Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 76

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 76

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 76: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 76. Cak ya tsaya yana dubansu,yadda suke dagawa sama da…

3,301 words

Cak ya tsaya yana dubansu,yadda suke dagawa sama da qasa a hankali da bugawar zuciyarta da yana iya ganisa sosai. Zai iya irga sakanni nawa yake bugawa tsakiyar qirjin nata,duk da yanajin wani abu me nauyi yana qarawa fitar nasa numfashin shima nauyi amma ya tantance zuciyarta a lokacin bata bugawa daidai.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 130*

A hankali yayi sama da idanunsa......kafadunta da suka dan bayyana kadan wadanda sukayi wani irin kyau da siririyar silver sarqar data zauna a dogon wuyanta. Ya lumshe idanunsa a hankali yana tuna wani baitin mawaqin balarabe daya qware wajen siffanta mata.

Yasha karanta waqar....yasha maimaitata da cin karo da ita a litattafai da dama......amma a yau yaga zahirin ainihin maganar mawaqin ido biyu. Idanunsa suka sake sauka akan lips dinta,take yaji maqogoronsa ya bushe har zuwa saman nasa lips din,sai yakai harshensa a hankali yana lashe labban nasa kafin ya turasu ya maidasu cikin bakinsa gudun samun kuskure. Yadda jikinta ke rawa sai yaji kamar nasa jikin yana dab da fara rawan shima.....saidai faruwar hakan yana nufin abubuwa da dama.....cikin taimakon Allah wannan zuciyar tasa ta maidashi hayyacinsa. Tunawa yayi inda ta fita haka,maza nawa ne zasu kalleta?. Wuyanta.....lips dinta.....qirjinta.......da dogon gashin da ya maidashi baya a dazu.

Numfashinsa yaji yana sake nauyi da zuciyarsa ta tuna masa da haka,sai yaji kaman shima numfashin wahalar fita yake neman yi masa. Shuru ya wani ratsa a tsakaninsu,saidai wannan shurun bai dauke bugun zuciyar kowannensu ba......a hakan zuciyarta ke raya mata ta bude idanunta.....ta cire wannan tsoron......ta gaya masa ya matsa daga gareta......idan batayi hakan ba zuciyarta na gaya mata bata da jarumtar ci gaba da daukan wannan yanayin.....

A hankali kamar me ganin wani abu ta fara ware manyan blue eyes dinta. Ta zubesu a kansa,saidai ta gagara budesu gaba daya a kansa,dole ta zabi maidasu ta lumshesu tana ci gaba da kokawar yadda numfashinta zaici gaba.

Kai ya girgiza yana ja baya a hankali bayan da kunnuwansa suka jiye masa alamun taku nesa kadan daga inda suke.

Besan wanne kalar kishi gareshi ba,saidai shi kansa yasan me tarin yawa ne. Kalar kishin daya sanya hatta dasu Aanani rumaisa da nanay kanta kishinsu yake. Ya hana musu drivers maza......ya hana musu bayi maza......duk wata harkarsu da maza zasu shiga ya soketa.

"Gani Allah ya taimakeka" Akhnan da hat yanzu bata farfado daga suman da tayi ba ta fada tana duban haisam. Baya yaja kadan ya bata umarnin da ko akhnan bataji me yace mata ba,saidai qasa da minti uku sai gata ta fito da abinda yace tana miqa masa.

Karba yayi yana warwarewa. Babbar lafaya ce fara qal me wani irin taushi da daukar idanu.

"Get on your feet" Ya fadi kafin kuma ya koma ya gaya mata da france.

"Tenez-vous debout" .

Kamar wata statue haka tayi tsaye,yana kewayeta a hankali har ya kammala nade adonta tsaf cikin fara lafayar. Gabanta ya zagayo yana dauke da ragowar sashenta,ya tsaya sosai da tazarar da dukka dukka bame nisa ba. Hannunsa dukka biyu ya saka ya dorata a saman kanta,ya qarasa rufe wadannan dogayen gashin nata.

Wani sabon salo kyan da tayi ya dauka....wani yanayi na daban ba irin na adon dazu ba.

Taku biyu yayi baya,sannan ya juya bayansa a hankali. Har yanzun bai gamsu ba.....har yanzun yanajin kamar akwai sauran abinda bai rufe ba,kamar ma be rufe komai ba. Bai daina ganin wani yanayi me fusgar hankali yana tashi tattare da ita ba.

Wannan karon kafada da kafada suka jero ita dashi. Jerowar da taja hankalin dukkan wanda ke gurin.

"Ya subhanallah" Aisa ta fada da wani irin yanayi. A yau tana jin yadda suka tafi da imaninta,a yau tana jin an gama tashin kanta gaba daya.

Zata iya cewa a duniyarta bata taba ganin couples da sukayi matching iya matching ba irin muhammad da khadeeja din.......kasa dauke idanunta tayi daga kansu,tana jin ko taku days nasu bataso tayi missing.

"Innalillahi.....aisa.....kalli takunsu fa......hatta qafarsu tare suke ajiyeta da dagata" Shehnaz da take qare musu kallo ta video din data fara musu bayan ta zuge window din motar ta fadi a matuqar gigice da yadda suka fita kamar wasu taurari.

"Na gani shehnaz.....na gani wallahi" Aisa ta fadi tana jin yau ko ita me iya biyewa shehnaz ce akan batun akhnan da haisam.

A cikin jikinsa yaji dukkanin adadin idanun da suke kansu....cikin idanun kuwa harda idanun mammina........idanun da suka cika da fusata,idanun da a yau takejin duk wani juriya tasu ta qare

"Muddin kika zabeshi....muddin kika yarda kyanshi ya rudeki kika fada soyayyarsa.......lallai a sannan zakisan me ake kira da ainihin AZABAR RAYUWA.....mission dina zai sauya a kanki.....zaki gaje kujerar SAFEENA da kyau,daga dukkan nau'in kalar wulaqantacciyar rayuwar dana jefata. Ta shayar dake a sanda take cikin HAUKA.....zai zama kuskure ko laifi idan rahoton yazo da bayanin KIN TSOTSI KALAR HAUKAR NE A NONON DA KIKA SHA NATA?" ta fadi can qasan ranta idanunta zube fes a kansu,tana kallom yadda suke takawa da salon tafiya daya......tana kallon sanda ya sanya hannu cikin wani girmamawa me nauyi data hanga daga dukkan motsinss,daga wani dogon nazari da tsinkayen data tabbatar ko akhnan din bata hangeshi ba,sannan ya zagaya da qasaitacciyar tafiyarsa me cike da shan qamshi izza da ginshira zuwa daya side din shima ya shige.

"Bazan bari hakan ta faru ba.....na kasa gano komai a tare dakai.....amma tabbas jikina da hasashena sun bani amannar KAI DIN JININ IBRAHEEM da KHADEEJA ne" Ta fada still a ranta tana dukan qafen veranda da hannunta data dunqule tana kuma cizon lips dinta na qasa.

Wani irin shuru ne ya ratsa cikin motar,kamar ba kowa a cikinta. Idanuwanta na gefan window tana kallon titunan da suke wucewa da matsakaicin gudu. Shimfidaddu tituna kuma lafiyayyu wadanda aka samar dasu a mulkin mahaifinta sultane muhammad hammud. Bawai titunan kawai take kalla ba,ba kuma wai don bata sansu ba.....a'ah. Wani abune lullube da zuciyarta me matuqar nauyi da take jin nauyin har saman qirjinta. Yatsunta take murzawa a Hankali,har yanzu tana jin kamar hannunsa yana cikin nata. Har yanxu tana jin zaman zara zaran yatsunnan nasa cikin nata,har yanzu wannan bugun zuciyar......fitar numfashin dama komai nata bai koma daidai ba.

Batasan wanne irin nau'in mutum bane shi da yake mata kwarjini har irin haka. Rauni......rauni takeji sosai a zuciyarta,wannan jarumtar tana ji tana zagwanyewa a jikinta a duk sanda yayi kusa da ita. Wannan jarumtar tana jin tana yin nisa da ita......tana jin tana nesa da zuciyar ta dama gangar jikinta gaba daya.

Tun suna dab da isa gurin abubuwa da tsarin suka fara daukan hankalin haisam. Karo na farko da zaiga biki na al'ada irin wannan a tsakiyar sahara. Wani abu da bai taba sanin dashi ba. Duk irin sonshi da zuwa yawon bude idanu,bincike akan nature da gurare masu dadin zama da wanzar da nishadi bai taba zuwa takan niger ba ballantana al'adunsu. Wata qesa ce da yake kallonta nesa dasu sosai. Ko sanda ya fara bincike a kanta.....bincikensa ya tsaya ne akan zargin wanzuwar me laifinsu da suke tuhuma SAMUUD.

A hankali motocin masu manyan tayoyi suka fara keta cikin saharar. Wata nutsatsiyar tafiya data sanya haisam bude manyan idanunsa a hankali yana duban yadda suke keta yashi. Daga nesansu sai yaga kaman wani tsuburin amma da sun kusanci gurin sai ya fahimci tudun yashi ne kawai.

"Innafi khalqissamawaati wal'ardi wakhtilafil laili wannahari la'ayatil li'ulil albab" Ayar tazo masa cikin kansa. Tabbas a iya halittar sama da qasa kawai ya ishi bawa imani.....ya ishi me rabo ya fahimci da gaske Allahn Allahn ne. Wata halittar tafi gaban abun halitta ya tsarata ko ya qirqireta.....ka kalli guri shimfide da wani irin lallausan rairayi,haka kawai aka halicci gurin,ba deboshi akayi aka zuba ba.

A hankali takejin wani siririn nishadi yana ratsa mata zuciya. Jinin nan na Tuareg jinin nan na ABZINAWA jinin BUZAYE yana motsa mata. Tana tsananin son festival din,yana daya daga cikin abinda ke bata sakewa nishadi da walwalar da batayi ba a baya.

Suna hango gurin amma tun daga nesa security ne a zube tako ina. Riqe da manya bindigu da wadanda ke nesa kadan da abubuwan bada kariya da kayan hangen nesa. Akwai tsaro sosai.....saidai qarin samun tsaron ya ta'allaqa da wanzuwar haisam da shawarwarin daya bayar,ya kuma gutsira musu idea 'yar kadan wadda ba zata bankada WAYESHI ba daga cikin tarin hanyoyi da dabarun bada tsaro na hukumar qwararru kuma gogaggu kan binciken sirri da kuma bada tsaro.

A nutse dukka jerin gwanon motocin masarautar agadez suka karkata kadan suna isa inda aka tanada domin ajiyar motoci. Kyakkyawar matashiyar minister din itama yau da kanta tana tsaye sanye da tufafinsu na al'ada cikin tsaro na guards dinta da sauran ma'aikatanta na kusa. A yau itama ta fita a matsayin cikakkiyar BUZUWA ta fita sak! Cikin shiga da kamanni na al'adar festival de l'Aîr,ta zabi zuwa da kanta ta marabci sheikh muhammad da princess akhnan hammud. Tunda tabar masarautar agadez couples din suke fado mata,lokaci lokaci kawai saita saki murmushi. Wani irin match da zazzafar soyayya take hango musu a gaba. Dukkaninsu bata hangen akwai wanda zai samu ya tsallakewa dan uwansa.

Tayi zaton zai bude murfin motar kaman yadda sama da motoci goma da sukazo dasu suka bude,sai taga driver din ya fita ya kuma rufesu cikin motar. Shuru ya wanzu,tana tuna abinda ya faru ranar taron makaranta,yauma yanason maimaita irin hakanne.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali taji zuciyarta tana motsawa,musamman data karkatar da kanta zuwa sashen da minister ke tsaye. Sunata wasa da dariya dasu aisa. Akwai sanayya da sabo sosai tsakaninsu da ita sama da yadda ita ta saba da ita,saidai tsananin kirkinta da kuma girmamawarta ga sultane ya sanya janta sosai a jiki.

Gaba daya gurin ya zama wata qaramar unguwa,jama'a ne masu yawa suketa kai kawo a gurin. Maza da mata,yara da manya harda tsofaffi da al'adar festival din take tsaye tsaf cikin jini ruhi da zukatansu.

Garin agadez yana daya daga cikin garuruwan da suka riqe al'adunsu da kyau sama da kowanne gari a niger,kama daga gine ginensu aurarrakinsu da sauransu,wannan ya sanya ya zama kamar wata cibiya ta gudanar da al'adu.

A nutse ya zaro wayarsa bayan ya sauke siririyar ajiyar zuciya. Yana jin ta yaya zata fita a haka?. Zagaye suke da maza muqarraban minister da sukazo tarbarsu,haka kawai yakeji zuciyarsa ta masa nauyi kadan,saiya rubuta gajeran rubutaccen saqo ya aikewa beeno.

A tsakanin tazarar dake tsakaninsu ya ajiye wayar a hankali. Wanda da ajiye wayar da soma janyewar maza ba'ayi minti biyar ba.

Ta glass din gaban motar ya hangi tahowar minister din,sai ya bude murfin motar,tana zuwa ta qarasa budeshi ta shigo.

Da cikakkiyar sallama,fuskarta shimfide da murmushi,cikin harshen France ta dubi haisam bayan ta dauke dubanta daga kan akhnan.

"Je m'excuse,monsieur(i apologize sir)" Kadan ya murmusa yana gyara zaman agogon hannunsa a nutse.

"Le festival se passe bien? C'est super de te voir gérer tout ça(Managing the festival okay?,great to see you working the crowd)" Murmushi tayi a nutse tana dors hannunta saman na akhnan. Dukkaninsu sun mata kyau.....sun mata wani irin kyau daya sake sanyawa take jinsu har cikin ranta take kuma fatan kasancewarsu tare. Ta gyada kai da sauri.

"Alhamdulillah.....komai lafiya,muna matuqar godiya bisa gudunmawarka......anjima da yamma mr President zaizo,yace a miqa maka saqon gaisuwa da godiya dama masarauta gaba daya da suka bada aron mutum irinka,komai yasha banban da yadda muka saba gudanar dashi,wannan karon kowa yana jin abun zaifi armashi" Kai ya gyada a hankali.

"Naga sabon tsari......na tashin kiran sallah jikin na'aurori a duk sanda lokaci yayi" Minister ta fada abun yana burgeta tana duban idanun akhnan da murmushi.

"II est très sincère dans sa religion et c'est vraiment admirable(He's very sincere about his religion and that's really admirable).....ya gina mana masallacin tafi da gidanka na maza da mata a sansanin nan....wannan shine karon farko da muka fara tunanin yin haka......raye raye na al'ada ya kebe gurin da mazan zasuyi nasu daban mata ma haka......sai abun ya bani sha'awa sosai " Ta fada tana qanqance idanunta da wani murmushi na burgewa.

Idan har tace bataji wani RESPECT ya sauka a hankali saman zuciyarta ba tayi qarya.....kwatankwaci saukar qaramin tsuntsu saman bishiya. Ta karkata kanta a hankali ta saci kallonsa kafin ta dauke idanunta da sauri gudun kada ya kamata.

"Na karbi amanarta yallabai.....zan kula maka da ita in sha Allah" Minister ta fadi tana murmushi tana kuma sake riqe hannun akhnan cikin nata.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 131*

Wannan karon murmushinsa sai daya d'ara labbansa,ya sauka kadan zuwa saman fuskarsa. Bai kuma ce komai da ita ba,ya danna locked ne kawai qofofin sun bude,tana riqe da hannun akhnan din suka fice.

"Soyayyaaaaaaa.........Allah yabar soyayyaaaaaaa" Shehnaz ta fadi tana daga hannu sama da salon waqar nan ta sogha. Murmushi madame minister tayi tana nuna shehnaz da yatsa.

"Ba zaki canza ba shehnaz?". Juya idanunta tayi tana dariya.

"Soyayya kala kala ce.....soyayya iri iri ce,soyayyar maso wani cuta to kowa yaso me so nai" Dariya sosai dukkaninsu ta basu,banda akhnan data tamke fuska tana jifan shehnaz da harara. Hannun akhnan ta sake riqewa cikin nata.

"Ki rabu da ita....nasan yadda zamu hukuntata....bata iya tsere ba.....anjima shi zamu sakata a raqumi" Wani murmushi ya subucewa akhnan din,har cikin ranta.....har cikin ranta taji dadi sosai,ta dade bata hau raqumi ba.....har dawakanta ma kusan duka ta manta dasu saboda rudanin nan data shiga,amma a yau tana jin saita cike wannan gibin.

Kusan tun daga saukarsu hidima ake akwai da hada hada. Baqi daga kowanne sashe da nahiya na duniya. Turawa larabawa harda faransawa da sukafi yawa,china india dukka suna cikin qasashen da suke halartar festival din. Karbar baqi kawai akaci gaba dayi ta ko ina. Akwai VIP tent da shiyyarsu ta zama daban dana sauran al'umma. Tent ne da aka tsarasu harda bandakunansu a ciki,sannan akwai spare daban da aka yisu kamar qaramin parlor,saidai an qawatashi da carpet carpet da kuma lausasan kujerun zama na wucin gadi. Ac ne na tsaye cikin dukkanin VIP tent din da parlor din,an samar da yanayi me kyau da zai sanya kaji kamar kana gida. Ita karan kanta sai dataga banbanci me nisan tazara na gaske da minister ke fadin ya samar. Komai na wannan karon yasha banban dana ko yaushe. Komai a tsare,wani irin yanayi da zaka dinga jin kamar kwanaki ukun da za'ayi kada su qare.

Daya daga cikin parlor din suke zaune,da minister da sauran manyan baqi. Hira ake cikin sakewa da juna da qaunar juna,ba wani banbancin launi ko na yanki ko kuma qabila.

Duk da cewa daga nesa ne,kaeo na uku kenan da take iya ganin mutanen da yaketa magana dasu. Kai kawonsa tare da manyan baqi daga qasashen waje,qasashe daban daban yare daban daban. Ta kafeshi da idanu sanda suke musabaha da wani balarabe,bakinsa yake motsawa a hankali cikin fara'a da sakin fuska. Batasan me yasa yake janye tunaninta ba,batasan me yasa yake janye hankalinta ba. A duk sanda zai gilma ta gurin,sai taji kamar an fusgi hankalinta zuwa gurin.

A hankali ta sake daga idanunta tana kai dubanta zuwa inda yake tsaye. Wannan karon a gefan mutumin,matashiyar balarabiya ce,sanye da baqar abaya me sulbi sosai. Tayo rolling da mayafin abayar har kana iya ganin gashinta daya sauka a bayanta. Sake maida dubanta tayi fuskar mutumin,babu ko shakka dukkan alamu sun nuna mahaifinta ne. Hannunta cikin na mutumin ta kwantar da kanta a kafadarsa.

A nutse akhnan ta gyara zamanta,tana dora qafarta daya saman daya idanunta zube fes saman fuskar yarinyar da aqalla zasuyi sa'anni da ita. Direction na qwayar idanunta tabi kai tsaye kuma suka kaita fuskar haisam.

"Shi take kallo?,shi ta zubawa ido haka?" Taji wata murya can qasan zuciyarta tana tambayarta.

A hankali ta sake maida dubanta kan idanun yarinyar......da gaske haisam take kalla.....da gaske idanunta yana kanshi,har kamar ma bata qiftawa.

"Saboda me?" Muryar ta sake tambayar akhnan da wani irin yanayi daya disa mata wani abu me zafi saman zuciyarta. Haka kawai taji kamar zuciyarta tana tattarewa tana kuma matsewa a qirjinta da wani irin yanayi data fara jinsa tsakanin qirjin nata tafin hannunta da qafafunta. Taci gaba da raba kallonta a tsakaninsu,zuciyarta tana sake tsukewa guri guda,saidai abu daya daya bata mamaki,abu daya data iya gani ta kuma fahimta,ko sau daya haisam bai aza idanunsa a kanta ba.

Kanta ta girgiza a hankali,still hakan be mata ba,haka kawai takejin tsaiwar batayi mata ba. Me suke fadi masa haka sama da abinda sauran suke gaya masa?. Me suke fada masa haka da suka dade dashi sama da kowa?. A hankali ta waiwaya inda birra ke zaune daban. Birran kawai ta ware ta yiwa umarnin zama cikin nasu tent din. Hannu tasa ta kirata a hankali,tana jin kamar ana tunzurata,tana jin tana da buqatar sanin abinda suke tattaunawa akai. Da idanu ta yiwa birra nuni,duk da birran ta fahimta,duk da birran ta gane me uwar gijiyartata ke nufi amma abun sai ya mata banbarakwai,sai kuma ta miqe a hankali tana ficewa don cika umarnin uwagijiyarta.

Cikin rashin jin sukuni tun daga zuciyarta zuwa ruhinta ta sake aza idanunta a kanshi,still idon nasa yana kan mahaifin,still dai ko sau daya bai kalleta ba,amma haka kawai takejin wani abu yana ci gaba da matse zuciyarta.

Bayan idanun yarinyar dake kansa.....kamar daga can nesa yanaji a jikinsa akwai wani abu na daban. Wannan wani horo ne da suka samu da baiwa da yake da ita wadda ta shafi aikinsu. Miqawa muhseen hannu yayi sukayi musabaha,yanason kawo qarshen hirar don mutanen dake jiransa yawa ne dasu. Yana zame hannunsa daga nasa yarinyar ta miqa masa nata hannun tana murmushi.

Karon farko daya aza idanunsa a kanta tsahon tsaiwarta.

"Tanason ku samu fahimtar juna da kusanci sosai" Mahaifin nata ya fada yana murmushi gami da duban fuskar haisam. Kadan ya jefi uban da murmushi,ya fahimci irin 'yan modern Muslim ne,a tsaiwar da sukayi na mintuna ya tabbatar duk yadda zai masa bayani game da komai bazai fahimta ba,don haka yayi taku biyu baya still yana duban uban

"Na gode qwarai sayyed muhseen" Cikij sanyin jiki yarinyar ta sauke hannunta qasa,sai uban ya kama hannun ya riqe cikin nasa cikin rashin jin dadin yadda haisam din yayi ya qiriqiri murmushi shima yana masa godiya.

Sanda suka taka suna barin gurin saita sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,abun mamaki a hankali taji qirjinta yana sassauta,still dai ta kasa dauke idanunta daga kanshi,yana tsaye sosai cikin rairayin saharar......BUZU sak,sai taga ya zaro wayarsa daga aljihunsa yana dannawa da wani irin qwarewar da zata gaya maka gwani ne gurin sarrafa na'ura.

Sassanyan murmushi madame agaichaata ta sake. Ita days ce ta lura da komai,ita kadai ce akayi komai saman idanunta. Ta tabbatar inda shehnaz ta gani da zuwa yanzu ta cika tent din da karadinta da kuma tsokana.

Readers Also Read

More by Huguma