L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 62
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 62: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 62. "Ki addu'a diyar mutane guda dayan nan ma ta samu…
3,373 words
"Ki addu'a diyar mutane guda dayan nan ma ta samu cikakken lokacinsa" Hansaa ta fada tana murmushi,sai nanay dinma ta saki murmushin.
*A G A D E Z P A L A C E*
Umarnin giwa a masarautar kadan ya rage yayi daidai da dukkanin wani umarni da sultane zai bayar,wannan ya sanya gurin da mammina ta ayyana saboda halartar taron ya zama a cike maqil.
Isowarta gurin ya sanya shuru ya wanzu a gurin,a daidai lokacin da haisam ke kwance cikin sofa a parlor din gidansa,yana kuma saurare da kallon komai kamar a gabansa yake faruwa.
Cikin nuna tsananin izzarta ta qaraso gurin,ta kuma zauna a kebantaccen gurin da aka tanada saboda ita idanunta d'ai d'ai akan kowa. Taji mamaki sosai cikin ranta na rashin samum ganin haisam a gurin,ranta ya wani sosu,wanda shi dake zaune daga parlor dinsa yana kallon komai ya fahimci ya kuma raya daya daga cikin abinda ya sosa ranta.
Sallama tayi musu,saidai ita dimma cikin izza,dukkaninsu suka hada baki don amsawa kafin shuru ya sake biyo baya. Koda bata ce komai ba sun sani,bayyanar giwa a yanayi irin wannan da kowa zai samu daman ganinta kai tsaye ba qaramin muhimmi bane
"Ku saurareni da kyau.....gajeran saqo ne amma mai matuqar muhimmanci" Maganar ta ratsa shurun gurin,kowa kuma yana sake bata hankalinsa da wani irin yanayi.
"A yau ba muna fuskantar barazanar b'arayi bane.....ko wani qaramin laifi....a yau babbar barazana ce ta shigo cikin agadez,ta kuma riskemu har cikin masarautarmu" Sake yin shuru tayi tana aje numfashi gami da duban fuskar kowa don fuskantar yadda maganar ta ratsasu.
"Bama fuskantar maqiyi na fili,boyayyen maqiyi ne wannan wanda ya shigo cikinmu ba tare da mun lura ba"
"Baqo ne"
"Me hatsarin gaske"
"Mai nutsuwa fiye da DIYOYIN CIKIN GIDAN NAN" Ta fada qirjinta yana nuna nauyin abinda take dauke dashi. Miqewa tayi tsaye tana dubansu da kyau gami da matsowa gaba sosai.
"Ya zama dole kowa ya lura ya maida hankalinsa.....saboda babbar barazana ce da zata iya shafar kowa.....ciki kuwa hardani mata ga sarki ba lallai na tsira ba". Sosai maganan ta kada kowa,don sai da yawancinsu suka daga kai suna kallonta. Maganan ya musu girma sosai,tunda indai har ita giwa bata tsira ba?,to waye yake ta batunsu?.
"Qwarai kuwa.....kada ku yarda da shuru......kada ku yarda da murmushi......wanda yafiyin shuru shine yafi sanin abinda yakeyi" Ta sakeyin magana tana ci gaba da dubansu.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Aiki ne yanzu akan kowa.....aiki ne da ba'a daukewa kowa ba.....dole kowa ya sanya idanu akan kowa.....ba wanda aka yarda dashi a yanzu. Dole kowa ya sanya idanu ga tsaron masarauta. Kome muqamin mutum idan har ka karanci wani abu na rashin yarda a tattare dashi to kayi gaggawar sanarwa.....karku nuna kun ganshi...ku barshi yayi tunanin shine yayi nasara.....domin wanda yafi wayo shine wanda yabar maqiyinsa ya bayyana kansa"
Kalamanta na qarshe suka sakashi sakin murmushi,don yana jin a ransa kalamaine da suke aiki tsakanin shi da ita,sai ya zare device din kunnensa,ya kuma kashe system din. Iya wannan kawai da yaji.....iya wannan kawai daya gani ya isar masa.
Tabbas yayi nasarar dasa tsoro me girma a zuciyar mammina....ya sani,ya saka zargi da hasashe gami da rudewar lissafi me yawa a tattare da ita.
Da gaske hakanne,don kuwa ko bayan rufe taron ta bada umarnin a maida qofar shiga da fita daga gidan guda daya. Tana zaton wannan ce kawai kyakkyawar hanyar da zata bata wani kaifi da hange akan komai.
Tsananin tashin hankali takeji a ranta a duk sanda ta tuna AN DAUKE ALMAZ. Almaz qarfinta ne,kuma wani mahadin sirrinta. Ta tayar da nemansa da wani salo a boye,don ta tabbatar zaman almaz a hannunsu barazana ce me girma a tattare da ita.
★★★★Sake tsaiwa tayi gaban babban madubin da birra ta ajiye mata kamar ko yaushe. Sosai take sake duban kanta,ita kanta shigar tayi mata wani irin kyau. Ta jima rabon da tayi ado irin wannan,saidai hakan ba yana nufin ta saki wannan muguwar tsaftar da qamshin dake tattare da rayuwarta ba. Ta motsa kadan tana saka takalmin qafarta buhaina ta nemi izni ta shigo dauke da wayarta dake ruri.
"Allah ya taimakeki sultane ne yake kira". Kyawawan idanunta da aka zizarawa baqin kwalli wanda yasa suka qara haske da kyau ta daga,sannan ta miqawa buhaina din hannu tana karbar wayar,ta taka a hankali ta koma saman sofabed ta zauna,sai dukkaninsu suka juya suka fice saboda bata daman amsa wayar sultane din.
Wannan cikakkiyar sallamar tasa,da wannan muryar tasa da ita kadai ta isa ta gaya maka farincikin da zuciyasa take ciki. Idanunta ta lumshe kadan,har ga Allah tanason wannan walwalar ta sultane,har ga Allah tana jin dadij yadda kulawarsa da nuna qaunarsa da dukka suka dawo a kanta,amma tana jin haushi idan ta tuna dukka hakan ya faru ne ta sanadin malamin.....tana jin wani qunci idan ta tuna anya zata iya jurar auren bare farincikin sultane ya dawwama?. Saidai wani sashen na zuciyarta yana gaya mata farincikin sultane din gaba yake da komai a wajenta.
Cikin girmamawar da duk duniya shi daya yake iya samunta cikakkiya kamar haka ta gaidashi,ya amsa mata kuma cikin kulawa.
"Kun fita ne biftun bappi?" Ya kirata da wani suna can da yake kiranta,sunan da take matuqar so amma abubuwa daketa faruwa suka rabata da jin sunan daga bakinsa. Dan murmushi ta saki kadan,tunda ta shaida masa tare takeso suje gurin bisa rakiyar haisam ta fahimci walwalarsa da komai nasa ya qaru. Ta tabbatar inda yasan abinda ke shimfide a ranta bazai tana goya masa bayan ya bita ba .
Itakam a yau.....tun a yanzu tanason tantance masa TAZARAR DAKE TSAKANINSU.....tanason ya gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane.
"Yanzun nan zan fita bappi" Ta amsa masa da lallausar muryar nan da ko yaushe take sake bayyana qasaitarta. Kai ya gyada kamar yana ganinta
"Ma sha Allah biftu....ma sha Allah,don Allah biftu,kibi mijinki,ba wani sauran buri yanzu a duniya irin na ganki qarqashin mijinki. Ko yaya ki daure ki dauki halin safeena.....har yanzu inajin ciwon rashinta,har yanzu ban maida madadinta ba,ta mutu tana biyayya ga mijinta,safeena ta sadaukarmin da komai,harda rayuwarta" Ya fada da wani sanyi a muryarsa.
Numfashi sosai taja ta sauke,har ga Allah wannan soyayyar ta sultane da mamminta tana burgeta. Tsahon shekaru komai bai sauyashi ba?,komai bai sauya zuciyarsa ba?. Yaushe?,a ina?,kuma ta yaya ma zata zamu miji irin bappinta?.
A tare dashi kadai take ganin irin soyayyar dake burgeta,a tare dashi kawai take ganin kalar soyayyar da takeso namiji yay mata,amma kuma bata tunanin AKWAI KAMAR BAPPINTA.....babu kamarsa shi daya ne tak!,safeena har yanzu itace akan gaba a zuciyarsa,duk da cewa ya samu jininta ta qut da qut. Macen data samu miji kamar bappinta.....ya cancani kowanne soyayya a bashi....amma nata fa?. Malamin da baisan komai ba.....malamin da wataqila koda cikakken sunansa bazai iya rubutawa,don itakam bataga alamu ba. Tana mamakin yadda kowa ya gaza fahimtarta,abu daya ta sani shine KYANSA da suke kodawa.....wanda ta tabbatar shi ya rufe musu ido a kansa. Tasha nanatawa kanta BA KOWANNE ABU ME KYAU BANE yake da qarko da ingancin daya isa ya tsaya a kowanne gurbi da muhalli ba. ZAKI take nema.....jarumin namijin da zai iya tsaiwa ya qalubalancin duniya saboda ita,karantar ba zata samu haka ba ya sanya tayi condemning mazan gaba daya......taga kuma ba wanda ya cancanta ya sameta sam.
"Kina jina biftu?" Kai ta gyada a hankali
"Inaji bappi.....in sha Allah"
"Allah yayi miki albarka" Ya maimaita har sau uku tare da qarin wasu addu'o'in.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 107*
*_Assalamu alaikum warahmatullah_*
*_Kina neman inda zaki saki samu TSALA TSALAN backpack/school bags masu kyau inganci da rahusa?_*
*_To huguma na muku promo nasu,akan farashin 9k da 7500_*
*_Free delivery free waybill idan har sunkai pieces shida zuwa sama_*
*_Direct zan miki refund idan sukazo hannunki basu miki ba,foreign ne sabbi dal_*
*_Akwai Abun hannu(bracelet)na gayu,unique one shima akan farashin promo,6pcs 2above free delivery free waybill_*
*_Ba iya wannan kayan suke available a qasa ba,akwai soft tops da shorts/lounge wears/short gowns sababbi dal na musamman_*
*_zaki iya magana dani kai tsaye koki tuntubeni a wannan number wayar_*
08187255862 ____________________________
Shuru tayi tana jin muryar sultane da addu'o'insa cikin kanta,wani irin dadi sautin yake mata cikin kwanya,da yawan addu'ar data samu a yau din,saidai kuma tana tuna SABODA WAYE yayi addu'o'in gaba daya sai komai ya dagule mata,taja qaramin tsaki tana miqewa a hankali gami da duba lokaci.
D'ai d'ai take taku da wani irin kyau da kayan suka mata. Wine color gown ce wadda ta dace da qirarta da kuma jikinta,shigarta na nuna zallar zamani.....sarauta gogayya a ilimin zamani qasaita da kuma wayewa. Duk inda ka kalleta sau daya idan tayi ado zakasan cewa KWALLIYA tazo gidanta,saidai hakan bai hanata lullube kanta ko yafa madaidaicin mayafin da zai lullube qirjinta zuwa mazaunanta ba,wanda ko ba'a gaya mata ba,ko ba'a mata fada a kansu ba tasan Allah ya albarkaceta dasu,wanda sau tari a yanayin slim body dinta ba zaka dauka tana da ajiyayyun kaya irin haka ba.
Cak mammina ta dakata daga takowar da takeyi xuwa sassan akhnan din saboda hango fitowarta. Idanunta ya sake sauka sosai akan akhnan din,wani abu me tsananin tsini da zafi ya sauka saman zuciyarta. Ba abinda take hangowa sai SAFEENA a tattare da ita,wannan sassanyan kyan na safeena daya xame mata barazana a dukka gidajen da tasha buri da alwashin rayuwa a cikinsu,ta qwace mata mazan da sukafi dukkan mazan data aura dacewa da ita,mazan da bata kawo rabuwa dasu a kusa ba.
Wannan kyan dai data tabbatar yana daya daga cikin abinds ya qara tumbatsa farinjinin akhnan din da qarin izzar da takeji. Gaskiya ne.....ba qarya tana da wani irin kyau da sai an tara mata masu yawa kafin a samo kamarta,amma a nata gurin wannan kyan daidai yake da DAFIN MACIJI.
Gefen zuciyarta kadan ta matsa tana saurare. Mamakin inda zata je?,har ta kammala shiryawa kuma ba tare data sani ba. A baya kome akhnan din zatayi,ko ina zataje ita take fara shaidawa.....da ita take fara shawara,sai abinda ta yanke,amma yanzun har ankai matsayin da akhnan din zata dinga zartarwa da kanta?.
Bata lura da mammina ba,har sai data kusa da inda take tsaye sannan. Idanunsu suka hadu guri daya,mammina ta sauke mata wannan murmushin,yayin da akhnan ta janye idanunta daga kanta cikin salon wannan miskilancin basarwar da qasaitar da yake iya gwadawa kowa shi. Duk sanda zataga mammina din sai taji wani abu me ciwo ya motsa a ranta,takanji a ranta,zuciyarta kuma na raya mata itace sila. Inda ace ta zaba mata namijin daya dace da haiba da kamalarta,da tuni yanzun wani zancan ake ba wannan ba......amma ta dauko mutumin da sam bai dace da basarakiyar mace irinta ba,ya dagula komai,ya dawo lissafi baya,ya gwamutsa mata qaddara da amsa sunan MATAR MALAMI.
Wani irin zafi mammina taji a ranta,ba kallo kawai ba,koda motsin yatsar akhnan kadai tana iya fassarashi......motsin yatsar akhnan kawai tana iya fadin ME TAKE NUFI?,ME YAKE DAMUNTA?,MEYE A ZUCIYARTA? ballantana kallo da wannan blue eyes din nata masu kama da idanun safeena sak.
Hakan bai kassarata ba.....bai karya mata gwiwa ba,bai kuma hanata furta.
"Maraba da d'iyata,.....sai ina kuma?" Kaman ba zata amsa mata ba haka ta gotata a hankali,kafin ta motsa labbanta da lip gloss ya yiwa wani irin kyau me daukan hankali.
"Zan fara gwada tawa sa'ar" Ta amsa mata a taqaice tana yin gaba. Bata gane sam inda maganar ta dosa ba,amma tana jin ba zata bar yarinyar haka ba,saita tako bayanta tana fadin.
"Wacce irin sa'a akhnan?.....wacce sa'a kike nema ke da kika mallaki uwa irin ZAITUNA?". Taji murmushi iya qasan ranta,duk da yadda zuciyarta ke quna,ta lumshe kyawawan idanunta da sukayi kama da wadda ta saka eyelashes.
" A yanzu na gane kuskure ne dogara da mutum daya....ko yaya a rayuwa ya kamata ka koyi yanke wasu hukunce hukunce akan qashin kanka.....don kaine shiga a rayuwarka.....kaine CEO na kanka da kanka" Wani irin duka maganar akhnan din tayi mata duka bana wasa ba. Ta sani....tana da dabi'ar fadin magana kai tsaye......tana da hali na gaza boye abinda yake zuciyarta wanda ya mata dadi dama wanda bai mata ba,sau tari furta wasu abubuwan miskilanci ne kawai yake hanata,amma idan ta tashi furtawa zata furta gaba daya ne. Wannan bai sanya tayi zaton akhnan din zata bata amsa kai tsaye irin haka ba,saidai mamakinta ya cakude da wani abu na daban sanda ta hangi haisam gurin parking lot na musamman na gidan.
Lafiyayyen yadin cashmere me asalin tsadar ne a jikinsa baqi,wanda aka yiwa dinkin kufta riga da wando sai wata riga ta musamman da ake dorawa a sama wadda ke kama da cloak thobe din da yake amfani da ita. Duhun yadin yayi wani masifar haskaka farar fatarsa.....kamar dai ranar daya shigo mata sanye da baqar jubah a jikinsa,saidai a yau din hular dara ce a kansa wine color data dace da wine color fij half shoe din qafarsa. Wani irin ajiyayyen kyau yayi,karon farko daya soma saka sutura da dinki irin na mutanen nigeria dama niger din.
Fuskar nan tasa wani irin kwantaccen kyau da kwarjini ne yake tashi,yana tsaye kusa da wasu hadimai yana sanya hannu kan littafin report din aikinsu don zasu shiga hutun kwana bibbiyun daya raba wasu zasu karbesu,saboda bawa kowa daman yin rayuwa bisa sakewa bawai ka qare a bakin aiki ba.
Zuba masa idanu tayi a hankali tana takawa xuwa inda ta sanya aka shirya motocin da zasu fita ciki. A hankali kamar da gayya iska ta soma kwaso wannan fitinannen qamshin nasa tana aikewa dashi zuwa ga qofofin hancinta. Karon farko da taga irin shigar ta kwanta jikin matashi tayi ladabi har fiye da yadda ake buqata. Ba murmushi yake ba,amma wani sakakkiyar fuska ce yau kwance a fuskar tasa sanda yake magana da hadiman. Magana suke me dadi da alama,don dukkaninsu sun rusuna suna sauraronsa,basu miqe sun gwada tsaho dashi ba,hakanan basu zube a qasa ba kamar yadda ya hanasu yin hakan,yace qasqantar da kaine.
Littafin ya miqa musu,ya kuma juya da nufin takawa ya koma bakin motocin abdii yana biye dashi.
Wani mahaukacin bugawa zuciyar mammina taji tayi,a yau kawai tana ganin wani abu tattare dashi. Shugaba take hanga kuma jagora bawai gama garin malami ba. Shigar ba abinda ta tuna mata dashi sai shigar tufafin manyan malamai daga Nigeria da niger sukeyi,musamman qasaitattun malaman da suka hada karantarwa da kasuwanci. Takunsa kadai ya ajiye mata wata qatotuwar ayar tambaya. IZZA DA QASAITA kawai take hanga muraran a cikin takunsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Ta bangaren akhnan itama takun nasa ne abu na farko daya fara janye hankalinta duk da ya juya baya bayan ta gama samun tabbacin ba suturarta bace a jikinsa......ba suturar data saka kudade masu yawa ta siya masa bace ya sanya. Ta lumshe idanunta tana budesu mamaki yana sake saukar mata,mamakin inda ya samu nau'in sutura data dace da al'adar qasar dama qasashen kusa dasu. Zuciyarta ta quntata guri daya,tana sake amanna da kalar girman kansa,karo na farko data fara kyauta aka wofantar da hannuwanta. Tana iya tuna samarin da suka dinga zuwa neman aurenta,duk cikinsu ba wanda sunansa bai zama fitacce a agadez ba......ba wanda bata hada da kyauta me nauyi ba a sanda zai koma zuwa ga ahalinsa don yaje musu da shaidar zuwansa agadez......amma a yau din,shi da yake malamin da bai da wata sana'a qwaqwara guda daya ya ture kyautar tufafin data masa?. Idanunta ta ware a hankali cikin bacin rai tana duban takunsa,wata nutsatsiyar tafiya me nuna kuzari da kamewa,sai kace toron mai cikakken iko cikin dajinsa.
Kamar idanu yakeji a jikinsa,saidai hakan bai sanyashi waiwayawa ba har ya iso bakin daya daga cikin motar yana sauraren driver din da me wada yace sultane ya bada izini ya jagoranci tafiyar,ya tsaya jikin motar yana kuma juyawa cikin hikima a nutse zuwa ga bayansa.
Da wani irin mugun hanzari ta kwashe idanunta daga kansa,qirjinta yana wani irin bugawa. Ba zata taba yafewa kanta ba muddin ta bari ya kamata tana kallonsa. Ba zata taba yiwa kanta afuwa ba muddin ya zamana yaga idanunta a kansa. Wai meye ma abinda yaja idanunta gurin qarewa shigarsa kallo?. Sai taja siririn tsaki tana sake shimfida wannan miskilancin saman fuskarta. Qasan ranta wasai takejin kanta,duk da bacin ran qin saka tufafin data aike masa dashi,don kuwa tabbas tun a yau zata sanyashi ya fara danasani da karbarta a matsayin matarsa.....bayan banda kyau batasan wani abu na daban da zaiyi tutiya ko ya nunawa kowa ba.
Fes idanunsa ya sauka a kanta. Tana takowa cikin jin tata izzar da isar.
Idanunsa ya lumshe a kanta ya kuma bude,yayi hakan har sau biyu waiko zaiji bugun da zuciyarsa keyi zata daidaita,hakanan fitar numfashinsa da yakeji ta masa nauyi ko zai koma daidai shima. Zuciyarsa fayau take a kanta,saidai can qasan zuciyarsa wani irin qunci yakeji da takura me yawan gaske daga kallon fuskarta wanda shi kansa baisan dalili ba. Idanunsa ya janye yana furzar da iska daga bakinsa waiko hakan zai sanya yaji sanyi ko ya samu daidaito akan abinda yakejin din,saidai hakanma ba abinda ya rage sai qara masa wani yanayi na takura da quncin zuciya da yayi.
"Me yasa?" Ya tambayi kansa da kansa. Wani yanayi na kishi yakeji,kishin daya d'ara yadda yakeji akan rumaisa da Aanani da noorah. Me yasa zaiji haka a kanta bayan ita din bata cikin jerin sahun dukka wadannan da zuciyarsa ta lissafa masa?.
"Martabar aure" Zuciyarsa ta amsa masa. Ya yadda da wannan amsar.....martabar aurensa a kanta yafi gaban komai.....martabar aurensa yafi gaban ya bari ta fita da duk shigar data mata. Ya sani tun asali,yana da kishi koda ba'a akan abinda yakeso bane.....ya sake tabbatar da haka a kanta. Ba so koda na wasa nata a zuciyarsa......amma zafin da yakeji a yanzu ya tabbatar yana tuna cewa duk wanda ya kalleta abinda zai fara fadi shine.....zai dangantata da kansa.......zaice matar HAISAM ce.....shi kuwa sunan MATAR HAISAM wani abune da bazai bari ya tozarta ko ya wulaqanta ba koda kuwa auren wasan yara ne a kansa.
Tana takowa zuciyarta na mata zafi,yadda ya dauke idanunsa ya maida wani sashe kamar baisan Allah yayi da wanzuwarta a gurin ba. Ta dade da fassara hakan da sunan GIRMAN KAI,ta dade da bawa wannan dabi'a tasa suna da JIN KAI IZZA DA FADIN RAI. Qaramin tsakin da ba wanda zaiji ta saki,taci gaba da takowa har zuwa bakin qofar motar.
"Koma ki canza wannan shigar" Ya fadi a taqaice da wata tattausar murya daba wanda zaiji daga shi sai ita,don hatta da birra kwarjininsa ya cikata,ta gaza qarasowa har bakin motar yiwa uwar dakinta rakiya kaman yadda ta saba.
Cak ta dakata daga takawar da takeyi,mamaki ya cika fuskarta sosai. Ta zube masa duka blue eyes dinta,saidai bata samu daman kallon fuskarsa sosai ba,don ya karkatar da ita yana kallon gefensu,sai kwa tacciyar sassauqar qasumbarsa mara cika da yawa data zama wai adon girma akan kyakkyawar fuskarsa data samu gani da kyau. Hasken ranar daya fito bame kashe idanu ba yana sake bayyana qyallin da takeyi,irin qyallin da zai baka tabbacin tsafta kulawa da kudaden da takeci kawai don a gyarata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 108*