L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 42
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 42: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 42. Koda morsa safiyya bata nema ba.....koda bata buqata ba…
3,328 words
Koda morsa safiyya bata nema ba.....koda bata buqata ba ya yankewa kansa yin revision a tarihin safeena.......ya azawa kansa wannan nauyin ba tare da shawarar kowa ko tunani na biyu tsakaninsa da zuciyarsa ba. Akwai abubuwa da yawa da yake buqatar saninsu......akwai abubuwa da yawa da bai kamata a barsu suci gaba da tabbata a haka ba. INA AHMAD ina jaririn dan yayansa?. Sun narke kenan?,sun shafe daga rayuwar safeena?,saboda tsoron salwantar rayukansu sai a tabbata a haka?. Jikinsa yana bashi tun daga farkon labarin cewa komai daya faru na farko dana qarshe a qulle suke da juna.....komai daya faru yana da alaqa da dana baya,ya zama dole GASKIYA tayi magana......ya zama dole wannan ZALUNCIN ya gushe hakanan.....ya zama dole a tabbatar da ZURI'AR SAFEENA suyi rayuwa me 'yanci kamar yadda kowacce zuri'a take rayuwa.....AMMA BANDA WANNAN AUREN.....wannan auren wani abune da bazai daukeshi a wuyansa ba sam.
Shuru itama morsa safiyya din kawai tayi,yayin da zuciyarta dake lullube a qirjinta take wani irin tsalle. Rawa kawai zuciyarta takeyi,tana cike da fata da sanya rai,tana cike da zullumin me zaya amsa mata dashi?.....tana tsaka da wannan zullumin e ya dubeta a hankali.
"Komai a hankali ake binsa da kuma nutsuwar da bazata kawo dana sani ba daga baya......."
"Kada ka bani amsa yanzu don Allah muhammad na roqeka.....kaje kayi tunani.....kayi tunani daga yau har zuwa kwana uku hudu biyar harma sati......amma ka sani,indai ka wuce haka komai zai iya faruwa da khadeeja" Ta qarasa maganar da wani irin rauni cikin idanunta. Zare idonsa yayi yana jin raunin nata yana tabashi,ya miqe a nutse,bayanansa dukka ya adana. Bawai zai iya gaya mata a halin daya ganta cewa kai tsaye bai karbi magananta ba.....don yasan aikata hakan zai sake jefata ne kawai cikin wani rudani na daban. Ta idanunta ya karanci dukkanin FATANTA yana kansa......ta sanya buri da fata me yawa a kansa.
"Na barki lafiya" Ya fada yana takawa a hankali.
"Na gode sosai muhammad da amsa kirana.....da jumurin zaman saurarona da kayi......na zabeka nayi kuma magana dakai a matsayin mutum me tsoron Allah.......Allah yana taimakon bawa muddin bawa bai gushe ba yana cikin taimakon dan uwansa" Magananta ta qarshe hadisi ne......hadisin da yaji yana kakkaryashi a hankali,don haka bai waiwaya ba bai kuma tsaya ba,yaci gaba da takawa yana fita a hankali daga sassan.
Ajiyar zuciya morsa safiyya ta sauke,ta gyada kanta a hankali tana daga hannuwanta zuwa sam. Wata sirrintacciyar addu'a ce tsakaninta da ubangijinta,ta shafa a nutse sannan ta waiwaya ta dauki wayarta tana laluben hairaan don ta turo mata armelle.
So yake ya koma personal residence dinsa.....so yake ya sake nisa da kowa da komai ko zai samu kwanyarsa tayi resettling na magangnun morsa safiyya da yakejin sun wani irin cika masa kwanya......amma kuma bai kamata daga shigowarsa gidan ace har ya sake fita ba. Saidai duk da haka hakan bai hanashi kebe kansa ba,yabar maleek da omar a qasa,ya haura zuwa samansa bayan ya sauya kayan jikinsa,sannan yayi zaune saman bedroom balcony ta bayan wasu flowers. Relaxing yayi sosai saman wani foldable bed dake a gurin,ya lumshe idanunsa yana sake bitar dukkanin labarin cikin kansa.
Ya jima cikin wannan yanayin,har zuwa sanda jikinsa ya bashi lokacin sallar magariba ya gabato,ya bude idanunsa a nutse ya jawo wayarsa dake gefansa,ya tarar da tarin miscal harda na omar da maleek,qarshe yaga gajeran saqon maleek dake gaya masa sun fita wani guri shida omar. Baibi kiran nasu ba tunda ya fahimci ma'anar kiran,sai kawai ya kira beeno ya fada masa ya duba email dinsa. Tashi yayi sosai ya zauna ya rubuta saqon da dukkan tsarin da yake buqatar ya aike masa.
Yana ji a jikinsa da ranshi akwai wani personal aiki da yahau kanshi......akwai xtra bincike daban da yahau kansa,ba kuma zai dakata ba har sai ya cimma gaci,har sai yakai inda jiki da zuciyarsa suke raya masa suke masa kuma tsammani.
Kamar kowanne lokaci da kansa ya dauki zafi irin wannan,sauraren karatun qur'ani da kuma karantashi ne kadai abinda yake zame masa nutsuwar zuciya da kuma hutu.
Yana zaune a farfajiyar da zata bashi daman ganin zirga zirgar kowa,da kuma sake karantar yadda dokarsa take aiki. Wani nazari yake sakeyi cikin gidan,motsin kowanne sashe,motsin kowanne hadimi da yanayin mu'amalarsa. Yana daga bangaren da ba lallai ka ankare dashi ba idan ba wucewa kazo yi ta gabansa ba,kuma koda kazo wucewar zaka dauka wani sha'ani daban ya keyi bawai nazarin yanayin gidan ba. Kunnensa manne da booth yana sauraren karatun qur'anin sheikh afif muhammad taj. Yawan lokuta yakan saurari qira'ar sheikh afif din,don yanason gani ko jin kamannin karatunsu da ake yawan fada. Tun yana da shekara sha takwas a duniya yake da nasa complete qur'an din audio,karatun da yawan manyan makarantun dake jimma dama Ethiopia gaba daya da wannan sound din suke amfani. Gidajen tv dana radio dinsu gaba daya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kiran daya shigo wayarsa ya sakashi tsaida karatun,ya maida hankalinsa akai a nutse sassanyar iskar dake tafe da hadari tana busashi da cikin Moroccan thobe din jikinsa data kasance olive color. Yanason abu me green qwarai,daga sanda yaji favourite colour na ma'aiki annabi muhammad s a w. Sai kuma kalar take bashi wani irin kwarjini gami da bayyanar da fatarsa me haske data d'ara ta al'ummar jimma oromia haske,wataqila hakan yana da nasaba da hutu da nutsuwa da yake ciki.
Nanay daya gani ya sanyashi katse karatun da yakeji,ya sanya hannu ya zare Bluetooth din ya ajiye,sannan ya katse kiran nanay yabi bayan kiran.
Ajiyar zuciya ta sauke sanda taji sallamarsa,hankalinta da tunaninta ya sake komawa kan saamee dake kwance saman gadon ROYAL CLINIC dake cikin masarautar jimma din. Tun ranar qarshe da sukayi waya da haisam din ta karanci damuwa ce fal zuciyar yarinyar,amma kawaici da alkunya irin na d'iya mace ya hanata nunawa. Tana tausayin dukkan wani maraya,saboda tasan me maraici yake nufi,maraicinma irin na UWA da ba'a maida makwafinsa.
"Ina fata ka yini lpy Muhammad?"
"Alhamdulillah nanay" Ya amsa mata safeena da safiyya suna dawo masa tar cikin idanu da zuciyarsa. Yana jin kamar ya shaidawa nanay din cewa yaga twin's dinta......amma yanaji a jikinsa lokaci baiyi ba,ba yanxu ba. Ba yanzu bane lokacin daya kamata ya fadi mata hakan ba,tabbas zata nema tako qafarta masarautar agadez ne......a yanzu kuma da komai ya sake warware masa ta labarin morsa safiyya bayajin ya kamata nanay din ta bayyana a yanzu.
"Ma sha Allah......magana zamuyi Muhammad" Ta furta a hankali tana tashi daga gaban gadon saamee gami da ficewa a hankali daga dakin.
"Yanzu kike buqata nanay?,ko zaki sanya wani lokaci da yayi miki saina kiraki?". Murmushi kadan ta saki,bata shakka ko kokwanton haisam.....biyayyarsa game da iyayensa ta dabance.....wata irin soyayya da jinqai yake gwada musu data jima bataga yaro irinsa ba.
"Idan nace zan bari zuwa wani lokaci muhammad sai na dinga ji kamar lokaci xai quremin......alfarma nake nema muhammad a gurinka" Kai ya girgiza da sauri kamar tana gabansa,ya zauna kuma sosai yana bata nutsuwarsa.
"Kinfi qarfin alfarma nanay,saidai umarni...." Murmushi me dan sauti kadan ta saki.
"Na sani muhammad.....amma wannan inaso a barshi a mazaunin alfarmar"
"Ina jinki nanay" Ya fadi cikin girmamawa.
"Ina tsoron wani abu muhammad......maraicin saamee yana tabani,don har yanzu bata saba da rayuwa ita kadai ba.....bata saba da rashin mahaifiyarta ba.....sai kuma na fahimci ta shiga wani yanayi da ita kanta nasan bata shirya masa ba". Shuru yayi yana saurarenta,kwanyarsa na qoqarin tattaro masa maganganun nanay guri daya ya aunasu a mizani.
"Muhammad.....ko kasan akwai alqawarin aure tsakaninka da saamee ta hannun mahaifiyarta kafin ta rasu?". Shuru ne ya gilma ta cikin kansa,kafin ya maida idanunsa a hankali ya lumshesu sannan ya budesu,zuciyarsa ta dauki
"Subhanallah" A hankali tana maimaitawa. Wani irin yanayi yana sake saukar masa,ya sake miqa hankalinsa akan nanay
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 73*
"Ba wai hakan yana nufin lallai saika auri saame ba.....ba kuma hakan yana nufin zan tilastaka bane....aah,kamar ganin dacewar hadin mukayi dani da ita. Saidai tako ina ban hango ta yadda hakan zai kasance cikin lumana ba.....banga ta yadda zaka shaqu da saamee ba har ku fahimci juna ba saboda yanayin aikinka....a daidai lokacin na karanci kamar zuciyar yarinyar ta harbu da sonka...." Sosai maganan nanay ta shigeshi,ya fahimci hakan tunda dadewa,sannan omar ya jima yana maimaita masa.
"Na sani nanay" Ta fadi kansa tsaye. Ba wani abu daya kebance game dashi wai yana boyewa nanay,nanay dinsa itace aminiyarsa ta farko dake sanin komai daya danganceshi.
"Na nesanta kaina da ita ne saboda banason ta saba dani......nayi hakanne saboda banaso ya zame mata wani ciwo a zuciyarta.....saboda ina ban hangi ta inda zata samu yadda take so ba daga gareni,ban shirya ba nanay......ina da abubuwa da yawa a gabana" Ya fadi da dukka gaskiyarsa da fatan nanay ta fahimceshi.
Shuru ya ratsa tsakani kafin nanay ta saki wani murmushi me sauti kadan.
"Sai yaushe?.....muhammad sai yaushe?,ko kasan kwanaki kadan suka rage aje nemawa hussam aure?ana kammala bikin rumaisa?" Maganan yadan bashi mamaki,amma yasan hussam,rawar kai plus farinjinin 'yammata.
"Hussam dai?" Ya maimaita da dan mamaki. Murmushi nanay ta saki.
"Kowanne burina ya cika haisam banda abu biyu,ganawa da 'yan uwana da kuma ganin surukai da jikokina.....ina buqatar ganinku dukka da aure" Bai iya cewa nanay komai ba,don anzo bangaren da yakeji bashi da wani shiri akai,kuma shidin ba wani gwani bane ta wannan maganar musamman da nanay din da kunya da nauyi irin na tsakanin uwa da d'a yake ratsawa a tsakaninsu.
"Kasan saamee tana kwance ana qara mata ruwa?.....ko tsananin damuwa ce a kanka ta jawo mata haka?" Maganar ta bashi mamaki sosai,ya danyi ciki ciki da idanunsa yana sauraren nanay. Koda bata ganinsa tasan yanayinsa,ta gyada kanta a hankali.
"A shawarce.....me zai hana ka ceto saamee koda ta hanyar bata kulawa muhammad?,wataqila zuciyarta ta samu sassauci?". Wani shurunne ya sake ratsawa a tsakaninsu,a nutse ya motsa labbansa masu kyannan.
"Indai hakan kikeso nanay sai ayi" Ya fadi a nutse yana jin wani nauyi ya sake hawa kansa.
Idanu Nanay ta lumshe,murmushi mara sauti yana qwace mata,alfahari da samun yaro irin haisam din yana sake shigarta.
"Allah yayi maka albarka.....Allah ya shiga dukkan al'amuranka,yadda kake qoqarin ceto damuwar wasu Allah ya ceto damuwarka"
"Ameen Ameen" Yake amsawa da ita yana ware tafukan hannayensa. Addu'ar nanay wani abu ne da baya wasa dashi komai gajatarta
"Zan sanya noora ko Aanani su dinga sanar maka komai a yanayin da ake ciki" Da wanna sukayi sallama da nanay din,ya zare wayar yana ajeta gefe nannauyan ajiyar zuciya tana kubce masa.
"Ya ake ciki man". Maleek ya fada yana daukan gorar ruwan dake gaban haisam din ya fara zubawa da kansa a cup. Kai ya girgiza a hankali yana nutsa yatsun hannunsa cikin sumarsa wadda ya yafa amama saman kansa. Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,saidai ba wanda ya samu daman cewa komai ta bayyana.
Falaak ce,dauke da kyakkyawan kwandon data cikashi da fresh 'ya'yan itatuwa,irin wadanda tassn akhnan na matuqar so. Kai tsaye daga lambunsu ta fito,ta kuma debosu da zummar zuwa ta kai kitchen su gyara ta wucewa da Akhnan din,dukka tanayin haka ne don cika alqawarinta data yiwa morsa safiyya.
Gefe daya wani sawai takejin qirjinta,nauyi me girma ya sauka ya kuma ragu daga zuciyarta. Farincikin kawai data sanya morsa safiyya ya isheta,tana jin wani dadi da yadda abinda tayi ya faranta ran morsa din.
A hankali idanunsa ya sauka a kanta sanda yake tsakiyar shan ruwan,daga omar har haisam da suke magana a tsakaninsu ba wanda ya lura da ita,sai qarar tarin qwarewar maleek. Haisam ne ya fara ajiye dubansa a saitinta sanda take wucewa ba tare data ankara dasu ba,sai kawai ya janye sannun da yake niyyar yiwa maleek din ya jefeshi da harara.
"Saika tashi ka bita ko?" Kamar baisan gatse ba,kamar bai fahimci gatse haisam din ya masa ba,ya kurbe ragowar ruwan daya tsaida masa tarin,ya ajiye cup din ya miqe da kuzarinnan nasa ya soma takawa yana bin bayanta.
Siririn tsaki haisam yaja......wato maleek zafin kai kawai yakeson qara masa,don haka ya miqe a nutse ya dauki wayarsa kadai yana juyawa zuwa hanyar da zata sadashi da sassansa,sai suka bar omar a tsakiya a zaune ba tare da yasan shi wacce tashar ya kama ba,qarshe ya zabi satar kallonsu maleek,don ta nan bangaren yasan zaifi samun labari me kyau da armashi.
Saura kadan tayi missing numfashinta sanda taji sallama a bayanta da wata irin nutsatsiyar murya. Ta tsaya cak ba tare data juya ba,muryar dai bata mata kama da muryar daya daga cikin hadiman gidan ba,to waye?. Sai maleek ya zagayo gabanta yana bayyana kamar me jiran takai ga tambayar kanta da kanta din.
Kai tsaye idanunsu suka gauraya guri daya,sai taja da baya kadan tana jin wani kwarjini tattare dashi. Murmushin dake fita saman fuskarsa ya daki zuciyarta da wani irin yanayi me nauyin gaske,tana jin kamar gurbi da muhallin loneliness da takeji a zuciyarta yana cikewa.
"Kawo na tayaki mana kona samu albarkacin princess?" Yayi maganan yana dage mata dukka girarta biyun. Kasa musantawa tayi,duk da batasan wayeshi ba,abu daya dake bata mamaki shine kwarjini da takejin yana mata masu cika idanu,shige wadanda take gani tattare da sheikh haisam,sai kawai ta miqa masa kwandon,yarima maleek din sai gashi da riqon kwando yana kuma jera kafada da ita a nutse suna takawa zuwa ciki ba tare da kowa yace da danuwansa komai ba.
*HAISAM*
A nutse yaji an kirashi da sunan da sukafi kiransa cikin masarautar na SHEIKH MUHAMMAD. Sai dakata yana juyowa a nutsensa. Me wada ne yake isowa gurin,cikin girmamawa ya rusuna yana fadin
"Barka da wannan lokaci" Murmushi kadan haisam din yayi yana bawa mewada din hannu,amma sai ya noqe. Wani girma suke bashi,wanda shikuma koda a jimma ba kasafai ya fiya son irin wannan abun ba.
"Musabaha a musulunci abune me matuqar muhimmanci,kankare zunubai da sadar da soyayya tsakanin bayi,assalamu alaikum" Ya qarasa fada yana sake bawa mewada hannu.
Cikin jin nauyi,cikin jin girman haisam din yana kai masa ko ina ya bashi hannu suka gaisa. Me wada ya zare hannun bayan sun kammala gaisawar yana girmama zatin Allah,da yadda ya sanya wasu halittunsa tun a duniya suka banbamta da wasu,wani irin laushi da qamshi tafin hannuwansa kawai keyi.
"Giwa ce tace a sanar maka tana son ganinka". Dubansa sosai haisam yayi,aiken yana dan saukar masa da mamaki qasan ranshi,amma sai ya gyara tsaiwarsa yana duban mewada.
"Ka shaida mata ka sanarmin,zan kuma amsa kiranta daga yanzu zuwa kowanne lokaci" Kai mewada ya jinjina a hankali. Qarfin halinsa,jarumtarsa da yadda yake iya aikewa giwa saqo kai tsaye game da abinda yake ranshi kuma ra'ayinsa kenan yana burgeshi qwarai.
"Zan shaida mata,na barka lafiya" Ya fada yana miqewa sosai ya fara takawa yana barin gurin.
Hannunsa ya goye a bayansa,sannu a hankali cikin nutsuwa yaci gaba da takawa yana nufar sassansa. Tunaninsa yana zurfafa,yana kuma laluben meye dalilin kiran da mammina din tayi masa?.
Daidai sanda zai gifta da qofofin da suka raba balcony dinta da nasa wadda zata kaishi kai tsaye zuwa sassan kowannensu. A hankali Idanunsa suka sauka akan sashen nata,sai ya zare idonsa dakai yana wucewa gaba.
Wani bangare na rayuwarta ya soma qoqarin dawo masa fes a kansa. HADARI ne sosai take fuskanta.....hadarin da yake kyautata zaton ya kamata ace hankalinta yakai kai.....amma me ya hanata fahimtar wasu abubuwan?......me ya hanata ta gane akwai QALUBALE?.....akwai GIBI a rayuwarta?. Ta sanya girman kai da izza gaba da komai nata?,bayan akwai tarin yaran SARAUTA da basu kai kansu inda takai kanta ba?.
Samun kansa yayi da jan siririn tsaki,ya dauki tunanin ya ajiyeshi gefe daya,saboda yana ji a ransa akwai wani aiki da yafi wannan muhimmanci da ya kamata ya maida hankalinsa akai.
*MAMMINA*
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Yatsunta kawai take murzawa guri daya sanda mewada yake gaya mata martanin sheikh muhamma haisam. Karo na biyu.....karo na biyu kenan yana fito na fito da martabarta. Karo na biyu kenan yana qalubalantar girman matsayinta naqin amsa kiranta a sanda ta buqaci haka. Qoqarin tauna fushinta da dukkan bacin ranta takeyi ta kuma hadiyesu kada ta furtasu ko ta bayyanasu gaban mewada dake matuqar girmamata da biyayya ga dukka umarninta.
"Zaka iya tafiya" Ta fadi a taqaice. Godiya yayi mata ya miqe yana barin gurin. Wani irin iska me zafi ta furzar daga bakinta,ta bude idanunta sosai sannan ta maidasu ta lumshe ta sake budesu,tana gayawa kanta ne yanzu ba lokaci bane na fushi,yanzu ba lokaci bane na bayyana zafinta ba,lokaci ne na kwantar da kai,lokaci ne na karbar duk wani abu da malamin zaiyi,har zuwa sanda haqarta zata cimma ruwa,a sannan ne zata banbance masa WACECE ZAITUNA?....WACECE GIWAR AGADEZ?.
"Farisa!" Ta kirayi daya daga cikin hadimanta dake can qofa tana jiran umarninta. Da gaggawa ta iso gabanta tana zubewa.
"Zan shiga naga akhnan,bana buqatar iso,bana kuma buqatar a gaya mata zuwa na".
" Hakan za'ayi Allah ya baki yawan rai" Ta fadi kanta a qasa sannan ta miqe itama ta fita.
Kwana da kwanaki tayi bata sanya akhnan din a idanunta ba,ba kuma wai don ta shirya faruwar hakan ba,sai don abubuwan da suka sha mata kai take qoqarin ganin komai ya tafi a tsari. Shirye shirye taketa yi,shiri kota kwana,maganan motsuwar daya daga cikin tarakuna Ethiopia ya tsaye mata a rai,shine kuma abu na farko da take kwana take kuma tashi dashi,sannan da kanta take bibiyar samun tabbacin abun,ta zare wakilci tana ganin kaman bazai mata ba.
Abinda yafi sanya mata wata fargaba shine......ganin yadda aka kasa samun cikakken bayani kai tsaye cikin sauqi kan da gaske akwai wanda yayi tafiya zuwa agadez?. Abinda yake sake luguiguita mata zuciya kenan.....yake sanya mata shakka da wasi wasin ANYA ba wani gagarumin abu bane yake shirin tunkarota?.
*AKHNAN*
Ba zata sake bari wani abu ya taba IKONTA ba.....ba zata sake bari wani abu ya girgiza duniyarta ba......ba kuma zata sake bawa kowa dama ya bude qofar rayuwarta ba.....koda wayeshi.....komai kusancin dake tsakaninsu.
Tun a dararen da suka shude ta yiwa kanta wadannan alqawuran,zata maida rayuwarta yadda take a baya a cikin satin. Zata maida kanta PRINCESS KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD dinta kamar yadda take a baya,zata rayu yadda takeso,ba shawarar kowa....ba sanya hannun kowa.....ba gudanarwa ko yankewar hukuncin kowa. Wannan ya sanya ba tare data shaidawa mammina ko tayi shawara da ita ba ta fara shirye shiryen komawa Niamey. Tun a daren jiya ta gayawa hannatu a gyaran gidan a maidashi kaman yadda yake a baya,a fadawa babban driver dinta na garin Niamey wato HARISU ya duba motocinta gaba daya da take fita office dasu a fita dasu a siyo wasu. Koda ta koma Niamey tana jin zatayi hutun sati daya cikin gidan kafin ta fara fita office. Zata zauna na sati daya ta maida wannan tunanin na CEO a kanta,ta sake kintsa nutsuwarta da yadda zata karbi ayyukanta.
A yanzun da take zaune cikin daya daga cikin falukanta da takan huta. Baida kujera ko daya,sai wasu irin lausasan Turkish carpet da tuntum manya masu dauke da tambari na sarauta da sunanta a jikin kowanne. ABIDA me mata gyaran gashinta ce,wadda ta iya nau'ikan manyan kitso na qasashe da qabilu daban daban,da kuma kalba manya da takan yiwa akhnan din a sanda duk zata koma Niamey idan ta gama hutun qarshen mako da takeyi a baya.
Tana mata kalbar data zama manya kuma tana hade jelarsu guri daya yadda ba zasu damu uwar gijiyartata ba,yayin da akhnan din ta maida hankalinta sosai ga ameesha tana sauraren bayanai akan kamfanin na watannin da tayi bata tare dasu.