Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 54

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 54

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 54: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 54. Zallar mamaki ya kama maleek,sai kawai ya zuba masa ido…

3,333 words

Zallar mamaki ya kama maleek,sai kawai ya zuba masa ido yana kallonsa. Yau a karon farko bayan dogon lokaci haisam din yana fada saboda wata mace ta bata masa rai?. Shi baya complain completely akan mata.....in fact ma bashi da wani hadi dasu,yana qoqarin avoiding nasu ne kawai akan komai nasa.

"What about this" Maleek ya fadi yana pointing qasan labban haisam din. Wani haushi ya kama haisam,yana masa maganan abinda yakeji yana bata masa rai yana nuna masa fuskarsa?. Duk da hakan baiqi ta maleek din ba,ya miqa hannunsa qasan lips din nasa yana dangwalo gurin,sai yaji danqo.

Koda ya dawo dashi zuwa ga idanunsa lipstick ya gani baby pink in color. Wuta tadan dauke masa,kafin ya mutstsuka yatsunsa yana batar da kalar dake jikin yatsunsa.

Qaramin tsaki ya sake ja,mintunan suna dawo masa akai. Baisan me ya jashi bata irin wannan taimakon ba.....baisan ya akayi ya hada jikinsa da nata ba har haka.

"Saboda ka ceci rayuwarta......saboda ganin girman sultane da morsa safiyya right?" Yaji maganan maleek tsakiyar tunaninsa. Kallonsa yayi kafin ya sake kauda kai yana cirar tissue guda daya yana goge duka area din lips dinsa.

"Ko ka karbi first kiss ne?" Maleek ya fadi qasa qasa yana duban haisam. Yi yayi kamar baiji ba,sai kuma ya shammaceshi yakai masa naushi,yayi kyakkyawar sa'ar samunsa a kafadarsa.

Gurin ya dafe yana yamutsa fuska yana duban haisam.

"Yanzu idan kayi nasarar karyani me zaka cewa me martaba?....me kuma zaka cewa falaak?".

"Idan kaga na shige maka gaba an baka ita kenan ba" Ya amsa masa yana nufar hanyar toilet,don ya fahimci a wannan karon dukkaninsu sun toshe kunnuwansu ne da idanunsu,dukkaninsu ba wanda ya daura aniyar fahimtarsa,kawai su auren yayi musu......kome meye a ciki nasa lissafinne shi kadai.

"Kada muyi haka daki mana.....ka dawo muyi magana,nayi alqawari zan fuskanceka"

"Bana buqata.....a yanzu dai bana buqata. Tunda kazo agadez soyayya sun hadu da omar sun lalatawa me martaba yaro. Ba zaka gane zancena ba,ba zaka gane maganata ba muddin ba zancan soyayya bane zan maka. Na yafe kaje,wanka zanyi,zan kwanta kuma idan na fito,sai lokacin sallah yayi zan fito da kaina.....na roqeku ku barni hakanan" Ya fadi yana tsaye bayan qofar toilet din yana hade hannayensa biyu alamun roqo.

Fuskar tausayi maleek yayi masa sannan ya juya yana jan qafa alamun yayi giving up ya fice.

Duk da bai shirya ba amma sai da murmushi ya subuce masa. Ya yarda da maganar nan da ake cewa abokinka matattarar sirrinka ne,dukkaninsu idan suka hadu kaman yara suke ga junansu. Idan suna wani abun a tsakaninsu,yakanyi tunani musamman a inda yake komawa da baya yayi relaxing,sai yaga meye na musamman a tare dasu mata ke nacin binsu haka?.

Tambaya ce dake dauke da daruruwan amsoshi da zai miqata ga dubbannin 'yammatan da burinsu shine ta mallaki guda daya a cikinsu.

*TAMIM*

Zufa kawai yakeyi wadda ta wankeshi tassss tamkar wanda aka dauki botikin ruwa aka watsa masa.

Wani irin fushi ne yake bayyana kansa da kansa saman fuskarsa.....fuskar da a yau tsananin fushin ya sauya mata kamanni zuwa wani yanayi me ban tsoro maras kyan gani. Hancinsa ya bude sosai,ya kuma ninka girman da yake dashi,hakanan idanunsa gaba daya sun juye sun sauya launi.

Bai taba zaton komai zai juye haka da hanzari ba......bai taba hangenta a matsayin MATAR WANI BA baya ga shi,tun sanda ya samu nasarar qara bugar da almaz ya samu ya rattaba mata saki uku.

Gwara auren almaz sau million akan wannan auren. Akan wannan auren bashi da wani sauran hange......akan wannan auren bashi da wani sauran tunani,akan wannan auren fatan a saketa nan da SHEKARA dubu ma gani yakeyi yayi kadan.

Matashin malamin nan fa?.....shi aka bawa,mutumin da tsaiwa kawai kusa dashi sai me dakkakiyar zuciya. Mutumin da har yanzu ba kowa ke iya kallon qwayar idanunsa ba.....mutumin da tun daga nesa kwarjininsa yake kasheka gaba daya,ta yaya zai iya warware wannan lamarin?.

Bazai taba yarda ba.....bazai taba aminta wahalarsa ta shekara da shekaru su tashi a banza ba.

Ba kalar bautar da bai ma mammina ba.....ba kalar hadarin da bai jefa kansa ba,ba kalar barazana da rayuwarsa data ahalinsa da bai gani ba.....hasalima ya rasa iyalinsa ne saboda sadaukarwa ga mammina......ya rasa kowa nashi saboda sadaukarwa......shi me yasa zata bari ya RASATA?. Yarinyar data girma a gabansu?.....yarinyar da yasha duqawa.....yarinyar da yasha kwanciya ta takashi tabi da kansa. Tsawa umarni kala kala ba wanda baibi ba nata. Dukkan wata kariya ta fili data boye ya baiwa yarinyar saboda TANADIN WANNAN RANA. saboda ya sani cewa komai da kowa na masarautar agadez yana qarqashin umarnin zeenatu.....komai da kowa yana qarqashin sarrafawarta,sai abinda ta tsara ya faru shi zai faru.....Cewa kawai zatayi NA BAWA TAMIM ya tabbatar kuma ta badu har abada.....amma sai gashi a karon farko bata masa kara ba......a karo na biyu ma haka?.

Tattare rigar jikinsa yayi ya watsar a saman shimfidar dake gurin. Abinda yake hange yana tasiri kadan kadan shine.....kamar K'ARFIN juya komai da zeenatun ke dashi kamar yana raguwa.....kamar yana ja da baya. Shi kuma ya sani,yayi rayuwa da sarakuna kala daban daban,a duk sanda irin haka ya fara faruwa,to tamkar fa komai yana shirin kwabewa ME IKO KENAN. Idan kuwa haka ne ko yaya ya kamata ya fanshe wahalarsa ta shekaru.

"Koda baka mallaketa qarqashin aurenka ba.....koda bata zama taka ta har abada.......ko sau d'aya tak ka d'ana wadannan abubuwan da kake kwana kana hasasosu,ko sau daya ka ratsa wannan ma'ajiyar izzar.....ko yaya KA GAURAYA JINI DA JINI TSOKA DA TSOKA" Wata mahaukaciyar dariya ya saki saboda yadda tunanin yayi masa dadi,ya sake qyaqyacewa yadda tunanin yayi masa daidai.

"Matar sheikh haisam take a yanzu fa?" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa tamkar me tunasar dashi.

Wani mahaukacin tsaki yaja,yana jin a yanzun koda babanta ne ke aurenta shima sai ya d'ana,koma waye mijin tabbas shima sai ya huce wahalarsa. Koda daga sannan fuskarsa zata bace Bat daga agadez,ballantana KWANYARSA tana wani irin mugun ja da bashi da kokwanton komai zai tafi cikin sirrin da saidai idan shi yaga dama ya yayeshi. Zubewa yayi saman kujerar yayi d'ai d'ai yana ci gaba da qyaqyata dariyarsa cikin nishadi.

*_TURQASHI!.....AH NACE TURQASHI.......LALLAI,ANYA TAMIM BAKA DEBO RUWAN DAFA KANKA BA KUWA?_*

*_KALLON MUHAMMAD HAISAM KAWAI KAKEYI BA TARE DA KASAN TRUE COLOR DINSA BA.....amma hausawa sukace shi me rabon shan duka ai bayajin bari sai yasha,muje zuwa_*

*AKHNAN*

Ba abinda ya canza tun daga awannin dazu har zuwa yanzun da yammaci tayi magariba kuma ke shirin kawo kai.

Kuka kawai takeyi kaman ba gobe....kuka takeyi kamar ta rasa komai nata. Duk da tanajin ta rasa komai dinne,tanajin rayuwarta ta naqasa,tana kuma jin duk wani buri nata ya gama mutuwa murus. Ina zata iya buda baki tace wai MALAMI ta aura?,dame zatayi tutiya?. Tana neman wayayyen namiji ne.....tana neman namijin da zai tsaya gaban duniya yayi magana da dukka yaren da ake buqata. Namijin da zai kama hannunta ya sakar mata dukkan 'yanci......ya sakar mata dukkan dama,ta jagoranci rayuwarta da kamfaninta daya kasance zuciyar dukiyarta zuciyar SULTANE zuwa matakin da ba wani company daya taba kaiwa har haka.

Birra tayi dabarun,tayi maganan duka a banza,don daga qarshe ma tsawa ta bugawa birra din ta koreta.

"Kada na sake ganin fuskarki a nan munafuka" Ta fada a tsawace kamar zata cinye naman birran danye. Sum sum birra ta miqe zata fice.

"Zoki tattara komai ki fita dashi,.....banason ganin kowa.....banason komai kuma" Ta sake fadi da fuskarta datayi jawur saboda awannin data dauka tana kuka.

A nutse birra ta qaraso tana kwashe kayan abincin da tun dazu take jerasu,tana satar kallon yadda ta tura kanta qasan pillow taci gaba da kukanta.

Tausayinta takeji har qasan zuciyarta,tausayinta takeji sosai,tana da kirki wanda saika zauna da ita sosai zaka fahimci haka,tana da qoqarin kyautatawa wanda yake hidima a qarqashinta,duk da tana da fada tana da zafi tana da izza amma hakan bai sauya kirkinta ba. Duk da kukan da takeyi ita har ga Allah tana murna da wannana auren. Jikinta yana bata abubuwa masu yawa game da mammina da rayuwar Akhnan din,saidai abune me razanarwa a iya zuciyarta ma kawai ta zargi GIWA ballantana akai ga furtawa.

Mamaki yana qara cika birra,ta rasa kukan mene ma Akhnan din keyi?. Ta yarda da gaske ne idan dadi ya yiwa bawa yawa sai yace ALLAH KASHENI NA HUTA. A iya rayuwar masarautu da sukayi tun tana mitsitsiyarta har kawo yanzu,bata taba ganin NAMIJI da ya dauki hankalinta ba kamar sheikh haisam ba. Ta gaza gamsuwa cewa ordinary sheikh ne......komai nasa yasha bambam da kowanne malami da idanunta suka taba gani ko suka taba zama dashi. Kwarjininsa yafi mata kama dana BASARAKE ko jinin sarauta. Sukan zauna wani lokaci su yasu suna gulmar kyansa.

"Jinin annabi yusuf" Shine sunan da sukan kirashi a boye. Yana da tarin ilimin daya sanya kwarjini da nutsuwa suka masa wani irin ado......to dukka bayan wadannan me Akhnan din take nema?. Sarauta ce kawai za'a ce bashi da ita.....ko kuma ace shi din ba jinin sarauta bane,a dabi'unsa da yanayinsa kuma bayyana SARAUTAR kawai sukeyi......amma baya ga wannan bataga wani abu na aibu ko tawaya a tare dashi ba,saidai idan kukan BADAN SARAUTA BANE Akhnan din takeyi.

"Zaki fita ko sai na miki duka!" Ta sake fadi ga birra wadda ke tsugunne tana tattare kayan tunani yaci qarfinta.

"Tuba nake" Ta fada tana qara hanzarinta,tana kuma jin wani dumi yana busowa daga inda Akhnan din ke kwance.

Babu ko shakka zazzabi ne,zazzabi takeyi,tana dadewa batayishi ba,amma birra ta sani,duk ciwo idan Akhnan ta tashi yinsa da qarfi yake durfafarta,sai taji a jikinta don tana dadewa bata yishi ba.

Tana tsoron kada ya kwantar da ita yadda ya saba mata,tana kuma tsoron gayawa kowa kada ya zamana tayi laifi,da wannan tunanin ta isa kitchen ana qwala kiran sallar magariba a babban masallacin dake manne da gidan sultane.

Umarni ta bayar dasu tattara komai da aka dafa su bayar,ta basu simple recipe na lite abu tace su dafa a ajjiye. Tayi hakanne incase don tasan dole ba zata bari Akhnan din ta kwana da wannan uban zazzabin ba,dole saita gayawa wanda ya dace don a samu a bata kulawa kada yayi mata yadda ya saba,don zafin yayi yawa,kada yakai matakin convulsion.

Kebantaccen parlor dinsu da aka ware musu hadimanta mafi kusanci su biyar dinnan. Birra buhaina bushira barratu da bara'atu. Su biyu ta tarar,suka bita da kallo sanda take zama gefan kujera tana daukar daya daga cikin wayoyin da ake ajiye musu saboda buqatar kiran gaggawa ga wani sashen ko wani a cikin gidan.

"Har yanzu bata haqura ba?" Buhaina ta fada tana duban birra. Kai ta jinjina cikin alhini tana lalubar number aisa.

"Wannan mahaukacin zazzabinne ma a jikinta,tsoro nake kada ta shiga convulsion ma" Tayi maganan daidai sanda ta danna kiran aisa.

"Ikon Allah......lallai dadi idan ya yiwa mutum yawa ba abinda bazaiyi ba......anya wannan karon qwaqwalwar gimbiya lafiya qalau take?" Buhaina ta fadi qasa qasa tana kama haba idanunta akansu dukka su biyun.

"Kema kina mamakin yadda take bore akan auren mutum kamar sheikh muhammad ko?" Barratu ta fada tana duban buhaina. Kai ta jinjina

"Sosai fiye da yadda kike zato......inama inama.....inama ace....."

"Dakata malama" Birra ta fada tana dariya.

"Ai karma ki qarasa.....aljanna tafi qarfin arne" Dariya suka saka su dukka ukun don kowacce ta karanci hasashen kowa.

Maida idanunta birra tayi kan wayar ganin an daga,gabanta yadan fadi tana fatan Allah yasa aisa bataji abinda suke magana akai ba.

Sake jaddada sallamarta aisa tayi tana basarwa birra kamar bataji tattaunawarsu ba. Bataga laifinsu ba ko d'is,don basu ba,ko ita tana wannan tunanin,ko ita tana cewa inama inama din...... Ba wata isashiyar mace da zata mallaki haisam ta raina.....kome isarki kome kuma matsayinki a duniya. Wani irin namiji daya zama LU'U LU'U cikin maza.....diamond ne uban gold kuma kakan azurfa. Amma batasan da wanne idanu Akhnan ke kallon abubuwa ba,ta iya yiwuwa bada irin idanun mutane take kallo ba,ta iya yuwuwa zuciyarta ta qarfe ce kota roba data kasa jin amincin da dukkaninsu sukaji da labarin aurenta da haisam din.. Amma ta sani,ko ba jima ko ba dade wataran zata fahimci cewa DIAMOND Allah ya dauka ya bata.

"Ya ake ciki?" Aisa ta tambayi birra.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 94*

"Ba wani sauyi,kuka take har yanzu,tun abincin safe bataci komai ba.....zazzabinnan nata me wuyar sauka ne yanzu haka a jikinta,kuma kaman ya fara qarfi" Kai aisa ta jinjina,itama ta sani,zazzabin Akhnan idan ya fara yana da wahalar magani yana da wuyar sauka kuma. Jini yake qone mata wani lokacin idan yaso tsiyarsa,wannan ya sanya ake tattalinta sosai,daya fara kuma ake tsayawa a kanta.

"Kici gaba da kula da ita,zan gyara lamarin".

"Godiya muke" Birra ta fadi aisa ta yanke kiran tana yabawa kalar hadiman da Akhnan din ta samu. Dukka yaran suna qaunarta qauna ta fisabilillahi,suna kuma dukkan qoqarin su a kanta gurin kula da ita da kula da abinda zai cutar da ita.

Wayar ta ajiye a nutse,ta kuma shiga closet dinta ta samu wadatacciyar abaya ta saka da baby hijab me dan girma,sannan ta yiwa hadimarta guda daya maganan tazo ta rakata.

*HAISAM*

Sam ya mance da abinda ya faru a dazun,saidai abu daya dake dawo masa cikin kansa lokaci bayan lokaci. Doguwar waya da maganganun da sukayi da sultane kamar me masa ban kwana ko wasiyya. A dukkanin hirarsa ya fahimci girma da tarin qaunar da yakewa Akhnan zallah cikin maganganunsa. A maganarsu ya sake fahimtar kamar akwai wani abu a boye dame damun sultane din wanda shima qila baisan meye ba.....kawai dai ya fahimci akwai wani abu da bai zama comfortable dashi ba. Bai iya dannewa ba,bai iya kawaici kaman yadda yaso ba,sai daya rufe maganan tasu da fadin.

"Don Allah.....kayi mata alfarma koda ita bata fahimci haka ba....taci tawa alfarmar......kayi mata riqo tamkar riqon da zaka yiwa qanwarka uwa daya uba daya. Ka maye mata gurbin ubanta sultane.....ka maye mata gurbin mahaifiyarta SAFEENA" Maganan ya tsaya masa sosai a rai. A duk sanda ya tuna labarin safeena sai ya sake jin girman baiwar Allah ya qaru a ransa......sai ya sake jin kamad ya zama WAJIBI a kansa ya tone JININTA GUDA BIYU data bar irinsu a duniya ake neman birnesu saboda rufewa da yanke bayanta.....saboda shafe IRINTA a duniya gaba daya.

Ta fuskanci wata irin birkitacciyar rayuwa......tayi sadaukarwa da dukkan qauna da soyayya,kalar sadaukarwar dake wahalar samu a yanzu. SOYAYYAR GASKIYA datayi wahala......tatacciyar qauna mara algus a cikin ta ko kadan. Yakanji kamar wani alqawari ne me girma a kansa da tuna labarin safeena kawai.

Zuwa yanzu da suke takowa daga masallaci zasu koma sassansa ransa fresh yake jinsa. Yana tsara yadda bazai kwana bane yau a gidan,so samu ya kwana a personal house dinsa,amma kuma bayaso hankula su fara kaiwa ga tunanin inda yake fita ya kwana din.

"Ta yaya wai zakaje damu gida captain?.....ka manta kana da iyali yanzu cikin gidan nan?" Muryar khadeem ta sanyashi daga kai yana dubansa. Bazaice ya manta duka ba.....amma tunaninsa ya aje zancanta a gefe,yanzun hankalinsa yafi karkata ga wancan asibitin na Ethiopia,don ya tabbatar akwai wata qura a lullube a gurin.

Kaman zaiwa khadeem din magana sai kuma ya dauke dubansa kawai. Ya karanci abun dadi kawai yake musu,shi baisan har haka sukeso ma yayi aure ba sai yanzu,baisan me yasa sukafi son suga yayi aure akan kowa ba,bayan dukkansu ba auren ne dasu ba saidai niyya.

Sallamar da akayi daga dan gabansu kadan da muryar mace ya sanyasu sukayi dif gaba Dayan su. Fuskar aisa din adan sake take gaidasu,suka amsa banda haisam daya maida hankalinsa ga wayarsa data dauki haske alamun shigowar saqo.

"Ko zan iya magana da sheikh muhamamd?" Aisa ta fadi tana duban haisam din kai tsaye,izzarsa da kamewarsa tana burgeta. Sai a sannan ya daga manyan fararen idanunsa ya sauke a kanta,tadan sassauta dubanta a kansa saboda yadda taji idanunsan sun mata nauyi. Kai ya daga mata alamun eh,sai khadeem da maleek suka fara tawa zuwa gaba kadan.

"Basai kunyi nisa ba........qarar amarya na kawo" Aisa ta fadi tana tattaro qarfin halinta idanunta akansu khadeem,don tana jin muddin suka bar gurin,muddin suka barta daga ita saishi ba lallai ta iya fadin komai. Tana jin tsaiwarsu zata taimaka,don tana hangen wani zuzzurfan sabo a tsakaninsu kamar shigen wanda ke tsakaninta da shehnaz da kuma akhnan din.

Qawataccen murmushi khadeem ya saki yana dubanta.

"Kamar a yarenku ance amarya bata laifi ai ko?" Yayi maganar da hausarsa shima da bata gama fita sosai ba. Murmushi aisa tayi,hausar tasu tana mata dadi sosai,yanayinsu kamar na sheikh haisam din,nutsuwa da kwarjini da wani irin kamewa a magana dake nuna zallar haiba.

"Wannan amaryar nata laifin yana da yawa,tun abincin safe bata sakecin komai ba.......kukanta bai yanke ba,babban abun zazzabi ne a jikinta,kuma zazzabinta yana da wahalar sha'ani,nan da nan yake mata illa,kowa ya kasa shan kanta......ko zaka taimaka......don Allah?" Ta fada tana duban fuskar haisam ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba.

"Subhanallah" Ya furta can qasan zuciyarsa da wani irin yanayi. Har saman ransa yaji ba dadi,ko ba komai amanace yanzu a hannunsa,haqqinta ya sauka daga kan kowa ya koma wuyansa. Cinsa shanta da lafiyarta gaba daya. Kome zataci yanzu a gidannan ko tasha a qa'ida haqqinsa ne......be kamata ace bai sake duba lamarinta tun dazu ba. Sultane baya nan,shi ya kamata koda ba igiyar aure a tsakaninsu ya kula da lamarinta tunda kusan haqqin kowa a masarautar yanxu a wuyansa yake.

"Ba komai,kije zanzo yanzu in sha Allah" Ya fada cikin kamala da kamewa.

"Na gode sosai da fahimta" Aisa ta fadi,mamakin sauqin kansa takeyi,a yadda take yawan kallonsa zaiyi wulaqanci izgili da wahalar sha'ani,yadda yake da yawan tsare gida haka take hasashen zai zama me wulaqanci ne kawai.

Takawa yayi zuwa ga inda su maleek ke tsaye,idanunsa akan khadeem dake bin aisa da kallo a sace. Dauke kansa yayi,bai masa magana ba bai kuma nuna masa ya gani ba,ya fidda wayarsa yana kiran number abdii.

Bugu daya ya dauka,ya saka wayar a kunne yana amsa gaisuwarsa.

"Ka yiwa hussam waya,ya saka maka kudi a canzaminsu zuwa CFA a darennan please da sauri.......adadi me yawa nake buqata,zan tura maka list na wasu abubuwa yanzu kaida salaana da sauran CFA din hannunka kayi amfani dasu a siyosu gaba daya"

"In sha Allah obbo" Abdii ya amsa masa a ladabce. Wayar ya tsinke yana sauke ajiyar zuciya,iska ya furzar a bakinsa yana sake lalubar wani number.

"Ka gayawa muminai maza da muminai mata suyi qanqan da ganinsu..." Ya furta a nutse,maganan ya jawo hankalin khadeem zuwa jikinsa,saiya kalli haisam din ya saki murmushi me sauti.

"Mr lowering gaze......wallahi nima inajin 'yar agadez ta kamani.....an samu wata buzuwar tayi wuf da zuciyata" Ya qarasa fada yana dora tafin hannunsa kan qirjinsa.

Da hanzari haisam ya daga kansa yana duban khadeem,maleek na gefe yana dariya amma ya dake kaman bai fuskanci komai ba.

Ci gaba yayi da kallon khadeem,idanun khadeem din kuma suna gaya masa ba gaskiyar abinda ke zuciyarsa khadeem din yake gaya masa. Su kuma wacce qaddara ce haka ta kirasu agadez daya bayan daya?. Anya wannan qaddarar zata tsaya a iya tona asirai na masu laifuffuka kuwa kadai?,kuma anya wannan qaddarar zata tsaya kawai akan aurensa da khadeeja?.

Kasa bawa khadeem amsa yayi,kawai sai ya maida wayarsa aljihu yana duban maleek.

"Dame dame ya kamata ace na siya?" Ba maleek kawai ba,hatta da khadeem sosai tambayar ta bashi dariya. Hade fuska yayi yana dubansu su dukka.

"Wai yaushe na zama abun wasanku ne guys?" Kai kawai maleek yake girgizawa.

Readers Also Read

More by Huguma