L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 57
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 57: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 57. A nutse da wani irin ba zata ta saman wayar ya daga…
3,352 words
A nutse da wani irin ba zata ta saman wayar ya daga wadannan idanun nasa masu kaifi yana saukesu a kanta. Ya shammaceta,bata dauka zai kalleta ba,da bazata taba bari ya ganta tana kallonsa ba. Ranta ya bace ta rufe qwayoyin idanunta,yanzu zai dauka yana da kyau ne.....yanzu zai dauka yaci galaba a kanta ne,yanzu zai dauka cewa ya isa ne ko dama can tana kallonsa,maganganun data dinga tattaunawa ita da zuciyarta kenan wadda ke bugawa da sauri da sauri.
"Bataqi kiranka ba.....zazzabine kadan ya kamata......gata muna tare ruwa za'a saka mata da allurai ko zai sauka da wuri.....na fahimta ranka ya dade" Amsoshin haisam din kawai kunnuwanta suke iya ji,tana mamakin yadda ya fadiwa sultane kansa tsaye suna daki daya.
"Allah ya sawwaqe.....jeka saka mata ruwan.....amma nasan halinta da tsoron allura muhammad......ka ajiye wayar a kusa na gani ko zan taimaka da wani abun" Sultane ya fadi ransa yana masa fari. Wani irin alfahari da haisam din yakeji. Tun a ranar farko ya fara ganin muhimmancin zaben NAGARTA akan komai. Ya tabbatar haisam ya karbi auren akhnan ne bisa ALFARMA amma hakan bai sanya ya watsar da ita ba. Hakan bai sanya ya gaza sauqe haqqin da yace zai iya riqewa ba,wanzuwa sultane din ko rashin wanzuwarsa a gurin bai sanya ya sauya hali ko dabi'a ba.
A nutse ya miqe da wayar a hannunsa,ya qarasa gefan bedside drawer ya ajiyeta.
"Khadeejatu" Ta tsinciki muryar sultane daga gefanta,abinda ya sanyata daga kai da hanzarinta.
Murmushi yane mata,murmushin da tashin farko ya daki zuciyarta. Ta zubawa mahaifin nata idanu tana hangen wani walwala da farinciki me yawan gaske a tattare dashi.
Kuka takeson sake masa.....roqonsa takeson yi ya raba wannan auren,alfarmarsa takeson nema ya barta ta rayu ita kadai.....amma kuma irin walwalar data gani a idanunsa.....irin farincikin data gani shimfide saman fuskarsa sai taji ya kashe duk wani karsashi nata......sai taji ba zata iya ba.....ba zata iya hanashi yaci gaba da jin wannan farincikin ba. Ya bata duk wani kulawa.....ya bata duk wani 'yanci.....ya bata duk wani dama a yanzun itama sai takejin kamar ya kamata ta barshi yaji wannan dadin.......kamar akwai WATA HANYA......akwai wani damar da zata warware matsalarta ba lallai saita cutar da farincikin sultane ba,ta cikin ruwan sanyi koda ba ayau yau ba....koda ba'a yanzu yanzu ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 98*
Cikin kulawa yake mata sannu,tana amsa mata tana kuma qoqarin boye rauninta da tashin hankalinta. Hankalinsa sam bayakan maganganunta da mahaifinta,ya tattara nutsuwarsa wajen zuqe ruwan allurar a syringe daya da kuma fasa drip din ya masa gurin tsaiwa. Dukka cikin horon aiki da suka samu ne.....sun koyi abubuwa masu yawa da kowannensu zai iya buqatar yiwa kansa ko dan uwansa na taimakon gaggawa wato emergency a bakin aiki.
Karo na biyu suka sake hada idanu dashi,shi ya fara janye nasa idanun yanajin qosawa a tare dashi. Babban syringe din tabi da kallo da cannula din daya riqo yana takowa a hankali.
*MAMMINA*
Kasa cikakken zama tayi cikin kujerar gaba daya kaman yadda ta kasa samun cikakkiyar nutsuwa. Tun tana zaune daidai har ta fara motsawa kamar wadda ke zaune saman qayoyi. A hankali zufa ke karyo mata lokaci lokaci tana sanya tafin hannunta tana sharewa. Duk da sassanyan iskar Ac dake parlor din,da kuma daddadar iskar dake kadawa a waje wanda zuwa lokacin yayyafi ya fara sauka sirara marasa sauti.
To wai me yakeyi?,me yakeyi a dakin yarinyar mutane sama da awa daya?. Me yake gayawa akhnan?,ita data sani da kafiya taurin kai da dan uban miskilancin da shi kadai ya isa ya sanya namijin shayin kallonta ko matsowa kusa da ita?. Me yake gaya mata har haka da dukkaninsu sukayi luf a dakin,ba alamun motsin koda me rai da take iya jiyowa duk kuwa da adadin kasa kunnen da tayi?.
Sanda agogo ya nuna mata zaman awa biyu cur tayi a gurin sai taji haqurinta yana qarewa. Ta miqe tsam tana kaiwa da kawowa kamar wadda takejin ba haya. Zuciyarta nata saqa mata ta shiga kawai duk da ta sani cewa a dokar masarautar aikata hakan laifi ne babba. Tsaki taja tana Allah wadai da tsayawa tambayar birra da tayi,inda ta shige kanta tsaye ma da laifin zai zamana da sauqi akan yanzun da tabbas birran tasan ta gaya mata.
A mamakance birra ta dakata tana dubanta,wadda tayi mantuwar kashe socket na Ac din parlor dinne,abinda ya sanyata dawowa kenan,don har bacci ya fara awon gaba da ita.
Sosai mammina ta hade rai,duk da tasan birran bata da hurumin kallonta.
"Allah ya taimakeki ko....."
"Kiyi abinda ya kawoki ki tafi" Ta fada mata a kausashe,saita gotata ta kashe sannan ta dawo ta sake ficewa tana barinta,can qasan ranta mamakin giwar yana sake kamata,tana kuma sake gamsuwa da yadda da halayenta wasu lokutan da basu da kyau.
Ci gaba tayi da irga lokaci,tun tanayi da yatsun hannunta har abun ya soma gagararta ta maida idanunta kacokam ga agogo. Tana jin yadda gari yake sake sanyi,tana kuma jin yadda gaba daya ruwan yake qara qarfi.
Zafi kawai zuciyarta keyi mata,banda gayawa kanta da taketa faman yi na cewa ba girmanta bane,bataga abinda zai hana hawaye zubowa a idanunta ba. Dole ta san yadda zatayi ta sake samun yarda da amincin akhnan,idan ba haka ba komai zai iya faruwa.....komai zai iya wargaje mata. Bata shirya barin zuciyar akhnan a yanzu taso kowanne d'a namiji ba,bata shirya barin akhnan ta yiwa kanta zabi akan kowanne d'a namiji ba....bata shirya qyale akhnan ta zabarwa kanta komai ba a yanzu. Wannan lokacin baiyi ba,wannan lokacin baizo ba tukunna.
*HAISAM & AKHNAN*
Cikin dauriya da dakiyar da batakai ko ina ba ta miqa masa sambalelen hannunta. Ya kauda idanunsa daga kallon sambala sambalan yatsunta da yake da ragowar jan lalle na wancan lokacin da akayi mata. Ya fidda cannula din ya cire tsinin allurar.
Kallonsa kawai takeyi tana kuma kallon allurar hannunsa. Ranta a shaqe fal da baqincikin taba mata hannu da zaiyi,zuciyarta kuma na cikin kokwanto tanaso ta gani zai iya kama hannunta gaban sultane?.
Saidai kamar jira yake ta qarasa yiwa kanta wannan tambayar ta tsinciki lallausan tafin hannunsa cikin nata. Har tsakiyar kanta taji tsigar jikinta ta zuba. Wani irin sanyi da laushi me ratsa jijiya da kuma jiki,wani abu ya harba cikin jininta da wani irin sauri,saita maida idanunta ta lumshe tana tambayar kanta.
"MENENE WANNAN?". bata samu amsa ba,sai amsar da daya sashen na zuciyarta ya fada mata,ya kuma tunasar da ita.
"Shi din malami ne fa kawai" Kalmar data sauka a zuciyarta da wani irin nauyi,ta kuma sanyata bude idanunta gaba daya tana kuma zare hannunta dake tsakiyar tafin hannunsa da wani irin sauri.
"Me haka biftu?....ke har yanzu ba zaki daina tsoron allura ba?,kin girma fa?" Sultane ya fada da wani yanayi da yafi kama da lallashi.
Hawaye ne sosai cikin idanunta tana kallon haisam din,wani irin duba take masa wanda ta kasa kallon qwayar idanunsa,sai kyawawan lips dinnan nasa da taga sundan motda kadan.
Wani zafi takeji har cikin ruhinta a sanda duk ta tuna MALAMI yake aurenta. Me yasa sultane zai mata haka ne?. Wannan tambayar ta nanatawa kanta ita tafi sau dubu,saidai ba amsa ko daya gamsashiya data samu.
"Muhammad.....bari na barku,ga daya daga cikin halinta nan tsoron magani da allura.....nasan zakaji dasu.. Mu tashi lafiya" Sultane ya furta,ba tare kuma daya bar kowa a cikinsu ya masa magana ba ya kashe wayar murmushi na fita a fuskarsa. Yau biftu dinsa ta samu me kula da ita,yau biftunsa ta samu wanda zaiji da wannan rigimar. Shikam baisan sai yaushe zata fahimci ta girma ba,amma koma meye yasan tabbas ta samu wanda zaiji da dukkan komenta.
Ci gaba yayi da kallon screen din wayar daya zama.blanck bayan yankewar wayar. Qoqari yake ya hadiye wani abu......yana jin girman yardar da sultane yayi dashi,yana jin kamar yadda sultane ya amince dashi abun yayi yawa,kamar abun yayi zurfi,kamar bai kamata ya yarda dashi aka diyarshi har haka ba. Bai bashi wannan assurance din ba,me yasa ya zurfafa a aminci dashi har haka?.
A nutse ya maido idanunsa a kanta ya zube mata su. Sosai ya kafeta da kallon da aqalla saida ta kusa sakanni goma sha biyar ba tare daya qifta ba,sai ya bude hannuwansa yana miqa mata tafin hannunsa ba tare daya janye kallon ta akanshi ba.
Hawaye ne sosai kwance cikin qwayar idanunta,saita samu kanta da bashi hannun kamar yadda ya buqata tana jin wani kuka yana qwace mata.
Meye haka a idanunsa me tasirin da yake iya sarrafata a duk sanda yaso?......wanne irin magnet ne a idanunsa masu tsananin qarfin da suke sarrafa tunaninta a sanda bataso ba bata kuma shirya ba.....wanne irin qarfi gareshi da iya umarnin ido kawai yake samun nasarar sarrafata ba tare da yace da ita komai ba?. (Nikam nace uhmmm yarinya,an gaya miki duk makarancin alqur'ani mutumin banza ne?,duk wanda ya aboci qur'ani ba shakka zai rabauta da wani irin haske da kwarjini).
Kyakkyawan mazauni hannun nasa ya samu cikin nata,a nutse ya dora babban yatsarshi saman hannun nata ya soma sama da qasa dashi yana laluben jijiya,abinda ya haifar musu da wani irin yanayi dukkaninsu shi da ita. Wani irin tashi tsigar jikinta tayi,ta same curewa guri daya hawayenta da bataso ya gani suna qaruwa,yayin da wani abu me nauyi shi kuma ya fara danne zuciyarsa.
Numfashinsa ya soma qoqarin canza yadda yake shiga da fita,da farko ya qaryata yanayin,saidai daga baya da dukka gangar jikinsa ke neman amsawa sai ya hada dukka jarumtarsa yana bawa kansa qwarin gwiwa tare da canza yanayin zuwa yanayinsa na Muhammad haisam. Karo na farko kenan a rayuwarsa daya taba riqe hannun wata diya mace har haka cikin tafukan hannunsa,sai yakejin kamar komai yana shirin kwance masa.
Har cikin qasusuwansa yakejin saukar kukanta sanda ya nutsa allurar cikin fatarsa. Ya tsani kuka,banda kuma haqqinta dake wuyansa da tuni ya jima da barin dakin. Qasa qasa ya saki tsaki saboda yadda sam baya son noises a rayuwarsa,kukanta yana masa waninirin kud'a cikin kunnensa.
Tsakin kuma ya sauka a kunnenta sosai,ya wuce zuciyarta yana aje mat wani tabo daya sanya kukanta ya qara tsananta.
Allurar jijiya ce don haka dole ya dinga turata a hankali,yana dakatawa gami da dubanta,ta riga ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana sauke kukanta a hankali. Idanunsa ya sauke a hankali kan dogon dokin wuyanta da gashinta daya fito ta qasan hularta yayi masa rumfa. Kamar rad'a abinda ya taba karantawa cikin littafin ibnul qayyum Aljauzy na RAUDATUL MUHIBBEEN. Cikin sifffofin kyau na diya mace daya lissafa,soyayya tsakanin mace da namiji.
Hannunsa daya masa nauyi kadan ya daga ya sake tura ruwan allurar cikin jikinta kamar me tsoron turashi a hankali,sai ya sake dakatawa don bawa ruwan daya tura din damar bin jikinta.
Gudun sake fadawar idanunsa inda yakejin bai cancanci ya sauka din ba,sai yabar kansa a qasa,saidai kuma a hankali idanun nasa suka zame,kai tsaye kuma suka sauka kan dogayen qafafunta da suke hade guri daya.
Wasu zara zaran yatsu,lallausar qafar da idanu kadai sun isa su gaya maka hakan. Fatar dake lullube da qafan itama me sheqi ce da daukan hankali kamar ba fatar qafa ba. Akwai gashi qananu saman kowanne yatsar qafar. Kaman tasan su yake kallo,ta motsa qafar tata a hankali,sai ya sake zare idanunsa daga kai yana jin yadda numfashinsa yake sake sauyawa.
Ya gaji da gane gane,don haka a wannan karon koda ya maida idanunsa ga allurar bai dauke idon nasa ba,sai daya qarasa tura mata ruwan allurar gaba daya,sannan ya zare syringe din.
Drip din ya matso dashi ya jona mata,idanunsa akan iv flow regulator din yana qoqarin daidaita ruwan,da deep and husky voice dinsa ya furta.
"Zaki iya kwanciya" Kamar haka take jira kuwa ta koma a hankali ta kwanta tana sake fashewa da kukanta.
"Ya salam" Ya fadi qasan ransa,saidai duk da haka bai kalli fuskarta ko sau daya ba. Bayason yayita kallon abubuwan da xasu zame masa matsala,wannan kusancin tsaf zai iya zame masa ciwo koda bai shirya hakan ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 99*
A nutse ya taka yana sake rage hasken qwayayen dakin,ya kuma sake daidaita iskar sannan ya maida windows din dukka yadda weather din dakin yasan zaiyi mata,yadda yasan zai dace da yanayinta. Ya zuba allurai cikin drip din daya tabbatar zasu saukar mata da zazzabinta,zasu kuma sanyata zuwa gobe ta tashi da qwarin jikinta.
Har zuwa sanda ya qarasa saman daya daga cikin sofa din dake can bangare daya na dakin ya zauna akai yana jin sautin kukanta can qasa. Idanunsa ya lumshe yana furzar da iska daga bakinsa. Shi kansa shi daya yasan me yakeji a ransa da jikinsa,gajiya.....kasala da wani irin qosawa. Qafarsa ya dora daya kan daya,ya kuma rungume hannayensa a qirjinsa sosai yana lumshe idanunsa a nutse.
Cikin wata irin nutsuwa,da wannan daddadan muryar tasa....da wannan daddadan sautin nasa yayi gyaran murya a hankali,sannan ya fara rera karatun qur'ani da wata tattausar murya,wannan qira'ar dake matuqar kama data sheikh Muhammadu afif taj. Laushin muryar......zaqin karatun,da nutsuwar da qur'ani ke sanyawa a zukatan bayin dake karantashi ya cakuda da sassanyan yanayin saukar ruwan sama a wannan daren.
A hankali sautin muryarsa ya fara ratsata,a hankali ta dinga jin wani yanayi me cike da nutsuwa yana saukar mata.....a hankali kuka da bugun zuciyarta suna fara daidaita,saita lumshe idanunta a hankali,komai tana jin yana mata shuru,sautin kawai ke shiga kunnenta,yayin da ruwan dake diga a jikinta a hankali ya soma wanzar da wani irin sassauci a jikinta,ruhinta kuma yaci gaba da samun nutsuewa da karatun dake tashi cikin dakin.
*MAMMINA*
Sau uku tana diba fuuuu tana nufar qofar dakin,saidai kuma data isa saita tsaya cak ta kasa qarasawa. Ita kanta batasan abinda yake tsaidata ba. Ita kanta batasan me yasa take juyowa tayi reverse ta koma parlor din data tashi da farko ba.
Wani irin zafi takeji ba iya zuciyarta kawai ba,harda gangar jikinta. Wani irin zafi takeji idan ta tuna yanzu haka haisam din ya kebe da akhnan......ya kwashi wasu a wanni a inda ba kowa daga shi sai ita,waye yasan me ya faru ma?,wa yasan me yake faruwa kuma?. Komai ma zai iya kasancewa.
Iska me zafi ta furzar daga bakinta,tana ji kamar hawaye na shirin balle mata,abinda ta manta rabonta da tayi. Tunda yaron ya shigo masarautar gaba daya komai yake zuwa mata a hagunce,ta lura abubuwa da dama basa tafiya daidai,indai kuwa ba jinin IBRAHEEM bane to waye?.
Kai ta girgixa da sauri ganin tana neman kaiwa sama da sha biyu na dare a zaune a gurin. Ya zuwa yanzu ya zama dole ta tafi,dukkanin alamu sun bata cewa kwana zaiyi kenan a dakin?. Tambayar data sauka zuciyarta da wani irin zafi da takaici. Wanne irin rashin ta ido ne wannan?,wanne irin soyewar idanu ce wannan?. Me ya gayawa akhnan har ya amintar da ita tayi ladab. A tarin aure auren yankin agadez bata taba gani ko jin labarin inda ango yakai kanshi dakin amarya ya kwana da ita ba,amma koma meye yakeji,koma meye yake taqama dashi dole gobe ta yiwa tufkar hanci.
Da mutuwar jiki kasala baqinciki da bacin rai ta juya ta fara komawa inda ta fito. Batajin duka yau zata iya kwanciya tayi bacci......ta sani zata yita lissafi ne tare da jiran awannin da zasu kaita wayewar gari.
A hankali ya soma slow da muryarsa sanda yakai qarshen surar,ya sauke idanunsa a kanta yana karantar yanayin fitar numfashinta. Tayi relax sosai,abinda yake gaya masa cewa bacci ya dauketa. Ya qarashe ayar qarshe yana lumshe idanunsa,shima yana jin wata nutsuwa me yawa da nauyi tana saukar masa.
Tsam ya miqe cike da nutsuwa kasala da mutuwar jiki ya kalli agogo. Sha biyu harda rabi na dare,sai ya taka a hankali ya qarasa gaban gadon don tattare kayan magungunan dake ajiye a gurin.
A hankali idanunsa suka sauka saman fuskarta,wadda kusan rabinta a duqunqune take cikin duvet,amma hakan bai hana manyan idanunta da zara zaran eye lashes da eye brows dinta bayyana ba. Idonsa ya dauke a kanta,ya matsar da komai yadda ya dace,ya saka hannu yana kashe hasken beside lamp dinta daya fuskanci digital ce.
Daukarta yayi a hannunsa yana duba wanne company ne. Yadda yaga gurin da ake kunna bangaren qur'anin da seal a jiki ya tabbatar masa bata taba kunnuwa ba. Yadan tabe baki kadan,wataqila batasan ma da qur'ani a jiki ba kenan?,tabbacin baime dameta ba?.
Baya yaja kadan ya cire seal din yana sake duba sunan company din. Sanda zasu fara fidda irin design na fitilun sun nemi izininsa kan karatunsa ya zama daya daga cikin karatuttukan da zasu dora akan na'urarsu,ya kuma basu dama,don haka yana kunnata kai tsaye ya tafi ga zabin farko qira'ar SHEIKH MUHAMMAD HAISAM.
Suratul baqra ya saka,ya kuma daidaita sautin sannan ya ajeta nesa kadan da ita ta yadda sautin bazai takura baccinta ba. Yadda karatun yake fita duk kuwa da cewa muryarsa ce qira'arsa ce amma shi kansa sai daya lumshe idanu,tsaiwar sakanni yayi sannan ya matsa ga wayar girke dake cikin dakin,ya kuma kira sassansu birra.
Birra dince ta daga,ya umarceta data zo yanzun,ya maida wayar ya ajiye idanunsa suna sauke sauka akan fuskarta.
"Stubborn girl" Ya fadi can qasan zuciyarsa. Bai taba ganin mutumin da bai damu da kansa ba irinta. Abubuwa masu yawa ne tattare da ita zagaye da ita amma anyi sealing tunaninta gaba daya an dunquleshi guri daya,kuma a hakan gani take tana da lissafi sama dana kowanne d'a namiji.
"Zamanka a rayuwarta taimako ne....lada ne me yawa ka fidda mutum daga hatsarin da baisan dashi ba" Yaji wani sashe na zuciyarsa yana gaya masa. Kai ya girgixa,baison raini,bazai sanya kasan canciki da rayuwarta ba.....zaiyi aikinsa ne kawai ya qare......sauran abinda Allah ya qaddara a rayuwarta da tashi a gaba shi kadai ya barwa kansa sani.
A ladabce birra ta shigo kanta a qasa. Muryarsa a sauqaqe ya bata umarnin shigowa ciki. Ita kanta yanayin dakin a yau sai ya burgeta,duk da dakin bawai baqonta bane,ba kuma yau ta saba shiga cikinsa ba,amma a yau sai take ganin kamar an sauya dakinne.
Umarnin zama ta kwana da ita ya bata,sannan ya nuna mata yadda zata kula da drip din har ya qare,da kuma yadda zata zareshi ta tsaidashi idan ya qare din gudun kada ya fara zuqar jini kuma. Ya sake gaya mata wasu abubuwan da zatayi bayan ta farka koda safe ko cikin dare
"ki tabbatar bata rasa sallar asuba ba" Ya fadi daga qarshen maganganunsa duka.
Wayoyinsa ya tattara da komai nasa ya juya yana fita a dakin cike da gajiyar zaman guri daya,kasancewarsa mutum me kazar kazar da yawan motsi,shi yasa zai wahala ka ganshi a zaune a guri daya.
*W A S H E G A R I*
A hankali ta bude idanunta sanda taji ana dan bubbuga pillow din da take kai ana kiran sunanta cikin girmamawa. Gefe daya daddadan sautin karatun qur'anin dake can qasa yana shiga kunnuwanta a hankali yana samar da nutsuwa cikin bude idanunta na farko da tayi a safiyar.
Fes ta bude idanunta da suka sauka kan fuskar birra dake rusune a gabanta.