L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 4
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 4: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 4. *MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
3,332 words
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE06* _________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _______________________________
A nutse ya sunkuya ya kuma fara sanya qarfen allurar cikin fatarta yana kallon yadda take shiga a hankali. Idanunta ta juya a hankali sanda tsinin allurar ya caketa tana dagasu zuwa sama inda take iya hangen blurry face dinsa. Yanayin buguwar poison din a jikinta ya sanya take ganin fuskarsa kaman dab da tata......yake kuma sake maida fuskarsa zuwa ga wancan ranar wadda ke lullube da yadin rawanin daya zagaye habarsa dashi.
Allurar na shiga tana jin ganinta yana sake daidaita,yanar data rufe ganin nata tana wankewa tana qarawa ganinta qarfi,wannan ya sanya kafin ya gama mata allurar wadda ake turata zuwa jikinta a hankali a hankali ganinta ya dawo tar.......ya kuma bata daman ganin fuskarsa sosai da clear view.
Zare allurar yayi,falaak ta sanya hannuwanta dukka biyun ta amsa ta taka zuwa ga dustbin ta sanyata a ciki,wani abu yana motsawa sosai a qirjinta game da haisam. Kusancinsu a yau,yanayin yadda yayi allurar cike da qwarewa da takatsantsan. Ita din dalibar lafiya ce,amma daga yadda yake allurar ta tabbatar akwai qwarewa me tarin yawa a cikin aikinsa.
"Zan wuce" Ya fadiwa sultane a taqaice cikin girmamawa. Kai sultane ya jinjina,ya fahimci baya buqatar ci gaba da zama a cikin su,amma yayi masa dukkan abinda ya kamata yayi,ya katse uzurorinsa da dama saboda matsalan iyalinshi......duk da cewa inda haisam zaici gaba da wanzuwa a tare dasu zaiso hakan,to amma kuma bai kamata ya qure kawaicinsa da yakanarsa ba,don haka yace
"Na gode qwarai sheikh muhammad......na gode"
"Allah ya bata lafiya" Ya furta a tausashe da yanayin daya sanya morsa safiyya sake ganin kimarsa,su ukun kuma sultane morsa safiyya da falaak suka amsa da ameen.
Yana takawa don ficewa mammina ta aza idanunta a kansa. Akwai tarin abubuwa da yawa......akwai tarin damarmaki da take dasu ta samesu a yanzun......akwai hanyoyi da suka bude mata da zata iya bata tsakaninsa da sultane......a gabansa takeson yin haka,amma batasan wanne irin kwarjini gareshi ba da ta kasa tsaidashi bare ta fadi Koda abu guda daya a akanshi da zai jefa koda kokwanto da wasiwasi a zuciyar sultane.
Sai daya kammala ficewa tas sannan ta maido hankalinta dakin,yanayin takunsa daban yake da takun data saba gani......akwai wani abu me girma da nauyi a cikin character dinsa.
Numfashi ya sauke sau uku a jere don ya samu yayi calming kanshi. Abubuwa da yawa......abubuwa da yawa idanunsa da kwanyarsa gaba daya suke hange.
Wayarsa ya sake fiddawa,sai ya samu miscall din su abdii ya qaru,wannan karon harda na omar,ga na maher daya tabbatar yana dai ci gaba da jiransa ne.
Duka bai kirasu ba,don bayason dogon magana ko dogon bayani,omari kawai zaifi fahimtarsa kaman yadda aka saba,don haka shi din ya kira kai tsaye.
Bugu daya ya daga da cikakkiyar sallama,haisam ya amsa masa can qasan maqoshinsa.
"Kazo ka dauke yaron nan abdii,ya sakani a gaba da tashin hankali,wai yayita kiranka baka daga ba,maher ma kuma yacemin ya kasa samunka,gashinan zaune kaman zai fashemin da kuka?".
"Ka cewa maher na daga fitan sai gobe......ka gayawa abdii ina lafiya,amma yau kam duka bana buqatar shashancin nan nasa........please ka karbi mota gurin salana kazo ka daukeni".
"Yanzu?" Ido ya lumshe yana girgiza kai.
"No.....zanyi wanka ne"
"Amma maher yacemin ka shirya har ka fito kuma".
"Eh.....wani dalili ya sanyani komawar". Ya furta very calm,yana fatan shima omari din kada yaja maganan da tsaho.
" Xan shigo palace kenan da motar?".
"Idan tunaninka ya kwance omar zaka iyayin hakan" Ya amsa masa a gajarce kawai yana kashe wayar,sannan ya sanyata a aljihunsa yana ci gaba da komawa sashensa na cikin gidan.
"Astagfirullah" Yaketa maimaitawa sanda yake fidda kayan jikinsa,kayan da bai taba tunanin akwai wani abu da zai sanyashi dawowa nan kurkusa ya canzasu ba.
Ruwa me matuqar dumi yana sauka saman kansa idanunsa na runtse yana tambayar kansa.
"Why?,me yasa ko yaushe sai ita?" Ya tambayi kansa yana jin wani abu yana bin sassaj jikinsa da ya sanya jikinsa wani mugun mutuwa tubus.
Zai iya rantsuwa da Allah hannunsa bai taba kaiwa jikin kowacce d'iya mace ba. Yana bala'in kame jinsa ganinsa dama hannuwansa harda qafafunsa daga dukkan wani abu irin wannan. Amma me yasa ta zama mace ta farko da gangar jikinsu keta haduwa haka?,ba daya ba ba biyu ba?,kusan sau uku kenan,kuma dukka ta dalilin wani abu?.
Zuciyarsa tana yin sanyi idan ya tuna komai bai faru bane akan son rai ko son zuciyarsa,ya faru ne kan akasi kawai irin na dan adam.
A gurguje ya shirya,don akwai maganganun da yakeso yayi da omar masu muhimmanci. Ya taka a nutse tun daga sassansa har zuwa ficewarsa daga gidan,yana takawa a nutsensa har zuwa inda suka saba tsaida mota su jirashi.
Tun daga nesa da omar ya hangoshi ya bude masa gaban motar kusa dashi,don yadda haisam din ya bashi command ya sanya baima sa salana ya tuqoshi ba,kawai sai ya karbi motar.
Tab ne a gabansa wanda yake video call shi da maleek da naseeb. Naseeb din suna guri daya da maleek ne saboda ziyara daya kai masa. Duk da yadda aiki ya banbamta musu guraren rayuwa,amma hakan baya hanasu kaiwa juna ziyara lokaci bayan lokaci. Kowa a cikinsu yana iya ziyartar dan uwansa a duk inda yake,kafin lokacin da suke haduwa ta lokaci guda dukkaninsu yayi.
Da tattausar muryarsa yayi sallama yana sako gangar jikinsa cikin motar,sam hankalinsa baya kan tab din,baima lura da ita ba,yayin da idanun maleek da naseeb da sukayi shuru suna son surprising nasa yake kansa cikin murmushin nan dake cike da soyayyar juna.
Hannu ya bawa omari sukayi musabaha kafin ya zame hannun yana azashi saman qirjinsa,sai kuma ya sake zame hannun yana neman madannin da zai bashi daman kwantar da kujerar yadda zai samu daman yin relaxing sosai. Tsaiwa kawai yayi yana kallon screen din,yayin da naseeb ya saki dariya sosai,maleek na tayashi ta hanyar murmushi kasancewar shima din ba ma'abocin yin dariya bane kaman dai haisam din.
"Mr lowering gaze......wai meye hakan?" Maleek ya tambaya da yanayin sarauta cikin jininsa shima kamar dai haisam din. Kai kawai haisam ya girgiza murmushi yana qwace masa,omari ya shammaceshi,hakanan wannan karon yaji kunya ta yadda aikin gaba daya ya shagaltar dashi daga barin nemansu.
"Wanne irin aiki ne ya shagaltar dakai haka?.....na dauka wata me rabon muka samu data dauke mana hankalin sheikh dinmu?" Maleek ya sake fadi yana murmushi.
"Ka sani ko ya samu nasarar kammala aikinsa da kuma gwagwgwabar kyautar princess of agadez?" Naseeb ya fada yana dariyar tsokana. Tsokana dabi'ar naseeb ce,har sun riga sun saba da haka,amma wannan karon maganansa ta yiwa haisam girma tare da maido masa mode da dabi'u dukka na akhnan daya sani,da sauri ya furta.
"A'uzubillah......a'uzubillah" Gami da miqa hannu ya kashe gaba daya karatun qur'anin dake tashi can qasa ta speakers din motar.
Harara ya fara watsawa omari........ya tabbatar akwai wata magana da suka fara dasu naseeb din,sai omar din ya fuske gami da mazewa yaqi yarda ya kalleshi,duk da yadda yakejin nauyin idanuwansa kamar kullum
"Don Allah......na roqeka wannan maganan ya fita a bakinka naseeb koda wasa kake......ban shirya wasa da zazzafar wuta ba" Ya qarashe maganan yana hade tafukan hannayensa biyun guri guda alamun roqo.
Dukkansu dariya ya qwace musu,maleek ya jinjina kai sannan yace.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Me kake tsoro obbo?......There's no woman on earth you can't deal with". Kansa ya jinjina a hankali yana kadashi. Ya lumshe idonsa a nutse sannan ya bude yana motsa labbansa da yanayin daya tabbatar musu akwai gajiya a tattare dashi,walau ta jiki kota tunani.
"I want peace always.......am not interested in drama". Maganansa ya sanya omari da naseeb sakin qaramar dariya,yayin da maleek yayi murmushi.
Kasantuwarsu daga gidan sarauta dukkansu shida haisam......hakan ya sanya akwai kamanceceniya na wasu dabi'u a tsakaninsu,don haka duk cikinsu bakwai din yafi kowa fahimtar haisam,saidai yafi haisam din mu'amala da 'yammata duk da cewa tsaftatacciyar mu'amala ce da yake sanya ran zaben matar aure a cikinsu. Kai ya gyada yana duban haisam din
"Kaima kasan ka taro match......tunda ka kayar da ita a gasa cikin yankinta". Kansa ya juya kadan,sai yanzu yanayin kallon da take masa ya dawo masa. Ya sani,ya kuma fahimta tanason fahimtar cewa shine abokin takararta ne,duk wani motsi da acting nata ya nuna masa hakan,saidai shi kuma sam bazai taba bata wannan damar ta gano komai ba. Ba drama ko wasa bane ya kawoshi yankinsu,ya kuma kawoshi masarautarsu,yazo ne kawai ya kammala wani aiki ya fice ya koma zuwa qasarsu. Aiki ne da zai tabbatar da zaman lafiyan iyayensa......zaman lafiyar qasarsa......da kuma zaman lafiyar yankinsa da qabilarsa.
Akan wadannan abubuwan daya lissafa ba shakka zai iya sadaukar da komai,shi yasa yakeji a cikin jikinsa da jininsa......ya shirya tunkarar komai don cimma nasara,musamman a yanzun da yake ganin wasu kebantattu kuma baqi sabbin abubuwa suna gilmawa ta gabanshi.
Hira sukai sosai irin ta abokai shaqiqai da suka saba da juna,hirar har takai sai da aka tabo su mutallab,dukkansu suka hadu cikin video call din cikin yanayi na kewar juna,duk da haisam din kusan yayi relaxing ne cikin kujerar,sai daya biyu kawai yake jefa bakinsa yayi murmushi a wuce gurin.
Sun saba da irin dabi'ar nan tasa,musamman a lokutan da bayason dogon magana,suma kuma sun iya tafi da 'yan miskilancinsa.
*AGADEZ PALACE*
Dukkaninsu hankalinsu idanunsu dama numfashinsu dukka sun tsaidashi ne akan doctor hadizatu data kasance qwararriyar likitar dake aiki cikin masarautar,qarqashin babban clinic na masarautar da yake aiki don duba marasa lafiya na cikin gida da ciwukansu basuyi girma da yawa ba.
A hankali ta zare allurar da kafin ta kammalata ta jiqe da gumi,allurar da tayi ta cikin cannula cikin takatsantsan da nutsuwa.
"Alhamdulillah" Ta fada tana goge fuskarta da handkerchief tana kuma kallon yadda gumi ya fara jiqa goshin akhnan.
Falaak ce ta sanya tattausan handkerchief din da aka kawo cikin tarkacen da aka ajiye a gurin ta soma share mata goshinta,yayin da aisa ta dauki remote tana dan qara qarfin Ac din dakin.
"Anyi nasara gubar ta fara sakinta in sha Allah,ga alamu nan.......amma tabbas lallai duk wanda ya kawo idea din mata allurar farko ba qaramin sanin abinda yakeyi yayi ba......allurar ta taimaka qwarai wajen saurin saukar da tasirin allurar da akayi mata yanzu.......sannna ta dakatar da harbuwar gubar zuwa sassan da idan ta tabasu to xai wahala a samu rai da rayuwa,kamar hanta qoda hunhu da kuma zuciya" Sosai wani irin kima da qaunar haisam ta sake samun kyakkyawan gurbi a zuciyar sultane. Da gaske muhammad din ya zama wani sashe me muhimmanci a tattare dashi raywarsa dama ta iyalinsa.
Baya tunanin inda bai wanzu a gurin ba akhnan zata kai wannan labarin da akeyi a yanzu......lallai yana sanya rai yana kuma kyautata zaton ubangiji ya laluba cikin tulin tarin ayyukansa ya aiko masa dashi ne kawai.
"Zata iya bacci har na awa kusan uku ko hudu,kada a tasheta,a barta ta huta sosai......idan ta farka kada ace mata komai,ku jira abinda zata soma cewa,sai a sanar dani da zarar ta farka,so samu gurin ya zama so quite" Kai morsa ke jinjinawa tana kuma fahimtar bayanan doctor hadizatu sosai.
"Ina ganin ya kamata abarta hakanan ta huta......."
"Aisa........falaak.......shehnaz.......ku zauna tare da 'yar uwarku,ku bata duk kulawar data dace har zuwa sanda zata farka". Morsa safiyya ta furta da wata kalar izza da take bayyana kanta da kanta a tattare da ita,tayi kuma maganar tata kanta tsaye ba tare data dubi koda shiyyar da mammina ke tsaye ba,wadda ke shirin tsara yadda za'ayi ta yadda zai dace da plan dinta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 07* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
"Hakan yayi.....don Allah.....wannan din ba qaramin abu bane da wasa ko shashanci zai shigo ciki,ku kula da ita da kyau,duk wani motsi da zai zamana kuna buqatar wani kuna iya kira" Nannie da tunda tazo ta samu guri ta zauna,gwiwarta tayi wani irin sanyi da bata taba jin tayi makamancinsa ba.
Hankali cikin kuma wani irin salo me kama da gilmawar walqiya ta shanye duk wani mamaki da bacin rai daya saukar mata na katsalandan wa umarninta da kuma hambarar da iyakokin da take qoqarin shatawa.
"Gaskiya ne.....don a wannan yanayin dole ku sake ninka kulawarku a kanta......kada sakacin da mukayi a baya ya sake maimaituwa......kada kuyi nesa da ita don Allah koda na sakanni ne" Mammina din ta fada tana sanya gefan tattausan mayafinta tana dauke hawayen daya gangaro mata.
A nutse morsa safiyya ta waiwayo ta kuma aje mata wani irin kallo kafin ta dauke kai. Har yanzu zuciyarta bata aminta ba bata kuma tsaya guri daya ba......amma kuma wani sashen na zuciyarta na gaya mata.
"Inda mammina ce.....inda mammina nada plan na kashe akhnan da bata kawo war haka a raye ba,bata kasheta a sanda take da cikakken dama a kanta ba sai yanzu data mallaki hankalin kanta?.
Kusan dukkansu morsa safiyya mammina nannie da kuma sultane suke fitowa daga bangaren akhnan din.
Ba wani a cikinsu da yake da kuzarin yin magana a cikinsu,duk kuwa da cewa kowa magana ne fal bakinsa.
"Ina gayyatarku zaman cin abinci gobe da daddare" Abinda sultane kawai ya fada kenan,abinda kuma yake gaya musu a yau bashi da muradin ganin kowa,sai yayi gaba yana ci gaba da takawa don isa farfajiyar da zata sadashi da hadimansa daya tabbatar suna nan tsaye suna jiransa a inda ya dakatar dasu.
Morsa safiyya ce ta soma yin gaba ba tare data waiwayo ko tace da kowa komai ba. Nannie ta bita da kallo kafin ta maido dubanta kan mammina.
"Har yanzu na kasa aminta da cewa biftu ce da kanta ta dauki guba tasha saboda qiyayyar auren wani?". Kaman dazun,hawaye masu yawa ta tsane da gefen mayafinta daya kasance cotton.
"Ni kaina Nannie banda an gaya min dama a jiya da magabatan hakeem suka iso da dukiyar aure ta fadi saita sha gubar,a gaban aisa da shehnaz da sauran hadimanta,wanda duka sai dana bisu daya bayan daya na tabbatar ta fada din......to amma kuskuren da nayi shine dana dauka abun shirme ne kawai,bawai tana fada bane da gaske.......ashe da gasken take,don Allah ku yafemin Nannie.......ki bawa me martaba haquri,a yau a karon farko yarda da tabbaci da ya bani akan d'iyarsa.....a karon farko na kasa.......na gaza,nayi sakacin barin magana irin wannan har taso tayi sanadin d'iyarsa tilo" Ta qarasa fada tana kama dukkan hannuwan Nannie ta riqe cikin nata tana sakin kuka me qaramin sauti.
Sosai abun ya taba Nannie,bata taba ganin soyayya irinta mammina da akhnan nan,saita riqe hannun mammina din sosai itama.
"Haba zaituna?......meye haka kikeyi?,kin manta matsayinki cikin gidan nan kuwa?,idan wani cikin hadimai yazo wucewa fa?".
"Na cancanci inyi wannan kukan Nannie,ku barni nayi ko zan daina jin kasawata akan akhnan"
"Baki kasa ba zaituna......shekara nawa take qarqashin kulawarki?,daidai da mummunan zazzabi bata taba yinsa ba,duk mutumin da zai kwashi wannan shekarun.....dondai kwana daya faruwar abinda baida ikon tsaida faruwarsa bai kamata a tuhumeshi ko ya zama abun tuhuma ba akai". Ta fada da sigar lallashi.
"Allah yasa morsa safiyya ta fahimci hakan.....Allah yasa ta gane haka" Ya fada muryarta tana rawa.
"Zata fahimta muddin ita din ba butulu bace" Nannie ta amsa da dukkan confidence dinta.
Murmushi ta saki sirrintacce a sanda suka juyawa juna baya. Nannie tayi hanyar da zata sadata da sassanta,itama kuma ta juya son isa ga nata sassan.
~ "Idan har tasan tayi iqirarin shan wani abu da zai iya cutar da lafiyarta......idan har tasan halinta na shekara da shekaru a matsayinya na wadda ta raineta.....idan har ya kasance ta kauda kai daga dukkan wannan ba tare data shaidawa kowa ba koda barazana ne ayi don dakatar da afkuwar abun.......lallai akwai babbar ayar tambaya a ciki.......akwai wani shiryayyen mission da nake iya sansanowa......" Omari yayi maganan yana qanqance idanunsa ciki,yana jin kuma wani abu yana jan hankalinsa sosai akan maganar.
"Omar" Haisam ya kira sunansa da alamun gajiya cikin muryarsa.
"Ba wannan maganan nakeso ka maida tunaninka akai ba......duk abinda mukaji......ko muka gani haka zamu barshi a yadda muka sameshi.......ba saboda wannan matsalar muka shigo masarautarsu ba.......ba qididdigar alaqar dake tsakanin junansu mukazo tantancewa ba......abinda ya kawomu kawai shine neman gujajjen me lafin da yaso bata mana alaqar diplomatic na qasashenmu........let's prioritize the mission" Ya furta da seriousness dinsa.
A nutse omari ya daga kai ya dubeshi. Ba tun yau ba,ya sani cewa mutum ne bame yawan shiga sharafin wasu ba,amma kuma hakan ba yana nufin bashi da tausayi ko taimako ba...... Yana da wata irin zuciya me taushi,duk da cewa wasu lokutan yana da kafiya da kuma zafin rai akan abinda yake gaskiyarshi kenan,amma a nan bai dauka zai wofantar da al'amarin da a yanzun da kanshi ya gama zube masa lissafin yadda hasashensa yake iya hangen komai ba.
"Amma.......what about your....."
"Ban hada maka zancansu dana aikinmu ba don ya zamana zamu sakashi lallai lallai cikin ayyukanmu ba......na hada maka ne don ka fahimta,ka kuma gane hasashena yayi daidai na sanya matar ta zama cikin sahun mutane na gaba gaba da zamu tsananta sanya idanu a kanta ita da duk wanda ya rab'eta?.......that's it" Idanu suka zubawa juna shida omari din,kafin omari ya janye nasa kallon bayan wasu sakanni.
"Amma ka sani.......ko akwai wani dalili da Allah ya aikomu a irin wannan lokacin cikin gidan?......ba lallai ya zamana dalilin kawai shine ceto martabar Ethiopia kadai ba........."
"Da kuma ceto rayuwar halitta mafi soyuwa a gareni MOTII.....kammaluwar aikin nan shine zai bani guarantee na safety din motii,bama motii kadai ba.....harda nanay dama duk wanda ya kwana ya tashi cikin aba jifar palace" Ya qarashe maganan da wani irin yanayi a muryarsa da idanunsa.
"Bazan hanaka ba taimako ba idan ka shirya yi......amma dole ya zamana bayan aikinmu ne bawai a ciki ko a gaban aikinmu ba........take heed.........akwai wasu mutane cikin masarautar da zargina ya soma sauka a kansu......akwai wasu mutane da bansan yawan adadinsu ba a masarautar da nake da tabbacin suna da alaqa me qarfi da oromo.......bansan su nawa bane,amma mutum biyu daga ciki masu suna iri DAYA sune suspect dina na farko. Tabbas akwai alaqa tsakaninsu da matar......saidai bansan iya zurfin alaqar da adadinta ba......sannan su nawa ne masu jin yaren?,tana cikin masu jin yaren ko wata qabila ce ita daban cikin Ethiopia bawai oromo ba?,akwak.kebantaccen dakin dakin daya zama na musamman kuma mallakarta ita daya,ta yaya zamu kai ga cikinsa?.......ta yaya hakan zai taimakemu zuwa ga inda ainihin me laifinmu yake?,.....wadannan sune abubuwan da zamuyi aiki akai yanzu.........salawi da beeno dukkaninsu zasu tattaro su dawo daga garuruwan da aka turasu,zasu kama haya cikin daya daga cikin gidajen dake daura da masarautar.......sannan kaima......" Sai kuma ya dakata kadan.
"Nima zan antayo cikin gidan?" Kai ya girgiza a nutse.
"Bana tunanin zaka hau wannan position din,saboda tunaninka da daidaiton da nake da buqata a gareka kaman yayi low,baikai adadin da nake buqata ba". Qaramin dariya omari ya saki,ya sani haisam ya fadi hakane saboda ya shigo da batun akhnan da case din cikin gidan cikin aikinsu.