L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 43
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 43: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 43. Kowanne bayani na ameesha sake bata mamaki kawai…
3,260 words
Kowanne bayani na ameesha sake bata mamaki kawai yakeyi,amma bata dakatar da ita ba,taci gaba da sauraronta duk da ba ganewa takeyi ba,amma ta aza hakan akan cakudewar bayanan ameesha dinne guri daya ya kawo haka,don bada wannan salon da kuma wannan yanayin suka gabatar mata da bayani ba.
Kanta taji abida ta saki,abinda ya sanyata dauke kai daha system din da suke video call da ameesha ta maida ga abida,sai idanun nata suka sauka akan mammina dake takowa cikin izza,da alama kuma ita ta saka hadimanta su bawa dukkan hadiman dake dakin umarnin fita.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 74*
Bata motsa ba,bata kuma ce da ita komai ba,sai kawai ta maida idanunta ga Ameesha sukaci gaba da tattaunawarsu cikin salon miskilancin nan nata da ya motsa.
Idanun mammina akan ameesha bayan ta daukeshi daga kan akhnan da rabi akayi masa kalbar ta kuma sauka lambas a gadon bayanta,sai rabin gashin da yabi gefan kuncinta ya kwanta.
A jikinta taji abubuwa biyu,bata kuma buqatar qarin bayani. Hankalinta ya kwanta da har take shirye shiryen komawa Niamey kenan?,sannan ya akayi ta samu access da ameesha?....me take gaya mata?.
Tana buqatar fahimtar komai kafin tayi magana daukan mataki na gaba ko kuma yin wani motsin,don haka ta samu tuntum daya ta zauna akai tana harde qafarta.
Still akhnan bata waiwayo ba,saidai yanayin ameesha da taga kaman yana sauyawa,kamar bayanin tana yinsa ne kawai ba tare da ita kanta tasan gundarin abinda take magana akai ba. A nutse ta lumshe idanunta sannan ta budesu a kanta.
"Ameesha" Ta kirata da muryarnan tata dake cike da aji gayu da sarauta.
"Ranki ya dade"
"Ki tattara komai ta yadda idan na iso zanji dadin dubawa,bazan wuce gata ba in sha Allah"
"To Allah ya kawoki lafiya,godiya nake" Ameesha ta fadi wani sanyi yana tsargawa qasan ranta. Tana fatan ta iso da wuri,ta kuma jima tana addu'ar dawowarta a lokaci irin wannan kafin komai ya qarasa kwabewa.
"Gata?" Mammina ta furta a nutse da salon tambayar da ba iya fili kadai ba.....hatta da zuciyarta ta aikewa tambayar. A nutse ta waiwayo ta dubi mammina tana kuma dakatawa da kashe system din.
"Eh gata" Ta amsa mata kai tsaye da wani irin yanayi da tasan sauran mutane kadai akhnan me magana dasu a haka ba ita giwa ba.
"Gata in sha Allah......ko akwai sauran abinda ya rage da zan zauna nayi?.....kowa burinsa ya cika,an daurawa akhnan aure,ta taba aure a tarihin rayuwarta dai ko?" Ta fada da dukkanin alamun dake nuna abun yana mata ciwo.....da dukkanin alamun dake nuna cewa abun yana mata radadi tare da jefata a danasanin amincewa da wannan yarjejeniyar tunda farko.
"Akhnan d'iyata" Mammina ta kirata bayan ya sake matsowa dab da ita,idanunta da jikinta dukka sunayin wani irin laushi.
"Ban taba zato ko tunanin wani lokaci yana zuwa da zaki zargeni koki tuhumeni da cutar dake ba" Ta furta hawaye yana saukowa daga idanunta. Har tsakiyar zuciyarta akhnan taji hakan,a karon farko taga abinda bata taba ganina idanun mammina ba tsahon rayuwarta,kuka ko hawaye
"Na rantse miki harda girman Allah......almaz shine kalar mijin da yafi dacewa dake.....kinsan a yanzu haka halin daya shiga saboda abinda ya aikata din?". Tayi mata tambayar tana tsareta da idanu tanason karantar yanayinta.
Kai tsaye akhnan din take duban mammina. Haka kawai tayi loosing interest aka komai daya shafeta......tana jin tana rasa dukkan wani confidence da qwarin gwiwa akan mammina din. Batasan me yasa ba,tana jin kawai komai ma ya fita a ranta,amma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata,bai kamata KUSKURE D'AYA TAK da aka samu daga bangaren mammina din ya zama wani abu ba.....ya zama wani dalili da zai sanya ta juya bayanta daga dukkan wani alkhairan mammina din a tare da ita ba.
Wata irin mutum ce ita da bata manta alkhairi komai qanqantarsa.
"Wallahi akhnan ya fiki shiga baqinciki bacin rai da kuma damuwa.......a yanzun ina me baki tabbacin baisan inda kanshi da hankalinsa yake ba,kuma dukka a kanki,dukka ta sanadinki" Mammina din ta fadi yanayinta yana nuna narkewar zuciyarta.
"Ta yaya zanyi saken da wani mummunan abu zai rabi diyata?.....ta yaya zanyi saken da halitta mafi soyuwa a zuciyata da rayuwata zata fuskanci wata barazana?,bayan bani da kamar wannan halittar duk duniya?. Ina jin wani irin mamaki kaman zai kasheni a duk sanda na kalli fuskarki,naga kuma ba abinda ya cikata sai tuhuma da ganin baqina" Mammina ta furta tana share qwallarta data sake gangaro mata.
"Amma duk da haka ni zaituna.....nayi alqawarin saita lamuranki,koda kuwa hakan shine abu na qarshe da zan aiwatar a rayuwata.......abu daya zan gaya miki.....ko mene zai biyo baya kada ki tuhumeni.....idanunki da hankalinki kawai nake buqata......amma karki manta da wannan ko sau daya a zuciyarki......ni mammina UWA nake a gareki.....bazan kuma taba canzawa daga wannan sunan ba har abada.....kamar yadda babu wani abu da zai sauya qaunar da nake miki har gaban abada". Daga haka ta miqe da wani irin yanayi dake nuna mutuwar jiki da damuwa me yawa.
Samun kanta tayi dabin mammina din da kallo,tana jin jikinta itama gaba daya yanayin wani irin sanyi. Tana jin kamar ya kamata tabi bayanta.....amma wani sashe na zuciyarta dake daqare da wannan izzar dake gauraye da jinin sarauta na gaya mata ta qyaleta.
Wani irin kewa takeji a yau......wani irin kadaici takeji duk da cewa tana zagaye ne da mutane. Samun kanta tayi da miqewa tsam,ta taka a hankali tana isa bakin qofar dakin,ya maidata ta murza mata key ta kulleta. Dawowa tayi a nutse zuwa bedside drawer dinta da ba wanda yake da alhakin taba gurin,ta murzata ta budeta,ta kuma fiddo wani dan zagayayyen akwaiti me matsakaicin girma ruwan gold. Budeshi tayi a nutse,ta saka hannu tana fiddo wasu hotuna qananu guda biyu.
Idanu sosai ta xubawa fuskar dake jikin hoton,fuskar dake dauke da wani lallausan murmushi. SAFEENA ce,idanunta a cikin hoton suna kallon camera ne kai tsaye,wasu irin kyawawan idanu da suke kama sosai da nata,banbamcinsa da natan ita fari da blue ne......yayin da na safeena ya kasance fari da baqi sidik......
Hannu ta sanya a hankali ta shafi hoton,a ranta tana raya abubuwa masu yawa.......a ranta tana raya inda tana raye yaya zasu fuskanci wadannan kwanakin masu tsanani da taurari a tattare da ita?,saita lumshe idanunta tana damqe hoton sosai a tafin hannunta.
Haka kawai takejin akwai wani abu da ba daidai ba......haka kawai takejin akwai wani KUSKURE da yake tare da ayyukanta da zartarwata......ko kuma yake tattare da tunani da hukuncin mammina?. Amsar da bata da ita batasan kuma yadda zata fassara abun ba.
*SULTANE*
Cikin kamala da nutsuwa irin tasa,wadda bata taba sauyawa ba ko a wanne bigire kuma ko awanne yanayi ya samu kansa ba ya qarasa qofar dakin bobbo muhammad dawud,wanda ya kasance daura dashi cikin daya daga cikin manyan hotels dake kusa da haramin madeena.
Sau daya ya nema izinin shiga,bobbo da kansa ya taso ya budewa sultane din bayan ya ajiye dan qaramin alqur'anin dake hannunsa.
"Ina fata kaima qira'arka irin ta yaronka ce ko?" Sultane ya fadi yana duban bobbo muhammad wanda ya ajiye masa ruwan daya ciro masa mara sanyi sosai a fridge. Bawai don daga wani guri sultane ya taso ba,ba kuma wai don yana jin ishirwa ba.....aah,kawai don tarin girmamawa ga tsohuwar abota.
Murmushi sosai bobbo muhammad dawud yayi. Zuwa yanzu har ya saba da yanda duk fitowar rana da kuma faduwarta sai sultane din ya ambaci hasaim. A irin ambaton da ko motii aba jifar baya tunanin yana ambatonsa haka.
"Duk wanda ya zauna da muhammad saiya dosani wani haske na alqur'ani daga gareshi" Obbo ya fadi yana zama gefan gadonsa yana fuskantar sultane. Kai sultane ya gyada a hankali,yana sake jin nutsuwa gami da gamsuwa me yawan gaske a tare dashi game da haisam din.
"Zanso nasan wadanne iyaye ne haka Allah ya yiwa baiwa da samun yaro irin muhammad.....tabbas ni na sani,suna cikin iyaye masu sa'a a duniya". Murmushi kadan bobbo yayi,ya sani ba abu bane me yiwuwa ya gayawa sultane cewa tsohon abokinsa motii aba jifar shine mahaifi ga haisam din. Yin hakan kamar ya tona asirin aikinsu ne.....komai kuma zai iya bayyana a lokaci da kuma muhallin da ba'a shiryawa faruwar hakan ba.
"Abokina ne......wanda ya damqa amanar muhammad a hannuna......ya damqa min da amana da gaskiya.....wanna ya sanya sau tari ni kaina nakejin muhammad din kamar nina haifeshi"
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Wannan shine dalilin daya sanya nayi tattaki zuwa gurinka.....don ka yimin alfarma.......don kuma ka nema min alfarma". A nutse bobbo ya daga kai yana duban sultane,maganganunsu suna zuwa masa a hagunce.
"Kamar yaya?" Bobbo ya tambaya kai tsaye da alamun kullewar kai a tare dashi.
Sosai sultane ya gyara zamansa,yana kuma tattarawa bobbo dukkanin nutsuwarsa,abinda yake gayawa bobbo cewa maganar tana da tarin muhimmanci mara misaltuwa.
"Inaji a jikina akwai qaddarar data sake hadamu a nan gurin dawud,bayan tsahon shekaru da mukayi bama tare,ba kuma tare da mun sake haduwa ba. Yanayinka da yanayin girman da muhamamad ke baka....labarin qarfi da girman amincinku ya tabbatar zaka iya tsaiwa a bigiren da mahaifine kawai yake tsayawa,Nazo ne na nemawa d'iyata khadeeja auren muhammad haisam a hannunka......kai kuma ka nema mata aurensa a hannun amininka mahaifinsa". Maganar ta zowa bobbo a bazata.....kamar yadda asalin salsalar maganar da sigar maganar ta canza daga anihin ma'anarta.
Duk da yadda maganan ta saukarwa bobbo a bazata,amma hakan bai hanashi sakin dan qaramin murmushi ba.
"Sultane......yaushe aka fara nemawa mace kuma auren namiji......har abada namiji ne yake neman auren mace". Kai sultane ya jinjina a nutse.
"Na sani......na sauya ma'anar ne.....na sauya yadda asalin yake,cike da fatan wannan sauyin ya zama tabbatacce har a qarshen rayuwar khadeeja". Cikin nazari qwarewa da sabo da aikinsu da security intelligence bobbo ya zubawa sultane idanu. Koda sultane bai zurfafa magana ba,koda bai zurfafa bayani ba ya fahimci kai tsaye daga zuciyarsa maganar take fitowa.....kai tsaye yake maganan daga ma'ajiyar dukkan lafuzzansa na gaskiya......hakanan ya karanci wani abu lullube a bayan furucinsa dake taba zuciyarsa.
"Sakin aurenta a kwanaki uku ne zai sanya sultane ka sake nema mata wani mijin?" Murmushi sultane ya saki a nutse yana girgiza kansa.
"Na maimaita istikhara a kwanakinnan har bansan adadi ba Akwai abubuwa masu tarin yawa da bansan yadda zan bayyanawa kowa yadda nakejin sukarsu a qirji da zuciyata ba......amma nasan abu daya da yayiwa tunani na da fatana karan tsaye shine......MAGANGANUN SAFIYYA WANI HASKE NE.....wani mabudi ne da sai a yanzu nake zurfafa tunanin zasu zama wani SANADI a rayuwar akhnan. Ba kalar wannan qaddarar na shirya gani a rayuwar biftu ba muhammad..... Wannan ya sanya na RUNGUMI kalaman safiyya a yanzun da dukkan nazari da dacewa a bisa ma'auni.......namiji me addini shine zai zama silar bango garkuwa da kuma me jangorar rayuwar akhnan bisa hanya me kyau.......ban shirya bawa diyata kowa ba sai HAISAM.....bari kaji dawud.....na jima ina kawaici.....na jima ina bege da fatan zukatansu su hadu guri guda.....to amma abun tsoron sai na fuskanci akwai wata irin tazarar nisa a tsakaninsu. Tun daga sannan na duqufa da addu'ar haduwar zuciyarsu da kawunansu,don ko tahowa nan da nayi jigon silar zuwana itace wannan addu'ar,cike da fata da kuma sanya rai....ban kuma cire tsammani ba har sai ranar da aka gayamin shi da kansa ya bada aurenta ga wani......ashe duka duka cikin kwanaki uku jarrabawar da kokwanton amsuwar addu'o'ina dukka zasu qare......"
"Dawud...." Sultane ya kira bobbo kai tsaye,bai amsa masa ba,amma kuma yaci gaba da dubansa.
"Nayi bacci har sau uku cikin raudha bayan na gama addu'o'ina da istikhara ta.......haisam nake gani a mafarkina da zarar bacci ya daukeni.......yana farautar duk wani abun farauta daga namun daji da suka kawowa akhnan hari......mafarkina na qarshe kuma tana boye a bayansa ya zame mata GARKUWA......kayimin alfarma.....kayimin kuma jangora haisam ya zama GARKUWA na gaske ga marainiyar d'iyata......" Yayi maganar zuciyarsa tana motsuwa saboda tuna safeena da yayi.
Wani abu ya ratsa bobbo,mamakin wani nannauyan abu me girma da yake hangowa cikin idanun sultane yana kamashi. Saidai sultane bai barshi haka ba,a nutse ya warware masa labarin SAFEENA da ya gangaro zuwa ga rayuwar akhnan.
A cikin labarin ya dasa ayar tambayoyi masu yawa......a ciki ya dinga hasashen al'mura masu yawan gaske.......saidai yayi imanin muddin haisam ya wanxu cikinsu ya rayu dasu na wata guda.....yana da tabbacin zai wahala baida labarin komai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 75*
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
"Zan shige maka gaba sultane....kafi qarfin komai a tare dani......"
"A al'adarmu,magana me girma irin wannan tana farawa ne daga iyaye ba daga yaro ba,yana da kyau ta fara daga iyayensa dama wadanda suka raineshi,don haka ina son ka tambayamin iznini,Amma kuma ina neman alfarma ka barni na nema alfarma ta bangaren haisam da kaina,Zan kira haisam da kaina,bawai don na tilastashi ba....ko don yaji kunyata ya amince ba.....aah,kowanne kamilin mutum iri haisam ya cancanci a bashi zabi da dukkan girmamawa".
"Nayi maka" Obbo yana sakin murmushi,saidai kuma akwai tarin tambayoyi fal kansa.
Sanda sultane ya fice ya barshi a dakin shi kadai,sai komai ya dinga dawo masa. Haka kawai yakejin akwai wani abu cikin rayuwar yarinyar,haka kawai yakejin wani karsashi na yin magana da motii,don haka sai kawai ya maida dakin ya kulle,ya kuma koma saman gado ya zauna bayan ya dauki wayarsa yana laluben motii din.
*HAISAM*
Kamar kowanne dare yana takawa a nutse gami da bin sahu sahu na masu gadi da tsaron gidan don tabbatar da komai akan tsari. Fitowarsa kenan daga ganawar da sukayi da wazeer,duk da cewa dare ya fara yi amma hakan bai hanashi duba amanar dake hannunsa ba.
Simple throbe ce a jikinsa da wasu tausasan flip-flops masu daukan hankali. Daukan hankalin har yakai kan idanun duk wani hadimi da zai giftashi.
"Qasaitaccen malami ne mutumin nan.....ban taba ganin malami irinsa ba......wani irin kwarjini yakemin,idan yana guri sai naji kamar ina tare ne da sultane"
"Bakai kadai ba.....kusan dukkaninmu da zaka zagaya kayi quri'a haka kowa zaice maka yana ji" Hirar da wasu hadimai biyu kenan keyi sanda yabar gurin yana takawa zuwa qofar gaba.
Shi da abdii suke tattakin,duk da yadda yaso abdii yabi su maleek zuwa personal home dinsa ya kwana amma yaqi. Hannunsa cikin aljihun throbe dinsa sanda hadimin dake gabanshi yake bashi bayanin yadda suka wuni. Yana maganar ne cikin wani irin tsoro,bawai na rashin gaskita ba.....aah tsaiwarsa a gurin da yadda ya kafeshi da farare sol din idanunnan nasa kadai suna sanyashi yaji hantar cikinsa tana kadawa.
A zahiri hadimin yake kalla,saidai kuma a badini maganganun morsa safiyya ne suke dawo masa akai sama da maganganun da sukayi da nanay ma akan saamee. Baisan me ya sanya ba.....baisan meye dalilin daya sanya maganganun suka tsaye masa haka a rai ba. Abinda ya dauka a wancan lokacin,koda tace yaje yayi tunani akai,yana ganin ba wani gurbi ko muhallin yin tunani akan auren da bai shirya ba.....akan kuma yarinyar da ya tabbatar kanwarsu ba zata taba jiquwa ba guri guda. Alqawari ne qwaya daya tal! Daya daukarwa ransa,kuma bayajin zai fasa ko ya ajiyeshi shine neman AHAMAD da jaririn dan uwansa dako suna ba'a bawa ubansa daman ya sanya masa ba.....wannan shurun da suke zato ko tunanin KARIYA ce.....zai ballaata da dukkan hikimarsa ikonsa dama qarfin qwanjinsa. Shuru akan wacan jaririn ya tabbatar shine ya bada qarfin gwiwa da dama me qarfin gaske akan ahmad.
Hannunsa kawai ya zard daga qirjinsa yana zurawa a aljihun rigarsa saboda sassanyan ringing mara hayaniya. Da hanzari abdii ya matso yana miqa masa wayar,sai ya sanya hannu kawai ya karba don ya manta ma wayoyin suna hannun abdii.
Screen din ya kalla sosai,a nutse ba tare daya daga kai ba yace.
"Zaka iya komawa bakin aikinka" Ya fada still idanunsa suna kan kiran,har zuwa sanda ya fara takawa a nutse yana daga wayar hadi da karawa a kunnensa.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Yayi cikakkiyar sallamar da ko yaushe take sake tunawa sultane muhimmancin sallama,take kuma sake sanya masa qaunar haisam da nutsuwa da halayensa.
"Wa'alaikumussalam muhammad haisam.....ina fatan ba takura maka ba da kirana a wannan lokacin?" Dan sirrintaccen murmushi haisam ya saki,nutsuwar kamilim dattijon tana burgeshi,tausayinsa da kuma zuzzurfan abubuwa masu nauyin gaske dake binne cikin masarautarsa ba tare daya sani ba suna dawowa haisam din.
"Ko kadan,kiranka tamkar girmamawa ne a gareni" Kai sultane ya gyada a nutse,yana jin wani abu me sanyi yana saukar masa.
"Na gode sosai da wannan kalar fahimta da kuma girmamawa,ban sani ba ko muhammad yana wani abu?,sultane yana so yayi magana dashi". Yanayin yadda sultane din yayi magana kadai ya sanya haisam din ya fahimci magana ce me muhimmanci da gaske,don haka ya taka a hankali ya samu wani concrete chair dake daura da sassansa ya zauna. Guri ne dake da wani irin kyau,wanda dama tun daga nan har zuwa cikin kebantattun sassanninsu gurare ne da yanayinsu yasha banban da yanayin kowanne sashe na gidan.
"Kowanne lokaci da zaka buqaci magana dani a shirye nake".
"Na gode haisam" Ya furta yana jin nauyi da kwarjinin haisam din,duk da cewa bawai yana kusa dashi bane.
"Muhammad......inason nayi magana dakai a yau a matsayin UBA ba'a matsayin SULTANE ba"
"Ina saurarenka ranka ya dade" Ya fadi da hausarsa dake gauraye da yanayin yaren oromo daya kama harshensa da kyau,kai kace bafillacen nigeria ne.
Numfashi sultane ya sake,yana ji lokaci yayi da zai fidda dukkan abinda yake ransa,yana jin lokaci yayi da zaiyi wannan aikin,wannan hobbasar,lokaci yayi da zai samawa diyarsa GARKUWA BANGO KUMA MAJINGINA. Yanaji a jikinsa rayuwar akhnan haka kadai ba tare da samun TSAYAYYEN bango majingina ba.....kamar wani abu yana dab da samun rayuwarta ya kuma lalatata. Zai iya jure komai amma banda shafewar JINI kuma irin safeena daga duniya. Ya jure salwantar Ahmad saboda a sannan yana sanya rai safeena zata rayu dashi,rayuwa me tsaho,zata kuma haifa masa wasu yaran da zasu shafe fiye da rabin gurbin rasa ahamd da sukayi,walau maza ko mata,sai gashi ashe duka duka rayuwar tata gajeriya ce.....ashe ba dogon zama a tsakaninsu.
"Muhammad......kana cikin mutanen dake da masaniyar komai daya shafi akhnan.....koda ban zauna maka dogon sharhi ba,tunda kusan tun daga zabar miji har zuwa mutuwar auren abune daya faru gaban idonka". Kai ya gyada a nutse,yana jin a ransa me ya hado zancan yarinyar dashi?,qasan ransa yana fata ba wani jagorancin ko nauyin sultane zai sake aza masa ba akan lamuranta.
"Gaskiya ne" Ya fada a nutse.