L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 53
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 53: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 53. Idonsa ya maida ga lips din,kafin a hankali ya maida…
3,366 words
Idonsa ya maida ga lips din,kafin a hankali ya maida dubansa kan kyawawan idanunta ma'abota yalwataccen eye lashes da suka yiwa idanun rumfa. Motsasu take a hankali tana qoqarin budesu. Bai taba zaton haka take tamkar tangaran ba.....bai taba zaton wannan taurin kai da kafiyar nata zaibar dabi'ar firgici da tsoro su wanzu a zuciyarta ba,ya tabbatar abu guda ne kawai ya sanyata a wannan yanayin....labarin aurensa. Inda tayi haquri,inda ta kwantar da hankalinta duka duka kwana nawa ne?.....wani mataki kawai yakeso ya taka,wani tsani kawai yakeso ya hau,wani guri yakeso yakai.
Duk wani tunani da ma'ana data bawa aurensu zata fahimci yaudara kanta kawai tayi......zata gane fahimtarta yasha banbam da ainihin ma'anar aikin.
Ya zubamata ido sosai,kafin a hankali cikin laushin nan nasa yace.
"Alhamdulillah" A fili. Wani irin sauka maganar tayi mata a kunne,da wani irin kusanci da bata taba kawoshi ba. Ta ware idanunta a hankali,zuciyarta na sake qoqarin komawa yanayin bugunta na dazu,saidai hakan bai hanata waiwayawa gefan hannun damanta ba.
Fes fararen blue eyes dinta suka sauka cikin nasa. Wadannan dream eyes din......wannan tattausan qamshin daya zame mata jarrabawa.......wannan kallon daya jima da sauke wani nauyi saman zuciyarta yau gasu dab da ita da taqin da bai wuce d'ani daya ba.
Kusancin ya saukar da wani rudewa a tattare da ita,wani irin take ganin kamar a mafarkan data saba yi. Ta yaya zaizo ya zauna dab da ita har jikinsa yana gogar nata?......ta yaya zai kasance kusa da ita da mugun kusanci har haka?.....ta yaya zai samu daman sanya idanunsa cikin tsakiyar nata qwayar idanun har yana iya sarrafa tunaninta da qwayar idanunta?.
Ya riqe dubanta sosai cikin nasa idanun......yana sane kuma ya hanata katabus saboda wani karatu da yakewa tunaninta. Ya fahimto tsoro mamaki da motsawar wannan izzar lokaci guda daga cikin Jininta,har yanzu bai sakar mata ido ba kamar yadda bai bata daman motsawa ba.
"Ki nutsu.....ina nan tare dake......nauyinki a yanzu na wuyana" Ya fadi da wani irin sanyi da nufin sanya nutsuwa cikin tunaninta.
Wani birkicewa ta sakeji tunaninta yayi,sanda kwanyarta ta dawo mata da abinda ya faru da ita a dazu,dazun da batasan adadin awa ko mintuna nawa bane da suka shude.
"Malamin nan dai......ma'abocin girman kai......malaminnan dai ma'abocin izza.....malamin nan dai data tsani komai daya shafeshi.....shine yanzu tsugunne dab da ita?,shine take shaqar numfashin dake fita daga qofofin hancinsa?,numfashinsa ke sauka saman fuskarta?,wani irin numfashi me dumi dake gauraye da wannan qamshin da yake shiga rayuwarta a duk sanda zata shaqeshi.....shine MIJIN AKHNAN....shine sultane ya aura mata.....ba yardarta.....ba amincewarta....ba saninta,sai labarin da ba'a sanya rai dashi ba koda cikin mafarkai?.
Baqinciki haushi da bacin rai suka turnuqeta gaba daya.....haushin kanta shine abu na farko data sake tana duban cikin idanunsa har tsahon wadannan mintunan,wani abu dabai tana hadata da wani d'a namiji ba tunda ta fado cikin duniya.
Da dukka qarfinta take yunqurin tashi bayan ta fahimci tafin hannunsa manne yake cikin nata.....bayan ta fahimci ko dankwalin arziqi babu a kanta.....bayan ta fahimci yadda suturar jikinta ta bayyana kowanne tudu na sirrin jikinta.
"Calme-toi" Ya furta da tataccen yaren faransancin daya kusa sanya numfashinta wucewa. Mamaki da razani da suka cakude guri daya suka sanya numfashinta sarqewa,saita fara jansa da qyar tana jin kamar duk wata qofar shaqar iska ta mata kadan. Ba wani tashin hankali ko rudewa sam a tare dashi ya qara kusancin dake tsakaninsu,ya riqeta da kyau ganin yadda qirjinta yake sake dagawa da alama tana yaqi da numfashinta ne.
"Kija iska sosai sannan ki fitar da ita ta bakinki" Ya fadi da nutsuwarnan da ba komai ke sanyawa tabar cikin jikinsa ba.
Batayi yadda yace ba.....ya kuma fahimci taurin kai da gasken gaske a jininta yake,sai yadan tsaurara muryarsa kadan,don da gaske idan bataja numfashin ba komai zai iya faruwa.
"Karkice zaki yaqi jikinki zuciyarki da hunhunki da suke buqatar iska don su rayu.....su din basusan ke GIMBIYA bace....basu da masaniyar yawan izzar da kike da ita.....numfashi kadai suka sani.....kija numfashi don ki rayu!!" Ya sake fadi yana jin ransa ya soma baci da kalar taurin kanta.
A lokacin ta soma jin wahala a qirjinta da hunhunta,bata da wani sauran zabi illa yin yadda yace din,taci gaba da maimaitawa,sai ya zare hannunsa cikin nata,ya dinga matsawa da baya da baya har ya bada tazara a tsakaninsu,sai ya zauna saman sofa din dake facing kujerar da take kai yana ci gaba da kallonta.
Tsahon wasu mintuna numfashinta ya sake daidaita. A hankali ta maida idanunta ta lumshe tana jin yadda gabbanta gaba daya suka saki. Ko bata bude idanunta ba,koda bata kalleshi ba tasan idanunsa yana kanta ne,tasan kallo yake qare mata,wataqila ma qirjinta kadai yake kalla.
Ta sani....ta kuma sani bata buqatar a maimaita mata. Maza irinsa mayun mata ne,wadanda sau da dama suke fakewa da addini su dinga kallon mata yadda sukaga dama.
Ballantana shi din. Har yanzu tana iya riqe adadin haduwar hannayensu guri daya data tabbatar intentionally ne bawai arashi ba. Me ta yiwa sultane data cancanci irin wannan hukuncin?......me ta aikata ga sultane data cancanci wannan izayar ta auren MALAMI?. Malamin ma datayi imani bata taba jin haushi tsana ko qin jinin wani malami kamarsa ba. Ya qwace mata sultane dinta.....ya qasqantar da darajarta......ya kuma nesantata da sultane ta hanyar taba kusancin dake tsakaninsu.
Samun tabbacin daidaituwar numfashinta ya sanyashi miqewa a nutse,ya soma takawa cikin nutsatsen takunsa daya hana akhnan fahimtar yama fita a dakin,taci gaba da kwanciya cikin qunan rai da baqincikin wanzuwarsa a gurin,yayin da shi kuma ya jima da ficewa a dakin.
"Sannu" Kalmar ta sauka a kunnenta. Taji aisa ce,don haka ta bude jiqaqqun idanunta a hankali ta saukesu a kanta. Kallon kallo suka yiwa junansu na wani dan lokaci,tambayoyi ne masu yawa cikin kanta.....tambayoyine tuli da takeson ta yiwa su aisa su. Dama can sunsan da plan din aura mata mutumin kowacce ta kama bakinta ta tsuke?,dama suna da labari amma sukaci amanarta sukayi shuru?,ko kuma yadda labarin yazo mata haka suma yazo musu?.
"Ki rufa mana asiri don Allah" Taji muryar shehnaz kuma daf da kafadarta inda yake zaune a dazu wanda ta jima da dauke kanta daga gurin gudun kada yaga fitar hawaye daga idanunta. Abinda take ganin zai zame mata qarshen abun kunya.....yaga weakness dinta?. Ta bari yaga hawaye daga idanunta?.
Idanunta ta bude akan shehnaz dake dafe da qirjinta,duk da fuskarta ta nuna tashin hankalin data shiga a dazun amma bata fasa fadin abinda ke zuciyarta ba. Kai ta gyadawa akhnan
"Eh ki rufa mana asiri karki sake suma.....don idanunmu ba zasu iya sake daukan nauyin kallon abinda muka kalla a yanzu ba.......bamu iya jura bama.....fita mukayi. Wani irin shauqi tun a yanzu akhnan?.....ya cika dakin da kwarjininsa gaba daya....." Idonta ta runtse da kyau.
"Don Allah shehnaz.....don Allah" Ta fada da wani irin sanyi. Maganganunta suna tuna mata yadda hannuwansa suka samu daman taba sassan jikinta ne kawai......hannunta.....gashinta.....bayan nan me dame ya taba ma?. Tambayar da tayi tsawa a kanta kenan,harta bude idanunta da sauri ba tare data shirya ba ta watsasu akan fuskar shehnaz,da murya me qarfi wanda sautinta ke fita da wani irin rauni don har rawa sound dinta yakeyi
"Don Allah shehnaz......me dame ya taba a jikina?" Sak aisa tayi,don tambayar ta mata girma saboda,amma ga shehnaz 'yar katobara sam.bataji komai ba,saima dadin tambayar dataji. Tana murmushi abinta ba tare da duba da yanayi da dalilin tambayar da akhnan din tayi mata ba ta gyara zamanta tana blushing.
"Connexion profonde(deep connection)Mouth to mouth resuscitation" Ta fadi kanta tsaye abun yana sake dawo mata a kwanyarta tana sakin murmushi.
Idanu sosai akhnan ta fidda tana fara shiga tunanin yadda bakinta ya hadu da nashi. Wani matsanancin bacin rai ya sauko mata,sai kawai ta fashe da kuka tana jujjuya kanta da sauri,wasu tawagar hawaye masu dumi suna sauko mata.
"Allah zai sakamin......wallahi Allah zai sakamin" Ta fara fadi kaman wadda zatayi iska. Tsoro abun ya baiwa aisa,ta watsawa shehnaz harara. Muddin akhnan din ta fara bore irin wannan abund me wahala sauko da ita ta sauqi,batasan ma ta inda zata fara ba indai itace zata gyara Barnar shehnaz din.
"Kowacce tambaya ma wai tana da amsa ne?....."💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 92*
Idanu shehnaz ta fidda tana kallon aisa.
"Meye laifi na?,tambaya tayi na bata amsa fa.....aisa mana....me nayi?,gaskiya na fadi mata fa" Iska sosai aisa ta furzar a bakinta,ta sauke hannuwanta tana nufar akhnan dake kuka sosai kamar qanqanuwar yarinya.
"Biftu mana.....kin manta wacece ke?,ya zaki abinda zaki zubda martabarki?,sassanki cike yake da hadimai kin sani....kinaso suji ne?". Wani kallo ta watsawa aisa din da jiqaqqun idanunta.
"Hardaku aisa.....hardaku aka auramin shi.....me zakucemin?....aisa banason ganin kowa!!" Ta fada cikin daga murya da qaraji. Baya aisa taja tana duban yadda gaba daya akhnan din ta birkice kaman ba ita ba. Ta iya rigima ta kuma iya tuburewa akan abu,wannan din wata dabi'arta ce da aisa ta jima bataga ta motsa ba......amma ta sani yau kam saita Allahu.
Duban juna sukayi ita da shehnaz,saita soma takawa tana fita. Ta gama yanke abinda zatayi,gwara kawai ayi.maganin akhnan din me gaba daya.
Banda iya shegen banza da wofi......idan aka cire SARAUTA da take taqama dashi ba wani abu data hanga wanda akhnan din zata gwadawa sheikh haisam. Ta wata fuskar ma idan aka cire SARAUTA din sheikh haisam din irin mazan nan ne da ake cewa KODA KUDINKA saida rabonka,bataga wani abu qwaya daya da zai sanya a gujeshi ba. Idan aka azata a mizanin aji.....idan aka dora a sikelin dacewa bata isa ta tsaya matsayi daya dashi ba,wai bahaushe yace IDO BA MUDU BA YASAN KIMA wannan karin maganar da haisam din kawai tafi dacewa.
Taso ta tarar da haisam din,saidai ta samu tuni ya wuce,sai yakumbo morsa safiyya da mammina dake yunqurin dawowa ciki duba jikin nata.
"Gwara ku shiga kuga abinda takeyi,nikam bazan iya ba" Aisa ta fadi tana ratsasu ta wuce abinta,saidai taci alwashin nan da wanni uku zuwa hudu muddin akhnan din bata shiga hayyacinta ba sai tayi maganinta. Ta tafi bawai don ba zata dawo ba,ba kuma wai don ba zata bibiyi al'amarinta ba,ta tafi ne ta lissafa awannin,ta kuma jira taga hankalin akhnan,taga ME ZAI SAUYA?.
Juyi tayi kawai tana yin rub da ciki saman gadon data tashi ta koma kai,ta jawo fiber pillows dinta masu tsananin laushi ta cusa kanta a qasansu.
Kuka take sosai,tana sake jin baqinciki yana ratsata. Kuka take har zuciyarta,irin kukan data manta rabonta da yinsa. Gefe guda tana jin wannan qamshin turaren nasa a duk wani motsi da zatayi baibaye da jikinta,abinda yake sake matse zuciyarta kenan,kukan yana sake narkewa gami da gangarowa tun daga tsakiyar zuciyarta.
Itakam ta sani,nata ya riga ya qare,ta sani ba qaramin abu bane zai sanya sultane daura mata aure irin wannan. Ba shawara da ita ba kuma neman yardarta. Ta sani ba jiya ba ba yau ba,ba qaramin ganin girma da martabar malamin yake ba. Abu na farko daya sake jawo tsanarsa kenan a zuciyarta bayan zargin da take dashi me qarfi na cewa shine mutumin hippodrome.
Ta tsani tana gaba wani ya tako ya karbe matsayinta. Ta sani tana sama wani ya jawo hannunta ya sauketa qasa. Bata ga maciji da duk mutumin da zai musa girmanta da martabarta. A cikin dukkanin wadannan abubuwan ba wani abu da bai aikata mata ba.....AKAN ME ZATA QAUNACESHI?.
Uwa uba ma shi din tsintacciyar mage ne. Bata da tabbacin akwai wani cikakken nasaba da yake da ita dangi ko ahali. Koda yana dasu wanne MATSAYI yake dashi a rayuwa?,wanne FADA AJI yake dashi?,wacce wayewa ya mallaka?. A sanda duniya ta dade da yin gaba,a sanda duniya ta jima da wayewa,a sanda idanu suke a bude da sanin ME AKE NUFI DA RAYUWA bataga wani abu daya hada MALAMI da dukkanin wadannan abubuwan ba.
MALAMI FA!.....ORDINARY MALAMI! Sunan ya sake bugawa cikin kanta,take wani sabon kukan ya barke mata.
Tana jin maganganunsu morsa safiyya,muryar dake sake qona mata rai,taji muryar mammina da dukka irin salon gwanancewarta da sanin yadda zata shawo kanta,amma dukka a banza. Nannie tayi nata haka yakumbo,ammo ta daga kai ta kalli wani a cikinsu ta qiya.
Tsaf morsa safiyya ta karanci yanayinta,wannan tsoho halin....wannan kafiyar,saita juya dukkaninsu ta kallesu.
"Ina ganin muje haka.....duk randa taga damar samawa kanta salama zata fahimci kalar abinda akeson gaya mata.....aure ne dai biftu ya gama dauruwa......haquri da kuma fuskantar gobenki ce kawai ta rage miki". Wani irin suka maganganun sukayi mata. Aita sani basai ta nuna mata ba.....ta sani cewa tana farinciki da hawayenta.....ta sani cewa tana walwala da dukka abinda zai bata mata rai,ta tsani jin dadinta ko dariyarta,tana kuma da yaqini da saninta da hadin bakinta sultane ya shirya wannan BARAGURBIN AUREN.
Wani irin murmushin nasara da mugunta mammina ta saki can qasan ranta. Duk da zuciyarta na mata kokwanto da suya na canjin data fara gani tattare da akhnan. Tun daga ranar da almaz ya saketa bata sake bata wata fuska ko dama kamar yadda take bata a baya ba.....to amma yanzun wata dama ce a wajenta na gyara wancan alaqar......wata dama ce a gareta na maido komai kan hanya.....na maido komai kaman yadda yake a baya.
"Bada wannan harshen ya kamata kiyi magana da wanda ke cikin damuwa bafa morsa......hankalinki har yanzu bazai taba zuwa daya daga akhnan ba". Wani kallo morsa safiyya ta watsa mata,kaman zatayi magana sai kuma ta juya abinta a nutse tana ficewa bayan ta ajewa mammina wani kyakkyawan murmushi. Murmushin da mamminan tayi imanin ba REAL MURMUSHI bane.....murmushin da tayi imanin akwai wani abu a bayanshi. Duk da tana benefiting da yawan fushin morsa safiyya da dabi'arta na gaza boye fushinta da abinda ke cikin zuciyarta......amma tana tsoron AMSA CIKIN SHURU irin wannan na morsa din.
"Muje mammina......wannan 'yar kashin bata inda zata fahimci mutane......amma ta bakin safiyya ai shima kuka yana da iyaka idan ba me rarrashi" Yakumbo ta fadi tana sanyasu a gaba suna ficewa,duk da ba haka mammina taso ba......ta kuma ci alwashin YANZU ZATA DASA SABON HARSASHI ta tafi badon ta tafi bane gaba daya......ta tafi amma kuma ZATA DAWO a nan kusa bawai a nesa ba.
*HAISAM*
Strange feeling kawai yakeji cikin jikinsa. Wani irin yanayi yakeji da bai saba jinsa tattare dashi ba. Wani irin mutuwar jiki,yana takawa da nutsuwar da bazata baka daman fahimtar abinda yakeji din ba ya nufi sashensa.
Iska ya furzar daga bakinsa. Wani abun ne da bai taba faruwa dashi ba tsahon rayuwarsa. Cakudedeniya da jikin diya mace. Mutum ne shi me yawan nesanta kansa da ire iren wadannana abubuwan qwarai da gaske. Ya sanyawa ransa akwai LOKACI. Lokacin dashi kansa ya tabbatar idan yazo bazaiji bari ba.......ya killace kansa ga HALAL dinsa kawai.....ya killace kansa wa halastacciyar matarsa. Matar da a sannan shi kansa bai taba hasashe ko tunanin WACECE BA....kawai ya sanya a ransa ME RABO,shine sunan kawai da yakan furta.
Sake fesar da iska yayi daga dogon hancinsa daya tsaya sosai saman fuskarsa. Baisan me yasa qamshin hair mist dinta ya maqale a hancinsa ba.....baisan me yasa qamshin turarenta ya nace shima a hancinsa ba. Gaba daya kansa sake tariyar moment din yake masa wanda duka duka yanzu ya baro gurin.
Idanunsa ne suka sake hasko mata qirjinta dake zaune cif tsakanin kafadunta guda biyu. Wani irin zubawa tsigar jikinsa tayi har sai daya dunqule hannunsa da kyau yana furta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Can qasan ransa. Duk yadda aka jarrabi maza da son gurin.....wanda bai tsame kansa da kansa ba.....don daya daga cikin abinda ya sanya ya wajabtawa kansa lowering gaze dinsa akan kowacce mace.......amma bai taba hasashensu haka kusa da kusa dashi ba.
"Idan ka samu kusanci sama da haka dasu fa?.....inda ace zaa bude......." Cikin azama ya tsawatarwa sashen zuciyar dake qoqarin qawata masa wannan tunanin cikin ransa......wanda ko a yanzun qoqarin yakice wancan image din dake cikin idanunsa da kwanyarsa yake.
"Halal dinka ce fa" Wata zuciyar ta tunasar dashi. Murmushi ya yiwa kansa da kansa,yana tuna cewa tuna hakan da maido hoton ga idanunsa ba haramun bane.....to amma kuma aurensa ba yana nufin wanzuwar komai a tsakaninsu ba. Aurensu yafi cancanta da a kirashi GARKUWA......zata zame masa garkuwa da zai wasa da hankalin mammina yadda ya kamata......ita kuma zai mata ALFARMA kamar yadda kowa nata ya buqata.
Da wannan kasalar ya murza handle din sassansa ya shiga. Still suna zaune suna hira abinsu,kamar wadanda suka shekara goma basu hadu ba. Wannan karon harda naseeb daya basu tabbacin ya koma Riyadh lafiya.
"Wancan angon har ya dawo daga gurin amaryar ne?" Naseeb ya fadi wanda shi daya ne ya hangi shigowar haisam da fara haurawa zuwa stairs dinsa,ya kuma qare masa kallon tsaf sanda yake takawa din.
Waiwayawa sukayi suna dubansa kafin maleek ya dawo da kallonsa akan naseeb yana danne dariyarsa
"Bari naje na sameshi"
"To kabi dai a hankali......kasan tsohon tuzuru ne......idan kuma kaje kayi abinda zaka tunzurashi yaqi shige maka gaba shikenan".
" Bazan fara ba.....don idan na rasata mutuwa.zanyi" Ya fadi yana haurawa ta bayan kujerun ya dirga yana wucewa stairs din. Yana jinsu suna masa dariya su dukka.
"Nidai naga alama sarakan nan basu iya zarmewa ba idan suka fada soyayya.....duk wani maintaining pride da sukeyi sai ya dinga rawa.....me yasa?" Khadeem ya fadi,yana jinsu omar na goyawa maganansa baya,sai ya saki murmushi kawai baibi ta kansu ba.
Shidai ya sani da gaske ne mutumin daya fiya shuru kamun kai da nutsuwa abune me sauqi soyayya ta rikitashi. Ya yadda da gaske falaak ta rikitashi,shi kansa idan ya tsaya gaban madubi yana kallon kansa sai ya dinga ji da ganin kamar ba shine maleek ba. To amma baida wani qwarin gwiwa ko tabbacin haisam zai fada haka da sauri.
Ya sani ba wanda zaice yafi qarfin siyayyay,tana da wani irin qarfi da take iya wargaza komai da kowa.......to amma bashi kadai ba,dukkansu sun sani ba abu bane me sauqi hakan ta kasance akan mr lowering gaze dinsu.
_uhmmmm.....nidai nace banda cika baki_
Sai daya zauna ya jirashi ya fito daga toilet. Kansa da damshin ruwan dake nuna alwala ya daura. Dubansa yakai ga agogo,akwai sauran kusan awa daya ko mintuna arba'in kafin lokacin la'asar yayi,to daura alwalar kuma ne meye?.
Kallo daya tak maleek yayi masa ya janye idanunsa daga kansa. Idanun nan na captain din.....wannan manyan idanun dake da wani irin kaifi da tsini gaba daya sun koma sun rusuna,sunyi wani irin laushi. Tattara duk jarumtarsa yayi yakai dariyanshi qasan ransa ya danneta,sannan ya debo tambaya ya dora akai.
"Wai me ya faru?.....wani abunne me tsanani?".
" Me ka gani?" Haisam ya jefawa maleek din tambayar da wani irin coolness. Yadda ya zuba masa ido yasan yanason samo.amsar tambayarsa ne daga kallon da yake masa,don haka sai ya basar yana amsa masa tare da sake danne dariyarsa qasan ransa.
"Aah....yanayinka ne yake nuna kaman ba lafiya ba". Shuru yayi kawai,ya maida idanunsa ya lumshe sannan ya budesu akan maleek.
"She was so fragile maleek......ina mamakin yadda stubbornness dinta yake da yawa bayan tasan duk wani strength nata bame yawa bane......ta dauki kanta da fadi maleek......" Haisam yayi maganar da alama dabi'un nan nata biyu suna ci masa rai. Yana iya jin maganganunta dasu aisa a kunnensa bayan ya fita,don bai nisa ba yadan tsaya yana amsa godiyar da morsa ke masa.
"Tana zaton ina da interest ne a kanta?.....kota dauka ina cikin jerin lusaran mazan da suka dinga zuwa neman yardarta ta auresu kaman ita kadaice diya macen data rage a duniya?.....to hell with her sarautan.....to hell with her mulkin.....da tasan yadda komai yake da bata suma ba.......sultane kawai nake kalla da morsa safiyya maleek " Ya qarasa maganan fushi yana nunawa qarara saman fuskarsa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 93*