Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 46

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 46

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 46: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 46. "Akhnan ta hadu da jarrabawar rayuwa ita sahihi kuma…

3,350 words

"Akhnan ta hadu da jarrabawar rayuwa ita sahihi kuma ingantaccen mijin data zaba....wanda a zahirin gaskiya ba qarya bane ya dace da ita. Suna yiwa junansu wani irin so dani kaina bansan dashi ba sai a yanzu bayan ya saketa kwanaki uku bayan daura aurensu,bisa makircin wasu da har yanzu ban gane su waye ba. Sun bugar dashi sun sanya ya fita hayyacinsa a ranar farko da zasu fara ganin juna,ya kuma yi mata mafi munin saki wato saki har uku" Saita dakata tana wani ajiye numfashi cikin nuna yanayin alhini na gasken gaske. Idanunsa ya lumshe a hankali ya sake budesu a kanta. Yana yabawa da jinjina yadda ta iya tsara wasan kwaikwayo me kyan gaske irin wannan. Yadda ta zama gagarumar me laifi da yadda ta maida qarya ha'inci da zamba cikin aminci ne kawai ke tafasa masa zuciya. Ba abinda yafi tsana kaf rayuwarsa irin qarya,ita kuma ya lura cewa tafi girmama QARYA sama da komai. A yadda take maganan nan banda dashi muhamamd haisam take magana.....mutumin dake kallonta tarrr a tafi hannunsa ba abinda zai hana tausayinta ya kama wanda take maganar dashi,ba abinda zai hana imani ya shiga zuciyar dan adam a kanta,wannan kadai ya sake tabbatar masa ME HADARI CE ita.

"Saki sheikh hasaim,wani abune dake barwa mace tabo koda bata da laifin komai yayin sakin......musamman saki irin wannan da aka yoshi a sanda ake ganiyar dokin haduwa da juna,ake kuma tsananin qaunar juna......"

"Ina ganin zaifi kyau ki wuce kai tsaye zuwa dalilin kiran" Ya samu kansa da katseta haka kawai yana jin bayanan nata sun fara cika masa kai. Cikin wata irin dabara ta qare masa kallo. Cikin izza yayi mata magana,tamkar dai tana magana da sultane. Ta sake duban yanayin zamansa dake nuna zallar QASAITA irin xaman da ba wani bawa ko hadimi daya taba zuwa gabanta yayi irinsa. Wani abu ta hadiye ta turashi can cikin maqoshinta,sannan ta qwaqulo murmushi ta aza saman fuskarta.

"Inaso na samar mata da nutsuwa,inaso na samar mata da daidaito cikin rayuwarta a matsayinta na amanar Allah a hannuna" Ta fadi tana dunqule hannunta. Sosai maganar ta wani irin ratsashi AMANAR ALLAH data kira ya sanya ya sake bude idanunsa sosai a kanta. Tabbas batasan girma da illar maganarta ba,tabbas batasan waye ALLAH ba......babu ko shakka batasan matsayin AMANA a musulunci ba,da bazatayi wannan furucin ba,sai ya sakejin matar gaba daya tana saare masa a rai....duk dama bai kamata ma ya tsammaci imani ko sanin Allah a tattare da ita ba.

"Naji cewa a musulunci ba laifi ko kuskure game da hada AUREN KISAN WUTA ko kuma AUREN YARJEJENIYA muddin bada sanin mace ba ko?....ko bada sanin miji da matar ba......muhammad,kaf duniya sultane bashi da wanda ya aminta dashi sama dakai......da kai kadai ne nima na aminta,na kumayi amannar cewa zaka iya taimakawa akhnan kamar yadda itama zata taimakeka" Sai ta dakata tana dubanshi kafin ta qarasa farke manufarta gaba daya,duk da tasan zuwa yanzu koda bai fahimceta gaba daya ba ya fahimci fiye da rabi na abinda take nufi.

Shima dubanta kawai yakeyi,hauka qarara kuma yake gani shimfide cikin maganganu da kalamanta. Jira yake ta qarasa fadin abinda take niyyar fada din a yanzu,abinda kawai ya rage masa kenan.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 79*

"Nayi imani kai ka dace.....auren KWANGILA AUREN YARJEJENIYA......bisa dokoki bayyanannu......ba takura ba matsantawa......ba sanya qa'idojin da zasu takuraka......ka auri akhnan na watanni biyu zuwa uku kawai.....don ka kubutar da ita daga fushin sultane,don kuma ka bata daman komawa abinda ranta yakeso......wanda dukkanin haka idan ya tabbata,ba shakka zakayi bankwana da sunan SHEIKH zuwa MILLONIER". Tana kaiwa nan ta dakata zuciyarta na wani far far da yadda taba ya zuba mata ido calmly yana kallonta,saidai abinda bata sani ba,wannan calmness din ya bayyana ne kawai iya saman fuskarsa......wani irin zafi yakeji zuciyarsa tana masa......

A zahirin gaskiya ba zaituna idanunsa suke gani ba,hakanan ba zeenatu idanunsa suke gani ba.....wata halitta ce daban datayi nisa da tsarin halittar dan adam. A kudin duk da take ganin zata bashi baya tunanin zasu kai adadin kudin ciyar da marayun da yake fitarwa a shekara daga cikin dukiyar da Allah ya bashi. Me yasa ita kanta yarinyar ta maida kanta tamkar wata HAJA a kasuwa?. Me yasa ta kasa fahimtar MARTABAR kanta?,me yasa take damqa dama da ragamar rayuwarta a hannun matar?. Me yasa GIRMAN KAI take bari yake yaudararta?. Koda wasu abubuwan shirya mata ake tsara mata ake.....amma lallai akwai hadin kanta me yawa a tattare da faruwar komai. Wani irin hatsari ne girma yake hanga tattare da rayuwarta,ita me yasa ko sau daya ta kasa hangowa kanta wannan?.

"Kada kace zakayi jayayya sheikh haisam.....Allah yana sonka da rahama shi yasa ya watsoka cikinmu a irin wannan lokacin.....shi yasa ya kawoka ya damqa wannan damar ta fado hannunka,wadda dama ce dana tabbatar miliyoyin maza suke nemanta koda ba za'a biyasu da komai ba......kawai su amsa sunan mijin GIMBIYA KHADEEJA SULTANE MUHAMMED HAMMUD kadai nasara ce a tare dasu" Tayi saurin fadi saboda tsoron kar amsarsa ta fito ba yadda takeso ba.

"Amma me yasa sai ni?" Yayi mata tambayar da salo na titsiye yana dubanta kai tsaye cikin idanunta. Kanta ta kawar kadan,da gaske idanunsa yana mata wani irin nauyi da kwarjini tamkar dai idanun IBRAHEEM.

"Saboda kai din ba dan nan bane.....kai din ba jinin SARAUTA bane......sannan na sani mutane ire irenka da dama suna zauna a masarautar nan.....amma basa dogon zango suke tafiya suyi gaba". Akwai wani abu cikin maganganunta daya tsinkaya.

"Kin saka zato da yawa a kaina" Ya fadi kansa tsaye. Kai ta gyada

"Saka zatona me yawa a kanka yana da alaqa da kula da mu'amalarka motsinka da takunka" Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu lokaci daya. Koda batayi subutar bakin fadin hakan ba ya sani......har yanzu akwai wanda ke bibiye dashi,kuma yana dab da durqusar dashi a gabanta saman gwiwoyinsa ya kuma tilastata bada ba'asin hakan.

Tsaf ya karanci tsoron a idanunta,kuma yanaso ya tabbatar mata da wannan tsoron,don haka ya miqe a nutse yana zube hannuwansa cikin aljihun jubah dinsa,abinda ya sake qara masa kwarjini kenan,idanunsa fes cikin nata.

"Lokacin da mabuqata akan samun wata dama suka yawaita......wani mutum qwaya daya yace baya buqatar wannan damar da shi ta fara zuwa hannunsa......ina kyautata zaton sauran da zasu samu hakan zai faranta musu fiye da zato......bana cikin wannan tsarin ranki ya dade,na gode sosai da tayin dama". Ya qarasa fada cikin nutsuwa yana takawa a hankali ya doshi qofa.

Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata,ta miqe tsaye cak tana kallon yadda yake yakunsa a nutse hankali kwance.

"Muhammad.....kada zuciyarka ta yaudareka kayi gangancin barar da buqatata.....yin hakan tamkar kirawa kanka masifu ne da bakasan iyakacinsu ba......komai zai iya faruwa da kai,komai zai iya faruwa da ahalinka dama dukkan wani makusancinka......" Tayi maganar da hargagin daya tilasta tafisu shigowa gurin da sassarfa,saboda yadda harshenta ya dagu har sautin yana yin nisa da inda suke tsaye.

Cak yatsaya,tsaiwar kuma data bawa mammina relief,har ta fara tunanin samun saukowa daga gareshi.

Saidai koda ya juyo gareta yanayin fuskarsa kadai sai daya sanya hanjin cikinta curewa guri daya.

"Kiran sunan AHALINA kawai lokutan shirme irin wannan akan harshenki zaituna zai iya zama babban kuskure a gareki" Iya gajeriyar kalmar daya fada kenan ya sake juyawa,saidai kuma girman kalmar ya daki zuciyar mammina da wani irin tarin mamaki da jin QASQANCI a tare da ita.

Babu wata rana a rayuwarta da zata iya tunawa wadda aka tsaya a gabanta aka gaya mata magana me kama da wannan. Ba wani dan adam me rai me qafa biyu ido biyu hanci daya daya taba jefa mata magana me tsauri irin wannan.

"Damar da qasqantaccen mutum irinka ya samu shine yake zaton KIMARSA da martabarsa takai da zai iya tsayawa gaba gareni ya gayamin duk maganar da tazo ranshi?......kana zaton akwai wani DARAJA da kake da ita ne da har ka cancanci ka rabi koda sunan SULTANE MUHAMMAD HAMMUD?. Kana zaton banda ni da zan zameka maka tsani har ABADA ka isa ka amsa sunan MIJIN GIMBIYA KHADEEJA koda na rabin second ne?.....baka da wannan damar HAR ABADA baka da wannan MARTABA DA DARAJAR......qasqantacce dama zai tabbata a yadda Allah ya halicceshi ne....koda kuwa an nufeshi da arziqi ne.....ka rubuta ka ajiyr har abada kaida samun wata martaba ko daukaka a rayuwa....zaku tabbata a qasqantattu qarqashin alfarmar wasu KAIDA DANGINKA GABA DAYA....KUDA MARTABA HAR ABADA!!!" Ta fadi maganganun da wani irin zafi har sai da tafisu ta riqeta.

Tsaf dukka kalamanta sukayi masauki a kunnensa. Wani iri murdawa zuciyarsa takeyi.....wani irin tashi jijiyoyin kansa kawai sukeyi. Wani irin fushinsa ne daya jima bai motsa ba yake motsa masa. Kansa ya wani harba da kalar bacin ran da yakejin dacinsa har saman harshensa.

AHALINSA da DANGINSA da take fada ya hada da NANAY da kuma MOTII ciki. Tsigar jikinsa ta zuba hannuwansa suka dauki rawar daya tabbatar idan fushinsa yakai wannan gejin akwai matsala ta gasken gaske,kuma komai yana iya faruwa,don haka ya sauya akalarsa zuwa daya daga cikin kebantattun guri na gidan.

Yatsunsa kawai yake cusawa cikin sumar kansa yana zarewa,can qasan ransa yana maimaita fadin.

"A'uzubillahi minash shaidanirrajeem" Ya sani,fushi irin wannan daga shaidanne.....kuma a hankali yaji qirjinsa yana sassauta daga yanayin da yakeji.

Nutsuwarsa ta dawo jikinsa,ya dinga zuqar iska yana fesarwa. Ya zama dole ya nunawa matar cewa YA ISA isar kuma da bata da alaqa sam da samuwarta. Zai sanya wani tabbataccen alqalami,ya kuma zana mata rubutun da ko nan da shekara dubu duk inda taji ance wannan sunansa MUHAMMAD sai hantar cikinta ta kada......zai sanyata da bakinta da kanta ta bawa wasu labarin wannan ISA da take inkarin yana da ita.

Kiran daya shigo wayarsa ya dauki hankalinsa kadan,kamar bazai duba ba sai ya tuna jiya bobbo yanata kiransa,abinda ya sanyashi cusa hannunsa a jubha dinsa ya fiddo wayar.

Bobbo dinne yake kiransa,ya fesar da iska kadan daga bakinsa yana daga Kiran ya saka a kunnensa.

"Kana lafiya kuwa Muhammad?" Shine abinda ya fara tambayarsa bayan sallama

"Alhamdulillah bobbo" Shuru ya ratsa kadan,yanayin muryar haisam din tana qaryata masa maganarsa. Ya san halinsa sarai,idan ya boye maka abu,bai shirya gaya maka ba,barinsa shine yafi,don haka ya sauke ajiyar zuciya yana cewa.

"Shikenan.....Allah yayi muku jagora......kunyi magana ne da sultane." Kai ya gyada tamkar yana gaban bobbo din. Har yanzu yanajin daci saman harshensa

"Munyi magana.....inaso ka shaida masa na amince......ka gayawa motii amincewata shima". Sosai bobbo yayi shocked,maganan na zuwa masa a bazata.

"Muhammad.....wanne irin hukunci ne haka da sauri?" Kansa ya sake girgizawa yana hadiye wani abu da qyar. Banda bobbo dinne tsinke wayar yafi muradin yi baci gaba da magana ba,don a duk sanda yake cikin fushi irin wannan yana taqaita magana ne qwarai gudun dana sani

(Wannan din koyarwar ma'aiki ce,idan har kana da dabi'ar yin shuru a sanda ranka ya baci ko yake bace,to tabbas ba zaka zama me nadama ba,amma muddin ranka yana bace kuma kace sai kayi magana,ko sai ka dau mataki,to akwai yuwuwar nadama da danasani me yawa a tare da kai)

"Wannan hukuncin dana dauka bobbo shine abinda ya kamata nayi.....shine abinda ya dace kowanne da na halak yayi".

"Amma kana tunanin d'iyar abokin mahaifinka ta zame maka wata garkuwa ne bayan garkuwar da akayi da ita ba tare da tasan da hakan ba?". Sai a sannan maganar bobbo ma ta harba masa wani abu cikin kansa.....sai a sannan yasan AUREN zai iya zamewa mammina wani BABBAR BARAZANA koda bai nufaci ya zame mata barazanar ba,koda iya manufarsa ta nuna mata ISA ce kawai. Baisan murmushi ya subuce masa har sai da shuru ya gilma.

"Zanji komai daga gareka bobbo bayan wani lokaci......zan zameta GARKUWA ne bawai ita din ta zamemin GARKUWA BA. Namiji ako yaushe zama yake madubi bawai ya buya a bayan wani ba ya zame masa madubin ba.....namaji GARKUWA ne bobbo.....zan zame mata garkuwa saboda albarkacin SAFEENA albarkacin NANAY......zan zameta GARKUWA ne zuwa lokacin da zan amintar da rayuwarta......zan sakar mata 'yancinta a sanda dukka wasu kuraye dake farautarta suka kwanta dama.....suka tsoraci kusantar inda take. Taci albarkacin SAFEENA taci albarkacin NANAY......uwa uba kuma ZUMUNCI ya siya mata wannan damar ta qayyadaddun lokuta.....badon MORSA SAFIYYA BA....ba don SULTANE Ba......albarkacin IGIYAR ZUMUNCI.....Albarkacn nagartacciyar uwa da QODARTA har yanzu ke rayuwa jikin YARUWA GA NANAY DITA. Zamuyi sauran magana bobbo.....amma a yanxun shuru nake buqata,amma Amincewata ta isa ga sultane da motii,kome sukace bobbo na baka dama akan hakan.......TA KIRA WUTA da kanta batasani ba......tayi wasa da DAFIN MACIJI tana tunanin ordinary ruwa ne kamar kowanne kalan ruwa" Yana kaiwa nan ya katse kiran a hankali yana jin wani sassauci a ransa.

Ya sani bobbo zai iya qalubalantarsa......amna a yanzun da kwanyarsa ta harbo masa tarin gajiyar da auren Akhnan zata mallaka masa gurin sake dulmiya mammina da sanyata fiddawa duniya da nunawa duniya cewa itadin asalin CRIMINAL ce,sai yake sakejin ba wani abu da zai dakatar dashi daga karbar auren Akhnan din.

*MAMMINA*

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 80*

"Allah ya taimakeki.....ba girmanki bane,kinfi qarfin kiyi jayayya da wani....kinfi qarfin wani dan tsako ya daga hankalinki wallahi" Tafisu ta fada cikin tsantsar girmamawa tare da son kwantarwa da mammina hankali. Da idanunta da suka sauya launi ta dubi tafisu dake durqushe a gabanta kamar me neman rahama,kamar itace tayi laifin,kallonta take sosai,tana son taji ko yaya ta yarda da kalaman tafisun akan cewa haisam din dan tsako ne,amma kuam zuciyarta ta gaza gasgata haka.

"Ina me tabbatar miki koda ace ya nuna miki taurin kai.....koda ace ya nuna miki yana kan bakansa.....koda ace ya nuna jarumtarsa.....tabbas can qasan zuciyarsa cike take da TSORO da kuma d'ar d'ar.....don ba wanda ya isa yayi jayayya dake ya kwana lafiya......ya tashi qalau cikin zuciyarsa.....kwarjininki da girman ikonki cikin qasar nan kadai ya isa kowanne dan adam shiga fargaba da zullumin saba miki". Wani numfashi sosai mammina taja. Karon farko da taji zuciyarta sam bata aminta da zantukan tafisu ba,karon farko da taji har cikin jikinta cewa zantukan tafisu na faranta mata ne zallah bawai na fadin anihin abinda yake shine gaskiyar magana ba.

Sai data tabbatar ta soma dawowa saitinta ta hanyar zuqar iska da fesarwa sannan ta kalli tafisun.

"Na rantse shine zaiyi wannan aikin.....don shi na hangowa cancantar yin aikin a sauqaqe.....sannan duka tsarin dukkanin plan din nasa ne.....QADDARAR wannan karon tashi ce" Ta fada da wani irin zafi

"Tabbas....babu ko makawa" Tafisu ta jaddada tana gyada kanta,wanda basu kai qarshen zancan ba yalwa ta shigo duka ilahirin jikin yalwa din yana tsuma.

Ido mammina ta tsareta dashi,yayin da yalwa din tayi qasa da kanta tana jiran umarnin fara magana daga gurin mammina,duk da yadda hanjin cikinta yake kaduwa. Cak mammina ta dauke kanta daga duban yalwa din,ta maida dubanta wani guri daban.

"Ki gaggauta fadin abinda yake tafe dake kafin fushina yakai ga sauka a kanki"

"Allah ya taimakeki.....tamim ne ya iso.....yace kuma cikin gaggawa yakeson ganawarku sama da duk irin gaggawar daya taba gabatarwa a gabaki".

"Ya shigo......yalwa" Ta bada umarni gami da kiran sunanta.

"Ina amsawa ranki ya dade"

"A tabbatar an nesanta duk wani me rai daga wannan area din" Ta fadi still idanunta na kallon wani guri daban,tana sauraron wani irin bugu da zuciyarta takeyi. Wani yanayi ne da muddin ta jishi tattare da ita yake alamta mata sunan MATSALA. Wani yanayi ne data tsani jinsa a tare da ita,yayi da can qasan zuciyarta yake danqare da tsanar haisam.

Silar banzayen dokokinsa ya sanya zata gana da tamim a karon farko kan wata magana da tafi.mata rayuwar duk wani me numfashi dake masarautar muhimmanci.....zata gana dashi a budadde guri irin wannan da bai dace da sirri irin nata ba.

Tafisu ta gani tana miqewa tsaye,saita waiwaya a hankali tana duban inda tafisun ke kalla.

Tamim ne ke takowa da wani irin sassarfa.....da wani irin yanayi me nuna zallar rudewa da dimuwa a tare dashi. Abinka da dogo kuma zabgegen mutum,ko ina na jikinsa gaf gaf yakeyi,har zuwa sanda ya qaraso gabanta ya kuma zube kamar me shirin tafiya sujjada.

Samun kanta tayi da gaza tambayarsa.......saita bishi da idanu sanda yake cusa hannunsa cikin babbar rigar jikinsa dake dauke da tarin aljihun da wani ma baisan da zaman wani ba,ya zaro wasu takardu yana miqasu kai tsaye ga mammina. Hannunsa dake riqe da takardun wadanda suke rawa tabi da kallo,dukkaninsu daga su har takardun shaking suke,sai kawai ta miqa hannunta ta karba din,ta koma da baya ta zauna ta fara budesu.

Wani irin yanayi taji yana saukar mata,a hankali taji ta fara daina gane komai daga karanta layi uku kadai da tayi na takardar wanda yake dauke da rubutaccen saqo da yaren oromo.

Gumi na lokaci daya ya yanko mata,iya abinda idanunta suka iya hange qwaya daya ne da take ganin kamar ga cika takardar gaba daya "ABA JIFAR ROYAL BLOOD". Bata sani ba.....tsohon karonta da MASARAUTAR karon da bai mata dadi ba ko qanqani shine yake son farautarta a yanzu?,yake mata yawo da qwaqwalwa da kuma tunaninta?,ko kuma da gaske sunan take gani jikin takardar. Sakin takardar tayi ta sulale tana duban tamim.

"Ba karatu a takarda nake buqata ba.....don ba ita na aika ta samomin muhimman bayanai ba.....NAMIJIN DUNIYA TAMIM nake buqatar gani a gabana.....ba zaburarren bawa ba,me kama da kazar da aka tsoma cikin ruwan sanyi". Wadannan maganganun nata sun dan tattaro kadan daga cikin qwarin gwiwar dake maqale a wani saqo na zuciyarsa,sai ya zauna sosai yana qoqarin share zufar fuskarsa.

"Uwar gijiyata....bincike ya cimma agadez!!" Ya fada da wani sauti daya aike da wani kalar razani kowanne lungu da saqo na jikin mammina. Wani irin abu yarrr ya sauka a jikinta yana zartawa har tsakiyar kwanyarta. Wani abu takeji yana kurkkurdawa kowanne lungu da saqo na jikinta,wani irin matsanancin mamaki yana cikata. Koda ace tana zaton anaci gaba da bibiyar sawunta ne.....amma koda wasa.....ko a mafarki bata taba tunanin akwai wanda hasashensa zai kawo ga AGADEZ din ba.....bata tunanin akwai wanda zaiyi tattaki ya tsoma kansa a bala'i wajen tunkararta cikin agadez ba. Agadez din da take jinta tamkar wani GIDA nata mallakinta da take da ikon sarrafashi da kuma juyashi. Agadez din da take da tabbacin ta kowacce fuska cimmata a cikinta zai zama abu me wahalar gaske.

"Wa ya taka wannan hanyar?" Ta jefawa TAMIM tambayar da idanunta da suka sauya launi tana dubansa.

"Ba'a ambaci suna kai tsaye ba......saidai inkiyar dana jima da saninta.....inkiyar dana jima da sanin tasirinta da kuma hadarin da take dashi.....bansan ma'abocin inkiyar ba......amma kuma hadarinsa kaifin kwanyarsa da tasirinsa a hukumar ya zarta na kowa.....naso sanin fuskarsa tun a wancan zamanin.....amma akwai wani irin amana da kutsen me kutse gurin samo sahihan bayanai yake wahalar gaske......"

"Duk inda kaji jita jita akwai qamshin gaskiya tattare da wannan labarin,koda kuwa zai kasance kaso casa'in cikin dari na labarin qarya ne.....mece inkiyar tasa?"

"Al-saamit......the silence one.....mai shuru" Sunan ya harba wani abu cikin kwanyar mammina sosai,ta girgiza kanta da gaske kafin tace.

"Shuru makami ne na gasken gaske,makami ne na masu hikima dabara da tsananin wayo.......waye ya aikoshi?"

Readers Also Read

More by Huguma