin lissafi ba irin wannan ciwon nata,komai daya sameta a baya tare muke fuskantarsa da mahaifiyata,shi kuwa wannan daya tashi zuwa ya samemu,ya samemu a sanda muka zama CIKAKKUN MARAYU,duk da tarin dangi masu matuqar riqo da zumunci da muke dasu......sannan hakan ya sameni ne a sanda nayi kwanaki bakwai kacal da fita daga takabar mutuwar mahaifin hairaan. Da hannu biyu na karbi kowacce qaddara......da dukkan imanina da yaqini na,nabar hairaan hannun qanwar mahaifiyata,na tattara na dawo cikin masarautar nan don zama da 'yaruwata mafi soyuwa a gareni. A wannan xama na saba da mutane da yawa suma suka saba dani ciki harda sultane daya tattare kulawarsa akan 'yar uwata,wannan abun ya qara kimarsa da martabarsa a idanuna sosai. Saidai wani abun mamakin shine......wata daya ya rage a haifi akhnan na kwanta wani irin ciwo,wanda daga qarshe nima ya bayyana matsalar qoda ne. Ban sani ba......bata gayamin ba.....bata bari an fadamin ba haihuwar AKHNAN akace CS zaayi mata,wanda yazo daidai da sanda zaamin aikin qoda.......ashe qodarta dayar data rage mata ga bani........" Wannan karon kasa riqe kukanta tayi,ta sanya fuskarta cikin tafin hannunta tana sakin kuka mara sauti.

"Subhanal malikul quddus" Ya furta a hankali yana jin wani abu yana yawo a jikinsa. Wannan wacce irin zuciya ce?,wannan wacce irin sadaukarwa ce?......wannan wanne irin 'yan uwantaka ce?,wacce irin qauna ce haka me girman gaske?"

"Ban sani ba sai dana tashi......ita ta zauna bata da ko guda daya......a ranar naji inama nasan inda ruhina yake na fusgoshi na qarawa safeena......ina riqe da hannunta cikin nawa......tana kuka ina kuka 'me yasa kikayimin haka safeena.....me yasa zakiyimin haka?,na rasa khadeeja ban shirya rasaki ba'. Budar bakinta cemin tayi "kinfini buqatar rayuwa safiyya......zaki iya abubuwa da yawan da ni bazan iyasu ba.....inata baki wahala safiyya kinata wahala dani.....rayuwarki tafi tawa muhimmanci......na baki amanar KHADEEJA don a yanxu ita kadai ta ragemin......ita kadai ce nake da tabbas akanta......ahmad da dan uwanshi bansan ya rayuwarsu zata kasance ba.......amma indai kin samu labari ko alamun suna raye.....muddin ci gaba da haquri.......muddin ci gaba da shuru akan lamarinsu ne zai basu daman ci gaba da rayuwa,don Allah safiyya na roqeki KICI GABA DA SHURU......don Allah ki barsu su rayu ta dalilin SHURUNKI"

Wannan roqon......wannan magiyar.......wannan muryar.....wannan sautin da wannan sadaukarwar sune suke riqe dani har yanzu.....sune suke takamin burki akan abubuwa da dama da nake gani nakeji. Safeena ta rayu akan wankin jini na kusan kullum saboda rashin qodojin dake tare da ita,muna rayuwa cike da fata tare da ita......amma ita sam ba wani fata tattare da ita saina mutuwa. Ba yadda sultane baiyi ta bari ya fita da ita a mata dashe ba,amma sai tayi murmushi.

"Ko an dasa bazan sake rayuwa me tsaho ba,iya kwanakin da aka debarmin nayi a duniya sun cika" Wata irin azababbiyar rayuwa tayi......ga ciwon rashin qoda......ga kuma wannan ciwon haukan da yake tayar mata lokaci lokaci babu qaqqautawa. Sam akhnan batasan dadin uwa ko duminta ba,sai a lokutan da safeena ke hayyacinta. Idan tana hayyacinta wuni take a hannunta,idan tana hayyacinta bata yarda kowa ya dauke mata ita,zata wuni ta kwana tana mata wasa,tana kallonta,tana mata addu'a ita da sauran 'yan uwanta,takance.

"Allah nayi imani dakai,nayi imani da dukka qaddarar daka aza a kaina.....na yarda komai ka tsarawa bawanka adalci ne.... Alla idan suna raye komai dadewar zamani ka hademin kansu guri guda.....Allah ka sanyasu qarqashin wani adali......wani adalar inuwa.....wani adalin shugabanci da zai amintar da rayuwarsu......wani ruhi da zai zame musu garkuwa ya basu amincin da ni na gaza basu,Allah ka albarkaci rayuwarsu,ka aminta dasu duniya da lahira". Bansan iya adadin sau nawa take maimaita wannan addu'ar ba a rana. Ranar da aka karbe akhnan daga hannunta aka daina barinta da ita,tana tsaka da riqonta ciwonta ya tashi,haka ta dagata ta saketa daqyar numfashinta ya dawo,koda safeena ta dawo daidai aka gaya mata abinda ya faru,abinta ta tambaya kawai shine BAN MATA ILLA BA KO? Ana amsa mata da EH ta saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa,saita maida kanta ta kwantar tana fadin

"Allah yasa haka ne yafi zama alkhairi a gareta"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Bazan Manta maganar qarshe da mukayi da ita ba,ana jibi zata rasu,ta kira sunana na amsa mata,sai ta saki murmushi tana kallon bangon gabas na dakin,wanda na lura tafi sati tana kallon gurin,a duk sanda take kalla kuma murmushin takeyi

"Nifa na kusa tafiya gida na,gidan daba qunci ba wahala,ba zalunci sai zallar adalci da rahama,na kusa tafiya inda zan huta....." Saita dakata murmushinta yana sake qaruwa. A sannan kowacce gaba ta jikina tayi matuqar sanyi,ina murna ne ganin kwanakin ciwonta ya rage tashi,ko wankin jininma da ake mata wanda take fita hayyacinta kafin ayi a yanzu ba wannan abun sam,ta sake wani kyau abinta,har ranar da zeenatu ta shigo dubata ta kasa shuru sai data magantu. Amma kuma a lokacin tazo da wani kalan magana daya zaremin dukka lakar jikina.

"Kina da gidan da yafi wannan ne safeena?" Na fada cikin tsoro,daga kai tayi da murmushi akan fuskarta ta kalleni.

"Wannan gidan?......akwai birnannun abubuwa,abubuwan da wadanda zasuzo gaba sai sunfi wanda muke ciki yanxu.....kiyi haquri safiyya.....kiyi haquri.....kiyi haquri. Karkiyi fushi da akhnan kome zaya faru.....kada ki juya mata baya don Allah,ki tsaya a tare da ita. Ni na sani komawarta hannun zeenatu ba alkhairi bane,amma na roqi Allah na ya kareta kuma nasan ya amsa min,na roqeshi ya sanyata a mafificin hannu......ya sanya kulawarta a hannun bayinsa masu tsoronsa.....ya kuma bata mafificin miji ma'abocin saninsa da tsoronsa wanda zai ja hannunta zuwa aljanna ba wuta ba......amma akwai abubuwa masu yawan gaske da zasu dinga faruwa a gidan nan,ba lallai yanzu ba safiyya....Allah ne masanin lokaci,don Allah kada ki qara bari zeenatu ta shigo gurina.....banason ganinta da gaske,wani irin baqin duhu nake gani a tattare da ita.....ta cutar dani amma na barwa Allah hukuncinsa" Ta qarasa fada wani hawaye da tunda ta shiga wadannan jarrabawar ban taba ganin ta zubdasu ba a ranar sai gasu suna fita daga idanunta. Komawa tayi ta kwanta tana murmushi sannna tace.

"Kin tambayeni ina da gidan da yafu wannan ne?,ina dashi safiyya.....gidan da koda wasa wannan gidan bai isa ya hada kansa dashi ba.....tazara ce me mugun yawa,inama zaki iya vaji da na nuna miki" Ta fada still tana kallon wannan bangon,wannan bangon da har yanzu idan na shiga ta gurin saina tuna komai kamar yau ya faru.

Safeenata ta rasu a tsakanin cinyoyina,a kanta na fara sanin yanayin fitar rai a jikin dan adam.....wani yanayi me wahalar gaske.....wani irin yanayi me nauyi da kai kanka da mutum yake jikinka sai kasan babban aiki ne a gabanka ba qarami ba.......magananta ta qarshe bada amanar akhnan a hannuna.....amanar akhnan a hannun sultane dake tsugunne gefe yana riqe da ita kamar zai hana a zare ranta,daga wannan sai kalmar shahadar data yota maimaitawa har sanda tabi wani abu da kallo idanunta sukayi sama,wanda nake da tabbacin ruhinta tabi da kallo......".

Katsewa maganar morsa safiyya tayi,ta lullube fuskarta da hannuwanta tana sakin wani itrin kuka maras sauti me d'acin gaske. Tana tuna komai,tana jin kamar a sannan komai yake faruwa.

A nutse ya zare idanunsa daga kanta,yanajin qirjinsa ya masa nauyi,wani iri zafi yakeji daga cikin qirjinsa. Ya jima baiji labarin daya taba masa zuciya tsakanin dan uwa da danuwansa ba irin wannan. Bazaice ga adadin ajiyar zuciyar daya dinga saukewa a boye ba kamar yadda ya saba a duk sanda ranshi ya dugunzuma. Ya tabbatar nanay dinsa ba zata iya jurar jin wannan labarin ba......idan nanay ce yayi imanin zata kamu da ciwon zuciya ne kawai. Labarin rayuwar safeena dinta da rasuwarta bayan rabuwarsu bame dadi bane sam. Ya miqa hannu a hankali ya jawo ruwa cikin tarin kayan ciye ciyen da aka ajjiye masa,ya dauki cup daya ya tsiyaya ruwan sannan ya miqawa morsa safiyya da batasan ma ya zuba ba. Da manyan idanunsan nan da suka rusuna yake duban yadda ta qudundune fuskarta tana boye masa hawayenta.

"Kiyi kuka don yana ragewa zuciya radadi.....amma ki karbi wanna kisha tukunna". A hankali ta sauke hannuwanta daga fuskarta tana kallonsa da fuskarta da tayi jajur......wani nutsuwa taji me yawan gaske a kalamansa,saita miqa hannu ta karbi ruwan kaman yadda ya buqata.

Tas ta shanyeshi,ta kuma ajiye cup din tana jin yadda zuciyarta ke samun sassauci daga radadin da take mata. Shuru ya ratsa gurin ba tare da kowa ya sake cewa komai tsakaninsu ba.

Sai daya bata mintunan daya tabbatar gudun da zuciyarta keyi ya daidaita sannan ya fara magana a nutse.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 72*

"Ba wani abinda yake tabbata sai ikon Allah......haramtaccen abune zalunci koda akan ubangiji daya haliccemu,ya haramtawa kansa zalunci,ya kuma sanyashi abun haramtawa a tsakaninmu,Allah yayi rantsuwa da kan kansa cewa saiya taimaki wanda aka zalunta koda bayan wani lokaci ne". Kai take gyadawa a hankali,tana jin wata nutsuwa na sake mamayarta. Tana jin wani qwarin gwiwa sosai a tare da ita.....tana jin qarfin gwiwa na gaya masa buqatarta kai tsaye......mafarkanta da safeena a satittikan suna dawo mata kanta,tana jin kamar safeena na tare dasu.

"Rayuwar safeena ta riga ta wuce muhammad......rayuwar akhnan ce kadai yanzu ta ragemin......ita kadai ce abinda zan iya daukan mataki ko bada kariya akai........mammina ta shirya lalata rayuwarta fiye da yadda take a yanxu.....ni na sani....ba iya haka taso taga biftu ba.......amma ban taba bacci ba tun daga wancan shekarun har yanxu,ina mantawa da hairaan da falaak saboda na shagala da addu'a wa akhnan.....wannan sautin MIJI NA GARI da safeena taketa roqawa akhnan a qarshen rayuwarta yanata maimaituwa akaina daga sanda yarinyar ta zama budurwa.....tana da wata irin izza....na sani,tana da taurin kai na sani.....tana da wahalar sha'ani na sani......amma an qara koya mata da wasu dabi'u da ba a cikin ainihin halittarta suke ba. Na tsorata da yadda take gudun aure.....na zurfafa addu'a.....bazan boye maka ba daga qarshe na fahimci bawai wani abu bane daban......halinta ne yazo a haka koda an hada da wani abun ma daban.......muhammad" Morsa safiyya ta kirashi a wannan karon tana duba zuwa cikin idanunsa kai tsaye. Shima ita yake kalla,sai yake ganin nanay dinsa cikin idanunta.

"Ba wanda ya cancanci ya auri khadeeja a wannan lokaci IDAN BAKAI BA!!!" ta furta da wani irin confidence daya bawa haisam din mamaki. Idanu ya zuba mata sosai,yana son karantar ko gano wani abu tattare da ita,saidai itama morsa safiyya din kamar kowa,kwarjinin idanunsa ya hanata ci gaba da kallonsa,saita dauke idanunta gefe,a sanyaye ta dora.

"Ina me roqarka muhammad........ka auri akhnan ko bazaka zauna da ita na HAR ABADA BA......ina roqonka kayi mata ALFARMA ka zauna da ita koda na wasu shekaru ne....zuwa sanda dukkan wani buri da aka ci a kanta zai wargaje.....zuwa sanda idanu sukaja baya a kanta.....ka bata GARKUWA muhammad ta hanyar aurenka......KA TAIMAKI RUHIN SAFEENA yaci gaba da kwanciya lafiya.....wallahi nayi imanin cewa,mutuwar auren akhnan a yanzu zai buda wasu sababbin qofofi ne da Allah kadai yasan adadinsu da kuma iyakarsu.....KAYI MATA ALFARMA ka ceci rayuwarta" Takai qarshen maganar tana dawo da dubanta kansa.

Wata magana ce datazo masa a bazatar da baiyi tunani ba. Wata magana ce da bai taba tunanin jinta daga bakin morsa safiyya ba. Wata irin BA ZATA CE a tare dashi data sanyashi yin shuru na wani lokaci,kaman yadda ya saba bawai kai tsaye yake amsa maka magana ba har sai ya bawa qwaqwalwarsa damar numfasawa na wani lokaci. Ta yaya zai fara auren da bai shirya masa ba?......da yarinyar da yayi imanin komai nasu baizo daya ba?. Babu ta inda sukayi tarayya ita dashi......ba wani abu dake nuna daidaito a tsakaninsu......ta yaya ma?....wanne irin aure ne haka wanda ko da wasa bai taba hakaitoshi ba?. Idan kuma yace zaiyi auren CETO na wani lokaci ne.....ai ya sani cewa haramunne a qulla aure bisa wata yarjejeniya,yarjejeniyar ma ta rabuwa.....baisan daga inda zai samo halascin haka ba. Ta kowacce fuska baiga dacewa ko yuwuwar abun ba.......don ya sani.....aure ba abune ba wasa ba......sunna ce mafi qarfi da ba wasa a cikinta ko kadan,ta yaya zai fara abinda baiyi niyya ba?,bai shirya ba?.

Readers Also Read

More by Huguma