L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 67
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 67: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 67. "Sallah tana daya daga cikin manyan ayyukan da ba bawan…
3,367 words
"Sallah tana daya daga cikin manyan ayyukan da ba bawan da zai tsallake ba tare daya samu cikakken report na ingancinta ba. Itace ta farko da Allah S W T yake fara dubawa cikin littafin aikin bawa,idan tayi kyau sallarka azuminka sadakarka da hajjinka umararka da sauran ibadu sun tsallake,idan batayi kyau ba dukka wadannan ibadun ba zasu amfaneka da komai ba. Daga cikin alamun sallarka tana karbuwa,akwai gyaruwar dabi'u da halayenka,komai naka zai sauya zuwa ga yanayi zubi da suffa ba mutumin kirki,haske zai yalwata a fuskarka,muhimmancin sallah ne ya sanya Allah ya umarci mu fara koyawa yaranmu ita tun suna da shekara bakwai,idan sunkai shekara goma basayi a nan gurin kadai Allah ya yarda a daki yaro,idan ya balaga baya yinta Allah yace a kasheshi,itace ibada mafi girma bayan kalmar la'ilaha illallah wato kalmar shahada,itace kadai saboda nauyinta darajarta da kimarta a gurin Allah,saida annabi muhammad S A W yayi tattaki yaje da kansa ya karbota daga gurin Allah,ita daya ce annabi muhammad ya yiwa wannan tattakin. Ba'a taba wanda ya riqe Allah gurin sallah ya wulaqanta ba,ba'a taba wanda ya nemi arziqi gurin sallah ya rasa ba" Ya qarashe maganan da wani irin cool tone. Wani abu me sanyi taji yana sauka a zuciyarta gaba daya,girman sallah taji yana sake qaruwa cikin zuciyarta,ta lumshe idanu maganganunsa suna mata amsa kuwwa a kunne.
Ashe tun daga shekara bakwai ne ake fara umartar yaro da sallah?. A hankali sai tunaninta ya koma baya,a hankali saita koma tata rayuwar shekara bakwai baya. Komai ya fara dawo mata tarwai kamar wadda aka dauko faifan CD aka saka mata.
"Duka duka nawa take da za'a dameta?,batakai minzali ba ki qyaleta kawai.....don dai bakyason yarinya saiki addabeta da sanyin nan a dinga tashinta sallar asuba?,tana tsakiyar wasa kisa hadimai su daukota su kaita tayi alwala?,kinfi kowa sanin Allah ne safiyya?,wanne irin matsi ne wannan?.....dondai bake kika haifeta ba?" Wasu daga cikin maganganun mammina suka dawo mata a sanda morsa safiyya ke qoqarin sanyata ta fara tsaida sallah a lokacin. Ta tuna sanda takai guraren shekaru goma,a sannan ma mammina ta daina tare mata,duk wani bawa ko hadimi daya matsa mata tayi sallah ranar yaga ta kanshi. Zata masa kome taga dama,zata gaya masa maganganun duka da sukazo ranta,daga qarshe kuma ta kaishi qara gurin mammina. Sanadin wannana abun kuma saiya karbi hukunci kamar wanda yayi wani mummunan laifi. Hairaan itace mutum daya data gagari mammina,zatayi mata dirar mikiya a dukka lokutan sallah,tana kuka tana zumbura baki haka zata tilastata suyi alwala tare suyi kuma sallar tare. Ba zata manta dambarwar da suka sha tsakaninsu da hairaan ba,baran baram sai daya zamana ba shiri tsakaninsu,amma daga qarshe ba zatace ga yadda akayi sallar tabi jikinta ba.
"Morsa safiyya tafi mammina gaskiya kenan a wannan lokacin?" Ta yiwa kanta tambayar da taji ta tsaya mata cak! Cikin kwanyarta.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 115*
Duk da idanunta suna qasa,amma kamar ya fahimci akwai abinda take nazari. Ya maida idanunsa kan agogon hannunsa,lokacin sallar magariba yayi,don kamar yana iya jiyo kiraye kirayen salla.
Idanunsa ya sauke kan ruwan gorar,ya dauka yana budeshi gami da juyawa ya bata baya ya fuskanci alqibla. Tana jin yadda yake zuqar ruwan a hankali,yanayin shan ruwan nasa sai takejinsa da wani sauti da yanayi daban kamar ba yadda mutane suka saba shan ruwa ba.
(Eh,da gaske ne,hatta da shan ruwa akwai hanyoyin shansa,musulunci ya koya mana yadda zakasha ruwa,wani daga annabi,wani daga malamai don rayuwa tayi albarka,musamman yaro anaso a tarbiyyantar dashi yanayin shan ruwa sosai don ya girma ya kuma saba da hakan,addinin musulunci yana da ban sha'awa sosai,kawai mun rufe idanunmu ne rayuwar yahudawa tana burgemu sama da wannan,bayan rashin fahimtar addinin yasa muke masa kallon kamar bagidajen addini ne,saidai kash.....duk wata wayewa da muke kalla me kyau da tazo duniya asalinta daga musulunci tazo.....daga larabawa take).
Tana jin sanda ya kammala ya ajiye gorar ruwan gaba daya,da tattausar muryarsa dake can qasa tajishi yana addu'ar.
"Zahabaz zama'u,wabtallatil uruuq,wasabatal ajru in sha Allah". Shuru ya ratsa dakin,ta daga idanunta a hankali ta gefansa sai taga kaman ya hade lausasan fararen tafukan hannayensa ya budesu guri daya yana addu'ar da bata iya jin komai a cikinta.
Yatsunta ta kalla tana irga ranakun mako,yau litinin,tabbas yau litinin,hakan yana nufin azumin litinin da alhamis yakeyi?,da wannan matsanancin zafin daminar da ake fama dashi cikin agadez?. Bata sake wani tunani ba taga ya miqe.
"Muyi sallah" Ya furta yana gyara tsaiwarsa,sai kuma ya waiwayo a hankali yana dubanta ba cikin idanunta kai tsaye ba.
"A bayana daga bangaren dama na zaki tsaya,nan ne gurin tsaiwar mace idan zatayi sallah da namiji" Ya fadi yana saita mata daidai gurin da yatsunta. Motsawa tayi kadan zuwa inda yake nuna matan,tana jin wani nauyi a ranta da zuciyarta. Bata taba sani ba,hasalima bata taba sallah cikin jam'i ba idan ba umra taje ba. Ta lumshe idanu tana tayar da kabbara itama bayan ya tayar da tasa,tana jin wani irin sakeena cikin zuciyarta.
*M A M M I N A*
Duk adadin masu tsaro da sanya idanun data baza tsakanin qofofin gidan dama qofar data zama ita kadai ce yanzu ta shigowa cikin gidan ba wanda ya bata labarin ganin dawowar sheikh muhammad haisam ballantana princess akhnan. Tun daga sanda ta koma ciki nutsuwarta ta sake qaurace mata. Dukka kwanakin dama gatanan gata nan ne,bacci cikakke bata iya yinsa,daga ta kwanta take tashi saboda zulumi da fargabar INA ALMAZ?. Duk irin kudin data narkar akan jami'ai kala kala na shige da fice cikin sirri wajen gano mata koda footprint na almaz yaci tura,sai kuma a yau din ta soma hango wata babbar faduwar da jikinta yake bata tana tunkararta.
A kaf tarihin rayuwar akhnan din.....wannan shine karo na farko data fara karbar umarni daga WANI ba ita ba ba sultane ba.......umarnin da binsa ya zama wani sassauqan abu har ita dake nesa ta shaida haka.
Tuna hakan kawai yana harba wani abu me qarfin gaske a zuciyarta da jikinta,yana saka wani babban shakku akan anya wannan din BA D'AN IBRAHEEM bane?.
Tun tana lissafin awa daya kacal zasu dawo,har ta koma lissafin zuwa azahar ne. Daga azahar ta maida fatanta ya koma la'asar,saidai shigowar magariba ya sanyata ta gaza haqurin hadiye maganar a cikinta. Sassan akhnan din ta fita da kanta,su birra da taga dawowarsu tun kafin azahar din tayi suka sake bata tabbacin tana tare da sheikh haisam din,kuma har yanzun basu shigo ba.
"Wanne irin take al'ada ce haka?,wanne irin rusa lissafi ne wannan?,ba izini ba komai ka dauki 'yar mutane?,shin ina ya kaita ma kenan?" Ta tambayi kanta saidai tambayar ta kasance a bayyane,abinda ya dasa mamaki sosai azukatansu buhaina din.
Birra ta gaza daurewa,don zuwa yanzu ta gaza fahimtar meke daga hankalin giwa ne a duk sanda wata kebewa ta ratsa tsakanin sheikh haisam da uwar dakin nasu?. A iya nata sanin aure aka daura musu,kuma aure na sunnah ma me daraja cikin raudar ma'aiki,ba kebewa kadai ba......tana ganin ko meye a yanzun sheikh muhammad zaiyi halas ne.
"Lafiya ce take buya Allah ya taimakeki....ina ganin tunda akwai mijinta a tare da ita ba ita kadai bace komai mai sauqi ne" Idanu ta zubawa birra tana qanqancesu ciki,saidai kuma duk kalar magana da hukunci da take qiyastawa akan yarinyar ya rushe sanda zuciyarta take nanata mata.
"Lullubabben sirri ne zeenatu,duk sanda aka matsa akan komai kowa zaiga abun banbarakwai,tabbas a idanun kowa yake mijinta,amma a naki idanun lamarin dabanne,ke kadai kikasan komai" Ta fadawa kanta.
"Haka ne...." Ta amsawa birra a taqaice ta miqe tana takawa a hankali tana barin gurin.
Kallon kallo suka koma yi a tsakaninsu,sai buhaina ta sheqe da dariya. Idanu suka fidda cikin tsoro suna yiwa buhaina alamar tayi shuru.
"Aita tafi....wallahi saina fada....hala ta manta sheqe ayar data dinga yi da me martaba farkon aurensu?,batasan iyayenmu sun bamu labari ba?,haka kawai ki tsagal ki dinga shiga tsakanin miji da mata?,na meye?,idan tazo tana mutuwar son mijinta maga yadda za'ayi". Dariya dukkaninsu suka saka,banda birra data murmusa.
"Kuma jikina yana bani kwanan nan haka zata faru......akwai abubuwa da yawa da nasan tanaso tattare da namiji.....wallahi dukka yana dasu" Ta fadi gana gyada kanta a hankali. Idanu suka zuba mata son son jin gulma
"Allah ko?" Bara'atu ta fadi,saboda ta sani dukkaninsu ta fisu kusanci sosai da akhnan din. Tafi kiran sunanta kafin na kowa,tafi nemanta kafin kowa.
"Jinin annabi yusuf kam koda baida abubuwan da takeso zaiyi saurin jan hankalin mace tabbas" Bushira ta fada tana girgiza kai.
"Yana dasu.....harda qari,wani LU'U LU'U ne dake sheqi wanda ba kowa ke gane qyallinsa ba,sai a hankali sanda ruwa ya wankeshi da kyau ya sake bayyana" Birra ta fadi tana murmushi,tana fata inama zata samu koda kwatansa ne,can qasan zuciyarta tana jin fata da burin ya zama mallakin uwar dakinnata na har abada.
Babbar balcony dinta na qarshe da zai bata daman ganin farfajiyar ajiyar motocinsu ta zauna,saman qananun kujerun dake gurin,ta sake daukar wayarta tana sake neman number akhnan din,ba kuma wai don tana da tabbacin samunta ba. Still dai kamar dazun wayar tsinkewa takeyi kawai,don ko computer bata tsaya fadi mata dalilin tsinkewar wayar. Ta kalli fuskar wayar tana jin jininta yana tafasa. Wannan shine kira na ashirin da tara data mata daga dazun zuwa yanzu,amma ba wanda aka bata dalilin qin shigar wayar ma ballantana kiran yakai ga shiga.
"Tafisu" Ta kira sunanta da wani irin birkicewa.
"Allah ya taimakeki"
"Ina gudun faruwar wani abu"
"Me kenan?" Ta tambayeta cikin kulawa.
"Zuciyar mace tafisu,tana da wani irin saurin aminta saurin yarda da saukowa gami da bada kai.....musamman zuciya irinta JININ SAFEENA......ta yarda ta auri ajani duk da bata sonshi,amma hakan bai hana hada jiki dashi ba harta haifa masa yaron da ko duniya zata tashi zai tabbata a maras alfanu har ABADA.....ya komai zai kasance idan zuciyar Akhnan ta zama irin ta uwarta?" Ta qarashe maganan tana duban tafisu dake rusune a gefanta kamar tana neman ainihin sahihiyar amsa.
*AKHNAN/HAISAM*
"Komai ma yana da tsarinsa?,komai ma yana da addu'a?" Ta yiwa kanta tambayar idanunta qasa qasa tana takawa cikin kamewa tana biye da haisam din.
Kowacce qofa da zai maidata ya kulle sai taji ya ambaci wani abu,abin ya dinga mata yawo akai,har zuwa sanda suka kawo bakin babbar budaddiyar balcony din data cikinta zaka wuce zuwa ainihin cikin gidan inda suka fito.
Tana lura dashi,ya daga kansa sama a hankali yana duban yadda ruwan sama ke sauka da qarfinsa.
"Allahumma sayyiban nafee'an" Ya maimaita a hankali har sau uku kafin ya sauke kansa qasa a nutse.
Addu'ar ta shiga kunnenta sosai,ta fara juyata a ranta tanason gane ita kuma addu'an mecece?. Wani gefen na zuciyarta kuma yana cike da taraddadin yadda zata shiga ruwan har takai bakin motarsu.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Cikin muryar nan tasa mai taushi da nutsuwa wadda ke da zurfi a wasu lokutan taji yana magana qasa qasa wadda bata haura ta second uku ba kafin ya kashe wayar. Aljihu ya jefata,yana ci gaba da kallon zubar ruwan saman. Addu'a yakeyi kala kala cikin ransa,wanda ya riga daya zame masa jiki,saboda lokaci irin wannan lokaci ne na amsar addu'a. Yaji kewa sosai cikin ransa,yaji kewar jimma tana taso masa,yaji kewar library dinsa. A irin lokaci irin wannan jimma tana zama koriya da Tarin tsirrai masu ban sha'awa. Kamarshi me son tsirrai da gandun daji,yana jin dadin yawon bude idanunsa sosai,ba qura ba zafi,duniya tana yin wani irin sanyi dake bawa zuciya da ruhi nutsuwa.
A hankali ta cure jikinta guri daya saboda sanyin da yake kadata na ruwan. Ya daga idanunsa ya aza a kanta yana karantar yanayinta. A nutse ya saka hannunsa ya zare rigar samanshi ta yadin cashmere din me zubin alkyabba sannan ya fara takowa inda take idanunsa a kanta.
Ba zato ba tsammani taji wani abu me taushi cakude da sassanyan qamshin nan daya zame mata JARRABI sun mamayeta. Wani abu ya tsarga mata tun daga tafin qafarta zuwa tsakiyar kwanyarta,ta lumshe idanunta tana jin yadda numfashinta yake fita da sauri.
Taku uku kawai yayi ya sake bata tazara bayan ya tabbatar rigar ta zauna a kafadunta,sai ya dauke dubansa daga kanta don ya bata daman gyarawa yadda zaiyi mata dadi. Dukka hannuwansa ya cusa cikin aljihun rigarsa yana dage kafadunsa sama gami da hade jikinsa kadan,still idanunsa kan farfajiyar dake da yalwa da haske tarwai.
"Mota ta kusa qarasowa" Ya fadi a taqaice sanda ta sanya hannuwanta dukka biyun tana qanqame rigar a jikinta,wani yanayi da tunda aka haifeta yana taso mata karon farko a matsayinta na cikakkiyar 'ya mace me cikakkiyar lafiya.
Hasken motar da aka rage da tahowarta gurin ya sanya ta daga kanta a hankali har zuwa sanda motar ta tsaya daidai gabansu dab dasu,ta yadda feshin ruwan ne qila kawai zai iya tabasu.
Wanda ya tuqa motar ya fito,maleek ne saidai yayi shigar basaja ta yadda sam ba zaka gane shima nasa matsayin ba. Suka hada ido da akhnan suka janye kuma lokaci daya,saidai haka kawai cikin jikinta take ganin wani abu daban tattare dashi bawai driver ba.
Shi da maleek din ba wanda ya cewa da kowa komai,ya bashi key din kawai,shi kuma ya karba yana cewa.
"Na gode" Sai ya waiwaya gareta ya kalleta sau daya,yanayin daya alamta mata yana gaya mata suje ne.
Ya rigata isa bakin motar,kamar daxun yanzu ma hannu ya saka ya bude mata qofar motar. Takowa take a hankali,kasala yana lullubeta,qamshin yana kassara jikinta,mamakinsa kuma yana saukar mata. Ya maida motar ya rufe,ya kuma zagaya da sassarfa don komawa nasa side din,ta bude idonta a hankali ta zubesu a kansa sanda yake zagayowa ta gaban motar zuwa nasa seat din.
Sake maida idanun nata tayi sosai ta rufe su,tambayoyi fal cikin kanta,tana jin sanda ya furta.
"Bismillahir rahmanir rahim" Sanda yake qoqarin kunna motar.
"Me yasa yake hidima da ita?" Tambayar datafi tsaya mata kenan da tarin ban mamaki. A dazu da yake bude mata mota cikin gida kafin su fito,ta dauka yayi ne kawai don idanun mutane dake kansu,yayi ne saboda ya burge,yayi ne don ace yana da kirki,sai gashi yanzun,a gurin daba kowa sai su biyu,a gurin da idan yana so zai iya wulaqantata,a gurin da idan yanaso zai iya tozartata,amma girma yake bata.
"Kiyi haquri" Ta sake tunawa da kalmarsa ta dazu daya maimaita har sau biyu.
Shuru motar ta sake dauka,saidai cikin kwanyarta da zuciyarta hayaniya ce kala kala take tashi. Ya mata zafi.....ya mata sanyi duka lokaci daya,wanne irin mutum ne?.
Abinda bata sani ba manufar zuciyarsa daban. Har yanzu yana iya tuna wani sashe daya karanta na tarihin annabi muhammad. Sanda yaci garuruwa da yaqi bai wulaqanta manyan mutane masu daraja ba,ya girmamasu daidai da yadda mutanensu kafin musulunci suke girmamasu,har yanzu wannan din halin da yake qoqarin koyi ne dashi. Yana cikin MULKI yana cikin SARAUTA yasan yadda sukebin jini suke barwa mutum wasu dabi'u koda bakayi nufin aiki dasu ba.
Shurun ya masa yawa,sai ya lalubo karatun sheikh sudais ya saka cikin suratul rahman.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 116*
Wata irin sabuwar nutsuwa taji tana sake saukar mata,ta sake narkewa sosai cikin seat din tana jin kamar zata hade su zama abu guda dashi. Sosai ta sake qanqame rigar cikin jikinta,wani dumi takejin tana bata.....wani irin yanayi da ita kanta ba zata iya tantanceshi ba.
Kiransa da akayi a waya ya sanyashi rage kashe dukka volume na karantun,tana fahimtar komai,girmamawarsa ga alqur'ani. A wacan ranar cikin dakinta ya barta da karatun qur'ani sanda zai fita,wanda kafin sannan ya rage volume dinsa gaba daya sanda yake magana da ita.
Omar ne,sai ya saka wayar a kunnensa yayi cikakkiyar sallamar data qarawa muryarsa da yanayinsa kamala.
"Maannn......kada kacemin har yanzu kuna gurin taron kammala karatun?" Muryar omar kawai da yanayinsa sun isa su tabbatar masa kiran bana Allah da annabi bane.....baya ga haka kuma Omar din da yasan gidan da yake?,duka duka awa nawa sukayi da rabuwa bayan sun kammala aikinsu?.
"Omar...." Ya kira sunansa da wannan serious voice din nasa data ratsa akhnan.
"Yana da mabanbantan siffofi" Ta fadawa kanta da kanta.
"Na dauka honeymoon ne ya fara,mu tattare kayanmu tun yanzu mubar agadez,mission accomplished tunda mun samu wadda tayi mana wuf da captain jagoran tafiya" Sarai yaji saukar dukka kalamansa,amma da wannan izzar da miskilanci ya sake basarwa.
"Muna kan hanya" Ya kuma amsa masa a taqaice yana fatan ya barshi haka.
"Kan hanya tun kusa awa hudu kenan?,hanyar ce ta qara tsaho?,ko kuma akwai wadda ta riqe hanyar da kyau?" Ya fadi yana dariya. Ba iya omar kadai ba,yaji alamun khadeem da amjada gurin,alamun sun hada baki kenan suka kira su tsuyeshi?.
Numfashi yaja a hankali yaja saukeshi a boye.
"Ka kira ne don kayi tambaya ko don ka qure mutum?"
"Duka biyun" Yaji amjad ya karba.
"Amjad mana" Haisam din ya fadi,saboda bayaso suja doguwar magana da zata fahimci wani abu.
"Ka manta muna jiranka ne?" Amjad ya sake tambaya.
"Akwai abubuwan da ba'a gaggautasu" Yayi qoqarin kaucewa zancan.
"Wannan sabuwar magana ce.....haisam da baya bata lokaci,baya qyalewa a jirashi?"
"Ya samu babban dalilin da ya sanya lokaci ma ya daina biyayya a gareshi....duka ma yana mantawa da wannan lissafin nasa na kiyaye qa'idar lokaci" Ya jiyo omar ya fada yana dariya.
Lips dinsa ya cije kadan da wani miskilin murmushi saman fuskarsa,yana kuma sarrafa steerig motar da kyau cikin wani irin gwanancewa. Wasu irin abokai ne na amana,da suka zame masa tamkar uwa daya uba daya,suna jin junansu har cikin jikinsu.
"Ka kiyaye kalamanka" Ya aikewa omar gargadi.
"Na kiyaye.....amma mun samu shaida mun kuma bada uziri,daga yanzu a duk sanda ka makara a wani abu.....tabbacin abinda ya sanyaka makara ba qarami bane......ya shiga cikin tsarin doka" Amjad ya fadi suna dariya sosai abinsu.
Koda baiso ba saida murmushi ya wanzu akan fuskarsa na wani dan lokaci kafin ya daidaitata. Ya saci kallonta don ba abune daya kamata ace taji ba,saidai gefe ya samu tana kallon titunan da suke wucewa.
"Zan iso in sha Allah,ku fara" Ya furta yana katse kiran,ya kuma maida karatun daidai yadda yake.
Duk wata fitar kalma guda daya daga bakinsa tana fita ne da wani irin tsari gami da iya tafi da wanda yake magana dashi,bada uzuri da kaucewa samun sabani,wannan shine abinda zuciyarta ta rubuta mata daya sanya ajiyar zuciya subuce mata.
Karatun shi yaci gaba da musu rakiya,har zuwa sanda suka isa masarauta. Masu tsaron qofofin suka dinga dage masa kai tsaye cikin girmamawa yana sanya motar a hankali cikin qwarewa. Kaman ruwan yafi yawa a ta nan,ko kuma jira yakeyi su iso sai ya qara qarfi,daidai sanda yake ajiye motar a kebantaccen gurbin ajiyar motoci na gidan.......daidai lokacin da mammina ta sauke idanunta akan motar.
Ido ta zubawa motar,cikin nazari da mamakin su waye a cikin ta. Sai ta zabi ci gaba da duban motar daga nan inda take zaune.
A hankali ya kashe motar gaba daya,ya zare belt din jikinsa cikin nutsuwa yana ajiyeta a gefe. Duban saukar ruwan kawai takeyi da idani,ta qiyasta yadda zai tabata da kyau kafin ta samu qarasawa ga sassan nata,gabanta yadan fadi ganin ya bude murfin motar ya fita.