Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 45

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 45

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 45: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 45. A hankali ta waiwaya tana duban wayarta dake ajiye…

3,169 words

A hankali ta waiwaya tana duban wayarta dake ajiye saman abun sallar da take kai daga gefanta. Idanunta ta ware sosai,zuciyarta tana wani irin bugawa da ganin sunan dake harbawa a fuskar wayartata.

"Captain obbo" Ta karanta sunan a fili tana jin yadda zuciyarta ke bugawa b'al b'al kamar zata huda qirjinta. Wani yanayi ne daban.....wani abune na daban me matuqar shammata da bata taba zaton faruwarsa ba.

Ko ina na jikinta rawa yakeyi,ta daga wayar ta karata a kunnenta. Sallama tayi masa,irin sallamar dake bayyana yadda muryarta ke sake raunana da wani irin rawa na zallar kwarjinin da yake mata.

"Barka da warhaka Obboleettii" Ta fada a sanyaye bayan ya amsa sallamartata.

"Barkanki sameera.....ya jikin naki?" Sai data lumshe idanunta a hankali,dadin muryarsa yana ratsata. Wani irin amo mejan hankali daya saukar mata da wata irin nutsuwa,har batasan ta saki siririyar ajiyar zuciya ba.

"Alhamdulillah obbo....da sauqi".

"Ma sha Allah" Ya fadi sannan shuru na wasu sakanni ya biyo baya kafin ya dora.

"A rayuwar dan adam gaba daya lafiya itace gaba da komai....yana da kyau ki sanya lafiyarki gaba da kowa da kuma komai.....ki zabi kanki kafin komai da kowa......sannan ki kusanta kanki fiye da baya da karatun qur'ani,domin da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa".

"Na gode obbo" Ta fadi da wani irin sanyi,tana jin dadi yana sauka mata a ranta. Ba'a banza zuciyarta take nacewa da soyayyarsa ba,ba'a banza takejin ta kowanne taqi na rayuwarta yayi mata ba,ba'a banza takejin da ita kadai ya dace ba. Miji take nema dan gaske me kamala koda shigen tasa ce.....mijin da zai kama hannunta ya kusantata zuwa ga Allah da kuma dokokin Allah,sai akayi sa'a idanunta suka sauka a kanshi. Duk kuwa da cewa zuciyarta tasha gargadarta akan cewa haisam din ya mata NISA.....ya mata TAZARA ya d'ara ajinta. Tana jin kamar ba zata sameshi ba......tanajin ita din sam ba ajinsa bace,to amma kuma ta rasa ta yadda zata fara tanqwara zuciyarta ta cire hakan daga ranta.

"Ki kula da nutsuwar ruhinki,abinci sannan magani". Ya furta cikin yanayin kulawar daya sanya murmushi qwace mata.

"In sha Allah obbo,na gode" Da godiyar tata da bataji abinda ya fadi ba kiran nasa ya tsinke,tana jin kamar ta tambayeshi yaushe zai dawo?,yaushe zata ganshi?.

Rungume wayar tayi a qirji tana lumshe idanunta. Wani irin murmushi ne kawai yake fita saman fuskarta. A iya maganganunsa na yanzun takejin basai ta sake shan wani magani ba kuma a yau din. Bata zata ba ta tsinci muryar nanay saman kanta.

"Ikon Allah......bacci kike ko idanunki biyu?" Nanay ta tambayeta tana ci gaba da leqa fuskarta dake shimfide da wani kalar murmushi. Da sauri ta miqe ta zauna tana sunkuyar da kanta.

"Idona biyu nanay,sallah na gama yi". Kallo Nanay tabi hannunta dashi,sai ta ganta damqe da wayarta,murmushi ya subuce mata. Da alama sirrin walwalarta haisam ne,taji hakan a jikinta,don ta tabbatar haisam din bazai tsallake alfarmar data nema ba dama.

"Shikenan yi kwanciyarki,zamu fita gidan marayu ne,nace bari na leqo naga jikinki"

"Saikin dawo nanay,Allah ya bada sa'a,na gode sosai" Ta fadi still tana kasa hada idanu da ita,itama saita juya ta fice ranta yana mata dadi ganin karon farko yanayin saamee din yana daidaita.

*HAISAM*

Samansa kawai ya koma,ya kuma wuce bathroom yana fidda kayan jikinsa. Faffada kuma lallausan towel ya daura a qugunsa,abinda ya bawa lafiyayyar qirar jikin nan nasa dama fitowa sosai. Faffadan qirji me dauke da mayalwatan kafadu......muscles da suka cika dantsensa wadanda yawan daga qarfe ya sanya suka zauna masa sosai. Tun daga saman cikinsa har zuwa qirjinsa lallausan gashi ne baqi sidik da ya yiwa fatar jikinsa qawanya,hakanan gwiwar hannunsa har zuwa tsintsiyar hannunza,kaman yadda cinyoyinsa har zuwa idanun sahunsa sassalkar gargasa ce dake qara nuna ainihin qirar cikakken lafiyayyen namiji.

Bai wani damu da adadin lokutan daya dauka ba,ya shirya fes cikin daya daga cikin throbe din da wani company daga qasar oman. Silk ce irin silk dinnan me asalin tsada da daukan idanu,sai ya daura amam a kansa da wani irin yanayi me birgewa,irin salon nadin matasan qasar saudiyya. Kusan deal ne tsakaninsa da fitattun kamfanonin throbe(jallabiyya) dake qasashen sudan,oman,saudiyya,dubai,Morocco,qatar,Kuwait. Duk bayan watannin da sukan fidda sabbin design na throbe na maza shine mutum na farko a Ethiopia gaba daya dake fara sanya new arrivals na throbe dinsu. Kusan duk wani malami ko diyan sarauta dake ji da kansa cikin Ethiopia da zagayenta yana kwaikwayo ne da sheikh muhammad haisam aba jifar. Yana da wani irin salo na iya ado tamkar dawisu,adon da har a yanzu a agadez bai canza ba. Dressing dinsa a koda yaushe unique ne,cikin wani irin yanayi da idanu basu saba ganinsa ba. Ya zamewa yaran sarakuna da yawa a Ethiopia role model,wajen qurewa ado gudu ba'a kaishi ba.

Tun daga kan cloak thobe.....jubahs da fitattaun kurta pyjamas a gurinsa ake fara ganin sample. Hakan kuma ya zame masa jiki. Tun yana da shekara goma a duniya ya zama DAN SARKI DA YASHA BANBAM DA SAURAN YARAN SARAKUNA.....kuma har yanzun da yake kan ganiyar samartakarsa ba abinda ya canza,saima sake daukan hankulan 'ya'yan manya dana malamai da yake sakeyi cikin qasar tasa.

Qamshin nan dai nasa da shi kadai ya mallakeshi ke tashi a jikinsa,ya zura wasu budaddun takalma masu wani irin aji a zubi da tsarinsu.

Yana saukowa daga sama idanun omar a kansa,suka hada ido sai ya janye dubansa yana duban maleek da ya miqe qafafunsa saman center table na glass yana aiki cikin system dinsa.

"Nidai kawai jikina yake bani akwai abubuwa da yawa da ake binnewa.....jiya bobbo dawud ya kirani yace komin dare na hadaka dashi......amma koda nazo tun daga babbar qofar shigowa sabuwar dokarka cikin masarautar nan ta hanani daman shigowa" Duk da ba haka yaso ba,amma yaji dadin jin hakan,hakan yana nuna masa da gaske ana tafi da dokar yadda ta dace kenan kamar yadda ya shimfida.

Sai daya gama saukowa gaba daya sannan maleek ya dauke idanunsa daga kan system din ya maida kan haisam sanda ya dauki dabino bakwai cikin wanda ke zube a wani qawataccen gold plate dake ajiye a gurin.

"Sai ina?" Maleek ya tambaya kai tsaye,don yanason ya zauna suyi magana da haisam akan falaak. Abinda yakeji tattare da ita ya girmeshi,yana jin kamar kwanakin da motii ya dauka be dawo ba suna da nisan gaske.

"Zanje.....zaituna nason ganina" Haisam ya fadi yana cire qwallon dabinon daya dauka din. Sosai omar ya koma ya zauna yana duban haisam.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Kiranka kuma?,to ko nazo muje?" Sosai maganan ta bashi dariya,amma sai ya saki murmushi sanda yake jefa dabinon bakinsa yana taunashi a hankali. Ya yadda qwarai da gaske garin suna da albarkar dabino suma kamar qasarsu,a wasu abubuwan hana hangen kamanceceniya kadan kadan.

"Ka rakani?,saboda me?"

"Saboda tsaro mana haisam" Omar ya furta da dukkan gaskiyarsa. Murmushi ya kuma saki,sannan ya fara takawa a hankali da alama yana nufar hanyar fita ne.

"Shi zaki koda ba'a cikin gandun dajinsa ba ya tsinci kansa yana yin farautarss ne yadda yaga dama,duk wani kira.....duk wani kebewa,duk wani magana da zata nemi tayi dani yana zamantowa kaman qarin dama ce a tare dani,qarin daman da zan samu na buda mata hanyar da zata dilmiya kanta da kanta" Ya qarasa maganar a huce kuma hankali kwance.

"Amma ko connection ya kamata ka hada dani"

"Babu buqata.....saina dawo" Ya fadi yana saka qafafunsa waje.

Ajiyar zuciya maleek ya sauke,ya kuma maida dubansa ga omar da har yanzu yabar bakinsa a sake.

"Duk inda kake ajiye haisam ya wuce nan gurin.....ya wuce hasashena da naka,hakanan ya zarta tunaninmu,duk wani motsi da taku da zaiyi lissafinsa daban yake da namu.....yanayin jarumtarsa yana bani tsoro a wasu lokuta. Baisan tsoro ba....baissn fargaba ba,baya banbamce guri me hadari da akasin hakan a duk sanda ya sanya gabansa gaba a kan aikinsa.....yana da yaqini cikakke ga mahaliccinsa......zai dawo omar.....zai dawo lafiya ina da yaqini da hakan.....addu'a ta ratsashi fiye da zatonmu da kallon da muke masa,a kwanakin nan ni kaina nasan da haka,shi yasa baya shakkar kowa da komai,baya kuma shakkar tunkarar komai din" Sosai omar ke jinjina kansa,yana kuma sake gamsuwa dari bisa dari da maganganun maleek.

*MAMMINA*

Wannan karon kuma a wannan lokacin da kanta take takawa zuwa bakin iyakar gurin,cikin salo na kai kawo tare da tarin tsammanin jiran isowar haisam din.

Har wani zabalbala takeji jininta yana yi idan ta tuna cewa yau itace ke maimaita kiran wani d'ana adam dake rayuwa cikin masarautar agadez qarqashin alfarmarta?,bayan yayi watsi da kiran kuma har sai ya zabi lokacin zuwa?.

Ranta yana son ya cimma qololuwar baci,amma kuma tana danne hakan daga ranta,don a yanzu ba fusata ko tursasawa take buqata suyi mata aiki ba. Kwantar da kai,maida komai ba'a bakin komai ba da kuma nuna masa zallar karamci da tarin abun duniyar da zai iya rabauta dashi,su kadai ne makaman da tafi buqata a yanzu.

Tana juya baya tana komawa ciki a karo na barkatai taji sallamar tafisu. Saita waiwayo da wani irin yanayi tana dubanta. Dubanta itama tafisu takeyi,cikin girmamawa take dubanta.

"Ki dade kiyi qarko,Allah ya baki yawan rai.....mene yake faruwa haka ne?". Wani bacin rai ya tasowa mammina,ta kasa amsawa tafisu har sai data samu guri ta zauna.

"Nida wancan wulaqaccen malamin mara asali ballantana tushe.....mutumin da har yau jiya zuwa yau dana shirya zama dashi an kasa ganomin danginsa ko daya na kusa ko na nesa.....sai almajiransa mutum uku da yake tare dasu,don na ukunma baiyi cikakken sati biyu cikin masarautar nan ba" Mammina tayi furucin tsananin fushi yana nunawa kan fuskarta.

"Ki kwantar da hankalinki ranki ya dade.....iname tabbaci da yaqinin komai zai tafi yadda akeso,kinsan abu me qarko bai fiya zuwa da sauqi ba......yanzu haka tamim ne ya tasomin,ya kusa isa diffa amma ya juyo,yace yana buqatar ganinki da gaggawa". Kai ta jinjina a nutse,don hankalinta a yanzu ba'a kan tamim yake ba. Hankalinta yafi karkata ga yadda zata tsara auren haisam da akhnan,tayi imani shi daya ne zata juya yadda takeso cikin sauqi tayi amfani kuma da wannan damar ta bata tsakaninsa da sultane,ta nesanta tsakaninsa dashi har abada.

"Wannan mutumin tafisu.....har yanzu na kasa samun gamsuwa da aurensa da akhnan" Murmushi tafisu ta saki tana waiwaya kadan,sai itama idanunta ya sauka inda mammina ta kafe da kallo.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 78*

Haisam ne yake takowa a nutse,shi daya da wani irin haiba kwarjini da kamala.

"Zaki ruftashi ne ramin rubutaccen alqawari da yarjejeniyar da bazai iya tsallake mata ba.....zaki daureshi da sasarin da bazai iya kunceshi ba dole saiya amince miki. Yasan girman alqawari,yana tattalin mutuncinsa da kimarsa,ko don gudun sarayar mutuncinsa da tsare tsaren da muka tanada zamu masa barazana dasu zai saketa salin alin". Kai mammina ke jinjinawa,maganganun tafisu kuma suna bata wani qwarin gwiwa na musamman.

Cikakkiyar sallama yayi yana takowa cikin nutsuwa,sai mammina din ta miqe cikin yanayi na girmamawa. Fuskarta dauke da wani kwantaccen murmushi take fadin

"Lale maraba da zuwan amintaccen sultane......ga gurin zama" Ta fadi tana nuna masa kujerar dake fuskantarta.

A nutse ya zube idanunsa ga kujerar,ya taka a hankali yana komawa bayan kujerar ya jawo wata can daban da bata cikin jerin jadawalin tsarin ya ajjiyeta a daidai inda yakejin ya gamsu dashi.

Wani boyayyen murmushi ta saki,a hankali ta maida idanunta kan fuskar tafisu. Cikin harshen afaan oromo,cikin yaren daya zame mata garkuwa,yaren da bata yarda ta yarashi sam a gabab mutane,saidai a kebantaccen guri irin wannan tace.

"Ko don na karya izzarsa....ko don na nuna masa shi din ba kowan kowa bane.....tabbas sai nayi amfani dashi......na rusa sultane na kuma rusa ragowar rayuwar AKHNAN,lokuta kadan ya rage,zai zamemin makami ba tare da shi kansa yasan da hakan ba" A wani irin jere maganganun suka shiga kunnen haisam wanda ya sanyo qafafunsa dab da gurin. Ya kamata ace yayi mamaki matuqa ko ya girgiza da jin futar furucin daga bakin ta,amma sai baiji komai ba. Mamakin daya mamayeshi kadai shine yadda yaren oromo daya dade da sanin tana jinsa a yau yake fita saman harshenta radau. Cikin rashin sani ta aza idanunta akan haisam tana me sakin fuska,sannan ta maida dubanta ga tafisu saboda tanaso ta sallameta kafin su zauna da haisam din.

"Tabani tamkar taba masarautar agadez ne tafisu,yayi ganganci daya aikata haka,don baisan yadda makomarsa zata kasance mafi muni ba.....baisan cewa ni zaituna bazan tabu ba.....ta kowacce fuska biyayya a gareni ne kawai zaman lafiyan kowa.......zan tilastashi ya karbi aurenta koda ya nuna wannan girman kan da kuma izzar da dagawar.....a shirye nake na sanya a batar da kafatanin ahalinsa muddin mazauna qasar nan ne da kewayenta"

"Kin dade da makara zaituna zeenatu" Haisam ya furta can qasan ranshi,saidai ko daya ba wata alama da zata baka cewa wai yana fahimtar yaren oromo gaba daya. A yau yaga amfanin adana yare da gasken gaske......a yau kuma da mammina ke sake fardewa cikinta wuqa zayaso ace NAMIJI ce ita. Zayaso wannan wasan......wannan yaqin......wannan farautar dan uwansa namiji ne a cikinta,saidai koma meye yayi imanin kawai BOYAYYUN MAZAJE cikin duk wani shirinta......wanda suma a kowanne mataki yake da lissafinsu da kuma alwashin birkitosu cikin da'irarsa.

Hakanan tafisu takejin maganar kamar tayi nauyi da yawa. Duk da cewa bayajin yaren amma wanda ake shirya komai a kansa?,kuma don saboda shi yana tsaye a gurin?.

"Maleeka......kibi a hankali kada ya fahimci wani abu" Murmushi ta saki me cike da izgili,sannan ta maida dubanta ga haisam dake takowa saman shimfidadden lallausan kilishin da aka qawata gurin dashi,ta saki masa murmushi cikin nuna alamun girmamawa.

"Qaraso sheikh,bismillah". Kai ya jinjina a hankali,yana sake riqe kansa da kyau gami da hanawa kansa nuna wani alama dazai bayyana shi din jinin OROMIA ne.

Maida kallonta tayi kan tafisu da wani salon kallon izza da isa.

"Ba wani alama tattare dashi dake nuna yasan yaren oromo.......oromia basa buya.....basa iya boye yarensu,yanayi da zubinsu da al'adunsu basa canzawa da wuri,ko ke kin manta yadda dukkanin ayarinku akasha wahala daku kafin ku saje ku koma ABZINAWA?" Murmushi tafisu tayi tana jinjina kai.

"Anyi haka maleeka". Sai itama mammina din ta jinjina nata kan

"Iya wannan ya isa amsa tafisu,kina iya tafiya,kafin mu kammala din naga tamim"

"A kammala lafiya" Ta fadi ta yunqura tana miqewa.

Saida tafisu ta kammala fita gaba daya sannan ta tattara hankalinta akan haisam,haisam din dake riqe da wayarsa yana sarrafata hankali kwance,saidai kunnuwansa da kwanyarsa suna bibiye da kowanne lafazi da zai fita a bakin mammina din.

"Ina neman afuwa sheikh......duk da tarin uzurori da nauyin masarauta dake kanka amma na matsanta game da batun neman haduwarmu dakai" Ta fada cikin kwantar dakai sosai,nuna karaya da tausasawa. Sai a sannan ya daga kanshi daga wayar,bai kuma kalleta kai tsaye ba saida ya yiwa wayarsa ma'ajiya sannan ya zube dukkanin idanunsa a kanta yana soke yatsun hannunsa cikin na juna. Wani irin magnet ya fusgeta da kyau,wasu kamanni suka gilma daga tsakiyar qwayar idanunsa cikin nata,sai tayi saurin janye qwayar idanunta a nashi can qasan ranta kuma tana tambayar kanta

"MENENE WANNAN?" Maganarsa ta kawar da tunaninta.

"Ba damuwa ranki ya dade". Har tsakiyar kanta taji kiranta da yayi ranki ya dade din bai zauna mata ba,don yau din a wannan lokacin kuma shine karo na farko data fara jin kalmar a bakinta.

"Aiki ne me muhimmanci a gabanki ZEENATU... Meye tattare da matashin malamin da zai firgitaki har haka?!!!" Wata zuciyar ta tsawatar mata,abinda ya sanya ta sake maida dubanta kansa a karo na biyu,saidai wannan karon ta kaucewa duban tsakiyar qwayar idanunsa kamar dazu,shima kuma ya karanci hakan.

"Na gode" Ta fada da murmushin nan.

"Bismillah.... Ga kayan sha da naci" Ta fadi tana nuna gaban shimfidarsa inda aka shirya komai. Sai daya dubi dukka tulin kayan da bai amince da koda cup daya dake gurin ba ballantana su kansu tarkacen cimar da aka cika gurin da ita,tamkar wanda aka gayyata wani party sannan ya maida dubansa a kanta.

"Godiya nake" Kawai ya furta a nutse. Ko a rayuwarsu ta yau da kullum,a tsarin aikinsu na security ba'a kowanne guri suke amincewa da kowa ba,kaman yadda ba'a hannun kowa suke amsar abu suci ba. Koda a office dinsu dake hukumar tsaro ta farin kaya masu girkinsu amintattu ne,musamman irinsa da suka zama manya. Uwa uba ma kuma shi din yana da bala'in tsantsami,ba kowacce mace ke masa girki yaci ba,wannan ya sanya Aanani ke yawan gulmarsa a bayan idanunsa.

"Captain din tsirfa......captain obbo inda macene nanay mun shiga uku" Bakinta baya gajiya da fadin hakan,musamman duk sanda zata tarara da nanay da shekarunta da komai.....duk da tarin hadimai dake gudanar da komai na gidan amma zaka sameta a kitchen a tsaye akan abincin Muhammad haisam din. Randa ta karkace tanaga gulmarsa,sam batasan yana qofan kitchen din ba,ya shigo gaida nanay dinsa ba,saida saamee ta tabata suman zaune tayi,baice mata qala ba ya qarasa shigowa kitchen din,ta samu ta sulale,sai data debi sati guda cur bata bari sun hadu ba,duk da sau tari shirunsa tasan wani punishment ne me zaman kansa,ta samu da qyar dai tasha zancan yabi ruwa,sai bayan wani lokaci ya tarfata. Bata da hanyar goge kanta,sai kawai ta fashe masa da kukan da tasan ya tsana,tattarata yayi yace ta bace masa da gani.

"Akwai muhimmiyar magana da nakeso muyi dakai.....wani muhimmin abu nake dauke dashi,wanda ba wanda ya cancanci samun wannan abun.... Wannan damar ta musamman face kai" Kai ya gyada a hankali yana ci gaba da dubanta don tabbatar mata yana tare da ita. Zamanta ta gyara sosai,tana kuma sauya yanayin fuskarta zuwa jimami da rashin sukuni.

"Ba shakka kai din wani babban mutum ne da ake girmamawa a nan,sunanka tsaftatacce ne......sannan mu'amalarka da jama'a me kyau ce kowa ya shaida hakan...." Saita dakata a hankali sannan ta dora.

"Magana ce akan shalelen sultane wato akhnan....." Wani yanayi ne a hankali ya ratsashi,ya kuma sake sanyawa ya tattara hankalinsa. Ba wani magana a bakin matar da zata zama me muhimmanci matuqa a tare dashi,amma kuma dole ta zama wani abu da za'a bawa nutsuwa....duk wani motsi nata.....duk wani fitar furuci daga bakinta ya sani tabbas YANA IYA KASANCEWA WATA SABUWAR RAYUWA.....WANI SABUWAR MASIFA GA RAYUWAR WANI,walau ta ambaci sunansa ko bata ambata ba.

"Duk da abubuwa da yawa sun faru,wadanda suka darsa fushin sultane a kanta,suka koma jawo raunin mu'amala a tsakaninsu,amma hakan ba abinda zai canza game da matsayinta a zuciyar sa......sannan kuma babu abinda zai hanashi yaji ciwo,kuma yaji zafi idan wani abu mara kyau yasameta". Still yana ci gaba da saurarenta ne ba tare daya furta komai ko ya motsa ba.

Readers Also Read

More by Huguma