Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 74

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 74

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 74: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 74. Wannan abun kadai shi ya haifar da zaquwarta wajen…

3,301 words

Wannan abun kadai shi ya haifar da zaquwarta wajen ganin yammaci ta sake komawa ga mahaifinta sultane.

Tsaf ta kammala shiryawa cikin Egyptian abayar me wani irin sulbi qyalli da daukan idanu. Maroon color ce,budaddiya sosai wadda aka zuba mata wasu irin stones masu kyau da daraja.

Ita kanta data tsaya gaban madubin da birra ta ajiye mata kamar yadda ta saba ajiye mata shi a duk sanda ta gama tayata ta shirya sai da taga yadda ta kwanta a jikinta da wani irin yanayi me daukan hankali.

Socks ta zauna birra ta zira mata. Umarnin yaa hairaan ce,batasan me yasa tazo yau din da kuma wannan salon ba,amma akwai wani sashe na respect da take bawa hairaan din,kuma socks din basa daya daga cikin abinda ke takurata don haka ta sanya,ta kuma zura qafarta cikin qawataccen takalmin da yazo mahadin rigar.

Ta miqe tsam,taku daya biyu aka murda handle din qofar,sannan kuma kai tsaye ba tare da jiran umarni ba aka shigo.

Mammina ce......murmushi kuma shine abu na farko data fara saukewa akhnan din tana qarewa shigarta kallo.

"Tabarakarrahman........diyata tafi ta kowa" Mammina din ta fadi a fili,amma can qarqashin zuciyarta kuwa,wata irin wuta ce ke kunnuwa......can qasan ranta wutar kota halin qaqa saita soma ganin tagayyarar akhnan da tabuwar rayuwarta shine abinda ke kunnuwa.

Wani abun mamaki......a yau din da take yabonta,a yau din da take kodata.......a wannan lokacin ba komai cikin zuciyarta game da dukka maganganunta. Wani yanayi da yasha banban da yadda ta saba ji akan kalaman mammina din,tun daga sands ta mallaki hankalin kanta zuwa yanzu.

Kalaman mammina a gareta suna da wani irin tasiri......suna da wani irin kaifi da suke sanya kanta kumbura da kuma huruwa,amma a yau sai taji bataji ko daya a kai ba.

"Zuwa nayi na biyo mu wuce sake gaida sultane ni da d'iyata" Ta fada tana neman gefan sofa bed ta zauna,abinda ya sanya birra fita a hankali tana bar musu dakin. Dan duban mammina tayi kadan,sai kuma ta basar da salon miskilancinta. A duk sanda ta waiwaya ta kalleta sai taga ba abunda take gani sai sakinta BARO BARO sama da guda goma da mahaukacin mutumin da itace silar shigowarsa rayuwarta yayi mata.... Tana jin ba dadi.....tana jin wani irin ciwo har qasan zuciyarta idan ta tuna cewa......ita kadaice keda tarihi irin wanna.....ita akhnan da labarinta ya shiga bakunan 'ya'yan sarakuna dana manyan attajirai da dama.

Sake dauke kanta tayi,duk yadda taso ta amsawa mammina din koda da qanqanuwar kalma ce ta kasa amsa mata. Sai ta fara takawa zuwa bakin qofa,a sannan ne ta samu ta fusgo kalmar.

"Na gode" A taqaice. Qanqance idanu mammina tayi tana kallonta,wani irin mamaki yana ratsata

"Ta canza.....tabbas ta canza" Ta fadi qasan ranta. Canji ne ba qarami ba,ba kuma na taqaitaccen lokaci ba,canji me girma da nauyi wanda koda yaushe yake zame mata barazana zuwa ga tabbatuwar tsarinta.

"Khadeeja" Ta kirata da wani yanayi me nauyi a muryarta. Mamaki ne ya sakata tsaiwa,saboda tunda take da mammina din bata taba jin ta kirata sunanta na asali kai tsaye ba sai yau. Bata umarceta tazo ba,saita tako ta cimmata.

"Meye yake damunki?,wannan yanayin naki yana sakamin shakku da kokwanto akan matsayin da kika daukeni a yanzu" A nutse ta waiwayo ta zubawa mammina idanu,bada kowanne nufi ba.....amma sai kallon ya yiwa mammina din nauyi,a karon farko taji akhnan a yau kawai ta mata kwarjini. Kwarjinin da tabbas tasan dashi,amma bata daukeshi da zurfi har haka ba,bata daukeshi da zurfi da nauyi kamar yau ba.

"Wani abu ya faru?" Ta tambayeta kai tsaye tana jin kamar tana bata mata lokaci. Mamaki ya sake shigarta,ta qanqance idanu tana dubanta sosai.

"Baki amince da dukka tsarina bane akhnan?" Idanunta sosai ta zuba cikin na mammina din na wasu daqiqu kafin ta janye dubanta,sannan taci gaba da takawa tana yin gaba,abinda ya sanya mammina din mara mata baya itama tana biye da ita.

"Basai na furta da bakina ba......ba kuma saina dakatar da aiwatar da abinda nima nakejin zan iyayi ba.....idan kin yarda da kanki mammina.....kawai kici gaba da abinda kika tsara.....basai kin gayan tsarikanki ba......basai kin tuhumeni nima akan tsarikana ba"

"Ta canza!" Ta fadi can qasan maqoshinta.

"Zaituna dole kema ki canza taku!!!" Zuciyarta ta gargadeta da mafi girman gargadi. Cikin sakewa.....cikin rashin nuna damuwa ta saki murmushi.

"Zaitunan nan dai ta jiya da shekaran jiya har yauma itace,....ba kuma zata canza miki ba,ba zata kuma fasa shiga lamuranki ba har sai sanda kika cimma gaci" Haka kawai taji kalaman basu burgeta ba,mutum ce ita da sau tari take zabar zaman lafiya da kwanciyar hankali sama da rikici da tashin hankali,wannan ya sanya take da dab'ar miskilanci.......wannan ya sanya take da dabu'ar kebe kanta a mafi yawancin lokuta ma.......a yanzun a wannan lokacin......tana jin nutsuwa da Kwanciyar hankali sama da sanda zaituna ke tsara al'amuranta dama bibiyarsu.

Tare sukaci gaba da takawa,saidai akhnan din ta zabi shuru sama da magana......ko dama can tafi zabar shurun,a yanzun kuwa ta fifitashi ne.

"Zan tabbatar miki da AUREN YARJEJENIYA ne tsakaninki da wancan malamin......alqawari na yiwa mahaifiyarki zan samar Miki da dukkan wani farinciki.....alqawari nayi mata bazan bari rayuwarki ta taba toxarta ba,alqawari ne zan samar miki da dukkan abinda kikeso......bazan bari komai da bakiso ko baki qauna ya shiga rayuwarki ba" Ta fada da marairaicewa,harda guzurin qwalla cikin idanunta daidai sanda suke dab da shiga farfajiyar da kebantaccen dakin hutawar sultane din yake.

Waiwayowa tayi kadan ta kalleta,wani abu yana tsalle da rarrabuwa a qirjinta. Wanne ne yafi dacewa ne?......ta tabbatar mata da MURADIN ZUCIYARTA?.......ko kuma zata tsaya wajen zaba mata abinda ya dace da ita?....koda zatayi kuka......koda zata quntata......koda zataji ba dadi?.

Rasa banbamce amsar tayi.......kasa tantance wanda yafi kamata ta zaba a ciki tayi saboda daddad'an qamshin nan nasa da ya shaida mata YANA GURIN.

Saukar da kanta da kuma idanunta qasa shine abinda takeso tayi,amma haka kawai taji ana sarrafa zuciyarta dama idanunta wajen watsasu a dakin hutawar sultane din,labbanta masu kalar ruwan hoda me haske suna motsawa da siririyar cikakkiyar sallamar data samu kanta da yinta,sallamar data zarce ta kuma hade da fadawar idanunta cikin nasa.

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 127*

Kamar kowanne lokaci da zata ganshi......yana zaune cikin wannan nutsuwar.......wannan kwarjinin......da wannan zaman da yake nuna wani babban abu tattare dashi.....babban abun da har yanzu ta gaza canko MENENE?.

Da qyar ta zare idanun nata daga kanshi da wani irin sanyi da batasan na meye ba. Kwana daya kwana biyu kwana na uku kenan bataga koda gilmawarshi ba.

"Kwana uku?" Ta tambayi kanta,sai taji wani abu ya mata tsaye a wuya,wani abu da batasan meye ba......wani abu me nauyi mara dadi a qirjinta. Ko a dazun cikin wadanda suka yowa sultane rakiya,ta samu kanta,ta kuma samu idanunta da jujjuyawa ba tare da tasan me take nema ba?. Haka kawai taji kamar akwai wani gibi ko wani gurbi ko muhallin da ba'a cikeshi ba.

"Taho ki zauna a nan" Kalmar data iya ji qwaya daya kenan Sultane yace da ita yana nuna tazarar dake tsakaninsa da haisam din.

Idanunta ta sauke a gun,tazara ce maras nisa sam,koda tayi kusa da sultane yayin zamanta.....dole zatayi kusa dashi ainun. Ta yaya?,ta yaya zata iya dauke wannan kusancin?,ta yaya zata iya shanyeshi?. Idanunta ta lumshe a hankali sannan ta bude lokaci guda. Ta tabbatar yau sai abinda ta gani.....qamshin nan......wannan qamshin tana jin zai iya hallakata tsaf kafin ta tashi daga tsakiyarsu. Batasan idea din wanne shu'umi bane......batasan wanne shu'umin ne ya samar da wannan qamshin ba.

"Wai zaman me kukeyi safiyya da baku miqawa muhammad matarsa ba tun ranar da aka daura aure?" Sultane yayi maganar kansa tsaye,idanunsa kan morsa safiyya. Morsa safiyya din da a yau takejinta tamkar an bata kyautar duniya da abinda yake cikinta.

Wani lafiyayyen murmushi ta sauke.....wannan murmushin dai dake kashe zuciyar mammina da wani irin makami da takejin ba na biyunshi a duniya wajen iya illata ZUCIYA......(zuciya irin tata ba......zuciyar maqiyi,zuciyar abokin adawa,ya rabbussamawat Allah ka doramu akan maqiya,Allah ka sani mu bama qin kowa......bama tsanar kowa,saboda mun sani duk wanda ka halitta bawanka ne,kuma kana qaunar abinka,bamu da hurumin da zamu tsaneshi ko mu qishi,tunda bamu muka halitta maka shi ba,ya Allah kai mana tsari da duk wanda yake da mummunar nufi a kanmu don isar shugaba S A W har izuwa ranar qarshe).

Maganar data saukarwa akhnan a bazata da wani mummunan faduwar gaba........ta kuma sanyata qarasa zama duk da bata gama kaiwa qasa ba. Ta saukar da wani nauyi a zuciyar haisam me yawan gaske.......a nasa plan din koda a haka aka tafi komai zaiyi daidai da tsarinsa......basai ankai nan ba......basai ankai inda za'a tattarata dukka a damqa masa ba.

"Idan da ace ka bada umarnin aikata hakan......la budda da sai mun zartar......saidai muna buqatar kimtsa diyata da kyau" .

Ido mammina ta lumshe,ta kuma ja numfashi sosai tana qoqarin kimtsa kanta.

"Ki nutsu zaituna......NUTSUWA MANA ZAITUNA!" Ta samu kanta da tsawatarwa kanta da kanta. Maganan yayi tasiri,don haka ta qaraso tana zama daga gefan morsa safiyya gami da fidda murmushi a fuskarta.

"Haka maganan yake ranka ya dade........d'iya ce ta musamman......wanda nima nake dakon safiyya ta gama nata shirin na dora da nawa"

"Ban yarda da wannan tsarin ba......shirin meye haka?". Numfashi haisam yaja,yana jin maganan tayi nauyi suci gaba da yinta a gabansa. Sultane yayi mugun bashi matsayin da yakejin bai kamata ya bashi ba. Ya kamata ko yaya ya rage wannan girman matsayin daya bashi,tunda komai TEMPORARY ne,komai FAKE ne......komai na WUCIN GADI NE.

"Zan iya qarasawa?" Ya tambayi izinin sultane cikin girmamawa.

"Au.....tafiya zakayi ka barni da yaqin karba maka mata?,kai ba zaka tsaya su baka matarka ba?" Sultane ya fadi cikin barkwanci . Dariya akayi,saidai tsakanin shi da mammina da akhnan data sadda kanta qasa cikin wani yanayin bugun zuciya dariyar kowa tasha banban data d'an uwansa.

"Ku gama duk abinda zakuyi ku bashi matarsa,don rana ita yau in sha Allah zasu wuce umra shi da ita.......kana da zabin dawowa nan?.....ko zaku wuce gida?". Kai ya jinjina a hankali. Ya akayi kwanakin da sultane ya yanke suke daidai da kwanakin CIKAR AIKINSA?.......ya akayi kwanakin da sultane ya dauka suke daidai da kwanakin KAMMALUWAR KUNDIN ZAITUNAN ZEENATU?. Ya akayi suke daidai da ranar farko da zai bude bakin BOMB din da zai fara kada rayuwar zaituna?.

"Zamu wuce ETHIOPIA" haisam ya fada kansa tsaye.

Sunan Ethiopia ya buga da wani irin qarfi a kunnuwa da zuciyar mammina. Sunan ETHIOPIA kadai barazana yake zame mata ballanta tuna QASAR. Ethiopia din da yanzu ta zame mata JARRABAWA na dukka darenta,duk wani dare da zata sanya kafadunta saman gadonta sai Ethiopia gaba daya tazo mata duk da kasancewarta qasa ba dan adam ba. A manya burikanta da tasan basu da ranar cika shine......shafewar Ethiopia gaba daya......shafewa ta har abada,inda tana da hali.....inda tana da dama da shafe qasar zatayi daga doron duniya dama dukka abinda ya shafeta.

Sunan qasar ya sake dokawa a kunnuwan morsa safiyya,ya taso da tsohon ciwon dake kwance a cikinsa.

"KHADEEJA" shine sunan data furta a hankali tana dauke wata qwalla data sauko mata. Haisam shi daya ya lura da wannan,haisam shi daya ya lura da motsawar labban morsa safiyya. Wani abu yaji ya sauka saman zuciyarsa.....bazai iya haqurin ci gaba da kallon morsa safiyya a haka ba.....bazai kuma iya haqurin ci gaba da barin nanay dinsa cikin duhu ba.....saidai ba yanzu ba.....ba'a cikin agadez ba......ba a wannan lokacin ba......sai a sanda yakai mata diyar safeenarta gabanta......a sanda ya hada hannun nanay dinsa da hannun copy na safeenarta.

"Ma sha Allah.....hakan yayi,to kunji.....saiku gama duk uzurinku,gobe zasu wakilceni a festival......kwana biyu nakejin zasuyi saboda visa dinsu ta fito tun ina can......khadeejatu" Sultane ya fadi yana duban akhnan.

"Na'am bappi" Ta furta da wani irin sanyi,da wani irin yanayi da yake sauyata daga akhnan dinnan.....wannan biftu din me tsananin kafiya da taurin kai......zuwa new version na princess khadeeja muhammad hammud.

"Naji dadi sosai.....naji dadi sosai yadda nazo na samu ba wata matsala,naji dadi sosai yadda na tarar da komai fiye da zatona.....na kuma sake alfahari dake sanda haisam ya tabbatarmin komai lafiya.....naji alfahari dake da ban samu labarin tarzoma ko wani abu makamancin haka daga gareki ba.....Allah ya albarkaci rayuwarki......ya baki ikon yin biyayya ga mijinki kwatankwacin yadda SAFEENA ta bini"

"Ameeeenn" Amsawar morsa safiyya da wani sauti dake nuna zallar qwarin gwiwa ta sauka a kunnen mammina,ta kuma gauraya da sautin sunan SAFEENA.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Qasa tayi da kanta tana jin wani ciwo yana diga saman zuciyarta.

"SAFEENA.....SAFEENA" Wai sai yaushe kunnuwanki zasu daina jin wannan sunan?,sai yaushe wannan sunan zai daina gilmawa cikin rayuwarki?,sai yaushe zaki samu AMINCI?,sai yaushe zaki huta?,yaushe SAFEENA ZATA daina zame miki barazana?.

"ETHIOPIA" sunan ya sake dawo mata fes cikin kanta,dawowar sunan daya sanyata daga kanta da hanzari takaisu ga haisam.

Cikin wata irin sa'a idamunsu suka gauraya guri daya. Wani irin bugawa zuciyarta tayi da ganin wadannan idanun bisa kanta.

"The silent one......jinin ibraheeem" Taji ana fadi tsakiyar kanta. Wasu irin idanu irin na ibraheeem sak.....wani irin kallo irin na ibraheeem......kallon da bazata manta dashi ba muddin numfashinta(WAYE IBRAHEEEM DIN?.....MEYE TSAKANINTA DASHI?.....AKWAI WATA A QASA NE TSAKANINTA DA MAHAIFIN HAISAM BAYAN WADDA TAKE TSAKANINTA DA MAHAIFIYARSA?).

Wannan kallon......wannan idanun.....dama dukkan abinda ya faru ranar a parlor din shine abinda ya tsaye mata a kai. Sunan Ethiopia ya dinga wanawa cikin kwanyarta kamar ana buga gwangwanaye kusa da kunnuwanta.

"Tafisu......inaji a jikina jinin ibraheeem ne wannan" Abinda ta kira tafisu kenan tana gaya mata. Kai tafisu ta girgiza cikin nutsuwar nan tata da kaifin basira.

"Idan kuma bashi bane bafa?,idan kuma wasa kawai yake miki da hankali fa?,idan kuma so yake ya dauke hankalinki kawai daga kan komai fa?" Sosai maganganu tafisu suka ratsata. Ta miqa hannunta tana dafa na tafisu. Tana jin gaba daya a yanzu rayuwarta kamar ta ta'allaqa da ita,tana jin a yanzu kamar bata iya wani tunani me kyau,kamar kwanyar tafisu ce ke iya hange mata komai.....kamar wata Katanga ta kusa GINE tunaninta.

"Gidancan na villa street" Shine abu daya dake kwanyarta a yanzu. Duk da tasani.....wani kebantaccen abune da ko tafisu batasan dashi ba,amma DAUKE ALMAZ tana kallonsa a matsayin gargadi.....daukeshi akayi da gasken.....ko yasha ta gaya masa qarya ya gudu da qafafunsa ya shriya daukeshi akayi?. Koma meye yana fatan ALMAZ ya narke har abada......koma tafiya yayi tana fatan ya tafi kenan har abada........tunda ko be tafi ba.....dashi da duk wanda jininsa yake yawo a jikinsa irin jinin nan data tsana......dole ne babinsu ya shafe gaba daya daga doron duniya.

*_FESTIVAL DE l’AÏR_* *_Sanda sabbin shafuka zasu bude.......tsaffin shafuka kuma zasu rufe kansu da kansu_*

Cikin wani irin yanayi da tsari na girmamawa sultane yasa aka shirya aka kuma tsara komai,yadda tafiya zata kasance daga nan har zuwa sansanin da za'a gabatar da bikin. Sansanin da zuwa yanzu idan ka kalleshi zaka rantse ba shimfidaddiyar sahara bace a kwana uku baya daya wuce ba.

An qawata gurin da komai na buqata,an gina tent tent na kwana da canopy saboda zama,bandakunan tafi da gidanka na wucin gadi,kujeru qawatattun na zama don hutawa.....hakanan baqi da suka fara sauka daga kowanne sashe na qasar niger dama qasashen duniya gaba daya. Wani yanayi aka samar me cike da daukan hankali da ba'a taba samun irinsa ba a tarihin festival de l'Aïr....tun daga yadda aka tsara tent din layi layi unguwa unguwa.....kamar yadda tsaron gurin ya zama na daban saboda kusan komai bisa shawara da tsarin sheikh muhammad haisam aka gabatar dashi a wannan shekarar.

*AGADEZ PALACE*

Har cikin jininta takejin jinin BUZAYE yana mata a yau,a yau din ta jita a cikakkiyar buzuwa wadda ta amsa sunanta,musamman data kalli kanta cikin shigar suturar al'adar buzaye. Wata irin shadda ce a jikinta data fidda ainihin zallar al'adar buzaye,wata irin color take bayarwa,ita ba dark purple ba.....ita ba ruwan hanta ba hakanan ita ba baqa ba,saidai kalar da tazo da ita me duhu ta haska ainihin fatarta gami da fidda zallar kyanta.

Irin wannan rana tana zame mata ranar alfahari.....ba ita kadai ba,rana ce me muhimmancin gaske agun kowanne buzu dama al'ummar niger mali da burkina faso gaba daya.

Baya kawai birra taja tana dubanta,murmushi na fita daga saman fuskarta. Wani irin kyau akhnan din tayi mata yau din.

"Kinyi kyau ranki ya dade" Ta furta cikin girmamawa. Maganan birra din ta sanyata maida dubanta ga madubin tana qarewa kanta kallo. A yau sai take ganin kamannin data gani saman hoton mahaifiyarta akan fuskarta. Hannu tasa ta jawo Locker din gabanta,ta zaro hoton tana kallonta. Murmushi take,murmushi takeyi sosai cikin hoton,tamkar ba abinda yake damunta.....kamar ba ita ta rasa yaranta har guda biyu ba,akwai alamun tawakkali sosai da imani da yarda da qaddara a tattare da ita. Tana da blue eyes irin nata......hancinta shape din fuskarta da sauran wasu abubuwan da suke sake bayyana tsananin kamanninta da ita.

Tare da birra suka dauke idanun daga kanta,ta sauke ajiyar zuciya,daidai sanda birran take cewa

"Allah ya gafarta mata" Samun kanta tayi da waiwayowa tana duban birra din,sai taji qafafunta sunyi sanyi

"Ameen" Ta fadi a hankali tana maida idamunta ga madubi.

"Allah ya gafarta mata" Itama ta samu kanta da fadi can qasan maqoshinta,tana kuma sake maimaita kalmar. Ba zata iya tuna rana ta qarshe da tayi wannan addu'ar a kanta ba.....ba zata iya tunawa ba,tana dai tuna sabani na qarshe da suka samu da morsa safiyya.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 128*

"Hairaan,duk sanda ta gama sallar nan ki sanyata ta yiwa safeena addu'a" A wata rana kenan bayan hairaan ta sakata a gaba tayi sallah. Ranar mammina bata nan,ta fita dubiyar marasa lafiya asibiti kaman yadda ta saba. Kusan dukanta hairaan tayi kafin ta fara sallar,tanayi kuma tana kuka,daga qarshe kuma hairaan din tace lallai saita yiwa safeena addu'a. A sannan bata gama tantance wace safeenar da ake damunta a kanta ba......ko sanda zata ta tance wace kuma tuni mammina ta sabar mata da kammala sallarta ta tashi ta kama sabgogin gabanta,ita kanta bata saba ta daga hannu ta yiwa kanta addu'a ba bare a sako da mahaifiyarta.

A yanzun.....a daidai wannan lokacin sai komai ya dawo mata kamar yanzu yake faruwa. Morsa da sultane a bakinsu kawai takejin

"Idan kinyi sallah ki yiwa safeena addu'a" Me yasa mammina bata taba gaya mata haka ba?. Wannan tambayar itace ta tsaya mata cak a rai,ta kuma hade da alamun bude qofar dakin da taji anyi.

Hairaan ce,sanye da tufafi itama shigen nata. Tana dauke da Aaron a kafadarta. Tayi wani irin kyau,irin wannan asalin kyan na buzaye wanda suka gajeshi tun daga salsalar turkawa.

Yaron tabi da kallo tana amsa sallamar tata,wani abu da hairaan ta lura ta koya kwanan nan. Tanason yara sosai.....ita kanta ta sani,saboda ta rayu tsakanin manya ne,ta rayu a inda bata ganin yara,amma wani abu ya taso ya danne wannan feeling din daga ranta. Rashin ganinsu da rashin sanin yadda idan an batasu koda riqewa na wasu mintuna yadda zatayi handling nasu ya binne komai daga ranta. Ko zamansu Aaera da Aafreen basu wani dameta can can ba,amma zuwan yaaa hairaan da qaramin yaron Aaroon kullum idan ta kalleshi sai taji yaron yana burgeta.

"Ma sha Allah" Hairaan ta fadi tana murmushi,ita kanta kyan akhnan din ya daketa,ya bugeta da wani irin burgewar data gaza boyuwa.

Readers Also Read

More by Huguma