Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 59

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 59

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 59: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 59. "Dubamin wannan......" Hannu biyu tafisu ta sanya ta…

3,330 words

"Dubamin wannan......" Hannu biyu tafisu ta sanya ta karba abun hannun,don kusan tafi kowa sanin darajarsa. Juyashi tayi da kyau na wasu mintina,kafin ta maida dubanta ga mammina data xuba mata idanu tana jin gabanta yana faduwa.

"Kinga wami abu daya canza daga gareshi?" Kai tafisu ta girgiza.

"Ba komai ranki ya dade,yana nan kamar yadda yake,akwai buqatar ma a wankeshi don yafi haka haske". Shuru tayi na sakanni sannan ta girgiza kai,ta miqa hannu ta karba ta saka a hannunta tana cewa.

"Muje".

Kamar ko yaushe duk wani bawa ko hadimi dake hanyar wucewarta ya shiga kawo gaisuwa,a hankali a hankali har ta isa sassan akhnan.

Fes abinda ya faru jiya ya dawo mata,zuciyarta ta matse bacin ranta ya dawo sabo. Wani tsanar matashin taji tana neman fara tofo a ranta. Bata tana haduwa da mutumin data gaza juyashi ta kuma sarrafashi ba sai SHEIKH HAISAM DIN. Ibraheem ne na farko wannan ya sanya take sake jin tabbaci da yaqinin cewa shi din JININ IBRAHEEM ne.

Fruit salad ne a hannunta,tana zaune cikin wasu manyan throw pillows masu tsananin laushi. Madaidaicin parlor ne cikin parlours dinta,wanda kusan komai na ciki fari ne qal. Aisa na daga gefe ta saka system a gaba,cikin kwanakin kawai qarfin hali takeyi,ta shiga bincike ne kawai cikin sirri a SAHEL COUTURE ba tare da sanin kowa ba. Saidai yanayin abubuwan da take gani da report din da take dubawa daki daki lamarin b'arnar da akewa company din ya fara bata tsoro. Duk da haka bata bari tsoron ya mata tasiri ba......tanason lallai saita cimma gaci,tanason lallai saita tono tushiyar matsalar. Saidai duk da haka bata hana hankalinta wa shehnaz dake zaune tana bata labarin wani film data kalla ba,bara'atu kuma tana gyaran farce wa shehnaz na qafafunta dana hannu. A cewarta ba zata sake lalle ba sai idan an tashi biki. Da aisa da akhnan din dukka kallon shehnaz din sukayi,suna buqatar qarin bayanin bikin wa?. Aisa ce ta fara dago me take nufi,saita watsa mata kallon gargadi abinda ya sanya shehnaz boye dariyarta kenan,amma cikin dakewa tace.

"Allah dai ya dawo da sultane lafiya,bamu yafe kowacce hidima ba ta al'ada data zamani"

"Shehnaz mana" Aisa ta fada tana bata rai

"Nayi shuru" Ta fada tana mazewa.

Hankalinta aisa ta sake maidawa ga abinda takeyi din,sai gurin ya dan dauki shuru kafin sallamar mammina ta maida hankulansu bakin qofar.

Idanunta a zube fes kan akhnan,idan bata manta ba idan kuma bawai tayi lissafi ba daidai bane......kwanakin data dauka bata ganta ba wasu kwanaki ne da basu taba faruwa ba a tsakaninsu a rayuwarsu. Koda tana Niamey ne bata rabo da kiran mammina din,video call ma,su kuma jima suna magana,komai zatayi saida shawarar mammina din,koda yanzun nan suka gama waya wani abun ya tashi to zata sake kiran mamminar.

Cikin girmamawa shehnaz ke gaidata,ta amsa musu sanda take shirin zama saman daya daga cikin throw pillows din dake kusa da akhnan,daidai sanda idanunta suka sauka kan system din aisa. A nutse aisa din ta juyo da zummar ta gaida mammina din itama,idanunta suka kai kan mammina wadda ta zubawa allon system din idanu tanason hango da karanto manyan rubutun dake jikin system din. Da dan hanzari aisa takai hannunta tana kife fuskar System din,abinda yaja hankalin mammina din ta dauke idanunta ta maida ga fuskar aisa din.

"Barka da warhaka mammina" Aisa ta kutso da gaisuwa tsakanin kallon qurillar da mammina ta kafeta dashi. Murmushi ta wanzar saman fuskarta cikin qasa da second daya tana gyara zamanta sosai.

"Barka kade.....aisa sarkin aiki,har a nan ma ba zaki huta ba?" Kai ta dauke daga kan mammina din,tana jin wani abu a kanta wanda bata taba jin makamancinsa ba,saidai hakan bai hana aisa sakin murmushi ba.

"To ya za'ayi......amana abace me nauyi da girma" Tace da mammina din tana dauke system din ta cusata cikin briefcase dinta. Kai mamminan ta jijjiga,har yanzu bata dauke dubanta daga kan aisa din ba

"Gaskiya ne.......Allah ya taimaka,yayi kuma jagora.....ai muna sanya rai in sha Allah 'yar uwarku tana dab da komawa bakin aikinta itama" Mammina tayi maganar tana maida dubanta ga akhnan fuskarta na fidda murmushi. Still dai akhnan bata kalleta ba,idanunta na zube cikin bowl na fruit salad din da take diba a hankali.

"Ya kamata mammina......kamfanin gaba daya ba dadi,abubuwa da ama sun dakata" Shehnaz ta fadi tana narke murya da kanta.

"In sha Allah shehnaz" Mammina ta fada cikin qarfin gwiwa da bada tabbaci. Duk da bata kalli mammina din ba,amma zuciyarta ta harba ta kuma motsu da kalamanta. Wanne tabbaci take dashi na daidaituwar rayuwarta harma da komawa bakin aikinta a dan qaramin lokaci?. Tambayar data tsayewa akhnan din kenan a ranta.

A nutse shehnaz da aisa suka miqe suna fita don basu guri. Hakan ya yiwa mammina din dari bisa dari. Ta sani yaran suna da wani irin hankali,suna da nutsuwa still,amma kuma hakan bazai sanya tayi sake akan canzawar motsi ko sanya idanun daya daga cikinsu ba.

"Na yiwa 'yan uwanki albishir.......amma ke kuma banji kince komai ba biftu" Mammina ta fadi tana tsare akhnan din da kallo,tana son karantar ko akwai wani abu a daren jiya daya sauya tattare da ita?.

Cikin izzar nan da mammina tayi mutuwar tsana.....cikin miskilancin nan da mammina din ta jima da sanin cewa rubutaccen abune a jininta,ta daga wadannan idanun dakema mammina din kanta kwarjini da zubesu akan mammina din. Banda mammina dince.....inda ace wani ko wata ne tabbas da bai isa ta sake koda kallonsa ba. Inda wani ne tabbas data jima da shafeshi daga babin rayuwarta.....data jimda taka masa burki gami da yi masa burki akan kowanne abu da ya shafi rayuwarta,to amma mammina ce......ko ba komai ita bata manta alkhairi a rayuwarta. A nutse ta motsa bakin ta bayan ta hadiye fruit din dake ciki

"Bansan me ya baki qwarin gwiwar yi musu kalar wannan albishir din ba.......ko kina tunanin akwai wani qwarin gwiwar ko wata kalma da kike da ita wadda tafi girman yardar da sultane ya yiwa malamin?. Ko kina zaton akwai wani qanqanin shiri dalili ko gajerun kalmomi da zasu amintar da sultane?". Murmushi mamminan ta saki,kamar ba zatayi magana ba kafin ta saki wani irin shu'umin murmushi.

"Yaro yaro ne.....kuma ta yaro kyau take bata qarko" Ta fadi idanunta zube a kanta. Da wani kallo tabi mammina,tana jin wani abu me kama da hope yanason taso mata.

"Hannu daya baya daukan jinka fa biftu......a sanda ka tasamma sauya wani abu,idanuwa da yawa kake kallo dasu,kunnuwa da yawa kake saurare dasu.....sannan kana qara adadin hannuwanka ne don sarrafa abinda qafafunka ba zasu samu isa ga gurin ba". Shuru ya wanzu a dakin,tana sake jefa shakka da buri a zuciyar akhnan. Kallon da akhnan din tayi mata ya gaya mata neman qarin bayani take.

"Eh.....kina tunanin zan bari burinki ya tafi a banza?.....baki mamakin yadda UWA me share kukan diyarta a wannan karon tayi wasarere da buqatar diyarta ba?....ta bari aka hadata da TAUYAYYEN mutum wanda yaci karo da dukka buri da muradan d'iyarta ba?" Shuru akhnan tayi,wani abu yana fusgarta game da maganganun mammina. Murmushi mammina taci gaba da jifanta dashi,kafin daga bisani wasu qananun qwalla suka fara zubo mata a fuska,ta sanya hannu tana sharesu,still bata daina murmushi wa akhnan ba

"Kina zaton cewa sa nayi zan tsaya miki......zan kasance tare dake da dadi ba dadi da wasa nake?.....kina tunanin don kin juyan baya ni hakan zai sanya na gujeki?" Saita girgizawa akhnan din kanta.

"Idan uwa tace tana son d'anta da gaske take tana sonshi,dadi ko wuya ba wani abu da yake sauya wannan......dadi ko wahala ba abinda zai sanya ta sauka daga kan wannan maganar tata.......Ban taba zaton KUSKURE daya tak zai iya zama sanadin rushewar alaqar dake tsakaninki da uwarki ba. Ban taba zaton AKASI guda daya da kika samu daga tarin shawarwari da uwa a gareki ta jima tana baki ba zaki kasai mata uzuri ta zama abar zargi a gurinki ba" Ta fadi hawayen still suna sauka..

Wani irin sanyi jiki da gwiwoyin akhnan sukayi,wani irin yanayi takeji a ranta maras dadi.....saidai duk da wannan akwai wani sashe daban na zuciyarta da bai sauya daga yanda yake tun a wancan ranar ba.

"Sultane bazai sauka ba bazai sauka ba bazai kuma warware abinda ya qulla ba.....saidai shi da kansa wanda aka daurawar zai warware da kansa.....sai sallameki ta hanyar da zata nesantashi da sultane har abada.....soyayyarki kusancinki da sultane zai koma kamar yadda yake harma ya rubanya na baya" Duban mammina takeyi cike da kokwanton abinda take fadi. Fuskar haisam na gilmawa cikin idanunta. Wannan kafaffen malamin da bata hangen sassauci ko sauqin kai a tare dashi?. Ta yaya mammina zatace zai sallama haka da sauri da kuma sauqi?.

"Kina mamaki ko?,to aurenki bai dauru dashi ba sai bisa sharadin AUREN YARJEJENIYA ne zaku qulla ke dashi.....don ki wanku a idanun sultane.....ki kuma samu irin 'yancin da kike fata" Da wani irin shuru bayanan suka wuce ta cikin kan akhnan din,tana jin sam sun gaza hawa mizanin da takeson dorasu.

Mizani na farko.....da irin idanun data karanci mutumin.....yana da wata irin izza da girman kan da bata taba ganinta jikin mutum me maqasqancin matsayi irinsa ba. Na biyu halayensa kaf basuyi kama da halayen mutum sassauqa da zai karbi duka wani sharadi doka ko umarni ba. A tsanake ta maida dubanta ga mammina,tana jin tarin kokwanto,tana jin tarin rashin nutsuwa da aminci.

"Karfa ki sake aikata wani abun da zai janyomin sabuwar matsala.....karki damqa ragamar rayuwata a hannun mutumin da zai sarrafata yadda yaga dama" Murmushi mammina ta saki,ta karanci tarin kokwanto a tare da akhnan,ta karanci shakkar abun sosai a tare da ita......saidai ta tabbatar zata bawa akhnan hujja da gamsuwa.

"Nasan kina shakka ko?.....shikenan,kiji dadinki,ki kuma kwantar da hankalinki,lallai babarki zata tabbatar miki da komai,zaki gani a gaban idonki" Mammina ta fada hankali kwance tana miqewa da wani kwataccen murmushi akan fuskarta. Murmushin da akhnan ta dade da saninsa,murmushin da idan ta yishi yana nufin ZAN AIKATA ko kuma ZAN TABBATAR.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 102*

*HAISAM*

A nutse ya ajiye wayarsa bayan sun kammala waya da sultane,wanda yake fadi masa kwanaki bakwai ko shida kawai zai qara ya dawo.

Wani irin nauyi sultane ke aza masa,yanata qara kusanci tsakaninsu. Duk sanda zai waya da sultane din cikin hikima ya fahimci yake sake tabbatar masa da amanar akhnan a hannunsa,cikin hikima yake sake gaya masa AMANNAR da yayi dashi,abinda ke sake sare gwiwar haisam kenan. Baiyi alqawari ba.....amma maganganun sultane suna zame masa kaman wani ginannen rami. Ko a yau din duka ya sha'afa da lamarinta,musamman daya tashi da mummunan labari akan motii,bai kuma yi niyyar sake zuwa inda take ba,don ya tabbatar taimakon daya bata jiya yana kyautata zaton yau zata tashi da cikakken sauqi,to amma kuma aiken kayan abinci niqi niqi dafaffe cikin Warmers na alfarma da morsa safiyya tayo masa ya sanya ya tuna da yarinyar. Duk da haka bai niyyar shiga ba,saida sukayi waya da sultane.

Yardar da yayi dashi a kanta dari bisa dari ce.....ba wani abu dake nuna kokwanto ko shakka a kansa. Wannan yardar kuma itake sakashi jin nauyin sultane din,ko sanda suna wayar yace masa.

"Biftu bata taba ciwon da naji hankalina bai tashi a kansa ba irin wannan.....na tabbatar tana hannu da qarqashin kulawar wada zai bata kula da kariya sama da yadda ni zan bata"

Ajiyar zuciya ya sauke yana balle maballan jallabiyyar jikinsa da zummar shiga wanka sannan ya fita ya leqata,daidai sanda kiran beeno ya shigo masa.

A nutse ya saka wayar a kunnensa,kuma cikin qasa da second biyu ya isar masa da saqon da dama shi yake kyautata zaton zaiji daga bakin beeno din.

"Tun dazu aiki ya kammala,kuma ko yanzu haka na lura da qaqqarfan motsi a gidan,da alama suna neman inda ya bace ne"

"Da kyau.....saina nemeka" Haisam ya fadi da husky and calm voice dinsa yana katse kira. Maher ya kira kai tsaye a amintaccen layin daya ware kawai saboda kiran nasa. Saidai tunda ya kira daya bai daga ba yasan qila yana bakin aiki,yayi kuma nisa da wayar. Sai ya aike masa gajeran saqo.

_"akwai wani boyayyen abu da takewa wani bala'in boyo a villa street,haske kawai nake buqata akai ba duka bayanan ba.....ragowar aikin na haisam aba jifar ne"_ abinda ya aikewa Maher kenan,sannan ya ajiye wayar. Karatun qur'ani ya matsa gaba kadan ya kunna ta jikin fitilar tsakiyar dakin,qira'ar sheikh maher almu'aiqaly da sasaauqan sauti mara amo sosai,sannan ya dauki lallausan babban towel din yana zarcewa bandaki. Karatun yana sake saukar masa da nutsuwa,yana kuma sake buda masa qofofin tunaninsa sosai.

Awa daya ya kammala shiryawa cikin black emirati kandora me wani irin sulbi da daukan idanu. Shemagh ya nada a kansa fari qal me adon black mara hayaniya da yawa,ya saye qafarsa cikin fari tas din half shoe. Wani irin kyau yayi me daukan hankali da idanu,baqar kandora din ta fidda asalin kyansa da haibarsa. Bai sanya agogo ba tunda ba nisa zaiyi ba,yadai saqala counter dinsa a yatsarsa saboda gudun tozartar da lokaci ba ambaton Allah a cikinsa. Wani irin counter ne da zaka rantse da Allah qawataccen zobe ne me asalin kyau da tsada. New model 2028 da company din suka fidda sample dinsa suka kuma aiko masa dashi saboda girmamawa.

Ba kowa a sassan nasa,sai abdii kawai dake siyan zaune saman kujera da system yana cinikin wasu litattafai daga Egypt misra. Dubansa kadan haisam yayi,kasuwancin litattafan ya fuskanci kamar sun karbi abdii din,don shima idan ya nema wani cikin wasu litattafan bai samu ba yana yiwa abdii din magana yake kawo masa. Ya yanke shawarar idan komai ya nutsa ya qara masa jari me kauri ya sake buda harkar tashi,duk da so yayi dukkaninsu ya zubasu a harkar kamfanin turarukansa,tunda ba yadda za'ayi kana aiki irin nasu ya zamana baka wata sana'ar daban da zata kadar da hankalin mutane daga ainihin aikinka.

"Obbo.....an samu naka littafin.... Million daya da dubu dari biyar" Abdii ya fadi yana sanya qwayar idanunsa akan haisam din,sai kuma maganar ya qarasa maqalewa saboda wani irin kyau da kwarjini da haisam din yayi masa.

"Ba damuwa,a aika dashi jimma.....ka fadawa mansoor(me kula da katafaren library dinsa) a bangaren da zai sakashi,ya hadashi da sauran" Ya amsa masa yana nufar qofa.

"Am....amma obbo....library dinka ya cika fa duk kalan littafin daya kamata ace akwai...." Abdii ya fada har qasan ransa shigar haisam din tana sake burgeshi,still kuma yana mamakinsa. Yadda yake sanya ko nawa ne ya siya littafi,duk da kudi ba matsalarsa bace,amma girman library dinsa ya isa. Yana daya daga cikin manyan dakin karatu da ake recommending ma mutane shi. Yana matuqar ji da ita sama da komai daya mallaka,don haka ba kowa yake samun dama ko izinin shiga ba.

"Bakasan girman ilimi ba abdii?,daga inda kake zaton ka qure masa,daga nan wani ya fara ma......ilimi.kogi ne,yana da girma da fadi,saidai kawai kayi iya yinka" Ya amsa masa sanda yake.murda handle na qofar parlor din. Dasauri ya miqe abdii din yana kashe system din.

"Zan iya rakiya?" Ya fada yana daga yatsarsa. A nutse haisam ya juyo ya kalleshi,sai yaga ya wani narke alamun roqo yake yana tsoron kada ya hanashi.

"Bismillah" Ya fada yana motsa kyawawan labbansa.

Wani dadi abdii din yakeji,jerawa da captain obbo din kawai wani dadi da alfahari yake sanyashi ji,yana jin zuciyarsa cike da fatan shima wataran ya zama kamar haka. A duk sanda suke tafiya kaman haka cikin gidan,yaga yadda hadimai ke gaida obbo din dariya abun ke bashi,ba shakka inda sunsan LU'U LU'UN da suke rayuwa tare dashi....ba shakka idan da sunsan YARIMAN dake rayuwa a masarautarsu qila da jan ciki zasu dinga wucesa,saidai shi din ko acan Allah ya masa daukan rayuwa da sauqi,baya daukan kansa a bakin komai.

∞Tun daga nesa idanunta suka hange mata shi,nesan data zame mata kamar wata kusa saboda tarin kwarjinin da taji ya fara dukanta. Idanunta ta rufe ta kuma budesu tana gayawa kanta da kanta cewa itadin mutum ce me daraja da tafi qarfin wani qaramar halitta irin wannan ya qalubalanceta ko ya saka mata shakka.

"Ku gaya masa ya dakata inason magana dashi" Tayi magana da tafisu da sauran hadimai biyu maza dake bayanta.

"An gama" Suka fadi suna qara sauri don su riski haisam daga inda yake su sanar masa da saqon mammina.

"Inason naga yanayin fuskarsa.....inaso in samu tabbacin saqon dana aike masa ya riskeshi?" Ta fada qasa qasa,tana magna da tafisu,idanunta akan haisam.

Sau daya tak ya kalleta yayi zuzzurfan karatu game da abinda ke shimgide a zuciyarta. Siririn murmushi ya saki cikin qasaita da izza wanda kai tsaye ya wuce ya kuma zarce zuciyar mammina duk da daga nesa take hangensa.

"Na bata wannan damar" Ya bawa hadimin amsa. Da mamaki yadan dubeshi na yadda yake fadin ya bawa giwa damar ganinsa amma sai kwarjininsa ya hanashi qarasa kallonsa da kyau. A nasa sanin,muddin ta buqaci ganinka kokai waye ba amincewarka take buqata ba,sanarwar da tayi yana gaya maka cewa ka tsaida duk wani uzurinka ne kawai ka saurareta.

Isowarta daura dasu yayi daidai da dauko kujerar da hadiminta yayi ya dasa mata a nan tsakiyar hanyar,tunda hanya ce dama ta iya su isassu ba kowa ya isa ya bita ba.

Wani abu ya tasowa abdii,girma martaba dama isar da masarautar JIMMA ke da ita ya motsa masa.....jinin jimmawa da martabar sarautarsu,sai shima ya taka da hanzari ya dauko kujerar yana ajiyewa haisam din.

Maimakon ya zauna saiya karbi kujerar kawai ya maidota gabansa yana dafe dukka hannayensa akai idanunsa akan mammina data zubawa abdii su tana kallonsa cike da mamakin WAYE SHI KUMA?.

Ya lura da kallon da takewa abdii,kuma shi kansa yasam abdii din yayi mafi girman motsin dabai kamata yayi ba.

"Ka bamu guri abdii" Haisam ya fada don kade kallonta dama dukkan tunaninta akan abdii din. Murmushi ta saki tana girgiza kai a nutse,nutsuwar da sam babu ita a zahirin zuciyarta.

"Yayi zamasa......ka zauna mana?" Ta fada tana masa nuni da kujerar dake gaban nasa wanda abdii ya miqo masa. Kai ya girgiza,sannan ya rusunar dakai cikin girmamawar da ita kanta bata zauna mata a inda duk wani girma da ake bata yake zama ba.

"Bai kamata ba.....tsaiwa ita ta kamata ranki ya dade" Shuru tayi tana juya amsarsa a ranta.

Shurun ya wanzu,kafin a hankali yaren oromo ya harba a gurin

"Haleellaa du'aa Motii irratti raawwatame(Harin mutuwa akan motii)" Ta furta da haruffan da suka fita a bakinta daya bayan daya,labbanta suna motsawa,amma idanunta a kafe saman fuskar haisam din. Neman reaction take a tare dashi komai qanqantarsa.....neman wani canjin yanayi takeyi a tattare dashi ko yaya da zai bata haske,amma abinda ya jefa shakku da kokwanto a ranta shine. Ko yatsarsa bai motsa ba ballantana ta sanya rai zaiyi wani motsi da zai bata wata alama komai qanqantarta.

Shock ta shiga sosai,ta sauke hannunta daga fuskarta tana sake qare masa kallo.

"Haleellaan hanga namni dhokataan of mul'isutti hin dhaabbatu(kai harin bazai dakata ba.....har sai sanda wanda ya boye kansa ya bayyana kansa da kansa)" Ta sake fadi tana hada dukkan fuskarta guri guda.

Wani murmushinne can qasan ransa shima,wanda ko kusa ko alama bai bada alamu ko qwaya daya ba. Saqonta ya isa gareshi fes.....wawancinta yana sake bayyana. Duk inda mace take macace,hakanan duk inda takai ga zurfafa tunaninta ta qureshi tunanin d'a namiji a nan ya tsaya.

Ba abinda yake kalla a yanzu sai ZAITUNA A TAFIN HANNUNSA.....bayan ta kashe asalin ZEENATU ta shafe babinta a Ethiopia ta maye gurbin suna tarihi da kuma dukiyarta.....TA'ADDANCINTA NA FARKO da take tunanin ya jima da bacewa!.

"Daga gurin waye ka samu iznin kwana dakin akhnan a daren jiya?.....baka da masaniyar a al'adarmu hakan haramun ne?" Tayi tambayar da nuna izza da isa,can qasan zuciyarta kuma da manufar kunyatashi gaban hadimai da bayin da take tare dasu.

"A al'adar ba'abzine.....bata inda namiji yake da ikon kwana dakin matarsa harsai an miqata gidansa......kana da qarancin sani game da al'adunmu.....nme yasa zaka takesu kayi gaban kanka?" Ta sake fadi cikin izgili da nuna isa.

Readers Also Read

More by Huguma