L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 52
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 52: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 52. "Biftu?.....ina biftu?" Ta fada tana laluben akhnan din…
3,292 words
"Biftu?.....ina biftu?" Ta fada tana laluben akhnan din dake kwance saman cinyar morsa safiyya duk kuwa da cewa ta ganta. Ba wanda ya iyace mata komai,saboda zukatan da yawa daga cikinsu tausayin mamminan sukeji. Suna duba da soyayya da kuma shaquwa ta ZAHIRI dake tsakanin mammina din da akhnan..... Suna duba da idanun zahirin da zai gaya maka mammina din ita zatafi kowa shiga rudani akan duk wani abu daya shafi akhnan din. Mammina din ita zatafi kowa damuwa akan komai da zai shafi akhnan din.
Idanu kawai morsa safiyya ta zuba mata sanda tayi gurfane gaban akhnan din. Saidai duk siyasarta da yadda taso maida akhnan cikin jikinta morsa safiyya ta hanata wannan damar.......taqi matsar da koda yatsanta daga jikinta,koma baya yadda ta saba a baya. Tana ja da baya ne a duk sanda mammina tazo kan al'amarin akhnan,tana matsawa ne ta bata dama da fili a duk sanda take ganin ita tafi cancanta da ita. Amma a yanzu.....a kuma yau din,tana jin komai yana canzawa game da ita,tana jin jinin nan na UWA yana dawowa jikinta game da akhnan......tana jin ba wata sauran dama da zata sake bawa mammina game da akhnan daidai da d'anin yatsa guda daya tak!.....don haka a daidai sanda take kiran yalwa da sauran hadimanta da sukayi mata rakiya kan su dauko wheelchair su dauke mata akhnan su wuce mata da ita sassanta......a daidai sannan ta kalli falaak da armelle.
"Maza ku gaggauta kiran MIJINTA.....ku gaya masa ni morsa safiyya ina kiransa da gagggawa,yazo matarsa bata cikin hayyacinta" Yadda morsa safiyya din ta basu umarnin da wata irin murya mai cike da zarra da kuzari kawai ya qarawa armelle da falaak qaimi. Su dukka sunsan me yake faruwa,bawai a boye komai yake a gurinsu ba,don haka da sassarfa suka soma takawa suna ficewa.
Wani irin duka kalmar MIJI da morsa safiyya ta fada ta yiwa mammina. Sai a sannan tunaninta ya sake dawowa jikinta. Da gaske a yanzun akhnan din ta zama MATAR BABBAN ABOKIN BURMINTA.....to amma hakan yana nufin zata saki kambunta?,hakan yana nufin zata sakar masa zaren?. Samun kanta tayi da bawa kanta amsa da
"A'ah" Wannan amsar ita ta yaudareta da bata qwarin cewa.
"Amma safiyya,ta yaya zamu zauna jiran wanda ba'asan yana kusa ko a nesa ba?,ki duba ki gani Yarinyar nan bata numfashi.....marabarta da gawa bugun zuciya!" Mammina ta fada a tsawace tana fidda idanunta cikin son nuna rudanin data shiga.
"MIJINTA.....shine mafi cancantar haqqi a kanta.....MIJINTA shine Allah ya dorawa alhakin kula da lafiyarta,MIJINTA shine majibancin lamarinta a yanzu BA MU BA" Kowacce kalmar MIJI guda daya da morsa safiyya ke fadi cikin kunnenta......tana maimaita kanta da kanta ne a zuciyar mammina din sau DARI. Tana jin bugawar sunan a kowanne jini da zai harba zuwa sassan jikinta.
"Ashe?.....ina soyayyar da kike iqirarin kina mata?,ashe ba zaki iya cetonta ba a sanda tafi buqatar ceto safiyya?.....sai mun jira zuwan wani?". Kai tsaye morsa safiyya take kallonta ido cikin ido,tanajin zuciyarta tana soyewa.
"Idan har shekaru ashirin baya basu kashe akhnan ba......a yanzun 'yan qananu kuma gajerun mintuna irin wadannan ba zasu taba daukan rayuwarta ba.......ta mutu a hannuwan MIJINTA yafi mata daraja akan ta mutu a hannun daya daga cikinmu,bamu da wuta ko aljannar da zamu bata.....amma kuma MIJINTA fa?" Ta tsaida ayar tambayar tana duban tsakiyar idanun mammina kai tsaye,abinda ta jima batayi ba......abinda ta dauki shekaru bata yi ba.
A duk sanda ta kalli idanun mammina din SAFEENA take hanga a ciki........a duk sanda ta kalli idanun mammina MUTUWAR SAFEENA take gani.....WAHALA da GALABAITAR safeena a kafatanin rayuwarta take kalla......QADDARAR safeena take gani rubuce cikin fuskar mammina din.....wannan ya sanya kallon fuskartata ya zama wani abu na qarshe a rayuwarta da takan jima bata yishi ba
*HAISAM*
Ya dauki wasu mintuna cikin masallacin yana gaisawa da mutanen maimartaba,karbar koke da sauran abubuwan daya zamana sultane dinne yakeyi duk bayan sallar juma'a,kafin daga bisani ya samu ya baro masallacin.
Shi da khadeem da maleek suke takowa,don abdii omar da Amjad sunyi gaba.
A hankali suke tattaunawa akan lamarin kasuwancin da kowannensu yake gudanarwa. Hirar kusan duka kan duniyar kasuwanci ce,saidai kuma tattaunawa ce dake muna zallar nutsuwa da ilimi a maganganunsu. Kusan baya cikakken taku biyar ba tare da gilmawar hadimai ba,kuma su tsaya su gaidashi cikin girmamawa sannan su wuce.
Da yawansu murna ce fal cikin ransu game da labarin daurin aurensa da gimbiyarsu da liman ya sanar bayan gama khudba. Da yawansu kuma suna son masa Allah ya sanya alkhairi ne,saidai yana musu wani irin mugun kwarjini da yake sanyawa daga gaisuwa saidai kawai su wuce ba tare da sun iya ce masa komai ba.
Shi ya fara hango abdii yana tahowa,yana magana da amjad amma sai ya tattara hankalinsa akan abdii din har zuwa sanda ya qaraso. Da ido ya tambayeshi,don kusan dabi'arsa ce magana da ido,duk kuma wanda ya saba rayuwa dashi ya saba karbar kalar tambayoyinsa da tuhumarsa da qwayar idanunsa.
"Aike akayi yanzu......ana buqatarka a sassan amarya......gimbiya....." Abdii ya rarraba zancan yana kallon idanun haisam din don duba sunan dashi haisam din zai iya karba.
"Akhnan?" Haisam din ya furta kai tsaye yana duban abdii. Kai ya jinjina masa.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 90*
"Gwaggonta morsa safiyya ta aiko.......tace kirane na gaggawa" Idanunsa ya janye daga kan abdii din a hankali cikin nutsuwa. A musulunce kuma a al'adance kiran morsa safiyya yana daidai da kiran nanay dinsa. Koda ita batasan hakan ba shi ya sani......she earn some respect kasancewarta UWA a gurinsa.
"Okay" Ya fada da wani coolness yanna motsa labbansa sannan ya fara takawa a nutse yana barinsu amjad a gurin.
"Idan da buqatar wani taimakon let us know" Amjad ya furta da nuna supporting zuwa ga abokinsa. Kai kawai ya gyadawa amjad din ba tare daya waiwayo ba,yayin da abdii yaji zuciyarsa ta tafi,bazai iya barin haisam din yaje shi kadai ba,sai kawai ya fara binsa a baya a nutse.
Suna dab da sassan haisam ya ankara da abdii. Cak abdii din ya tsaya yana duban haisam daya waiwayo yana dubansa.
"Don Allah obbo" Ya fadi cikin karyar da murya. Idanun nasa ya dauke ya juya yana ci gaba da takawa,abinda ya gayawa abdii kenan ya barshi ya biyoshi,don haka ya qara hanzari kadan yana taddoshi.
Kai tsaye yake takawa cikin sassan akhnan din,karo na farko tunda yake a gidan,don ba wani abu da yake ganin zai hadashi da gurin. Iyakacinsa daga bedroom balcony dinsa,sai kuma dogon veranda din da ta hada sassan nasu,wanda yawancin lokuta ma bata nan yake biba. Cikin girmamawa bayin dake hidima ta kowanne sashe na sassan nata suke zubewa suna gaidashi,kawunansu a qasa cikin salon da suke gaida uwargijiyar tasu. Koda a baya yana da girman matsayi cikin gidan,amma a yanxu matsayinsa da girmansa sun ninku a zuciyarsu saboda zamowarsa mijin gimbiya akhnan.
Tun hankalinsa baikai kai ba har yakai din,ya lura kamar sashin nata yafi kowanne sashi na gidan yawan bayi da hadimai,duk da cewa kusan mafi yawansu mata ne amma adadinsu ya ninka na kowanne sashe.
Kai tsaye birra dake daga bakin qofa ta juya itama tana sadda kanta qasa.
"Zan iya maka jagora zuwa muhallin da suke" Ta furta a hankali tana jin yadda kwarjininsa a yau yake dukanta sosai.
"Dama haka yake?" Ta tambayi kanta,don yau din shine karo na farko data fara tsaiwa a muhallin da yake tsaye. Bai amsa mata ba,tadai juya da zummar yin gaba,saidai kuma a qasaice ya umarceta da cewa ta koma bayansa. Da dan mamaki ta dakata tana komawa bayansa,shi kuma ya shige gaba.
Abdii ya sani,yasan tsarinsa shi yasa baiyi mamakin hakan ba. Baya taba yarda macen da take ba muharramarsa ba tayi tafiya a gabansa,saboda koyi da sunnar annabi musa. Ya taba tambayarsa bai kuma zargi tambayar abdii din ba ya zaunar dashi yana karanta mass k'issar.
Lokacin da ya shayar da dabbobin daya daga cikin annabawan Allah,kuma d'iyoyin annabin da suka kasance mata suka dawo domin kiran annabi musa,ta shaida masa mahaifinsu yana son ganinsa don ya saka masa ko ya biyashi shayar da dabbobinsu da yayi kaman yadda qur'ani ya bada labari cikin suratul qasas......a yadda k'issar tazo cikin sauran litattafai ta nuna tayi gaba ne don ta masa jagora xuwa gidansu,sai iska ta daga zaninta kadan,sashen dugaduginta ya bayyana,sai annabi musa ya runtse ganinsa,ya kuma umarceta ta koma bayansa. Sosai abdii ke jinjina kai,lallai akwai hikima kenan cikin abinda haisam din yakeyi duk sanda tafiya irin haka ta hadashi da mace,zama da me ilimi akwai dadi,dole abubuwa da yawa naka zasu gyaru,al'amuran duniya dana lahira ma gaba daya.
Tun daga wannan lokaci shima abdii sai ya zame masa dabi'a.
(YAKE UWA!!!.....akwai abubuwa masu kyau da yawan gaske daya kamata ki koyawa diyarki.....kunga diyoyinkunnan mata SUNFI ZINARE SUNFI LU'U LU'U DARAJA DA TSADA.....kyan diyarki ba'a fuskarta yake ba,kyan diyarki yana ga kyawawan dabi'u halaye da tarbiyyar da zaki bata....KADA KI YARDA DIYARKI TA ZAMA BARAGURBI ki sanyata ta zama kyakkyawan fure me qamshi ga al'umma,abar rububi ga dukkan namiji wajen son mallakarta. Ki koya mata kaucewa maza a hanya yayin tafiya.....koda tana tafiya wani yana binta a baya,ki koya mata tsaiwa ta rabe ya wuce gaba ita ta bishi a baya....YIN HAKAN KARE MARTABARTA NE.....YIN HAKAN KARE KIMARTA NE.....YIN HAKAN KOYA MATA MUHIMMANCIN KUNYA NE.....Allah ka bamu ikon fidda yabanya masu kyau).
Mamaki kadan yake kama birra ganin yana bin duka hanyoyin da zasu sadashi da gurin kanshi tsaye kamar dama yasan ya gurin yake,bai kuma tambaya ba saida suka zo mararrabar da zaka hau stairs din akhnan din da kuma inda zaka zarce hanyar parlor din.
"Hannun dama" Ta bashi amsa cikin kamewa.
A nutse ya waiwaya ya bawa abdii umarnin dakatawa daga nan,sannan yaci gaba da shiga kai tsaye da wannan kuzarin nasa.
Kallon kallon sukaci gaba dayi da morsa safiyya bayan takai qarshen maganganunta. Sosai take hangen wani abu me tsananin zafi da tsini daga idanun morsa din,irin wanda bata taba ganinsa ba sai yau din.
"Sanyi zeenatu.....sanyi......zafi ba komai yake bayarwa ba" Wani sashe na zuciyarta ya d'arsa mata kaman yadda wasu lokutan yake gaya mata.
Janye idanunta tayi kadan tana hadiyar wani abu a zuciyarta,tana jin wani irin nau'in qasqanci da morsa safiyya ta gwada mata gaban tarin bayi?.
"Lokaci yayi da ko yaya ya kamata itama na tabata.....ya kamata taji a jikinta" Ta furta can qasan muguwar zuciyarta tana hadiye bacin ranta. Daidai sanda takai qarshen maganar,daidai lokacin haisam ya bayyana bakin qofar parlor din da sallamar dake nuna nutsuwa me yawa a tare dashi. Wani irin muguwar faduwa gabanta yayi,yana tsaye kyam saman qafafunsa da cikakkiyar tsaiwar da a yau karon farko ta fara ganin murjewa jiki da tsahon da yake dashi. Giant ne sosai wanda qirarsa ta sake d'arsa mata zargi na biyu a ranta. Ko ba'abzine ko dan qasar habasha wanda suke kadai keda wannan siffar a qabilun data sani. Kwarjininsa da haibarsa gaba daya taji sun cike dakin,qamshinsa kuma ya fara gayawa kowa isowarsa.
"Wa'alaikumussalam" Morsa safiyya data daga kanta daga kallon akhnan da har yanxu bata motsi ta fadi tana sauke idanunta akan haisam din.
Wani irin abu taji ya tsarga mata me dadi,tsoronta taji ya zabge daga kaso dari zuwa kaso.ashirin cikin darin. Bayyanarsa kawai a wajen sai takejin kamar bayyanar haske a yayin da duhu ya yiwa wani kogo mamayar gaske.
A kanta idanunsa ya sauka,sanda take rungume jikin morsa safiyya din. Tashin sheshsheqar kuma yakeji cikin kunnensa,sautin da baisan daga inda yake fitowa ba don ba ma'abocin aza dubansa akan komai da komai bane,saidai koda bai qarewa dakin kallo ba ya tabbatar akwai mutane da dan yawa a cikinsa.
Hannunsa dake cikin aljihun kurta dinsa ya zare,yaci gaba da takowa tsakiyar parlor din.
"Me yake faruwa?" Ya tambaya a nutse idanunsa akan morsa safiyya duk da yaga mammina a gefe.
"Suma tayi muhammad......kuma da alama suma ne me zurfi,don duk abinda ya kamata ayi mata an mata amma bata farka ba" Morsa safiyya ta furta cikin nutsuwa saidai akwai wani nauyi cikin muryarta da ya jiyo can cikin kunnensa zuwa zuciyarsa.
Matsowa yayi dab da inda kafadunta suke,ya tsugunna saman qafafunsa yana duban fuskarta kai tsaye karon farko tun shigowarsa.
Sumarta me santsinnan har yanzu tana baje saman fuskarta sassan wuyanta dama kafadunta,saita zamewa tattausar farar fatarta kamar wani ado na musamman. Idanunsa ya zare a hankali daga kan fuskartata,wani abu yana kadawa can qarqashin zuciyarsa da wani yanayi.....da kuma wani amo mara qarfi.
"Ya isa.....muna buqatar shuru" Ya fada da coolness dinsa,don sai a yanxu ya fahimci muryar falaak ce tafi fitowa sosai.
"Muna buqatar iska......ya kamata kowa ya matsa" Ya sake fadi yana miqewa tsam sannan ya fara tattaki yana nufar windows din gurin.
Sum sum hadimai da bayin dake dakin suka fara hada kansu suna ficewa,ya rage shehnaz aisa falaak nannie yakumbo da morsa safiyya.
A nutse yake bude windows din da glass doors din parlor din,take iska fresh ta fara wadatar parlor din.
"Magana ake ta rai da rayuwa,dawowar ruhi gangar jikin mutum,me ya hada hakan da bude windows?......baku lura da halin da ake ciki bane?,tana buqatar taimakon gaggawa.....bawai a tsaya wasu hirarrki ba" Mammina tayi maganar tana nuna akkhnan da hannu,tana kuma nuna fushinta cikin maganarta. Baiko nuna yasan tayi magana ba.......duk wani kallo da take binsa dashi tun shigowarsa dakin yana jinsa a jikinsa,saidai yau deciding nuna mata rashin muhimmancinta ne....don baiga muhimmancin da take dashi ba,lokacin da zata tonawa kanta asiri da kanta kadai ya rage mata yanzu a duniya.
"Ko zaku sake bamu space?" Yayi tambayar haisam kai tsaye yana duban fuskar nannie.
"Me zai hana.....saimu jira daga waje ko?" Nannie ta fada tana duban mammina. A nutse morsa safiyya ta zame akhnan daga cinyarta tana kwantar da ita sosai saman couche din da suke zaune akai.
"Yakumbo keda shehnaz ku zauna ko zaa buqaci wani abun" Tayi maganan ne don yankewa mammina duk wani hanzari ko qoqarin zama da akhnan din. Ta santa farin sani,wannan din ba baqon abu bane a wajen morsa safiyya. A komai daya shafi akhnan saita nuna kusanci,a komai daya shafi akhnan saita nuna itace ahaqqu dashi,ita kuwa a yanzu ta shirya kashe dukkan wadannan abubuwan da take ganin tana da tasiri a kansu. Sai data zubewa morsa safiyya wani iri kallo sannan ta juya tana bin Nannie dake fita,sannan morsa safiyya ta zamana a qarshe ta take bayan mammina din.
A nutse ya tsugunna gaban couche din da take kwance,karo na farko wani irin kusanci mafi kusa ya wanzu tsakanin shi da ita. Idanunsa ya sake zubewa kan fuskar tata,wani irin skin dake glowing kaman bayan tarwada. Idonsa ya lumshe a hankali,yana jin yadda bugun zuciyarsa ya soma canzawa. Kusancin ya masa kusa da yawa.....har yana iya jiyo qamshin hair mist da take amfani dasu saboda inganta sumarta.
"Nauyi ce ita a kanka.....haqqine a wuyanka lafiyarta" Can wani sashe na zuciyarsa ya tunasar dashi. Hannunsa ya cire a hankali ya miqa ga hannunta dake kwance sambal gefanta. Hannunsa ya sanya ya kama hannun cikin nasa da nufin duba bugun jijiyar dake tsintsiyar hannunta. Har cikin bargonsa yaji wani irin abu ya harba yana kuma ratsashi. Karo na farko daya soma hada hannunsa da wata diya mace har haka.....karon farko da hannunsa ya manne jikin hannun wata 'ya mace da zurfin alaqa har haka.
Jijiyar tana bugawa,ya sake janye idonsa daga kan hannun yana maidawa ga qirjinta. Idanu ya zubawa gurin yana lissafa bayan kowanne second nawa zuciyarta ke harbawa don tantance daga inda matsalar take. Second daya biyu kawai yaji kamar ana zare masa duk wani laka dake jikinsa. Akwance yake plate,a miqe sambal,wannan yanayin kwanciyar kuma ya bawa dukiyar fulaninta dake zaune das a qirjin nata cikin tattararar dinkin material din jikinta damar fitowa das kamar an dorasu.
"Ko akwai wani abu da ake buqata?" Muryar aisa data roqa itama a barta ta ratsa kunnensa,abinda ya sanyashi tattara dukka jarumtarsa ya sake maida dubansa saman qirjin nata karo na biyu.
"Pulse Oximator" Ya fada a taqaice. Tsam aisa ta tashi da wani irin hanzari tana ficewa.
Idanunsa ya daga kadan ya kalli shehnaz da idanunta suka fito saboda kuka. Sumar kan yakeso a tattare a kuma saka mata hula da dankwali. Janye idanunsa yayi daga fuskar shehnaz din,ya lumshe idanunsa yana sake budesu sanda ya sake dora hannunsa saman tsintsiyar hannun nata,yana sake jin bugun jijiyar hannun nata. Sake maida idanun nasa yayi still,yana jin kamar wani weakness yana bin kowacce jijiya ta jikinsa dake bashi kuzari.
"Ba'a samu pulse Oximator ba......sai stethoscope" Aisa ta fada tana miqa masa. Alama ya mata da inda a inda zata ajiyeshi,ta ajiye din tana komawa da baya ta zauna hankalinta da idanunta akan akhnan din. Ya sani dukkaninsu suna ganin kamar zasu rasata ne......dukkaninsu sun damu da ita ne,damuwar da ya tabbatar ita bata damu dasu din kamar haka ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 91*
Sake matsawa yayi dab da ita,ya miqa hannunsa da wani irin sanyi yana tattare mata sumar tata dukka zuwa gefe guda,abinda ya sanya fuskar ta wuyanta da qirjinta fita fes. Wani nauyi dukkansu sukaji ya kamasu su da suke gefe sanda ya aza hannunsa saman qirjinta nata ya dora bakin stethoscope din bayan ya sanyashi a kunnuwansa. Bugun zuciyarta ya fara ji sosai cikin kunnuwan nasa,abinda ya sanyashi lumshe idanu sosai. Zaka dauka wani hasashe yakeyi,saidai wanzuwar hannunsa a gurin kawai yana sanya wani abu harbawa da gudun gaske cikin jijiyoyin jikinsa. Yadan cije lips dinsa kadan yana jin nasa gudun zuciyar kamar yana neman haura nata,kamar yana neman hautsinewa da nata gaba daya,yaja iska sosai yana bude idanunsa wanda yayi qoqari sosai kada su sake kai kansu zuwa ga qirjin nata.
Xare abun gwajin yayi daga kunnensa yana ajiyeshi a gefe.....ya fahimci tana buqatar iska ne sosai kafin dawowar numfashinta yadda ya dace. Ya sani,akwai mutane a dakin,akwai mutanen daya kamata aji nauyinsu,amma muma ceton numfashinta da lafiyarta ya zame masa kaman dole.
"Ko zan sake samun raguwar mutane?" Ya fada a hankali yana sake kusanta fuskar sa da tata,abinda ya sake sanyashi qara ganin komai dake saman lafiyayyar fatar fuskarta.
Kusancin daya qara a tsakaninsu ya saka kunya ta kama kowa a dakin,falaak da yakumbo suka juya suna neman hanyar fita,yayin da aisa tayi qasa da kanta,shehnaz kuma abun taji ya fara mata wani tasiri a ranta. Tana cikin yanayin son ceton ran akhnan din da gaske ne.....amma wanzuwar shiekh haisam a gefan akhnan din kamar me shirin bata kyakkyawar runguma sai taji yana sauya komai a ranta.
Kamar wanda wani magnet yakeja haka yake sake rage tazarar dake tsakanin fuskokinsu.....bugun zuciyarsa na sake ninkuwa da gudun dashi kansa ya d'arsa mamaki a ransa,dab da zai aza bakinsa saman nata ya lumshe kyawawan manyan idanunsa yanajin bugun zuciyarsa yana ci gaba da sauyawa.
Kyakkyawan mazauni lips dinsa suka samu saman nata,ya miqa hannunsa yana riqe hancinta me tsaho da dan tudu kadan wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta.
Iska ya shiga hura mata sosai don taimakawa numfashinta da yake fita ba yadda ya dace ace ya fita din ba,tsahon wasu sakanni kafin a hankali ta amsa ta hanyar zuqar iskar daya aikamata din da kyau,taja wani irin numfashi daya sanya qirjinta dagawa sosai ya mannu a jikinsa,sannan ta saukeshi duka lokaci guda.
Ganin ta amsa ya sanyashi ya janye bakinsa daga cikin nata,saidai kuma bai janye fuskarsa ba dab da tata. Mannuwar da tayi a jikinsa ya sanyashi damqe tafin hannunsa da yake cikin nata yana kiran sunan Allah can qasan zuciyarsa,yanayin daya sanya fitar sassanyar iska daga bakinsa dake gauraye da qamshin fresh mint mouth fresh na brand din bonjour care breath spray. A hankali idanunsa suka sauka kan wani dan digon baqi dake saman lips dinta,daidai sanda labbanta masu wani irin color me daukan hankali suke motsawa.