L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 60
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 60: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 60. Bayason ya zuba mata dukka idanunsa ya hanata cewa…
3,362 words
Bayason ya zuba mata dukka idanunsa ya hanata cewa komai,yanaso ya karanci abinda ke sakaye a zuciyarta......don haka bai kalli cikin idanunta kai tsaye ba sai fuskarta kawai,wani irin abu yana tasiri a ransa......JININ OROMO da asalin sarautar gidan aba jifar suna motsa kowaccs jijiyar jini ta jikinsa.
Sosai abdii dake tsaye a bayansa ya zuba mata idanu. Cikin ranshi yakeji inama ace cikin jimma suke a yanzu haka?,inama ace ba boyayyen aiki bane ya kawosu agadez?,shakka babu da sai ya sanya matar ta cika da nadamar yadda take magana da prince din nasu. Baisan me yasa haisam yaketa dauke abubuwa da yawa daga gareta ba,bata ca canci wannan kawaicin ba.
A nutse ya juyo da kujerar yana dora tafin qafarsa guda daya akai. Idanunsa fes a kanta,muryarsa da wani madaidaicin sauti dake nuna qarfin da zuciyarsa dama dukka gangar jikinsa suke dashi. Qafarsa dake sanye cikin takalmin asalin fata saqar qasar italy tabi da kallo. Gabanta yayi wani mummunar faduwa,wannan din wani sign ne na alamun qanqantarwa da rashin bada girma a qabilar oromo,saita zarce da duban fuskarsa da sam bata nuna fushi ko dimuwa ba. Kai tsaye yake duban idanunta a wannan karon
"Bana buqatar neman izini a sanda zan shiga halastaccen muhalli a gurina.....na shiga a matsayin MIJI ba dan aike ba.....ba bawa ba ba kuma hadimi ba.....sannan kuma na shiga a matsayin me ceto.....shi kuwa me ceto baya jiran umarni kafin yayi ceton,a al'darmu ceto gaba yake da neman izini.....ceto baya jiran ixini,izini ne yake jiran ceto a koda yaushe......a tamu al'adar.....MIJI yana zama abun tir a sanda ya gaza kare MATARSA da nauyinta yake wuyansa,bawai a sanda ya karya wata al'ada ba da bata da alaqa da addini......amma idan kina ganin kasancewata da ita a daren ya zubda mutuncinta.....kina iya shelantawa duniya ki fadiwa kowa laifina a fili" .💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 103*
Idanunta ta lumshe a hankali tana jin yadda ya sauke mata magana masu zafi,amma cikin wani salo na taushi da kwantar da harshe,ba hayaniya ba daga murya,amma nauyinsu da zafinsu a gurinta yakai wani mizani me girma a zuciyarta. Yanason mata rami ya jefata ne a ciki,me zata ce ya kaita gurin Akhnan din a irin wannan daren?,wanne amsa zata bayar a sanda idanuwa zasu kalleta da tuhumar ya akayi tasan da wanzuwarsa a dakin duka daren?.
Fes ta sake bude idanunta a kanshi,baici banza ba,ba kuma zata qyaleshi ya bata kalar wannan amsar gaban hadimanta ba kuma ya tafi salin alin
"Ku matsa ku bamu guri" Ta fada cikin bada umarnin daya sanyasu watsewa da sauri. Yatsa kawai ya murzawa abdii ya motsa daga gurin,yadda ya murza yatsan yaja hankalinta matuqa. Wani yanayi ne na salon izza da sarautar Ethiopia.......salo ne na isar sarauta ga BASARAKEN oromo. Saita sake zuba masa idanu gabanta yana faduwa,amma wani halin na rashin son faduwa ya mamayeta.
"Ni na fara nemanka da wannan auren" Ta fadi tana dakatawa
"Baka bani amsa ba" Ta sake dakatawa,yanayin daya tabbatar masa maganar tana da girma da nauyi a zuciyarta.
"Saika barni.....mahaifinta kuma ya kiraka,saika amsa masa ka kuma karba" Ta sake fadi tana nutsa idanunta cikin nasa,sannan cikin daga murya kadan da kaurarata ta dora.
"Me yasa baka sanar dani ba.....me yasa naji labarin daura auren nan kamar bani da hannu a ciki?" Ta fada cikin fushin da taketa qoqarin danneshi tana kokawa dashi,maganar tafisu tana mata yawo akai inda tace 'kamar akwai izza a tare dashi,idan kikace ta fada ta umarni nakai tsaye zaki biyo masa ba zaki taba nasara ba giwa.....kamar dabi'unsa na SARAKI ne'
Wani irin shuru yayi mata yana dubanta,irin shurun nan me sanya shan jinin jiki ga mutum,shurun daya sanya mammina komawa hayyacinta,saidai ba zata barin ba ya gane hakan bane.
"Ki kula da yadda kike tambayata" Amsarsa ta fito da wani yanayi daya sanya mammina buda idanunta dukka a kansa. Kansa ya jinjina mata shima yana ci gaba da dubanta,abinda yake bata tabbacin eh maganar daya fada din yana nufin ita dince daga bakinsa kuma ta fito.
"Ka kula da wadda kake magana da ita" Itama ta mayar masa da shigen salonsa. Wani murmushi yayi na gefan baki kadan,sannan ya sauke qafarsa ta dama dake saman kujerar ya maida ta hagu.
"Ba dole bane saina sanar dake.....duk da kafin ke wasu mutane da sukafiki cancanta da kusanci da ita sun nema min ita?.....ko sun nema mata ni?" Ya fadi kaman ya rasa yadda zai bada maganar. Shigarta maganar tayi......kafin ita kuma?,waye ya rigata?.......SAFIYYA? Ta tambayi kanta tunaninta yana girgiza.
"Lokacin da kika nemi aurena.....ban amsa ba saboda ban shirya ba....duk da ba kece ta farko data nema hakan ba....." Ya sake maimaita maganan yana duban idanunta sannna ya dora.
"Sanda mahaifinta ya kirani ya bani aurenta.....na karba ba kuma don roqo ba....sharadi ko wata qa'ida ba.....na karba ne saboda na yanke shawara" Ya sake fadi kansa tsaye cikin wani coolness da mammina ta tabbatar ba iyakarsa kenan ba......akwai wani abu a badini
"Bana dawowa na nema izini ga wanda bai mallaki shawarata ba"
"Wannan auren baizo da tsari ba sam....yazo da gaggawar da zata iya kai hankulan wasu akan manufar yinsa" Ta fada da hanzari ganin yana sauke qafafunsa qasa......tana tsoron rasa control nashi.....tana tsoron rasa wannan gabar......tana buqatar juyashi daidai da buqatar ta.
Wani kalan murmushi ya sauke yana daidaita tsaiwarsa sosai,da wani yanayin da zai gaya mata CIKIN IZZA DA IKO AKA HAIFESHI.
"Idan labarin yazo miki ba zato ba tsammani to haka rayuwa take ga mutumin da bai zama cibiyar hukunci ko yanke hukuncin ba" Wani abu ya naushi zuciyarta,magana ce ya yaba mata me girman gaske,ta maida dubanta a kansa sanda yaci gaba da takawa yana barin gurin,alamu dukka suna gwada mata gurin Akhnan zai shiga.
"Ki saba da jin labarai daga waje.....ba daga bakina ba" Ya qarasa fada da wani salon izza da yakejinta a yau mamminar ta motsa masa shi.....jinin aba jifar ya soma harbawa a jikinsa da qarfin gaske. Dukka wannan suffar daya azawa kansa yaji kamar zai gagarata riqeta nan da wani dan lokaci kadan.
Da sauri tafisu ta dafeta wadda ta garzayo kusa da ita da gaggawa ganin yadda komai ya gudana. Ta tabbatar komai zai iya sake damalmalewa tsakaninsu.
"Kada kice komai.....akwai wani abu cikin jininsa,tabbas akwai wani abu me qarfi a jininsa,ki lallabashi harki cimma burinki"
"Tafisu?....meye banbancinsa da sauran mazan dana taba sarrafawa?" Mammina ta jefa tambayar ga tafisu tana dubanta duba na mamakin da haisam ya shayar da ita
"Baki buqatar fushi a daidai wannan lokacin sam,bashi da amfani a tattare dake" Tafisu ta fadi tana dannar mammina.
"Akwai lokaci....a sannan ne zaki nuna masa qaryarsa.....a sanda rayuwar Akhnan ta dawo hannunki zaki sarrafata yadda kikeso ki kuma b'alb'alta rayuwarta dama ta ubanta data uban dukkan wanda kikaga dama" Maganganun suka sauka a kunnen haisam daidai sanda idanunsa suke sauka saman fuskar Akhnan din.
Har yanzu tana zaune tsakiyar throw pillows din,idanunta wannan karon akan system din dake gefanta suna magana da ameesha,dankwalinta yadan zame kadan wannan ya bawa kwantacciyar sumarta me sulbi daman fitowa ta gaban goshinta,fuskarta tayi fayau tayi wani haske me daukan hankali. Hannu ya sanya yasake danna Bluetooth din cikin kunnensa sosai,yana jin maganarta ta qarshe haka kawai ta sauka zuciyarsa da wani irin nauyi a kunnensa da qirjinsa. Ya yarda device dinne dan qarami a gurin,bai dauka zaiji wani abu me muhimmanci da yawa ba.
"Ya jawowa Akhnan.....gwargwadon wahalar daya bani.....gwargwadon yadda zan sauyawa rayuwarta fasali da la'antaccen yanayi....."
"Allah ya baki yawan rai" Maganan mammina yaji ta katse a kunnensa,muryar tamim cikin yanayi na haki ya maye gurbin tata.
Shigar qamshin cikin qofofin hancinta ya sanyata daga kanta a hankali daga fuskar ameesha dake system din zuwa bakin qofar,inda haisam yadan dakata kadan yana bada hankalinsa ga maganganunsu mammina......saidai kuma hakan ya sanya su aisa sun zaci kamar yana buqatar gusawarsu ne daga gurin,don haka aisa ta tattare kayanta,hakama shehnaz suna gaidashi cikin matuqar nutsuwa saboda tsananin kwarjinin da yayi musu. Da kai kawai ya amsa musu yana qarasa shigowa ciki don ya basu daman fita daga dakin,kowacce kaman zata kifa haka sukeji suka fice daya tana bin daya,abinda ya bashi daman maida qofar ya kulleta,ya kuma ci gaba da tsaiwa hannunsa saman handle din.
Ci gaba da duban ameesha tayi,amma kuma a wannan lokacin ta soma daina fahimtar bayanan ameesha din. Shuru takejin kanta da qirjinta,sai qamshinsa daya cika dakin ya kuma sanya bugun zuciyarta ya tsananta. Lumshe idanunta tayi tana tambayar kanta,meye dalilinsa na tsaiwa mata a qofa?,jiran girmamawa ko gaisuwa yakeyi?...
"Bazai yuwu ba" Ta fadawa kanta da kanta ba tare da tasan dukka kunnuwansa dama fiye da rabin hankalinsa akan maganganun mammina da tamim suke ba.
A hankali ta matsar da idonta zuwa ga siririn madubin da bai rabin fadin hannu ba,saidai yana da tsaho sosai wanda akayi wani ado daga gefan inda take zaune.
Fes idanunta suka sauka a kansa,tsaf ya fito ta cikin madubin,still hannunsa yana kan handle din,idanusa sunyi qasa yadda baka iya ganin qwayar idanun.
Idonta ta sauke daga kan qafafunsa. Ma'abotan dogayen yatsu farare sol,dogayen yatsun da kowanne samansa yake da wata gargasa a kwance. A hankali tayi sama da idanunta. Saidai kafin takai qarshe kwanyarta da zuciyarta sun gama lissafa mata
"GIANT ne" Tsahon data tabbatar idan ta tsaya a gabansa zata zama yana kallon tsakiyar kanta ne.
Kwantacciyar sumar dake habarsa zuwa kuncinsa guda biyu,cikakkiya da aka yiwa wani gyaran daya gagara tsallake qawar zuciyarta,idanunta suka gangara ga lips dinsan nan masu daukan hankali kamar wanda ke using lip balm. Shape din hancinsa daya zauna da wani irin yanayi me ban qaye tabi da kallo,wanda ya kaita ga girarsa wadda ta kusa haduwa da juna,kafin idanunta su zarme su sauka cikin manyan idanunsa da iya saninta ba'a bude suke ba a dazu,saidai a yanzun tana kai qwayar idanunta cikin nashi qwayar idanuwa hudu suka sarqafe cikin na juna.
Wani irin mugun kaduwa tayi,ta kuma janye idanunta da wani irin sauri tana maidasu kan system din,saidai banda wuyanta ba abinda ya nuna motsawar da tayi,abinda ya sanya wani miskilin murmushi yana subuce masa. Murmushin abu biyu ne. Da gaske tana da GIRMAN KAI DA IZZA irin na kowacce isashiyar mace. Ta sakankan kan ta cikin madubin kawai take qare masa kallo a fakaice,a nata tsammanin ita kadai tasan da zaman madubin. A sanda ta tabbatar kuma ya ganta tsabar JINKAI da K'I FADI ya sanya tayi wani reaction da zaka dauka arashi aka samu na haduwar idanunsu,bawai kallo take qare masa ba,tabbas ta gwanance wajen iya kare kai da maintaining steex dinta. Da gaske bata yarda komai ya taba wannan MARTABAR tata. Murmushinsa na biyu muryar tamim....muryar mammina......rudewar mammina da tashin hankalin da sound dinta ya gwada masa
"AN DAUKE ALMAZ RANKI YA DADE!!!".duk da baisan kalar ashar din qabilar abzinawa da yarukan da suke iya amfani dashi ba.......amma kuma zagi jikinsa yake bashi ta auna me qarfin gaske.
"An dauke almaz?.....waye?....yaushe?.....a ina?" Duka ta aunawa tamim wadannan tambayoyin da muryarta kamar wadda ta zare.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 104*
Disconnecting device din yayi,ya fara takowa zuwa cikin parlor din. Sallama yayi da muryarsa wadda a yau ta bada wani irin taushin amo.....taushin amon daya tuna mata da karatun qur'anin daya kwana jiya yanayi,ya bata wani yanayin bacci me dadi da kwantar da hankali. Karon farko ta daidaita muryar qira'ar jiya da tasa,sai a sannan ta tuna,ta lumshe idanunta tana sake budesu kan system din da ita kanta ba zatace ga abinda takeyi a ciki ba. Sai taji a sanda karatun yake dab da ita kamar yafi dadi akan daga nesa da take jinsa.
" Can qasan ranshi yana maimaito kalaman mammina......yana hasashe da hangen yanayin mammina da yadda zata fuskanci wannan qalubale. Ba wannan ne kadai challenge din daya shirya bata ba.....ba wannan ne kawai rudanin daya shirya bata ba.....amma wannan shine abu na farko da zai fara aike mata a matsayin gargadi.
Sau daya tak ya kalleta ya zare idanunsa daga kanta. Sanda tayi zurfi wajen satar qare masa kallo,shima nashi idanun suna kanta,yana jira yaga adadin gudun ruwanta.
Tana latsa system din amma kuma tana jin takunsa har cikin jininta,duk taku daya da zaiyi sai taji kamar yana matse space din dake tsakaninta dashi fiye da kima,qamshinsa yana sake cika mata hanci,yana kuma tsananta bugun zuciyarta.
Ga mamakinta sai taga ya wuceta,ya zarce zuwa window din dakin ya budesu sosai kaman yadda yayi a daren jiya. Ya juyo ya dawo da cikakkiyar nutsuwarsa. A hankali ya tattako zuwa gabanta,ya tsugunna saman qafafunsa idanunsa aka hannunta.
Cak wuta ta dauke mata,taqi daga idanunta ta kalleshi kamar batasan da wanzuwarsa ba a gurin,yayin da zuciyarta kuma ke wani irin bugawa,qofofin hancinta kuma suna zuqo mata qamshinsa sosai fiye da kullum,dakatawa da motsa yatsunta dake saman system din tayi,tana jin kusancin sun mata yawa,tana jin kamar ya cike gurin gaba daya,tana jin kamar ko yaya tayi motsi jikkunansu suna iya taba na juna.
Idanunsa sosai cikin fuskarta,yana dubanta da wani irin yanayi na sake karantar halayyarta. Jin kai izza da qi fadi,kamar ba ita bace jiya ke tsoron qanqanuwar aba irin allura ba,kamar ba ita ta suma kawai saboda ance an daura mata aure ba......kamar ba ita ta kwanta tana rusa kuka kaman jaririya ba. Duka a bayan wannan izzar akwai wadannan dabi'un na tsoro raki da sakalci a tattare da ita?.
Hannunsa kawai ya shimfida yana miqa mata,taja wasu sakanni kafin ta daga kanta tana duban idanunsa. Wani irin abu ya sake sauka cikin nata idanun. Baqar rigar jikinsa ta haskashi da yawa,ta kuma haska fatarsa da yawa,tana shirin janye qwayar idanun nata ya mata nuni da alamar ta bashi hannunta,jim tadan tsaya tana tunani,ta yaya zata dora hannunta saman nashi?,to amma kuma idan bata bashi ya cire mata cannula din ba sai yaushe za'a rabata da ita?.
"Idan na tashi bazan sake dawowa na zauna ba" Ya furta da zaratan idanunsan nan dake kafe a kanta. A hankali ta daga hannun nata tana miqa masa gami da sake daure fuskarta,ta kauda fuskar gefe tana hada rai kamar wadda aka yiwa dole,can qasan zuciyarta tana wani irin bugawa,tana jira taji hannunta sun sauka cikin nasa tafin hannun,saidai ga mamakinta sai tajisu saman pillow.
Qaramin pillow ya sanya a tsakaninsu,wannan ya bawa hannuwanta daman zama saman pillow din,baiko taba koda fatar hannunta ba,ya soma cire plaster din a hankali. Idanunta ta runtse,yayin da kuma can qasan zuciyarta wani abu me kama da haushi ya d'arsu a ranta. Me yake nufi da ajiye hannunta saman pillow?,don ya samu daman ganin hannun nata ma cikin sauqi har haka?,ko yana zaton son hada hannu takeyi dashi?.
"Wash" Bakinta ya subuce ta furta a hankali tana sake runtse idanunta saboda fara taba cannula din da yayi. Dakatawa yayi daga qoqarin zareta da yakeyi,ya daga idanunsa a hankali ya ajiye a kanta. Fuskarta tana kallon wani gurin ne daban......kai tsaye dubansa ya sauka akan dogon wuyanta daya bayyana saboda zamewar dankwalin kanta. Ragowar gashinta me sulbi wanda ko tayi parking baya kamuwa yana kwance saman farar fatar wuyanta,hakan sai sake qawata gurin sosai.
Idanunsa ya janye yana lumshe idon nasa,har cikin jininsa yaji wani abu ya harba,sai ya maida dubansa a nutse kan hannun yana qarasa janye cannula din,ya kuma maida cotton wool gurin sannan ya miqe a hankali ba tare da yace komai ba ya taka a nutse ya fice bayan ya jefa cannula din cikin dust bin.
A hankali ta waiwayo,idanunta suka sauka akan inda ya tashi,saidai tamkar bai tashi ba,kamar yana gurin har yanzu sanadin qamshin lallausan turarensa daya bar mata. Qaramin tsaki taja kadan tana shafa inda aka cire cannula din. MALAMI NE KO LIKITA?,ta yiwa kanta tambayar da sai gata a zahiri ta bakin shehnaz data fado parlor din.
"Wannan man din naki.....MALAMI ne ko likita?,na kasa banbancewa" Cewar shehnaz hankalinta kwance tana qarasowa ciki. Idanunta ta daga ta watsa mata harara.
"Da zai fita da kin tsaidashi kin tambayeshi......amsar da nakeso na sani kenan nima.....don ku kanku bakusan wanda kuka bawa d'iyar da kuka gaji da ita ba saboda bakwa sonta......ko tsafi ma yakeyi duka ba wanda ya damu da hakan don salwantar rayuwar akhnan ba komai bane". Wani irin dariya shehnaz ta saki tana kwantawa.
"Allah bazai taba bawa mutumin banza kalar kwarjinin da wannan guy din yake dashi ba......na rantse idan har zan samu irinsa inaso koda ba'asan asalinsa ba......nidai an gama min komai......kin ganshi kuwa yau?" Shehnaz ta fada ta miqe tana zama sosai tana duban akhnan.
"Ina kyautata zaton ya hada jini da larabaw......."
"Shehnaz!.....ya isheni hakanan" Akhnan ta fada murya a kaurare,idanunta da fuskarta dukka suna nuna fushi.
"Nifa sai kinyi haquri dani,bazan fasa fadin abinda na gani ba......kuma wallahi kome zaki fadi akan shi din TSINTACCIYAR MAGE NE bazan taba yarda da hakan ba.....komai nashi perfect ne,bani kadai kuma na fada ba" Shehnaz ta sake fadi tana kwanciyarta abinta ba tare data samu da yanayin akhnan ba.
"Me yasa kowa yake yabonsa?,me yasa suka kasa gane cewa yana da naqasu?,me yasa suka kasa gane cewa ya gaza?......a dauke ilimin addini.....eh ta yarda yana da daidai nasa......amma kuma ilimin zamani fa daya zamana shine JIGO kuma JAGORA a idanun kowa?".
"Ki shirya wasu abubuwa mana.....ki tsarawa kanki yadda kowa zai gane bai iya komai ba.....bai kuma san komai game da ilimin zamani ba......kiyita kunyatashi mana harsai ya tabbatar da cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE......har sai ya gane zaren ba kalar yadin bane" Wani qaramin murmushi ya subuce mata saman fuskarta,ta girgiza kai a hankali. Tabbas wannan itace hanya mafi sauqi da zata nuna masa TAZARAR DAKE TSAKANINSU......itace sassauqar hanyar da zata nusar da sultane kalar rashin dacewar dake tsakaninsu,wataqila ma ya hango illar da hadin auren zai haifar tsakanin DIYAR BASARAKE da malami. Wani murmushi ya sake subuce Mata.....qila ta samu mafita ne a sauqaqe,ba tare da tabi doguwar hanyar tsarin mammina ba.
*M A M M I N A*
Tsaye take a filin gurin ita da duk wani boyayyen hadimi nata dake mata gurbatacciyar hidima. Mutane ne dake rayuwa cikin gidan sultane suka kuma saje da bayi da hadiman gidan ba tare da sanin mutanen gidan ko nuna wata alama da zata bayyana maka akwai wani rayuwa suna da identity a jikinsu a boye ba bayan wanda ake ganinsu dashi.
Tun daga wancan ranar da aka rasa almaz har zuwa yau bata kwanta tayi bacci ba,idan bacci ya dauketa to barawo ne.
Tana lissafa ta yaya zata dauko tsintuwa daga wata qasar,tana riritata da zummar cin gajiyarta da alfanunta,kuma katsam kawai sai ace ta bace cikin rairayi da sahara?.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ina me sake maimaita muku tambayar da har yanzu na kasa sanin amsarta a karan kaina da kuma ku kanku......su waye suka shigo har cikin gida suka dauki AJIYATA cikin sauqi har haka?,harda sukunin ajiye rubutacciyar takarda suka samu.....wanne irin sakaci ne da sassauci da aikinka TAMIM?" Ta jefa tambayar ga tamim wanda kiran sunansa kadai da tayi ne abinda ya dawo dashi cikin tunaninsa. Fes abinda take magana akai baiji ko ya riqe ko qwaya daya ba,don shima a yanzu a wannan qadamin mafitarsa yake nema....nasa tunanin ya karkata ga yadda zai lashi kalar ZUMAR daya tabbatar tunda uwarsa ta kawoshi duniya bai taba lasar irinta ba. Qasa yayi da kansa yana nuna girmamawa a fili,saidai badini zuciyarsa da gangar jikinsa ta fara gajiya da tattali da kuma binciken KAB'AKIN da ba'asan ranar samuwarsa ba. Kowanne shekaru watanni kwanaki da darare suna qarar dashi ne wajen shiryawa wannan lokaci,saidai a yanzu jikinsa da hasashensa suna bashi akwai wani babban qalubalen da yake tunkararsu.
"Wannan ya nunamin ya kuma bani tabbacin lallai Al-saamit yana tare damu.....yana kallonmu kuma yana rayuwa damu.....indai sheikh haisam shine Al-saamit.....lallai zai ruga zuwa Ethiopia don duba mahaifinsa motii,jininsu qarfi ne dashi,sukan zabi JINI akan NASARARSU......idan kuma ba shi bane.......TO WAYE?" Tayi musu tambayar tana duban fuskokinsu daya bayan daya. Shuru ce ta kasance amsar kowa a cikinsu. Dukkaninsu kusan basa fatan sheikh haisam ya kasance wanda suke zargin,don sun sani muddin ya kasance shi dinne.....basa jin qamshin nasara a tattare dasu......kowanne FADUWA kawai yake hangowa qasa warwas a kansu,faduwar kuma tana shirin RASA RAYUKA MASU YAWA.