Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 64

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 64

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 64: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 64. "Kai" Ta fada cikin ranta tsananin mamaki yana cinta.…

3,373 words

"Kai" Ta fada cikin ranta tsananin mamaki yana cinta. Me malamin nan yake nufi?,fitar ce ba zatayi ba kwata kwata?,ko kuma sanda yakeso?,sai sanda yaga dama?,sai sanda ya bata izini?. Magana yakeso tayi?,idan haka ne kuwa ya makara.

Babu ta yadda za'ayi ta nema ALFARMA daga gareshi,don kuwa bashi da ita,shi kansa alfarmar tata yakeci.

Shuru yaci gaba da wanzuwa cikin motar,saboda dukka gilasan motar a rufe suke ruf. Mintina suka ci gaba da harbawa suns niyyar hada awa guda. Zuwa sannan zuciyarta ta gama tunzura,ranta ya gama baci,ta daga idanunta zuwa ga glass din gaban motar,sai taga qananun yayyafi sun fara sauka,abinda ya sake tunzurata kenan,har taji kamar zata fashe,sai kawai ta fidda wayarta ta soma kiran shehnaz kai tsaya.

Bugu biyu aka dauka,cikin muryarta da ko fushi takeyi ba zakaji ta kaurara ko ta canza salo maras dadi ba.

"Shehnaz kinga abinda mutumin nan yayimin?,ya kulleni a mota yana jiran saina karya girmana na masa magana?".

"To meye a ciki biftu,karyowa miji faduwa ne ko asara ce?" Muryar aisa ta mamayi kunnenta a madadin shehnaz data kira. Sosai akhnan taji ta hasala

"Kinsan abinda yakeyi ne yanzu aisa?,ya kulleni a mota kamar wata yarinyarshi?,wai ba'a gayawa malamin nan wadda ya aura bane?" Maganar ta tsaya a zuciyar aisa,ta kuma sauka a kunnen haisam daya saki boyayyen murmushi. WANNAN IZZAR.....WANNAN GIRMAN KA?. Ya fada can qasan zuciyarsa.

"Akhnan.....miji ne wannan.....ba ordinary malami ba akhnan......"

"Wai me yasa ba zaki gane ba aisa?,tozartani yakeson yayi aisa......yana kwance abinsa yana lumshe idanu kaman ban wanzu a gurin ba". Tana iya jin dariyar shehnaz ta cikin wayar,wadda ita abun ma dadi yayi mata. Zataso ace tana gurin,ta tabbatar yadda yanayinsan nan yake cike da miskilanci idan baiso ba da aji abun zai dadin kalla. Shi qasaita ita izza.

"Nice scene" Ta fadi daga kunnen aisa har sai da aisan ta juya ta tureta.

"Akhnan,ki tambayeshi me yasa yayi hakan,ta yuwu akwai dalili...."

"Bazan tambayeshi ba Allah aisa......bazan bashi wannan nasarar ba" Sai ta gintse wayar kawai don ta fuskanci ita aisa ma sam bata fahimtar abinda take fada......kamar aisa haisam ta sani,dukkansu ma ba wanda yake ta tata,kowa kaman goyon bayansa yake.

Wani miskilin murmushi na qasan zuciya ya saki,tana magana hankalinta kwance bisa dukkanin tsammanin baya jin yaren France,hakan ma yayi masa,kuma zaici gaba da barinta cikin duhunta.

Motsawa yayi a nutse yana duba kiran beeno.

"Obbo.....gurin yayi clear,komai yana a daidai,nan da mintuna talatin taron zai iya tashi"

"Okay" Kawai ya furta ta hanyar motsa kyawawan labbansa,muryarsa can qasa da wani irin zurfi da nutsuwa.

Da cikakken kuzarinsa ya miqe yana zama sosai,yadda ya zauna cikin zafin nama yaja hankalinta,amma saitaqi waiwayawa ta dubeshi,saboda idanunta dake cike taf da hawaye. A wannan lokaci ita kanta ta yabawa kanta qoqarin da tayi na riqe kukanta. Bata qaunar abinda zai sanya aga faduwarta ko kasawarta,wannan dalilin ya sanya bata taba yarda wani yasan rauninta bare ya cusguna mata har yaga hawayenta.

Ya riga ya tsada yadda zai fara mata karatun da zata san rayuwarta a yanzun ba daidai yake data baya ba. Ya sani,wani aiki ne da dole sai ya yishi,a kafiyarta da taurin kanta zai iya zame masa me wahalar gaske.....amma ya shirya fahimtar da ita da dorata bisa tsarin tarbiyya. Ya kamata tasan cewa zuwa yanzu tana da iyaka,ba komai ne zataci gaba da yinsa yadda takeso ba da kuma yadda ta tsara....akwai umarni ko hani daga wani da zai iya zuwa mata kowanne lokaci,dole ta koyi saurara,ta koyi bin tsarin da zai ci gaba da zaba mata.....zata fahimci kuma ba duk inda takeso zata dinga tafiya ba......saidai izininsa da amincewarsa. Dole ya riqe martabar igiyar aurensa,koda auren kwana daya ne tal!.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira 1,000 kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 110*

A nutse ya bude idanun nasa,sannan a hankali ya miqa hannunsa ya cire lock din.

Sai daya zura qafafunsa dake saye cikin tsadajjen royal half shoe din qafarsa sannan ya furta kalaman a jejjere cikin izza.

"Idan zaki shiga ki shiga yanzu,lokutana masu muhimmanci ne,bazan sake tsayawa ba" Sai ya qarasa fita waje yana tsaiwa saman qafafunsa gami da barin qofofin motar duka a bude.

A nutse yake gyara rigar jikinsa,yana kuma qarewa gurin kallo. Da a haka takeso su shiga?,sanda gurin yake a yamutse da mutane?,daidai mintunan data bayar don isowarsu gurin?. A lokacin ya tabbatar kowa yana qagauce da ya ganta,tunda wani abune da bata taba yi ba. Cikin kwanaki uku ya binciki komai daya shafeta,mu'amalarta da mutanenta dama komai. Yaji wani abu kadan daya burgeshi a halayenta,duk da ita bada wannan manufar tayi ba BATA DA YARDA SAM bata kuma yarda da abinda zai taba izzarta. Abune me kyau gurin mace,ki zama me izza.....ki zama maras yadda amma akan MAZA KAWAI. Dabi'a ce ta jin isa daga jininta,amma kuma siffa ce me kyau ba tare da ita tasan da hakan ba.

Kusan wannan shine karo na farko ma da zata bayyana a taron jama'a irin haka. Ba kowa bane yasan fuskar princess akhnan din ba,ya tabbatar akwai dimbin masu jiran ganin bayyanuwar fuskarta,abinda idan ya tuna hakanan sai yaji kamar su koma a fasa shiga. Baisan dalili ba,bai kuma san me yasa yakejin hakan ba,kawai yabar yanayinne akan AMANARTA da sultane yaketa maimaita masa.

Gwagwarmaya sosai tayi da zuciyarta kafin ta maida hawayen da suka cika mata idanu. Ba wani dan adam daya taba baqinciki irin wanda haisam din yake bata.....WAYESHI WAI?,ya akayi ya samu power da yake iya sarrafata haka cikin sauqi?

"Meye na damuwa?,ke da kika kawoshi gurin da zaiji kunya ya kuma muzanta sama da abinda yayi miki?". Wannan tunanin ya sanya taji zuciyarta ta sassauta sosai,wannan tunanin ya sanya taji relief.

Daidaita mode na fuskartata tayi,sannan cikin irin tata nutsuwar ta miqo qafafunta a hankali ta saukesu qasa,wanda suke saye cikin high hill shoe me igiyoyin da birra ta tsugunna ta dauresu saman kyakkyawar fatar qafarta. Idanunsa suka sauka akai a hankali,sai ya dauke kansa da sauri gudun faruwar wani abu,yaja numfashi yana duban hanyar da zata kaisu babbar farfajiyar taron kai tsaye.

Tayi mamakin ganin ya fara takawa kai tsaye,ba wani hadimi ko bawa ko dogari a tare dasu. Wani iri taji,wani banbarakwai,wanne irin raini yakeson jawo mata cikin al'ummarta.?. A duk sanda zataje guri irin haka koda ba cikin qasarta da yankinta ba,cikin tarba ta musamman ake tararta. Koda taron qarawa juna sani zataje a france ko dubai,hagu da damanta duka dogarawa ne suke tsaye da ita,amma a yau din sai gata suna takawa daga ita saishi su biyu qwal?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Me yasa sultane bai gano wannan ba?,me yasa sultane be gane banbamcin dake tsakaninsu ba?. Tayi imanin inda ace JININ SARAUTA NE SHI wani Dr ko professor din da tuni gurin ya cika da tarin 'yan biko suna marabtarsu,koda kowa ace ba JININ SARAUTA BANE. Amma yadda yake takawa hankalinsa kwance haka kawai ya nuna nata BAI SABA da duk wata girmamawa ba. Wai me yasa kyansa yake rudarsu?,me yasa kyanshi kawai suke hangowa?,me yasa basa hangen kowanne quality a tattare dashi?.

Tsakiyar tunaninta beeno abdii salawi Aabeer da salaana suka bayyana,saidai da idanu ya musu alamar kada su qaraso,kada ma su nuna suna da wani alaqa ta girmamawa tsakaninsu idan ta wuce ta gaisuwar abota kawai. Take suka janye suka kuma saje da mutanen gurin. Hangota ya sanya hadimanta dake tsaiwar jiran isowarsu suka taso musu,abinda yaja hankalin me gabatarwa da sauran mutanen dake gurin. Sanarwa aka fara yi kai tsaye da yanayin daya bawa akhnan mamaki.

"Muna maraba da isowar wakilin me martaba.....sheikh muhammad haisam tare da me dakinsa" Sanarwa ya mata wani banbarakwai,komai ma sai taji kamar baizo akan tsari ba saidai kuma hankalinta ya sake daidaita a jikinta duk da mamakin da yake mintsinarta sanda taga dukka manyan baqi dake gurin sun fara tasowa.

Kai tsaye haisam din suke dosowa,murmushi ya subuce mata daga can qasan zuciyarta. Lokaci yayi da zai fara fahimtar ba kowanne dan adam bane kake kutsa rayuwarka cikin tasa ba......a yanzu zai fara jin me ake nufi da KUNYA da toxarci.....zata ga da wanne yare zai iya magana da wadannan mutanen daketa wani girmamashi sama da yadda suka nuna mata bangirma,tamkar sunga me martaba. Ta tabe baki tana dubansa qasa qasa,sun taso sunyo gunsa gaba daya kamar shi ta yowa rakiya taron.

Da wannan murmushin nasa dake sake bayyana kamalarsa dama nutsuwarsa yake basu hannu,a hankali tataccen larabci taji ya soma tashi daga harshen haisam din zuwa ga manyan mutanen da yake musabaha dasu daya bayan daya.

A mamakance ta daga manyan blue eyes dinta tana saukewa a kansa. Fuskarsa a sake da wani irin yalwataccen yanayi,daya bayan daya kuma cikin girmama juna yakeci gaba da musabaha da mutanen,kowa kuma kaman yana qoqarin lallai saiya gaisa dashi kamar wadanda sukaga wani babban basaraken da babu irinsa.

"Me yasa?" Ta tambayi kanta

"Ko suma yana musu kwarjini ne?" Ta sake tambayar kanta a mamakance,saidai bata ko musa hakan ba sanda taga alqalin alqalai na niger gaba(chief justice ahmadu hambali) ya riqe hannun haisam din da kyau cikin rusunawa.

"Me kenan?,meye wannan?" Ta tambayi kanta.

"Duka wannan girmamawar ta meye?" Ta sake tambaya still ganin yadda ya tattarawa haisam hankalinsa yana saurarensa. Cikin nutsuwa Haisam ke magana dashi,cikin yaren larabci da ya sanya ta gaza fahimtar akan meye suke magana haka me muhimmanci?.

"Muje ko?" Ta tsinci muryarsa daidai kunnenta,abinda yazo mata a bazata saboda lulawa da tayi duniyar tunani. Kamar ko yaushe kusancinsu taji ya mata kusa sosai,qamshinnan da tun dazun ya zame mata jarrabawa yana sake kusantar hancinta,kafin ta daga qafa har ya soma yin gaba,saita taka tana biye dashi daidai sanda mutanen suka soma gaisheta itama.

Hakanan taji idanuwa sun mata yawa,har taji qafafunta kamar sun mata laushi. Ba wannan ne karo na farko data tsaya cikin taron jama'a ba kamar haka. Ta tsaya a taron da yafi wannan girma da tara manyan manyan mutane daga qasashen duniya,amma me yasa wannan yafi ratsa da tsaye mata a rai?. Saidai sanda ta daga idanunta a hankali saita fahimci......ba sauran idanun bane suke damunta ba.....ba sauran kallon da ake mata bane damuwarta ba.....aah idanunsa shi kadai.....kallonsa shi kadai ya hadiye dubbannin kallon da ake mata na bayyanar fuskarta a karon farko cikin taro cikin qasar agadez kamar haka.

Idonsa ya dauke a kanta,ya kuma karanci me yake damun zuciyarta da kallo daya tak,abinda tayita qoqarin tarewa saidai bai samu ba. Sassauta yanayin tafiyarsa yayi,ya rage karsashinta don ya bata dama su jera kafada da ita ko hakan zai rage mata nauyin da takeji.

Ci gaba da marabtarsa mutane daban daban sukaci gaba dayi cikin nuna kulawa da girmamawa. Bai fasa ba,da wannan karamcin nasa.....da wannan dattakon nasa yaci gaba da bada kulawa,saidai gaba daya sai yake jinsa kamar an masa dabaibayi. Idanun da suke kansu sunyi yawa,idanu ne dake cike da kallo na burgewa,sai yakejin kamar idanun sunfi yawa a kanta,kamar sunfi yawa akan fuskarta kasancewarta MACACE. Ya saka samun sukuni sam qasan ransa,har zuwa sanda suka isa mazaunin da aka ware musu,ita tana side din mata daga hannun hagu,shi yana side din maza daga dama,seats din sai suka kasance opposite na junansu. Ya taka sau daya zai zarce mazauninsa kamar yadda itama ta doshi mazauninta bisa takewar bayansu birra barratu buhaina bushira da bara'atu.

Tsintar yatunsa guda hudu tayi cikin wani abu me dumi da laushi ta qasan lafayarta,wanda sai bayan ta samu taja numfashi sannan ta fahimci hannunsa ne.

Wani irin abu taji ya tsarga mata saboda yadda yake murza yatsun nata sosai cikin tsakiyar tafin hannunsa.

"Ki gyara lullubinki,ki maida qafafunki ciki sanda kika zauna a seat dinki" Ya furta adan rarrabe saboda yadda zuciyarsa ke bugawa da qarfin gaske,sai ya saki yatsun nata yana wucewa mazaunin nasa cikin kame kansa da qoqarin daidaita nutsuwarsa.

Wani yanayi yakeji sosai cikin jikinsa,ya murza yatsunta ne kawai don ya fahimtar da ita maganarsa tafe take da kyakkyawan gargadi.....saidai kuma abun yazo masa da akasin abinda yayi niyyar aike mata.

Murmushi take qoqarin azawa kawai saman fuskarta ganin yadda kowa ke qoqarin gwada mata qauna da kulawa,saidai sam murmushin ba zaka kirashi da murmushi ba saidai washewar fuska,har zuwa sanda komai ya daidaita na murnar zuwansu aka dora da gudanar da taron.

Wani numfashi taja me nauyin gaske har qirjinta yana dagawa a hankali. Har yanxu jikinta amsawa yakeyi,ta lanqwashe hannunta cikin lafayar,ta saka daya hannun tana riqe yatsun daya riqe mata dazun tana murzasu a hankali waiko hakan zai.maye gurbin dumi da taushin tafin hannunsa da tambarinsu yaqi matsawa daga fatarta dama zuciyarta.

Tanata jin abunne cikin jikinta,zuciyarta na sauyawa da wani irin yanayi,yanayin daya dinga tunzurata lallai saita kalli fuskarsa......lallai tanaso ta gani ya yanayin nashi fuskar?. Da gayya yayi mata ko kuma arashi ne,sannu a sannu ta dinga wasa da idanunta a kewayensa,tana son duban yanayinsa,tanason duban me yakeyi?,ita yake kallo ko wani gurin,amma bataso ta zubda kimarta,saidai kuma da wani saurin idanunta suka fada a akansa ba tare data shirya ba.

Dukkanin hankalinsa ya tattara kan me jawabin da yake magana cikin harshen larabci,wanda ba duka take gane me yake cewa ba don bata da sani ta wannan bangaren. Kyakkyawan gemunsa da gashin dake kwance gefe da gefan fuskarsa yanata glowing da wani yanayi daya qarawa lafiyayyar fatar fuskarsa me wani irin haske me daukan idanu kyau. Ya dan karkata fuskarsa wannan ya sanya taga shape na lips nasa.....shape na manyan idanunsa da suke lumshe kadan,da hancinsa daya zauna sosai saman fuskarsa kamar an ajiyeshi. Bame tsini ko tsaho bane sosai,yana da tsaho din amma yana da dan tudu daya sanya qwayar idanunsa ta fidda yadda ya kamata.

Motsawar da taga yayi ya sanyata dauke idanunta da sauri,saidai kuma ko data sake dubansa sai taga idanunsa ya maida kan wayarsa. A hankali ta sauke dubanta kan zara zaran yatsun hannunsa da yake danna wayar da sauri,yanayin da zai gaya mata qwarewarsa wajen sarrafa waya. Daga nan inda take tana iya ganin fararen yatsunsa dama fararen nails dinsa da suke wani irin tarwai kamar glass. Zoben azurfa ne qwaya daya kawai a hannun nasa me dauke da wani irin blue din stone a samansa da yafi mata kama da DIAMOND saboda yadda blue din ya kasance wani me sheqi da dukan hankali. Agogon Rolex din dake dake tsintsiyar hannunsa ya kwanta luf cikin fatar nan tasa ma'abociyar gargasa sosai.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira 1k kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 111*

Batasan ya akayi ba wani numfashi ya qwace mata,zuciyarta kuma taso tsaiwa a qirjinta sakamakon dago kansa da yayi suka kuma hada idanu cikin ba zata.

Da wani irin hanzari ta qwace idanunta tana jin zuciyarta tana lugude

"Me yasa?" Ta tuhumi idanunta da zuciyarta da suka tunzurata kallonsa har haka.

"Sheikh haisam ne fa?,ordinary malam?" Ta fadiwa kanta da kanta. Bata sake kowanne tunani ba taji me gabatarwa yana magana ta mic

"Muna neman alfarma ga sheikh muhammad haisam yazo ya wakilci me martaba gurin miqa certificate na girmamawa ga zaqaquran dalibanmu". Idanu ta qanqance,zuciyarta tana matsewa a qirjinta. Wannan matsayin nata ne.....inda babu shi,banda ya wanzu a gurin itace zata wakilci sultane,sai taji wani bacin rai yana lasarta,ta sake daga idanunta tana dan satar binsa da kallo sanda yake takawa a qasaice zuwa saman steps din,duk da sunyi nufin matsowa da abun maganar gurin ya basu daga inda yake a zaune.

Yadda yadin cashmere din jikinsa ke daukan idanu wani abune na daban na musamman kuma da zai sake bayyana maka tsadarsa. Hakanan tsarin dinkin da akayi masa kawai abun burgewa ne.

"Yana da daukan hankali malamin nan......irinsu cikin malamai ne qalilanne......ga izza ga ilimi" Maganan ya sauka daga bayanta wadda taja hankalinta. A hankali ta soma maido da dubanta da nufin fahimtar wadanda ke maganar. Saidai kafin takai garesu ma idanunta sun nuna mata yadda dubban idanu suka raja'a a kansa kafin muryarsa me zurfin nan data sake kwarjini ta soma fita ta cikin mic din.

Kujera ta musamman suka aje masa still a gurin duk da ya taso din,sannan ya karbi mic din ya fara da sallama. Kai ka sani koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci gwani ne wajen magana cikin mutane.

Sallama yayi wadda ta bada wani irin sauti me daukan hankali,dukka suka amsa suna tattara hankalinsu a kanshi.

Cikin taqaitaccen lokaci ya gabatar da jawabi cikin harshen larabci,jawabin data fahimci kusan duk wanda kejin harshen larabci a gurin yana ratsashi. A nutse idanunsa da bakinsa ke juyawa,bakin dake fidda haruffan larabcin cikin wani irin zallar qwarewa da fahimtar harshen. Tana numfashi sosai taja fiddashi a hankali. Karon farko data tsaya ta saurari yaren larabci zalla irin haka da kyau,batasan me yasa ba batasan kuma dalili ba,sai taji yaren yana mata wani irin dadim da farko ta dauka ba yaren da yakai yaren abzinanci da French dadi......amma a yau sai takejin wani irin yanayi daban yana ratsata.

Yana kammalawa dukkanin gurin ya dauki kabbara me qarfin gaske,mc din ya qarasa ya karbi mic din cikin girmamawar dashi kansa baisan yana yinta ba,ya saka mic din a bakinsa ya fara magana cikin yaren Tuareg.

"Na jima banji tataccen larabci daya tsumani da harshe me kyau irin wannan ba......nasan dukkanin udaba'u masana yaren larabci a yanzun sheikh muhammad haisam ya tayar musu da shauqi,muna godiya sosai" Ya fada yana rusunawa.

Daya bayan daya ya fara kiran 'yammatan daliban da suka cancanci girmamawar yana miqa musu certificate din,karbar certificate din daya zama jidali ga dukkan 'yammatan. Ba wadda bata bar gurin da wani irin bugun zuciya ba saboda wani irin kwarjinin tsayawa a gabansa.

"Khadeeja rabi'ou sa'adou" Mc din ya kira sunan dalibar me suna khadeeja har sau biyu.

Ta tsakiyar daliban ta fara takowa da dan hanzarinta. Baqar buzuwa ce wadda bata cika hasken fata ba,saidai tana da kyanta daidai gwargwado. Kallo daya ne haisam din keyi bisa al'adarsa,baya kuma d'ara hakan,ya dauke idanunsa yana miqewa a nutse,miqewar data bawa kowa mamaki. Tsaiwa dalibar tayi a gabansa,saita sad da kanta qasa kwarjininsa yana cikata,daidai sanda yayi magana da abdii dake gefansa. Murmushi abdii din yayi,ya matsa ya yiwa MC din magana,sautin murmushin Mc din ya harba ta cikin mic din yana duban kowa d'ai d'ai.

Karbar nata certificate din haisam yayi,yadan duba kadan,sannan ya miqa mata,ta sanya hannu biyu ta rusuna cikin girmamawa tana karba.

"Muna miqa saqon godiya ga sheikh muhammad haisam....ya miqe don karrama khadeeja da kansa,saboda ita din taci sunan mahaifiyarsa ne......dalilin wannan sheikh muhammad ya bayar ga kyauta ga kowacce daliba har na CFA 390,000 yayin daya ninka wannan adadin ga daliba khadeeja" Wani irin abune a hankali taji yana saukar mata a gangar jikinta,wani abu da batasan meye ba. A nutse ta dora idanunta akan dalibar,wadda duka duka batafi sa'ar falaak dinta ba. Idanunta sukayi kyakkyawan gani,don kuwa lura tayi da idanunta suna kan haisam din dake saukowa daga step din a nutse don komawa muhallinsa. Murmushi takeyi sosai wani irin murmushi dake nuni da farincikin da zuciyata take ciki.

"Kyautar CFA 390,000 ga kowacce daliba?.....daliban da aqalla sun kusa sun tamanin?. A ina ya samu wadannan kudaden?,yasan ma abinda yake fadin yayi kyautar dashi kuwa?,yasan kuwa adadin kudaden daya ambata kuwa?" Ta tambayi kanta da kanta tana son maida idanunta kan fuskarsa,saidai zuciyarta tana gargad'arta game da hakan.

Readers Also Read

More by Huguma