L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 68
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 68: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 68. Saman idanun mammina ya fito,ta qanqance idanunta da…
3,330 words
Saman idanun mammina ya fito,ta qanqance idanunta da kyau tana jin wani abu me nauyi yana sauka a qirjinta. Daga nan inda take kwarjininsa ne still yake iya taras da ita harma yana dukanta,abinda ya sake qara gudun zuciyarta kenan,ta kuma samu kanta da kanta da tambayar ME YASA YAKE MATA KWARJINI NE HAR HAKA?.
Ita da akhnan din dukkansu suka bishi da kallo sanda yake zagayawa daya seat din da akhnan din ke zaune. Saidai dukkaninsu ba wanda yasan da kallon da daya yakewa daya.
Babbar lemar dake riqe a hannunsa ya matsa,sai gata ta bude,ta kuma bada yalwatacciyar rumfa da zata hana ruwan sama cimmata.
Bata lura da hakan ba,har zuwa sanda ya bude murfin motar,ya kuma ja da baya kadan yana dubanta da manyan idanunsa.
Qasa ta rusunar da idanuwanta,tana jin abun da wata matuqar martaba da girmamawa,ta kuma motsa a hankali tana fita a motar,yayin da shi kuma ya saita lemar daidai kanta don hana ruwa daman tabata.
Batasan ruwa akeyi haka sosai ba sai data sanyo qafarta waje,ta bayanta ya zura hannu daya ya maida motar ya kulle,daidai sanda ta waiwayo saboda jin yadda kusanci yayi yawa a tsakaninsu. Saura qiris fuskokinsu su hadu guri daya,sukayi musayar numfashi shi da ita,abinda ya sake kassarata gaba daya har sai data riqe numfashin nata na wasu sakanni. Ta budesu a nutse,daidai sanda ya kawo hannunsa saitin yadda zata gani yana mata nuni da hannunsa da hanya alamun suje.
Tsam mammina ta miqe tana jin zama yana gagararta. Ta matso bakin qarfen balcony din tana qarewa duk wani dagawa da saukar qafafunsu kallo..
A sanda yake biye da ita a bayanta.....a sanda yake maida qafarsa a duk wani gurbi data dauke nata.....a sanda ya sanya lema ta zame mata rumfa da kariya daga ruwan sama,ba kkmai yake hangowa ba sai ZAKI dake bada kariya ga ZAKANYARSA.
Wani irin gizo suke mata dake sanya zuciyarta bugawa. Wannan tsahon daya maidashi GIANT na anihi,gaba daya ya laqume akhnan din a gabansa. Manyan kafadunsa da qirarsa me bayyanar da qarfi kai tsaye,gaba daya ya katangeta wanda yake bayansa ma ba lallai ya iya ganinta da kyau ba.
Tamkar dama wannan tsaron masa......tamkar dama wannan qirar tasa dukkaninta an halicceta ne don AKHNAN kadai.
Tana takawa ne cikin tsantseni saboda yadda yake dab da ita,ta tabbayar motsi kadan zatayi jikinta ya gogi nasa. Ta sani lemar ba lallai ta iya daukesu ba ita dashi,bata da tabbacin ruwa baya tabashi koda ta baya ne.
Saidai kuma duk yadda taso kiyaye alaqar jiki a tsakaninsu hakan ya faskara. Don kuwa kyakkyawar walqiya akayi wadda ta sanyata tsaiwa cak ba tare daya waiwayo ba. Banda yana da hanzari da zafin nama,tsaiwarta katsam zata iya jawo cakuduwar jikinsu koda basu shirya hakan ba,saidai ya tsaya cak saboda zafin naman daya nuna gurin tsaiwar da ainihin tazarar dake tsakaninsu na farko.
Bugawa kawai zuciyarta takeyi,ta riga ta camfa muddin akahi walqiya tsawa tana tafe,to yaya zata Fahimtar dashi tsoronta?,idan aka samu tsawar yaya zatayi?.
Tsawar kam bata barta ta samu amsa ba,ta tarwatse cikin sararin subhana tana me isar da saqon da mahaliccinta ya bata. Wata qaramar qara ta saki,ta juyo da wani mugun hanzari,ba tare data tsaya tantance me takeyi ba ta fada jikinsa tana masa wani kyakkyawan riqo.
Kyakkyawan masauki ta samu cikin qirjinsa,tana cusa kanta cikin qirjinta kamar wadda wani mummunan abu ya biyo zai kama,zuciyarta na wani irin bugawa da sauri da sauri.
Cak komai ya tsaya masa......cak mumfashinsa buguj zuciyarsa jinsa dama ganinsa ya na wasu daqiqu kafin ya zuqosu da qyar yana fesarwa.
Hannunsa ya daga a hankali da zummar dagota,yana iya jin bugun zuciyarta cikin allon qirjinsa,kaman yadda yake iya jin riqonta har cikin bargonsa........amma sai ya samu kansa da aza tafin hannuwan nasa saman bayanta a hankali.
Da gaske ya fahimci takeyi,da gaske ya fahimci tsoro takeyi,sosai kuma ya fahimci ba qaramar razana tayi ba.
Ya dauka minti daya ko biyu ne kawai zata dago.....ya dauka sakanni qalilan zatayi ta tashi,amma sai yaji abun yana niyyar zarcewa wadannan mintunan saboda ci gaba da haskawar walqiya a sararin samaniya bayan kowanne second. Idanunsa ya lumshe,tashi zuciyarce take bugawa,tashi zuciyarce ke wani irin tsalle a qirjinsa.
"Alhamdulillahil lazi yusabbihur r'adi bi hamdihi wal mala'ikatu min kifatih" Ya furta a hankali yana ci gaba da maimaitawa.
Sannu a hankali addu'an ya soma shiga kunnuwanta,sannu a hankali numfashinta ya soma daidaita,sannu a hankali tafin hannunsa dake tsakiyar bayanta ya soma nutsar da wani abu cikin b'argonta da jininta,nutsuwa ta fara saukar mata.
Kamar wadda aka radawa.
"A jikinsa kike" Tayi azamar miqewa daga jikinsa bugun zuciyarta yanaso yaci gaba da harbawa,saidai maganarsa ta bada wani irin relief me shiga zuciya da wani irin sanyi.
"Tsoro halitta ne.....amma ba abinda ke kwantar da zukata irin ambaton Allah a lokutan tsoro da fushi". Idanunta ta lumshe tana jin wani nauyi yana saukar mata. Wai me yasa yau komai yazo a haka?,me yasa yau komai yake zuwa a hagunce?.
"Bismillah" Ya furta a nutse da wannan coolness din nasa,wanda a yau har cikin gabbansa yakejin wannan sanyin da mutuwar jikin.
A nutse ta soma takawa tanayin gaba,yaci gaba da biye mata riqe da lemar.
Har cikin ranta takejin wani safety da tsaro me girman gaske,sosai takejin aminci da wani irin girma sanda yake biye da ita.
Wani irin numfashi mammina taja ta kuma sauke tana jin yadda qirjinta ya riqe. Hannu tasa ta dafe gurin sosai tana runtse idanu saboda wani irin suka da yake mata. Biftu?,akhnan?,akhnan dince a kwance qirjin wani?,akhnan dince rungume da wani namiji?,hakan fa yana nufin abubuwa masu dama....hakan fa yana bude qofofi ne masu yawa da girman gaske.
Ta juya da dan zafi da nufin fita ta sauka ta cimmata,amma sai tafisu da taga komai daya faru ta riqeta da sauri.
"Kada kiyi gaggawar zuwa yanzu Allah ya baki nasara.....karki zama cikin alamun matsi da takura. Matsanta mata da takura mata a yanzu ba abinda zasu haifar sai qarin bijire miki".
" Tafisu.....bakiga yadda yake juya akalar komai yadda yaga dama ba?,bakiga yadda komai yake canzawa daga muhallinsa ba duk don saboda shi?,bakya hangen akwai yuwwar hurewa biftu kunne?,dole inason haduwa da ita,inason in sake karantar inda tunaninta ya dosa".
"Za'a kira miki ita,amma bada kanki ba" Tafisu ta furta cikin girmamawa. Shuru ta danyi kaman me nazari,kafin ta zame hannunta daga riqon da tafisu tayi mata,ta taka zuwa bedroom dinta,wannan ya bawa tafisu tabbacin ta aminta da wannan,don haka tabi bayanta ta kuma sauka tana umartar yalwa da kiran gimbiya akhnan din.
Sanya qafarta cikin balcony dinta,da samun tabbacin zuwa inda ruwa bazai tabata ba ya sauke lemar a nutse yana lanqwasheta. Taci gaba da takawa da wani irin sanyi zuwa babbar qofar sashenta dake maqotaka da tashi,tana jin wani abu cikin jikinta sosai yana mamayarta.
Yau din ta tabbatar tun daga nan ta ajiye mata wani memory me girma da kuma nauyi,abubuwa da yawa basuzo yadda ta tsarasu ba,sun faru kaman yadda Allah ya hukuntasu,amma kuma akwai wani abu me qarfin gaske daya tsaye mata cakkk wanda batasan meye ba.
"Barkanku da isowa" Da ita dake qoqarin qarasawa sassanta,dashi dake tsaye qyam saman qafafunsa,hannayensa zube a aljihun rigarsa yana duban inda duk take saukewa da dauke qafarta yana son tabbatar da shigarta sashenta kafin ya wuce nasa sashen muryar armelle ta sauka a kunnensu.
Fuska ya saki a hankali yana amsa mata gaisuwar data masa sannan ta maida dubanta ga akhnan.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 117*
"Komai dare morsa safiyya tace a shaida miki tanason ganinki lallai lallai" Maganan yazo mata a wani iri,karon farko data taba kiranta kai tsaye zuwa sassanta. A duk sanda takeson ganinta ko magana da ita idan haka ya kama ko ya zama dole,tana tattaki da kanta tazo ta sameta ne,idan taga dama ta ganta,idanma bataga dama ba taqi bari ta ganta.
"Ki shaida mata......"
"Zatazo.......zatazo yanzu in sha Allah" Muryar haisam ta mamayi tata. Murmushi ya subuce a fuskar armelle,murmushin farinciki,murmushin jin dadi,yaqini yana sake sauka a zuciyarta TABBAS TSAYAYYE NE SHI DIN ta fadawa kanta da kanta.
"Muna godiya" Armelle ta furta cikin tsananin farinciki sannan ta taka a nutse tana barmusu gurin.
Da kallo tabi armelle,yayin da shi kuma ya zubawa fuskarta idanu. Ido ya lumshe a hankali yana janye dubansa daga gareta. Wannan baby face din ta cika da dan siririn bacin rai,ita dole ance taje ga matar da take a mazaunin mahaifiya a tare da ita?. Wannan girman bacin alaqar har ina?.....wanne irin aiki akayi haka me zurfi wajen raba wannan qarfi da kaurin JININ?.
"Komai zai gyaru....komai zai gyaru in sha Allah.....bazan jewa nanay da albishir din ganin obboleettii lamaan dinta da wannan mummunan yanayin ba......diyar safeena bata dauki safiyya a matsayin uwa ba?.
Dubansa takeso tayi cikin tsakiyar idanunsa,taga wanne qarfin gwiwa ne ya bashi daman yanke mata hukunci?,me ya dogara dashi da zai tilastata ko ya sanyata zuwa ga morsa safiyya a sanda batayi niyya ba?. Yau kadai yana zaton ta bashi wannan zarrar?. Yau kadai yana tunanin ta bashi wannan damar?,ta bashi wannan qwarin gwiwar?.
Duka tayi wannan tunanin ne a sanda take duban idanunsa kai tsaye,duk da wani irin nauyi dake cikin nasa idanun dake barazanar durqusar da nata qarfin gwiwar. Shima yana tsaye......da wannan tsaiwar dake fadiwa me kallonsa tsayayyen ne tun daga haihuwarsa har kawo yau.....wanda bai gajiya da tsayawarsa akan dukkan komai.
Tsaf ya karanci abinda ke kai kawo a zuciyarta. Sai ya zare idonsa a hankali ya kuma fara juyawa.
"Qanwar uwa a matsayin uwa take a musulunci,kyautata mata daidai yake da kyautatawa mahaifiyar data haifeka......hakanan munana mata kai tsaye kamar munanawa mahaifiyar taka ne" Bai dad'a ba bai qara ba,yaci gaba da sauka a nutse,bai kuma sake koda waiwayarta ba.
Duk yadda taso kada maganansa ya mata tasiri ko kadan amma hakan ya faskara,tabi yalwatattun kafadunsa da kallo har ya bacewa ganinta,saita juya tana murda handle din qofar data kasance kebantacciya saboda ita kadai ta tura tana saka qafafunta.
Taku daya tak masu kula da qofar suka fara mata maraba. Ba wanda ta kula don kanta cike yake kawai da kalamansa. A haka ta ratsa dukka parlors dinta ta haura zuwa bedrooms dinta. Har ta gifta bedroom din dake fuskar gaba sosai ta ginin nata saita koma da baya,abinda ya sanya birra takowa da sassarfa ta bude mata don ta karanci nan take da sha'awar kwana,idanun birra dai akan rigar dake maqale saman dukka kafadunta,wanda ta tabbatar rigar sheikh haisam ce.
Da mamakin birra tayi tsaye yau da kanta tana fidda dankunnenta da sarqarta ba tare data jira an cire mata ba. Sai datazo zuge zip na rigarta sannan ta waiwayo ta kalli birra. Ta tako a hanksli hankali ta tsaya gabanta,amma saita kalli rigar saman jikinta. Itama dubanta takai ga jikin nata,rigar ta kwanta luf tana fidda qamshin nan nasa saika dauka yana cikin dakin. Ta manta kwata kwata da ita,birra ta miqa hannu zata janye mata ita,saita samu kanta da dakatar da ita,ta saka hannu ta zareta a hankali tana jin yadda yadin yake wani yauqi yauqi a hannu ne dadin tabawa. A nutse ta ajiyeta gefan gadon,sannan ta juyawa birra ta tayata rage kayan jikin nata.
"Yalwa ta shigo yanzu yanzu kina dab da shigowa" Birra ta fadi tana qoqarin ninke rigar data cire din. Bata amsawa birra ba,tana zare band dinta daga kanta,abinda ya bawa doguwar yalwatacciyar sumarta daman warwatsuwa a kafadunta zuwa gadon bayata daura da mazaunanta. Shurunta ya ganar da birra komai,don haka ta wuce zuwa ga fadin saqon.
"Tace giwa na buqatar ganinki a daren nan" Sai maganan ta tsaya iya nan kawai. Ko daya bataji a ranta zata je ba,to taje tayi me?,tana zaton duk wani deal tsakaninta da mammina din ya qare,abinda ya rage kawai ta bata dama taga nata qoqarin ba tare data nemeta kota gaya mata komai da takeyi ba. Kaman yadda zata bawa mamminan dama itama,zata tantance NASARAR WAYE akan gaba.
Bata amsawa birra ba ta wuce zuwa toilet kawai abinta. Wanka takeson tayi,don ta tabbatar da wannan qamshin da take jinsa a jikinta gaba daya ba lallai ya barta ta sake ba. Shuru birra tayi tana zaton zata amsa mata,saidai ganin har ta shige batace komai ba saita tattara kayan data watsar a nan kamar yadda ta saba ta killacesu a inda kowannensu ya dace,ta juya don bawa yalwa amsa.
Turus yalwa tayi,abun yana daure mata kai,maganan tana mata girma da yawa. Giwa ce a yau zata nema ganin akhnan amma ba bijirewa hakan?. Maganan ya mata girma da yawa,a gefe daya ita kanta tana wassafa yadda zata shaidawa mammina din ba tare da tayi laifi ba,saita juya kawai tana ficewa a sassan ba tare da tace da birra komai ba,tunda ta sani daga ita har birra din kowa aiki yake,umarni kuma yake bi na uwargijiyarsa.
Tayi kwance kawai cikin bathtub tana maimaita maganganunsa. Bata rayu rayuwa me tsaho da annee dinta ba,amma har yanxu tana iya tuna sunanta,har yanzu tana iya tuna yadda take kiranta,har yanzu kuma tana iya tuna yadda take zaunar da ita ta gyara mata gashinta......ta mata wanka,ta shiryata,sannan ta zaunar da ita saman cinyoyinta ta bata abinci a baki. Wani abu guda daya wanda bata sake samunsa ba duk da tarin gata da kulawar da ake nuna mata.
Ta rasa macen nan me suna UWA guda daya da zata jingina da cinyarta taji irin wannan dumin na UWA. Ta rasa macen nan guda daya da zata mata wanka ta shiryata irin yadda UWA kewa d'iyarta.
Har sanda take shiryawa cikin sassauqar doguwar riga me rubi biyu ta barci tunanin baibar cikin kwanyarta ba,komai da komai daya faru a ranar,ta sauke idanunta a hankali saman rigarsa dake gefan gadon nata.
Wani numfashi taji taja a hankali ta kuma saukeshi. Alama ce ta girmamawa,tabbas alama ce ta girmamawa,dabi'a ce da idan basarake ya maka ya gama girmamaka. Ya dauki suturarsa tufafinsa ya lulluba a gareka,koda normal yanayi ne ya kawo hakan bada kyautar rufar dake a jikinka zuwa ga wani alama ce ta girmamawa ta gaske. Ta tuna a duka rayuwarta sultan ne kadai yake mata kalar wannan girmamawar.
Neman rikicewa tunaninta yakeyi. Bata hangi sauqi ko sassauci a tare dashi a kanta ba,amma kuma irin wannan girmamawar daga ina ta samo asali?
"Baki sani bane.....ba wanda yakai malami iya riqe mace da tattalinta inde yasan abinda yakeyi,suna girmamawa matansu,akance da matar malami data basarake ba kowa ke iya aurensu ba idan suka sakesu,saboda riqon mahaukaci sai sarki". Ta tuna wani hira da taji shehnaz sunayi ita da aisa. A sannan ma qaramin tsaki taja,ta kuma tattare kayanta tabar musu gurin saboda gani take shirme ne kawai a hirarsun. Haka abun yake?,ko kuwa dai kawai yayi ne saboda wani dalili nasa na daban?.
Qarasa jan zip din rigarta tayi daidai sanda biftu ta shigo mata da abinci shirye saman wani tray me kyau da dukan hankali. Shimfida ta mata,ta zauna akai tana cewa da ita.
"Karki zuba komai.....bani fruit da madara kawai" Tace da ita a taqaice. Hada mata tayi kaman yadda ta buqata ta miqa mata,tana shirin miqewa ta fita ga dakatar da ita.
"Zauna na qarasa,zan shiga gurin momma". Maganan yadan bawa birra mamaki,amma batace komai ba ta zauna tana jiranta kamar yadda ta buqata.
Sanda suka fito ruwan ya janye sosai,sai sanyi da ruwan ya sakarwa garin. Akwai kebantacciyar hanyar da take iya tasu ce wadda ba lallai ruwa ya tabasu harsu isa inda zasuje din.
*MORSA SAFIYYA*
Cikin qwataccen parlor din dake dauke da wasu gajerun kujeru masu tsananin taushi. Wani irin pink color ne komai na parlor din,pink me taushin kala da haske. Saman kujerun suke zaune,ita da falaak da kuma hairaan. Aaroon da Aeeda na kwance saman mabanbantan kujeru da alama bacci ne ya kwashesu,don ga kayan wasansu nan barbaje a qasa. Anwar yana saman cinyar hairaan din.
Wani nutsatsen qamshi ne yake tashi cikin parlor din,qamshin daya hadu da sassanyan ni'imar garin ya bada wani qamshi me aji na hadadden turaren wuta daga kamfanin SHUWA INCENSE AND MORE(0704 229 3387).....wani sirrin qamshi guda daya da morsa safiyya din keji dashi. Qamshi ne da mammina ke matuqar adawa dashi,saboda yadda ta fahimci yana daya daga cikin sirrikan daya sanya sultane ke mararin kebancewa da morsa safiyya,kuma qamshin da har yau mamminan batasan sirrinsa ba.....batasan kuma daga inda ake samoshi ba.
A iya parlor da dakunan me martaba kadai zakaji wannan qamshin,sai kuma lokaci irin wannan idan tana kewar me martaba din takan saka a wannan parlor din Shima qwalli daya tak.
Kusan hirar tasu akan akhnan ne da shirye shiryensu da sukeyi wanda ba kama hannun yaro. Dawowar sultane ne kadai ya rage musu,sai gyaran jiki da lecture class dim da morsa safiyya keson akhnan din ta fara,daga bisani kuma hirar tasu ta sauya akala ta koma basu labarin safeenarta wadda ba wanda ya santa a cikinsu,don ko hairaan ba komai take iya tunawa ba.
Hira ce wadda zai wahala a farata a kuma gamata lafiya lau ba koke koke. Tana jinta cikin kadaici,tana jin kamar ita kadai take rayuwa a duniya,saboda ba khadeejanta ba kuma safeenarta. Wani lokaci takance.
"Baisan wacce hikima Allah ya boye ba wajen barina a duniya ni kadai naci gaba da rayuwa......lokuta da dama nakanji mutuwata ce kawai ta ragemin,ina son na kwanta na huta nima,ina shauqin na tafi na ruski safeena da khadeeja ta.
Kamar yau din da hotunan safeena din ke gabansu,wanda yawanci a Ethiopia aka daukesu,sai yanzu kuma wasu daga ciki da aka daukesu cikin agadez a sanda safeena din ke sharafin kyau da quruciya,kamanni na sosai suna bayyana tsakaninta da akhnan din.
Sallamar akhnan din ya sanyasu maida hankalinsu dukka a kanta. Morsa safiyya tasa tafin hannunta tana share hawayen da yake kwance. A dukka tunaninta safeena ta tafi bata tafi bane,a sanda ta rasu tabar akhnan.....saidai a yanzun tana ganin safeena ne kawai daga wani sashe daban na jikin akhnan din,bawai safeena take gani completely dukanta ba.
Zuciyarta ta mata sanyi sosai sanda ta binciki dabi'un akhnan din......tana cike da fata ko yaya a kanta ta samu wani abu daya da zai sake bata nutsuwa a kanta. Ta samu labarin sirri data aminta dashi......tana wata irin kyauta da sadakar da bata yarda asan ita bace....bata kuma amince sunanta ya fito ba.
Taji wani irin dadi daya sanyata sakin zallar hawaye,irin sadakar safeena,irin halayyarta. Ta yiwa mutane da dama da yawan gaske alkhairi,irin alkhairin da sai bayan ranta sannan aka yita sani,sannan aka yita fadinsa,sannan yayita bayyana.
A hankali ta dauke idanunta daga fuskokinsu ta maida saman hotunan dake zube a tsakiyarsu,tun bata qaraso ba kuma ta fahimci hotunan waye?.
Inda ace ba'a kanta ya faru ba zata qaryata. Kaso mutum bayan rasuwarsa ka kuma kasa mancewa da soyayyarsa. Soyayyar mahaifiyarta daban ce,daban takejin soyayyarta a zuciyarta. Koda me irin sunanta taji sai taji kamar an fusgi hankalinta a kanta. Soyayya takewa me irin sunan na daban,a yanzun da take hangen hotunanta masu girma da wankuwa sosai fiye da wanda take dashi ita sai takejin wani abu yana taso mata.
Sanda take zama a gurin shuru ya mamayi ko ina,sai takejin jikinta kamar wata baare a cikinsu.
"Gani momma" Ta fada a hankali ba tare da tasan meye ya sanya ta fadi hakan ba. Wani abune da bata taba yinsa ba tunda suke da morsa safiyya din,abun kuwa ya saukar da murmushi saman fuskarta,ta kalli su hairaan tace dasu.
"Ku bamu guri" Haka suka miqe kuwa,falaak ta dauki Aeera.....Aafreen ta dauki Aaroon,falaak ta saba anwar a kafadarta suka fice.
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 118*
Batasan ya akayi ba wani numfashi ya qwace mata,zuciyarta kuma taso tsaiwa a qirjinta sakamakon dago kansa da yayi suka kuma hada idanu cikin ba zata.
Da wani irin hanzari ta qwace idanunta tana jin zuciyarta tana lugude
"Me yasa?" Ta tuhumi idanunta da zuciyarta da suka tunzurata kallonsa har haka.
"Sheikh haisam ne fa?,ordinary malam?" Ta fadiwa kanta da kanta. Bata sake kowanne tunani ba taji me gabatarwa yana magana ta mic