L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 75
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 75: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 75. Karon farko ta samu kanta da sakin wani qaramin…
3,375 words
Karon farko ta samu kanta da sakin wani qaramin murmushi mara zurfi,mamaki ya sake kama hairaan sanda taga akhnan din tana miqa hannu zuwa ga Aaroon. Sai data kalli akhnan din sosai,tanason tabbatarwa kanta itace?. Kallon daya sanya akhnan taji nauyin hairaan din ya saukar mata. Tunda take haife haifen yaranta ko Allah ya raya bata taba cewa ba ballantana akai ga yunqurin daukarsu. Batace komai ba ta zame Aaroon dake bacci daga kafadarta ta miqa matashi,ta sanya hannu biyu yadda taga anayi ta tallafeshi sannan ta rungumeshi a jikinta.
"Ashe haka akeji?" Ta tambayi kanta sanda dumin yaron ya ratsa jikinta. Shehnaz itace sarkin rakace rakacen yara,takance mata.
"Yaro.....yana da nishadi da debe kewa,akwai wani abu na musamman tattare da yara.....ko dabba idan kikaga ta cutar da yaro ba qaramar azzaluma bace". Idanunta ta dauke daga fuskar yaron ta maida ga hairaan
"Bacci yake" Kai ta gyada mata,tana jin dadi da mamakin sauyin dare daya haka?. Duk da ba'a mamaki da ikon Allah,ba'a kuma raina qarfin addu'a,addu'a ma irinta momma data dauki sama da shekaru ashirin kullum sai tayi.
"Tunda abida ta gama shiryashi yahau bacci....." Ta amsa mata,kafin shuru ya sake mamayar dakin. Neman izinin shigowa daga birra kuma ya katse shurun.
"Me wada yace na shaida miki komai na tafiya ya kammala" Kai ta gyadawa birra ta fara yunqurin miqewa da Aaroon a hannunta,sai hairaan ta miqe da sauri da zummar karb'arsa.
"Ki qyaleshi,zan iya" Ta fada da qarfin zuciya,duk da ita kanta mamakin qarfin halin da tayi takeyi. Bata taba daukan yaro ya jima haka a hannunta ba,yau gata itace rungume dashi har zasu fita.
"Anya akhnan sheikh haisam zai bari ki fita a haka?" Hairaan ta furta tana tsaiwa a bayan akhnan din.
Gaba daya shigarta ta fidda sigar kyanta,wanda dama hakan kamar wani abune daya zama jiki. A duk shekara a gurin bikin princess of agadez din daban take fita,kyanta kwarjininta dama kamalarta. Fuska kadan ta kyabe tana duban hairaan.
"Meye aibun shigata ummin Aaroon?" Murmushi hairaan ta saki,yau tanata ganin abun mamaki tattare da akhnan din. Ummin Aaroon ba a bakin akhnan take jinsa ba,saidai ta jishi a bakin falaak ko wasu cikin causing dinta.
Tare suka jero da hairaan da falaak wadda tayi wani irin kyau itama cikin shigar suturar al'adar,saidai wasu kaloli da suke bambanta kadan kadan dana wasu.
A yau sai takejin kamar festival din ya banbanta dana kullum,haka kawai takejin wani irin sanyi da sakewa a ranta,nutsuwa ta musamman takeji a tattare da ita. Saidai kuma haka kawai ta dinga jin faduwar gaba kadan kadan sanda suke dab da qarasowa farfajiyar farko da zata fiddosu zuwa ga babbar harabar gidan data tabbatar kowa da kowa yana jira. Abinda ta lura dashi,a yau din ba wani cikin hadimai ko bayi maza tare da ita,daga ita saisu birra din,sai hairaan da falaak dake biye dasu.
Duk da ba zuzzurfan sabo bane da sanayya tsakaninta da falaak din ba,amma ta fuskanci akwai wani kwantacciyar walwala tattare da ita. Sau uku kuma suna hada idanu da ita tana sake mata murmushi,ana hudunne ta kalli hairaan.
"Ummin Aaroon......wai ba zaki gayawa yaa akhnan bane?".
"Me?" Hairaan ta fadi tana duban falaak din,sai kuma ta furta.
"Au.....sannu mara kunya.....wai tanaso saita gaya miki itama sultane ya bada ita......ya bada ita wa maleek......aboki ga sheikh haisam" Daga kanta tayi da sauri tana duban falaak,ta dauka zataga samu yanayinta ya canza......ta dauka zata ganta yanayinta ya sauya zuwa yanayin bacin rai ko kuma qunci,amma ga zallar mamakin ta sunne kai ma falaak din tayi tana murmushi. Idan har idanunta sun gane mata daidai,idan har idanunta ba qarya sukayi mata ba falaak dariya take me cike da walwala da annashuwa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Abokin sheik haisam" Maganar ta sake maimaituwa cikin kanta. Inde hakane me ya banbamta yanayinta dana falaak?,me yasa falaak take walwala ita kuma ta kasa samun wannan yanayin?,me falaak ta hango wanda ita bata hangeshi ba?. Me yasa falaak take farinciki da samun abokin shiekh muhammad amma ita ta gaza jin hakan a tattarr da ita?. Bata samu sararin amsa wannan tambayar ba,ta tsinci sautin mammina tana isowa gurin itama.
Ji tayi kamar wani abu yayi disturbing nata da bayyanar mammina din. Ta daga idanunta a nutse tana dubanta sanda take dubanta itama.
"Meye haka?" Mammina ta mata tambayar da dukkaninsu ba wanda ya gane ma'anarta ballantana amsarta.
Cikin nutsuwa hairaan ta tako gaban akhnan.
"Kawo Aaroon din mu wuce kafin ku gama" Janye yaron dake kafadarta akhnan tayi.
"Qyaleshi bacci yake.....zamu taho" Hairaan batace komai ba ta juya tana kama hannun falaak sukayi gaba.
Ba tun yau ba.....ba tun yanzu ba,haka kawai Allah ya zuba mata tsanar matar. Tana dannewa ne kawai bata nunawa,don ta tabatar morsa safiyya ba zata bari ta nuna ko tayi wani abun na ba daidai ba.
"Ms kike shirin nunawa duniya ne?" Mammina ta fadi fuskarta na nuna zallar bacin rai qarara. Irin bacin ran da idan ta nunashi a baya yake daga hankalinta,irin bacin ran da idan ta nunashi a baya koma me take buqata ta gama samunsa daga gurin akhnan din,saidai a yau.....a kuma yanzu gaba daya batajin komai game da yadda ranta ya baci.
"Auren da nake shirin 'yantaki a kanshi?,shine kike shirya jere kafada dashi?,a gurin taron al'adun da duk duniya idanunsu yana kai?,zakije dashi a sunan mijinki?,MALAMIN AKHNAN?".
Sam sam bai lura ba tahowarsu ba,saboda hankalinsa yana kan qaramar na'uarar dake kafe a filin festival din,wanda yake sarrafata daga inda yake tsaye.
"Gata nan fa.....ya subhanallah" Muryar maleek da wani irin amo taja hankalinsa,ta kuma sabbaba masa daga kansa zuwa gareta ba tare daya shirya hakan ba.
Idanunsa ya dauke yana jan siririn tsaki.
"Ka nutsu maleek.....ka nutsu.....bazan tolerating wannan susucewar da kayi ba". Haisam din ya fadi a dake idanunsa akan na'urar,saidai kuma can qasan ransa yake jin kamar akwai wani abu da aka rasa a gurin,kamar daya kallesu akwai wani abu daya da bai cika ba a gurin.
"Saidai kayimim afuwa da gafara mr lowering gaze......na yarda na yarda na yarda akan mace ba wani wada yake da sauran IZZA ko SARAUTA......na rantse maka har ga Allah,ban dauka akwai macen da zata kwacemin kai haka ba a duniya......sai ga wani irin so daga falaak muhammad hammud" Da wani irin nauyi yanayi da amo yayi maganar,abinda ya sanya haisam daga kai ya dubeshi don ya tabbatar da gaske yake?.
Sai a sannan ya kula.....wai ashema ya baje ne ajikin amjad ne yana suburbudo wadannan kalaman,shi kuma amjad din ya wani tallafeshi kamar a film din india.
Haushi sosai ya cika haisam.....baisan yaushe maleek yakeso yabi sahun su omar ya koma dan wasan kwaikwayo ba.
"Buzuwar nan ta tafi dani"
"Aiba kai kadai ba dan uwa.....gwara kai ka kama dahir.....ni bansan a wane matsayi nake ba" Amjad ya furta yana shafa kafadar maleek kamar me lallashin qaramin yaro.
Cak haisam ya dakata,sai ya ajiye na'aurar a wani abu me kama da side table dake gaban seat din da yake zaune,yasa yatsunsa ya kama habarsa kawai yana kallonsu,ya rasa me zaiyi,fada zaiyi ko kuma me?.
"Obbo.....gimbiya ce kawai ta rage" Abdii ya leqo daga seat din bayansa da nasa tsurkun yana fadi.
"Nima ban hangeta ba" Khadeem ya fada. Waiwayowa yayi yana raba dubansa tsakanin abdii da khadeem. Kenan duk wata fitowa tata suna ankare da ita?,ko kuma aikin hakan ya basu?.
Yaji a jikinsa dama akwai wani abu da yayi saura,kuma ko a yanzun da 'yan riga malam masallacin nasa suka gane masa jikinsa ya bashi wani abu. Yaga fitowar mammina da mutanenta......ta ganshi ya ganta sunyi idanu hadu,ya sauke kansa daga dubanta,saidai bai sake bibiyar motsinta daga kwanyarsa ba,don haka koda ta juya tana komawa hankalinsa da nazarinsa yana lissafe da ita.
"Ku canza mota please kafin na fito" Kawai yace dasu bayan ya bude murfin motar a taqaice yana sauke qafarsa qasa wadda ke sanye da wani kyakkyawan rufaffen takalmi.
Bai ko waiwayo ya dubesu,bai kuma damu da kallon kallon da sukewa juna ba ya fara takawa zuwa hanyar da zata sadashi da sassan akhnan din kai tsaye. Dukka masu tsaron hanyoyin,kowanne ya janye masa yana sadda kansa qasa cikin girmamawa da yadda kwarjininsa ke bugarsu a kullum.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 129*
*M A M M I N A*
"Ki dawo hankalinki akhnan.....ki dawo cikin hayyacinki mana......ta yaya zaki dinga aminta kina fita da mutumin da baki shirya zama dashi ba?,ta yaya zan samu nasarar yi miki abinda kikeso bayan kina nunawa duniya kina tare dashi?,yana nunawa duniya yana baki kulawa.....me kikeso ace?,ya kikeso a kalleki?.....ke da kanki zaki jera da malamin daya kasance qarqashin inuwa da alfarmar mahaifinki?". Idanu sosai ta xubawa mammina,karon farko a rayuwarta da taji gaba daya maganganun mamminan suna sauka mata a zuciya da wani irin rashin tsari. Sai data sha numfashi sosai,ta lumshe idanunta sannan ta sake budesu fes akan fuskar mammina din.
"Eh......tsarin sultane ne.....abinda kuma zai iya bawa sultane farinciki kenan a daidai wannan lokacin" Tayi maganar tana duban idanun mammina kai tsaye. Wani murmushi mammina ta sake,a bayan burin sultane.....a bayan tsarin sultane daya tilastata,tana hangen wani abu daban daga can wani nisan nisa.
"Tsarin sultane?,ko kuma kece aminta da hakan?" Ta fadi tana son auna gwargwadon abinda ke shimfide a zuciyarta. Kanta ta karkatar gefe tana cije lips dinta,tana jin gaba daya mammina a yau ta cikata,tana jin kamar daidai da iska me kyau ta hanata shaqa.
"Kina so nayi fito na fito kai tsaye da tsarin sultane?" Tayi tambayar tana dagewa mammina dukka girarta sama. Maganan ya danso taba mammina,abinda ya sanyata saurin gyara harshenta dama tsaiwarta kenan. Tana jin wani matuqar tuqewa,tana jin matuqar kaiwa maqura. A yau din itace tsaye gaban akhnan suna musayar ra'ayi?.....suna musayar yawu?,suna kuma musayar maganganu?.
"Ko kadan.....saidai kin saki zaren ne yayi sakwa sakwa........baki da zarafin kaucewa maganan sultane,.......amma hakan bawai yana nufin kiqi nuna ra'ayinki ba.....ke sarauniya ce akhnan......bai kamata ace kina yawo da namiji ba,wanda har yanzu na tabbatar ke kanki bakisan ASALINSA BA!.....Wayeshi?" Tayi maganar da wani irin nauyi daya daki qirjin akhnan. Wannan maganan ya samu matsugunni sosai cikin zuciyarta. WAYESHI?,da gaske batasan wayeshi ba.....da gaske batasan komai a kansa ba,da gaske ba zata iya dorar da komai daya shafeshi ko ya danganceshi ba.
"Ki tuna matsayinki mana......ki tuna kanki biftu ki tuna wacece ke!.....baki cancanci mutum mara asali ba!" Tayi maganan da karyewar zuciya,tanason BUDE WATA QOFA......tanaso ta budewa akhnan wata qofar da zata zama me nisan zango,qofar da zatayi tafiya me matuqar nisa a cikinta.
"ASALI shine mutum,ba wanda ya damu ya duba miki wannan,ba wanda ya damu ya tabbatar da nutsuwarki wajen sanin hakan,kowa idanunsa ya kulle....kiyi aure......kiyi aure,haka soyayya take?....da uba ake ado! Kamar yadda kike ado da taqama da naki uban!.....waye nasa UBAN?". Ta sake fadi tana waro idanunta waje tare da qoqarin nunawa akhnan girman abinda ke fuskantota. Shuru ne ya wanzu a gurin,yayin da zuciyarta ta fara mata wani karatu.
"Karki kuskure akhnan......karki kuskuren fahimtar littafin da yake a rufe.....karki kuskuren fahimta littafin da baki bude koda shafi guda kin karanta ba".
Kamar wani abu ya fusgi hankalinta,saita dauke idanunta a hankali daga kan fuskar mammina dake sake bata yaqini da kuma dasa mata zargi,sai gashi sun sauke kansu da kansu a hankali a bayan mammina da tazarar takun da yakai goma sha biyar.
Da farko farin zabgegen buxu ta gani......irin jinsin da yafi kowanne jinsi nasaba da qarfi cikin jinsin buzaye. Giant zabgege fari tas,sanye da wannan turkudin(wani nau'in abu kamar rawani me kalar bula bula da sirki sirkin ruwan hanta da buzaye ke amfani dashi a taruka da dama irin nasu.
Gwanintarsa da qwarewarsa wajen sarrafa rawani......sarrafawa irin ta matasan malamai da sukasan sirrin ado da gayu daga matasan larabawa ya sanya nadin turkudin ya zama na musamman a kanshi da kuma fuskarsa,zabgegiyar takobi ce rataye a kafadarsa ta dama tayi crossing a jikinsa zuwa cinyarsa ta hagu. Kaman a wancan ranar......zagayen idanunsa kadai......zagayen idanunsa kawai take iya hange,wasu irin idanu masu matuqar haiba da kwarjini. Yayi wata tsaiwa hannuwansa goye a qirjinsa ya sarqafe su yana dubansu.
Wani namijin damisa take hange......a tsaye a kafe kamar gini ko zanen daya tsaru daga hannun qwararrun masu zane,masana kan yadda zaka sarrafa alqalaminka.
Sanda ta qifta ido a karo na biyu tana son sake tantancewa,sai SHEIKH MUHAMMAD HAISAM ya fito mata sak da dukka kamanninsa,qifta ido na biyu da tayi kuma tana bude idanun sai taga ya fara motsi yana takowa a hankali zuwa inda suke tsaye,tabbacin ba ZANE ko GINI bane.....shine din dai. Shine dindai jinin IBRAHEEEM da YUNNUS JALLATA.....gadon sarauta ta kowanne fani na uwa da uba. Kalaman mammina na ASALI sune abinda ke masa kururuwa a kunnensa.
"WAYE UBANSA?" maganar da tayi tsaiwar mashi cikin tsakiyar zuciyarsa.
"Ki tsaya ki zuzzurfan tunani biftu.....nidai ina kar......" Maganan ya tsaya mata cak a maqoshi saboda inuwarsa data hanga,wanda cikin qiftawa da bismillah kuma ya bayyana gaba dayansa. Abinda ya haifar mata da wata irin firgita,wata irin firgitar da tunda take tsahon rayuwarta bata taba jin irinta ba,don kuwa cikin qasa da second goma da yayi na kafeta da idanuwan nan nasa dake da tsananin KAIFI gumi ya jiqe mata fuskar tamkar wadda ta daura alwala.
Cikin nutsuwar nan tasa yake takowa zuwa gaban akhnan,wani irin taku cikin QASAITA da GINSHIRA. Cak ya tsaya a gabanta yana zube idanunsa cikin tsakiyar nata. Wani abu ya tsarga mata,wani irin abu mai kaifin gaske.....wani irin abu me tsananin nauyi da ratsa jini har zuwa b'argo.
"Ya isa......ya isa" Ya maimaita sau biyu yana lumshe idanunsa gami da budesu a tare,idanunsa fes akan fuskar Akhan da wani irin kusanci don tazarar daya rage tsakaninsu qilan yaro me qananun shekaru ne kawai zai iya shiga ya cike gap din.
Hannu ya miqa a hankali ba tare daya dauke idanunsa daga kanta ba,ya riqe jelar dogon gashinta masu kauri guda biyu da aka kitsata ta zubo a gefe da gefen fuskarta yana maida mata su baya,don kadan ya rage su saukar fuskar Aaroon dake baccinsa abinsa..
Still idanunsan nan suna kan fuskar Akhan din,ya sanya hannu ya karbe Aaron daga hannunta,sai ta samu kanta da sakar masa yaron. Wannan shine maslaharta,koda bata bata Aaroon bama taji jikinta gaba daya ya gama mutuwa,hasalima rawa takeji ya soma mata,wannan kallon tana jin kamar dafi ya tattara ya zuba mata a jikinta gaba daya. Baice komai ba,ya zura hannunsa ta gefanta ya kamo lallausan tafin hannunta ya runtse cikin nata,sannan ya fara takawa a nutse ta gaban fuskar mammina.
"Abu mafi kyau ga kowanne dan adam shine......ya gina kansa fiye da yadda sunan uba zai ginashi.......sunan uba yana daga mutum ne idan ya dace dashi......amma mutunci.....mutum ne yake ginawa kansa shi......idan wani yana iqirarin baisan mahaifinka ba.....ba hakan yana nufin babu shi ba".
Wani hazo hazo ta fara gani,kamar jiri yana shirin kayar da ita. Babu shiri ta soma lalubar duk abinda ke kusa da ita,cikin taimakon Allah ta samu nasarar damqe daya daga cikin bishiyoyin da aka yiwa gurin ado dasu,wannan ya taimaka mata gurin tsaiwa saman qafafunta.
Wani irin mamaki.....zallar mamaki ne kawa ke yawo cikin kwanyar akhnan. Maganganunsa dake nuna zallar jarumta.....sanin ciwon kai da kuma sanin darajar kai din suke bata mamaki.
Ya iya maida amsa.....ya iya bada amsa a taqaitattun kalaman da amsar zata kai maka ko ina. Hannunta.....hannunta dake cikin nasa shine wani hanya guda daya da take aike kasala da mutuwar jiki zuwa kowanne sashe na jikinta. Gumin da tafin hannun nata ya fara yi kuma.......yadda tafin hannun nata ya nutse tsakiyar nasa saita dinga jinsa kamar ba'a jikinta ba.
Cak ya tsaya da ita,dab da hanyar qarshe da zata fiddasu zuwa farfajiyar. Yatsunsa kawai ya murza,daya daga cikin hadiman dake qoqarin kwashe busassun ganyen dake tsakanin flowers din ta dago.kai da hanzari. Mutuwar tsaye tayi.....yadda ya qware wajen bada umarni?. Da murza yatsa kawai duk wani bawa duk wami hadimi yana iya fahimtar saqon da yakeson isarwa?.
Aaroon ya saka mata a tafin hannuwanta,da qasaitacciyar muryar nan tasa idanunsa suna kallon wani guri ya mata magana da kalaman da basu da tsayi sam.
"Ki kaiwa mamansa shi.....ki aiko da birra" Cikin girmamawa ta rungume Aaroon,da sassarfa kuma ta fara takawa tana barin gurin.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Ita dashi din gaba dayansu da kallo suka bita harta bacewa gurin. Shuru ya ratsa gurin,baka jin komai sai kukan tsintsaye dake yin masauki saman tarin bishiyoyin daka gurin.
Ba iya wannan kadai akhnan ke iya ji ba,tana iya jin fitar numfashinta dama bugun zuciyarta gaba daya a lokaci guda,kafin husky voice dinsa ta ratsa shurun da wani irin kakkaifar tambaya.
"Wa ya baki damar fitowa a haka?". Cak tambayar ta tsaya cikin iska da wani irin yanayi,wani irin yanayi me ban mamaki.....wani irin mamakin daya sanyata dole ya tilastata daga idanunta ta zube akan fuskarsa ba.
Bata iya ganin fuskarsa,don ya bata baya,amma tana iya ganin kadan daga cikin sumarsa me santsi da bata samu shigewa cikin nadin turkudin kansa ba. Izzar tadan motsa mata.......cakude da mamakin yadda bata masa KWARJINI ne kaman kowa?,har yake iya bata umarni kai tsaye gami da qalubalantarta?.
"Banga aibun shigata ba......"
"Kece bakiga aibun shigarki ba" Ya furta da wani yanayi na fusata yana kuma juyowa zuwa gareta da wani irin zafin nama.
Juyowar tazo mata a bazata,juyowar ta bata wani irin ajiyayyen tsoro daya sanya tayi baya da sauri ba tare data shirya ba. Idanunta cikin nasa tana hangen wani abu......fushi ne?,baiyi.kama da fushi completely,wani abune dake da tsananun zurfi da kuma kaifi daya taso tun daga zuciya.
Step biyu ya tako zuwa gaba......sai ta janye baya da sauri ganin yadda ta rage gap din dake tsakaninsu. A hankali yake ajiye takunsa duk inda ta dauke nata,sannu a hankali yake sake matsarta yana kuma cike duk wani tazara data bayar a tsakaninsu,sai jinta tayi ta hade da babbar bishiyar dake bayanta.
Da sauri ta waiwaya tana duban bayanta,ba wani sauran taku daya rage mata da zatayi,ta maido dubanta kansa,sai taga still matsota yake sakeyi. Idanun nan dake zagaye tsakiyar nadin kansa da habarsa.....idanun nan dake kasheta alhali da ranta da numfashinta. Wani irin abu me kama da fushi take hanga mamaye da fuskarsa duk da bata iya ganin fuskar tasa gaba daya.
Duk wani taku qwaya daya da zaiyi sai taji kamar numfashinta zai dauke....duk wani taku qwaya daya da zaiyi sai taji girman kusancinsa har tsakiyar tsokar zuciyarta,zuciyarta ta qara gudu,qirjinta ya soma dagawa a hankali da wani kalar tsoro ganin inches ne da basu fi biyu suka rage a tsakaninsu ba.
Taku daya ya rage yayi filling gap din.....taku daya bame nauyi ba,don haka ta runtse idanunta a hankali,tsoronta yana ninkuwa,tsoron daya sanya qirjinta dagawa sosai saboda kokawar jawo numfashinta da fidda she da takeyi saboda yadda takejin kamar qofofin shaqar iskarta sunyi mata kadan.
Tana iya jinsa cikin jikinta,tana iya jinsa sanda ya raba qafarsa tsakanin nata qafafun,tana iya jin wannan qamshin.....tana iya jin wani irin dumi dake tsakanin cinyoyinsa suka ratsa nata suna kuma aike mata da wani irin shock zuwa kowanne sashe na jikinta,kafin a hankali hannunsa saman qugunta.
Idanunsa ya ware sosai saman matsoraciyar fuskarta data sake wani kyau saboda yadda tsoro ya bayyana qarara saman fuskartata. Karon farko da yaga tsoro shimfide akan wannan fuskar ma'abociyar kafiya da kuma taurin kai. Sam bada niyyar wanzar da irin wannan kusancin tsakaninsu ba ya waiwayo,saidai wani irin qyalli daya hanga cikin idanunta.....da kuma matsoraciyar fuskarta sai ya tuna masa da wancan dare. Yadda fuskarta take cikin screen......yadda dukiyar fulaninta take cikin rigar baccin data kwanta a fatarta sosai.......take wani abu ya d'arsu cikin zuciyarsa. Yanason yaga da gaske abinda ya gani a na'urar shine a zahiri?..dagawar da numfashinta yakeyi shi ya sabbaba dagawar qirjinta,abun sai ya zame masa tamkar wata tsokana ne.