L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 56
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 56: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 56. Zama tayi a gefan tafkeken bath tub dinta,har birra ta…
3,371 words
Zama tayi a gefan tafkeken bath tub dinta,har birra ta gama hada mata ruwan,kanta a qasa tana jin yadda hawayenta yake diga. Saida birra takai qofa sannan tace mata.
"Ki ciremin kaya masu kauri ki kawominsu nan,ki ajiyemin,ki kuma kullemin qofata idan kin fita......ban yarda a bawa kowa izinin sake shigomin ba.....ko wanene" Ta fada da mugun bacin rai tana miqewa. Cikin girmamawa birra ta amsa mata,ta kuma duba closet dinta ta fitar mata da irin kayan da tace tana so din. A sashen shiryawa bayan gama wanka na tafkeken bathroom din nata ta ajiye mata,ta juya tana fita don cika umarninta.
Saidai sanda take sako qafarta cikin dakin baccin,daidai lokacin yake shigowa dakin a karo na biyu. Wayace maqale a kunnensa,da alama kira yake amsawa,yayin da hannunsa daya yake riqe da wata madaidaiciyar jaka me jikin kwali.
Qasa birra tayi da kanta,ta kuma tsaya gefe guda har ya kammala shigowa,sannan ta juya da hanzarinta tana fita a dakin.
"Wai Allah na,wannan bawan Allah badai kwarjini ba" Ta fada qasa qasa bayan ta samu ta fito din tana raba idanu,sai kuma murmushi ya qwace mata. Ita dai har ga Allah wani dadi takeji,dadi takeji sosai idan taga uwar gijiyartata tare dashi. Duk da ta fuskanci tsananin taurin kan nan nata take take taken gwada masa,to amma ta sani yanayinsa sam baiyi kama da yanayin wanda zai dauki wannan ba.
Da lallausan towel din ta tsane jikinta,ko tarin creams din da aka shirya a gurin kamar wani qaramin shago bata kalli ko daya daga cikinsu ba,ta zanya riga da wandon masu kauri gami da tsananin taushi. Ta lumshe idanu tana jin yadda sama ta fara bada qarar rugugin hadari. Cikin ranta take tambayar kanta ya zatayi yau ta kwana ita daya?. Duk tsanani idan ana ruwa.....duk yadda sukai fada dasu shehnaz ko aisa sai tasan yadda aka shirya. Ko ita ta bisu dakinsu,ko tasan yadda zatayi suzo a kwana tare. A yau kam batajin zata nema,koda kuwa tsoro zai kasheta,don bata ma tsara bude dakinta ba kwata kwata har nan da awa ashirin da hudu. Kai hasalima daga aisa din har shehnaz ba wanda batajin haushinsa.
Saidai kuma tana sanya qafarta cikin dakin bayan ta dauke qafafunta daga saman water proof door mat din turarensa ya ajiye mata tabbacin yana dakin.
Tsaye yake yana fidda wasu abubuwa daga madaidaiciyar jakar kwalin daya ajiye saman bedside drawer dinta da bata gama gane meye da meye ba. Wani irin bugawa taji zuciyarta tayi,idanunta suka sauka kan dokin wuyansa dake kwance da wani sashe na sumar kansa me santsi. Hasken fitilar daya dan sake qarota ya haskeshi fes cikin Olive color Moroccan thobe din jikinsa.
Ta karanci waya yakeyi,amma abun mamakin ba'a jin abinda yake fadi sam. Izzarce da girman kan nan nasa abinda zuciyarta ta gaya mata kenan,tayi taku biyu kamar zata koma toilet din,amma wata zuciyar ta gaya mata DON ME?,keda dakinki?,ashema kin damu dashi.....ya isama ashe yakai kenan. Wannan tunanin ya sanyata ci gaba da takowa tana dauke kanta daga gareshi,tana fatan kafin ya waiwayo ya kalleta ta isa ga gadonta ta nade cikin duvet.
Dukka addu'arta ba wadda taci,don tana isowa tsakiyar dakin ya waiwayo da wannan shimfidaddiyar nutsuwar yana zube idanunsa a kanta.
Maida idanun nasa yayi ya lumshesu kana ya ciresu daga kanta. Butter color din sleep wear ne a jikinta masu tsananin laushi da bonnet cap a kanta data cusa gashinta gaba daya,amma hakan bai hana wani daga ciki bullutsowa ta gaban goshinta da qeyarta ba. Wani irin sassanyan kyau kayan sukayi mata,sun hadu da ramar da tayi iya yau kadai,da ramar da tayi kwanakin da suka shude duka sun sake fidda zallar quruciyarta
Wannan kayan da sauqi,ba wani abu nata daya fito don long sleeve ne rigan,amma duk da haka wannan faffadan qugun sai daya bayyana kansa da kansa ta cikin wandon kayan.
"Zan kira" Ya fada kalar hausar nan tasa da take kama da wani yaren daban ba hausa ba yana sauke wayar a kunnensa. Tsaki yaja qasa qasa,kwanyarsa na maido masa da hoton fuskarta daya kalla a yanzu. Qiyasin shekarunta ya tafi yi sanda yake latse wayar gami da maidata silent. A iya abinda nazarinsa da qididdigar lissafinsa yake bashi,ba zata haura sa'ar Aanani ba,bama rumaisa ba.
"Sai rashin kunya da zallar girman kai" Ya fada can qasan zuciyarsa. Kwatanta shekarunta dana Aanani qanwarsa na kusan uku ya sanya ya sakeji a jikinsa kawai kaman Aanani dinne a gabansa. Sai ya dauki jakar kai tsaye yana nufar gadon,gadon da tuni ta haura tana kwashe qafafunta zuwa sama. Ranta a quntace tana jin wani irin dan banzan haushi yana cikata.
Koda su shehnaz akwai sanda take tafiya abinta ta kwana ita daya idan 'yan halin nata suka motsa. A sanda sam batason damuwa ko takura,a sanda take buqatar kadaici takan so zama shuru kawai......saidai a yanzun shi gashi cikin al'amuranta,wani BAQO cikin rayuwarta gaba daya,wanda sam ba wani abu da takejin ya hadata dashi.
Tanata qoqarin gyara hannun rigarta dana wandonta tana karance dashi. Cup din da birr ta hada mata tea ya matsar. Ya tsiyaya wani ruwan zafi sosai da batasan dashi ba,ya bude zuma ya zuba,ya kuma bare dabino ya zare qwallonsa ya dora duka saman qaramin madaidaicin tray.
Zuwa sannan ta maida qafafunta saman gadon,ta kuma jawo duvet tana shirin lullube. Caraf taji an kama duvet din an riqe tamau,a hankali ta sauke idanunta saman hannunsa dake riqe d duvet din. Zara zaran yatsuntsa sun shige sosai jikinsa wanda dukka alamu suka nuna mata ba qaramin riqo ya masa ba,don tana ganin lafiyayyun jijiyoyin hannun nasa dake lullube qasan lallausar gargasarsa. Tasan koda wasa bata da qarfin da zata qwata,saita daga idanunta a hankali da xummar zube masa kallon gargadi,saidai kuma inaaaa......
Kallo daya tak ya bata daya qarasa zare dukkan wata guntuwar karsashi da take dashi,kallo Dayan daya hanata sakewa har ta kalli qwayar idanuwansa.... Kallo daya da taji ya mata wani irin girma. Bai magana ba bai kuma saki duvet din ba,yaci gaba da tsareta da ido ne yana hukuntata da idanuwan nan dake dauke da wani maganadisu,har a hankali ta zare yatsunta daga jikinsu,saiya tattara duvet din ya tureshi gefe,ya kuma maida nini foldable table din ya maye gurbinsa tsakanin cinyoyinta.
"Dauki kisha" Ya fadi yana tsare gida da kyau cikin siga ta umarni irin nakai tsaye. Idanunta ta lumshe tana jin wani irin bacin rai yana taso mata. Taja numfashi me zurfi sannan ta sauke tana jin wani tarin tawagar hawaye suna yo gangami don isowa ga idanunta. Shanyesu tayi da wani irin taurin kai da kafiya. Ba zata taba bashi daman ganin hawayenta a karo na biyu ba.......kome da yakeyi yanzu kuma na lokaci ne,rashin lafiyarta da rashin qwarin jikinta shine sila......amma daga yau.....daga wannan ranar taci alwashin bazai sake samun kusanci da rayuwarta haka ba.
"Bai kamata kisha wannan yanzu ba......amma gangar jikinki tana buqatarki a raye" Ya fadi cikin I don't care manner ba tare daya dubeta ba. Ya fara jin komai so boring.......sultane da morsa safiyya kawai yake hangowa suke sanyawa yake sake bawa kansa qarfin gwiwa. Yanaso ya kula da amanar sultane yadda ya dace,yanason sultane ya tabbatar da kansa da kansa cewa ya kula da kowa da komai kamar yadda ya dace ace yayi.
Maganarsa sai tazo mata a hagunce......bacin ranta ya sake motsuwa,hawayen da take riqewa suka samu hanyar fita kansu tsaye,ba wani shamaki ba kuma wani abu da zai taresu. Fuskarta takeson boyewa amma ba komai kusa da ita,wannan ya sanya tayi amfani da bayan tafukan hannayenta ta lullube idanunta irin yadda yaro keyi a sanda ya fashe da kuka.
Qaramar stool ya jawo hankali kwance zuwa gabanta. Zaman nan nasa yayi wanda ya zame masa jiki,zaman dake qara masa haiba,yake kuma zake nuna SARAUTA dake cikin jininsa.
Kamar kowanne kuka na diya Mace,wannan ma sai yaji yana sauka masa saman zuciya. Sai yaji yana masa wani iri ba dadi daga can lokon zuciyarsa......sai kuma ya dinga jin wani irin weakness da bacin rai suna ratsashi.
Wai dukka wannan kukan saboda kawai ta gani ta samu tabbacin shi muhamamd haisam ya aureta ne?. Ta dauka komai na gaske ne?,ta dauka komai zai tabbata ne?,ta dauka zata zama kamar kowacce matar aure ne?.
Hakan mazan da suka auri matan da basa sonsu suke ji a ransu?. Ya lumshe idanunsa yana sake budewa a kanta,can cikin ransa yana sake bawa kansa alwashi da tabbacin har abada bazai taba yarda ba,bazai taba sakewa ya auri macen da bata sonshi ba.
Dama can tsarinsa ne......zabinsa ne ya auri macen da soyayyarsa a zuciyarta ya haura wanda shi yake mata.....a yanzun ya sake samun yaqini da tsaiwa saman ra'ayinsa dari bisa dari.
*MAMMINA*
Cikin taku daya daya ta dinga ratsa falukan akhnan tana kuma mamakin qauracewar hadimai haka tunda wuri,don duka duka a sannan data duba agogo tara ne da mintuna na dare. Kusan ma kowanne living room da sitting room qwayayensu a kashe yake,abun yadan bata mamaki,amma saita alaqanta hakan da yanayin da akhnan din take ciki.
Parlor na dab da qarshe wanda daga shi sai sassan stairs din akhnan da down stairs bedrooms dinta ta iske birra.
Burners din dake kowacce corner da kusurwa na falukan take kashewa. Wani sirri kenan na daban da sassan akhnan din ya kebanta dashi. TAMBARIN QAMSHI,komai na sashenta zaka samu tambarinsa kenan,da wannan kadai ya isa ka gane ababen sassan gimbiya akhnan.
"Dukka ina sauran hadimai da suka tafi haka da wuri?,waye ya sallamesu bayan nasan zai wahala zuwa yanzu biftu tayi bacci?" Dan rusunar da kanta tayi.
"Eh bata jin dadi ne......"
"Kuma kuka barta ita kadai harda tafiya da wuri?" Mammina ta fada cikin hargagi tana fiddawa birra idanuwanta.
"Ai tana tare da sheikh muhammad" Birra ta amsa mata a ladabce. Wani irin abu mammina din taji kamar an doka mata tsakiyar kanta,tana tare da haisam?......har sun samu kebewa?,akan wanne dalili?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 97*
"Tun yaushe ya iso?" Ta tambaya tana jin qirjinta yana wani irin bugawa.
"Tun bayan sallar isha". Ta amsa mata. A sace mammina din ta kalli agogo,aqalla awa guda kenan?.
"Shikenan.......zan zauna a nan,ki shaida musu na qaraso ina jira" Qasa birra ta sakeyi da kanta sanda mammina ke neman gurin zama. Tanaso ta gaya mata inda zai yuwu mafi alkhairi shine ta koma,don bataga alamun fitowarsa yanzun ba. Banda ma rigima irin ta giwa,ta yaya sabon aure irin wannan a irin wannan lokaci ki buqaci shiga shiyyarsu?.
"Kamar dai ma saida safe fa ranki ya dade" Wani kallo ta watsawa birra tana kallonta.
"Kamar yaya kenan?"
"Ya kulle qofar daga ciki ranki ya dade" Birra ta amsa mata a ladabce.
Wani irin fushi ne ya taso mata gauraye da tashin hankali. Har tana iya jin yadda qirjinta yake bugawa.
Me ya kaishi wanzuwa da akhnan din a ranakun da ko bisa al'ada ba'a bawa namiji daman kadaicewa da matarsa ba. Don dai kawai batajin dadi?,ita akhnan din ita ta bashi fuska?,har ta warware daga suman qiyayyar data masa a dazu?.
"Tun yaushe ya shiga?" Ta sake tambaya gumi yana tsatstsafo mata,ta manta da cewa birran ta bata amsa a dazu.
"Bayan sallar isha'i" Shuru kawai tayi tana jin wuta tana dauke mata gaba daya. Birra taci gaba da tsaiwa tana jiran umarninta.
Mintina kusan biyu suka shude dukkaninsu suna tsaye a haka,mamaki fal zuciyar mammina naci gaba da zamansa a ciki,zuciya kuma tana mata kalar saqe saqe daban daban. Qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu dauketa ba,sai kawai ta koma da baya ta zauna saman kujera.
"Jeki....zan jirayesu" Ta fadawa birra. Rusunawa birra tayi tana yin gaba,zuciyarta fal da mamaki,wannan sanya idanun da bin diddiqin har ina?,mema ya kawo irin wannan sanya idanun na giwa?,mutum da matarsa?,auren sunnar da kowa ya tabbatar an daurashi?,a muhallin da yafi kowanne tsarki da daraja duk duniya.
*HAISAM*
Ci gaba yayi kawai da sauraren kukan da take rairawa ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ko hanata ba kwata kwata. Yanaso tayi yadda zai isheta,ta yadda idan ta gama din ba zata sake damun kanta da nasa kunnuwan ba da qirqirarrun hawaye ba. Bai zaci fara hawayenta da ganin kukanta haka da wuri ba,bai dauka tana da rauni ta wannan bangaren ba sam. Taurin kanta izzarta dama kafiyarta dukka basuyi daidai da raunin da yake gani yanzu a tare da ita ba.
Idanunsa ya lumshe sannan ya sake zubesu saman tafukan hannunta dake a bude saboda idanunta data rufe da bayan hannunta.
"Ya isa......ya isa" Ya fada da wani irin coolness. Abinda ya bata mamaki yadda ta samu kukan yana zuqewa a hankali a hankali,kafin ya tsaya cak tamkar suma idanun nata suna bin umarnin haisam dinne.
"Dauki kisha.....idan kukan yana burgeki ne daga baya kina iya ci gaba dayi" Ya fadi yana sauke idanunsa akan mug din dake tururin zafi.
Wani abu ya matse a qirjinta,wato ko ta mutu ko tayi rai duka wannan shi ba damuwarsa bane?. Ya shigo mata daki,ya mata bake bake kuma yana gaya mata duk maganan da yaha dama,yana bata umarni bisa zaton tabi umarninsa,wanne irin mutum ne shi me shegen jin kan tsiya da wulaqanta mutane?.
To amma a wannan gabar yadda takejin hanjin cikinta suna murdewa guri guda kamar zasu tsinke,ba wani abu da tafi buqata irin ruwan zafin.
Bakinta da jikinta dukka basu da wani energy da zata iya nuna masa kuskuren shiga sharafinta da yayi.......so take ko harara ta watsa masa,amma kuma sanda ta daga idanunta a kansa,qwayar idanunsu suka gauraya sai taji kaman tana neman daburcewa,sai kawai ta zarce da daukan cup din duk daba abinda tayi niyyar yi ba kenan. Kallon cikin cup din take,tana tunanin wanne kalar tea ne wannan,kuma an hadashi ba madara sai honey?. Bata taba sha ba,amma hakanan takai bakinta tunda ta riga ta dauka din,kada ya rainata,ya dauka bada niyyar sha ba dama ta dauka.
Tsam ya miqe daga saman stool din sanda yaga ta fara sipping tea din. Idanunta ta lumshe sosai ba tare kuma data budesu ba. Duk da bakinta ba taste,zazzabin daya dan sauka yakeson ya dawo mata,amma hakan bai hanata jin wani dadi ya ratsa harshenta ba. Kurba daya tayi niyya,amma sai gashi yana sha kadan kadan har sai data kusa shanye duka cup din.
Qwayar idonta ta sauke cikin cup din,tana jin wani kunya yana saukar mata ganin yadda ta kusa tashi dashi gaba daya,a hankali ta ajiye saman foldable table din tana sauke idanunta daga kanshi sanda yake takowa zuwa bakin gadon,hannunsa riqe da wani abu da batasan meye ba don bata kalleshi ba.
Ajiye drip din da cannula din daya dauko yayi daga gefe,ya sunkuya a hankali yana nade foldable table din da yake saman cinyoyinta.
Wani irin faduwa gabanta yayi,zuciyarta ta soma qara adadin bugun da takeyi,yayi mata kusa da yawa.....kusar da har tana iya jin hucin numfashinsa dake gauraye da wannan mayen turaren daya zame mata jarrabi. A duk sanda zataji scent din saita samu kanta da wata irin kasala......a duk sanda zata shaqi scent din sai taji wani emotions daga can qasan zuciyarta wanda batasan asalinsa ba.....a duk sanda zataji qamshin sai taji tasirin wani abu qasan zuciyarta me kama da nishadi wanda batasan meye yake kawoshi ba.
A nutse yake nade table din,ba tare daya daga kai ya dubeta ba. Idan yace zaiyi hakan tazarar inches ne kawai zai zaman tsakanin fuskokinsu. Tanason masa wani abu da zai sanya ya janye daga kusancin daya haifar tsakaninsu.....amma tana jin koda ta buda baki zatayi magana bugun da zuciyarta takeyi ba zata bari kalaman bakinta su fita daidai ba. A hankali taji wani irin sanyi yana ratsa qasusuwanta,wanzuwarsu a hakan sai takejin kamar ba mintuna ya dauka ba,kamar shekaru ya dauka a duqe yana maida table din yadda yake. Sanda ya kammala ya miqe a nutse yana ajiyeshi a qasa,ji tayi kamar wani qatoton fili ya bayar na tazara a tsakaninsu,saidai bata ajjiye wannan numfashin ba ta tsinci husky voice dinsa yana furta.
"Gyara" Idanunta nan da suka qara wani jeme jeme saboda kuka ta daga tana dubanshi dasu. Ta lura tunda ya dawo dakin bai kalleta koda sau daya ba,wannan girman kan da jin ya wuce ajin ya kalleta ne yake motsa masa?. Tambayar da batasan amsarta ba,saidai maida dubanta ga allura da cannula harma da drip din hannunsa ya tashi hankalinta.
Idan a duniya akwai abar data tsana take sanyawa tsigar jikinta tana zubawa lokaci guda itace cannula,tana iya haqura da ciwo duk nauyinsa da zurfinsa muddin akwai allura a lamarin maganinsa.
Zubawa allurar idanu tayi,bataso ya rainata da yawa,bataso ya gane rauninta,rainin zai yawa idan ta bashi hannunta don mata allura,hakanan rainin zai yawa idan ya fuskanci tsoron allura takeyi. Batajin zata yarda da wannan mulkin kama karyar da yake mata......ya isa haka,ya tilastata tayi abubuwa da yawan da ko shine sultane sai haka,a wannan lokacin zata gwada masa har yanzu AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD take. Ya samu access da ita da yawa dalili dame?. Ya jefata a qunci amma kuma yanayin kamar baisan komai ba?. Dama akwai wata manufa a ransa game da ita?.
Dukkaninsu tunaninsu ya yanke sanda wayarsa ta dauki wani daddadan sautin kukan tsuntsaye. Wani abu ya sauka a ranta tare da fitar sautin. Kukan tsuntsaye na daya daga cikin abubuwan da takeso sosai,don haka kusan komai nata da zai bada ringing da notifications duka shine.
Ganin sunan sultane yana yawo saman video call din ya sanyashi takawa a nutse saman stool din daya tashi ya zube ruwan da alluran gaba daya,sannan ya koma saman dressing table ya zauna a nutse yana daga kiran.
Fuskar sultane da muryarsa gaba daya ta bayyana cikin wayar da dakin,muryar daya sanya akhnan tattaro dukka nutsuwarta ta aza cikin ranta,wani bangaren na zuciyarta kuma wani dadi taji. Zataga yadda zai kalli sultane ya fadi masa yana daki daya da diyarsa......zataga da wanne idanu zaiwa sultane bayanin dalilin zamansa a dakinta a daren nan.
Wani irin murmushi ne yake fita daga fuskar sultane din,wanda yake zaune cikin haramin makka. Tun daga wadancan awannin da suka shude zuwa yanzu zuciyarsa ke cikin wani kwanciyar rai da walwala gami da nutsuwar da bai taba jin irinta ba. Yaso ya daure zuwa gobe ya kira akhnan da haisam don ya sake tabbatar da lafiyar komai amma ya gaza daurewa,ya kikkira akhnan bai sameta ba,don haka ya maida kiran ga haisam,sai gashi cikin sa'a ya sameshi.
Daga inda ta cure ta ware idanunta sosai akan fuskarsa. Kyawawan idanunsa da lips dinsa da hasken screen ya sake fidda color dinsu da kyansu sun bayyana tarwai kamar glass. Ba murmushi bane saman fuskarsa......amma akwai wani sakakken yanayi daya qara masa wani irin ajiyayyen kyau. Madaidaitan Lips dinsa suna motsawa a hankali wadanda suke ajiye tsakanin gashin qasan habarsa dana saman lips din nasa da suka sake qawata kyau da darajar fuskarsa na cikakken namiji. An ornament for a man.....he has completeness. Wasu words guda biyu suka fado a kanta,tana tuna wani lokaci a French,sanda ta shiga cin breakfast a kitchen nasu na school,ta zauna gefan wasu 'yammata da suketa hira a tsakaninsu,qarshe dayar ke nunawa dayar hoton saurayinta. Yana da gemu da cikakken saje,kuma da kalmomin data yabeshi dasu kenan.
Idanunta ta janye a kanshi,tana jan qaramin tsaki. Haushi yana qara cikata,yana kuma sake tunzura zazaabin da takeji a jikinta. Don yana da gemu sai me?,don yana da saje meye damuwarta?,wanne kyau zai nunawa sauran maza?,tambayar data sake sanyata maida idanunta a kansa kenan da zummar tantance tambayar.
Cikin girmama juna suka gaisa,wani abun mamaki shine yadda haisam din a wannan lokaci yaji nauyi da girman sultane ya dadu a ransa. Wannan transparency din da yakeji a baya game dashi a yanzun wani abu ya sauyashi.
"Inata kiran khadeejatu amna na kasa samunta" Sultane ya fadi yana kai dabino bakinsa.