Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 73

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 73

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 73: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 73. "Ki ajiyemin madara me dumi da cup da ruwa saiki wuce.…

3,375 words

"Ki ajiyemin madara me dumi da cup da ruwa saiki wuce. Ta fada tana maida kanta saman pillow gami da sakin rigar kadan.

Samun kanta birra tayi da sakin dariya gami da sanya bakinta tana rufe bakin nata gudun kada ta jita.

Shi yasa ta hana taba gurin?....ko shi yasa ta hana a dauke rigar?,ta hana koda hannunta yaje kusa da ita?. Ita din da bata bari abar mata komai saman gado idan ka dauke pillows din da ta saba bacci a cikinsu,ta saka wasu daga bayanta ta rungume wasu?.

"Turqashi" Birra ta fadi murmushi still yana subuce mata. Abun yana da girma.....abun zai zama wani na daban na musamman idan har ya kasance abinda zuciyarta ke mata hasashe ya tabbata.....amma anya kuwa?,anya?,badai akhnan din ba.

Tana jin sanda birra ta dawo ta ajiye komai,sannan cikin takatsantsan ta kashe mata dukka fitilun kamar yadda ta saba tamkar wata qaramar yarinya,ta rufe dakin bayan ta fice.

Idanunta ta bude a hankali,sannan ta juya zuwa hannun hagunta,tana jin yadda bacci yayi wani irin nisa da idanunta. Ta lumshe idanunta cikin duhun ta sake budesu tana sauke ajiyar zuciya.

Batasan me yasa komai nasa yake dawo mata a kai ba,tafiyarshi maganarshi yanayin magananshi da tafi mata wani irin idan yana magana da harshen France.......sai kuma uwa uba qamshinsa da tafi jinsa fiye da ko yaushe saboda rigarsa dake cukuikuye cikin duvet dinta.

"Turaren kawai yake burgeni.....inason turaren nan,dole na mallakeshi" Ta fadawa kanta da kanta tana cusa kanta tsakanin rigar,saidai kuma hoton fuskarsa ne ya gilma mata. Wannan tattausan murmushin da lokaci na farko kenan data fara ganinsa saman fuskarsa. Murmushin daya soma jefa mata tunanin DAMA YANA MURMUSHI?.....da gaske kyau yana qarawa mutum kyau?.

Wani irin emptiness takeji cikin zuciyarta da gangar jikinta. Ji take kaman ita daya take rayuwa cikin dakin,bugu da qari idanuwanta sam babu bacci,saita ture duvet din,ta miqe a hankali ta zura qafafunta qasa ta sanya bedroom slippers dinta tana gyara maballin silk sleep wear din dake jikinta daya zame.

*H A I S A M*

Private bedroom balcony din na daya daga cikin guraren da yakan zabi zama idan zaiyi aikin sirri daya shafeshi ko ya shafi gidan,saboda yana da tabbacin area din was secured hundred percent.

A yanzu yana tsaye ne,sanye da da lausasan cotton wool sleep wear da dukkansu suka kasance kalar sararin samaniya. Wando ne dogo har qasa,sai rigar data kasance long sleeve ce.

Takalmin qafarsa me tsananin taushi shima blue color ne,sai mug na zazzafan coffee dake riqe a hannunsa yana sipping a hankali. Baya buqatar yau yayi bacci da wuri,aiki ne me matuqar muhimmanci da yake sanya rai zai zama wani mataki na qarshe da zai warwarewa NIGER da ETHIOPIA wacece mammina?.

Yana tsaye qyam.....the giant sheikh dinnan,hannunsa daya soke cikin aljihun wandon kayan baccin nasa,hannun damansa kuma riqe da mug din. Idanunsa a zube fes saman system din dake ajiye saman daya daga cikin kujerun dake zaman banza a gurin,yana kallon progress din da aka fara samu akan request din daya tura game da takardun.

Cikakken information ya fara nema kan waye ya yiwa mammina su?,cikakken details na ma'aikatar da aka yisu,wanda yayi dama dukkan wanda ya jagorancin aikin. Ya gama tsara yadda zai bullowa kowa da komai,tabbas a wannan karon akwai buqatar ya shigo da yaudara barazana da wasan kwaikwayo a ciki. Yanaso ya kaucewa zuwa festival din,saidai sultane dama madam minister sun gama masa dabaibayi.

"Kwana uku ne kawai haisam,ka daure ka fidda masarautar agadez kunya a matsayinta na me masaukin baqi" Sultane yace dashi yanayin muryarsa kamar yana roqonsa. Yanayin ya masa nauyi da yawa,don haka dole ya amsawa sultane din,saidai yanaso kafin gobe sultane ya dawo.....kafin gobe da zasu wuce festival din ya kammala da kaso mafi girma na wannan gagarumin aikin na qarshe.

Dukka hannuwanta biyu ta sanya ta daure gashinta a baya,kafin tayi pulling qofar ta turata tana budeta a hankali.

Iskar damina me kyau ta taso da hanzarinta tana shigewa hancinta gami da sanyaya fuskarta,abinda ya sanyata lumshe idanunta a hankali tanajan iskar sosai tana kuma jin wani numfashi sassauqa yana kubce mata.

Ta saman screen din system dinsa yaga alamun motsi ta nahiyar cameras daya saka a gurin,bai motsa ba,bai kuma nuna alamun yaga dan adam ba,yaja arrow zuwa kan sashen camera din dake harbawa ya bude hoton gurin tarwai,wanda ya bude masa da cikakken hotonta live daya cika screen din system din gaba daya.

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 125*

Lumshe idanunta tayi,sannan ta bude hancinta sosai ta shaqi sassanya kuma tatacciyar iskar da Allah ya yiwa halittunsa baiwa da ita.... Ba don kowa ya biya ba ko kuma yana biya,sai don zallar rahama da kuma ni'imarsa ga bayinsa.

Fesar da iskar tayi a hankali,ta taka sosai zuwa tsakiyar balcony din tana jawo wata qaramar cushion chair,a nutse ta zauna,sannan ta ware idanunta a hankali tana saukesu akan balcony din dake fuskantarta. Balcony din sheikh muhammad haisam.

Kamar haka yaga budewar idanunta ta cikin allon system din,wadannan blue eyes din,idanun dake da wani launi da suka sanya ya dade yana girmama zatin Allah. Tun yana shekarar farko a university yayi binciken dalilin samuwar hakan. Da farko ya dauka cuta ne ko lalura,saidai shi tun da can baya zama da abinda baisan meye ba.....bai iya zama cikin duhu ba kuma baya bari kansa yayi murfi,daga baya ya fahimci low melanin ne da kuma gado na halitta.

Tamkar tasan yana kallonta kamar tana a gabansa,tamkar tasan idanunsa yana kanta ta juya idanun nata a hankali tana dora hannunsa saman sassalkar sumarta.

Idanunsa ya lumshe sannan ya budesu duka lokaci guda yana jin zuciyarsa tana bugawa a hankali.

"Subhana khalequ kulli shay'in" Ya furta can qasan zuciyarsa. A qasar da yawancin idanun mutanenta brown ko black......ga wani ido daban daya banbanta dana kowa.....ba kalan blue sosai kaman fenti ba,wani irin quite sky blue.

Tana sauke hannun nata gashin ya biyota ya warware gaba daya yana lullube kafadunta zuwa gadon bayanta. Qaramin tsaki taja,wannan santsin nasa yana daya daga cikin abinda ya sanya sau da dama sai birra ta taimaka mata wajen daureshi,har yanzu bata iya daureshi yadda ya kamata ba.

Hannu ta sake sakawa tana gwada tattareshi din kamar dazun,wannan yanayin ya bawa qirjinta da ko brazier bata saka ba daman gantsarowa gaba.

Sauran kadan......saura qiris mug din hannunsa ya subuce ya fadi a qasa,saidai cikin zafin naman nan nasa ya saka daya hannun nasa ya tallafoshi. Wani irin abu me kaifin gaske yaji yana tsarga masa,sai ya koma da baya ya zauna saman qanqanuwar kujerar dake gefansa yana ajjiye mug din hannun nasa. A hankali ya maida idanunsa saman screen din,haka kawai,duk da yadda zuciyarsa ke gargadarsa ya kauda idanunsa akai smma sai ya samu kansa da miqa hannu ya jawo system din sosai gabansa. Ya sani ba zata iya ganinsa ba idan bashi yaso hakan ba,saboda yana bayan wata qatuwar flower guda daya da aka ajjiye a gurin don bada iskar oxygen me kyau.

Tafukan hannunsa ya hade guri daya yana matsesu sosai gami da fidda siririyar iska daga bakinsa. Ta kasa daure gashin,ta sake sakinsa tana yamutse fuska gami da jan siririn tsaki. Sakewarta a gurin ya tabbatar masa tana jin amincin ita kadai ce a gurin.

Hannayensa ya sake rabawa daga cikin na juna a hankali,wani abu yakejin yana fusgarsa,so yake yayi closing side na camera din inda take zaune,saidai kuma zuciyarsa na ingizashi sosai.

"Halal dinka ce.....idan ka kalla baka sabawa Allah ba......sau daya kawai.....sau daya a dukka rayuwarka muhammad" Zuciyarsa ke fadi masa cikin taushi. Miqa hannunsa yayi da wani irin zafi zuwa kan system din,sai a sannan ya lura,sai a sannan ya gani. Rawa hannunsa yakeyi sosai,kamar wanda sanyi ya kama. Meye dalili?,me yasa dukka bai sani ba,abu daya kawai ya sani,abu daya yake iya ji cikin jikinsa,abu daya yake iya fahimta,yanaso yayi zooming video din sosai,yana so ya matso da video din dab dashi......yanason karon farko lokaci na farko a rayuwarsa ya qarewa wata mace kallo. Ya kalli abubuwa da dama,ya kalli abubuwa da yawa da yakejin matasa na fadi akan halittar diya mace.

Ya karanta.....ya kuma haddace.....ya karanta komai daya shafi halittarsu har kamar yana jinsa shi wani likita ne a kansu,ya karanta komai daya shafi hali da dabi'arsu har kamar ya gama sanin halayyarsu gaba daya......amma ko sau daya bai bari ya sauka daga umarnin Allah ba.

"Ka gayawa muminai maza da mata su runtse ganinsu,su kuma kiyaye farjinsu" Ya sani,yayi dukkan iyakacin iyawarsa.....yayi dukkan qoqarinsa na ganin ya kiyaye,bai taba yarda zuciya ta tunzarashi ba ya tsallake doka ko hurumin ubangiji......ya riqe kansa,ya yiwa zuciyarsa linzami.....duk da irin abinda yakeji,duk da irin yanayin dashi kadai yasan yadda yake wanzuwa a tattare dashi. Wannan din dai yayi imanin ko meye ya kalla Allah bazai taba rubuta masa zunubi ba,saidai tarin lada me yawan gaske. Koda ba don so ba.....ko da ba wani qaqqarfar alaqa ko dangantakar zuciya tsakaninsu......amma yana da tabbacin wannan halal dinsa ne.....wannan IKOnsa ne.....wannan damarsa ce Allah ya bashi.

Wani irin abu yaci gaba da zagayawa kowacce jijiya ta jikinsa,tafin hannuwansa da qafafunsa dukka sukayi sanyi,kamar yadda numfashinsa ya soma sauya yanayin fitarsa. Yayi relaxing sosai cikin kujerar kamar zai narke su zama abu daya shida kujerar,idanun sun masa wani irin nauyi,idan yaji da kyau ma kamar hawaye ke taruwa a cikinsu.

Hankalinta kwance take kai kawo tsakanin qarfe zuwa qarfe na balcony din,cikin wani nutsatsen taku. Tana jin ko hakan zai taimaka mata wajen zazzage dukkan wani tunani nasa. Idan tace shine abu na farko a duniya daya taba tsayewa tunaninta batayi qarya ba. Bata taba damuwa da komai da kowa ba,bata taba damuwa da wani abu ba......amma me yasa ya tsayewa tunaninta haka?. Meye dalili?. Amsar itace bata sani ba.

Lokaci lokaci take duban balcony din nasa. Wani abu takeji can qarqashin zuciyarta da ruhinta. Ba motsin kowa,ba motsin komai,hasalima a iya abinda idanunta suke gani fitilun bedroom din a kashe suke.

"Qila ma ya dade da yin bacci" Taji zuciyarta na gaya mata. Tsaiwa cak tayi tana dawo da maganar a kanta. Ya dade dayin bacci?dama saboda shi na fito?,meye damuwa na da baccinsa?,meye damuwana da motsinsa?. Tambayoyin da suka dinga dawowa cikin kanta kenan,suka sanyata kuma a hankali a hankali ta dinga takawa da baya da baya,har takai bakin qofar da zata maidata bedroom din ta shige da sauri.

Wani irin numfashi ya sauke yana runtse idanunsa gami da matse jikinsa guri guda. Wani irin numfashi yaci gaba da saukewa yana jin zuciyarsa na wani irin qarfi,har yana jin alamun sautinta cikin kunnensa. Iskar da yake shaqa da komai ma yana jin kamar an sauya masa su ne gaba daya.

Baisan adadin mintunan daya dauka a haka ba,ya sani dai yaji motsin bude qofar balcony din,ya kuma bude idanunsa yaga system din har ta shiga sleep mode saboda rashin wani motsi cikakke a tattare da ita.

Idanu suka zubawa idanu shida omar din,omar din da bai sake bari sun hadu ba tun wancan ranar da yayi subutar baki. Ba yadda baiyi ba yazo su qarasa aiki yace masa shikam ya tafi hutu. Maleek ne dan sasanci a tsakaninsu,dariyar da maleek yayi a wannan lokacin bata da iyaka. Ga sasanci ga gulma da nashi dariyar yana cinsa.

"Haisam dai?......zasuga yadda wannan al'amarin zai kaya.....zasuga yadda zai kasance.....baya sonta amma yana kishinta......auren CIMMA MANUFA ne amma komai yana tabashi game da ita?.

" Kana lafiya?" Omar ya tambayeshi yana tsareshi da idanu. Besan me zai cewa omar din ba.....baya fatan ma ya fahimci komai,don haka ya daga masa kai kawai yana janye lumsassun idanunsa daga kanshi.

Sake zuba haisam din idanu omar yayi,a jikinsa yakeji bai yarda da maganan haisam din ba.

"Captain......" Daga masa hannu haisam yayi,bayaso yace komai,don yana jin yafi buqatar kadaicewa a yanzu. Takowa omar yayi,yana sake nazartarsa

"Idan bakajin dadi ka tashi muje kasha magani zaifi kyau,baka zauna yadda ka saba ba......ga wasu document can dana shigo maka dasu". Idanu ya waiwayo ya zubawa omar,idanun da omar yaji kallonsu har cikin jininsa,kwarjinin nan ya dakeshi a hankali,sai ya dakata daga takowar da yake. Mamaki kadan yana sauka fuskar omar din,meye haka ya birkita haisam?. Bai taba ganinsa a bikice haka ba koda fushi yayi.

"Kaje zan fito" Ya bawa omar din umarni nakai tsaye. Yana jin ta yaya?,ta yaya zai iya miqewa a yanayin da yake ciki har yayi tafiya.

"Haisam....."

"Omarrrr" Ya kira sunansa yana danjan sunan. Sak omar din yaya,kafin kuma ya juya yana ficewa a hankali,bai kuma tsaya a nan ba,koda ya fita din daga bedroom din gaba daya ya qarasa ficewa yana bar masa saqon daya shigo dashi.

Ya sani bashi da tsawwalawa.....baida zafi baida yawan fushi,shi yasa duk yanayin daya nuna musu suke qoqarin yi masa abinda ya nuna yanaso. Idan baison magana da gaske yake baya so,idan ya nuna beson tambaya da gaske yake baya so,hakanan idan ya nuna bayason kusanci da gaske shima baya so.

Da wata irin mutuwar jiki ya fito daga wankan daya zame masa tilas yayi,jikinsa gaba daya yayi wani irin laushi,ya zauna da bathrobe a jikinsa na lallausan auduga da zare yana sauke ajiyar zuciya.

"Me nayi haka?" Ya tambayi kansa da kansa bawai don yasan wacce amsa ce daidai da tambayarsa ba.

"Haisam ka nutsu......ka nutsu haisam,me kakeyi haka?,akhnan ce fa?" Ya gayawa kansa da kansa. Sai tunaninsa ya koma can baya.....farkon fara sanin wanzuwarta a gidan,farkon fara sanin WACECE ITA.....maganganunta a kansu hakeem da ire irensa,sai yaja qaramin siririn tsaki yana miqewa a hanksli.

Tabbas kome Allah yayi hani akai akwai hikima a cikinsa. Yanzu irin wannan yanayin ko makamancinsa mazaje masu kallon haramci ga matan wasu suke tsintar kansu?. Me yayi zafi?,yanzu shima banda halal dinsa ya kalla yana da zunubi cikin littafin ayyakansa.

"A'uxubillah" Ya furta a hankali,ya dora hannunsa yana shafar qirjinsa yana jin wata qanqanuwar nutsuwa data saukar masa.

"Halal is the best.......tabbas halal is the best" Ya furta can qasan ransa.

Koda ya sake shiryawa cikin wasu kayan baccin,yayi sallolinsa daya saba sai kawai yaja files din yana dubawa. Ya zauna sosai yana nazarinsu daya bayan daya. Wani abu ya saki a hankali daga qirjinsa tamkar qullewar wani bahagon dauri. Fuskarsa ta sassauta daga daurewar da tayi. LALLAI BA SHAKKA AKWAI TARIN BIYAN BUQATA GA DUK ADDU'A DA LAMARIN DA AKA SANYA ALLAH A GABA,ya fada can qasan ransa yana sake girmama hukuncin ubangiji da yace zai sauqaqewa bayinsa abu me wahala.

★★★

A washegarin ranar tamkar wata sabuwar duniya haka masarautar ta kasance. Sultane ya kasance na musamman a zukatan al'ummar agadez gaba daya,kamar yadda ya kasance wani jigo kuma abun soyuwa ga al'ummarsa. Adalcinsa,tausayinsa da yadda yake bada kulawa me girma ga talakawansa ya siya masa wata qauna a zukatansu,bawai iya cikin masarautar kadai ba.💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 126*

Awanni uku da dawowar sultane din,can cikin kebantaccen parlor din daya kasance guri ne na musamman,guri ne da ba wanda yake iya kaiwa wajen sai iyalin me martaba,sai kuma kebantattun bayinsa dake hidimar kula da gurin,wanda hidimar gurin ma ya zamana kamar gado ne. Asalin masu hidima da gurin idan sun rasu 'ya'yansu ake dorawa akai.

Su biyu ne rak cikin parlor din,sultane wanda ya gama hutawa bayan shigowarsa,da kuma sheikh muhammad haisam.

Dukkaninsu suna zaune saman lausasan sofas dake parlor din. Hira suke shida haisam din,wani irin kalar hira da kana kallonsu zaka tantance zallar aminci da yarda daga idanun sultane din zuwa ga haisam din.

Cikin nutsuwar nan tasa.....cikin kamewar nan tasa yake amsawa sultane din. Dashi aka dauko sultane din daga airport......tare suka shigo da sultane har cikin gidan,saidai kuma suna dab da shiga sassansa ya samu ya zame ya shige cikin jama'a ya fice daga gidan.

Akwai aikin da zausuyi da beeno a ranar......wannan gidan dake kan hanyar villa street,gidan daya tabbatar akwai wani killataccen abu me tsananin darajar da girmansa yakai qololuwa a gurin zaituna.

Bai kuma shigo gidan ba sai ana dab da sallar la'asar,a masallaci suka hadu da sultane din,sukayi sallah a sahu daya

"Ina ka shiga ne muhammad?.....na tambayi iyalinka itama batasan inda kayi ba" Maganan yazo masa a wani ba zata,iyalinsa kuma?. A hankali sai kansa ya kawo wuta,ya tuna yana magana ne akan akhnan.

"Wani uziri ne na gaggawa ya tasomin ranka ya dade"

"To ba laifi,idan ka kammala ina buqatar ganawa da kai".

"In sha Allah" Ya fadi. Can qasan ransa yana sake yaba dattako da kamalar dattijon. Yana da ikon bashi umarni kai tsaye a matsayinsa na wanda ke rayuwa qarqashin masarautarsa da dokokinsa.......saidai kuma duka baiyi hakan ba,ya zabi bashi zabi.....ya zabi neman ALFARMA a madadin bada umarni nakai tsaye.

Wanka kawai yayi,ya kuma shirya cikin wata maroccon jallab me sulbi da daukan idanu. Hasken fuskarsa ya fita ta qarqashin kalar maroccon jallab din jikinsa data kasance ruwan sararin samaniya,hakanan kwarjininsa ya sake fita sosai.

A yau nauyin sultane yakeji sosai,nauyin da shi kansa baisan dalilinsa ba. Amma yadda sultane din ya sake sosai kamar yadda motii ke sakewa dashi ya sanya ya tattara nutsuwarsa a kansa.

Yadda yake bashi labarin komai daya shafi tafiyar yake sake azawa haisam din wani nauyi saman zuciyarsa.

"Ya yarda dani fiye da tunani na......yaya zaiji a duk sanda ya fahimci cewa na aminta na auri diyarsa ne saboda na danawa MATARSA TARKO?". Iya wannan tambayar kawai ta sanya yaji wani nauyi saman zuciyarsa kamar sultane din yana fahimtar abinda yake tunani a daidai lokacin.

*MORSA SAFIYYA*

Rana ta farko a rayuwarta da takejin wani nutsuwa a zuciyarta. Rana ta farko da takejin wani alfahari yana ratsata,rana ta farko kuma da takejin kome sultane yayi mata ya gama wankuwa a idanunta. Ta gaza hana kanta murmushi a duk sanda ta tuna akhnan din a yanzu tana qarqashin iko da mulkin sheikh muhammad haisam. Mutumin da dukka addu'arta a kansa nutsuwa take bawa zuciyarta. Ko zatayi addu'a dubu,ko zata maimaita istikhara irin wadda ma'aiki ya koyar guda dubu tabbas shi din takejin hankalinta yana sake kwanciya dashi.

Batasan me yasa sultane ya gayyaceta a wannan yammacin ba,amma abinda tafi sanya rai shine wani liyafar cin abinci ne ya shirya saboda dawowarsa,kaman yadda tayi masa ba zata ta hada masa wani qaramin liyafar a dazun.

Tsaf ta shirya cikin wani qawataccen shadda me tsananin tsada da daukan hankali,marron color ce wadda aka zuba mata wani qasaitaccen aiki da yake tabbatar da cewa ita din jinin BUZAYE ce. Wani irin kyau ta ajiye.....wani irin ado data manta yaushe rabon da tayi irinsa.

A yanzun take jinta a matsayim rayayya,a yanzunne take jinta a matsayin mutum kamar kowa,tunda tana da dukkan yaqini da nutsuwar jinin safeena ya isa ga SAFE ZONE.

A baya ba zata iya dorar da komai ba. Duk wani dare da wuninta da zai gilma ya kuma gushe cikin rudani da lissafin wanne hali AKHNAN take ciki?,wanne hali zata kasance.....wannan tunanin shine abinda yake kassarata a kowacce rana.

Da karsashinta take isa sassan sultane,a yau din hatta da hadiman da sauran bayi dake da aikin kula da wadannan hanyoyin sunsan akwai wani ajiyayyen farinciki tattare da morsa safiyya.

*AKHNAN*

Ba abinda ya dagata daga gurin sultane sai don ta barshi ya huta,dukkan wata qauna da soyayya tana jinta tsakaninta da mahaifin nata a yau kamar an sabuntata. Wani wakeken gibi....wani babban space da takeji a rayuwarta a yau yana cike gurbinsa a hankali.

"Ashe akwai wani gurbi da muhallin daya zamana MALLAKAR UBA ne shi kadai?" Ta dinga tambayar kanta sanda take komawa sassanta. Mamaki ne yake maimaituwa cikin kanta,tanason banbance yanayin da dana yanzu......tana banbance yanayin data tsinci kanta a sanda sultane ya miqa mata ragamar komai......ya barta ta auri zabinta,da kuma yañzun da ta aminta da abinda yakeso.

Tabbas nutsuwar ta dabance.....tabbas farincikin na dabanne......wannan yanayin baya mata kama da kowanne.

Iya aminta da tayi da auren da sultane ya rataya mata shine abinda ya haifar da wannan walwalar aminci da kuma gyaruwar alaqar a tsakaninsu?.

Wannan tambayar ta yita maimaitawa kanta.....wannan tambayar da take buqatar amsarta......tambayar data sanyata tsaiwa gaban madubi tanata duban fuskarta daketa glowing saboda yadda fatarta ta karbi gyaran da ake mata fiye da yadda take zato.

"Farincikin dake cikin yin biyayya ga umarnin iyaye ya haura duk yadda zaki fasalta biftu......" Aisa dake hada wasu document ta fadi kamar tasan abinda yake zuciyar akhnan kenan.

Readers Also Read

More by Huguma