Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 71

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 71

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 71: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 71. "Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana…

3,319 words

"Bazan jima a gurin nan ba" Ta amsa masa kai tsaye tana jin tsoro yana shigarta. Tsoron yadda zai fita ya barta a gurin da yake mata wani irin kwarjini,ta yaya zai killaceta haka ita kadai?.

"Zaki zauna ki jira har zuwa sanda zan kammala tattaunawa da mutane".

" You speak as if......"

"As if you're under my responsibility?" Ya amsa mata da tataccen turancin nan da ko yaushe nasa yana fita da wani tone saboda zaman yaren oromo a bakinsa. Idanunsa sun mata nauyi,saboda ya datsi numfashinta ne ya fada kai tsaye yana kuma waiwayowa bayan ya tsaya daga bakin qofar.

"Yes.....because you're" Ya qarasa bata cikakkiyar amsa.

"Amma ni ba yarinya bace" Ta maida masa tana qoqarin tattara qarfin halinta. Murmushi yayi can qasan zuciyarsa,wannan qarfin halin nata da kafiyarta yana fusgarshi wani lokaci.

"Na sani.....yara basa cikin tsarin mammina.....shi yasa na gasgata ke ba qanqanuwar yarinya bace me girma gimbiya......amma dai....ni nake da zabin sanda zamu tafi.....rest well" Ya furta yana saluting nata sannan ya juya a nutse yana ficewa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 121*

"nan diwa kike fa.....meye zai dinga zauta tunaninki irin haka?" Tafisu ta fada cikin sassauta magana,muryarta acan qasa. Wannan lafazi na tafisu shine abinda ya zaburar da ita.....wannan magana ta tafisu shine abinda ya tilastata gayyato dukkanin nutsuwa ta azawa fuskarta.

Wani irin gumi takeji yana tsargawa daga tafin hannunsu dake manne da juna yana bin sassan jikinta,idanma taji da kyau,idanma ta lura da kyau kamar jikin nata shaking yake kadan kadan. Kusancin ya mata yawa......ga jarababben turaren nan dake sake daga mata hankali.

A nutse yake takawa da ita a gaban tawagar madame soufiane aghaichata guichene,minister al'adu ta qasar niger. Taku kadan ya rage tsakaninsu,sai ya sassauta tafiyar yana zame hannunsa daga cikin nata.

"Ki nutsu,akwai idanu da yawa a kanki.....ki qarasa ki fara marabtarsu" Ya fadi da wani sauti me taushi can qasa kamar wanda ke mata rada,abinda ya sanya tsigar jikinta zubawa gaba daya.

A hankali take nufar Madame aghaichata,fuskarta sake da dan murmushi kaman yadda fuskar Madame aghaichata take a sake sosai. Cikin zuciyarta tanajin wani abu yana sauka a hankali......ya girmamata kenan?.....ya karramata ya mutuntata,ya kuma bata damar data zama tatace. Damar fara tarbar baqin da suke na masarautarsu,ko kuma rashin iya boko ne?,tsoron magana da harshen France da bai iya bane?.

Farar matashiyar buzuwa data kasance fara sol,ba wani sofanin baqi sam a tare da ita. Kyakkyawar minister din data zama mace ta farko data fara zama minister cikin zuri'ar buzaye.

Yare daya qabila daya.....murmushi sukewa junansu ita da akhnan din. Akwai tarin sanayya sosai tsakaninsu,don kusan akwai abota me qarfi tsakanin kakanninsu,abotar data sanya iyayensu da wasu sashe cikin dangin biyu suke da kyakkyawar mu'amala. A hakam akhnan din bame sakewa bace.......bata da saurin sabo,uwa uba yawa izzarta ya sanya shehnaz da aisa ne kawai take mu'amala dasu a sake. Irinsu Madame aghaichata suna da yawa da saidai idan sun hadu a taro ko kawo ziyara irin wannan su gaisa cikin mutunci da kimanta juna.

"Amaryamu.....gimbiya akhnan......magana a kanki ya cika garin agadez gaba daya.....boyayyar gimbiyar nan da ba kowa ke samun iko da damar ganinta ba.....amma fa a yau na sake ganin dalilin da ya sanya akeyin shuru cikin jin nauyi da girma kafin a ambaci sunanki" Murmushi akhnan ta saki me taushi wanda sam bata shirya fitarsa ba. Ta sani Madame aghaichata nada barkwanci sosai,tun a wata seminar da suka hadu da ita a france ta lura da wannan.

"Na gode matashiyar minister dinmu" Tayi qoqarin maida mata barkwancinta.

Gaishe gaishe suka fara gudana a tsakaninsu ita da akhnan din,da hirarrakin da ba masu tsaho ko tsauri ba,yayin da haisam ke musabaha daya bayan daya da permanent secretary,jami'in protocol,diministerna tarihi da al'adu na minister,da secretary din yada labarai.

A hankali hankali da idanuwan akhnan suka sauka a kansa. Karon farko data fara ganin fitar murmushi saman fuskarsa.....karon farko da murmushi ya zame mata wani abun kallo a duniyarta.

"Haka murmushi yakewa kowa kyau?,ko a iya shi kadai ne?" Ta tambayi kanta da kanta.

Abu mafi girma da yafi bata mamaki yadda taga bakinsa yana juyawa a hankali. Kyawawan labban nan nasa suna motsawa da alama magana yakeyi.

"Da wanne yaren?,da wanne harshen?" Ta tambayi kanta da kanta. A dukka tawagar minister data kalla ta tabbatar ba wanda kejin wani yare na daban idan ka cire yaren Tuareg da france. ta sake juya idanunta a hankali.....wani abu take gani......tarin banbanci me yawan gaske tsakaninsa da dukka mazan dake kewaye dashi suna gaisawa. Koda daga nesa idan ka hangesu zaka iya fiddashi daban a cikin su. Wani irin kwarjininsa ne yake fasuwa yana bayyana kansa. Maganarsa motsinsa dama kallonsa gaba daya yana bayyana asalin banbancinsa da dukkan mazan dake gurin. Ta sake motsa idanunta kadan,dukkaninsu suna masa magana ne amma kowa zaka iya hangen tsantsar girmamawa daga gareshi zuwa ga haisam da har yanzu yake sakin murmushi yana kuma saurarensu da nutsuwar nan tasa.

Da sauri ta dauke idanunta a kansa sanda hannunsa ke cikin na protocol,ta saukesu a qasa tana jin bayanan madame aghaichata. Can qasan ranta take tuhumar zuciyarta.

"Me yasa?.....me yasa ta damu da sai ta kalleshi bayan bata taba kallonsa a sa'a ba?.....me yasa zuciyarta ke yawan zugata da tunzurata ta kalleshi,bayan duk sanda zata kalleshin sai ya kamata?....kada ka kije ki zuba ajinki.....karki je ki zubda kima da martabarki.....kada ki sa ya dauka saboda wani abu daban kike kallonsa?". Abinda zuciyarta keta nanata mata kenan,wanda ya bata dukkan qwarin gwiwar qin sake yarda ta kalleshi.

"Sheikh muhammad haisam" Ta kira full name dinsa tana dubansa fuskarta dauke da murmushin nan nata dake bayyana kalar kirkinta da sauqin kanta,kaman yadda idanunta tsaye a kansa,saita dakata kamar me zaben kalmomin da zatayi magana dashi. Da gaske taji kwarjininsa sosai,har ya sanya take laluben kalmar daya kamata ta fara magana dashi,wannan dakatawar tata kuma ya tsaida komai a qirjin akhnan. Sassanyan murmushi ya saki me nuna sanin kima da darajar kai.

"Madame aghaichata" Ya kirata a taqaice shima.

Tsoro take......tsoro take kadda ta zarce da masa magana da france......gurin cike yake da 'yan press,batasan ya zai amsa mata ba,batasan ya zai fahimta ba. Cikin qasa da second daya wai tsoro ya zarta a qirjinta sanda taji muryar Madame aghaichata tana magana cikin faransancin nan nata.

"Ina ganin akwai mutanen da ake gabatar dasu ta hanyar muqami......amma akwai wadanda kasancewarsu ce kadai take gabatar dasu" Tayi maganan da girmamawa sosai cikin muryarta.

Kai ya gyada a hankali cikin nutsuwa,ya fahimci ita dinma tana cikin jerin sahun mutanen da basa iya boye haqiqanin abinda ke ransu.

"Kwarjinka yafi jin labarinka yin magana" Ta sake fadi da dukka gaskiyarta.

Zuwa sannan tsoro ya hana akhnan sakat,ta daga kanta a hankali ta zubesu akan haisam. Haka kawai takejin kamar ta zama me masa tafinta,idanunsu suka hadu dana juna,yadan zuba mata idanu na wasu sakanni yana karantar tsoron dake cikin idanunta.

Mamaki kadan ya kamashi,idan ya fahimta daidai irin wannan ranar irin wannan lokacin take fata,sanda zata tabbatarwa da duniya bai iya faransancinsu ba,yanzu me ya canza mata wannan ra'ayin?,me yasa manufar ta sauya?. Amsa bai sani ba,don haka ya dauke kansa ya maida zuwa ga minister

"Son charisme resplendit,pas le mien,je me contente de baigner dans son aura(Kwarjinin nan nata ne,ba nawa ba.....kawai nima ana rabani ina amfana ne kawai)" Wani irin sake numfashi tayi kamar wadda numfashin ke shirin tsinke mata. Da wani irin yanayi.....da wani irin accent yaren ke fita daga bakinsa. Wani irin accent me matuqar jan hankali da nuna zallar qwarewa.

Murmushi madame aghaichata ta saki a nutse,yadda ya sarrafa faransancinsa a baki yana burgeta.

"Na fahimci dalilin da yasa ake saurarenka ba tare daka daga murya ba" Ta furta tana jinjina kai da gaske.

Qaramin murmushi da iyakarsa lebe kawai ya saki.

"Masarauta na maraba dake cikin farinciki wannan ziyara da girmamawa" Ya fada cikin nuna girmamawar.

Gaba daya Madame rose dake gefe,matar da aqalla zata kai shakarun haihuwa hamsin haisa din ya gama burgeta,ya kuma gama tafiya da ita,don haka sanda ta lura bai ganta ba saitayi masa sallama da gurbataccen yaren da harshen nasara dake kan harshenta. Sai a sannan ya lura da ita,cikin hikima da sanin darajar girma koda na kafiri ne ya sakar mata murmushi,yabi hannunta data miqo masa da nufin suyi musabaha da kallo,sau ya hade dukka tafukan hannayensa kawai yana gaidata,ganin alamun bazai bada hannun ba itama saita amsa da yanayin da ya gaidata din.

A biye take dasu kawai,yawun bakinta yana daukewa gaba daya. So take ta tuna dame dame ta fadi masa a gabansa da yaren France bisa tsammani da tunanin baya ji. Waye ya koya masa?.......ya akayi yakejin yaren da wani irin yanayi dako ita kanta bata iya sarrafa harshenta kamar haka?.

Haisam din da sauran directors na Madame aghaichata suna gaba,ita da Madame din da mata biyu da suke mata rakiya hadi da Madame rose suna biye dasu.

A nutse yake karantar mammina,wadda ke tsaye daga qofar qarshe da zata sadasu da cikin gidan. Dab da ita suka dakata,ya janye a hankali yana basu space suka gaidata,suka fara yin gaba kafin Madame aghaichata ta qaraso.

"Gaisuwa nake giwar me martaba.....nace wannan karon biftu aka miqawa ragamar aikin gaba daya kenan" Madame aghaichata ta fadi da wannan salon barkwancin nata. Wani murmushi ya subuce mata,ko banza tasan cewa matsayinta yana nan,ko banza kuma 'yan press dake tare da minister ta tabbatar zasu haskawa duniya da abokan adawa na boye da baka sansu ba,dana filin ma da suka bayyana cewa har zuwa yanzu ba abinda ya canza daga wannan matsayin nata.

"Kinsan kana girma kana dora 'yan baya akan turba me kyau,sabida yanayi na rayuwa"

"Gaskiya ne" Madame aghaichata ta amsa mata,suka sake gaisawa.

"Ku qarasa......haisam zai jagoranci komai shida matarsa,bayan kun kammala saimu zauna tattaunawar" Mammina ta fadi saboda tana buqatar kebewa koda na minti ashirin ne tayi tunani akan haisam din.

Komai akan idanunta ya faru,komai saman idanunta ya wakana. Riqon da yayi mata....maganar rada qasa qasa ba abinda yake sake shaidawa duniya da masu kallo aurensu akwai qauna da fahimtar juna. Ba haka takeso ba,ba haka taso ya faru ba,saboda samun tabbacin mutanen duniya a soyayyarsu ba abinda zai kawo sai tarnaqi ga nata plan din.

Kai tsaye suka wuce zuwa kebantaccen kuma makeken parlor din sultane na alfarma wanda ya saba ajiyar baqi irin haka.

Tsarin kayan ciye ciye ne kala kala aka gabatar musu,basu dade da ba suka wuce qaramin gurin tarihi dake cikin masarautar daura da babbar fadar sultane.

Baya yaja sanda aka shiga gurin,karon farko yake duban akhnan din.

"Ranki ya dade ke zaki wannan bayanin" Ya fadi kai tsaye yana janyewa baya. Murmushi dukka suka saki,musamman Madame aghaichata da komai yake burgeta dangane dasu. Haka kawai taji hadin yayi mata,tsarin kuma ya burgeta sosai,tana ta karantar wani abu me nutsuwa sosai a tattare da komai nasu.

Nauyi taji ya aza mata sosai,tadan lumshe idanunta tana fidda numfashi,sannan ta taka zuwa gaba a hankali.

Tana sane ta zabi tayi bayanin da yarenta harshen Tuaregh. Shuru ya ratsa gurin,haisam ya saki murmushi kadan. Koda batace komai ba,koda bata furta komai ba yasan dalilin da yasa tayi hakan,sai yayi kaman bayaji din,sai yayi kaman baya fahimta har zuwa sanda ta kammala bayanin.

Kai Madame aghaichata ta jinjina.

"Da gaske daga gidan sarautar agadez kika fito" Ta fadi da murmushi me laushi akan fuskarta tana duban akhnan da take kallonta kamar qanwarta ta jini. Itama qaramin murmushi ta saki,murmushin daya tilastawa haisam dauke kansa daga kanta a hankali,sannan ya jagoranci tawagar zuwa gidan museum din dake daura da gidan sultane din.

A qafa suke takawa,wata nutsatsiyar tafiya a hankali. Yana dage gefan akhnan din,suna kuma magana da Madame aghaichata,saidai ga mamakinta da hausar nan tasu da dukka bata nuna ba suke magana. Abinda ya sake daure mata kai,ta shiga shakka da kokwanto,france din yakeji?,ko kuma dai yayi yaren ne kan sa'a.

Jin qafafunta kawai takeyi kamar ba'a jikinta ba. Duk taku daya biyu sai kafadarta ta gogi tasa. Bata sani ba,shima yana ji?,nunawa ne baiyi ba ko kuma ita daya ce?.

Nan da nan security suka zagaye museum din,sannan aka buda musu hanya suna wucewa ciki.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 122*

A nan din akwai ma'aikaci dake qarin bayani akan komai daya shafi gidan tarihin da kayan dake ajiye a ciki. Har xuwa sanda suka kammala suka kuma yada zango suda manya managers na gidan ajiyar kayan tarihin don tattauna yadda za'a gyara gurin da kawo sauye sauye da ci gaba.

Relaxing yayi sosai cikin kujerar,kunnuwansa suna biye da dukka tattaunawar da akeyi da kuma musayar ra'ayin da suke a tsakaninsu,saidai idan ka dubeshi yadda yake zaune zaka dauka baya gurin,don idanunsa na saman wayarsa ne yana duba wani aiki da aka turo masa daga hukumar national intelligence security services.

Saqo yake tafawa,amma sai yadan dakata kadan sanda ta fara magana. Cikin izzar nan dake qara mata nutsuwa. Kusan itace ta qarshe data fara magana,bayan ta gama satar kallonsa tana jira taji ko zaice wani abu. Can qasan zuciyarta zuciyartata take raya mata qila ma baya gane me ake magana akai,qilan ma maganar dazun yaje ya haddace duk abinda zai fada ne,kuma komai yazo da arashi din.

"Kinyi magana me kyau me ma'ana.......ranka ya dade ba wani abu da zaka dora?" Madame aghaichata ta fadi da murmushi tana duban haisam.

A nutse ya ajiye wayarsa a gefensa,ya motsa idanunsa gefansa suka fada cikin na akhnan. Wani siririn muskilin murmushi ya saki. Ya sani idanuwa dukka suna kansu shida ita,koda bai kallesu ba yana ji a jikinsa,sai ya kashe mata ido daya a hankali yana zare dubansa a kanta ya maida kan Madame aghaichata.

" Elle est vraiment brillante,elle a fait un excellent travail,et j'ai quelques idées à(Tana da fikira,tayi qoqari sosai kuma,saidai akwai wasu qarin shawarwarin da zan bayar)" Tamkar daukewar ruwa dakin ya dauki shiru,sai sautin muryarsa dake zarcewa har ta saje da shurun dakin.

"A ina ya koyi faransanci ne?" Madame aghaichata ta tambayi kanta da kanta,saidai idanunta suna kansa tana gyadasu a hankali cikin gamsuwa da dukka kalamansa. Batasan mutum yana jin bugun zuciyarsa daga qirjinsa zuwa kunne ba sai a sannan,tun daga kashe kashe mata idon da yayi,zuwa kalamansa na yanzu da bata da tabbacin yabonta yayi ko akasin haka?,accent dinsa me wani irin kashe jiki da nuna zallar salon iya sarrafa harshe tayi qasa da idanunta bata kuma iya sake dagosu ba.

"Nasan zamu samu fa'ida sosai daga tsarinka,muna saurarenka ranka ya dade" Madame aghaichata ta fadi tana gyara zamanta cikin jin kwarjininsa yana sake mamayarta.

A nutse ya maida bayansa ya jingina da kujerar,yadda suka cika dakin da hayaniya da fadin ra'ayiyyika abun yadan bashi murmushi kadan. A tsarin aikinsu wannan yanayin ba abun karba bane.....sannan duk abinda suketa cecekuce a kansa me sauqi ne,don haka cikin qwarewa da iya sarrafa harshe ya fara magana da tattaccen harshen faransanci kamar dama can yarensa ne na gado.

"Ba gyara kawai muke buqata ba,muna buqatar labari.....kowanne abu anan ya kamata ya samu murya"

"Ta wacce hanya?" Madame aghaichata ta tambayeshi cike da son jin qarin bayani. Yadan motsa kadan,yana ji a ransa ba halittar da takai ta mace gaggawa.

"Ta hanyar qananun na'urorin sauraro,mutum zaizo ya saka a kunne,yaji tarihin abinda yake gani cikin harshen daya zaba" Batasan ta daga kai ta kalleshi ba saida suka hada idanu. Wani idea me girman gaske....wani tunani me kyau data tabbatar zai daga daraja da martabar gidan kayan tarihinsu,me yasa su basu taba irin wannan tunanin ba?.

"Merveilleux(wonderful)" Madame aghaichata ta fadi tana jinjina kanta. Ba ita kadai ba,kowa a gurin saida fuskarsa ta bayyana yadda idea din ta qayatar dashi.

"Kan tsarin gyara kuma.....banso a rufe gidan gaba daya ba,hakan zai dakatar da kudin shiga na wannan jahar,zanso muyi gyaran sashe sashe,don kada al'umma su rasa alaqa da tarihinsu zuwa wani lokaci sanadin gyaran"

"Gaskiya ne" Minister ta sake fadi cikin jinjina kaifin basirarsa. Tana jin inama zai karbi wani muqami cikin tafiyarsu?,inda zai amince da zataji dadi da hakan,ta tabbatar ba qananun ci gaba za'a haifar ba.

"Dan gane da ganuwa da manyan katangun tarihi da kukayi magana akai kuma......" Ya fadi yana aje numfashi a hankali. Mamaki ya sauka a zuciyar akhnan,wanne irin mutum ne shi?,dama yana sauraren komai?,amma yayi kaman baya gurin?,yayi kamar besan me ake fadi ba?.

"Guraren tarihi basa buqatar ado me yawa,abinda suke buqata shine tsaro,haske......da bayanai na asali" Ya sake tsayawa yana sauke numfashi,abinda yake sake gayawa minister tsantsar nutsuwar dake gareshi.

"Zamuyi amfani da matasa masu koyon tarihi daga yankinnan,su zama sune jagorori ba baqi ba".

"Yana hada ilimi da martaba" Zuciyar akhnan ta fadi a hankali tana jin gamsuwa da bayanan suna sauka saman zuciyarta.

"Baya magana har sai an nemi yayi....har sai an sanyashi cikin al'amarin" Madame minister ta furta qasan zuciyarta tana jin yadda gaba daya haisam ya hade bayanansu ya rushesu,yana basu bayanan da zasu dace da yanayin,ba tare daya qalubalanci bayani ko qoqarin kowa a cikinsu ba

"Tarihi baya buqatar yabo,yana so a barshi ne yayi magana da kansa"

"Wannan ba malami kawai bane......jagora ne" Madame aghaichata ta raya hakan a ranta. Kasa boye abinda yake ranta tayi,ta sake gyara zamanta kamar yadda takeyi tun dazu saboda yadda har yanzu takejin kwarjininsa.

"Amma.....muna neman wata alfarma guda daya mana idan ba damuwa" Ta sake fadi da harshen faransanci. Agogon hannunsa ya kalla sannan ya maida dubansa a kanta.

"A gurguje.....lokacin sallah yana dab da shiga" Maganan ya sakata murmushi,ya kuma sanya kowa mamaki. Karo na farko da wani ya taba magana da minister din kai tsaye irin haka,karon farko kuma da wani ya nuna muhimmancin lokacinsa sama dana minister.

"Me zai hana kayi aiki da hukumarmu?" Shuru ya ratsa na sakanni,yayin da akhnan ta tattara dukka hankalinta akan amsar da zai bayar. Zai amsa.....zai karba abinda zuciyarta keta fada Mata. Dama ce babba ga kowa miqa qoqon bara harda neman alfarma daga minister din,don haka shima bata zaton zai tankwabe dama irin wannan. Yawanci abinda kowa ke buri da mafarki kenan,don haka shima bazai tsallake ba. Saidai kuma ya bata mamaki Kamar yadda ya saba,ya hada yatsunsa cikin na juna ya fara magana da wannan salon nasa me nutsuwa.

"Ina godiya qwarai Madame minister,wannan gayyata alfarma ce babba,kuma tana nuna amincewa da yarda" Idanu minister ta zuba masa tana gyada kanta a hankali,tana fatan amincewarsa ta biyo bayan bayanansa.

"Amma ina da dabi'ar yin aiki ne idan na tabbatar zan iya bada gudunmawa me amfani,bawai suna kawai ba"

"Idan manufarku itace kiyaye tarihi da al'adu,zanyi farincikin baku duk gudunmawar data dace.....banqi karbar tayinki ba......saidai Inaso a bani lokaci na duba tsarin aikin,in duba inda zan iya shiga da iyakacin iyakokina...." Ya daga idanunsa a hankali,ba zato yana saukewa akhnan dake satar kallonsa qasa qasa.

Tayi matuqar qoqarin ganin ta janye idanunta daga kansa,saidai yayi mata wani daidabayi ta hanyar sarqafe kallonsu.

"Idan gimbiya ta amince,zanji dadin yin aiki tare da hukumarku". Yayi maganan idanunsa suna cikin na akhnan.

Dariya gurin ya dauka da surutai kadan kadan,yadda yayin ya burge kowa......yadda yayin ya isarwa da minister saqonsa kai tsaye. Baida sha'awar aikine dasu,amma bazai gaya mata kai tsaye ba saboda kare matsayinta da girmanta......kada kuma ya bari taji ya tozartar da matsayinta.

"Ranki ya dade muna neman alfarmar ki sake mana wannan fasihin al'ummarmu su qaru dashi" Madame aghaichata ta fadi tana dariya idonta akam akhnan.

Readers Also Read

More by Huguma