L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 61
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 61: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 61. "Ba bada kwana uku......kwana uku kawai duk inda almaz…
3,372 words
"Ba bada kwana uku......kwana uku kawai duk inda almaz yake.....muddin yana qasar niger da maqotanta a nemoshi" Ta fadi maganar tana juyawa da sauri tana barin sansanin.
"A gayawa me wada......ina buqatar ganawa da dukka bayi da hadimai dama duk wanda ke rayuwa qarqashin umarni doka da tsari maza da mata na gidannan,yaro da babba a filin taro na bayan gida.......a shaidawa sheikh haisam" Ta sake fadi wasu abubuwa suna qulluwa a zuciyarta.
"Me hakan ke nufi?" Tafisu ta tambayi mammina dake takawa don komawa zuwa ga motarta.
"Inason sake gwaji a kansa tafisu,har yanzu ban yarda shi din ba jinin aba jifar bane.....ban yarda shi din ba jinin ibraheem bane" Idanu tafisu ta zuba mata,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,ta saki qaramin murmushi sannan a hankali tace.
"Allah ya taimaki uwar dakina" Cikin nuna kambamawa da bayar da qarfin gwiwa.
*MORSA SAFIYYA*
Wata cikakkiyar nutsuwa ta samu a kwanakin,irin nutsuwar da ta jima rabonta da ita. Irin nutsuwar da tayi hannun riga da ita tun shekaru masu tsaho da suka shude. Shirye shirye takeyi sosai na gudanar da duk wani abu daya shafi auren D'IYA ga mahaifiyarta,shiri takeyi na gaske tamkar wadda zata aurar da yara goma. Cikin tsanaki take shirya komai,kama daga dukkan wani kayan qawata gida da diya macen da za'a aurar take buqata.....shirin gudanar da baki na alfarma,suturar da akhnan zata sanya,falaak da ita kanta. Kudaden gudanar da hidimar bikin,sabon dinki ga kowanne hadimi da bawa na gidan....sai kuma babbar shahararriyar me gyaran jikin nan data karade qasashen sudan niger mali dama sauran qasashen africa.
A jikinta takejin aurar da diya zatayi kamar a karon farko,don haka gagarumin shiri takeyi silently ba tare data qara bi takan akhnan ba ko wani magana ya sake hadasu. Kawai abu daya ta sani shine.....a wannan karon zata fitowa da akhnan zafinta a duk sanda tace zata bijirewa duk wani shirye shirye nata......zata gwadawa akhnan ita din UWARTA ce da gaske,kuma ba'a sauyawa tuwo suna.....lokaci yayi da zata gwadawa mammina JINI YAFI RUWA KAURI,lokaci yayi da zata tunasar da mammina ZUMUNCIN MAHAIFA ba wani dan guntun makirci daya isa ya rabashi.
Tun a yanzun ta fara aike zuwa ga kowanne dan uwa da dangi na kusa dana nesa tana shaida musu kowa ya zama cikin shirin auren diyar safeena. Abinda kawai ya rage mata jiran dawowar sultane,su tattauna idan akwai inda yake buqatar gyaran shiri sai a gyara. Bata jiran sultane don karbar ko sisi a hannunsa......tana ji cewa koda zata qarar da dukka abinda ta mallaka akan diyar safeena wannan karon bata biya koda digo daya na zumuncin safeena da halascinta ba a kansu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 105*
Tare da falaak da hairaan suke gudanar da komai,hatta kuma da falaak bata gwadawa akhnan akwai gagarumin shirin biki ba da momma din keyi ba.
Abu guda daya ne kawai ya tsayewa morsa safiyya a rai. Ta yaya za'a lanqwasa akhnan a maidata MATAR AURE TA GASKE?. A nata tsarin a nata burin a kuma nata mafarkin,kaman yadda ta horar da hairaan.....har hakan ya siya mata soyayya me girma a zuciyar mijinta.... Kamar yadda ta horar da falaak kuma ta tabbatar ba zuciyar wanda ba zata mallaka ba ba tare da asiri ba......haka takeso akhnan ta kasance. Tanason akhnan tasan me ake kira da AURE......tanason akhnan tasan me ake kira da BIYAYYAR MIJI......tanason akhnan tasan sirrikan mallakar miji da sake shiga zuciyarsa.....don ta tabbatar akan AURE gaba daya akhnan din bata da sani kwata kwata.
Sun zauna da hairaan sun tattauna,amma a wannan karon hairaan kanta dariya ta dinga yi.
"Momma wannana aikinki ne......ke zakiyishi.....bana tunanin akwai wanda biftu zata zaunawa yayi mata wannan karatun,saidai ki dauki wannan nauyi kawai,ki koya mata ki kuma karanta mata abinda ya samu.....sauran aikin sheikh haisam ne,nauyin ya hau wuyansa........sauqinta daya maza irinsu dama hatta ga matansu malamai ne.....suna kuma zurfafa nazari da uzuri ga matansu,balle irin sheikh haisam.....tabbas zata samu rayuwa sama da duk yadda take mafarki,kuma kuma zaku sameshi sama da yadda kuke fata,ni nayi imani da wannan". Maganganun sun shigi momma,to amma a yanzun ita da bata da cikakken zama a kwanakin bata jin tana da chance,saidai ta yanke shawarara duba qwararriyar malama me hikima koda na sati daya ne su zauna da akhnan din ita saita qarashe sauran aikin.
★Takardu biyu ne suka iso gabansa da dukkaninsu suka sanya murmushi subucewa saman kyawawan labbansa. Takardar farko ta mammina ce wadda itace silar asalin murmushin nasa......takarda ta biyu kuwa daga akhnan ne.
Rubutacciyar saqon gayyata zuwa bikin yaye dalibai a babbar makarantar secondary ta kwana ta 'yammata dake garin agadez.
Already wannan sultane ya kirashi,sunyi magana,ya kuma nema alfarmar
"Ina nemawa diyata alfarma mijinta ya rakata,itama da kanta ta buqaci hakan" Maganar ya zowa haisam a bazata,mamaki kadan ya kamashi,saidai isowar takardar gayyatar a yanzu gabansa hade da wani qaramin akwati me dauke da kayan sawa ya bashi mamaki.
Yana daga zaune yayi relaxing ya sanya abdii ya dinga daga kayan daya bayan daya. Murmushi ya subuce a hankali,abinda ya sanya abdii dubansa cikin mamaki.
"Ka ninkesu,ka bawa salaana" Ya fadi a taqaice kawai Yana maida hankalinsa akan aikinsa. Tsaf ya karanci inda komai ya dosa,wani abubuwan yanzun yadda suke tafiya murmushi kawai suke bashi.
"Amma kamar basu qarasa kayan da kake raba musu obbo" Abdii ya fadi yana daga kayan gami da sake jujjuyasu. Kai ya daga ya kalli abdii kadan sannan ya gyada kai.
"Na sani.....wannan kyauta ce kawai,ba lokaci ne na rabon sutura ba". Bai sake cewa komai ba abdii din ya ninke yana maidasu jakar,ya dauka yana ficewa.
*JIMMA(Ethiopia🇪🇹)*
*_Abba jifar palace_*
Cikin makeken dakin da aqalla zai iya daukan kayan gado na alatu set biyar.....tafkeken bedroom dake dauke da gadaje qwaya biyu,wall wardrobe da komai set biyu da sukayi nesa da juna saboda yalwar dakin.
Daga saman daya daga cikin gadajen take kwance. Saamee ce kwance rub da ciki. Manyan curtain masu nauyi tsada da alfarmar daraja da aka zagaye dakin dasu ya sanya ba wani cikakken haske a dakin,uwa uba kuma ta lullube kanta da duvet fuskarta na tsakiyar pillow.
Hawaye takeyi sosai,har tana jin jijiyoyin kanta suna bugawa saboda ciwon da suka fara. Ta tsincin zancan ba tare da tasan zata jishi ba.....zancan da ya kusa sanya zuciyarta ta buga saboda fargaba da kuma tsananin razani. AUREN CAPTAIN OBBO. Idan tace ya mata kama da mafarki ma tayi qarya.....wani abune daya zame mata sama da mafarki wajen sanyata a tsananin razani da tashin hankali.
Ta jima tana fargabar zuwan wannan ranar......ta jima tana tunanin yadda haisam din zaici gaba da kasancewa me sauqaqa kallonsa akan diya mace ba tare daya samu wata ta fusgi hankalinsa ba. Koda shi bai qawatu da kowacce mace ba,lallai ba shakka ta sani wataran zaa samu wadda zatayi nasarar janyeshi gareta.
A jigace ta miqe tana ture bargon jikinta,sannan ta lalubi hanya zuwa toilet don rage fitsarin daya cika mata mararta,tana kuma jin zuciyarta kamar zata fashe.
Daidai lokacin kyawawan 'yammatan oromo din guda biyu suka tura qofar dakin suna shigowa. Rumaisa aba jifar da kuma Aanani aba jifar. A halittar ne yawan magana......fara'a da son tsokana,har wani lokaci yayarsu KANSAA wadda ita ke bin sheikh haisam takance.
"Kamar ba daga jinin aba jifar kika fito ba?" Aanani din ita da hussam su kadai ne halinsu daban,amma za'a iya cewa dukkanin yaran nanay suna da wani hali na miskilanci da jinin sarauta da sukayi gado daga bangaren nanay da motii din gaba daya. Shi yasa izzarsu ta daban ne,da gaske kuma jinin yake zagayawa a jikinsu saboda gadonshi da sukayi ta uwa da uba. Saidai kuma tasirin ilimi da tarbiyya sosai yake gwada aikinsa a kansu. Basu iya wulaqantar da d'an adam ba komai kashinsa.
"Har yanzu mamaki nake yaa rumaisa.......kaman ina mafarki fa......Captain da aure?.....yaushe yaa rumaisa?......yaushe ya tsayar da idanunsa ya kalli macen har tantance tayi masa?. Yaushe dukka ta cancanta ta tsallake tulin uban tsarikansa?,yaushe ta cinye dukka wadannan jarabawar tasa?"
"Aanani mana?....ahaan?,daukomin kawai na wuce,idan ya dawo kya ita tambayarsa kamar zaifi sauqin samun amsoshinnan" Rumaisa ta fadi cikin daurs girarta. Baki Aanani ta rufe da tafin hannunta tana dariya.
"Koda wuqa bazan iya ba kin sani,shine zakimin turin mutuwa." Goye hannuwanta sosai rumaisa tayi a qirji tana duban Aanani din. Ta sani,tafi kowa sanin Captain sheikh din. Har yanzu tana tuna yadda ya kori abeed da salon tambayoyinsa?,wai aure ba abun wasa bane.....koda nanay tayi magana sai ya bata haquri,ya fadi mata ko shine idan ya tashi aure sai matar ta cinye tarin jarabobin da tambayoyinsa harma da gwaji.
Yaaa khansaa tayi dariya sosai a sannan
"Duka ban manta ba,kuma nima ina yiwa kaina wannan tambayar,amma ni dake duka wazai iya tunkararsa?. Mu tsaya kawai mu gani,lokaci zai bayyana komai" Rumaisan ta amsa mata gudun kada ta tsaidata,don hadimanta suna waje suna jiranta da zasu rakata daukan jarabawar da zatayi ayau din..
Wani dan juyi Aanani ta saki,ta dauki remote ta danna wani wani locker dake gefan gadonta ya bude kanshi da kanshi,ta qarasa tana cirowa rumaisa takardun.
"Naga yaaa kansaa tazo,sun qule da nanay......nasan duka shirye shirye ne......kaman bazan iya jiran lokacin da Captain zai iso da amaryarshi ba.....inaso.inga gwanar sa'ar nan ta duniya" Ta qarasa maganan tana miqawa rumaisa takardun,saidai bayanta da taga rumaisa din tana kallo ya sanya itama ta waiwaya.
Saamee ce ke takowa a hankali,hirarsu tana sake kashe mata jiki gaba daya da dukka wani hope nata.
"Baki da lafiya ne saamee?" Rumaisa ta tambaya cikin kulawa. Da qyar ta iya qaqalo murmushi tana kada kai.
"Lafiya lau nake....ciwon kaine,amma nasha magani,ina sanya rai zai sauka in sha Allah a kusa". Kai rumaisa ta jinjina,ba kuma don ta yarda ba
" Allah ya sawwaqe" Ta fadi daidai sanda ake na'aurar dake maqale da qofar dakin kaman yadda yake a sauran dukkanin manyan dakuna na gidan take shaida musu isowar mutum da neman izinin shigowa. Haka hake a tsarin gidan,kowacce qofa saida izinin me dakin,saidai dukkanin 'ya'yan motii anyi register na finger print din kowa da sauran qofofin da suke da alaqa dasu na al'amuran yau da kullum,kai tsaye suna iya buda kowacce qofa su shiga,saidai duk da hakan idan ba dakunansu ba sukan tsaya na'aura ta shaidawa mamallakin dakin,sai idan shigar ta gaggawa ce ta taso.
Sunga me neman izinin,obsa ce,daya daga cikin bayin rumaisa. Sanye da asalin tufafin da dukkan wani bawa dake qarqashin gidan sarautar aba jifar ke amfani dashi muddin macace.
Tufafi ne me launin fari da aka yiwa ado me kyau da jan zare,cikakkiyar sutura da aka dinka daga zare me laushi kyau da daraja da sheikh muhammad haisam ya sanya aka samar da ita wadatacciya ga kowanne bawa da hadimi na gidan. Be yarda kowa a cikin su yayi maimaicen sutura ba,kwanaki biyar dinnan da suke sanya kalar kayan kowacce rana wami daban kake sakawa saboda tabbatar da tsaftarsu. Sannan da zarar ka gaji dasu kana iya bayarwa,zakayi magana ne kawai cikin dakin ajiya na gidan a sake baka sabo dal adadin da kake da buqata,kamar yadda ranakun alhamis da juma'a suka kasance ranakun da duka wunin zaka sanya kalar tufar da kakeso,duk da ragowae ranakun ma a iya awannin aikinka ne kawai zaka sanyasu saboda fidda tsari da cikakken tsaro na gidan,abinka da JININ hukumar binciken sirri da qwarewa ta farin kaya.
Hadimai dake sashensa gaba dayansu maza ne.....tasu suturar kuma tasha banban data kowanne hadimi.na gidan,launinta da kuma tsarinta,kamar yadda girma da kimarsu a gidan fita daban dana saura.
Kai tsaye ta nufi inda rumaisa ke tsaye,saidai kafin takai gwiwoyinta qasa yadda suka saba ta miqa mata takardun idanunta akan saamee din amma obsa take bawa umarni cikin tataccen yaren oromo.
"Ki magana da masu bangaren clinic na gida,suzo su duba saamee....." Kai a qasa ta amsa mata tana ficewa a ladabce.
"Aanani ki dinga dubata,idan da akwai wani abun ki fadiwa nanay.....Allah ya sawwaqe" Rumaisa ta furta ga saamee tana dosar qofar fita zuciyarta fal da tausayinta.
Ta jima tana zato me qarfi akan saamee din ta fada tarkon son captain obbo din. Saidai ta dade tana addu'ar Allah yasa ba gaske bane,domin kuwa ita kanta da suke ciki daya ta sani,haisam din ba shakka allura ce cikin ruwa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tana da alaqa me kyau da 'ya'yan sarakuna irinta na cikin Ethiopia dama wajenta. Wasunsu tare da ita sukayi degree dinsu,a makarantar da tayi,batasan kuma adadin wadanda har yanzu suke kamun qafan son haisam din daga gurinta ba. Abinda basu sani ba ko ita din bata iya tsaiwa suyi magana makamanciyar wannan dashi.
Yana da sakewa 'yan uwansa da kuma nuna girma ta hanyar basu lokacinsa ya saurari damuwoyinsu. Amma kuma yana da tsare gida,yana kuma da wani irin kwarjini da duk yadda kaso masa wata magana idan dai har bashi ya bada qofa da fuska ba baka iyayi masa ita.
Da idanu saamee ta rakasu,saita maida idanunta ta lumshe tana sakin wani numfashi me nauyi. A hankali wani sashe na zuciyarta ke tambayarta.
"Anya haisam baifi qarfinki ba?,anya wutsiyar raqumi batayi nesa da qasa ba kuwa?" Iya su rumaisa kawai idan ta kalla wani lokaci zuciyarta tana yin rauni. Tana ganin girman matsayi na iko da mulki da suke dashi,saita dinga jin kamar haisam din ya mata nisan nisa....kamar haisam din yafi qarfinta,kamar haisam din ba sa'anta bane. Ajiyar zuciya ta subuce mata,ko yaushe tana jin hakan,tana kuma gayawa kanta hakan,amma ta kasa cireshi daga zuciyarta. Wacece ya aura yanzu? Tambayar da taketa nanatawa kanta tun daga wancan lokacin kawo yanzu.
*N A N A Y*
Cikin qawataccen setting room din daya kasance shine dakin hutawarta na shidda cikin dakunan hutawar data mallaka,zaune take saman wani ottoman me tsananin laushin da har nutsewa takeyi a ciki. Daga opposite dinta kyakkyawar mata ce da tashin farko zaka kirata da MATASHIYA. Saidai ko kadan,tsabar dukiya hutu kwanciyar hankali da kula da kaine zai sanya ka dauka shekarun nata kadanne. Wani irin salon kula da kai da jiki ta hanyar tsara cima me kyau da itatuwa da suka koya daga UWA TA GARI wato khadeeja yunnus jallata(nanay).
Hansaa kenan da suke kiranta da khansaa......itace 'ya ta biyu a gurin ibraheem aba jifar da kuma khadeeja yunnus jallata bayan yaronsu na farko daya rasu. Yaya ce ga haisam,wanda shi ya biyota sai NUDRA kuma ta biyo haisam din,amma dukka ya hadiyesu ya zama Kamar shine yayansu gaba daya.
Lullube jikinta yake da wata lafiyayyar laffaya milk color daya kusa sajewa da kyakkyawar fatar nan dake kwance lumui. Idanunta akan nanay,murmushin nan irin nasu dake nuna zallar nutsuwa take jifan nanay dashi
"Da gaske nanay,har yanzu mamaki yaqi sakata.....da gaske sheikh dinmu ne ya zabi mace?,da gaske sheikh dinmu ne yau ya zama me aure.....nanay idan ana maimaita maganan saina dinga ji kamar za'a dawo ace bashi bane abdii ne" Ta qarashe maganan da qaramar dariyar da zata tabbatar maka ra gaske take maganartan. Murmushi nanay din ta sauke,har abada dai girma baya taba nunawa ga mutumin da yake da iyaye a raye,komai girmansa saiya taba wani aby na quruciya. Ita kanta banda waya da sukayi dashi ta samu tabbaci daga gareshi ta dade tana juya abin,saidai har yanzu bata zauna sunyi wani cikakken magana akan auren ba. Motii ya mata daidai bayanin da ita ta gamsu,abu daya ta yarda dashi,aure dai ko ya yake aure ne,kuma alqawari ne wannan zata yiwa DANTA mafi soyuwa a ranta duk wani abu daya dace uwa tayi a al'ada da kuma addini,zata kuma tayashi karbar duk kalar macen da yazo da ita,duk da abun yazo ba zata,ga saamee da tausayinta yake maqale a ranta. Kafin takai ga cewa komai sallamar Aanani ya katse maganan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 106*
Idanun nanay a kanta tana duban nanay din sanda take qarasowa cikin yaren oromo dinnan da yake kama da yaren fullanci.
"Don Allah nanay kiwa yaa hussam magana magana mana.....ya barni na fita ni kadai.....kawai karbowa zanyi na dawo" Ta furta a shagwabe kamar noorah auta ke magana.
"Bazaiyuwu ba Aanani,kin manta da dokar haisam ne?,ko har kin manta da abinda ya faru kwana biyar kawai daya wuce?.....dukka ice cream da kalar madarar da muke dasu don kawai ba flavours din da kikeso sai kice saikin fita da kanki?,kuma ke daya?,ba hadimai ba kowa?". Jikin Aanani din ya danyi sanyi,tana tuna tashin hankalin da suka shiga a sannan,har ana tunanin cikin motii din ko Aarif an rasa wani,amma cikin taimakon Allah dukka aka shigo dasu guda s raye cikin kuma qoshin lafiya,saidan bubbugewar da ba za'a rasa ba.
"Ba suna delivery ba?" Hansaa ta katse maganar tana duban Aanani din.
"Kiwa abla magana ko ke magana dasu su kawo miki" Ta fadi tana wurga mata key. Da farinciki tabi key din ta dauka,tasan key din meye,aljihun motarta ne da take ajiyar kudin,tunda yaa hansaa din tayi mata haka,hakan yana nufin kona nawa ne ta dauka a siya,saita juya tana duban qaramin gadon yara da aka kawoshi aka ajiye musamman daga gefansu saboda zuwan hansaa din.
Kyakkyawar yarinya ce kwance a ciki,wadda fatarta gaba daya taqi biyo kalar fatar qabilarsu. Fara ce tas 'yar kululluba,baccinta take haiqan hankali kwance,kaman tasan tana qarqashin kyakkyawan tsaro cikin iyali masu girman daraja aba jifar Royal blood.
"Allah ya rayaki housanna" Tana dan gwalo wa hansaa. Bata bi ta kanta ba,don indai Aanani ce zaka gaji,uwa uba kuma maganansu da nanay yanzu yafi daukan hankalinta kan yadda zasu shirya komai. Duk da basu da tabbacin lokacin isowar haisam din,amma ta sani,ko a yau ta cewa haisam din ya iso Ethiopia to komai dare zai iso.
Dawowar anani yasa hansaa zuba mata harara
"Afwan yaaa hansaa.....nanay saamee fa bataji dadi ba,amma yaaa rumaisa tasa an kira clinic su dubata". Motsa fuska Nanay tayi tana dubanta.
" Me yasa batayi magana ba kuma?"
"Tace da sauqi ne".
" Ki biya ta gurinta ki tabbatar kinbar wasu hadiman a gurinta kafin na shigo".
"An gama" Tace da nanay tana sake ficewa.
Fuskarta da damuwa sosai take kallon hansaa,wadda rashin 'yan uwanta biyu ya sanya ta zame mata itace aminiyarta(kamar yadda hairaan ta zama aminiyar morsa safiyya).
"Kinji maganan da nakeson miki.....yarinyar nan tana shan wahala saboda muhammad.....anya bazan sanya motii ya daura auren nan ba idan yaso ya riqesu gaba daya,zai fara sonta idan har ta zama mallakinsa,kuma na sani,koda baya son saamee bazai cutar da ita ba,bazai kuma mata rashin adalci ba" Tayi maganan da damuwa sosai.
Idanu hansaa ta fidda tana kallon nanay.
"Nanay.....ki rufa mana asiri......muhammad din da ban taba tsammanin zaiyi aure da quruciyarsa ba?,fada miki ne fa ban taba yi ba,saboda kada na tada miki hankali. Munsha hira dashi,duk kuma da bata da tsaho sosai amma na fahimci ya saka aikinsa gaba da komai. A yadda na fahimci muhammad koda zaiyi aure ba yanzu a nan kusa ba. Tsarin matar da yake muradi kuma daban take da namu tunanin.....bance kada ki masa maganan saamee ba.....amma karki matsa,karkuma ki bayar da abun ta fuskar umarni. A fara samun fahimtar juna ma tsakanin su tukunna,komai da zai biyo baya me sauqi ne" Kai nanay ke gyadawa,ita din macace me fahimta,bata da tsauri sam ko matsantawa akan komai ma.
"Na fahimceki hansaa"