Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 72

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 72

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 72: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 72. Wani irin abu taji,da qyar ta fusgo murmushi saman…

3,367 words

Wani irin abu taji,da qyar ta fusgo murmushi saman fuskarta. Me yasa yake kasheta?,me yasa yake kasheta haka?,me yasa yake dasa mata abubuwa masu qarfi har haka?,me yasa yake kafa mata hujja a gaban mutane?. Wannan girmamawar.....wannan bada damar?.... Wai me yasa murya guda daya tal daga bakinsa take sawa kowa yayi shuru?,baya daga murya.....amma kowa yana saurarensa........

Karon farko da taga namijin da bai nemi burgewa ba amma kuma yake burge kowa. Bai nuna kansa ba.....amma so ake aji ra'ayinsa, Ta maimaita kalmarsa ta.

"Inaso in duba inda zan iya shiga,da iyakacin iyakoki na" Kalaman sun mata kama da kalaman mutumin da baya neman matsayi,.....matsayinne yake nemansa da kansa.....AMMA HAR ZUCIYARSA HAKANNE?. Tambayar data maqale mata cak tsakiyar zuciyarta......tunaninta ya fara dawowa daga nisan kiwon da yayi sanda ya miqe a nutse yana tunasar dasu lokacin sallah.

"Ina fatan zaka sake bamu lokaci bayan mun kammala sallar,ka tayamu rubuta jadawalin komai a sauqaqe,don bamu da tabbacin daga nan idan ka kubce mana zamu sake samun dama irin wannan" Murmushin da kumatunsa ne kawai suka motsa yayi ya jinjinawa Madame minister kai,sannan ya juya yana ficewa sauran mazan suna rufa masa baya.

Tayi zaune tana duban minister da baturiyar dake gulmar haisam bayan sun kammala sallar magariba,sallar magaribar da haisam din yayi limancinta,sautin karatunsa kuma ya ratsa kowacce kusurwa cikin masarautar da sauran sasannin unguwar.

"Ma sha Allah.....ma sha Allah" Kawai Madame minister ke fadi tana juya kai. A nutse kuma ta sauke idanunta akan akhnan.

"Idan naji labari daidai khadeeja.....kamar haisam.bai kasance zabinki ba da farko?" Ta qarashe maganar da tambaya. Idanu kawai akhnan ta lumshe ba tare data bawa minister amsa ba. Ta sani,ba lallai tayi magana ba dama,bata damu da wannan ba ta jinjina kai.

"Hakan ba laifi bane,ba kuma kuskure bane,saidai inda zai zama laifin dama kuskuren gaba daya idan kika kasa riqeshi da kyau......kinsan ina da labarinsa tun kafin na sako qafata masarautar nan?......hirarsa ta zagaye agadez da yadda ya maida masarautarku cikin tsari?.....naji hirarsa ba daya ba biyu ba....nayita addu'a na sameshi,don haka na buqaci sultane ya bamu wakili yayin ziyara,bisa zato da yaqini na kuma ya bamu sheikh muhammad haisam.....". Fararen blue eyes dinta ta daga tana duban minister.

"Yes.....ki ribaceshi khadeejah......na gano abubuwa masu yawa da alfanu tattare dashi......ba shakka LU'U LU'U ne wannan" Murmushin qarfin hali kawai ta sakewa minister din tana dubanta,hakan ya bawa Madame damar ci gaba da magana.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 123*

"Sheikh muhammad ba irin mutanen da ake gani bane yau da kullum.....naga kalar mutumin da qasashe ke neman irinsa,saboda ilimi da kwarjinin dake lullube dashi......irin wannan mutumin idan kina tare dashi zaki kasance me ninkin qarfi,ki kula da wannan ni'imar" .

Kai ta jinjina a hankali,me yasa suke iya ganin abinda har yanzu bata gama gani ba?.me yasa kowa ke ganin qarfin ikonsa?,me yasa kwarjininsa bai bar kowa ba?" Ta tambayi kanta.

Batasan ya akayi ba,batasan me yasa ta tsinci kanta da lafewa cikin kujeru ba,ta zubawa dogaye kuma zara zaran yatsunsa farare tas idanu sanda yake rubutu cikin wani yanayi me daukan hankali saman doguwar takardar tsare tsare kamar yadda minister ta nemi alfarma. Ya sake zama,ya kuma rubuta komai kaman yadda yayi alqawari.

"Ba mutumin banza ne yake iya cika alqawari ba" Madame minister ta fadi qasa qasa saitin kunnen akhnan. Madame rose ta gyara abun jin magana dake kunnenta,wanda yake iya fassara maka magana daga duk yaren da akayi magana zuwa yaren da kai kakeji,wanda akwaishi a kunnen kowa dake cikinsu. Kasa daurewa tayi,itama qasa qasa ta fara magana da minister.

"There was an unmistakable aura of authority around him.....he carried him self with quite dignity" Murmushi Madame minister tayi tana jinjina kai. Ko Madame rose da take me banbancin aqida.....banbamcin al'ada da banbancin yanki ta fahimci abubuwa masu yawan gaske a tattare dashi.

"Seriously madame......he had a commanding presence quite dignified and impossible to ignore" Sauran maganar Madame rose ya maqale sanda ya ajiye abun rubutun yana tura takardar gaban Madame minister.

"J'ai tenu ma promesse(na cika alqawari na)" Hannu tasa tana daukan takardar cikin jin dadi.

"Merci,vous avez tenu parole(tabbas ka cika alqawari,na gode)".

Cikin wani yanayi suke mata rakiya har zuwa bakin motocin da suka kawota a dazu,fuskarta cike da murmushi ta sake cewa cikin harshen faransanci

"Na dade banji dadin ziyara irin wannan ba saboda haduwa da mutane irinka abune sai mai sa'a....muna godiya da karramawa......sannan muna me miqa saqon goron gayyata a gareku,duk da cewa zamu turo wasiqa officially......zaku zama manyan baqinmu na wannan gurin......zaka zame mana me tsara komai.....kwanaki biyar zuwa bakwai kadai zakayi cikin sahara.....zaku zama baqin ma'aurata na musamman.....muna fatan hakan bazai takuraku ba?" Madame minister ta fadi tana murmushi da raba dubanta tsakanin fuskar haisam da akhnan. Haka kawai taji tanason ta qulla wannna kusancin,haka kawai taji ya kamata ko yaya wannan kyakkyawan hadin ta bashi gudunmawar qara danqo da wanzuwa.

"Na tabbatar dukkaninku ba zaku wofantar da gayyatata ba......ina fata zaku riqe kwanan watan da komai.....zan shaidawa sultane da kaina,za'a tsara komai yadda zai dace da tsarinku.....na gode qwarai" Ta fadi tana miqawa akhnan hannu.

Da wani irin faduwar gaba ta bawa minister hannu sukayi musabahan qarshe. Gabanta ke wani irin faduwa,me yasa madame zata mata haka?. Yaya take nufin komai zai kasance akan tsarin?.

"Sheikh muhammad....ina fata qasata zata koyi yadda kuke hada zamani da kuma girmamawa" Yadan murmusa kadan,da alama gwanar hira ce,yana ganin kimarta sosai saboda aure dake wuyanta,amma yayi magana yau harta zarce qa'idarsa da yadda ya saba.

"Muna maraba da duk wanda wanda ya girmama abinda muka gada" Kai ta jinjina sosai tana daga masa hannuwanta biyu alamun girmamawa,sannan ta shiga motar da aka bude mata.

"A bawa giwa haquri,akwai wadanda ke jirana yanzu haka,lokaci na gaba idan na shigo xamu xauna sosai da ita". Kai akhnan ta gyada a hankali,don da alama ita aka bawa saqon.

A hankali motocin minister da jama'arta keyin nisa da gurin,wannan nisan dake qara wani irin nauyi da kunya a qirjin akhnan. Batasan da wanne idanu zata waiwaya ta kalleshi ba,tunda batasan adadin meye da meye ta fadi da France ba a kansa,idan taje har zaginsa tayi batayi qarya ba,ashar ne kawai bata d'ura ba.

Iska yake zuqa a hankali shima da wani irin nutsuwa yana fesarwa. Wani qamshi na daban daya tsinkaya yau a tattare da ita yana busawa da wani irin yanayi zuwa ga qofofin hancinsa. Abu na farko daya fara jan hankalinsa ya kuma sanyashi baiwa mazan dake biye da ita umarnin dakatawa da binta gaba daya a wunin yau.

Yasan fitinar da qamshi yake dashi a gurin d'a namiji.....ya sani yana daga cikin girman abinda ke motsa sha'awar dan adam,tuna wannan kawai ya sanya sanda ya gansu biye da ita duk da su birra dake tsakani yaji kamar wani abu yana yankewa daga qirjinsa yana faduwa.

"Muje na maidaki ciki" Ya fada da wani irin dakewa. Har ranta taji maganan tasa da wani irin nauyi. Kamar zata bata?,ko.kamar batasan kan gidan ba?,kamar ma itace baquwa bashi ba?.

Saidai wani irin borin kunya takeji a zuciyarta,ba zata iya tsaiwa jayayya da musu dashi ba,fatanta ta isa sassanta ta samu ta zauna ta nutsu,ta kuma tariyo dukkan maganar da tayi a gabansa a wadancan kwanakin da wancan yaren.

Har jikinta ta dinga jin wani abu sanda ya sanyata a gaba yana biye da ita a baya,tamkar wanda aka bawa gadinta. Batasan me yasa yake son take mata baya har haka ba,ina tashi izzar?,ya sarayar?,ko kuma yana da wata manufa na qare ma bayanta kallo,kamar yadda yawan maza suke da wannan dabi'ar.

Iya tuna wannan kawai ya sanyata taji qafafunta sun sarqe saboda tuna yadda taji shehnaz na fadin daurin lafayar ya fidda shape na mazaunanta kadan. Ta tafi luuu zata fadi,cikin wani irin zafin nama taji ta fada a jikinsa. Daga idanunta tayi a tsorace idanunsu suka gauraya da juna. Da sauri ta dauke idanunta tana jin wani nauyinsa karon farko......karo na farko a rayuwarta da nauyin wani mutum data yiwa ba daidai ba ya mamayeta. Jikinta ta fara qoqarin zarewa daga jikinsa da hanzari,saidai da zafin nama ya furta.

"Attendez(wait)" Ya fadi,kalmar ta sauka saman zuciyarta tana qara gudun zuciyarta. Still dai da France zai mata magana?,sai taji kaman yana zaginta ne ko maida mata baqar magana.

A nutse ya saketa ta tsaya da qafafunta,saidai bata iya tsaida qafarta dayar sosai ba,sai kuma a sannan ta fahimci abinda ya sanya yace ta dakata din.

Dogon hill shoe dinta ne ya gurde,a nutse matsa gaba kadan. Ga mamakinta sai ta ganshi yana duqewa saman qafafunsa yana tsugunnawa a gabanta. Hannunsa ya miqe a hankali ya kamo lallausar farar qafarta,wadda gyaran jikin da ake mata ya sake qarawa fatar haske laushi da kuma sulbi.

Zara zaran yatsunta yabi da kallo,kafin yaji wani abu yaarrrr ya sauka zuwa dukka gabansa.

"Hasbiyallahu wa kafa" Ya fadi can qasan maqoshinsa,adams apple dinsa yana motsawa sama da qasa a hankali.

Takalmin ya kama ya cireshi dukka daga qafarta,yana kuma mamakin qarfin halin mata da suke iya sanya takalma irin wannan,kuma ace wai duka wadannan awannin suna qafarta?bata gaji ba?bata kuma tsoron faduwa kamar haka?.

Ajiye mata yayi a gabanta yana miqewa tsaye,saita soma tura qafar tata ciki mamaki yana sake kasheta,ta daidaitashi a qafarta,mamakin ya kasa barinta ko yi mata linzami,tilas ta daga kanta a hankali tana saukewa a kansa don tabbatar da cewa shi dinne?.

"Vous n'êtes pas blessée(bakiji ciwo ba?)" Yayi tambayar da seriousness dinnan nasa. Idanunta ta lumshe a hankali tana daga masa kai. Bata hangar komai cikin idanunsa sai kwatankwacin girman nan da YAYA yake dauka akan QANWARSA.

Sake goge mata hadda yakeyi gaba daya akan haddar daya goge mata dazun. Dukka wannan jarumtar tsaiwar da iya tsara komai ina ya samota?. Haka malaman suke?,ko kuma shi dinne haka?. A duk sanda yayi magana da France yana sake sanya fargabarta qaruwa,yana sake sanyata feeling guilty sosai a jikin jininta.

Kamar me tafiya akan qwai har suka isa mararrabar da zata sadata da sassanta. Bata waiwayo ta dubeshi ba,amma a cikin jikinta takejin ya tsaya ne kawai cak. Ya tsaya ne kawai ba tare daya qara taku ko daya ba,sai tafiyarta ta sake zama slow,a hankali har ta gifta ta wata doguwar bishiyar turare dake gurin.

Samun kanta tayi da tsaiwa jikin bishiyar,ta yadda ba yadda za'ayi ya ganta,saidai ita tana iya hangensa. Ya saki hannuwansa dake goye a qirjinsa a nutse ya juya.

Saidai baiyi taku ko daya ba wata murya ta wanzu a gurin,tare da kukan yaro qarami

"Inda kinsan darajar abun nan da baki yar dashi ba.....ni bazan iya tsaiwa tayaki nema ba,idan kin ganshi kya taho" Idanunsa da suka dan rusuna saboda gajiya ya daga zuwa sashen.

Daya daga cikin hadiman gidanne,shi da matarsa itama dake aiki cikin gidan,tana dauke da yaronsu daya hannun kuma torch light ce,duk a gigice take,da alama wani abu me girma suke nema.

"Akaramakallah....dakata mana" Haisam ya furta a nutse. Da sauri ya tsaya ya waiwayo,sai gashi kuwa sa sassarfa ganin wanda ke kiran.

Zubewa yayi niyyar yi,amma haisam din ya riqe kafadarsa yana fadin

"Tashi abinka" Sannan suka fara takawa zuwa inda matar keta dube dube,wanda yake daura da inda akhnan ke tsaye tana kallon komai.

"Jeka karbi yaron hannunta da fitilar hannun nata" Kwarjininsa ya isa ya hanaka tambaya akan duk hukuncin daka yanke,jikinsa na rawa saboda yadda ya hada kafada dashi,harda aza hannunsa saman kafadar tasa ya isa inda take.

Sororo tayi da mamaki tana kallon mijin sanda yake karbar yaron da fitilar. Abune da bata zata ba,sai kuma hankalinta ya kawo kan haisam a sannan,ta durqusa da nufin gaidashi,sai ya daga mata hannu yana mata nuni data koma cikin gida.

Hannu yasa ya karbi yaron daga gurinsa,idanu sosai yaron ya zuba masa,sai haisam din ya sake masa murmushi. Tamkar yaron yasan hannun kyakkyawan ruhi me taushi da tausayi da yazo,sai kukan nasa ya ragu a hankali,ya sauke kansa yana kwantarwa a qirjin haisam din,sai haisam din ya sake gyara riqonsa sosai yana rungumeshi cikin qirjin nasa,yaron ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi luf a qirjinsa.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 124*

"Dan bayi?" Ta tambaya can qasan ranta cikin mamaki. A nutse ya dubi mutumin

"Lawan ko?" Cike da mamakin yadda akayi ya iya shaidashi ya kuma fadi sunansa haka kai tsaye ya gyada masa kai.

"Kasan wacce wasiyya ce annbi muhammad S A W yayi ta qarshe?.....mece maganarsa ta qarshe?" Kai lawan ya girgiza da sauri yana saukar da kansa qasa.

"Rifaqan bil qawarirr.....istausu binnisa'i khaira........yace kuyi a hankali,ku kuma lallaba wadannan kayan qarau din wato mata.....sannan yace kuyi wasiyya da alkhairi wa mata........annabi muhammad bai tsaya a nan ba sai daya qara da fadin. Ba me karrama mata sai karimi,babu me wulaqantasu sai wulaqantacce.....mafi alkhairi a cikinku shine mafi alkhairi ga iyalinsa....manzon S A W yace nine nafi zama mafi alkhairi ga iyalaina. Allah yanason mutum me tausayi me rahama koda akan dabba bare dan adam....me yasa ba zaka zama me rahama da tausayi ga matarka ba?,uwar 'ya'yanka?,me kwantar da hankalinka?,meye a cikin tsugunnawa kawai ka tayata neman abinta daya fadi......kasan taimama?" Kai lawan ya gyada yana share gumi.

"Kasan asalin halascin taimama a musulunci?" Kai ya sake girgizawa. Sai ya saki tattausan murmushin da hatta akhnan dake tsaye tana iya hangen haskenshi.

"Sanadin ummuna nana aisha R.A. qarqashin tawagar yaqi bisa jagorancin mafi alkhairin halitta manzo S A W,abun adonta ya fadi,take manzan Allah S A W ya shelanta,yasa aka tsaida wannan tawaga gaba daya ana neman abun adonta ita kadai......an tsaida dubban maza saboda ita,akayita nemansa har lokacin sallah,gashi ba ruwa a inda suke,mahaifinta sayyadina abubakar RA yazo yana zungurinta gami da tuhumarta akan ta tsaida annabin Allah da sahabbansa saboda ita kadai?. A nan ne Allah ya halasta taimama idan an tsinci kai a inda ba ruwa......kuma kasan me?" Haisam ya fadi very friendly murmushi na sake kubce masa.

"Ana motsa raquminta yana miqewa sai gashi,ashe shi ya danneshi.......kaga anan sanadin mace sauqi ya zowa al'umma har ranar da za'a tashi duniya......sarki me girma da darajara da tafi ta kowanne dan adam ya dakatar da tawagar yaqi guda saboda matarsa......kai waye da ba zaka dakata saboda matarka ba?".

Idanunta ta lumshe a mugun slow,tana jin wani abu me sanyi yana sauka a zuciyarta. Rana ta farko data fara jin wani abu me tsaho da fadi daya danganci annabi muhamma irin haka,tausasawarsa da nuna kulawarsa.....

"Shine dalilin da yasa nake samun wannan kariyar dake gareshi?,koyi yake kenan?" Ta tambayi kanta da kanta tana jin wani abu yana ratsa zuciyarta. Wani irin kwadayi taji yana taso mata nason karanta tarihin manzan Allah S A W gaba daya.....da kuma rayuwarsa a cikin gidansa.

"Nayi kuskure tabbas,kuma daga rana irin ta yau in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba". Kai haisam ya gyada cike da gamsuwa da jin dadi.

" Muje ka duba mata......idan mace t qwallafa rai akan abunta bai kamata a karya mata zuciya ta hanyar hanata samunsa ba" Yayi magana yana soma takawa lawan yana gefansa yana sake haska masa duk da cewa akwai haske.

Cak ya tsaya sanda ya hango qyallin dan kunnen,saidai koda ya sanya qafa da niyyar motsashi yaga ko shine sai idanunsa suka sauka kan dogayen yatsunta,tsaiwa yayi na sakanni,sai qaramin murmushi ya subuce wanda ba lallai ka iya gani ba.

"Me takeyi a nan?" Tambayar daya yiwa kansa kenan,sai ya umarci lawan ya sauke fitilar qasa,da hannu ya masa nuni ya ciro dan kunnen,don bayajin ya dace ya taba abun da yake rayuwa jikin matar wani. Cire yaron daya fara bacci yayi daga kafadarsa yana miqa masa shi.

"Allahumma bareek" Ya fada yana jin yaron yana burgeshi. Dan lukuti dashi,baccinsa kuma yake hankalinsa kwance ba tare da yasan a kafadar wa yake ba.

Godiya ya dinga masa sosai,ya sanya yaron a kafadarsa jiki a sanyayr ya juya yana wucewa.

Hannayensa dukka ya zube a aljihun rigarsa,shuru ya ratsa gurin,yayin da akhnan ke lullube cikin shuke shuken zuciyarta na bugawa fat fat a qirjinta.

"Na tafi?,ko zaki fito na qarasa dake?"

"Ya Allah.....me yasa bata sa'a akan komai?" Ta fadi cikin zuciyarta. Bata taba kawawa zai ganta ba,tunda kuma ya riga daya ganta me ya rage?,sai kawai ta fito,ta dauke kanta tana basarwa.

Ba wanda yace da dan uwansa komai,har suka qaraso mararrabar sashen,sai kawai ya zabi shiga sashen nasa ta baya duk da ba a nan ya shirya kwana ba,don aiki yakeso yayi me yawa a daren nan,ya taka bai waiwayeta ba yana wucewa ta tasa qofar.

*T A M I M*

Dukka akan idanunsa suka wuce shi da ita. Ya koma baya ya zauna yana sakin wani irin murmushi. Murmushi ne najin dadi,murmushi ne dake nuna NESA TA MATSO KUSA. Idan yace ga adadin farincikin da yakeji yayi qarya,sam bai dauka ba baiyi kuma zaton komai zaizo da sauqi har haka ba. Bai taba daukan Festival de l’Aïr zai masa rana ba irin yau......bai taba zaton zai samu wani alfanu me tarin yawa ta dalilinsa ba.

Miqewa yayi tsam,yana daukan wata rigar fatar damisa ya sanya a jikinsa,ya jawo manyan takalmansa da suka zama abokan rayuwarsa,don duk wanda ya sanshi dasu ya sanshi,ya soma takawa yana ficewa daga kebantaccen dakinsa dake cikin masarautar.

★★★

*_W A S H E G A R I_*

Komai ta kammala na kwanciya bacci tana jin gajiya tana bin qasusuwanta,bugu da qari wani abu na daban takeji yana mata yawo a dukka jikinta. Wani kalan magani daban yau yaa hairaan ta bata,bayan wunin gyaran jiki da aka wuni anayi mata,don za'ayi hutu na kwanaki uku ne kafin a sake dorawa. A gobe kuma suke sanya ran dawowar sultane,har cikin zuciyarta takejin wani irin farinciki yana saukar mata. Idan face tayi kewarsa daya ma kenan. Wani irin mugun zaquwa takeji taga sultane dinta,da wannan sakakkiyar fuskar,da tarin soyayyarnan da yake nuna mata da kulawa wadda tayi tsananin kewarta.

Ta maida idanunta a hankali ta lumshe sanda ta narke cikin lallausan duvet dinta tana sauke numfashi a hankali. Saidai kuma sake zuqar numfashin da zatayi sai ta sheqi daddadan qamshin nan har tsakiyar kanta.

"Ya salam" Ta furta a hankali,gabanta yana faduwa tana bude idanunta,tsoro yana kamata,kada fa ace bayan tunanin komai daya faru daya fara kawo mata ziyara cikin madaidaicin duhun dakin still kuma qamshinsa ya fara biyota?.

Saidai ko data bude idanun nata saita Fahimci meya kawo hakan. Lallausan rigar cashmere dinsa dake ninke saman kanta. Ta zuba mata idanu sosai kwanyarta na dawo mata da yanayin dukka shigarsa a wancan ranar. Ta sake lumshe idanunta tana budesu a kan rigar,zuciyarta na hasko mata kyawawan labbansa dake motsawa a hankali,sanda yake karanta addu'ar saukar ruwan sama.....sanda yake karanta addu'ar tsawa. Batasan ya akayi ba wani siririn murmurshi ya subuce mata saman labbanta,ta miqa dogayen yatsunta a hankali ta dora saman rigar.

Kawai tana tuna ba zatar da yayi mata ne,yadda taji a sanda taji yana yara yaren France. Tsahon rayuwarta bata dauka ba sam cewa zataji nauyi ko kunya saboda shi ba,bata taba zaton akwai sanda zata zauna tana lissafin me dame ta cewa wani dan adam ba. Ta yamutsa yadin cashmere din cikin tafin hannunta. Koda ba'a gaya mata ba ta sani me daraja ne da tsananin tsada

"Baimin kama da ordinary malam ba" Ta tsinkayi muryar shehnaz

"Shemagh dinsa kamar a kansa aka halicceshi.......jinin annabi yusuf,tana tuna kayan data aike masa dashi.......bai saka ba,ya zabi kalar shigarsa....baiqi zuwa gurin ba,saboda sultane ya sanar dashi......ya girmamata da dukkan girmamawa.......ya kuma bata kariya irin wadda take so.

ZAKI takeso......amma wani lokaci DAMISA ma take gani tattare dashi......nutsuwarsa da da kwarjininsa batasan me yasa suke tilastawa kowa girmamashi ba.....batasan yadda ya akeyi yake iya sarrafa kowa da shirunsa ba........batasan ta yadda yake iya bada umarni da idanu kawai ba tare daya daga hannu ba.

Dukkan wani yanayi nasa yana gaya mata BANASON RAINI......yana da alamun dabi'ar girmamawa. Kaman anyi mix cikin halayensa ne......taushi da tsauri,batasan wanne ne yafi yawa ba a ciki.

Batasan ta jawo rigar cikin jikinta ba......batasan ta qanqameta ba sosai sai da taji birra na magana.

"Na kammala ranki ya dade,shikenan zan iya tafiya?" Ta tambaya tana rusunawa. Rai ta hade sosai tana shan mur,ta manta tana gurin,batasan kuma yaushe ta dauka a tsaye tana mata magana ba.

Readers Also Read

More by Huguma