Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 58

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 58

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 58: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 58. "Allah ya taimakeki......lokacin sallar asuba yayi" Ta…

3,343 words

"Allah ya taimakeki......lokacin sallar asuba yayi" Ta fada tana rusunar da kanta qasa. Kaman ba zatayi.magana ba,ta xubawa birra idanu tana mamakin yadda yau ta gaza jin alarm dinta.

"Ina fashin sallah....ina wayata?" Ta tambaya da muryar masu bacci bugu da qari da wani yanayi a cikin muryar tata da wani irin sanyi sosai.

"Bari a duba miki ita" Birra ta fadi tana miqewa,saidai batayi nisa ba ta ganta kusa da bedside lamp din.

Idanu akhnan ta sauke kan fitilar,mamaki kadan yana kamata. Bata taba zaton akwai qur'ani a jikinta ba,tana daga kwancen ta miqawa birra hannu tana karbar wayar gami da jefa mata tambayar

"Waye ya kunna karatun nan?" Tayi tambayar sanda take sauke idanunta akan fuskar wayartata

"Sheikh muhammad ne" Ta amsa mata a ladabce. Qaramin tsaki taja tana jin wani haushi yana kamata. Ba professor ba ba doctor ba......sheikh?...sheikh?.....itama matar sheikh kenan nan gaba kadan za'a kirata?.

"Idan kin gaza samarwa kanki mafita ba,....idan kika yarda kika rayu dashi" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa.

"Ya akayi wayar ta mutu?" Ta sake daga kanta tana daga kwancen ta tambayi birra.

"Shine ya kasheta da zai fita" Mamaki yadan kamata,taja qaramin tsaki tana jefa wayar bayanta ta maida kanta ta kwantar. Har birra din ta juya sai ta sake bude idanunta.

"Waye yace ki tayar dani sallar subh?"

"Sheikh muhamm....."

"Ya isa haka nan" Ta katse birra da hanzari tana sake jan wani dogon tsakin tana maida idanunta ta lumshe. Tanason sanin waye ya cire mata ruwan ma amma tasan qilan idan ta tambayi birra zatace mata shine,don haka gwara ta riqe tambayarta a ciki tafi mata alkhairi.

Tayi zaton zata koma bacci ne,amma abun mamakin sanda ta rufe idanunta sai daren jiya ya dinga dawo mata,wani sashen na tunaninta kuma yanata dibansa kan daddadan sautin karatun qur'anin da har yanzu ke fita can qasa ta cikin fitilar. Kamar tasan muryar,da gaske kaman tasan malamin,amma tunaninta daya lula da ita can duniyar abinda ya faru tsakaninta dashi a jiya ya janye zurfin nazarin bin qwaqwafin inda ta sanshi din.

Fes wadannan idanun suka dawo mata.......lips dinsa da suke motsawa da wani irin yanayi.....kwantacciyar sumar dake fuskarsa data qara cika siffarsa da kamalarsa ta kwarjini,laushin tafukan hannunsa da suka nutse cikin nata.

Bata farga da lokutan data bata ba a kwance tana tilawar abinda ta gayawa kanta daga baya baida amfani ba sai bayan wani lokaci. Wani tsaki taja me qarfin gaske tana bude idanunta. Cike take da tuhumar kanta,ba wannan tunanin ya kamata tayi ba.....wayeshi da zata bata lokutan masu tsada a kansa?. Samun kanta tayi da tula tarjn zarge zarge da laifuka ga zuciyarta data dauko mata wannan shirmen a cewarta.

Koda ta bude idanunta saita riski birra harta kimtsa dakin tsaf. Taja numfashi sosai da nufin furzarwa.....amma saita riqe numfashin ta gaza fiddashi har na tsahon wasu sakanni kafin ta sakeshi.

Wannan qamshinne sosai take jinsa cikin hancinta,wannan qamshinne yake ratsa qofofin hancinta sosai. Saita ware idanunta sosai tana a kwance tana juyasu tsakanin inda ya zauna a daren zuwa yanzu.

Fari qal din handkerchief ta hanga zaman stool din daya zauna a jiya. Ta zuba masa idanu kamar haisam dinne zaune a gurin. Wannan abun kadai ya manta amma kuma yake isar da qamshi haka har cikin kwanyarta? Wanne irin turare ne wannan? Ta jefawa kanta tambayar.

Sake jin qaunar mallakar turaren tayi ya kamata. A nata hasashen sam ba dashi kalar turaren ya dace ba......irin wannan turaren a hannun sarakuna da JININ SARAUTA ya kamata a sameshi ba hannun malami ba. Muddin kamfanin suka bata tabbacin mallaka mata qamshin saita haramta fidda sample dinsa a kasuwa gaba daya ballanta ya samu ya siya. Ta sake jan tsaki,waya sani ma ko da qyar yake iya hada kudin siya?,tsabar girman kai da son nuna izza a muhallin daba nata bane kawai ya sanyashi lallai saiya mallaka. Tafi kyautata zaton na wasu daga cikin manyan shugabannin larabawa ne qilan aka taba bashi kyautarsa.....ko kuma da dagiya irin ta malamai ya nace sai daya siya. Ta tabbatar badai a ce ya iya mallakarsa ta sauqi ba.

"Ya kukayi da company perfume dinnan?,wacce amsa suka bayar?" Akhnan ta fadi bayan ta fito daga wankan data sanya birra ta hada mata ruwa me zafin gaske,birran kuma tana tayata tsane jikinta don tayata ta shirya.

"Sun maido amsa.....wannan yanayin da aka shiga ya sanya tace kada mu sanar miki yanxu....mu bari sai komai ya lafa" Fararen blue eyes dinta ta daga ta jefi birra dasu.

"Bayan auren wancan mutumin na farko?....kina nufin a yanzu kowa yasan ni matar malamincan ne?" Ta fada da wani irin emotions me zafi da suke tasowa daga zuciyarta.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 100*

Qasa birra tayi da kanta,batasan amsar da zata bata da zata gamsar da ita ba. Yadda tayi maganan kawai tasan akwai wutar dake ruruwa cikin zuciyarta.....to amma maganan gaskiya ba cikin masarautar agadez kawai ba......maganan daurin aurenta a yanzu da sheikh haisam ya bazu a yankunan niger dama maqwabtanta. To amma wani hanzari ba gudu ba....tafi kowa sanin QARYA na cikin halin akhnan na qarshen qarshe. QURU QURU CE ita,kome zata fadi zata fada maka kai tsaye,koda kai hakan bai.maka ba,koda kai hakan bai dace da abinda kakeso kaji ba.....zata fadi maka ne da iyakar gaskiyarta,duk yadda zaka dauki abun kuma ya rage naka....wannan halin nata ya sanya ta tsani ayi mata qarya.....ta tsani HA'INCI....ta tsani YAUDARA kamar yadda tayi matuqar tsanar CIN AMANA.

"Shuru ba shine abinda na tambaya daga gareki ba" Akhnan din ta fada tana jin zuciyarta tana mata rauni.

"Tabbas.....kowa ya sani....ba a iya....."

"Ya isa.....me company sukace?" Ta sauya akalar maganar,don iya amsar birra ta farko kadai ta wadatar da ita.

"Sunce qamshine da mutum daya kawai yake da haqqin mallakarsa......amma zasu tura buqatar zuwa gareshi.....idan ya amince ya sanya hannu zasu iso da saqon amincewarsa......idan kuma bai amince ba,saidai ki zabi wani scent din na daban zasuyi miki shi". Kai ta girgixa a hankali.

"Tunda wancan malamin ya samu qamshin to tabbas sun fada ne kawai......duk da banda tabbacin waye ya bashi.....don tunda suka fadi hakan alamace na sammasa qila akayi.....maganace ta kasuwanci da kudi,ki gaya musu su shaida masa ko nawa ne zan biya.....yau nakeso ki gaya mata,kada kuma ta wuce kwana biyu zuwa uku bata isar musu da saqona ba"

"In sha Allah" Birra ta amsa mata tana ci gaba da taje doguwar sumarta kafin ta saki kanna hankali ta tafi ta dauko hair burner da take zuba mix na turarukan wuta masu dadi daga kamfanin INCENSE BY KABODAUGHTER 0803 211 9803.

Tsaf ta gama gyara mata gashin ta kuma daure mata shi yadda ba zata takura ba,ta shirya cikin wasu sauqaqaqqiyar doguwar riga me dogon hannu. Koda ta kalli fuskarta a madubi sai taga kaman tadan qara kyau kadan. Tsaki taja,wanne kyau za'a samu cikin tashin hankalin da malamin ya sanyata?. Na nutsuwa ba kwanciyar hankali ba walwala?. Ta rantse har gwara lokacin maganan auren almaz akan yanzu,batasan wanne irin nisan qin jini tayima mutumin ba.

Cannula din hannunta ta daga ta kalla.

"Banason wannan abar birra,a cireta"

"Kiyi haquri yazo,baice a cireta ba" Harara ta watsa mata wadda ta tilastawa birra din sadda kanta qasa.

"Dama shima ba aikinsa bane.....bansan wanne shishshigi ne ya hada malunta da harkar lafiya ba....." Ta fadi har cikin ranta tana shan mamaki. Wancan karon ance shi ya mata allura sanda ake suspecting guba taci,yazun gashi ya sanya mata qarin ruwa,bayan abune da da yawa ma wasu masu aikin jinya saka cannula ke musu gardama,amma shi tsirawa daya taga ya samu kan jijiyar

"Ni bamma yarda da mutumin nan ba.....baida gaskiya,ya kamata sultane yasan ainihin waneneshi" Ta samu kanta da fadi tana duban inda ya ajiye paper bag din me wani irin daukan idanu,tana tuna tea din daya bata jiya. Me yasa ta karba?,inda kuma ya zuba mata wani abu a ciki fa?.

"Muje ki ban breakfast.....ki fita da wancan jakan" Ta fada tana nuna mata inda jakar take ajiye sannan ta juya a hankali cikin rashin qwarin jiki tana fita zuwa babban setting room dinta.

Ko zama batakai gayi ba shehnaz da aisa suka shigo,shehnaz ce tayi sallama don aisa amsa waya takeyi. Daga amsa sallamar bata qara komai akai ba ta zarce kai tsaye zuwa ga dining,aisa ta zauna saman kujerun parlor din tana ci gaba da amsa wayar da da alama taja hankalinta da yawa,shehnaz kuma ta tako tana biyo bayan akhnan. Kujera birra taja musu su dukka suka zauna a kusan tare.

"Shi cin abincin safen amare ma daban yake.......yanzu qarfe sha biyu sannan zaki karya?" Ta fada tana duban idanun akhnan.

Bata amsa mata ba,har birra ta gama shimfida mata fari qal din lap napkin dake dauke da tambarin masarautar agadez ta kuma ajiye mata abubuwan buqata a kusa kaman tissue.....toothpick da sauransu sannan ta koma ta fara serving dinsu da plate uku,don ta hangi shigowar aisa ma.

"Ki kira barratu ta hadamin tea" Ta fada da miskilar tattausar muryarta sannna ta maida fararen blue eyes dinta ga shehnaz.

"Ba yau ba shehnaz.....ba yau ba....idan rigimar kike buqata ki bari na zama free.....ko na maida hankalina jikina" Maganan ya bawa shehnaz dariya sosai. Duk abinda zai sanya akhnan tayi magana haka da ita with calmness lallai babba ne,yana kuma taba zuciyarta da gaske. Saidai tasan halinta,tana kuma tsoron tattalin energy dinta kawai takeyi.

"Ta yaya zanyi fada da amarya?.....amaryar ma ta manyan mutane,babban makarancin qur'ani irin sheikh muhammad haisam......kawai jiya na zauna kallo abinda na dade banyi ba,dana gaji na fara lalube laluben channels..... Kinsan wani abu?....manyan channels uku na kama kawai sai naji karatunsa sun saka da hotonsa yana rotating?" Shehnaz ta fada da mamaki sosai saman fuskarta.

Har akhnan takai chips na farko bakinta ta fara taunawa ta tsaya tana watsawa shehnaz harara. Abinda zuciyarta ta bata kawai shehnaz tazo tayi mocking nata ne don ta auri malami.....abinda taketa gudu kenan,idandai har shehnaz zata zama ta farko da zatayi mocking nata to waye kuma bazai mata ba?. Waye haisam din da har wasu kanyan channels data lisaafo zasu saka hotonsa ko karatunsa?. Waye ma ya sanshi a iya agadez kawai kafin akai ga niger gaba daya?.. Banda kalar girman da taga kowa yana bashi da shugabancin riqon qwayar da sultane ya bashi wanda ya qara masa girman kan da yakeji tsaf zata iya cewa a masarautar ma ba kowa ya sanshi ba balle a tafi ga wani abu me fadi irin duniya.

"Idan a jaridun duka duniya na jiya kikaga an sakashi ba damuwata bace.....ki riqe labarinki....banason qarin bacin rai.....aisa ki mata magana tun kafin aji kanmu" Ta fada da wani rauni da bacin rai tana maida dubanta ga aisa.

Dariya kadan da mamaki suka kama aisa wadda ke takowa gurin bayan ta kammala waya. Duk da wayace me wani irin girma da nauyi a qirjinta,amma yadda yau kai tsaye akhnan ke kawo qarar shehnaz sai da abun ya sakata boyayyen murmushi.

"Da alama bakiji abinda nannie ta fadi ba kafin mu fito ko?" Ta qarasa maganan tana jan Kujera a tsakiyarsu ta zauna. Hannu shehnaz ta saka alamun tayi zipping bakinta,saima ta jawo farfesun kayan cikin da birra ta zuba mata tahau ci,ita kuma aisa ta maida hankalinta akan akhnan tana tambayarta jikinta ba tare data dauko mata maganan jiya ba.

*H A I S A M*

Wani irin bacci yayi me nauyi daya sakashi makara a komai ma,don ko yanzun da yake breakfast shi da maleek ne kawai zaune cikin setting room din dake gefe daban na gidan.

Yana breakfast din yana sauraren maleek da list din yadda zasu gabatar da bikinsa. Tissue ya ciro yana goge hannunsa gami da aza manyan fararen idanun nan nasa akan maleek. Tunda ya tashi yau kawai yakejin yanayinsa wani irin,sai yakejin yau yafi buqatar kebewa da zaman shuru akan kowanne lokaci na rayuwarsa. Amma indai yana tare da wadannan mutum shidan,koda bai shirya ba ya sani lallai sai sun sakashi ya magantu.

"Da zaku fahimta da kun ajiye komai yanzun"

"Zuwa yaushe kenan?" Maleek ya tambayeshi kai tsaye. Hannunsa ya sanya ya dauko system dinsa ya kunna ya fara daidaitata kafin ya amsawa maleek.

"Aikina......sanda aikina zai cika.....sanda aikina zai kammala" Ya amsa masa yana soma duba emails din da bai duba a jiya ba,gudun kada ya samu kwantan emergency message.

"Captain" Maleek ya kirashi bayan ya ajiye wayar hannunsa.

"Ba wanda zaka hana yin biki tsakaninmu ko nanay haka ne?" Kansa ya dago yana duban maleek kafin ya dauke dubansa. Ya sani tunda maleek ya ambaci sunan nanay tabbas akwai magana da sukayi da ita,saidai bakai ga cewa komai ba abdii ya shigo da sallama.

Yanayin yadda sallamar abdii din ta fita ya sanya haisam daga kansa yana aje dubansa a kansa. Wani irin rikici yake ganin cikin idanu da fuskar abdii din daya sanyashi zare hannuwansa daga kan system din gaba daya ya zuba masa ido kafin yace masa.

"Shigo abdii" Kaman jira yake yace hakan ya fara takowa da wani irin rauni,idanunsa akan haisam din.

"Kanata tsaiwa.....ka zauna abdii ko ka tafi" Haisam din ya fada wani abu yanajin yana dan taba zuciyarsa.

A hankali ya sauke gwiwoyinsa yana kuma zama saman throw pillows din dake gaban haisam inda ya miqe qafafunsa a tsakaninsu ya aza system dinsa akai.

"Labari yazo daga jimma" Abdii ya fada muryarsa da wani nauyi. Idanun kawai haisam ya zuba masa,har na tsahon wasu sakanni saidai abdi bai sake cewa komai ba,don haka yace dashi.

"Ina saurarenka"

"Motii was attacked" Ya fada yana sauya harshe,don yanajin yayi nauyi ya furta da yaren oromo ko hausa. Daidai sanda omar ya fado dakin shima fuskarsa na nuna tashin hankali sosai.

A hankali haisam.ya maida idanunsa ya lumshe yana kiran sunan Allah daga can qasar zuciyarsa. Ci gaba da maimaitawa yayi,yana jin wani abu yana ratsa jikinsa gaba daya,innalillahin da maleek ke maimaitawa a sarari tana cakuduwa da tasa da yake maimaitawa a zuciyarsa.

"Da yaushe?" Haisam din ya sake tambaya bayan ya bude idanunsa da wata iri jarumta yana daidaita bugun zuciyarsa.

"Dazu da sassafe......ya baro inda yaje ya kwana daya,sai sukayo tafiyar asubah.....a hanya akayi attacking nasu". Omar ya bada amsa wannan karon.

"Wanne yanayi suke ciki gaba daya?"

"Akwai wadanda sukaji ciwo......saidai dukkaninsu ba wanda ya rasa ranshi.....don guards din dake tare dashi Allah ya basu ikon yin abinda ya dace,da qwarewar aiki kuma da suka samu daga gareka". Wani irin shuru ya ratsa cikin kansa.....wani irin shuru daya zarce har cikin kwanyarsa na wasu daqiqu,duk da tambayoyi da tattaunawa da sukaci gaba dayi su da maleek.

Wani abu ne ya harba cikin kansa,yayin da wani irin bacin rai ya mamayeshi lokaci guda. Yatsunsa dake harde cikin na juna tun dazun ya rabasu da 'yan uwansa.....ya jinjina kai da wani irin yanayi daya sanya kowa juyowa yana dubansa.

"Kiramin beeno" Ya bawa abdii umarni kai tsaye.

"Beeno kuma?,na dauka zata shirya wucewa Ethiopia yau......ya kamata kaje kaga condition din da motii din yake ciki,a halin yanzu nasan ba wanda zaiso gani a kusa dashi sama dakai" Omar ya fada fuskarsa a rikice.

Idanu haisam ya lumshe sannan ya budesu akan fuskar Omar din,ya kada kansa a hankali kafin ya motsa labbansa da yanayin fuskar nan tasa data tabbatar YAU SAI TA ALLAH......HALIN YA MOTSA ya kuma cakuda da bacin ran da sukaga ya sauko masa lokaci daya.

"Bazan samu xuwa Ethiopia ba omar.....ba Ethiopia kawai ba.....bazan motsa ko ina ba daga cikin masarautar nan"

"Me yasa captain?" Maleek ya tambaya cikin tsananin mamaki. Abune da basu taba zata daga gareshi ba,fadin irin shaquwa qauna da soyayyar dake tsakaninsa motii ma bata bakine.....koda yau ya sauka a addis ababa,anjima kadan akace masa motii yana ciwon kai,to tabbas zai juya ya koma jimma. Har tsokanarsa suke wani lokaci da sunan DAN BABA.....amma a yau babban abu ya samu motii irin wannan kuma yace bazaije ba?.

"Ta zabi motii ne.....saboda tanason gwada SHURU ya koma SAUTI....if i leave i confess.....if i rage.....i reveal......i will do neither" Ya fada yana fidda wani irin numfashi.

Abdii da omar kai tsaye kansu ya kawo wuta,duk da maleek ya gano wani abu amma ba duka ba. Wani irin kallo omar yakewa haisam din,yana sake girmama kaifin kwanya da basira da Allah ya bashi. Tashin farko shi daya.....shi kadai ya gano abinda cikin dukka su ukun basu ganeshi ba......ta zunguri motii ne saboda tana zargin haisam daga nan ya fito,ta zunguri motii saboda tanason yiwa haisam hukunci da reaction dinsa.

"Saidai abu daya da bata sani ba......tasa muqulli ta budewa kanta da kanta qofar farko ta BAYYANAWA DUNIYA DA KANTA DA KANTA ITA WACECE" Ya fada da wani irin qawa zuci da fushin da yakejin yana tasowa daga qasan ransa.

A duniya ba wanda zai taba mutum biyu halittu biyunnan ya qyaleshi,ko wayeshi,muddin da rai da lafiya a gangar jikinsa.

Wayar abdii ya miqa masa bayan ya hadashi da beeno.

"Wannan gidan.....wannan ajiyar da take ciki inason TA BACE BAT!.....Ayi mata kuma kyakkyawan guri,bincike na farko nakeso a zurfafa a kan ajiyar......ba dare ba rana,banason a jima komai bai kammalu ba" Ya furta da salon bada umarnin daya tabbatarwa da beeno babban aiki ya fara ballowa.....hakanan abdii da omar dake zaune dukka a falon.

Awanni ya kwashe yana kiraye kirayen waya tsakanin jimma da Ethiopia......sai daya tabbatar da komai lafiya da kuma qarin samun tsaro,saidai bai magana da nanay ko motii din ba,yace a barsu su nutsu tukunna.

Zuwa sanda ya kammala qarfe daya harda rabi,sai sukayi alwala gaba dayansu,omar ya jasu sallah a nan setting room din nasa.

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 101*

*M A M M I N A*

Cikin wani irin walwala take jin ranta,gaba daya fresh takeji a yau din saboda samun tabbacin qaddamar da harin da tayi imanin shi zai bata haske akan komai.

"The silent one" Ta furta sunan a fili tana duban fuskarta a madubi

"Al_saamit" Ta sake fadi tana sakin murmushi. Tabbas indai har shi din jinin aba jifar ne.....tabbas a yau zata naqalci hakan. Ta dakatar da murmushinta,ta saka hannu cikin jewelry organizer dinta tana fiddo warwarayen da sai sanda takejin girma da izzarta cikakkiya take sanyashi. Sanyashin yana tuna mata da abubuwa masu yawan gaske,sanyashin yana tuna mata da cewa ita dinfa me nasara ce.

Dan dakatawa kadan tayi tana kallonsa ganin yadda ya shige hannunta zuruf,ba kaman a baya ba idan zata sakashi saita dan turashi saboda matseta da yayi,don asalin mamallakinsa batakai cikarta ba. Juyashi ta sakeyi cikin hannunta tana mamaki,to ramewa tayi?,ta tamabayi kanta da kanta,tambayar data sakata dauke dubanta ta mayar ga fuskarta a jikin madubi. Sam a zahiri bataga wata rama ba,ta sanya hannunta jikin wuyanta tana shafawa. Mamaki ya sake saukar mata,ta sake duban abun hannun da takeji kamar nauyinsa ma bai qarasa wannan ba..

Haka kawai taji wani faduwar gaba ya kamata,ta xareshi daga hannunta tana sake kallonsa,shine dai,ba wani banbamci,to meye ya sanya takejin kamar akwai wani abu na daban a tattare dashi?.

Ta jima a tsaye bata hango komai da zai bata yaqinin abinda takeji ba,ta tabbatar kuma zata batawa kanta lokacine kawai,don haka ta qarasa shiryawa tana riqe da abun hannun ta fito.

Tafisu ta samu,ta zube bisa gwiwoyinta tana gaidata kanta a qasa

"Mun tashi lpy alhamdulillah.....naji dadin zuwanki yanzu,don zamu shiga duba akhnan ne.....idan da hali kuma ina buqatar ganin malamin can,saidai banason kiranshi kai tsaye,don zuwa yanzu ya kamata na fara tattalin izzata,ya kamata kuma yasan girman da izzata ke dashi da gasken gaske" Ta fadi tana miqawa tafisu abin hannunta.

Readers Also Read

More by Huguma