L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 49
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 49: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 49. Sarkin Cameron Gabon da ghana dukkaninsu suna hade a…
3,373 words
Sarkin Cameron Gabon da ghana dukkaninsu suna hade a gurin,wanda kusan ibadar umara ce ta kaisu abun kuma yazo a daidai. A gefe ga sarakunan Ethiopia din da motii ya aiko wakilci,abun ya zama na SARAKAI kawai.....sarauta kawai ke magana.
A babban hotel na five-star hotel dake dab da haramin madeena sukayi masauki dukkaninsu. Royal suit dake dauke da dakunan alfarma. Cikin babban parlor din da yake dashi,ana raha da hira irin ta manya.....hira irin ta sarakai hira irin ta tsaffin abokai,an saje gaba daya harma da wanda ba'asan juna ba.
Shiga ce ta alfarma jikin kowannensu,sutura dake nuna zallar sarauta da kashe ido,sassanyan qamshin turarukan da zai nuna maka manyan mutanene kawai a gurin,masu ji da ilimi dattako mulki dama sarauta din gaba daya.
A nutse sultane yabar gurin yana fita zuwa private balcony din da suit din yake dashi,ya ciro wayarsa yana laluben nannie.
*AGADEZ*
Tun a daren jiya da sultane ya gaya mata abinda ya yanke da yadda komai ya gudana tsakaninsa da haisam ta kasa bacci. Ta rasa da wanda zatayi maganan,don ya umarceta dayin shuru har zuwa sanda komai zai tabbata. Yace don wannan din HUKUNCINSA Ne baya buqatar wani gyara ra'ayi tsaiko ko dakatarwa.....koda kuwa daga bakin AKHNAN dinne.
Tayi imanin koda morsa safiyya itama bata sani ba.....ta tabbatar inda ta sani tabbas zata ganta tazo gareta.....zata ganta tazo gareta don kawai ta fadi mata.
Murmushi nannie ta saki,haka kawai takejin wani farinciki da nishadi da batasan na meye ba,haka kawai takejin wani abu me dadi yana ratsa zuciyarta tun safiyar ranar. Abu daya tayi shine ta kira aisa kan tanason ganinta a yau juma'a,tace tabar kome takeyi ta iso agadez kafin sha biyu na rana,ta siya ticket ta biyo jirgi. Ta san tabbas sai an samu tashin qura,so dole Akhnan din tana buqatar su aisa din a gefanta. Aisa din taso bata uzurin matsalan da company yake ciki da kuma ganin cewa kwana nawa duka duka da komawarta amma nannie bata tsaya sauraren wannan ba.
Idan ta tuna da waye sheikh muhammad haisam din,sai taji tabbas ne ya dace.....ya cancanta........an ajiiye qwarya a gurbinta.
Tana kammala sallar walaha qarfe goma da rabi na safe kiran sultane din dan uwanta shaqiqi ya shigo mata.
Da cikakkiyar sallama,muryarsa da tata dukka wani irin wasai suka amsa da junansu.
"Imam da wazeer dukka sun qaraso ko?" Kai sultane ya gyada.
"Dukkaninsu muna tare,nan da mintuna talatin zamu wuce masallaci in sha Allah......"
"Allah ya tabbatar da alkhairi,yasa wannan din ya zama sanadin zuwan qarshe duk wani damuwa tata da gyaruwar komai".
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ya amsa mata sannan ya dora.
"Na gode......fatima.....inaso Akhnan ta shaida d'aurin aurenta da idanunta,bawai don ban ban isa bane....aah.....inaso ta samu yaqini da tabbaci har cikin jinin jikinta......inaso ya zama rubutacce cikin idanunta da zuciyarta cewa ita din mallakin sheikh Muhammad haisam ce ta har abada......ki shaidawa morsa safiyya,ki shaidawa zaituna,ku isa sashenta,zan kiraki ko kuma ita na kirata,ina buqatar ki ajiye mata video call din a gabanta don ta shaida komai" Kai nannie ta gyada a hankali. Har ranta taji hakan yayi,hakan kuma zai sauqaqa musu komai.....zai sauqaqa musu wani bayani na gamsar da ita faruwar komai.
Basu jima ba suka yanke kiran,ta miqe a nutse ta sanya aka nemo mata aisa da shehnaz......sannan tayi tattaki zuwa sashen morsa safiyya da kanta,bayan an tabbatar mata mammina din bata gidan,ta fita tunda safe duba marasa lafiya gami da basu tallafi,kaman yadda ta saba tana yi lokaci lokaci.
Ta samu morsa safiyya din da baqi,saidai tana kan sallamarsu sanda ta shigo,don haka ta samu guri ta zauna tana monitoring yadda morsa safiyya din zataji da labarin. Yanayinta yana burgeta,komai zatayi na kyauta sadaka ko kyautatawa tanayin abinta ne a qunshe cikin sashenta,ba tare da kowa ya sani ba sai wanda akayi abun dominsa wato Allah da kuma shi wanda aka taimakawa din. Wani irin yabo take samu a zukatan al'ummar agadez,wanda ba kowa yasan dashi ba,wani irin matsayi na yadda take lullube asirin ne neman taimako,ta taimaka da dukkanin iyawarta ba tare data fallasa asiri ko ta bayyanawa duniya kalar buqatar ka ba.
"Saqon alkhairi nake tafe dashi" Nannie ta fadi tana murmushi idanunta akan morsa safiyya.
Murmushi ta saki itama.....bataji wani tashin hankali ko d'arrr ba,don mafarkin da tayi daren jiya har yau yanzunnan shine a ranta. Dalilin daya sanyata fidda sadaka me yawa kenan a safiyar juma'ar yau ta bayar,duk da dama ta saba,halinta ne kuma dabi'arta ce.
A daren jiyan taga safeena cikin wani kyakkyawan yanayi,cikin farinciki tarin walwala da annashuwa,cikin taron wasu mutane dake da kyakkyawan shiga.
Sunyi hira me yawa amma bata iya tuna komai da sukace,abu daya ta iya riqewa a kanta.
"Na gode safiyyah.....ina cikin farinciki sosai yau,kinga kowa ma yana tayani murna?.....ki gaidamin khadeeja,ina kewarta,duk dadai tana kawomin ziyara ma". Maganan ya tsaya mata sosai a rai,saidai hankalinta be tashi ba,saboda koma meye tasan alkhairi ne. Mafarki mamaci yana cikin farinciki da taron jama'ar da suke cikin kyakkyawan kamala da siffa alkhairi ne ta sani.....saidai maganan khadeeja daya tsaya mata arai,don ko bayan ta farka a wannan mafarkin mafarkin khadeeja din tayi,saidai ita din daga nesa suka hango juna,sunata yiwa juna murmushi a wani guri da suka saba haduwa a shekarun quruciyarsu suyita wasa,har sai falmata ko bilkeesu maman khadeeja din ta sanya bayi sun daukosu. Idanunta akan khadeeja sai kuma taga ya juya ta shige wani guri,ta bita da sauri amma bata ganta ba,tana tsaye taji ana jan hannunta zuwa hanyar,batasan waye yake jan nata ba kiran sallar asuba ya farkar da ita.
"Allah yasa muji alkhairi" Safiyya ta fada tana zama gefan nannie.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Alkhairi ne safiyya.....don kuwa a wannan juma'ar sultane ya yanke shawarar daura auren diyarmu Akhnan da sheikh haisam a masallacin madeena" Idanu morsa safiyya ta kulle gam gam,wai tanaso ta tabbatar da cewa mafarki take ko idanu biyu ne?.
Dama sultane yayi accepting maganar yayi mata shuru kamar bai gamsu ba?,dama sultane ya gamsu da abinda ta fada amma yayi bakam kamar bai gamsu ba?.
Bata kai ga bude idanunta ba ruwan hawaye suka silmiyo mata.
"Kuka safiyya?.....baki ganin gurin akwai hadimai?" Nannie tayi saurin fada tana riqe hannunta. Idanun ta bude murmushi yana mamaye fuskarta.
"Duk wanda ya yarda da Allah bazai taba tozarta ba......duk wanda ya damqa amanarsa a hannun Allah ubangiji bazai taba cin wannan amanar ba.....ubangiji ba maciyin amanar bayinsa bane.......sai yanxu na sake tuna maganan da mukayi jiya safeena a mafarki.....wadannan kalaman tayita maimaitamin.....kana mace ko kana raye muddin zaka bawa Allah amanar rayuwarka dama amanar abinda ka mallaka....lallai ne Allah xai cika wannan amanar musamman ga zukatan da suka miqa wuya ga Allah.....ba kokwanto.....ba shakka......ba munana zato.....nannie,ko a yau na mutu burina ya cika.....nasan gudar halittar data ragewa safeena da qarfin ikon Allah ta kubuta.....ta kuma tsira" Morsa safiyya ta fadi hawayenta suna qaruwa tana kuma riqr da hannun nannie sosai.
Dubanta sosai nannie takeyi,ta gane zancanta,amma bata fahimci maganarta ta qarshe me take nufi ba,amma farincikin dake ranta,dama abinda yake gabanta ya shafe komai,ya shafe tsayawa sauraro ko neman fashin baqi.
"Zaki iya shiryawa muje gareta?,don sultane yana son ta shaida komai a idanunta" Murmushin nan yana kwance saman fuskarta ta zame hannunta daga cikin na nannie.
"Banaso naci gaba da bata alaqata da d'iyata.....bayyanata a yanzun a gurin bazai bata daman kwantar da hankalinta ta fahimci abinda akeso ta kalla ba.....zan shigo daga baya....sanda komai ya gama bayyana a idanunta....inanan tafe koda zata gutsiremin kai. Kome akhnan zataji a kaina tuwo sunansa bazai taba canzawa ba....". Kai Nannie ta gyada tana miqewa a hankali,ita kanta tana jin wani iri,tana jin ba dadi na yadda har yanzu alaqa taqiyin kyau.....taqi daidaituwa tsakanin morsa safiyya da akhnan din,duk kuwa da cewa a gabanta ta girma.....a gabanta ta zama mutum,bawai baqin juna bane ga rayuwar kowannensu.
*AKHNAN*
Cikin lafiyayyen daya daga cikin bedroom dinta cikin bedrooms din da take dasu daban daban har guda uku take kwance. Bedroom ne dake dauke da wani irin weather me sanyi da dadi.....bedroom din da tattausan qamshin turarukan icce dana ruwa da tsirrai na kamfanin INCENSE BY KABO DAUGHTER 0803 211 9803 ya kama dukkan wani curtain duvet bedsheets dama towels harda lallausan Chinese Carpet dake malale tsakiyar dakin. Hatta da pillows dinta qamshin ya kamashi sosai,batasan da hakan bama sai a kwanakin nan data koma kwana a dakin,don tabar kwana sauran bedrooms din,saboda dukkaninsu ba wanda bai bata bad memories ba.
Tsakiyar lafiyayyen royal bed din take kwance rub da ciki,ta toshe kunnuwanta dukka biyun da earpiece tana sauraren waqar nan tata ta love story.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 85*
Ta love story. Sanye take da qananun kaya.....Palazzo ne a jikinta da kuma crop top wadda hakan ya bawa plate tummy dinta bayyana sosai kaman zai hade da bayanta,kamar bata zubawa cikin nata wani abu me suna abinci a cikinsa. Gashinnan nata na asalin BUZAYE me tsahon da ya sauka har kusa da mazaunanta ya baje saman pillow din data dora kanta akai,wani kuma ya sauko a sashe da sashen fuskarta,har yana neman tsone mata idanu,lokaci lokaci tana sanya hannunta tana maqale shi a bayan kunnenta.
Kyawawan idanunta suna rufe,tana sauraren waqar da tunanin zata samu sassauci zata rage kewa kamar yadda ta saba,amma kuma a yau sai takejin gaba daya waqar tana mata wani irin sautin amo mara dadi,kamar ma tana sake dagula mata sauran lissafinta da d'an guntun nutsuwar da kwanciyar hankalin data samu.
Siririn tsaki taja,ta zura hannunta tana zare earpiece din daga kunnenta,kaman hakan kuwa ake jira taji an fara knocking na qofar tata.
Manyan fararen idanunta masu sirkin blue ta bude cikin dakin dake da matuqar qarancin duhu ta zubawa qofar dakin idanu. Wasu sakanni suka biyo baya anaci gaba da knocking din can qasa kamar ana tsoron buga qofar ne. Ranta ya sake baci.....me yasa idan ta sanya dokar kada a nemeta kuma kada a dameta su birra ke gaza kiyayewa a kwanakin nan?. Bata buqatar kowa.....bata buqatar magana da kowa,jiran dawowar sultane kawai takeyi. Sultane kawai take dako,ya dawo su fahimci juna ta tattara ya nata ya nata ta wuce Niamey ita kuma da agadez ba rana ballantana wata,wataqila sai kuma zagayowar wani festival de l'Aïr din.
Batace ma mai bugun ko cikanka ba,har sai data miqe a nutse tana gyara zaman shirt din jikinta data bayyana dukiyar fulaninta da suka cika qirjinta sosai kamar sun raina fadin rigar,wanda banda ta gurin qirjin kota ina rigar tayi mata daidai,ta sanya hannunta ta tattara sassalkan gashinta guri daya ta daure da siririn band din data cire ta ajiye gefa a dazun don taji dadin kwanciyar,ta zira qafafunta qasa cikin tattausan royal bedroom flip flops dinta.
A yangance da wannan yanayin nata mai cike da qasaita me yawan gaske ta furta.
"Waye ne?" Cikin harshen faransanci da ya zauna sosai saman harshenta da wani irin qwarewa da gwaninta.
"Birra ce ranki ya dade" Ta amsa mata cike da ladabi da kuma yaren faransancin. Dokarta ne tama magana da wani yare ka maida mata amsa da wani yaren daban,koda yarensu na buzaye kuwa. Bata qaunar jahilci don haka duk cikin hadimanta na kusa ba wanda baiyi karatu ba,ba wanda bayajin faransancin tas a bakinsa. Don ko sanda zata tafi France karatu da dukkaninsu su biyar din ta tafi,kuma ta sanya kowacce a makaranta daidai da matsayinta,ta rarraba musu lokuta yadda bazaici karo da lokacin hidimarsu a gareta ba. Shuru tayi kaman ba zata amsa ba....wanda banda da birran take magana inda wani ne da yake baqo ga sanin halayyarta zai tafi ne ya dauka ba zata amsa din ba.....sannna ta sake magana tana saka qaramar hula me sauqi saman gashinta.
"Yaushe kika fara karya doka da umarnina ne birra?". Ta fadi da wannan muryatata dake cike da yauqi da gayu. Duk da bata iya ganinta amma hakan bai hanata rusunar da kanta ba
"Kiyi haquri ranki ya dade.....an kammala hada ruwan wankanki ne". Mamaki kadan ya kama akhnan.
"Sau nawa zan maimaita miki idan ina buqata zan sanar miki?"
"Eh na sani.....bawai ina jayayya dake bane.....nannie ce tace ki tashi ki shirya" Maganan ya sanyata dakatawa daga qoqarin bude scrub dinta da takeyi tana kallon qofar kai tsaye
"Nannie kuma?.....zaki barmin qofar daki birra ko saina hukuntaki?" Maganan ya sanya birra janyewa babu shiri ba kuma tare data sake cewa komai din ba.
Wani siririn tsakin ta saki,wankan zatayi din......amma izzarta ba zata barta ta tsaya yiwa birra bayanin saita gama goge gogen fuskarta da cleansers dinta da take amfani dasu ba kafin ta shiga din,wanda aqalla suna daukarta kusan minti talatin kafin ta gama hidimarsu ta shiga wankan gaba daya.
Stool ta jawo ta zauna gaban mirror din,sannan ta miqa hannunta ta kunna makunnin qwan dake zagaye da mirror din nata wanda ke bata haske sosai a duk sanda za'a gyara mata fuska ko zatayi wani abu irin haka. A cikin jininta yake,son ado da gyara,tana kula da lafiyar jikinta da kuma fatarta sosai fiye da kima,wannan ya sanya ba wani halitta da zai kalleta bai sake marmarin kallonta ba,mace ko namiji babba ko yaro. Ta mallaki dukkan wata sura ta kyau,wata irin lafiyayyar fata diri da zubi da kowacce mace zata buraci inama ace nata ne?,sai ya hadu da mulki sarauta izza da kuma dukiya.....uwa uba gata da kwanciyar hankali,wannan ya bawa dukkanin siffofin damar fitowa dayin tasiri yadda ya kamata a tattare da ita.
Knocking ta qaraji anyi,zuwa yanzu ta fusata da wannna fusatacciyar zuciyartata. Ta waiwaya a hankali ta lumshe idanunsu ta kuma budesu lokaci daya tana bude bakinta da zummar yin magana,saidai kuma batakai ga cewa komai din ba hairaan ta murza qofar ta tura ta shigo. Dama a bude take qofar,saidai kuma ba wanda ya isa ya shigo din idan bada izininta ba.
Idanunta suka gauraya daya hairaan,saita janye dubanta a kanta a hankali tana maidawa kan dressing table din. Batasan me yasa ba.....hairaan din tana mata wani nauyi.....tana dan jin shakka kadan kadan a kanta,batasan ko abubuwan da suka dinga gudana tsakaninta da ita zamanin quruciya bane yayi tasiri?.
A nutse hairaan tayi sallama a yau din,ba wani qorafi fada ko mita ta dubi akhnan din.
"Ki ajiye wannan aikin,ki shiga kiyi wanka....so samu ki shirya yau da kanki,yau dai sau daya tak.....amma idan hakan ya gagara birra zata shigo ta shiryaki yadda kika saba" Hairaan ta qarashe maganar tana ajiye wasu kayayyaki da akhnan din batasan meye ba saman bedside drawer.
Bin hairaan din tayi da kallo sanda taga ta juya salin alin tana fita a dakin ba tare data sake ce mata komai ba. Ta danyi mamaki,don ta saba duk sanda zasuyi face to face haka bata gaidata ba sai tayi magana.....hakanan sai tayita qorafi da mita kamar zata balbaleta da fada. Zuwanta ne kawai qasar wannan karon ya sassauta wasu abubuwan.
Haka kawai taji jikinta yayi wani iri sanyi. Duk abinda zai hana hairaan qorafi haka to lallai babba ne. Samun kanta tayi da saka hannu ta ciro dump face wiper ta goge scrub din data fara shafawa,ta miqe daidai sanda birra ke shigowa.
Ido ta zubawa birra din,kanta a qasa taqi duban uwar dakin nata tazo ta giftata zuwa toilet don hada mata sabon ruwan wanka a nan.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Har ta fito tana tsaye,ta sake binta da kallo.
"Saboda nace a qyaleni bazanyi wanka yanzu ba shine kikaje kika fadiwa titi hairaan?" Tayi tambayar da wani irin quruciya da sakalci cikin muryata,wanda ba kasafai wannan sifar ke nunawa a tattare da ita ba.....duk da lokaci lokaci takanyi abubuwa da yawa da birran ke hangen quruciya sakalci da ta taso a ciki,wanda idan itace ba zata yisu ba. Fushi taqiyin wani abun,ko fushi tayi wani abun duka wani lokaci birran ke boye tayi dariya.
Duk inda izza da sarauta suke a jikinka,indai akwai wannan gatan ya maka yawa.....indai akwai wannan quruciyar lallai wataran saita bayyana kanta da kanta.
"Kiyi haquri" Kawai birra tace da ita,saita gyada kai kawai taja qwafa tana nufar bandakin.
Har takai qofa ta dakata,ta waiwayo tana qarewa birra kallo.
"Waime meye na sanyani a gaba yau nayi wanka?,bayan ina da dukkan zabi nayin yadda nakeso a sanda nakeso naga dama?,ko wani sabon munafuncin ne?,naga fuskarki kamar kina murmushi?" Akhnan din ta fada still yanzu ma da sakalcin nan sosai a tattare da ita.
Allah ne ya taimaki birra,kadan ya rage murmushi bai fita a fuskarta ba. Tunda samia baiwar morsa dake hidima a sassanta ta tsaigunta mata maganar da taji anayi ta samu kanta cikin matsanancin farincikin daya gaza boyuwa. Ta sake samun tabbaci sanda nannie ta shigo sassan,ta kuma wuce can kebantaccen parlor din akhnan din dake qasa,wanda ita daya ke shiga ciki saiko su shehnaz,ta kuma kirata ta gaya mata dukkan abinda take buqatar ayi.
Ganin birran bata amsa mata ba,tsaiwar kuma kamar tana bata mata lokaci ne sai kawai taja tsaki yana wucewa cikin toilet din qasa qasa tana gunaguni.
Tsalle birra ta buga ta sake juyawa. Sukam tako ina sheikh muhammad haisami yayi musu,ba ita daya ba,dukkan hadiman sashen da tasu tazo daya da suka fara tseguntawa juna kowa tsalle yake bugawa. Kai tsaye ta juya zuwa sassan walk-in closet din akhnan din,ta shiga lalubar mata kayan da zasu dace da yanayin,wadanda ba zasu nuna wani gagarumin abu ba,ba zasu kuma takurata ba a dukka yanayin rudanin da zata shiga,don ta tabbatar rudani kam akwaishi.....daaru na akwaishi,kallo kam su hadiman da suke kusa zasu shashi,fatan da takeyi kome zai biyo baya yazo da sauqi,ya kuma zamanto me sauqin gaske ga uwar dakin nata. Don har ga Allah suna sonta,suna qaunarta qwarai da gaske,tana da tarin akkhairanta garesu,tana da matuqar kirkin da idan kana nesa da ita ba lallai ka fahimci hakan ba,sai zama ya kawoka kusa da ita,kuma ka zauna da ita lokaci me tsaho. Wasu dabi'un nata basa damunta,tunda ita din an haifeta cikin gidan sarauta ne,tasan duk wasu dabi'u da halaye da JININ sarauta ke sanya diyoyinsa aikatawa,wanda haka yake kawai a dabi'arsu,ba rashin kyautawa bane,gado ne kawai a cikin jini ya zame musu normal life.
Kaman kowanne lokaci wankanta yakan dauki lokaci kafin ta kammala. Tazo ta zauna birra na tayata shiryawa,harta kammala.
Kayan data bata ta sanya ya sakata daga kai ta kalli birra din,kamar zatayi magana amma sai kuma ta fasa ganin birra din ta saukar dakai qasa.
Tsaf ta fita cikin wani cotton material me asalin tsada da daukan hankali. Butter milk me adon red roses manya a jiki. Daga qirjinsa yasha wata tattarar roba,wadda take bawa rigar daman budewa daidai da fadin qirjin wanda ya saka rigar. Cup hand ne da rigar wanda duka duka iya damtsenta ya tsaya,ya bada wani style me kaman cup. Earrings ta miqa mata red color ta saka a kunnenta a hankali,idanunta still yana kan birra dai,birran daketa nuqu nuqu tana qoqarin boye duk wani baqon mode nata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 86*
Sake kallonta tayi sanda ta miqa mata awarwaraye da suka dace da kayan jikinta. Ta zubawa birra din idanu,haka kawai takejin yau bata yarda da birra ba,haka kawai takejin wani baqon yanayi a tattare da ita.
"Maidasu basai na saka ba"