Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 55

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 55

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 55: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 55. "Idan ance ka shigo sha'anin bikin auren wani saika…

3,370 words

"Idan ance ka shigo sha'anin bikin auren wani saika doje.....kafi ganewa ka rayu kai kadai kaida tunaninka.....yanzu qananun siyayya daya dace ka fara yi ma baka sani ba?" Bude musu wadannan kwarjantattun idanun yayi yana binsu da kallo,sai kawai yaja musu siririn tsaki yana takawa zuwa hanyar da zata sadashi da shiyyarta ba tare daya sake cewa da kowa komai ba.

Sunsan bazai tsaya ba tunda ya tafi,bazai kuma sake sauraren komai daga bakin kowa ba a cikinsu a yanzu dai,don haka suka rabu dashi,saidai khadeem bai haqura ba

"Saida safe kenan?...." Ya jishi sarai,bai kuma juyo ba,ya kuma fahimci fes abinda suke nufi,sai ya saki qaramin miskilin murmushinnan nasa ba tare daya nuna alamun yaji ba.

Ba zasu taba yarda ba,ba kuma zasu gane ba......idanunsu ya rufe,fatansu kawai da burinsu auren ya juye zuwa irin wanda sukeso,abinda shi kuma ya riga ya sani bame yuwuwa bane. Ba wani muhalli ko gurbin soyayya ko daya a zuciyarsa ba,bazaiso abinda zaizo yana wahalar dashi ba,bazaiso abinda zai tafi ya barshi ba watarana.....

Babban kuskuren da zai tafka ma gaba daya a yanzu shine yaso yarinyar. Ya tabbatar za'a iya amfani da ita ta kowacce fuska......SONTA shine RAUNINSA da za'a iya cin galaba dashi. Don zuwa yanzu mammina kawai ya gani.....amma bai yarda cewa ITA DAYA bace......bai gamsu ita kadai ta shirya ta tsara ta kuma aiwatar ba.....yayi imani akwai SAURA akwai RAGOWA kuma akwai wasu,yayi alqawari kuma sai ya tattarasu gaba daya cikin da'ira guda sannan ya sanyasu su fallasawa duniya SU SU WAYE?.

*AKHNAN*

Da qyar ta bude idanunta ta kalli lokaci,abinda ya tabbatar mata wunin wannan ranar duka data tsara zata fita tasha iska,zata fita tahau doki don ta huce takaicinta,zata fita tayi abubuwa da zasu bawa zuciyarta nishadi a yau dukka sun rushe. Maimakon hakama baqinciki qunci da tashin hankali su suka zama makwafi.

Zazzabin dake cin naman jikinta tana jin kamar yana dab da gama tsotse jinin jikinta,ta fara jin wani yanayi da yake alamta mata yana dab da shiga hadari,don haka ta yunqura ta motsa ta miqe a daddafe.

Rigar jikinta data sanya tun dazun ta cire,wani abu da bata taba yiba tunda take. A qalla a rana tana wanka biyu har uku ma idan garin da zafi,sutura tana iya sauya kala uku zuwa hudu kawai sai taji ta dace da yanayinta.

Rigar ta zame daga bakin qofar da zata kaita closet dinta,ta zare brazier din jikinta duka ta zubesu a gurin,sannan ta qarasa ciki.

Rigar farko data fara tararwa a hanger ta cire,silk sleeping gown ce wadda duka duka tsahonta bai wuce gwiwoyinta ba,armless ce wannan ya sanya kana iya hangen gefe da gefan breast dinta. Wuyanta ma lace ne me v-shape,shima hakan yake bawa idanu daman ganin tudunsu da tsaiwarsu daga sama.

Da qyar ta jawo kanta zuwa saman gadon nata,ta koma rub da ciki ta kwanta,lulluba takeson yi amma duvet din ya mata wani irin nauyi,dole iyaka qugunta duvet din ya tsaya,ta dunqule tana sake sakin sabon kuka a hankali.

Daya bayan daya take wuce parlors dinta da setting room dinta. Bai kuma sha wahala ba ya gano dakin da take ciki cikin dakunan dasuke mallakinta ne gaba daya.

*MAMMINA*

"Daga Ethiopia......daga yanzu zuwa kowanne lokaci daddadan labaei zai riskeki....ki zamana cikin shiri" Saqon muryar data samu kenan daya sanyata sakin dariya cikin nishadi tana ajiye wayar gefe.

Ba abinda ke mata yawo irin yadda yaron yake neman zame mata qarfen qafa. Ba abinda yanzu yake damunta yake tashinta a barci irin al'amarin yaron. Abu mafi daga mata hankali shine sanin WAYESHI?......idan daga daya daga cikin masarautun ya fito tanason tasan wacece a ciki. Masarautar JIMMA zatafi zame mata suna mafi girman barazana ga kwanyarta.....masarautar GUMMA kuma zata zama ta biyu. Amma tayi imanin wannan MATAKIN shine zai bayyana mata SHIEKH HAISAM ne?.

Koma waye tana jin zaizo mata da sauqi muddin bashi bane,hakanan tayi imanin indai shine JININ IBRAHEEM bazai lamunci yin shuru ba.

Akhnan a yanzu itace gaba ta biyu da takeso ta saita,bai kamata ta bari al'amarin yayi nisa a haka ba,dole komai ya zamana akan sarrafawarta tsarinta juyawarta da kuma umarninta,wannan ne kadai zai bata dama da ikon isa ga muradanta.

Dole safeena ta fuskanci wannan uqubar a cikin kabarinta.....dole ta dandana dacin da yafi na mutuwa a gurinta.....dole ta sanyata ta nemi tsarin sake zama KISHIYARTA koda a aljanna ne.....dole ta sanyata fahimtar illa qwace abun ZAITUNA ko qwace abinda zaituna keso daga hannunta. Kai tsaye ta nemi alkyabbarta ta zura saboda iskar dake kadawa wadda ke bada tabbacin kwantaccen hadarin da zai samar da ruwan sama daga yanzu zuwa kowanne lokaci. Ta shirya tsaf,tayi tsaye kuma a gaban madubi tana kallon kanta da kuma salon kirarin data saba yiwa kanta da kanta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 95*

"Zaituna ikon Allah....zaituna iccen kabari......zaituna kabewar kan kabari......zaituna zamani goma sarki goma...zeenatu kuma me zamanai daban daban" Ta qarasa maganan tana sakewa kanta murmushi.

Tana marmari,tana muradi tana kuma burin ganin yadda fuskar shiekh haisam zata sauya a sanda yaji wani abu ya faru da mahaifinsa. Wani dariya ta kuma saki.....da gaske ta sani,tayi kuma imanin koda wanne irin suna ne laqabinsa a wannan gabar shuru bazai yuwu a tare dashi ba. Jinin OROMO jinin IBRAHEE suna da wani irin TSAIWA da JAJIRCEWA akan martabarsu.....ta yadda bazai qyale ba....dole!.

Shiga takun saqa da wasa irin wannan da jinin jimmawa ta sani ba abu bane me sauqi.......saidai kuma a wannan karon zata shige yaqi dasu da dukka QAWAZUCINTA. Zata maida martanin da abaya bata maidawa IBRAHEEM ba,har yayi zaton TA KASA har yayi zaton TA TSORATA ne ta janye....akwai HATSARI akwai WUYA amma dukka ita wadannan abubuwan basa sanyata janyewa daga yin dukkan abinda tayi niyya. Indai D'ANSA ya aiko mata zata tabbatar masa KUSKURE mafi girma da muni a tarihin rayuwarsa.

Sai kuma taja da baya da sauri daga gaban madubin sanda wani tunani yazo mata.

"Kada ya nemi kusanci ko kasancewa da ita!!" Maganan daya sanya zuciyarta wani irin bugawa da qarfin gaske. Sai kuma murmushi ya subuce mata data tuna WACECA AKHNAN. Tayi imanin akwai qura me kaurin gaske ga kowanne d'a namiji kafin ya samu daidaito cikin wannan zuciyar data sanya aka cika mata ita da izza da ganin fifikon saman kowacce halitta koma bayan ita. Hanya dayace take sanya rai wataqila ya samu sassucin isa gareta shine HANYAR YADDA DA DUKKA SHARUDDANTA na auren yarjejeniya.... Babban abinda yake sake jefata a duhu da take neman hanyar warwareshi shine. Me yasa bayan ya amince bai magana da ita ba?....a maimakon haka sai ya zabi yayi magana da sultane?. Tambayar da bata da amsarta kenan,amma ko yaya tasan zata iya samun haske ta bangaren sultane,don haka ta sanya takalmanta tana takowa zuwa waje tana kuma kiran sultane kai tsaye.

Koda ya daga wayar narke masa tayi sosai,harda guntun kukan munafuncinta kamar qaramar yarinya.

"Ta yaya za'a yimin haka?......ta yaya za'a shammaceni?,a lokaci irin wannan daya kamata ni UWA niya kamata ace na fara sani kafin kowa ya sani?". Murmushi ya saki,murmushin daya sake bawa mammina tabbacin zuciya da ruhinsa gaba dayansu qulle suke da madaukakin nishadi.

"Kina da rauni me yawa zaituna wani lokuta akan diyarki.....zamu iya gama magana na waiwayo naga kun hademin kai ke da diyarki". Maganan yadan tabata kadan ta fuskar RAUNI daya dangantata dashi. Tana tsoron kada yaci gaba da aiwatar da komai daya shafi akhnan bada saninta ba,kada ya maida akalar shawara cikin rayuwar akhnan ga safiyya. Ta wani fuskar kuma yabo da tabbaci gami da yaqinin data samu saiya mata dadi ainun,ya gama sakankancewa da soyayyar da takewa akhnan din.....tabbas wannan din WANI MAKAMI NE dazai mata wani sabon amfanin a gaba.

"Amma ranka ya dade.....banda zabar mata abokin rayuwa nagartacce.....abokin rayuwarma irin sheikh muhammad....Nagartaccen da kowanne ahali zasuyi alfaharin hada nasaba dashi"

"Ban sake jin alfahari da hakan ba sai dana sake samun tabbacin daga irin zuria'ar daya fito da jama'ar da suke kewaye dasu" Saura kadan qafarta ta zame daga stairs din da take saukowa,haka kawai gabanta ya fadi amma zuciyarta na mata zillo AKWAI.HASKE wataqila da zata sake samu game da rayuwarsa.

"Dan babban gida ne kenan kamar yadda muke fata?" Tayi tambayar zuciyarta cike da zullumi da addu'a. Kai sultane ya jinjina a hankali

"Iyayensa ba masu sarauta bane.....ba kuma attajirai bane.....amma dai.manyan mutanene masu tarin ilimi" Ajiyar zuciya ta sauke,har takai kunnen sultane ya kuma tambayeta.

"Nayi murna da naji samun tabbacin ilimin addininsa na gado ne tun daga gida,rayuwar diyarmu zata daidaita da yardar Allah,bari na qarasa zan hadaka da ita,amma na roqeka kalaman kwantar da hankali kawai a gareta" Ta fada tana narke murya da.langabar da kai. Murmushi me sauti sultane ya saki

"Har abada diyarki zakita zaba sama da kowa zaituna?"

"To ina da wata diyanne duk duniya bayan ita?" Ta fada a raunane. Tausayinta ne ya sauka a zuciyar sultane,ka rayu baka taba haihuwa ba abune me ciwo,tabbas inda yana da halin siyawa zaituna haihuwa daya siya mata,don ta kowanne fuska ta cancanta.

"Tunda ina da khadeeja kuma ai ta isarmin,sai kuma inda qarfina ya qare" Ta rufe maganan da kalar kalaman da kullum suke qara mata girma da soyayya a zuciyar sultane din. Da kuma wadannan mayaudaran kalaman ta katse kiran,tana sake jin ta samu sassaucin rudanin da take ciki. Tayi imanin inda haisam jini ne na sarauta dole sultane zaiga alamu,zai bayyana ma,ta tabbatar da hannunsa sultane bazai bada auren akhnan baida wata makama me qarfi akan nasaba da alaqar sheikh haisam ba,duk kuwa yadda yaso ga hada auren. Ta samu relief sosai.....wataqila masu nata binciken ne basu gano daidai ba.....idanma sun gano din,daren yau zuwa safiyar gobe zasu bata alarm.

*BIRRA*

Su dukka biyar din tayi shawarar su shiga su lallashi uwar dakin nasu ko zata samu ta sanya ko ruwan zafi ne a cikinta. Suka shirya komai suka kuma wuce kai tsaye zuwa dakin.

A sannan kukanta ya zama mara sauti sai digar ruwan hawaye kawai. Jikinsu a sanyaye suka jere komai sannan suka zauna daga qasan gadon.

"Muna neman afuwarki a madadinmu dama kowa dake cikin gidan nan.....cikin nuna damuwa da yanayin da kike ciki,ki taimaka koda ruwan zafi kofi daya kisha saboda lafiyarki" Idanunta kawai ta lumshe tana sake jin yadda azabar zazzabin yake dukan qasusuwanta,ga wani irin hautsinewa da cikinta yayi guri daya.

Har sun fidda rai da zata amsa sai sukaga ta motsa. Birra ta tashi da sauri tana tayata yaye duvet din,sannan suka taimaka mata ta zauna sosai ta jingina bayanta da fuskar gadon tana share damshin hawayen saman fuskarta.

Tea foldable table ta bude mata daga gefanta,ta kuma zaunar dashi saman gadon sosai,ta hada tea din ta dora mata akai ta koma tana tattara kayan,duk da akwai sauran farfesun danyan kifi daya wadata da spices,amma ba zata mata tayinsa ba yanzu tukunna har sai an samu ta shanye tea din,daidai sanda aka murda handle din qofar dakin.

Qamshinsa shine abu na farko daya soma musu sallama. Yana sanye da Moroccan thobe olive green me kyau da daukan idanu. Sallama yayi da tattausan nutsatsiyar muryarsa. Qasa dukkaninsu sukayi da kansu,kowacce tana qoqarin kame kanta da jikinta,kafin su fara miqewa a hankali suna dosar qofar fita a dakin.

Cikin qasa da second biyar dakin ya zamana shuru,kamar ba'a wani me numfashi daya taba wanzuwa cikin dakin.

Wani irin nauyi takeji cikin qirjinta,zuciyarta na matsewa guri daya,sanda ta tabbatar shi da ita yanzu suna musayar numfashi ne iri daya...qarqashin roofing daya.....cikin tsakiyar dakinta da take ganin baida hurumin shiga mata.

Dakinta sirrinta ne......sirrinta guda dayan da bai kamata ya keta alfarmarsa ya shigo mata ba,tunda dai batajin matsayinsa yakai ya wanzu a qarshen sirrinta. Zuciyarta ke wani irin bugawa da kyau,tana jin yadda qamshinsa ya cika dakin gaba daya tamkar tun asali a nan ake ajiye turaren. Batasan wanne irin bugu zuciyarta keyi ba a duk sanda zataji qamshin,ko hakan yana da nasaba da ranar data fara jin irin qamshin ne a hippodrome?. Ko wannan lokacin baqincikin take tunawa?,shi yasa bugun zuciyarta yake banbamta dana kowanne lokaci?.

Ko sau daya bai dubi sashen da take zaune ba,sai yaci gaba da takawa abinsa yana nufar windows din dakin dukka yana budesu don samun wadatacciyar fresh air bawai ta ac din da suka balbalawa dakin ba. A asalinsa mutum ne shi me son natural air,shi yasa yake yawaita shuke shuke a duk gurbin da yake rayuwa,yake matuqar son yawo kuma cikin guraren da suke da yawaitar tsirrai.

"Me ya dauki kansa ne?,waye shi?!" Ta tambayi kanta tan ajin zuciyarta na mata zugi na yadda yake tafiya cikin dakin hankalinsa kwance yana bude mata curtains ba tare da izininta ba cikin wannan izzar tasa data tsana tamkar ma shine mamallakin dakin ba ita ba.

Bakin qofa ya sake komawa,ya sanya hannu yana daidaita hasken dakin,yana kuma daukan remote na Ac da fitilar tsakiyar dakin don ya daidaita sanyi da hasken gaba daya.

Wani irin bugawa zuciyarta takeyi kamar zata fita daga qirjinta,ba zata jurewa zama dashi a daki daya ba......a yanayin da ba kowa daga ita saishi,ba zata juri shaqar iska guda daya dashi ba......wannan tunanin bai barta ta fahimci yadda jikinta yake rawa ba......wannan tunanin bai barta ta fahimci zazzabin jikinta yakai iyaka ba.....wannan tunanin still dai ya sake mantar da ita kalar suturar dake jikinta,sai kawai ta zuro qafafunta qasa ta miqe harda saurinta,saurin daya sanya kanta wani bugawa har sai data dafeshi kadan ta sake miqewa tsaye tana takawa da burin kaiwa qofa ta fice ta bashi guri.

Sosai silk rigan ya lafe a jikinta,sosai ya nuna dukiyar fulaninta da mazaunin kowanne da kuma space din dake tsakaninsu,shape dinsu ya fita sosai kamar yadda qugunta ya bude sosai ta cikin rigar dake mannuwa da fatarta. Sumarta me santsin nan ta warwatsu daga kafadarta zuwa gadon bayanta,tana dafe da gefan kanta da hannunta guda daya tana kuma nufar qofar da ayau take ganin tazarar dake tsakanin bed dinta zuwa bakin qofar,wanda bata taba ganinsa ba sai yau.

Baiji takunta ba saboda a hankali lallausan tafin qafarta yake sauka saman marbles din dakin me wani irin santsi da daukar idanu,don haka sanda ya kammala saisaita komai sai ya waiwayo a nutse da nufin komawa ainihin cikin dakin.

Kyakkyawan gani yayi,don tana takowa ne dab dashi da zummar giftashi ta fice ba tare data kalleshi ba. Dukka idanunsa suka zube akan fuskarta,kafin wani abu me qarfi ya fusgeshi zuwa ga cikakkun dukiyar fulaninta.

Numfashinsa ne yaji kamar zai dauke daga hunhunsa. Zuciyarsa ta wani irin bugawa data tilasta masa lumshe idanun nasa wanda kafin ya budesu sun rusuna qwarai sun kuma sauya launi.

"Subhanallah" Ya furta a hankali can qasan ransa yana motsa kyawawan labban nan nasa masu daukan hankali. Sanda ya bude idanun nasa ta gotashi,ya kuma fahimci waje takeson fita cikin qasa da second biyar.

Baisan yadda akayi ba.....baisan me ya saukar masa da jin wani mummunan tashin hankali ba daya ingizashi riqo hannunta da sauri,sannan yayi taku biyu ya isa gefanta. Dukka idanunsan nan masu wani irin kwarjini ya zube mata,duk da cewa sumar kanta me santsi ta rufe wani sashe na fuskarta.

"Ina zaki?" Ya fada da salon tambayar dake nuna wani irin zafi da zurfin muryarsa,girarsa tana tattarewa guri daya yana jin wani abu me zafi a qirjinsa. Sama sama takejin abinda yake fadi,don jiri takeji sosai,burinta kawai ya saketa ta qarasa parlor ta kwanta,amma hakan bai hanata bude masa manyan fararen blue eyes dinta ba,sannan ta zame hannunta daga cikin nasa da dan guntun qarfin da take dashi

"Ka sakeni.......Ne me touchez plus jamais(don't touch me again)" Ta fadi da harshen faransanci,duk da tana ji a jikinta ba lallai yana jin abinda take fadi ba.

Wani irin kallo yake watsa mata,yana jin wani abu me zafi yana sauka saman zuciyarsa. Ya qyaleta ta fita?,a haka?,da wannan kayan a jikinta?,fitarta na nufin kowa ya kalleta?,fitarta na nufin kowa yana da damar ganin surar jikinta? Wataqila ma wani cikin hadimai ya shigo isar da aike ko kawo wani saqo?.

Bai jira ba,bai kuma bawa kwanyarsa daman yin tunani na biyu ba ya sanya hannunsa dukka biyun ya rabata cak da qasa.

Wani abune da yazo mata a mugun bazatar da bata taba kawota ba. Bata taba hasashe ko tunanin faruwar hakan ba,shi yasa tayi wani irin mugun kaduwa ga tunaninta faduwa ce bawai daukarta ba,wannan ya sanyata cukuikuyeshi gaba daya numfashinta yana shirin daukewa.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 96*

Jikinsa ta shige sosai kamar wadda ke neman mafaka sanda wani abu na tsoro ya biyota,wannan ya bawa qirjinsa daman haduwa da nata da wani irin yanayin da sai daya sanya yaji kamar shocking aka jona masa. Hakan bai sanya yayi sako sako da ita ba,bai bata dama ba har sai daya isa saman gadon ya kuma duqa yana sauketa.

Yadda tayi zullon kubuta daga hannunsa ya sanya saura kadan ta sanyashi ya fada saman gadon,amma yaja ya turje ya tsaya kyam saman qafafunsa yana zube hannunsa a aljihun Moroccan thobe din jikinsa yana fidda wata irin iska daga bakinsa.

Wani irin abu yakeji yana yawo cikin tafukan hannayensa yana bin duk wasu hanyoyin jini zuwa gangar jikinsa. Wani irin yanayi daya kusa kamanceceniya da yanayin dazu,saidai har yaso yafi yanayin dazu qarfi da qoqarin d'ai d'aita masa tunani.

Tsaiwar kimanin mintina biyar yayi saman kanta kafin ya samu ya daidaita numfashinsa da nutsuwarsa. Ya hade ranshi tsaf yana ware idanunsa kadan a kanta. Tana qudundune cikin duvet tunda ya sauketa tana jin yadda kanta ke sara mata. Mamaki kadan ya kamashi jin sautin kuka can qasa yana futa daga boyayyar fuskarta. Bai taba tunani ko zaton zata zama me saurin kuka har irin haka ba......duk wannan taurin kan?,duk wannan musu da kafiyar gami da gaddamewar?.

Hannayensa ya fidda duka biyun yana murxasu a hankali. Zafin da yaji cikin jikinta a dazun shine abinda ya fara fusgar hankalinsa. Dole akwai buqatar ta rage zafin jikin,idan ba haka ba komai yana iya faruwa. Amma ya fahimci da wannan taurin kan nata da kafiyar nata dole sai yazo mata da zafi,cikin lokaci qalilan,wasu alaqoqi da sukayi daga nesa,jin halayenta daga mabanbantan bakuna ya fahimci zuma ce ita sai da wuta.

Takawa ya sakeyi yana komawa bakin qofar dakin,ya murza handle din ya budesa,sanda wata irin iska me dadi dake bushawara ga mutane na tahowar ruwan sama ta fara busawa.

Komawa yayi ya duba sashen da yasa ana ajiyar waya a kowanne daki na gidan,ya danna yayi kira ga sassan hadimanta.

Birra ce ta daga kamar ko yaushe

"Shigo" Ya bata umarni a taqaice yana ajiye wayar.

Kamar tana bakin qofar sai gata ta iso,ya fara nufar qofar fita yana bata umarni.

"Ki hada mata ruwa mara zafi tayi wanka yanzun nan.....kada ku haura mintuna biyar,idan bata tashi ba ki sanarmin kawai"

"In sha Allah" Ta fada da matuqar girmamawa,bata kuma daga kanta ba har sai daya fice a dakin.

"Jikinki yayi zafi da yawa,kiyi haquri ki watsa ruwa.....wataqila yace kiyi wankanne sabo....."

"Ya isheni haka birra!" Akhnan ta fadi da qarfin hali duk da yadda muryarta da labbanta ke rawa. Bata qaunar qara maganarsa ballantana wanzuwarsa a gurin,don haka ta miqe da taimakon birra ta shige toilet din.

Readers Also Read

More by Huguma