Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 69

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 69

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 69: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 69. "Muna neman alfarma ga sheikh muhammad haisam yazo ya…

3,359 words

"Muna neman alfarma ga sheikh muhammad haisam yazo ya wakilci me martaba gurin miqa certificate na girmamawa ga zaqaquran dalibanmu". Idanu ta qanqance,zuciyarta tana matsewa a qirjinta. Wannan matsayin nata ne.....inda babu shi,banda ya wanzu a gurin itace zata wakilci sultane,sai taji wani bacin rai yana lasarta,ta sake daga idanunta tana dan satar binsa da kallo sanda yake takawa a qasaice zuwa saman steps din,duk da sunyi nufin matsowa da abun maganar gurin ya basu daga inda yake a zaune.

Yadda yadin cashmere din jikinsa ke daukan idanu wani abune na daban na musamman kuma da zai sake bayyana maka tsadarsa. Hakanan tsarin dinkin da akayi masa kawai abun burgewa ne.

"Yana da daukan hankali malamin nan......irinsu cikin malamai ne qalilanne......ga izza ga ilimi" Maganan ya sauka daga bayanta wadda taja hankalinta. A hankali ta soma maido da dubanta da nufin fahimtar wadanda ke maganar. Saidai kafin takai garesu ma idanunta sun nuna mata yadda dubban idanu suka raja'a a kansa kafin muryarsa me zurfin nan data sake kwarjini ta soma fita ta cikin mic din.

Kujera ta musamman suka aje masa still a gurin duk da ya taso din,sannan ya karbi mic din ya fara da sallama. Kai ka sani koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci gwani ne wajen magana cikin mutane.

Sallama yayi wadda ta bada wani irin sauti me daukan hankali,dukka suka amsa suna tattara hankalinsu a kanshi.

Cikin taqaitaccen lokaci ya gabatar da jawabi cikin harshen larabci,jawabin data fahimci kusan duk wanda kejin harshen larabci a gurin yana ratsashi. A nutse idanunsa da bakinsa ke juyawa,bakin dake fidda haruffan larabcin cikin wani irin zallar qwarewa da fahimtar harshen. Tana numfashi sosai taja fiddashi a hankali. Karon farko data tsaya ta saurari yaren larabci zalla irin haka da kyau,batasan me yasa ba batasan kuma dalili ba,sai taji yaren yana mata wani irin dadim da farko ta dauka ba yaren da yakai yaren abzinanci da French dadi......amma a yau sai takejin wani irin yanayi daban yana ratsata.

Yana kammalawa dukkanin gurin ya dauki kabbara me qarfin gaske,mc din ya qarasa ya karbi mic din cikin girmamawar dashi kansa baisan yana yinta ba,ya saka mic din a bakinsa ya fara magana cikin yaren Tuareg.

"Na jima banji tataccen larabci daya tsumani da harshe me kyau irin wannan ba......nasan dukkanin udaba'u masana yaren larabci a yanzun sheikh muhammad haisam ya tayar musu da shauqi,muna godiya sosai" Ya fada yana rusunawa.

Daya bayan daya ya fara kiran 'yammatan daliban da suka cancanci girmamawar yana miqa musu certificate din,karbar certificate din daya zama jidali ga dukkan 'yammatan. Ba wadda bata bar gurin da wani irin bugun zuciya ba saboda wani irin kwarjinin tsayawa a gabansa.

"Khadeeja rabi'ou sa'adou" Mc din ya kira sunan dalibar me suna khadeeja har sau biyu.

Ta tsakiyar daliban ta fara takowa da dan hanzarinta. Baqar buzuwa ce wadda bata cika hasken fata ba,saidai tana da kyanta daidai gwargwado. Kallo daya ne haisam din keyi bisa al'adarsa,baya kuma d'ara hakan,ya dauke idanunsa yana miqewa a nutse,miqewar data bawa kowa mamaki. Tsaiwa dalibar tayi a gabansa,saita sad da kanta qasa kwarjininsa yana cikata,daidai sanda yayi magana da abdii dake gefansa. Murmushi abdii din yayi,ya matsa ya yiwa MC din magana,sautin murmushin Mc din ya harba ta cikin mic din yana duban kowa d'ai d'ai.

Karbar nata certificate din haisam yayi,yadan duba kadan,sannan ya miqa mata,ta sanya hannu biyu ta rusuna cikin girmamawa tana karba.

"Muna miqa saqon godiya ga sheikh muhammad haisam....ya miqe don karrama khadeeja da kansa,saboda ita din taci sunan mahaifiyarsa ne......dalilin wannan sheikh muhammad ya bayar ga kyauta ga kowacce daliba har na CFA 390,000 yayin daya ninka wannan adadin ga daliba khadeeja" Wani irin abune a hankali taji yana saukar mata a gangar jikinta,wani abu da batasan meye ba. A nutse ta dora idanunta akan dalibar,wadda duka duka batafi sa'ar falaak dinta ba. Idanunta sukayi kyakkyawan gani,don kuwa lura tayi da idanunta suna kan haisam din dake saukowa daga step din a nutse don komawa muhallinsa. Murmushi takeyi sosai wani irin murmushi dake nuni da farincikin da zuciyata take ciki.

"Kyautar CFA 390,000 ga kowacce daliba?.....daliban da aqalla sun kusa sun tamanin?. A ina ya samu wadannan kudaden?,yasan ma abinda yake fadin yayi kyautar dashi kuwa?,yasan kuwa adadin kudaden daya ambata kuwa?" Ta tambayi kanta da kanta tana son maida idanunta kan fuskarsa,saidai zuciyarta tana gargad'arta game da hakan.

"Daliba guda daya an ninka mata adadin?" Ta sake tambayar kanta tana maida idanunta kan yarinyar da tuni ta koma ta zauna.

Murmushi takeyi sosai,dukkan alamu na matsanancin farinciki sun nuna akan fuskar yarinyar,lokaci lokaci tana daga idanu ta kalli sashen da haisam yake tsaye yana sallama da manyan mutanen daya samu a gurin.

Wani harbawa guda daya taji zuciyarta tayi,ta lumshe idanunta tana tambayar kanta DALILI?. Saboda kawai sunanta khadeeja?,me yasa yake iya ninka kyauta saboda suna daya?. Sauke numfashi tayi sanda birra ta rusuno tana gaya mata

"Zamu wuce ne ranki ya dade......yallabai yayi umarni" Idanunta ta daga a hankali ta kalli birra jin sunan data sauya masa,saita miqe a nutse abinda ya sanya hankula suka sake yowa kanta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Bata manta ba,batayi qasa kuma a gwiwa ba ta waiwaya a hankali tana sauke idanunta ga mutum biyu dake bayanta. Suka hada idanu sai suka sakar mata murmushi. Shugabar hukumar ilimin bai d'aya ce ta qasa,hajiya nihla Ousmane......da baquwar da batasan wacece ba. Kudi kyau gami da dukiya dukkaninsu nihla tana dasu,tana cikin mata matasa masu qananun shekaru da suka samu aiki me girma cikin gwamnati,saidai duk da haka nihla din bata taba aure ba.

Hada idanu sukayi,cikin girmamawa hajiya nihla wadda ta miqe tana miqawa akhnan hannu. Duk da cewa ta girmi akhnan nesa ba kusa ba.....akhnan din kamar qanwa take a gurinta,qanwar ma ta bayan baya,amma hausawa sukace sawun giwa ya take na raqumi,dole ta bawa akhnan din girma kamar nata shekarun sunfi nata.

Wani kallo ta sakewa nihla din na cikin idanu,'yan abun miskilanci sun motsa,a nutse cikin wannan fuskar da sarauta da izza ke kaiwa suna kawowa ta zare idanunta,ba tare data maidawa nihla hannunta su gaisa ba.......ta zare idanunta tana juyawa a nutse ta fara takawa su birra suna take mata baya.

A nutse sukaja da baya sanda take dab da riskarsa. Yana takawa hankali kwance yana amsa waya da hausarsa da bata gama fita gaba daya. Idanunta ta lumshe tana budesu,tana tuna komai daya faru a yanzu. Damuwarta alqawarin daya dauka na kudade masu nauyi da yace zai bayar ga daliban. Ta sani,baida abinda zai iya biyan wadannan kudaden daya ambata,zai karya siffarsa yayi musu qarya ya gudu?,ko kuma karba daga lalitar mahaifinta da sunan shine ya bayar?.

Haka kawai a jikinta taji bata gamsu da dukkanin wadannan amsoshin ba. A jikinta take jin indai wannan mutumin ne.....indai wannan malaminne ba daya daga ciki da zaiyi.

Ta saci kallonsa kadan sanda ya sake matsawa da kansa ya kuma bude mata qofar motar a karo na biyu. Ganin zai waiwayo ta dauke dubanta a kansa. Tana jin wani d'aci a ranta,wannan nutsuwar rashin fushin da take gani saman fuskarsa bata sonsu.

Ko data maida idanunta sai taga seat din gaba ya bude mata. Mamaki yadan kamata,a iya rayuwarta idan ba Niamey ta shiga ba bata taba zama gaban mota,kullum a baya take,driver yana janta. Ta sake daga idanunta cikin alamun rashin fahimta tana dubansa,tsareta yayi da kallo da wannan zafafan idanun nasa,sannan ya mata sign din ta shiga.

Wannan zuciyar.....wannan kwanyar data soma jin haushinsu sai suka bata qwarin gwiwar shiga din. Ta sauke numfashi me nauyi sanda ta daidaita cikin seat din. Wai me yake faruwa?,me yasa komai ya juye?,me yasa komai ya sauya daga asalin yadda yake?. Shi ya kamata ya zama cikakken d'an rakiya a idanun kowa.....amma ita ta buge da zama 'yar rakiyar.....shi ya kamata ya shiga qunci kunyata da takura amma ita dince ranta a bace bashi ba......me yasa haka?.

"Bismillah" Taji an ambata a hankali. Wani irin baqon yanayi ne a hankali ya mamayeta,qamshinsa yana sake kusantarta da wani irin yanayi dake jefa zuciyarta zuwa ga wani irin shauqi. Ta saba jin hakan a duk sanda qamshin zai bugeta,zuciyarta wasai.....qirjinta wasai,nutsuwa kuma zataji tana mamayarta.

Wannan zuciyar dake bugawa cikin qirjinta itace ta soma tambayarta SHI ZAI DRIVING?.....ina driver na?. Zuciyarta taci gaba da bugawa cikin qirjinta da tsoro,tana tsoro kada bai iya motar ba....kada yayi ganganci da rayuwarta,abinda ya sanyata bude idanunta da sauri,daidai sanda ya miqa hannunsa don kunna motar.

Da wani irin tsoro ta miqa hannunta da zummar dakatar dashi,tafin hannunta ya sauka a bayan hannunsa,dumin jikin junansu ya harba cikin kowacce magudanar jini ta jikinsu,yakai kuma saqo kwanyarsu. A tare kuma lokaci guda wuta ta daukewa dukkaninsu. Ya daga idanunsa a hankali ya aza saman nata adam apple dinsa yana motsawa da wani irin sauri. Kaifi da tasirin idanunsa suka ratsata,tunaninta da jinin jikinta suka koma daidai,ta samu nasarar janye hannunta da sauri daga saman nasa. Kauda kanta tayi tana son bugun zuciyarta ya daidaita sosai. Me yasa taketa yin shirme ne?,me yasa ta kasa mallakar kanta?,me yasa taketa abubuwan da bai kamata tayisu ba?. Idan ya rainata fa?,idan ya zaci wani abu a kanta fa?. Saita lumshe idanunta sanda taji ya tayar da motar,cikin wani irin coolness yayi reverse ya soma fita da ita daga gurin.

Sai daya daidaita motar saman kwalta sannan ya miqa hannu ya kunna A.c din motar saboda yadda yakejin kamar suna cudayyar numfashi da yawa shi da ita. Wani irin shuru ya ratsa motar,tuqi yake cikin nutsuwa mutuwar jiki da kuma kasala. idanunsa akan lafiyayyar kwaltar dake shimfide saman titin,koda batayi magana ba yasan tanason sanin inda zai kaisu ne,bai kuma shirya magana da ita ba.

Yanaso ta fahimci IKO da yake dashi a kanta......yanaso ta fahimci maganarsa dama tsarikansa sama suke da nata. Sai ya fara zare mata UMARNIN MAMMINA daga ranta gaba daya,sai ya fara fahimtar da ita tana da wata rayuwa......tana da wani umarni......tana da wani IKO sama da ikon mammina saman wuyanta. Sai ya fara tabbatarwa mammina akwai tazara yanzu tsakaninta da ita,sai ya fara koyar da mammina akwai wani QARFIN IKO daya fara mallaka daga cikin nata kason ikon.

Sanda ya rage gudun da yake ya gangara zuwa wani street din daban saita bude idanunta a hankali. Mamaki ya sake cikata ganin ba kowa tare dasu. Basu birra,ba sauran guard's dinta maza da suke kula da tsaronta a duk sanda zasu fita din.

Idanu tabi ginin dashi,tunda take a agadez ma batasan gurin ba,saidai koda ba'a gaya mata ba,ta fahimci kodai hotel ko kuma wani hamshaqin guests in dinne.

Amma kuma gaba daya ba symbol ba alamu na sunan gurin,saidai girma da tsaruwar ginin kawai ya sanya ta gaza gasgata gida ne.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1,000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 119*

Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa.

Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe

"Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar.

Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba.

"Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya.

"Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta.

Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu.

"Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata

"Na fadi maka nan din ba gidana bane".

"Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba.

Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske.

"Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa.

A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA.

"Sakanninki suna dab da cika...."

"Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna.

Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu.

"Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda.

"Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan.

"Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun.

Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta

"Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba.

Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai.

"Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan.

Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya.

Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau.

Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi.

A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan.

Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa..

A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje.

"Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki.

"Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?.

"Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane".

" You speak as if......"

Readers Also Read

More by Huguma