L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 77
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 77: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 77. "Ba wanda zai qwace miki shi.....yadda yake tsaye kafe…
3,367 words
"Ba wanda zai qwace miki shi.....yadda yake tsaye kafe cikin rairayin saharar agadez.....na rantse miki yanayinsa yamin kama da irinsa mazannan ne da idan suka fara so ba gudu ba ja da baya......yana da kyau dai kawai ki koyi yadda zaki adana zuciyarsa...... Ki killaceta,don na fahimci taki zuciyar itama kamar tana da muradinsa". Ta qarashe maganar can qasa,yadda b wanda zaiji me suke fada daga ita sai akhnan din. Bata tantance wanne yanayi taji game da maganan madame ba taji qarar shigowar saqo wayarta.
_Ki rage kallona madame princess.....ina da hadari fa ni kaina na sani_
Wani irin bugawa zuciyarta tayi,ta zubawa saqon idanu sosai tana sake karantashu. Da sauri ta daga kanta zuwa inda yake tsaye a dazun saboda hasashen da zuciyarta tayi mata. Take idanunta ya manne cikin nasa. Ta tsakanin wannan rawanin.....wannan nadin dake qarawa idanunsa wani irin kyau da kwarjini. Girarsa dukka biyin ya dage mata,bai kuma barta tayi tunani na biyu ba ya juya yana takawa a nutse yana barin gurin.
Da wata irin kasala ta janye idanunta da sauri,ji take kamar zata narke a gurin,wai me yasa?,me yasa bata iya kaucewa kallonsa?,me yasa muddin yana guri saita kalleshi?.
A kansa ta fara sanin NACIN KALLO wata dabi'a ce data tsana.....wata dabi'a data saka ta sanya aka hukunta mata mutane da yawa tsakanin agadez da Niamey,ta tsani a yawaita kallonta,ta sani mutum me KALLO,amma ya akayi a kansa shi kadai!....a kansa SHI DAYA TAK! take neman jarabtuwa da wannan dabi'ar?.
"Bazan bari haka ta faru ba" Ta gayawa kanta qasa qasa tana tuhumar kanta da kanta. Tana jin murmushi madame agaichaata......amma kuma kunya da nauyi sun hanata motsi.
*S* ake narkewa tayi gaba daya cikin mazaunin sahun farko na manyan baqin da aka tanada sanda ake gudanar da bikin bude fara festival din.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Ba ita kadai ba kawai.....hatta da manyan baqin dake zazzaune a mazauninsu.....baqin da suka fito daga qasar faransa gaba daya ya tashi hankulansu da yadda yake sarrafa french akan harshensa. Yadda yake gabatar da jawabinsa cikin wata irin tarin nutsuwa,nutsuwar data dauki hankulan daruruwan mutane dake gurin,da miliyoyin mutane dake iya kalla daga akwatin talbijin dinsu daga gida ciki kuwa harda mammina da wani mummunan ciwon kai ya hanata zuwa ko ina.
Nutsuwar dake cikin bayanin ya sanya shuru ya wanzu a ilahirin gurin gaba daya. Murmushi kawai mademe minister ke saki,tana jin gaba daya an tashi kanta.
Duk wani qwarewa da take taqama dashi.....duk wani tutiya da take dashi akan yaren a yau akhnan tana jinta kamar 'yar koyo.....kamar me gwagwarmayar son iya yaren bawai yaren qasarta bane. Wasu kalmomi da wasu jimlolin yadda yake fadinsu kamar a duniya bai taba sanin wani yare ba daban bayan France.
Ta lumshe ido a hankali tana jin yadda yake gauraya jawabansa da ayoyin qur'ani. Lokacin da yake karanto ayar da cikakkiyar qari'ar nan tasa......cikin microphone din daya gaurayr nisan saharar da tafiya me tsayi sai da taji tsigar jikinta ya tashi.
"Mene nasa naqasun?,meye nasa aibun?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta. Duk wani motsi da tayi duk wani tunani da zai fado mata tana ganin lokacin da zaiji kunya yazo sai ya juye zuwa wani qarin tarin girmamawar daga mutanen ma da basusan wayeshi ba.
Sanda ta bude idanunta sai suka sauka kan yarinyar dazu dake zaune rukunin kujerun dake facing nasu. Ta zuba mata idanu sosai tana kallon yadda take nadar video din haisam din a babbar iPhones din dake hannunta. Wani abu taji ya zarta ta maqogoronta,hoto na biyu sai ya sake dauko mata wata budurwar ta daban daga bayanta da itama ta saita tata wayar. A hankali ta dinga bin fuskokin matan da kallo,sai taga fiye da rabin kyawawan 'yammatan buzayen dake gurin Idsnunsu da hankulansu dari bisa dari yana kanshi.
Wani abu taji ya tsaya cak a kwanyarta,daidai sanda shima ya dakata cak da bayanin da yakeyi,yayin da kiran salla ya mamaye gurin gaba daya.
Yadda yayi shuru haka kowa yayi shuru,kowa yana sauraren kiran sallar dake tashi cikin wata kwantaciyyar murya. Wani irin nutsuwa da haske ya mamayi musulmin gurin,manyan baqi dake gurin musulman cikinsu wani irin nutsuwa ta sake shigarsu kaman yadda tsarin ya burgesu.
Qasa qasa yake karanta addu'ar bayan kammala sauraren kiran sallah,baka jin abinda yake fadi tar amma kadan kadan muryarsa tana motsawa ta mic din.
"Allahumma rabba hazihid da'awatittaammah.....wassalatil qa'imah.......aati muhammadanil waseelata wal fadeelah,waddaraja'tur rafee'ah......waba'ashullahumma maqaman mahmudanillazi wa'adtah......innaka la tukliful mi'ad" Dukka akhnan taji addu'ar sosai cikin kunnuwanta,tamkar yayita ne a bayyane,kamar ya furta da murya me qarfi da kowa zai iya ji.
(Manzan Allah da kansa yace mu dinga wannan addu'ar......yace mu roqa masa Allah,annabi da kansa yace ku roqamin Allah maqaman mahmuda.....karki xama shugabar marowata mana....ma'aiki ya mana gatan da duk duniya daga farkonta har qarshenta ba wanda yayi mana,daure ki nuna halasci ko yaya a duk sanda kikaji kiran sallah idan an gama kiyi wannan addu'ar,sai kuma ki biyo baya da taki addu'o'in biyan buqatar,saboda lokaci ne na amsa addu'a,Allah ya qara mana soyayyar shugaba ya sadamu dashi S A W,kar a manta har yara a koya musu 🙏🏽).
A gurguje ya qarasa kammala jawabansa saboda qaratowar lokacin sallah,ya rufe da gajerun addu'o'i masu ma'ana.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 132*
Duban birra takeyi sanda take zura safar hannunta,ta shirya tsaf cikin wata doguwar rigar data dace zatayi daidai da tsarin tseren. Ta batad da duk wani shape nata,kamar yadda ta boye ainihin kamanninta. Bata zato ko tunanin a tanadin shigar da tayi akwai wanda zai shaidata da sauqi.
"Kaman yadda na gaya miki dazu.....'yar qasar Morocco ce,kuma ta qware wajen sukuwar dawakai a qasarsu,hasalima idan kika dubata a Instagram da TikTok duka an santa,an shirya tseren ke da ita kamar yadda kika buqata,an kuma boye sunankin kamar yadda kikace an shaidawa madame hakan.......na samu dauko wayartata" Kai akhnan ke gyadawa a hankali,jinin SARAUTA yana tafasa cikin jinin ta.
Tun daga ranar da abun ya faru a hippodrome daya ja mata matsaloli da yawa,bata sake hawa doki ba koda kuwa da nishadi ne,amma a yau ta shirya hawa saboda abubuwa da dama. Daya daga ciki yarinyar.....yarinyar me suna yumna. Tanaso ta nuna mata qasarta ta shigo,tanaso kuma taga iyakarta.
"Bana buqatar wayarta,kawai duk wani video da yake kai nakeso ta rasashi".
"Na wayoyin sauran 'yammatan fa?" Taji muryar shehnaz tana fadi. A nutse ta waiwaya tana dubansu,dukkansu sun sake shiga akasin ta dazu a tent dinsu da yake daban da nata. Idanu ta zubawa shehnaz.....amma da yake 'yan miskilancin suna kusa saita dauke kai taqi tanka mata,ta jawo qaramin hijabin da zata fara dorawa saman kanta don ya sake boye fuskarta da tudun gashinta kafin ta saka medium din. Shigar black tayi gaba daya tun daga takalman qafarta har tufafin jikinta.
Idanun aisa a kanta sanda take zama gefen wata lallausar kujera,tsarin dakin kuma yana burgeta sosai.
"Shirinki fa kamar na masu tseren dokin nan biftu" Aisa ta fadi. Taji aisa din tsaf,amma sai tayi banza da ita,batajin akwai wanda zai dakatar da ita,don haka ba buqatar shawararsu takeyi ba.
"Akhnan.....karki fara inde hakan kike shirin yi" Aisa ta sake fadi idanunta akan akhnan din. Still bata kulata ba sai data kammala gaba daya sannan ta juyo ta kalleta.
"Na roqeki....karki bata bakinki.....na yau ne kawai aisa....komai an hanani.....komai ban samu yadda nakeso ba.....hawa dokinma sai a hanani?,ba don kaina zan hau ba.....Saboda qasata ne" Tana kaiwa nan tayi gaba birra na biye da ita. Duban aisa dake zaune shehnaz tayi. Tana tsoron doki sosai,wani lokaci gwara mata raqumi a kansa,tsaf zata hau ta sarrafashi,saidai hakan kuma bai hanata sha'awar dokin ba da kuma yadda akhnan ta qware wajen sarrafashi. Idan taga akhnan na sukuwa tana bata lokaci sosai wajen zama kallonta,wanda idan itace ko yaya za'ayi da ita ba zata hau ba..
"Kizo muje.....gaba kadan da nan za'ayi,awa daya ne an tashi zuwa da rabi saboda sallar magrib" Dubanta aisa tayi.
"Ke kam ma ko a jikinki.... Kina zaton ta shaidawa mijinta?"
"Zata fara hawa ne bata gaya masa ba?" Ta fadi tana waro idanunta waje. Shuru aisa tayi,ta sani inde shagala ce shehnaz tana kan gaba,bata bakinta kawai zatayi wajen fahimtar da shehnaz.
"Anjima da daddare zaki rakani zan sake siyan turkud'i" Aisa ta fada tana miqewa.
"Dazun ban samu shiga kasuwar ba,duk da wannan karon naga itama na canza tsarin saida kayyayakin al'adun" Dubanta shehnaz tayi
"Tarhanine zaizo anjima kin sani?kinsan kuma yadda nake mutuwar son waqoqinsa,banajin zan bar gurin har sai sanda aka tashi"
"Ko shekara zaki a gurin ki rakani na fara siyayyata tukunna,saboda zan koma Niamey ne ranar litinin da safe.....ya kamata shehnaz ki saki komai ki dawo muyi gyaran nan tare,b'arna ce ba qarama na shehnaz,bakya gani?". Shuru ya ratsa tsakaninsu,shehnaz na kada kanta a hankali kafin tace.
"Na sani aisa....na sani,haka kawai aiki a qarqashin wadannan mutanen nakejin bai kwanta min a rai ba,kamar tafiyata zatafi zama alkhairi"
"Ba zaki tafi ba.....tare zamu gyara".
" Zanyi shawara da nannie" Ta abawa aisa amsa a taqaice ba kuma don tanajin zata iya komawar ba.
Duk da yanayinta da yadda wasa yayi mata yawa,amma wani lokaci tana da dogon nazari da tsinkaye.
★Kebantaccen guri ne da aka zuba duwatsu da kwalta sosai,tafiyar kilometers bame yawa ba. A kewaye yake yana da fadi da tsaho daidai yadda zai isa wasan tsere a nishadance.
THUNDER shi ta zaba......ta aika takanas daga gida aka dauko mata shi,dokin da takejinsa a ranta sosai.....dokin da bata da kamarsa a dawakanta. Bawai don ya fisu tsada bane.... Aah,hatta kyansa na dabanne,da kuma wanda ya mallaka mata shi kyauta wato SULTANE.
Dukkaninsu suna saman dawakansu,saidai akhnan din ba wani abu nata daya bayyana saboda hijabin dake jikinta. Yumna ta gyara gashinta da iska ke wasa dashi. Ta yaya matar dake lullube da hijabi haka tayi nasara a kanta?,nasara kawai take hangowa tattare da ita.
*T A M I M*
Ta gaban idanunsa suka wuce yana kallon inuwarsu dama wucewarsu gaba daya,wannan ya bashi daman motsawa da zummar shiga dakin,saidai yana daga qafarsa daya daga cikin masu bada tsaro a gurin ya iso bakin tent din. Tsaiwar mutumin a gurin da dadewar da yayi yana kai kawo a gurin ita ta bata masa lokaci. Yaci gaba da duqewa a gurin,wani irin gumi yana yanko masa.
Bai taba zaton samun cikas me girma har haka ba,don a iya saninsa da dukka festival din a shekarun da yayi a qasar,tsaron da ake bawa gurin baikai koda rabin haka ba,sai gashi a wannan karon......a wannan lokacin da yake da babbar buqata komai yana zuwa masa da wani irin wahala.
Numfashin gushewar tsoro ya sauke sanda yaji takunsa yana wucewa zuwa rukuni na gaba,cikin takun dudduqe da sanda ya dawo ta gaban tent din ya buda ya shige.
Qarewa dakin kallo ya yakeyi,yana duba area din da zata bashi sauqi da damar buya cikin kwanciyar hankali. Idanunsa suka fada saman kayanta data cire birra ta adanasu saman kyakkyawar luggage dinta ruwan gold,ya miqa hannu ya daukesu yana kaiwa hancinsa.
Sosai ya zuqi daddadan qamshin da suturar tata me laushi da santsi take fitarwa. Yaji wani abu ya motsa masa,qarin qaimi da qarfin mallakarta da dukkan qarfinsa. Wani murmushi ya qwace masa,wanda banda yanayin da yake ciki dariya zai saki,nishadi ya samu sosai,musamman da kwanyarsa ke gaya masa wannan qamshin ya kusa zama mallakinsa na har abada.
Zata bace bat daga DUNIYAR da aka santa......zai tafi da ita dangin mahaifiyarsa can wani qauye da basa rayuwa da baqi. Qauye ne da duk baqon daya shigo sunansa gawa. Tun daga sanda aka taba cinsu da yaqi,abinda yayi silar kama mahaifiyarsa aka fito da ita zuwa wata masarutar a matsayin baiwa,har aka samu cikinsa aka haifoshi,bata sake komawa garinsu ba saida wani fada ya harqe a masarautar da suka ribatota din,ta samu ta falle zuwa qauyensu,tun daga sannan suka saka tsaro me qarfi da doka akan yankinsu,don haka yasu yasu suke rayuwa,ba kowa ma yasan da zaman wata qabila a gurin ba.
Kayan ya saki a nan inda suke......ya soma birkita kaya dake ajiye tsaf a dakin don samun muhimmin gurin buya.
"Commenc!(start!)" Me kula da tsarin fara tseren ya fadi da madaukakiyar murya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Sautin ya sauka a kunnen haisam,daidai sanda yake saukowa daga can sama inda yahau yana sake duba tabbacin tsaron gurin. Baya daukar komai da sauqi.....duk abinda aka dorashi a kanshi a matsayin amanar al'umma dukiya ko rai baya taba bari gangar jikinsa da ruhinsa su huta.
Tun daga nesan yadda ake sarrafa dokin ya dauki hankalinsa......tun daga nesa yake iya hangen banbanci qarara daga mahayan dokunan guda biyu. Yana iya gane fuskar dayar,yana iya gane wacece......saidai dayar dake sanye da baqar sutura wadda take neman yin wasan kura da yumna itace wadda tafi daukan hankalinsa.
Duk da yana nesa amma sai yake jin wani irin kusanci da sanayya me qarfi tsakaninsa da dayar.......tamkar ana fusgar hankalinsa zuwa kanta duk da irin gudun da take tsulawa akan dokin.
Cikin filin duka ba wanda yakejin muryar wani saboda karadi sowa ihu da fito da suka rude dashi. Gaba daya larabawan nan......mazansu da matansu hankalinsu ya tashi akan akhnan din. Sun jima basuga mace da bata tsoron sarrafa doki irinta ba,ako ta ina manyan wayoyi da cameras ne kawa suke haskawa.
Har cikin zuciyarta takejin wani sanyi da aminci sanda ta fara hangen tsoro da sarewa daga yumna. Murmushi take saki kawai ta qasan qyallen data yane fuskarta dashi. Wannan din ya tuna mata zamanin quruciya. Sanda take biftu dinta 'yar shekara goma sha daya zuwa sha biyu. A tsakaninsu yaran sarakuna,duk wadda take bata haushi,duk wadda take matsanta mata bata tashi koya mata hankali sai lokacin taro irin haka. Zata kadaki ne ta daga miki hankali har sai ta tabbatar kin horu,wannan ya sake bata qaimi ta bawa thunder qaimi da kyau......qaimin da batasan shine zai zama SILAR MATSALARTA BA......QAIMIN DA BATASAN SHINE ZAI XAMA SILAR RABUWARTA DASHI BA HAR ABADA.
Zuciyarsa yaji tayi wani motsi me qarfin gaske sanda yaji wani sashe can daga zuciyarsa yana gaya masa.
"Akhnan ce" Ya zuba mata idanu sanda take surfa wani irin gudu yana lissafa adadin tsahonta da fadinta daya dade da riqeshi cikin kansa. Tsaf lissafinsa ya bashi itane,ya sauke dubansa kuma dai akan dokin da take kai.
"Thunder?" Ya fadi a hankali yana jin ransa yana sake ninka baci. Dokin da yayi mata magana a kansa?,dokin daya gaya mata a taqaice yana buqatar kulawa ta lafiyar kwanyarsa?. Ya riga ya zabura tun a wancan ranar.......ya dauka zata bari ne ya samu cikakkaken hutu?.
"Ba zaki sake ba" Ya fada da wani irin coolness yana zaro wayarsa daga aljihun rigarsa duk da cewa zafi kawai zuciyarsa take masa.
"Ka gayawa kowanne dan jarida ya sauke camera dinsa.....wannan daukar kada ya fita daga nan inda aka yita......idan kuma wannan sukuwar ta qare......akwai sabon wasa da wani mutumin" Abinda ya fada kenan duka a dunqule a kuma jere,sannan ya sauke wayar yana katseta gami da furzar da iska me dumi daga bakinsa,sannan ya taka a hankali yana sauya akalarsa daga gurin.
Cikin qasa da minti talatin takai yumna ga faduwa. Ta cinye wasan da wani irin salo na cinyewa da kuma qwarewa.
Kowa nata ne.....kowa kuma da yazo baqonsu ne......amma haka kawai Madame minister takejin wani irin farinciki da qarin alfahari da akhnan din yana ratasata. Tabbas princess dinsu ta dabance......ta sake gasgata hakan bayan ta sake samun kusanci da ita na wanacan ranar da kuma yinin yau.
Duk labarin da ake a kanta.....duk zuzutatan da akeyi sai take ganin yayi kadan ma,kamar ma basu gama saninta bane shi yasa zantukansu suka tsaya a haka.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 133*
Lokacin da me sanarwa yake sanar da neman lokacinta don tsere na biyu saita tsaya cak,muryarsa tana ratsa dukka lasifiqar dake daure a gurin wadda take qarawa sautin qarfi.
Wancan lokacin shine abinda ya dawo mata a idanu..... Sak komai yake dawo mata kamar a wancan karon. Sanda baqin dokinsa yake takowa da wani irin qasaita da taku d'ai d'ai. Qafafunsa suna bada wani sauti kamar yana bata tabbacin wani abu ne.
Idanu ta zuba masa sosai kaman yadda ya zuba mata idanu cikin wani kwantaccen bacin rai.....yauma nannade da wannan rawanin......nannade cikin hiramin da yabad zagayen idanunsa a wancan lokacin.
Idanunta ta lumshe sannan ta budesu dukka lokaci guda a kansa. Wani irin buguwa zuciyarta takeyi kamar zata ballo qirjinta ta fado qasa. Kamar shine take gani ake dawo mata dashi.....kamar faifan video dinsa aka sanya mata take sake maimaicin kallo.
Sanda yazo ya daidaita tsaiwar sa kuda da nata don karbar umarnin fara tsaren sai taji kamar an zare mata dukka lakarta sakamakon qamshin nan.....wannan qamshin turaren da ba wata rana da zata fito ta fadi bata shaqeshi cikin rigarsa da bai sake bi ta kanta ba.
"Idan har shine,....inde ya tabbata shine......a nan gurinne kawai ya kamata ki rama.....kyakkyawar dama kika samu da zaki maida masa zazzafan martani,dama ce me kyau a tare dake khadeeja muhammad hammud.....ahalin abun ce ke.....ya kamata ki gwada masa BANBANCIn JIMIN SARAUTA da gama garin mutane" Taji wata zuciyar tana qarfafarta..
Iska ta sake zuqa me kyau ta fesar a hankali,tana jin qwarin gwiwarta dama komai nata yana dawowa. Qaimi ta bawa thunder sanda aka furta kalmar
"Start" Da faransanci,gurin ya cika da ihu da sowa,sowar dake sauka har tsakiyar zuciyarsa tana sake tunxurashi da bata masa rai,saidai kwance kwance yayi mata,ya barta da murna da karsashin ganin ta tsere masa.
Sau uku tana dubansa da wani irin kallo dake furta ma'anar.
"Ba tsararka bace ni" Da wani murmushi da ba kowa zai iya ganinsa ba cikin idanunta,saboda boyayyar fuskarta.
Ya bata dukkan nasara da dama a zagayen farko dana biyu,ya bata dama me kyau a zagaye na uku,kafin ya yiwa dokin wani irin qaimi da umarnin daya soma cilla wani irin gudu me daukan hankali.
Bata zata ba.......bata kuma taba kawowa ba. Nasara kawai take hanga dab da ita,saidai cikin mamaki ta jiyo taku me matuqar qarfi. Hankalinta yayi matuqar tashi sanda ta jishi dab da ita,abinda ranta ke gaya mata kawai ya taso ne don ya wuceta ya isa ga finished line. Saidai kuma sanda ya cimmata saiya saisaita gudun dokin.
Waiwayowa tayi a hankali,idanunta ya fada cikin nasa. Wani irin kallo yayi mata,kallon da ya zuba wani irin rudewa a zuciyarta gaba daya. Idonsa da kansa ya dauke daga kanta,sannan ya sake miqewa saman bayan dokin yana gigitashi kamar yadda umarnin ya hada harda thunder ya gigitasu gaba daya.
Fara ruda mata hankali yayi,ya fara kadata daga hagu zuwa dama,daga dama zuwa hagu da wani irin salo daya qarasa gigita nutsuwarta. Thunder taketa qoqarin controlling......amma kamar yadda ya faru a wancan ranar ya gigice mata. Cikin qasa da mintina goma sha biyar ya goge mata hadda gaba daya.....cikin qasa da mintina goma sha biyar ya sanyata ta manta cewa ITA GWANA CE,qasa da mintina goma sha biyar ya sanyata tayi loosing control na thunder kwata kwata tamkar bata taba sarrafashi ba. A gaban idanunta ya isa finished line,ya kuma cire tutar gurin ya dagata,abinda ya sake hautsina gurin da mabanbantan sautukan burgewa.