Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 5

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 5

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 5: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 5. "A duk sanda ka shirya kawoni kusa da kai ina maraba" Ya…

3,368 words

"A duk sanda ka shirya kawoni kusa da kai ina maraba" Ya furta yana miqa hannu gami da tashin motar. Dubansa yayi kaman zai tambayeshi sai kuma ya fasa,omari din ya fahimci haka,yasan kuma tunda yayi hakan miskilancinsa bazai bari ne ya tambaya din ba,sai ya buda baki a nutse.

"Zan kaika wani guri......ina sanyan ran zaka samu kalar yanayin da kake buqata" Be amsa masa ba,saidai ya jawo system dinsa da yasa omari din ya fito masa da ita,ya azata saman cinyarsa ya kunnata sannna ya fara shigar da bayanan da yake da buqata. Ganin haka sai omari din ya maida karatunsa yana sanyashi a matsakaicin sautin da bazai dameshi ba.

★★★ Idanunta ta sake maidawa ta lumshe gami da jinginar da kanta da fuskar gadon da take kai. Kusan dukkan wanda ya shigo tsakanin Nannie.....mammina......aisa...shehnaz.....harma da falaak maganganunsu dukka akan abu guda daya suke maimaitawa. Abu guda dayan da itadai batasan dashi ba,batasan kuma da zamansa,batasan ma yaushe ya faru ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Abu daya ta sani tasan kuma ta furta,ZATA SHA GUBA wanda bayan janyeta da shehnaz da aisa sukayi zuwa daki maganganunsu sun sanya wannan kalamin ya zagwanye daga zuciyarta tas ya fice,taji kuma bata da wani sauran marmari ko niyyar aikata komai,ta kuma kwanta ranta ba komai face zallar zugi radadi da fatan janyewar sultane daga dukkan qudurinsa da yasha alwashi akai......ta kuma kwana ne da zazzabin data dinga jinsa sosai cikin jikinta,baya ga haka ba wani abu data wayi gari dashi a ranta a ranar.

Abu na biyu birra.....birra na cikin amintattunta da tayi imanin koda zabin a kashe akhnan ko a kashe birra dinne.......yarinyar zata zabi mutuwarta akan wani abu da zai taba lafiyar akhnan din. Uwa uba kuma ma shine,a gabanta birra ta gama hada komai suka fita a tare. Ba wai tana wani guri bane na daban aka hada mata tea din,da normal ruwan da ta saba amfani dashi cikin gidanne,to amma yaya akayi aka samu wani abu ya shiga har cikin tea din dabai dauki tsahon lokaci ba daga hadashi har zuwa shanyeshi?.

Wani irin daurewa kwanyarta kawai take sakeyi da wani dogon tunanin da bata hangi hanyar da zata samu tarin tambayoyin dake sarqafe da ita ba,uwa uba ba wanda ya tsaya ya saurari komai daga bakinta,sai tarin fada da nuna mata kuskurenta da kowa yake qoqarin yi. Abinda yafi daga mata hankali rashin ganin koda gilmawar sultane tun jiya kawo yau din,ba kuma wanda ya mata maganarsa ko yace komai a kansa. Abu irin wannan idan har zai sameta ta tabbatar sultane zai iya zama mutum na farko da zai kasance tare da ita bayan mammina.........idan bai zama na farko ba saboda tsananin kulawa da damuwa da al'amuranta da mammina takeyi to lallai babu abinda zai hanashi kasancewa na uku.

Itama batayi yunqurin kare kanta ba ko kadan,saboda batasan ma idan ta bude bakinta me zata ce ba?. Da wannan kalar tunanin birra ta nemi izinin shigowa dakin,ta kuma murda handle din ta turo qofar da sallama ta shigo.

Idanunta ta ware a hankali tana dubanta,a nazarin farko ta karanci zallar tashin hankali da rudanin dake kwance saman fuskar yarinyar. Ko digo a ranta bataji akwai wani mugun nufi da zai fito daga bangaren birra din ba,muryarta can qasa tace.

"Ranki ya dade......lokacin wankanki yayi.....zan shiga na hada ruwan wankan,nace ko zaki kasance tare dani a yayin hada ruwan?" Ta tambaya jikinta yana rawa da zaka iya hanga idan ka zuba mata idanu.

Zare dubanta akhnan tayi daga dubanta,muryarta can qasa ta bata umarni nakai tsaye.

"Shiga ki hada" Kawai tace da ita. Ba musu ko saba umarni tsakaninsu daga gurin uwar gijiyarsu,hakan yana daidai da aikata laifi me girma,don haka ta taka tana wucewa shiyyar da bandakin yake.

Bata jima ba ta fito dauke da bathrobe me azabar laushu fara qal da takalman wanka,wanda kusan duk bayan kwanaki ake sauya mata su,kuma idan aka fiddasu ba'a dawowa dasu sun gama aiki kenan.

Tsugunnawa tayi ta ajiye mata takalman,ta ajiye rigar a gefanta sannan ta taka a hankali ta nufi wani sashen na daban inda facial care products dinta suke da tame using wasu kafin ta shiga wanka wasu bayan ta figo ta dauko box dinsu gaba daya don sauqaqe mata tashi zuwa inda ta saba zama tayi amfani dasu. Saidai tana takowa ta mata alama da hannu ta juya ta maidasu.

Da taimakon birra din ta shirya cikin wasu sauqaqan English wears riga da skirt. Sai fuskarta tayi wani fayau,ramar da tayi tsakanin jiya da yau ta fito sosai kamar wadda ta shekara tana ciwo.

Skin cream perfume dinga ta matsa tana shafawa a hannunta. Idanunta suka sauka daidai inda yayi mata allurar a jiya wanda ya bada wani dan siririn tabo kaman an diga baqin lalle a gurin saboda zafin allurar. Yatsanta takai ta shafa gurin,tana son tunawa,yayin da tunawar tazo mata da wani irin mummunan faduwar gaba.

Stool din dake bayanta ta koma ta zauna akai tana tuna komai.....

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 08* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _____________________________

"Shine......shine" Abinda zuciyarta ta maimaita mata har sau biyu,a cikin jikinta ma still tana jin shine.

"Comment est-ce possible?(yaya hakan zai kasance?)" Ta tambayi kanta tana juya abun. A hankali kuma sai wani tunanuka suka soma cushe kan nata,ta gaza daidaita tunanin ya zauna da kyau a kanta har ya gamsar da ita.

Ta yaya malamin da baisan komai ba sai karantarwa zai samu irin wannan experience din na sarrafa dawakai?......har ace ya tsere mata?,ya kere iyawarta ita da aka haifeta cikin sarauta tsahon dukka rayuwarta?. Yaushe ya mallaki wayewa?,yaushe ya mallaki qwarewa da sanin makamar sarrafa halittu masu yawan sarrafawa irin dawakai?. Kai ta girgiza a hankali,ba wani abu daya bata gamsuwa akan abun,illa abu biyu rak da tabbas suke sanyata takejin KAMAE SHINE. qamshinsa da kuma wadannan idanun da batasan wani ido a duniya da takejin wani na daban a kansa ba.

Miqewa tayi tana yanke tunanin,saboda samun tabbacin da tayi tana dab da zaluqo ko waye. Tasan tamim zaiyi dukkan abinda zaiyi don tabbatar da wannan,tana jin ya kamata ta aje hankalinta akan wannna na wani lokaci,ta fara fuskantar yadda zata yakice Hakeem daga rayuwarta kwata kwata.

"Mammina ta iso......tana dakunan qasa,tana so tayi magana dake" Birra ta fadi kanta a qasa,har yanzu taqi hada idanu da akhnan. Kai kawai ta daga,ta sanya hannu tana daukan wani dan qaramin scarf ta dora saman kanta bawai don kwalliya ba,amma sai ya zame mata tamkar ado ya sake qawata fuskar nan take dake da wani irin sirrintaccen kyau.

Cikin mutuwa da rashin qwari jiki take saukowa. A dazun tana kwance mammina ta shigo,bata bude idanu sunyi magana baki da baki ba,amma kunnuwanta na iya sauraren fadan da taji tana yi harta gama ta fice.

Ko a yanzun tana tsaye ne kawai cikin falon da ba kowa daga ita sai mammina. Wani yanayi take hanga saman fuskar mammina da bata taba ganin irinsa ba.

"Ways kika aika ya siyo miki gubar da kika durawa kanki?" Ta tambayeta a kausashe,da kuma wani bayyanannen fushi da ya raunata zuciyar akhnan din karon farko.

"Kema mammina......kema kin yarda ni da kaina nasha guba?" Ta motsa labbanta tana fadi da wani yanayin karaya daya tara ruwan hawaye cikin qwayar idanunta duk da basukai ga zubowa ba.

Rauninta ya bayyana sosai,raunin da ba wanda ya sanshi ko ya taba ganinsa,daga ita sai sultane,sai kuma morsa safiyya data kasance ta ukunsu.

"Bansha komai ba mammina......ki yarda dani,banda tea da nasha a lokacin,dana kammala kuma nayi nufin amsa kiran da kikayimin.....a hanya abun ya faru dani". Ta sani,wannan itace amsar da zata bata idan ta matsa,saidai kuma bata shirya amsar wadannan bayanan ba.....bata kuma shirya bata ko qofa guda daya da zata fidda bayanan zuwa ga wani ba ko kuma wani guri ba......don wannan shine makaminta......sassauqar hanyar kuma da zata sadata zuwa ga cikar burinta MATAKIN FARKO.

Dubanta takeyi ba wani sassauci a tattare da ita.

"Yaushe kika fara yanke hukuncin shirya qaryawa mamanki biftu?.......kin manta da iqirarin da kikayi da kanki?,kin manta cewa keda bakinki kika ce sai kinsha?......okay.....yanzu kina son qaryatawa kenan?,kinason nunawa duniya da abokan adawar mahaifinki cewa sultane ya gaza bawa gudar d'iyarsa kariya?......idan ya gaza bawa gidansa cikakken kariya da tsaro hakan yana nufin baya iya mulkar jama'arsa al'ummarsa da talakawansa yadda ya dace,tunda har aka iya keta dukkan wani shinge da tsaro aka zuba gubawa gudar diyarsa......hakan yana nuna shi gajiyayye ne kasasheshe ne da bazai iya tabuka komai ba.......to kiji da kyau......muddin hakan ta faru KEMA KIN RASA TAKI DARAJAR.....duniya zataci gaba da kallon mahaifinki ne a matsayin uba me rauni maras alfanu.

Tsaye kawai tayi tana duban mammina......yadda a yau din mamminan ta gaza fahimtarta,yadda ta gaza mata uzuri......ta gaza fahimtarta. Mammina tafi kowa saninta a duniya,tafi kowa fahimtar halayenta,tafi kowa sanin abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba. Tafi kowa sanin qarya sam bata burgeta,qarya bata bata sha'awa......qaryar kuma tana cikin jerin sahun abu na qarshe da bata iya aikatawa a rayuwarta.

Tafi ganewa ta tunkari tsanani ko sauqi da dukkan gaskiyarta,tafi ganewa bayyanar da zahirin abinda yake rai da zuciyarta a madadin yin qaryar.

"Koma me kika aikata bazai canza sunanki daga sunan DIYATA ba,kuma hakan bazai karyamin gwiwa ba,bazai kuma hanani tsaiwa don samar miki da masalar rayuwarki da abinda rai da zuciyarki suke muradi ba". Mammina tayi maganan a sanda take qofar qarshe na fita daga falon.

Hanyar data wuce akhnan take bi da kallo. Koda mammina bata fita ba,bata da wani sauran energy da zatayi mata wani bayani,ta gama bayaninta tana ji har ranta yarda da ita ko takurawa wani ya aminta da ita bai zama dole ba.

Wani shu'umin murmushi ne yake fita saman fuskarta,tana kuma takawa zuwa qaramar fadar sultane daya shirya zama dasu a wannan lokacin cike da cikakken qwarin gwiwar lallai zata fito da nasararta.

Taji dadi qwarai da yadda maganganunta suka dakushe yunqurin akhnan na bayyana gaskiyarta. A yanzun ba gaskiyar akhnan take da buqata ba.........shurunta shi tafi buqata,shirunta shine tsani na farko kuma hanya mafi sauqi da zata sadata da muradanta.

Tun daga qofar farko ta samu sanarwar yana tattaunawa ne da wazirinsa alhaji ahmadu sallau,da alama kuma ba dashi kadai yake ganawa ba,don haka ta zagaya ta wani daki na musamman dake liqe da gurin wanda aka tanadeshi don zaman jiran sultane din irin haka.

Duk bayan daqiqa saita duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta,tana sane ta rage wasu daqiqu masu yawa daga lokacin da sultane yace zasuyi zaman,saboda tsarinta da plan dinta yafi tafiya a daidai,sai kuma tazo ta cimmasa da baqi.

Qaramin tsaki taja sanda takejin fitar baqin sultane,ta miqe a hankali ta buda qofar da zata sadata da ainihin falon faadar tana sanya qafafunta da zummar jiransa. Ko yaya ne tana lissafin akwai mintunan da zasu bata daman kebancewa dashi kafin zuwan kowa,saidai kuma tana zama sallamar morsa safiyya wadda suke takowa tare da sultane ta yanke mata dukkan wani hanzari da takeyi.

Fes momma ta ganta,amma saita dauke idanunta daga kanta tana tattara hankalinta ga sultane cikin sakin sassanyan murmushin da tayishi ne saboda jifan tsuntsu biyu da dutse daya.

Cak wani abu yayi mata tsaye a qirji,daidai sanda idanunta ke sauka akan morsa safiyya din,da alama wata magana sukeyi da sultane din da batasan meye suke tattaunawa ba.

Iska sosai ta furzar daga bakinta tana qoqarin daidaita numfashinta da kuma sanyaya zuciyarta da takejin ta matse sosai a qirjinta,sannan tattaro dukkan wani yanayi da zai iya baka cewar cikin nutsuwarta da walwalarta take ta dora saman fuskarta.

"Marhaba......barka da shigowa zaki gwarzon mazaje" Ta furta da wannan salon na girmamawa tana miqewa tsaye,sanda morsa safiyya ke qoqarin kwashe masa pillows din saman kujerar da zai zauna a kai,abinda ya sake dasa wani kakkaifan mashi saman zuciyarsa sanda morsa safiyya ke neman gurin zama daura dashi ta zauna da wannan nutsuwar da basarwar tata. Yanayi da nature dinta guda daya dake taba mammina kenan......tana da fada......tana da zafin zuciya,amma tana da wata kalar kamewa da idan bataso ba ko fuskarka ba zata kalla ba bare tasan da wanzuwarka a wajen. Wani lokaci wannan dabi'artata......wannan halin nata yana ma mammina kwarjini sosai.

"Barkanki giwar agadez" Ya fadi da yanayin da yasa mammina alfahari sosai,duk da fuskarsa bata nuna ainihin abinda bakinsa ya fada.

"Ina fatan ka yini cikin aminci da qoshin lafiya?"

"Alhamdulillah.....kema ina miki fatan hakan" Anzo gurin da takeso,tambayar kuma tazo mata daidai,saita rusunar da idanunta cikin wani yanayi.

"Ba wannan nutsuwar sam a tare dani......banajin wani aminci ko kwanciyar hankali,tun daga sanda na fahimci akhnan tasha guba dalilin auren dole" Ta furta da wata irin rusunanniyar murya. Shuru sultane din yayi yana dubanta,kamar yadda morsa safiyya ta dakata da komai,ta kuma zuba idanunta akan mammina din.

"Ban zaci abun zaikai har haka ba......ban dauka da gaske take zata sha ba me martaba......."

"Wannan hujjar kika riqe kika qi shaidawa kowa iqirarinta?......" Muryar morsa safiyya da dukka qoqaromta na hadiye abinda yake ranta ya kasa cimma gaci.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yadda tayi tambayar da wani irin yanayi cikin muryarta.......yadda sautin ya fita yaja hankalin sultane da mammina,harma da nanay dake sanyo kai gurin ba tare da kowa ya ankara da shigowarta ba.

Kai tsaye,kuma ido cikin ido morsa safiyya ke duban mammina.

"Indai har da gaske ne iqirarin da kikeyi.....ke kika raini biftu.....kinsan kowanne hali da dabi'a nata.....kinsan komai da zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya aikatawa ba.......indai har da gaske ne kina jinta kamar diyar data kwanta a mahaifarki watanni tara kika haifeta,koda baki gayawa kowa ba.....koda kowa bai sani ba,mahaifinta......sanadinta,kuma jigonta yana da haqqin yasan iqirarin diyarshi......indai ba akwai manufa shiri ko wani tanadi ba cikin shurun......bai cancanci ayi shuru ga dukka iqirarin da d'iyar dake da kafiya da taurin kai irin AKHNAN ba".

Idanun morsa safiyya da kallonta kawai a kanta ya gaya mata akwai babbara barazana......akwai abubuwa masu tarin yawan daya kamata tayi garkuwa dasu kafin wani abu ya girgiza gaskiyar dake lullube da ayyukanta a zahiri.

"Me kike cewa safiyya?.....me kike shirim cewa?" Ta fadi tana son gano bakin zaren komai ta dora ga aikinta na gaba.

"Bance komai ba,ban kuma shirya fadin komai ba......saidai tarin qalubalantata a gareki na rashin shaidawa mahaifin biftu iqirarinta har sai dame afkuwa ta afku......nayi imanin inda kinsan ZAFIN HAIHUWA inda kinsan DARAJAR 'YA'YA ba zaki aikata haka ba" .

Maganan ta daketa da zafin data saba dukanta,saidai kuma da wurwuri ta gano ta kuma fahimci akwai wani d'anannen tarko cikin maganan morsa safiyya,da biyu a yau ta maimaita maganan gaba sultane,gaban nanay da ta lura ita daya ta ankara da tsaiwarta daga qofa. Duk da cewa tarko ne maganar tata,amma ta hango tarin mafita a cikin tarkon......ta hango hanyar bullewarta.

"Ya isa safiyya" Sultane ya fada da sigar dakatar da momma safiyya,amma saita murmusa don har yanzu batakai gaci ba.

"Ka barni na gaya mata,zan gaya mata abinda yake shine.......illar bada tarbiyya ga macen da batasan ciwon haihuwa b........"

"Ya isheni haka safiyya!.....ya isheni!!!" Mammina ta magantu cikin wani irin fushi tana miqewa tsaye. Irin wannan fushin morsa safiyya ke fata da burin gani a tattare da ita......irin wannan fushin da take fata ya kaita ga yakice akhnan ta barta zuwa gareta......ta barta zuwa ga ainihin UWAr data cancanci rayuwarta........ta barta da AHALINTA na haqiqa........ta barta taju GARDIN soyayya da 'YAN UWANTAKA daga ahalinta na asali.......ahalinta na tsatso.

"Ki jima kina jifana da miyagun kalamai saboda haihuwa......kin dade kina fadamin dukka maganan da yazo bakinki akan akhnan......."

"Baki kyauta ba safiyya.......ba halinki bane,bai kuma kamata a yanzu ace kinyi ba,bai dace ki rama alkhairi da sharri ba" Muryar nanay dake bayyanar da zallar bacin rai ta iso gurin Nanay din tana takowa zuwa ciki gami da gaza jure ci gaba da tsaiwa daga bakin qofar don kada ta shigo ta yanke maganar da yakeyi da iyalin nasa. Amma ganin maganganu suna neman juyewa zuwa zafafan musayar yawu daka iya bada sakamako maras kyau taga ya dace ta qaraso ta kamawa d'an uwanta wannan rigimar da take hange cewa ta yau din ta dabance......ta yau din me girma ce.

Da sassarfa mammina ta taka tana cimma Nanay. Idanunta cike fal da hawaye ta kama hannunta.

"Don Allah ki gaya mata.......ki kuma tambayeta sai yaushe zata ga alkhairi na?.......sai yaushe zan zama MACEN ALKHAIRI a idanunta. Me takeso,me take buqata nayi bayan wanda nayi da zai gamsar da ita?" Mammina ta fada hawayen da ya tarar mata yana saukowa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 09* ___________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________

"Tsahon shekaru ashirin da suka yita shudewa kawo yau.....ko meye ya kamata morsa safiyya ki fahimceshi......ko menene ya kamata ki yafeshi" Murmushi me dauke da wani nannuyan ciwo morsa safiyya ta saki. Tana hangen wani kwantaccen hali dabi'a zubi da tsari na musamman daga kowanne motsin mammina din. Abubuwan suna sake kwance mata kai,amma alqawari ne ta yiwa kanta,bakin rai bakin fama......ba zata taba sassautawa muradan mammina ba......ba zata taba rusuna musu ba......ba zata taba sauke mata kai ba......ba zata taba bari ta mulketa ba......ba kuma zata daina adawa da kowanne tsari da shiri nata ba muddin bata saki kurwa da rayuwar akhnan ba.

"Akwai wani lulluben duhu dake nannade cikin wasu irin yankuna masu tsananin duhun daya kusa fin duhun da suke boye dashi......ba zaku fahimci komai ba......wani yare ne da baya buqatar harshe ko motsi na labba ballantana akai ga fitar sauti.........abu daya data tambayeni kan me zatamin na yaba.....abu dayannan shine KI 'YANTA RAYUWAR AKHNAN.....KI RABU DA ITA DA DUK ABINDA YA SHAFETA".

Sosai kalmarta ta farko tayi duka me sauti a qirjin mammina.......bada hankali ga kalmar kuma na nufin d'arsuwar alamu masu tarin yawa ga zukata da kuma ayyuka,don haka ya zabi yin duk wani tattaki nata da fidda salon iya kauda hankalinta akan jimla ta biyu,don haka ta saki hannun Nanay a hankali,wani murmushi yana subuce mata maras armashi,tayi taku uku tana sake kusanta kanta da inda morsa safiyya ke zaune.

"Wannan shine cikar burinki......shine cikar burin da har ki mutu ba zaki sameshi ba muddin ba kyakkyawar niyya da nufi bane a zuciyarki......HAR ABADA bazan wulaqanta akhnan ta hanyar banzatar da ita da rayuwarta ba kaman yadda kike fata,jinin sultane yafi qarfin wulaqanci ko kuma tozarci na har abada a hannun zaituna.......idan baki da labarin soyayya KOMA KI TAMBAYA cikin hamshaqiyar qasar data tara isassun mata irin ZAITUNA.......Zan sadaukar da farincikina saboda farincikin akhnan.....zan iya yaqi da kowa don akhnan ta samu 'yancin da yayi daidai da rayuwarta........kamar yadda a yanzu nake tsugunnawa saman qafofina nake roqarka ka janye auren hakeem akan akhnan......ko don ka ceto rayuwar da qwaya daya tal da ita kadai SAFEENA ta iya baka" Mammins tayi maganan tana sulalewa saman gwiwarta gaban sultane.

Readers Also Read

More by Huguma