Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 47

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 47

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 47: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 47. "Ba'a bayyana ba.....amma dai hukumar tsaro ta masu…

3,366 words

"Ba'a bayyana ba.....amma dai hukumar tsaro ta masu tsananin kaifin basira.....wayeshi kai tsaye da kuma wanda ya aikoshi abune da bai gama bayyana ba,an boye bayanan sosai".

"An boye ko kuma an kare?" Sosai tamim yakejin wani gumin yana tsatsatsafo masa. Yanayin tambayoyin uwar dakin nasa yana jinsu a yau da wani irin tsauri da nauyi a kansa.

"Dukka zai iya yiwuwa.....saidai a dabi'unsa baida yawan magana.....baida yawan tambaya.....saidai yawan sauraro....sanya idanu cikin hikima har zuwa sanda zai gano bakin zaren". Shuru tayi me wani irin zurfi,tana kuma zubawa guri daya idanu.

"Yasan abinda yake nema.....tabbas ko waye suka aiko yasan abinda yake nema" Ta fada tana jijjiga kai

"Yana cikin mu.....yana a kusa damu,alamun da jikina ya dade yana bani ba qarya bane,alamun da jikina yaketa karantamin gaskiya ce da ba qarya a cikinta....wasu abubuwan sunzo a rufe....amma ba zasu gagari zeenatu ba"

"Zanci gaba da bincike ne?" Tamim yayi tambayar da madaukakin tsoro da fatan a bashi dama ya toshe duk wata hanya duk wata kafa da qofa.

Wani kallo ta watsa masa tana qanqance idanunta.

"Karka qara kowanne motsi,kada ka qara kowanne taku,ci gaba da bincike yana iya fadakar da maciji.....amma kuma......me sunan ABA JIFAR yakeyi jikin takardar?". Zama ya koma yayi sosai yana jin yadda cikinsa ke hada gangamin zazzafar gudawa,shi kansa iya bayyanar sunan kadai ya masa wani irin gigita da kuma ba zata.

"Akwai kyakkyawan zaton ya fito daga masarauta.....akwai kyakkyawan zaton Prinsii ne cikin jerin masarautu ukun da aka bani......masarautar jimma......."

"Dakata!" Mammina ta dagawa tamim hannu tana tsaidashi da wani irin mahaukacin bugun zuciya.

"Kada ka qarasa lissafo kowacce masarauta a ciki......tafisu...." Ta kirata tana maida dubanta kanta.

"Allah ya taimakeki" Ta amsa tana rusunawa.

"Jinin IBRAHEEM kenan fa?.....indai ya tabbata prince of jimma ne ya shigo AGADEZ?"

"Qwarai kuwa" Tafisu ta amsawa mammina da wani irin qaqqarfan amo dake bada tabbaci ga mammina din.

Cak mammina ta miqe tsaye,tana jin kamar zama yana shirin gagararta. Gwara kowanne dan aike.....gwara kowanne dan leqen asiri da ace JININ IBRAHEEM ke farautarta.

"Wanne D'A ibraheem ya sake samu?.....wanne d'a ibraheem ya sake haifa dake da tsananin tsaurin ido haka?. Hala ibraheem bai gaya masa wacece ZAITUNA ba kafin ya jefo kansa da kansa a da'irata?.....kafin ya jefo kansa da kansa a TASKU na da BALA'I na?"

"Wanne tabbaci kike dashi dan masarauta jimma ne ranki ya dade?". Wani irin murmushi mammina ta saki,sannan ta juyo tana duban tafisu.

" Kinsan QARFIN JININ OROMO?.....KINSAN JARUMATA DA SADAUKANTAR DA SUKA GADA SAMA DA KOWACCE KINGDOM data taba wanzuwa a HABASHA?.....Kinsan waye ibraheem?......kinsan meye zai iya aikatawa da wanda bazai.aikata ba?.....ibraheem shine mutum qwaya daya da yafi kowa sanin sirrikana......mutum daya days gagareni na kauda shi,mutum daya da yafi SULTANE sanin wacece zeenatu zahirinta da badininta.....masarautarsu ba banzar masarauta bace....masarauta ce da JARUMTA da SADAUKANTAKA ce ta ginata.....masarauta ce da tun a baya ta gagari QABILATA dama sauran QABILU.....IBRAHEEM shi daya ne nake qarfafa zargina a kansa......masarauta OROMO....amma zan gani.....zan gani....zan gani,kafin sannan.....tamim.....na baka nan da awa daya kawai,ina neman alqalumma da jadawalin baqin da suka shigo shiyyar na dama cikin masarautar nan gaba daya".

"An gama" Ya fada yana miqewa,gami da tsatstsafe gumin daya jiqa masa gaban riga da hannun babbar rigarsa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 81* __________________________ *_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_* https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

*BAYAN AWA DAYA*

A iya awa dayar data bawa tamim,ta kasa zama ta samu nutsuwa koda na minti biyar ne. Kaiwa kawai da kawowa takeyi tsakanin parlor dinta data koma,saboda tana jin iskar gurin da hasken gurin kamar sun mata kadan gaba daya.

Duka ta tsiyayar da tunaninta ta kuma qarar dashi akan hango wani abu da taga ya sauya tattare da ita mu'amalarta da mutane ko jama'ar da suka shigo rayuwarta suka kuma fita a watannin. Tako ina idan ta zagaya tunaninta mutum DAYA take gani.....hasashenta mutum daya yake hanga......saidai ba wani dalili ko hujja me qarfi da zata iya riqa.

Zama tayi bayan cikar awa dayar,tana jin gaba daya tunaninta ya gama jigatar da ita.

"Akwai wanda kike zargi?.....akwai wanda hasashenki yake kaiwa kansa?" Mammina ta tambayi tafisu idanunta a kanta. A nutse tafisu ta girgiza kai

"Zuwa yanzu tunani na baikai kan kowa na tukunna......amma mu jira.....mu dakaci dawowar tamim....zai iya yuwuwa mu samu haske daga alqalumansa"

"Amma baqon malamin da na yiwa tayin auren akhnan fa?" Daga kai tafisu tayi tana dubanta,kafin a hankali tace.

"Me yakai tunaninki kansa haka?". Shuru mammina tayi na wasu sakanni,sannan ta sake fesar da iska.

"Akwai tarin wasu abubuwa dana jima ina mamaki tattare dashi.....har yanzu banga alamun rauni ko qasqanci tattare dashi ba,mutuwar zuciya,fadanci neman shiga iin wanda nake gani tattare da dukkan malamin daya rayu cikin fada qarqashin umarnin masu mulki......irin dabi'ar data assasa gaba me yawa tsakanin biftu da dukkan wani malamin addini.....MAKAMIN da na fara taqar d'a namiji a zuciyarta dashi kenan. Tun ranar da naji safiyya na fadin burin safeena zai cika na samarwa akhnan miji ma'abocin addini....tun a ranar na daura damarar saqa tsana da gaba tsaninta da dukka wani me irin wannan siffar,.....daga qarshe kuma na tsara idan hakan ta yiwu ma zan sake sanyawa su zama wani dalili na sake bacinsu a idanunta. Ban samu wannan damar ba sai a kansa,don shi daya ne matashin malamin dake da dukka qualities din da nake hange......saidai yana da wani abu cikin jininsa da na kasa gane meye shi.....yana da wata IZZA yana da ZARRA yana da KWARJININ da jikin BASARAKE kawai ake samun kalar wannan kwarjinin......." Maganarta ta yanke da sallamar yalwa.

"Tamim ya dawo"

"Ya shigo" Ta bada umarni nakai tsaye. Dan jim yalwa tayi.

"Shigowarsa nan zata karya doka ne....."

"Ya shigo inji ni ni giwa!" Mammina ta fada da wani irin zafi daya sanya yalwa juyawa ba shiri tayi masa iso.

Kai tsaye ya miqa mata takardar,tafisu ta karba a nutse ta wareta. List na jerin sunan mutanen daya bayan daya ta fara bi tana karantowa mammina. Yayin da parlor din ya dauki shuru,kowa kuma yayi shuru din yana sauraronta.

"Sheikh muhammad haisam......."

"Aba jifar?" Mammina ta samu kanta da qarasawa ta salon tambayar data daukewa kowa wuta a cikinsu,don dukkaninsy basu fahimci abinda take nufi ba,sai kallon kallo a tsakaninsu. Yayin da cikin kanta kuma takejin wata irin zabura sanda lokaci guda sautin haisam din ya karade kunnuwanta da sirrintaccen sunanta na ZEENATU

Sake miqewa tayi tana nufar tafisu,jikinta yana son ya dauki rawa,ta sanya hannu tana zare takardar daga hannunta tana kai idanunta kan list din,saita saki takardar tafisu ta saka hannu ta cafeta.

"Tun daga labarin zuwan.....zuwa hasashen sunansa......karanta sunansa da kuma sake kallon sunansa da nayi a yanzu jinina ke zabalbala.....nakejin wani abu yana harbamin kwatankwacin wanda nakeji game da IBRAHEEM......Bana ko shakka sheikh haisam shine ABUN ZARGINA a yanzu......zan JARRABA hakan.....idan kuwa ya tabbata da gaske.......lallai ya jefo dansa ga halakarsa" Ta fada da wani irin yanayi tana dukan tsakiyar tafin hannunta.

"Prince haisam zaiyi magana.......ba shakka zai bayyana kansa"

"Idan yaqiyi fa?" Tamim da yakejin rayuwarsa ta gama kaiwa ko ina yayi tambayar da bai shirya yinta ba. Shi kadai yasan yadda shehin malamin yake masa barazana a idanunsa.....shi kadai yasan irin yadda kallon idanunsa kadai yake sanya masa firgici......yayi imani idan ta tabbata SHINE lallai zai faraucesu daya bayan daya kamar yadda damisa ke farauta cikin daji.

"Kowanne mutum yana magana tamim....indai ansan yadda ake magana dashi.....TAMIM.......a shirya farmaki.......mafi bada barazana......mafi bada girman gargadi.......qarfafan dakaru nakeso a aika......amma kuma BA RAYAYYU BA......da matattu nakeso nayi amfani,saboda shafe duk wani sahu ko alama da maibin diddigi zai iya bi......Al-SAAMIT the silent one zaiyi magana da gasken gaske.....da kansa.....zai saki signals da alamomi da zai bani hasken shiga lamarin kai tsaye".

"An gama" Ya fada cikin tsoro shakka da kokwanto. Halittar tsoro data jima da mutuwa cikin qirjinsa da zuciyarsa,sai gashi yau THE SILENT ONE da sunansa kawai ya raya wannan halittar.

"Farmakar motii ba wani qaramin abu bane me sauqi.......ka kula......ka kula.....ka kula" Ta maimaita masa sau uku tana masa alama da hannu akan ya wuce.

*HAISAM*

Da wannan zaman nasa dake nuna SARAUTA dake yawo a jininsa yake duban na'aurar dake gabansa. Abood daya daga cikin ma'aikatansu na hukumar sirri ne ke ci gaba da bashi bayanai daki daki kaman yadda ubangidan nasa sheikh muhammad haisam ya buqata da gaggawa.

"Komai data fadi maka ya faru a asibitin haka ne ya faru......saidai kuma tun daga kwanan watan shekaru rana da lokaci dana samu a record dinsu dukka yasha banbam da wannan daka bani a rubuce........iya abinda na fahimta shine,ba wani tsohon ma'aikaci cikin asibitin,dukkaninsu sababbi ne,kuma basusan salsalar asalin labarin ba......suma sunzo ne kawai sun tadda komai a rubuce yadda suka nunamin suka kuma bani. Kowacce qofa obbo a kulle take ta samun komai daya danganci lamarin batan jaririn......ba wata sauran hanya don na gwada duk wata dabarata ban samu wani sabon abu ba kuma" Kai ya jinjina da wannan cikakkiyar nutsuwar tasa da ba komai ke girgizata ba,ya raba yatsunsa dake soke cikin na juna tun dazu.

"Kayi aiki me kyau abood......a huta gajiya,na gode"

"Obboo galatoomaa (thank you" Abood shima ya fada cikin rusunawa da girmamawa.

Idanunsa ya daga a hankali ya zubesu akan omar dake zaune a gabansa yana dubansa. A iya tsahon rayuwar aikinsu omar din bai taba jin wani aiki daya masa nauyi akai.....aiki me wahala.....aiki dake cike da mugun mummunan qulli ba irin wannan.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Shekara talatin ta binne komai?". Idanunsa haisam ya lumshe sannan ya budesu,a zahiri murmushi ne qasan zuciyarsa,amma kuma ya kasance salon murmushin nan nasa dake cakude da miskilanci,don haka ba kowa ke fahimta ba. Ya sani......aiki ne me girman gaske a gabansa......amma baisan me yasa wasan yake masa dadi ba. Komai idan ya tabo ta kowanne bangare sai ya dinga ganin qofa ce me girma take bude masa.

"Shekara talatin bata birne gaskiya ba......tadai lullubeta ne kawai".

"Amma ta wanna fuskar haisam ka fahimta.....komai ya qare fa,ba sauran wani abu da bazai bada haske" Kansa ya girgiza a nutse

"Komai bai qare ba omar......hasalima komai yana sake saitamu ne akan hanya,yana qara nuna mana hanya ne kawai"

"Nuna mana hanya?" Yayi tambayar yana duban haisam cikin mamaki,ta ina ya hango hanyar?.

"Sosai.....ka fadamin.....waye yake da iko ko qarfin gwiwar shiga dakin haihuwa ba tare da barin sunansa ba?" Shuru kada omar yayi kafin ya amsa.

"Only someone above the hospital administration"

"Good" Ya fadi yana gyada kansa da lumsassun idanunsa.

"Waye kuma zai sace yaro ba tare da ya kasheshi ba?"

"Wanda yake buqatar yaron a raye"

"Exactly" Haisam ya sake amsawa omar da wani low tune.

"Amma koda hakan gaskiya ne.....there's no way to prove it now"

"I'm not looking for proofs.....I'm looking for pressure" Ya amsa masa calmly da wani accent cikin English dinsa me wani irin dadi saboda saboda da oromian language da yayi.

"Pressure on whom?" Wannan karon dole wannan sassanyan murmushi ya subuce,kyawawan labbansa suka motsa kadan.

"On the person who has spent thirty years protecting silence"

"Mammina?" Kai tsaye omar yayi tambayar yana duban haisam"

"May be.....amma ka sanya idanu.....mutanen dake dauke da tsaffin sirrika suna da saurin nuna kansu fiye ma da masu laifi a wadansu lokutan". Komai omar ya gama fahimta.....ya gama gane kuma inda haisam ya sanya gaba. Shuru kawai maleek yayi dake zaune a gefe sannan ya saki qaramar ajiyar zuciya. Iya zaman da yayi da aminan nasa a wannan dan taqin ya bashi tabbaci cewa aikinsu sai CIKAKKEN NAMIJI JARUMI daya amsa sunansa. Ya fahimci abubuwa masu yawa,yarukan da baka isa ka iyashi ba idan kai din ba mallakin intelligence agency bane......da gaske aikin na masu INTELLIGENT ne.

" Aure zanyi" Haisam ya saki maganar hankali kwance sanda ya jawo system dinsa da zummar turawa bobbo wasu bayanai

*_Ayimin afuwa,yau dai baqi nayi,ban samu daman rubuta abun arziqi ba,ina fata za'ayimin uzuri,naso yau muzo gurin😂,don nasan abinda duk muke jira kenan harda nima😂_

_na gode sosai,na gode da qaunarku da jumurin bibiyata_🙏🏽

SON SO🥰🥰🙏🏽

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 82*

Dif wuta ta daukewa omari da maleek,kada ma omar yaji labari shida yafi kasancewa da haisam tsahon lokaci sama da kowa.

Yadda sukayi shuru haka yaci gaba da matsa system dinsa hankali kwance,ya basu isashen lokaci da zasuyi mamakinsu su gama,saboda ya sani mamaki dole ne......basu kadai bama,koma waye yazo da wannan maganar tsakaninsa dashi mamakin shine abu na farko da zai fara yi.

Sunsan halinsa dukkaninsu,tunda har yayi shuru bazai sake cewa dakowa komai ba,sai idan kai ka buqaci qarin bayanin.

"Wai.....da gaske kake ko wasa?" Omar ya fadi ba tare da samun yaqini cikin maganarsa ba,saboda kuwa yafi kowa sanin halin haisam din,baya fadin magana sau biyu......baya qarya koda kuwa da wasa ne......sai wasan ma da baya cikin tsarin yanayin dabi'ar halittarsa gaba daya.

"Aure zanyi omar,da gaske nake" Ya sake maimaitawa very calm,abinda ya sake tsumasu da gaske,ya sake kuma tabbatar musu abinda yake fadi din da gaske yake. Tashi maleek yayi daga relaxing din da yayi cikin kujera,ya zauna sosai yana duban idanun haisam dake saman system abinsa hankali kwance. A hankali dariya ya kubcewa omar,don hankalinsa ya gaza gasgata abinda kunnuwasa suka ji masa,duk da baida yaqinin ba gaskiya haisam yake fadi ba. Bai motsa ba bai kalli omar ba,ya barshi yayi dariyarsa yadda yakeso.

Sosai maleek ya tsareshi da idanu,yana karantar gaskiyar dake sama fuskarsa. Sai ya motsa labbansa a hankali.

"Haisam......aure fa?,a daidai wannan lokacin?" Sai a sannan ya dauke dubansa daga kan system din ya zubesu a fuskar maleek. Ya karanci maleek ya soma gasgata maganarsa shi yasa yaga yana da lokacin sake fahimtar dashi.

"Yes.....aure maleek,nan da juma'a in sha Allah.....kwana uku kacal masu zuwa" Idanu suka waro gaba dayansu,omar yana jin kamar wata dabi'a da basusan haisam da ita bane yake qoqarin fara kwatantawa. Suman wucin gadi sukayi,kafin maleek ya qara aro qarfin hali

"Amma haisam wanne irin cin amana ne wannan?......ba sign ba signal......ba alamar komai?". Ya fada yana jin nauyi da girman al'amarin. Bai ce masa komai ba......har zuwa sanda omar yayi nasa qoqarin.

"Wacece wannan a kwana uku kawai haisam?......kwana uku fa?,ko saamee ce?"

"Akhnan ce" Yayi maganar sanda ya zubewa omar dukkanin manyan fararen idanun nan nasa dake da wani irin kwarjini me narka zuciya.

Zabura omar yayi ya miqe tsaye,fuskarsa da wani irin mixed emotion,mamaki......kokwanto.....farinciki da kuma zallar rudewa.

"Akhnan.....akhnan Muhammad hammud?......dama kuna soyayya haisam baka taba bari na fahimci komai ba?" Omar yayi tambayar wadda maleek ma shi sam a wannan karon ya kasa tambaya. Idanunsa ya janye daga kan omar,sai kawai ya fara tattare kayansa da xummar barin gurin,bayajin zai iya zama ya amsa tarin tambayoyin daya fuskanci sun shirya yinsu a kansa d'aya bayan d'aya.

Caraf maleek ya riqe hannunsa gam,sanin halinsa sarai zai iya barinsu cikin rudaninsu. Ba kowanne lokaci yake zama yayi dogon bayani ba.

"Bakka eessayyuu deemuu hin dandeessu (ba zakaje ko ina ba).......akhnan dai kake magana akai kaman yadda omar ya fada?,nima inaso na sani" Maleek ya fadi shima yana tsareshi da idanunsa.

"Eh.....itace" Ya amsawa maleek kai tsaye yana duban cikin idanunsa kamar yadda shima yake duban nasa. Sake masa hannu maleek yayi yana sakin wata dariya shida omar me cike da nishadi,yasan kwanan zancan......yasan kuma me zai faru,idan ma ya tafi a yanzu be tsira ba,tunda suka fara wannan dariyar,sai kawai ya koma ya zauna salin alin,yayi relax sosai cikin lallausar sofa din yana qare musu kallo.

Tsam maleek ya miqe,ya soma takawa yana nufar briefcase dinsa yana fiddo system dinsa.

"Wannan labarin bazai cika ba,bazai kammala ba sai dasu khadeem a kusa......nikam bazanyi wannan cin amanar ba,ayi wannan sha'anin babu su?" Ya qarasa fada yana daidaita system din nasa gami da qoqarin kiran kowa a cikinsu. Idanu kawai ya lumshe,gwara ya barsu suyi iyayinsu,ba lallai su fahimci komai ba......ba kuma lallai yayi musu bayanin komai da komai ba.

Bayaso su kalli lamarin da wani idanu daban,shuru shi yafi dacewa ya zama amsa......koda kuwa hakan yana nufin zasu amince da cewar SHI YA ZABOTA.....shi yake sonta.

Wani irin aminci ne a tsakaninsa da zai wahala wani yaga kiran wani ya share,don haka cikin qaramin mintuna ya hadasu gaba daya,sai gasu sun cika su bakwai cif harda haisam da omar da maleek din dake guri daya a gari daya.

"Me yake faruwa da mr lowering gaze?". Naseeb dake zaune ciki parlor din gidansa yana shan fruit da alamu ke nuna matarsa ce a gefe tana yankawa tana miqa masa ya fadi,ganin har suka gama zama online dukkaninsu haisam bai motsa ba bai kuma ce komai ba.

Murmushi da yafi kama da dariya maleek yayi,irin wanda sunsan ba dabi'arsa bace. A cikinsu dukka shida haisam dinne keda wannan jinin sarautar a jikinsu,so izza wani lokacin zuwa musu kawai takeyi. Dariyar maleek taja hankalin kowa,don Omar gabadaya ya kurumce,bayajin yana da bakin bayani,yayin da ta wani gefe kuma zuciyarsa ta kasa gasgatawa da kuma yarda da inganci da sahihancin auren.

"Lowering gaze ya qare daga yau......mr man aure zaiyi,nan da kwanaki uku masu zuwa kawai". Dariya suka sanya gaba daya,kowa da irin abinda zai fada,abinda ya sanya haisam zama sosai yana ware idanunsa da suka dan sauya launi a kan screen din,wannan ya basu daman ganinsa sosai,sai kuma kowa ya fara komawa nutsuwarsa. Shuru ya ratsa ko ina,ya bude baki da nutsuwar nan da suka sanshi da ita.

"Da gaske maleek yake gaya muku.....ruwanku ku yarda.....ruwanku kuci gaba da duban abun ta fuskar wasa" Yana kaiwa nan ya sake relaxing abinsa,saidai kunnuwansa suna tare dasu,duk da qasa qasa yake kallon screen din da salon kallon da zaka dauka bacci yakeyi. Maganan ta saukarwa kowa a bazata.

"Haisam dinnan da baya iya kallon mace sai biyu?......guys a duba maganan nan fa?" Amjad ya furta sounding so amazing.

"I'm serious" Ya fada da wata murya kaman mejin bacci,yanayin dake nuna musu ya gundura da yadda suketa avoiding labarin.

"Wacce jarumar?.....wacce kuma me tsananin sa'ar ce?" Mutallab ya tambaya cikin son jin wadda tayi nasarar.

"Akhnan" Omar ya amsa wannan karon kai tsaye yana tallabe da kumatunsa,irin mamaki ya masa kisan mummuqe.

Yadda suka kama sunan kusan lokaci daya ya sanya haisam sake girman idanunsa yana jifan omar da kallo. Da alama akwai wani labari nata da suke dashi?. Tambayar data girmi tambaya a wajen haisam saidai qarin tabbaci,don kowa maganan naseeb ta tabbatar masa da haka.

"Akhnan?......the princess of agadez?.....stubborn and silly girl?" Naseeb ya jero gaba daya. Maganan ya sakashi qarasa bude idanunsa gaba daya ya azashi kan omar. Omar din da yaqi yadda ya kalleshi.

Komai kenan da yake fadi akan yarinyar akan kunnen omar ne?,komai omar yana hankalce dashi kenan?,komai omar ya labartawa su khadeem.

"Amma Captain......waye ya tilastaka.......gaya mana sai inda qarfinmu ya qare" Mutallab ya fadi yana matsowa dab da screen din gami da lowering muryarsa irin sirrin nan za'a gaya masa. Yadda mutallab din yayi ya sakasu dukkaninsu kwashewa da dariya,banda haisam daya murmusa kawai yana bin fuskokinsu da kallo daya bayan daya.

Readers Also Read

More by Huguma