L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 65
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 65: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 65. "Daliba guda daya an ninka mata adadin?" Ta sake…
3,352 words
"Daliba guda daya an ninka mata adadin?" Ta sake tambayar kanta tana maida idanunta kan yarinyar da tuni ta koma ta zauna.
Murmushi takeyi sosai,dukkan alamu na matsanancin farinciki sun nuna akan fuskar yarinyar,lokaci lokaci tana daga idanu ta kalli sashen da haisam yake tsaye yana sallama da manyan mutanen daya samu a gurin.
Wani harbawa guda daya taji zuciyarta tayi,ta lumshe idanunta tana tambayar kanta DALILI?. Saboda kawai sunanta khadeeja?,me yasa yake iya ninka kyauta saboda suna daya?. Sauke numfashi tayi sanda birra ta rusuno tana gaya mata
"Zamu wuce ne ranki ya dade......yallabai yayi umarni" Idanunta ta daga a hankali ta kalli birra jin sunan data sauya masa,saita miqe a nutse abinda ya sanya hankula suka sake yowa kanta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Bata manta ba,batayi qasa kuma a gwiwa ba ta waiwaya a hankali tana sauke idanunta ga mutum biyu dake bayanta. Suka hada idanu sai suka sakar mata murmushi. Shugabar hukumar ilimin bai d'aya ce ta qasa,hajiya nihla Ousmane......da baquwar da batasan wacece ba. Kudi kyau gami da dukiya dukkaninsu nihla tana dasu,tana cikin mata matasa masu qananun shekaru da suka samu aiki me girma cikin gwamnati,saidai duk da haka nihla din bata taba aure ba.
Hada idanu sukayi,cikin girmamawa hajiya nihla wadda ta miqe tana miqawa akhnan hannu. Duk da cewa ta girmi akhnan nesa ba kusa ba.....akhnan din kamar qanwa take a gurinta,qanwar ma ta bayan baya,amma hausawa sukace sawun giwa ya take na raqumi,dole ta bawa akhnan din girma kamar nata shekarun sunfi nata.
Wani kallo ta sakewa nihla din na cikin idanu,'yan abun miskilanci sun motsa,a nutse cikin wannan fuskar da sarauta da izza ke kaiwa suna kawowa ta zare idanunta,ba tare data maidawa nihla hannunta su gaisa ba.......ta zare idanunta tana juyawa a nutse ta fara takawa su birra suna take mata baya.
A nutse sukaja da baya sanda take dab da riskarsa. Yana takawa hankali kwance yana amsa waya da hausarsa da bata gama fita gaba daya. Idanunta ta lumshe tana budesu,tana tuna komai daya faru a yanzu. Damuwarta alqawarin daya dauka na kudade masu nauyi da yace zai bayar ga daliban. Ta sani,baida abinda zai iya biyan wadannan kudaden daya ambata,zai karya siffarsa yayi musu qarya ya gudu?,ko kuma karba daga lalitar mahaifinta da sunan shine ya bayar?.
Haka kawai a jikinta taji bata gamsu da dukkanin wadannan amsoshin ba. A jikinta take jin indai wannan mutumin ne.....indai wannan malaminne ba daya daga ciki da zaiyi.
Ta saci kallonsa kadan sanda ya sake matsawa da kansa ya kuma bude mata qofar motar a karo na biyu. Ganin zai waiwayo ta dauke dubanta a kansa. Tana jin wani d'aci a ranta,wannan nutsuwar rashin fushin da take gani saman fuskarsa bata sonsu.
Ko data maida idanunta sai taga seat din gaba ya bude mata. Mamaki yadan kamata,a iya rayuwarta idan ba Niamey ta shiga ba bata taba zama gaban mota,kullum a baya take,driver yana janta. Ta sake daga idanunta cikin alamun rashin fahimta tana dubansa,tsareta yayi da kallo da wannan zafafan idanun nasa,sannan ya mata sign din ta shiga.
Wannan zuciyar.....wannan kwanyar data soma jin haushinsu sai suka bata qwarin gwiwar shiga din. Ta sauke numfashi me nauyi sanda ta daidaita cikin seat din. Wai me yake faruwa?,me yasa komai ya juye?,me yasa komai ya sauya daga asalin yadda yake?. Shi ya kamata ya zama cikakken d'an rakiya a idanun kowa.....amma ita ta buge da zama 'yar rakiyar.....shi ya kamata ya shiga qunci kunyata da takura amma ita dince ranta a bace bashi ba......me yasa haka?.
"Bismillah" Taji an ambata a hankali. Wani irin baqon yanayi ne a hankali ya mamayeta,qamshinsa yana sake kusantarta da wani irin yanayi dake jefa zuciyarta zuwa ga wani irin shauqi. Ta saba jin hakan a duk sanda qamshin zai bugeta,zuciyarta wasai.....qirjinta wasai,nutsuwa kuma zataji tana mamayarta.
Wannan zuciyar dake bugawa cikin qirjinta itace ta soma tambayarta SHI ZAI DRIVING?.....ina driver na?. Zuciyarta taci gaba da bugawa cikin qirjinta da tsoro,tana tsoro kada bai iya motar ba....kada yayi ganganci da rayuwarta,abinda ya sanyata bude idanunta da sauri,daidai sanda ya miqa hannunsa don kunna motar.
Da wani irin tsoro ta miqa hannunta da zummar dakatar dashi,tafin hannunta ya sauka a bayan hannunsa,dumin jikin junansu ya harba cikin kowacce magudanar jini ta jikinsu,yakai kuma saqo kwanyarsu. A tare kuma lokaci guda wuta ta daukewa dukkaninsu. Ya daga idanunsa a hankali ya aza saman nata adam apple dinsa yana motsawa da wani irin sauri. Kaifi da tasirin idanunsa suka ratsata,tunaninta da jinin jikinta suka koma daidai,ta samu nasarar janye hannunta da sauri daga saman nasa. Kauda kanta tayi tana son bugun zuciyarta ya daidaita sosai. Me yasa taketa yin shirme ne?,me yasa ta kasa mallakar kanta?,me yasa taketa abubuwan da bai kamata tayisu ba?. Idan ya rainata fa?,idan ya zaci wani abu a kanta fa?. Saita lumshe idanunta sanda taji ya tayar da motar,cikin wani irin coolness yayi reverse ya soma fita da ita daga gurin.
Sai daya daidaita motar saman kwalta sannan ya miqa hannu ya kunna A.c din motar saboda yadda yakejin kamar suna cudayyar numfashi da yawa shi da ita. Wani irin shuru ya ratsa motar,tuqi yake cikin nutsuwa mutuwar jiki da kuma kasala. idanunsa akan lafiyayyar kwaltar dake shimfide saman titin,koda batayi magana ba yasan tanason sanin inda zai kaisu ne,bai kuma shirya magana da ita ba.
Yanaso ta fahimci IKO da yake dashi a kanta......yanaso ta fahimci maganarsa dama tsarikansa sama suke da nata. Sai ya fara zare mata UMARNIN MAMMINA daga ranta gaba daya,sai ya fara fahimtar da ita tana da wata rayuwa......tana da wani umarni......tana da wani IKO sama da ikon mammina saman wuyanta. Sai ya fara tabbatarwa mammina akwai tazara yanzu tsakaninta da ita,sai ya fara koyar da mammina akwai wani QARFIN IKO daya fara mallaka daga cikin nata kason ikon.
Sanda ya rage gudun da yake ya gangara zuwa wani street din daban saita bude idanunta a hankali. Mamaki ya sake cikata ganin ba kowa tare dasu. Basu birra,ba sauran guard's dinta maza da suke kula da tsaronta a duk sanda zasu fita din.
Idanu tabi ginin dashi,tunda take a agadez ma batasan gurin ba,saidai koda ba'a gaya mata ba,ta fahimci kodai hotel ko kuma wani hamshaqin guests in dinne.
Amma kuma gaba daya ba symbol ba alamu na sunan gurin,saidai girma da tsaruwar ginin kawai ya sanya ta gaza gasgata gida ne.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1,000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 112*
Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa.
Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe
"Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar.
Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba.
"Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya.
"Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta.
Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu.
"Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata
"Na fadi maka nan din ba gidana bane".
"Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba.
Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske.
"Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa.
A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA.
"Sakanninki suna dab da cika...."
"Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna.
Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu.
"Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda.
"Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan.
"Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun.
Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta
"Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba.
Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai.
"Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan.
Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya.
Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau.
Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi.
A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan.
Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa..
A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje.
"Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki.
"Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?.
"Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane".
" You speak as if......"
"As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar.
"Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa.
"Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci.
"Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 113*
Wani irin numfashi taja tana saukewa a hankali
"Yara basa cikin tsarin mammina?" Ta maimaita maganasa. Me ya kawo maganan mammina cikin wannan al'amarin?,me maganarsa take nufi da haka?.
Rikicewa lissafinta yayi gaba daya,ta sanya hannu tana dafe goshinta duk da haka idanunta suna yawo cikin gurin. Wani irin gurine da har yanzu tsaruwarsa yake bata mamaki,saidai abinda takeji game dashi daga qasan ranta ya sanya tana danne komai.
Qofa bayan qofa yaci gaba da kutsawa cikin gidan,gidan daya zama killatacce kuma na musamman. Cike gidan yake da wani irin tsaro tako ina,shi kuma ya tsara gidan daidai da yadda yakeso. Wani irin tsari da yakan iya sarrafa wayar mutum daga sanda ya shigo gidan har ya fita. Irin wannan gidan kamar mini copy ne na babban ainihin gidansa dake Ethiopia.
Wani irin cabinet ce da zaka dauka litattafai ne a shirye a gurin,saidai ko daya matsa wani guri sai ga qofa ta bayyana.
Dakine da ko ba'a gaya maka ba kasan an tanadeshi ne saboda aikin sirri,a gaggauce ya shirya komai,ya zauna gaban wani siririn screen da sam baiyi kama da system ko babban computer ba,fuskar omar ta bayyana.
"I'm sorry omar" Haisam din ya fada yana jawo mug din coffee dinsa ya surba. Murmushi kadan omar yayi,bada haquri gurin haisam din ba wani bane me wahala,saba alqawari kuma ba halinsa bane sam sam,inde kaga hakan ta faru saida babban dalili.
"Ai sai an maka uzuri captain"
"Go straight mana omar" Ya fadi yana komawa serious. Shima omar din yasan aikin babba ne,don haka ya koma serious dinsa.
Saluting na haisam ya fara yi yana daga hannunsa zuwa gefan kansa. Tsaiwa haisam yayi yana dubansa kafin omar ya sauke hannunsa a hankali.
"Dukkan hasashenka ya zama gaskiya,tabbas kawai wani babban abu da take boyewa a gida.....hasashenka ya tabbata,saidai kuma gidan zagaye yake da wani irin tsaro me tsananin gaske. Fiddo da wadanda ke cikin gidan ko cimmasu kamar yana buqatar muyi wani adjustment dan kadan....." Kai kawai haisam yake gyadawa a hankali,yana jin qirjinsa yana yin wani irin wasai. Da gaske ubangiji yana jin dukkan addu'ar me neman d'auki,da gaske ubangiji na tare da dukkan wanda aka zalunta,fadarsa ne cewa zai taimaki wanda aka zalunta koda bayan wani lokaci ne.
"Muyi focusing akan gidan omar.......juyar da camera.......inaso cikin sati daya kacal a gama da batun gidan......kamar inaji a jikina shine abu na qarshe daya rage mana" Yayi maganar da dukka seriousness dinsa,yanayin da yake gayawa omar da gaske haisam din ya shirya koda kwana ne a tsaye.
"Ka hada connection dasu beeno,kowa ya kasance a matsayarsa" Ya fadi yana tattare hannun rigarsa,abinda ya baiwa kwantacciyar gargasarsa daman fitowa sosai ya aza manyan idanunsa dinnan masu haske saman system din da dukka bada hankalinsa.
Batasan adadin sau nawa taja tsaki ba tana duban lokacin daya fara gudu yana qara zurfi. A qalla ta zaci bazasu haura awa daya ba komai dadewar da zaiyi,sai gashi qarfe biyu na rana na dab da hada kanta.