L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 6
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 6: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 6. SAFEENA dukkan rauninsa ce......safeena dukkan qwarin…
3,281 words
SAFEENA dukkan rauninsa ce......safeena dukkan qwarin gwiwarsa ce a sanda yake raye. Sa'insarsu gaban should wani abune daya jima irin haka bata sake faruwa ba a gabansa. Kamar kowacce ta mance da wanzuwarsa a gurin,kamar kowacce ta mance da hukuncin aikata haka a gabansa?.
"Zan dauki alhakin komai......amma bazan iya jurar rasa biftu ba.......ta fara da shan guba.....dukkanmu gaba bamu da tabbacin abinda zai faru da rayuwarta".
Wani irin masifaffen tashin hankali ne morsa safiyya taji yana yanko mata. Idan ana lissafin ANNOBA tana ganin cewa mammina tafi gaban a kirata da sunan ko a sanyata a sahun......tafi qarfin sunan ANNOBA saidai wata halitta daban da tasha banban da yanayi da tunanin dan adam. Soke auren akhnan da hakeem hakan yana nufin dawowar kowanne lissafi baya?. Hakan yana nufin maida kowanne lissafi izuwa farkonsa?,tarin gwagwarmaya tarin dauki ba dadin da akayi dukka sun koma farkon lissafi?. Akwai wani tunani......akwai wani target akwai kuma wani ajiyayyen abu kuma boyayye a bayan kowanne faruwar al'amari.
"Soke auren hakeem da akhnan da zakayi shine babban kuskuren da zaka aikata sultane...." Morsa safiyya ta fadi tana girgiza kanta gami da qoqarin boye dukkan tsoron dake cin ransa.
Da wata irin fusata mammina ta waiwayo tana duban morsa safiyya.
"Wannan shine kalar maqaryaciyar soyayyar da kike iqirarin kina yi mata?......kar ya soke auren?.......yau tasha gube gobe tasha ruwan batir?......burinki kawai tayi aure?,tabar gabanki bayan ba saman kanki take rayuwa ba?,me ta tsare miki?.....tayi aure kowanne yanayi ma zata shiga ba damuwarki bane?,saboda BAKE KIKA HAIFETA BA?,SABODA BA FALAAK BACE?"
"ZAITUNA!......kul dinki.....kul bakinki ya sake....." Maganan da morsa safiyya ta fara da wani irin zafi daya sanyata miqewa tana nuna mammina da yatsa maganan ya katse saboda tsawar da sultane ya sakar musu.
Ba wadda bataji ta koma hayyacinta ba,don baquwar halayya ce ga sultane din. Yana da wani irin girma da yake bawa kowaccensu saboda kowacce akwai wani ajiyayyen dalili da yasa take da girma da daraja a idanunsa.
"Idan har wanzuwata a guri bata hanaku aibata kawunanku ba.....meye zai sanya ku fasa?" Yayi tambayar da harshen da yasa kowacce jinin daya fara tafarfasa a jikinta ya fara sanyaya.
Ganinta da jinta taji kaman ya makance na wucin gadi,yau ita ake duban cikin idanunta ake cewa jinin safeenarta BA ITA TA HAIFETA BA?. Wata bare can?,wata cikakkiyar abokiyar adawar da dukka tsahon rayuwarsu basu data biyunta?,tabbas.....idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba.....inda safeena tana raye a yau,zataji ciwo sama da ciwon da ita takeji yanzu cikin qirjinta,saidai wannan ciwon.....wannan radadin ta haramtawa mammina ganinsa.....ba zata taba bari ta fahimceshi ba.
"A shirye nake na dauki mummunan mataki akan kowaccenku......muddin kasancewata a guri ba zata zama sitiyarin control dinku ba!" Ya sake fadi wani fushi me kaifi yana gilmawa ta cikin idanunsa yana nuna yatsansa dan manuni.
"Kayi mana afuwa" Nannie ta furta ita kanta a yau tana jin banbanci tsakanin yanayin sultane na yau dana kullum.
Shuru ne ya ratsa dakin,tamkar ba ragowar wani abu me numfashi a cikin dakin.
Numfasawa sultane yayi,yana qoqarin daidaita kanshi da ragewa kansa damuwar da yakeji tana tasiri kadan kadan cikin zuciyarsa. Yana jin qwarin gwiwar hukunta akhnan.......yana jin takai lokacin da zata fuskanci fushinsa dama hukuncinsa,yana jin wani tasiri na maganganun morsa safiyya a ransa,yana ganin wasu daga cikin gaskiyarta,koda ta kasance me taurin kai,koda ta kasance me kafiya,koda ta kasance me tsaurarawa da yawa.
"Dole ne na janye auren akhnan da hakeem.......tunda wadanda keda alhakin karbar auren sun janye suma".
Tsahon rayuwarta zata iya cewa,ta jima bataji wani labari daya saukar da wata irin farinciki me girman gaske cikin zuciyarta ba.......ta jima bataji abinda yazo mata a bazata irin wannan a wadannan shekarun ba. Murmushi ko dariya take buqatar tayi a irin yanayin don furzar da yanayin da zuciyarta ke ciki,amma saita rikide da nuna alhini dama tsoro baro baro saman fuskarta.
Yadda morsa safiyya ke dubansa da wani irin dimaucewa,haka mammina ke kallon sultane da yanayin daya kebanta da zuciyarta kadai. Wani irin zafi zuciyarta ke mata,tana so ta riqe bakinta,tana so tayi shuru kada ta tanka,amma tana jin idan tayi haka,idan har sai ta jira sultane yace wani abu da kanshi zuciyarta zata fashe,zuciyarta ba zata iya dauka ba.
"Amma.......ba nadama?......ba kuskure cikin faruwar?......"
"Sun janye saboda labari yaje musu.......'yar da d'ansu ke burin kawowa cikin ahalinsu da ake zaton mace ta gari ce......yarinya nutsatsiya me biyayya ga maganar magabatanta abun ba haka bane..........a dazu na aika an maida musu da dukiyar aurensu da komai da komai nasu cikin mutuntawa kamar yadda suka kawo......" Shuru gurin ya sake dauka,kafin a hankali nannie ta magantu.
"Koda basu janye ba,koda basu fasa ba ni a nawa hasashen janyewar shi yafi alkhairi.......a duk sanda irin haka ta sake faruwa,ba wanda yake da tabbacin abinda zai ci gaba da faruwa,koma meye......ko yaya yanayin yakai ga hasala ko baci akhnan diyarmu ce,kuma lallai muna qaunar rayuwarta sama da yadda zamu qaunaci rayuwar kowa" .
Ji tayi bata da wani sauran zama a gurin,ji tayi bata da sauran abinda zata zauna tayi a gurin,tana jin idan taci gaba da zama abubuwa sake kwabewa zasuyi,idan har tace zataci gaba da zama abubuwa zasu lalace ne. Ba zata iya shuru ba,ba kuma zata iya ci gaba da saka idanu tana kallon komai yana tafiya a yadda yake a yanzu ba. Da nannie da sultane akwai wani abu daya gifta ta cikin idanunsu da batasan sai yaushe zai bude ko ya yaye ba. Bata sani ba......shin cikin qullin mammina ne data sha ALWASHI?,ko kuma tsananin soyayyar akhnan ce take jawo wasu abubuwan?.
"Ayimin afuwa......na barku lafiya" Abinda morsa safiyya ta fadi kenan tana miqewa a hankali tana jin kamar bata ganin gabanta sosai ta fara takawa tana fara fita a dakin.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Da kallo nannie ta bita,zatayi magana sultane ya daga mata hannu kawai alamun ta barta. Ya sani,zataji tsananin rashin jin dadi,ya sani zata zargeshi a zuciyarta,ya sani,zataga zallar rashin adalcinsa......to amma inda ta haqurqurtar da wannan zuciyartata me yawan fushi,me saurin fusata da zata fahimci komai bai canza ba.
"Janye auren hakeem bai canza komai ba!" Ya fada da yanayin daya dawo da hankulansu mammina kanshi.
"Eh......kwanan watan dana sanya na auren akhnan bazai canza ba......hakanan duk wani shiri da nayi akan bikinta ban canza komai ba......komai yana nan akan tsarinsa.......watanni biyu masu zuwa tabbas diyata akhnan zata zama MATAR AURE......" Maganan saita dan saka rudani a zukatansu,musamman zuciyar mammina dake cike da babban buri da kuma shirin da take fata ya fado yayi daidai da wannan lokacin.
"Ki gayawa 'yarki.....daga sultane of agadez......Muhammad hammud.......taci nasarar janye maganae auren hakeem a kanta......amma ba abinda zai canza wa'adinta na zama matar aure,watanni biyun aurenta.......sune watannin da take dashi na kawo duk wanda takeso........don nayi alqawari......ni ba mutumin banza bane,qafar wani d'a da zummar son ganinta ya aureta ta yanke daga zuwa gidan nan indai a kanta ne.......watanni biyu kacal take dasu ta kawo wanda takeso ta aura.......ku rubuta ku ajiye......daga yau zuwa biyar ga watan sama,a ranar juma'a,muddin bata kawo wanda takeso ta aura ba......ni.muhammad hammud zan daura mata aure da duk wanda naga dama. Ba kuma lallai ya zama kalar mijin da takeso ba......ba kuma lallai tasan waye ba wataqila har sai ta shiga dakin aurenta......aure na dindindin.......auren da saidai a fidda gawarta daga gidansa" Ya fada da wani irin sauti daya tabbatarwa nannie da mammina ba wani sassauci ko sauyi a maganarsa.
Ba qaramar juriya tayi ba data iya shimfida tashin hankali saman fuskarta ba. Sunan ALMAZ kawai ke mata yawo saman harshe da kwanya,saidai ba yanzu ba.......ba da sauri haka ba......ba'a wannan taqin ba.......akwai ragowar taku biyu zuwa uku daya kamata tayi.
"Amma sultane......ta yaya mace kaman akhnan.......mace me tarin martaba da mutunci za'a buqaci ta fidda mijin aure a wannan tsukakken lokacin,shi baka tsoron ya zamana tayi zaben tumun dare?".
" Zaituna" Ya furta da tarin nutsuwar nan tasa da yau take cakude da bacin rai.
"Daga rana irin ta yau....bana son wata magana data shafi akhnan akan aure a sake tasomin da ita,abu daya nake jira ta sanarmin ta samu miji shikenan". Qasa tayi da kanta,wani irin farinciki yana shawagi da zagayawa da ita a duniyarta.
"Allah ya huci zuciyarka,tuba nake" Abinda ta furta kenan kanta a qasa ba tare da sun hada ido ba.
♣️:~ Juyawa tayi ta sake juyawa ita daya cikin dakin tana jin kamar wani kida ko sauti na musamman ake busa mata. Irin wannan yanayin yanayi ne da yafi dacewa ka rabashi da wani mutum na musamman daga gefenka,to amma ita din bata gama aminta da dukkan kowa ba ballantana ta saki jiki yasan dukkanin fuskokin data mallaka.
Tana da tarin girma da alfarma,banda haka tabbas ya cancanci tayi wannan juyinne a sararin da zata shaqi iska da kyau.
BURINTA MAFARKINTA da kuma MURADINTA na shekara da shekaru a yau yana dab da cika. Ta yarda a karan kanta cewa ita din WUTA ce......wata irin WUTA me tsananin had'ari duhu da kuma baqin HARSHE dake iya nakasta rayuwar duk wanda ya rab'eta.
Wannan lokacin ta jima tana jira,cikin tarin mafarkan IDO BIYU da tashayi a zaune cikin duniyarta. Wannan lokacin data lashi takobin ajiyewa kaf familyn DIORY MUMMUNAN TARIHI da zaita bibiyarsu har qarshen rayuwarsu. Wannan lokacin da tasha alwashin sanya SAFEENA kuka da hawayenta.......tasha alwashin sanyata cikin tarin NADAMA DA DANASANI koda kuwa qasa ta lullube idanunta.....koda kuwa tana kwance cikin kushewarta.......wannan lokacin wani lokaci ne daya girmimi a kirashi da DAUKAN FANSA......lokaci ne na ajiyewa ahalin gaba daya MUMMUNAN TARIHI.
Z'a haife 'ya'yan da ba za'a taba alfahari da samunsu ba.....'ya'yan da zasu zamewa tarihi BARAZANA.....'ya'yan da za'a ce zaman uwarsu JUYA shine mafi Alkhairi sama da haihuwarsu. 'Ya'yan da muddin suna raye a duniya.....muddin sun wanzu a doron duniya.....to a kowacce rana da qwayar idanuwa zasu sauka a kansu......baqinciki ne zaici gaba da hallaka zukata da yawa d'aya bayan d'aya har zuwa ranar da tarihi rayuwa da tsahon zamani zai shafe babinsu gaba daya.
ALMAZ da AKHNAN dukkaninsu cikin tarko suke......cikin tarkon da babu me iya fahimta,koda kuwa TAMIM ne......koda kuwa YALWA ce......koda sauran boyayyun ma'aikatanta ne......wannan din wani sirri ne dake tsakanin zuciyarta zuwa qirjinta kawai. (Tofa.....me karatu?,wanne irin qudunannen sirri ne wannan?.......Allah yasa ko yaya mammina ta buda mana zuciyarta ko zamu iya fahimtar me take qullawa haka tsakanin almaz da akhnan).
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 10* ____________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Batayi wani gaggawar zuwa ga akhnan ba,sai misalin qarfe sha daya na dare. Tanason tabar mata dukkan daren ya qare a tunani da neman mafita,mafitar data tabbatar bata da ita......neman mafitar kuma shine zai danganata da zuwa inda take.....zuwan nata kuma shine abu na qarshe da take fata da burin kasancewarsa.
Qasaitattun kayan baccin alfarma masu taushi da kyau ta saka a jikinta,sannan ta dora doguwar riga yalwatacciya akai,don tana saka ran daga nan ta biya ta sassan me martaba ta sake kashe awanni don sake dasa abubuwa da take buqatar sanyawa da ajiyewa cikin zuciyar sultane,ajiyar da zata mata amfani wata rana.
Daga ita sai yalwa kawai suka fita,suna ratsawa cikin gidan da sawaye suka dauke saboda kutsowar dare,sai gilmawar hadimai da fitarsa a sannan ya zama dole,da kuma masu bada tsaro na sashe sashe dama gidan gaba daya.
Sanye yake da Moroccon jallabiyya da aka saqata da wani silk yadi me sulbi da wani irin daukan idanu,yayin da qafarsa ke sanye da wani lallausan halfshoe daya dace sosai da yanayin rigar. A daren hula ce kawai saman kanshi kalar rigar,wanda yawan larabawa ke amfani da ita.
Wani irin dare ne daya cika da hasken watan da zai gaya ma mutum wata ya fara nisa,abinda yake sake zaburar dashi kan aikin kenan,ya kuma hanashi kwanciya a daren.
Target biyu yake dashi,wanda ya tabbatar yana buqatar kulawa da takatsantsan. Samun matsayin D'A a wajen sultane ba yana nufin zaiyi komai bane gaba gadi.......dole komai ya zamana akan tsari kulawa da kuma takatsantsan.
Tsakanin jiya da shekaran jiya....bayan shudewar kowacce daqiqa tunaninsa yana sauka akan banguls din hannuwanta.......abun adon da yake da tabbaci cikin kaso saba'in cewa qirar qasar ETHIOPIA ne.......abun hannu me daraja da tsada kwatankwacin wanda suka taso suka gani nanay tana amfani dasu a yawancin lokuta.
Abun ado ne da yawan matan sarauta da attajirai na qasan Ethiopia a wasu shekaru a baya suke amfani dashi......to amma aikinsa aiki ne dake tafe da yaqini da samun tabbaci gudun samun kuskure. Dole yana buqatar wannan abun hannun......dole yana da buqatar sa a hannunsa don turawa ayi masa bincike tare da bashi tabbacin wanda hasashensa ya yawaita a kai ne?.
Dakin ajiye ajiye na gidan......wani guri na biyu da shima yake cikin lissafinsa......amma kafin isa gareshi yana buqatar sanin abubuwa da yawa. Canzawar motsi zirga zirga da kai kawo na gidan daga daqiqa zuwa daqiqa.......yaya kowanne qofa window da sashe na gidan yake kasancewa daga kowacce daqiqa zuwa wata daqiqar......wannan shine abinda ya fito dashi,yana kuma tafiya ne da cikakken nutsuwar nan tasa,can qasan zuciyarsa kuma suratul rahman yake karantawa ba tare da sauti ba,sai motsawar tausasan lips dinsa da motsawar Adams Apple dinsa lokaci zuwa lokaci.
Idanunsa ya dauke daga windows din da yake qoqarin kiyaye adadinsu da kuma wadanda kake iya hangen haske a cikinsu da wadanda ma duhu ke lullube dasu,alamun dake nuna akwai guraren da masu rayuwa a ciki sukayi bacci a daidai wannan lokacin. Alamun takun da yaji shi ya sanya ya sake sassauta yanayin tafiyarsa,haruffan dake cikin surar suna sauka a zuciyarsa gami da wata irin nutsuwa,ma'anoni da girman ubangiji dake bayyana cikin ta yana jin kamar suna sauka a ruhinsa da kuma zuciyarsa kai tsaye......a daidai wannan lokacin idanunsa suka sauka a kanta sanda take takowa cike da wani kalar karsashi.
Duba na nutusuwa yayi mata kafin a hankali ya zare idonsa daga kanta yana maidawa ga inda yake sauke sawayenshi. Qasan zuciyarsa yana sake jin abu me qarfi yana dasuwa a ranshi. Ita dimma kamar wancan mutumin,akwai dan wani abu daya jirkita yanayin zubinta dana al'ummar agadez......akwai wani tasiri na daban cikin yanayinta da babu shi jikin agadasawan yankin,duk kuwa da yadda shigarta yanayinta damu'amalarta suke maidata ba'abzina ta sosai.......amma yanayin da kamannin da yadda a komai nata al'adar abzinawa ke shiga tayi kane kane ya soma d'arsa wani qaqqarfan zargi a ransa.
Dare daya tal ya kwashe yana bincika tarihi yanayi da al'adun kowacce qabila dake cikin qasar da yankin na nijer,a wannan daren guda daya bacci bai ziyarci idanunsa ba ko sau daya. Yasha coffee har baisan iyaka ba,amma kuma bai damu da rashin baccinsa ba,don ya tattara dukkan abinda yakeso,ya kuma san duk abinda yakeso ya sani,wannan ya sanya daga wannan kallon yaji cewa tabbas akwai wani abu daba daidai ba.
Bata ankara dashi ba,har sai da tazarar data rage tsakaninsu ta kasance bame yawa bace. Yalwa ce ambaci sunanta a hankali,yanayin kiran kadai ya gaya mata akwai wani abu,don haka kai tsaye gabanta ta kalla bawai sashen yalwa ba.
Wata irin bugawa zuciyarta tayi,amma sai tayi gaggawar zuqar iska sosai tana daidaita kanta,kafin a hankali ta sauke numfashin tana gayawa kanta da kanta wani abu.
Sarrafa kansa yake qoqarin yi don yanayinsa ya dace da yadda zaiyi magana da ita. A yanayin kallonta ya tabbatar akwai abubuwa da yawa game da ita. Yadda take kallon kowa da yadda take hada nutsuwarta a duk sanda taga wani baqon abu da bata saba gani ko mu'amalanta ba. Wani yanayi da yake bayyana a tattare da wasu mutane da suke dauke da baqin abubuwa a cikin halayyarsu da dabi'arsu.
"Barka wannan lokaci" Ya furta a nutse yana qoqarin daidaita matsayinsa da yanayinsa da yadda ya fahimci tana mu'amala da hadimanta.
Murmushi ta kawo ta aza saman fuskarta,ta kawo wata irin sakewa ta sake shimfidawa a sama sannan ta amsa masa.
"Barka kade sheikh muhammad........ina fatan ba wani matsala bace ta fito dakai cikin irin wannan lokacin?". Kai ya jinjina yana daukar wasu abubuwa cikin kalamanta yana turasu wani sashe na zuciyarsa tare da shirya amsar da zaya bata duka cikin qasa da second biyar.
"Ba wata matsala.......ina buqatar iska me kyau ne kawai" Ya amsa mata a taqaice ba tare daya kalli idanunta ba. Kai ta jinjina a hankali,burinta da muradinta shine ya kalleta,tana son karanto wasu abubuwa cikin idanunsa.
"Amma ai da kasanar......yanzun kai din kamar d'a kake a wajenmu.......sai a hadaka da wanda zai maka jagora gudun shiga shiyyar da bai dace da girmanka da matsayinka ba". Murmushin qasan zuciya y saki wanda ko labbansa bai motsa ba bare ka gani,ya sake aikewa da kalamanta wani sashe na zuciyarsa,sannan ya motsa kadan alamun yana nufin wucewa.
"Bazai zama damuwa ba.......ba wani zurfi ko nisa tattakin zaiyi ba......duka duka na awa daya ne......a fito lafiya" Ya fada da salon girmamawa yana ci gaba da wucewa a hankali.
Bin bayansa tayi da kallo komai na tunaninta yana warwarewa lokaci guda.
"Tabdijan" Ta furta a sanda yake bacewa ganinsu tana aza idanunta akan fuskar yalwa.
"Ya wuce a sanda bani na bashi umarnin hakan ba,bai kuma nemi izinin wucewa ba.....bai kuma dakata da tafiyarsa ba a sanda ya ganni.....hakanan ba wani alamun kwarjini da nakewa kowa a cikin muryarsa.......yana bani amsa ne da wani irin qwarin gwiwa da tsaiwa a muryarsa.........lallai akwai wani abu.......akwai wani abu daban cikin JININSA.....ko ya kasance irin abinda ke cikin jinin SARAUTA ko kuma halittarsa zuciyarsa da ruhinsa masu tsananin qwari ne......yalwa" Ta kira sunanta tana ci gaba da takawa a nutse.
"Allah ya baki nasara" Ta amsa da girmamawa.
"Kinga dukkan abinda na fada?"
"Qwarai da gaske......abu daya ne kawai dana gani,baya kallon mutane"
"Yana da addini da kuma sanin addini.....maza irinsa suna da wannna dabi'ar.......bawai tsananin girmamawa bace a gareni.........inason insan wayeshi?......idan har sakamakon yazomin mutum ne yadda muke zatonsa ordinary kaman kowa.......to lallai ina buqatar sa cikin tafiyata........ina buqatarsa a gefe na.......".
"Sheikh haisam din?" Yalwa ta tambaya cike da tantama. Qaramar dariya ce ta kubcewa mammina.......tana jin wani nishadi yana ratsata.
"Da kamar wuya ko?......abune me sauqi yalwa.......KUDI ba sune masu maida abinda bazai yiwuwa ba ya yiwu......kudi sune masu juya kowanne mutum zuwa yanayi da siffar da kake buqatar ganinsa a kanta. Idan kana buqatar mallakar wani abu......ko wani mutum idan ka gutsira masa IKO cikin ikon da kake dashi komai ma zai sallama maka......malamai a wannan lokacin sunfi kowa son zuciya da mutuwar zuciya......mallakar wannan malamin shine abu mafi sauqi da nake hange zanyi......inaso daga yau dukkanin motsinsa ya zama abun bibiya......inason daga wannan lokacin duk inda zai saka qafarsa.....duk inda zai sauketa ya zamana abun kiyayewa......bacci ne kadai idan zai kwanta na yarda ma rataye da aikin yaje ya huta a sannan.....na bawa tamim wannan aikin......amma inaso wannan ya sake zama wani aikin na daban ba tare da kowa ya sani ba".
Yatsansa yakai kunnensa ya taba a hankali,wani tattausan murmushi ya subuce wanda ya tsaya saman labbansa.
"Tamim" Ya maimaita sunan a hankali yana motsa labbansa. Ya fahimci akwai tarin abubuwa tattare da mutum biyun nan da suke sharing suna GUDA DAYA,sai ya jinjina kansa cikin wata irin nutsuwa