Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 66

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 66

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 66: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 66. Miqewa tayi ta fara takawa kadan kadan a hankali,a…

3,299 words

Miqewa tayi ta fara takawa kadan kadan a hankali,a ranta tana raya gwara tayi alwala tayi sallah,qila kafin ta kammala sallar ya gama shigo.

Ci gaba tayi da kewayawa cikin dakin tana laluben qofar toilet,saudai har ta dawo zuwa anihin inda ta baro bataga wani alamun qofa ba.

Mamaki ya sake kamata,ta sake takawa a hankali tana dawowa,saidai still kaman dazun ne. Ganin zata batawa kanta lokaci ne kawai ya sanyata komawa ta zauna tana zubawa sarautar Allah idanu. Ta maida idanunta zuwa ga wayarta a mamakance sanda taji tana qwala kiran sallah. A iya saninta ba wani alarm ko app data taba azawa wayartata don tunasar da ita lokutan sallah,ta miqa hannu ta dauki wayar ta soma sarrafata. Kaf bincikenta bataga wani app ko wani abu daya kawo dalilin kiran sallar ba,har tayi kiran ta qare,sai kawai ta maidata ta ajiye a ranta tana saka ran qilan wani automatic abune ya soma aiki a ciki.

A hankali taci gaba da duban lokaci da yake wucewa da sauri,yayyafin dake sauka a sararin sama yana dan qara qarfi. Ranta ya soma baci ganin lokacin sallar azahar ya kubce mata. Duk yadda taso ta hana zuciyarta baci amma abun yaci tura,quna kawai zuciyarta takeyi. Wai a haka basa ganin aibunsa har yanzu?. Ashe bayaga abinda take gani ya hada da wulaqanta dan adam da banzatarwa. Ba zata juri wannan ba sam,saboda komai da yayi tasan yana sane yayi,yayi ne kawai don ya wulaqantata,yayi ne kawai don ya tozartata. A komau nasa idan baiyi qoqarin kai kanta qasa ba bayajin dadi,a yau itakuma tayi alqawarin zaiga irin tsaiwar da take dashi,sai ta jawo wayarta tana laluben wanda zata kira.

Kiran duniya kowanne kira yaqi isa ga wanda aka yishi,data kira sai kiran ya yanke,data kira sai kiran ya katse,sai kawai ta ajiye wayar tana dora hannunta akan fuskarta.

"Bazan iya wannan tafiyar ba.....bazan iya ba" Ta fadawa kanta da kanta. Har tsakiyar zuciyarta takejin ta gashi dashi,har tsakiyar zuciyarta takejin ya isheta,har qasam zuciyarta takejin ta qosa da wannan tarin umarnin nakai tsaye da yake bata.

A hankali kiran sallar ya sake maimaituwa a wayar tata,wanda koda ta kalla sai taga lokacin sallar la'asar ne ya shigo. Zuciyarta ta sake tunzura,ta fara tuhumar kanta me yasa taci gaba da zama ne a gurin?,me yasa ba zata tafi ba tunda tana da qafafu koda kuwa a qasa ne?. Da wannan shawarar tayi amfani ta miqe a hankali ta dauki jakarta da wayarta tana nufar qofa.

Hankali kwance ta bude qofar,don shigen qofofin gidanta ne na Niamey. Ta fara takawa ta hanyar da suka shigo,saidai tun bataje ko ina ba ta rude ta kasa tantance waccece hanyar?.

Koda ta zabi hanyar da take ganin itace,sai gata ta bulla wata farfajiyar ta daban. Wani irin guri dake cike da shuke shuke masu daukan hankali. Turus tayi tana kallon yadda ruwan sama ke sauka a hankali,abinda tafi tsoro kenana duniya irin wannan yanayin. Lokaci na ruwan sama da zata kasance ita daya koda da rana bare dare,saboda tsoron walqiya da tsawa. Ta taka baya a hankali tana girgiza kai saboda tasan ta bace hanya,saita juya zuwa baya da sassarfa hawaye na sauko mata,amma saita sanya hannu ta dauke tana fadin.

"Ba yanzu ba" Kamar jira ake ta sanya qafafunta aka saki wata irin walqiya data haska sararin samaniya da wani irin matsanancin haske,ta runtse idanunta ta kuma toshe kunnuwanta zuciyarta na wani mugun gudu tana jiran jin saukar tsawa,abinda ya sanayata ci gaba tayi da tafiya da wani irin sassarfa,saidai kuma still dakin dazu kawai ta gane hanyarsa,dole ta yanke shawarar komawa ciki.gudun kada ta sake qoqarin fita a samu wata walqiyar me hade da tsawar.

Zubewa tayi gaba daya saman daya daga cikin luxury sofas din dake dakin tana sakin ajiyar zuciya. Sosai tayi yaqi da kanta da kanta,ta kuma hana kanta da kanta kuka,saidai zuciyarta kawai suya take mata,ta sake duban lokaci wanda ya nuna mata biyar harda rabi da wasu mintuna na yammaci,nan da awa daya ko da rabi ana iya kiran sallar magariba,sai kawai ta cure guri daya ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta. Kukan takeso tayi,amma ta hana kanta,abinda ya taru kenan ya tsananta xafin da zuciyarta takeji.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Subhanallah" Ya furta da sauri yana ajiye paper din daya dauko saboda tunawa da yay cewa tare suka shigo gurin shi da ita. Miqewa yayi da hanzari ba tare daya damu da sauke hannun rigarsa daya nannadeshi zuwa gwiwar hannunsa ba,ya kashe system din gaba daya da sauran na'urori da fitilar dakin,ya kuma kwashi takardun da zai kwasa a gaggauce ya fito daga gurin bayan ya maida komai kamar yadda yake.

Da sassarfa yake takowa zuwa dakin,yana kuma duba agogon hannunsa.

"Ya salam" Ya sake furtawa a hankali. Har cikin zuciyarsa da gasken gaske yana ji ba dadi,kwata kwata ya manta tare suka shigo,duk da cikin jikinsa time to time yana jin kamar yayi mantuwa ko akwai wani abu daya kamata yayi baiyishi ba.

Binciken yazo masa da wata irin nasara,aikin ya daukesu dogon lokaci,amma yana sanya ran duk ranar da suka nufi gurin zasu samu dukkan wata nasara da suke sanya rai. Ya sanya ayiwa komai sakin talala,saidai suna biye da motsin komai kuwa.

A nutse wannan nutsuwar da ta zame masa jiki yayi scanning fuska da hannunsa qofar ta bude masa kanta da kanta ya tura yana shiga. Bakinsa dauke da sallama,da wannan muryar tasa me wani irin laushi da zurfi.

Tana zaune kawai,kanta a qasa kamar me duban cinyoyinta. Sallamar ta sauka a kunnenta tana tattaro dukkan wani rauni da take ta boyewa ta aza saman zuciyarta da wani qarfi daya wancakalar da duk wata juriyarta.

Idanunsa a kanta yake takowa a hankali yana qoqarin karantarta,saidai bai samu daman ganin fuskarta gaba daya ba,ya qarasa saman wani abu ya dora takardun gaba daya yana fadin.

"Afw........"

"Mu wuce gida" Muryarta ta fita da wani irin sanyi duk da ba wannan sautin taso maganarta ta fita ba.

A nutse ya waiwayo,idanunsa suka sarqe da nata,abubuwa da yawa ya karanta ya kuma fahimta a tattare da ita,ya jisu ya kuma fahimcesu har cikin jikinsa,sai ya zare idonsa daga kanta yana qoqarin karantar yanayin dakin ya gani ko wani abu ya sauya.

Baiga komai ba,koda bottle na ruwa kuwa,hakan yana nufin ba abinda taci ko tasha?. Baiga komai game da cima ba. Mamaki ya kamashi,ya soma takowa inda take idanunsa a kanta fuskarsa tana nuna wani yanayi.

"Bakici komai ba?......akwai komai a dakin nan fa" Ya fadi da tausasawa yana dubanta yana sake nazartar yanayinta.

Batace masa uffan ba,saboda idan ta tuna cewa batayi sallolinta ba duka tana jin kamar tayita kurma ihu. Tana da riqe lokutan sallah,tun wani fada da suka taba yi da hairaan a lokacin duka duka shekarunta sha biyu hairaan tana da biyar. Tun daga wannan lokacin abun ya zaunar mata akai,bata sake fashin sallah ba,bata kuma sake bari lokacin ta ya wuce ba. Hasalima ita din tana da wani abu.....tana masifar ganin girma da kimar duk wanda ke qoqarin kiyaye sallah,ko wayeshi kuwa. Abun yana burgeta sosai,takanyi lamo tana duban birra wani lokaci idan ta ganta tana sallar dare,abun yana burgeta,amma sai take ganin kamar idan tace ita zatayi ba zata iya ba,kamar ba zata jura ba,wannan yana daya daga cikin dalilan daya sanya birra din ta shiga ranta sosai fiye da sauran hadimanta.

"Khadeeja" Ya kirayi sunanta na asali da wani irin sauti me taushin gaske. Idanunta ta runtse da kyau saboda matsananciyar faduwa da gabanta yakeyi,tanason yana hawaye tsatstsafowa a idanunta.

Tana jin bugawar zuciyarta da kyau har cikin kunnuwanta. Batasan yaushe ya qaraso gabanta ba,tadai jishi ya kira sunanta ne kawai yana tsugunne saman qafafuwansa.

Batasan me ya kawoshi gabanta ba ya tsugunna irin haka yana bar mata qamshinsa ba. Ta bude idanunta a hankali jin bai sake magana ba tana zaton ko ya tashi ne,saidai dukkanin idanun nata sun sauka ne saman lafiyayyar fatar hannunsa dake kwance da gargasa me santsi data bayyana sosai a nade hannun rigarsa take har zuwa gwiwar hannu.

"Khadeeeejaah" Ya sake kiranta da asalin yadda sunan yake a larabce da bayyanar kowanne harafi yadda yazo a larabci,saidai kafin ta sauke wannan tunanin taji kalma mafi girma a bakinsa.

"Kiyi haquri......na manta ne.....na manta ne kwata kwata". Kalmomin biyu suka daketa sosai,har ta samu kanta da daga idanunta da sauri a kansa tana dubansa.

"KIYI HAQURI" Da sauri haka?,kalmar haquri daga bakinsa a sauqaqe har irin haka?.

"NA MANTA NE" Ya manta yace.......yana nufin ya manta da ita kenan fa?. Raurau idanunta sukayi har yana iya gani sosai. Wani abu ya sauka saman zuciyarsa,rauni qarara yake gani daga idanun wannan gimbiyar......wannan gimbiyar me tarin IZZA da jin QASAITA?. Kamar tasan me yake yawo a zuciyarsa sai tayi qasa kawai da kanta tana hana mishi ci gaba da kallon qwayar idanunta.

Ya lura da yanayin data shiga,sai ya miqe lallausan tafin hannunsa yana miqa mata ta qasan fuskarta,daidai lokacin da hawayen masu dumi suka gangaro suka kuma diga akai.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 114*

Wani irin abu yaji ya sauka a jikinsa da saukar hawayen. Ya lumshe idanunsa a hankali ya bude saman tafin hannun nasa Kamar yadda itama ta ware dukka idanunta tana kallon tafin hannun ba tare data dago ba.

Hawayen da take boyewa ne gasu a tafin hannunsa?. Saita daga fuskarta da niyyar maidata gefe,amma cikin wani shammatarta yayi ba tare data ankara ba,ya saka yatsunsa biyu yana riqe habarta gami da waiwayo da fuskarta zuwa saitinsa. Batayi qoqarin qwacewa ba,tunda me ya rage?,abinda take gudu ya riga daya gani,ba gani kawai ba.....hasalima ya sauka ne a tafin hannunsa,kawai saita barshi,ya saki hawayen suka fara zuba abinsu,don dama sun mata qoqari riqe kansu da sukayi kusan awa hudu zuwa biyar baya.

"Ya salam.....kuka?" Ya fada a hankali yana duban yadda kyakkyawar fuskarta ta fada baci da hawaye. Duk da kukan take da gaske tana jin radadin yana fita,amma kuma tana karantar yadda yanayinsa yayi irin sauyawa. Yadda ya furta..

"Ya salam.....kuka?" Da yanayin mamaki da nauyi cikin al'amarin sai ya bata mamaki.

Dukka jikinsa ya amsa gaba daya,da gaske ya tsani kuka......kukanma na mace da ya sani ko Allah baya sonshi. Ya sani ko ubangiji ya rarrashi mata cikin qur'ani a gurare da dama,kamar mahaifiyar annabi musa.......nana maryam da sauransu. Sake mata fuskar yayi,ba zato ta tsinci hannuwansa masu taushi da duminnan cikin nata.

"Kiyi haquri" Ya sake maimaitawa yana jin saukar furucin daga qasan zuciyarsa. Nauyi kalmar take mata,duk da tana cikin fushi da bacin rai,amma duk sanda zai furta TAYI HAQURI din bata mamaki sosai yake sakeyi.

Har cikin qasusuwanta takejin riqon da yayi mata. Wani irin yanayi ne yake bin jinin da yake harbawa zuwa kowanne sashe na jikinta,turarensa da yanayin kusancinsu tana jinsa har b'argonta. Hannunta ta zame kadan cikin qarfafawa kai gwiwa,sai shima ya zame nasa hannun a hankali. Miqewa yayi tsaye,yayi taku biyu baya yana zube hannuwansa cikin aljihun wandonsa. Zuciyarsa yaji tana nauyi a qirjinsa,bayason ya zama silar kukan wani ba bisa kowacce hujjs ba,muryar sultane kawai yakeji a kunnuwansa sanda yake sake jaddada masa.

"Ka riqemin amanar biftu.....na sani tana da wahalar sha'ani.....amma har yanzu qaramar yarinya ce....shekarunta ba masu yawa bane,akwai quruciya akwai wauta na sani sosai tattare da ita".

Taku biyu yayi da baya da baya a hankali kafin ya juya zuwa wani abu me kama da fridge kusa da fridge din. Koda ya bude sai ya zamana kamar wani qaramin kitchen ne a ciki. Mini coffee maker ya jona,ya kuma hada kayan coffee din dake jere a gurin cikin qananun mazubi. Cikin sakanni ya hada komai ya.maida ya rufe,yayi tsaye a gurin hannunsa rungume a qirjinsa. Lokaci lokaci yana daga idanu ya kalleta,har yanzu kukan takeyi,ya lumshe idonsa da qarfi yana sauke ajiyar zuciya. Da gaske kukan dagula masa lissafi yakeyi,yana jin kamar ya mata wani zalunci ne da zata kaishi qara gaban Allah.

"Ya rahman.......ka dafamin,kasa mu gama da ita lafiya qalau" Ya fadi yana kashe na'urar. Har a ransa yana ji bayason ya dauki nauyinta har biyu a kansa. Yayi amfani da ita gurin aiki sannan kuma ya cusguna mata a zamansu?. Bayason wannan taurin kan,bayason wannan musun,wannan rashin ganin girma da darajar dan adam din dukka baya sonsu,to amma shima da kansa ya sani dole saiyayi aiki kafin ya rabata dasu. Duk da komai ma temporary ne,koda zataci gaba daga baya kenan bayan komai na aikin ya kammala.

Qaramin table din gefe ya jawo zuwa gabanta,ya ajiye tray din daya saka cups na coffee din akai sannan ya jawo wani qaramin ottoman ya zauna sun saka tray din kenan a tsakiya.

Cup daya ya dauka na coffee din ya miqa mata. Ta daga idanunta da taji suna mata yaji yaji ta kalla. Tun bai iso gabanta ba qamshin komai ya cika mata hancinta.

"Karbi" Ya fada a tausashe yana tsareta da idanunsa. A hankali ta miq hannunta ta karba din,don ita kanta tasan qarya take tace bata buqatarsa,saidai taji wani banbarakwai saboda bata saba cin komai gaban maza ba. Gaban sultane kawai take iya cin komai,ta miqa cup din zuwa bakinta a hankali zata kurba amma maganansa ya dakatar da ita.

"Bismillah" Ya furta a nutse idanunsa a nutse a kanta saman dan qaramin bakin nan nata masu wani irin siraran lips masu kyau. Dubansa tayi kadan sannan ta janye cup din daga bakinta,tana jinta kamar a takure,fahimtar hakan ya sanyashi zare idanunsa a hankali daga kanta ya maida kan cups din shima ya dauki daya.

Kusan lokaci daya sukakai cup din bakinsu,don haka bismillah din da kowa ya fadi ta fito daga bakinsu kusan lokaci guda,wannan ya sanya kowa kallon dan uwansa,kafin kuma dai su sake janye idanunsu dukka a tare.

"Sallah....banyi sallah ba" Ta fada bayan ta jiye mug din hannunta wanda koda yakai idonsa ya fuskanci ba wani shan kirki tayi masa ba. Haka take tun asali,tana iya kwana da kwanaki dama bataci cikakken abinci ba sai qananun abubuwa irin haka.

"Subhanallah" Ya fada a hankali yana ajiye nashi cup din

"Duka?" Ya tambayeta da wani irin yanayi yana duban tsakiyar qwayar idanunta. Kai ta gyada a hankali tana jin kallonsa yana mata nauyi.

"Garin yaya?,sallah fa.....aikin bawa na farko da za'a fara dubawa ranar qiyama?" Kai ta dauke gefe,tana jin haushi yana kamata. Tana cika sallarta,bata wasa da ita sam sam,kada mana yayi mata kallon me wasa da salla bayan yau dinma laifinsa ne,shine yaja mata?,saita tura bakinta gaba kamar na qaramin yaro dake jin rigima.

Sarai ya gani,abun kuma sai yaso sanya murmushi a fuskarsa. Da gaske abubuwan quruciyarta suna da yawa,ya tura ottoman din yana miqewa sanda take fadin.

"Ba toilet din da zan alwalan" Murmushi yayi kadan ya soma takawa yana nufar wani bango. A sace ta bishi da kallo,wannan tafiyar me izza ba abinda yake canzata ne?,ta tambayi kanta da kanta. Ga mamakinya hannunsa ya dafa kawai ya motsa gefe qofa ta bayyana,gabanta ya wani irin faduwa,tayi qasa da kanta tana ware idanu a hankali.

Ya akayi bata lura ba?,ya akayi bata gwada ba?,kada fa ya dauka bata iya bane?.

"Amma da gaske ban dauka bangon zai bani qofar toilet ba" Ta fadawa kanta da kanta,saidai kafin ta sake tuna komai taji lallausar muryarsa.

"Bismillah" Ya ambata idonsa akan wayoyinsa dake ajiye a gefe wadanda suke haske. Omar ne yake kiransa,ya daga wayar a nutse yana sakata a kunne daidai sanda take takawa tana nufar bandakin kamar wadda bata da kuzari.

Idonsa ya dauke a hankali daga kanta,daga can qasan zuciyarsa yana jin ba dadi kadan. Ya amsa sallamar omar yana aje numfashi,saidai kafin yace komai kiran ya katse,don haka ya maida wayar ya ajiyeta yana sakata a silent.

Idanunta ta ware a hankali tana duban toilet din,tsarinsa yana wani burgeta sosai. Tayi mamakin yadda aka sarrafa ginin har ta gaza fahimtar ina qofar toilet din yake. Ta shiga qasashe da dama taga gine gine iri iri,don haka komai!na toilet din bazai mata wahalar sarrafawa ba,saita taka a nutse tana nufar inda zaifi dacewa da alwalarta.

Yana nan tsaye yana jin motsin ruwa har zuwa sanda ta kammala ta fito. Fatarnan da bata riqe ruwa saboda santsinta tayi damshin ruwa da digo digon ruwa kadan kadan. Da hannu ya mata nuni,ta maida idanunta gurin. Lallausar dadduma ce shimfide a gurin,da babu ita a gurin,sai bayan shigarta toilet din,hakan yana nufin shine ya shimfida mata da kanshi kenan?. Ta daga idanunta ta maida kansa a sace,saita samu ba ita yake kallo ba,ya maida hankalinsa ga cire agogon dake daure a hannunsa. Haka kawai taci zuciyarta tadan matse kadan,tayi tsammanin zata ganshi tsaye ne yana dubanta,saita juya tana takawa a hankali zuwa saman abun sallar,shi kuma ya juya yana wucewa bandakin.

Tafin qafarta ya nutse saman lallausar daddumar,ta daidaita nutsuwarta ta kabbara salla. Sanda tayi sujjada sosai hancinta ya zuqo mata wannan qamshin. Wannan qamshin nasa da ta tabbatar zuwa yanzu a duniya ba wani turare da yayi daidai dashi a gurinta. Wannan qamshin da tayi imanin ta gama son kowanne turare bayanshi. Ta sauke ajiyar zuciya sanda take zaman tahiyya na farko.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Cikin zuciyarta takejin wani irin nutsuwa,a yau sai takejin kamar sallarta ta banbanta data ko yaushe. A yau din tana jin kamar sallar daban take da wadda ta saba yi duka shekarun baya,wata irin cikakkiyar nutsuwa dake sauka a dukka ruhi da gangar jiki,wanda kafin ta kammala ramuwar azahar dinta tana jin yadda wannan nauyin da quncin zuciyar ya dauke gaba daya.

Tana tsaka da ramuwar la'asar ya fito,tayi sallame tana karkatar da kanta kafadar damanta. Idanunta ya sake sauka a kansa,qaramin towel ne fari qal a hannunsa dan qarami yana rage damshin ruwan dake hannuwansa saboda leman dakan zauna a hannun duk sanda ya taba ruwa sakamon gargasar dake kwance a gurin. Ta motsa idanunta kadan tana duban girarsa data jiqe da ruwa,dogayen eye lashes dinsa suma sun harhade dana juna saboda lema,karon farko idanunta yakai kan sumarsa itama data warwatsu saboda shafar kan da yayi lokacin alwala.

Wani abu ya harba kadan a qirjinta,suma ce me santsi da yawa kamar sumar yawan yawan mazan buzaye,saidai tasa ta dabance,tana da santsi sosai da baqin da koda baka taba ba a idanu kawai zaka iya gani,ta kwanto masa kadan ta gefan fuskarsa da kuma gaban goshinsa.

Gabanta ya fadi sanda take dauke idanunta a kansa saboda daga kansa da taga yayi. Kadan ya bita da kallo,yaji a jikinsa kamar ana kallonsa,amma koda ya daga idanunsa baiga kowa ba,sai ya kautar da kansa gudun raunanar alwalarsa yana sake dawowa cikin dakin sosai.

Wani guri ya daga,ya sake ciro wani abun sallar ya shimfida daga gaban tata kadan. Ya sake matsawa kusa da freezer din ya ciro ruwan gora maras sanyi yana takowa a nutse zuwa saman shimfidar. Tayi shuru tana tattara hankalinta guri daya,tana jin kamar zata narke saboda zama da yayi sosai saman abun sallar suna facing din juna.

Qamshinsa ne kawai ke kai kawo a tsakiyar gajeruwar tazarar dake tsakaninsu,ya zube mata manya farare tas din idanunsa dukka a kanta. Idanunta taja ta lumshesu,tana jin wani abu me suna KWARJINI dan gaske yana dukanta kamar zai hallakata. Mamakin bugun da zuciyarta keyi ya saukar mata,kafin kuma a hankali muryarsa ta mamayi kunnenta. Duk da akwai tazara tsakaninsu amma sai takejin muryar cikin kunnuwanta sosai.

Readers Also Read

More by Huguma