L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 70
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 70: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 70. "As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da…
3,346 words
"As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar.
"Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa.
"Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci.
"Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 120*
Ta daga idanunta sanda aka zuge makeken gate din tana duban layin. Dukka gidajene a tsare masu matuqar daukan hankali da bada sha'awa.
Wani qawataccen parking lot ya sanya motar,bai wani damu da daidaita tsaiwarta a gurin ba yadda ya dace,abinda zai nuna maka alamun ikon da yake dashi a gurin. Wani farin matashine sanye da baqaqen uniform ya qaraso,ya kuma rusuna ta bakin window din. Batasan me haisam din ya miqa masa ba,kamar yadda bataji me yace dashi ba tunda yayi magana dashi ne da wani yare da batasan wanne yare bane,amma.kamar tana jin wani sashe na yaren daga bakin morsa safiyya ko mammina jifa jifa. Maida glass din yayi ya rufe
"Alhamdulillah" Taji ya furta can qasa da muryarsa me nauyin nan.dogayen yatsunsa ya sanya ya kwashe wayoyinsa dake gurin,sannan ya zura qafarsa ya fita,sai a sannan ya lura da yayyafin daya fara sauka. Ya taka a hankali ya zagaya inda seat dinta,yasa hannu yana sake bude mata motar.
Manyan blue eyes dinnan nata da hasken garin da bame kaifi ba saboda yanayin hadari ta daga tana dubansa dasu. Still da ido ya sake mata maganar ta fito. Sauke qwayar idonta tayi,me yasa idanunta da zuciyarta dukka basa iya qureshi da wannan kallon nata dake nunawa mutum kuskure idan ya mata abu?,me yasa basa iya jurewa ne?. Wanne irin izza gareshi haka da zai dinga tafi da ita da umarni da idanu kawai?. Aurensa tayi ne don yayita bata umarni?,anya mammina bata sake cutarta ba?,anya bata jefata inda ba zata taba fita ba?. Bata hangi ta inda wannan kafaffen me shegen izza da girman kai zai sallameta ba. Bataga muhallin da maganganun mammina zasu samu gurin zama ba.
"Fito" Yayi magana a karo na farko yana dubanta. Umarnin nan na kai tsaye,magana da izzar nan ya fara cikata,ta tattara dukka jarumtarta guri daya.
"Bazan sauka ba,don nan din ba gidana bane" Tayi maganan tanason nuna jarumta,saidai tsakiyar hakan ya hangi tsoro qarara tattare da ita. Wani siririn murmushi ya subuce masa can qasan zuciyarsa ba tare da hakan ya bayyana akan fuskarsa ba. Dole saita nuna yanayin tata jajircewar,kuma alhalin idanunta suna qaryatata suna kuma bada ita wajen fallasa masa labarin zuciyarta.
Kyam ya tsaya da dukka wannan tsahon nasa daya biyu da murjajjen jikinsa ya nada structure me kyau. Wani kallo yake aje mata,irin kallon da zai sanya har cikin jininka kaji ana aunaka ne,ya zuqi iska ya fesar,ya daga kansa yana kallon sama dake zubda wani yayyafi siri siri,ya sauke kansa a hankali a kanta karo na biyu.
"Ki sauka" Ya kuma maimaitawa hankali kwance. Fusatattun idanunta ta daga tana dubansa,yadda yake magana hankali kwance kaman baisan yana tana ranta ko yana bata mata rai ba shine abinda yafi komai baqanta mata
"Na fadi maka nan din ba gidana bane".
"Na sani" Ya amsa mata a nutse yana duban yanayin fushinta da yadda izzarta take magana. Idanunta ta mayar gefe,tana jin hawaye suna son ciko mata amma ta hana hakan faruwa. Tanaji a ranta yanason nuna mata iko,yana son karyata da izzarsa,ita kuma karaya da faduwa wasu abubuwa ne da bata yarda dasu a rayuwarta ba.
Agogonsa ya daga ya kalla a tsanake,muhimmiyar magana zasuyi da omar da shine ya jagoranci zaman da aikin da kansa. Bai saba bata lokaci ba,bai saba saba magana ko canza lokaci ba,baya so kuma ayau ya fara,saboda aikine me girman gaske.
"Kina da zabi biyu......daqiqa goma kawai zan baki ki tunani....ko ki saiko da qafafunki ki shiga.....ko na maida motar na rufe ki zauna ciki,don bazaki koma gida ke daya ba". Mamaki ya sake kamata,sai kawai taji hawayen suna shirin gangaro mata,tayi saurin sadda kanta qasa.
A rayuwarta ba'a taba matsanta mata haka ba.....a rayuwarta bata taba ganin juyawa da bada umarni kai tsaye irin haka ba. Tana baqincikin yadda SHURUNSA kadai yake da ikon sarrafata.....tana takaicin yadda ya samu ikon sarrafata da sauqi haka ta cikin qwayar idanunsa kawai. Kamar yana gaya mata ne a sauqaqe IKO BAYA BUQATAR HAYANIYA.
"Sakanninki suna dab da cika...."
"Bazan shiga ba.....ni ban yarda ba" Ta fada still tana jin zuciyarta tana quna.
Abu na farko da yafi tsana MUSU TAURIN KAI abinda ya sanya Aanani qanwarsa tasha wahala sosai a hannunsa kenan har sai daya lanqwasata ta koma tsarin tarbiyyar qabilad oromo. Hannunsa guda daya ya dora saman roofing motar,ya sunkuyar da kansa sosai samanta kamar me shirin mata rumfa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wannan tsaiwar da yayi saman kanta.....wannan kusancin daya qara a tsakaninsu ya qarasa tsinke duk wata jijiya a jikinta dake bata qwarin gwiwa da damar yin musu.
"Dole ki shiga duk inda na kaiki gimbiya akhhnaan" Wani abu yaso sarqe numfashinta yadda ya furta sunan da hausar nan tasa da bata zama tattacciya ba,yadda taji iskar bakinsa dake gauraye da qamshin mint leaves ta fito a hankali tana sauka a fuskarta,sai komai ya qarasa jagule mata,lissafin ya fara harhadar mata guri guda.
"Second uku ya rage miki.....ko kikai kanki da qafanki....ko kum...." Bata tsaya ya qarasa fadi ba ta sauke qafarta ta farko a qasa ganin yaja baya yana nade hannun rigarsa. Sai ya dakata da abinda yakeyi a nutse,ya matsa gaban motar ya bude mata murfin sosai yadda zataji dadin fita gaba daya,yayin da idanunsa suka sauka kan zara zara yatsun hannunta data damqe wayarta da kyau a ciki,sai yaga kaman hannun nata rawa yake kadan.
"Matsoraciya" Ya fadi can qasan ransa yana sake gasgata kalar tsoron daya gani shimfide a idanunta dazun.
Gaba yayi ta soma binsa a baya a hankali,murmushi ya qwace masa kadan bayan wani tunani ya d'arsu a ransa,ya kuma furta
"Allah ya sawwaqe" Ya sani wataqila zuciyarta tana raya mata zai nema tarayya ne da ita.....shi ya saukar mata da wannan tsoron?. Ko daya baima shiryawa kalar wannan rayuwar ba,bada ita bama da kowacce mace,koda zai karba yana jira ne daga halittar data mutu a sonshi ne,ba wadda bai tunanin ba qaddarar halittar so a tsakaninsu ba.
Tun daga qofar farko data kasance kamar wani lobby ne tsararre idan an budeta mamaki ya cikata. Cikin gidan yafi wajen kyau,wani irin tsari ne me daukan hankali daya kusa kulle mata kai.
"Gidan su waye ya kawoni?" Abinda take fadiwa kanta kenan.
Gaba daya ta gama tsinkewa sanda sukabi wani dogo kuma siririn hallway,sai taga sun bace daga ainihin lobby din sun balla wani dan guri kamar reception sannan suka sake shiga wata qofa data kaisu wani irin parlor. Kai tsaye ba zatace parlor bane,kuma bai kamanda bedroom ba,hakanan bai kama da office ba,amma dukka zai iya daukan wadannan ma'anonin gaba daya.
Akwai wasu irin lafiyayyun sofas da zaka iya maidasu gado ko kujera da aka qawata gurin. Wasu iri marbles masu tsananin kashe idanu da daukan hankali,wasu irin curtains da suke fusgar idanu,dunqulallen table madaidaici sai qananun side tables da aka qawata tsakanin kujerun dasu. Wani irin freezer dispenser da qawatattun trays da cups da butucin shayi masu tsananin kyau.
Komai na gurin fari ne qal ba wani sirki ko kadan,banda daukan idanu ba abinda yakeyi. Gagara zama tayi,sosai take jin kanta a baqon guri,shi kansa gurin kwarjini da daukan hankali ne dashi.
A nutse kuma kansa tsaye taga yana ci gaba da takawa. Ya fara zare rigar alkyabbar saman kayan nasa a wani irin nutsuwa,abinda ya sake nuna fadin kafadunsa da kuma murjajjen jikinsa ta cikin doguwar rigar cashmere din ta sama da aka mata dinki me zubin kaftaan.
Jikin wani abun rataye kaya me qyalli dake tsaye da qafafunsa ya rataye rigar,sai ya taka gaba kadan yana cire agogonsa yana ajiyewa,ya jawo wani qaramin na'ura ba tare da saninta ba ya soma searching network din wayarta yayi connecting da na'urar,sannan yayi disabled na network dinta. Baya buqatar doguwar magana ta hanyar amsar wayarta da kasheta,amma kuma baya buqatar kowa ya kirata ya sameta ko ita ta sameshi. Yanason tsahon awannin da zasu zauna cikin gidan a rasa gane inda suke. Yanason hankalin mammina ya tashi koda na wunin yau ne kawai,yanason ta kasa nutsuwa,yanaso tayita cigiyarsu ba tare data isa tayi cigiyar tasu a fili ba......wannan din kadan tashi da hankalin Aareef yayi ne.....shine dan abinda zai iya rama masa dashi sanda tasa akayi attacking nasu,bawai kuma don yaji ciwo ba,don subul ya fita,motii ne kawai yadan buge kadan a qafar hagunsa..
A nutse ya maida na'urar yadda ba zata lura da ita ba,ya miqe ba tare daya kalleta ba dai,ya fara takawa yana nufar waje.
"Ki duba ko ina ki dauki abinda kike buqata.....idan baki samu bama ki danna madannin dake jikin switch na fitilan can,za'a zo a saurari buqatarki.
"Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?.
"Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane".
" You speak as if......"
"As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar.
"Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa.
"Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci.
"Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 121*