L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 78
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 78: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 78. Ba cinyeta da yayi a yanzu ne damuwarta ba,damuwarta a…
3,342 words
Ba cinyeta da yayi a yanzu ne damuwarta ba,damuwarta a yanzu shine irin gudun da dokin yakeyi da wani wajigata. Tana dab da isa inda haisam din ke tsaye.......amma sam bataga alamun thunder zai tsaya ba......ta tabbatar muddin ya wuce nan kuma zai nutsa da ita cikin sahara ne kai tsaye,batasan kuma inda zata tsaya ba....batasan inda zai dosa da ita ba. Bacewa bat.....bacewa ta har abada a cikin sahara ba wani baqon abu bane,abinda ya sake daga hankalinta kenan musamman da taji fit sun wuceshi sun kuma soma nausawa cikin saharar.
Hannu ya dagawa kowa yana bashi tabbacin aminci,sannan ya zunguri nasa dokin gami da juya akalarsa yabi bayansu.
Wani irin kaduwa zuciyarta kawai takeyi.....wani irin tashin hankali takeji sanda taga kai tsaye ya tunkari tulin lallausan yashin da zai.kaisu ga gangarawa,gangarawar data tabbatar idan ta yita Allah ne kadai yasan me zai faru da ita.
Kan nasa dokin ya miqe gami da ranqwafawa ya riqe linzamin da kyau,cikin wani irin sauri.....cikin wani irin karsashi ya kamo thunder.
Da hannu daya ya samu nasarar dauketa cak zuwa saman nasa dokin bayan ya samu nasarar dukan thunder da qafa,dukan daya sanyashi jan wata turjiya yayi haniniya yana juyawa,saidai bai sake takun gudu guda ba saboda wani abu da taji haisam din ya fadi cikin tsawa wanda batasan meye ba,sai dokin yaja ya tsaya cak,saidai kuma yana ci gaba da haniniya kamar idan aka bashi dama kuka zai saka.
Saman dokin suka koma suka zauna dabas ita dashi,yayi mata rumfa cikin yalwataccen qirjinsa saboda ajiyeta da yayi a gabansa,hannuwansa kuma suna riqe da linzamin dokin.
Baya taji ba shiri saboda miqewar da dokin yayi kamar zai zubar dasu,ta samu wata kyakkyawan mazauni a qirjinsa kafin a hankali dokin ya ajiye qafafunsa a qasa.
Dukkaninsu ba wanda yayi qoqarin motsawa,daga ita har shi suna saman dokin a zaune. Tana jin yadda yayi mata rumfa da hannuwansa,tana jin yadda qamshinsa yake sake mamayarta,tana jin yadda wani irin dumi daga faffadan qirjinsa yake mamayar ilahirin zuciyarta da gangar jikinta,yana kuma haifar da wata nutsuwa yana amintar da ita daga dukkan tsoron daya taso ya soma lullube mata zuciya.
A hankali kamar wandada ke shirin narkewa taji tana qara shiga jikinsa sosai.....a hankali taji habarsa saman kafadarta.....a hankali hucin numfashinsa dake fita daga dogon hancinsa ya soma sauka a fatar fuskarta,abinda ya sanya tsigar jikinta zubawa.
Da wani tattausan harshe amma mai cike da kaushi a maganganunsa.......da wata magana dake fita daga can qasan maqoshinsa......wata magana me kama da maganar da akeyinta cikin sirri,sirrin da ba'a buqatar kowa yaji yace.
"Ki daina gwada kanki a inda hatsari yake.....Ba'a shiga tseren doki don nuna girman kai.....musamman ba tare da izini na ba".
"Izini?" Ta fada can qasan ranta. Har yanzu idan ya fadi hakan tana jin mamaki......ta kasa sabawa.
"Izini fa.?" Ta maimaita maganar zuciyarta tana lumshe idanunta zuciyarta tana bugawa. Kusancinta dashi yana haifar mata da wani abu,tana jin kamar ba zata iya riqe kanta ba,kawai saita zabi ta shammaceshi,ta sauka daga saman dokin da wani irin sauri.
Saukar da tazo mata da tsautsayi......tana dire qafafunta qafartata ta bada wani sauti daya tilastata furta.
"Wash Allah na" A mugun wahalce tana dafe qafartata.
Cikin qiftawar idanu...cikin wani yanayi na zafin nama.kamar sadaukin daya dawo daga yaqi ya dire a qasa da dukka qafafunsa.
"Kin rasa hankalinki ne?" Ya fadi da wani irin yanayi daya tilastata daga kanta tana duban qwayar idanunsa duk da irin zafi da radadin dake ratsata har kwanyarta.
Wani irin rudewa take gani cikin idanunsa,kafin ya qaraso ta tattara dukka juriyarta ta miqe,saidai ta tsaiwa din batasan sanda ta sake furta.
"Wayyo Allah na" Da siririyar muryar nan tata data karye sosai ba.
Da wani irin zazzafan taku ya isa gareta kafin takai qasa yana riqe dayar kafadar tata,riqon daya sanya mata tsoro,tafin hannunta yakai saman faffadan qirjinsa.
Daga kai ta sakeyi a karo na biyu tana duban fuskarsa dake shimfide da rudani. Bugun zuciyarsa take iya jiyowa......bugun zuciyarsa sosai da wani irin qarfi da bata taba kawowa ba.
"Tsorata yayi?,me yasa ya damu haka?" Ta tambayi kanta da kanta tana sauke dubanta kan qafarta.
Kamata yayi ya maidata ya zaunar da ita sosai yana miqe mata dukka qafafunta. Hannu ya saka ya dago dayar,dagawar data sanyata runtse idanu ta kuma saka hannunta ba shiri tana riqe hannunsa idanunta a runtse tana furta.
"Wayyo Allah bappi". Yadda ta furta din ya ratsa kunnuwansa da wani irin yanayin. Muryarta ta sauka sosai cikin kunnensa saboda kusanci da fuskarsa tayi da tata.
" Ki nutsu" Ya furta a tausashe yana qoqarin daidaita nutsuwarsa.
" Da zafi" Ta fada tana yarfa hannu cikin tsananin azaba. Sake kama gurin yayi,saita sake cafke hannunsa da hanzari,abinda ya sanyashi daga kansa yana dubanta a hankali.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Da gaske zafi takeji,ya fahimci hakan saboda kalar gumin data hada sosai cikin qanqanin lokaci.
"Don Allah" Ta fada a narke,saboda ta fuskanci da gaske so yake ya taba ciwon,tare da manta cewa roqonsa ma takeyi. Wani abu daya zamana na farko a rayuwarta.....roqon ALFARMA da neman alfarma daga gurin wani mutum na daban......ba SULTANE ba.
Yadda tayi maganan a shagwabe ya sanya yaji wani abu ya tsarga cikin kansa. Ya daga kan nasa a hankali ya zube idanunsa saman fuskarta. A shagwabe tayi maganan sosai.....da shagwaba irin wadda a baya mammina da bappi sultane kawai take iya yiwa su. Ruwan hawaye yake gani sosai cikin idanunta a kwance,karon farko da yaji wani rauni me kama da tausayi ya saukar masa.
Bayason kuka,bayason hawayen mace. Tunda ya karanta cikin qur'ani a nazarin da yayi masa sanda yake karatun qur'anic science,yazo ya kammala tafseer dinsa gaba daya. Cikin qur'anin ayoyin da dukka sukazo akan MACE Allah yana tausasa mata kalamai ne da lafuzza,sai abun ya zame masa jiki.
Zare nadin dake kansa yayi a hankali,abinda ya bawa sassalkar sumar nan tasa me santsi baqi da cika kai daman bajewa saman kansa da wani sashe na fuskarsa. A hankali idanunta suka kai......yawan sumar ya bata mamaki don bata taba ganinta full kamar haka ba. Duk da duhun magariba daya shigo amma kana iya ganin qyallin da take bayarwa.
Warwareshi yakeyi a nutse,yayin data samu kanta da kafeshi da idanu,tana kallon yadda sumar ta sake canza kamanninsa.
"Wanne yare ne?.....balarabe?" Ta tambayi kanta da kanta tana lumshe idanunta gami da budesu lokaci guda saboda radadin ciwon dake ratsata.
Daga idanunsa yayi,sai suka hada ido,tayi saurin kauda idanunta shi kuma yayi kamar bai ganta ba. Ya miqe yana wareshi sosai ya shimfidashi a qasa ba tare daya damu da rairayin dake gurin ba.
Ya tako a hankali zuwa gabanta,ya miqa mata hannunsa kai tsaye yana dubanta. Nauyi taji ya aza mata,ta fahimci me yake nufi sarai......amma kuma ita kadai tasan me takeji duk sanda ya hade tafukan hannunsu guri daya. To amma ya zama dole ta tashi,don ba zata iya takawa da qafafunta ba ita kadai.
"Levez-vous(Stand up)" Ya fadi da wannan karya harshen da yake sanyata takejin wani yanayi a cikin ranta duk sanda zai furta France.
A nutse ta miqa masa dogayen yatsunta,ya runtsesu tsakiyar lallausan tafin hannunsa sannan ya dagota. Ido ta runtse,zata sake fadin.
"Washa Allah" Sai ya rigata.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya maimaita har sau uku. Kasa fadin wayyo Allah din tayi,a hankali sai taji zuciyarta tana maimaita abinda ya fadi din. Sai da yaga ta samu daidaito a tsaiwar sannan ya umarceta ta taka,saidai hakan yaqi yiwuwa. Har cikin zuciyarta takejin radadin sosai.
Kaman daga sama ya shammaceta,sai jinta tayi yayi sama cak da ita da hannuwansa biyu yana mata kyakkyawan riqo cikin jikinsa.
Ji tayi kamar numfashinta zai dauke,tsoro sosai ya kamata. Ko nauyinta baiji ba?,ko girmanta shi baya gani?. Idanunta kawai ta zube akan qirjinsa,qirjin da zuciyar dake cikinsa take bugawa da wata irin nutsuwa ba kamar dazu daya tallafeta ba.
"Me ya hautsina bugun wannan nutsatsiyar zuciyar a dazu?" Ta tambayi kanta da kanta. A yanzu da take kallon qirjinsa da yake dage.....dagewar da take tabbatar mata cikakken qarfi ne kwance a gurin. Sai taji tana sha'awar sake aza tafin hannunta a gurin,sau taji tana sha'awar sake jin wannan kyakkyawan bugawar dataji a dazu,bugun zuciyar tasa daya dinga ratsa jininta da wani irin gudu yana son samar da connection da wani sashe na jikinta.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 134*
Gaban Shimfidar ya tsaya,ya sauke dubansa a kanta,daidai sanda itama ta daga kai tana dubansa. Shi ya fara dauke kansa wannan karon,ya tsugunna saman gwiwoyinsa a hankali yana ajiyeta gefan Shimfidar.
Tana zama suna jin taku daga bayansu,don haka kai tsaye ya miqe yana waiwayowa. Wasu daga cikin guards na gurinne da kuma na masarauta.
"Minister tace fatan komai lafiya?" Kai ya gyada a nutse yana basu alamun tabbacin lafiyar. Thunder yasa suka janye suka bar nasa dokin,sannan suka juya suna barin gurin.
Idanunsa a akanta,ya sake haurowa saman Shimfidar. Zama yayi sosai a gabanta yana tanqwashe qafafunsa,wani irin zama me tsananin kusanci a tsakaninsu. Hannu ya sake kaiwa zai kamo qafar ta zabura ta riqeshi,sai ya dakata cak,ya zuba mata idanu da kallon data gaza jurewa,abinda ya bashi daman kama qafan cikin zafin nama,don ya fuskanci idan ya biye mata fa to zasuyita zama ne a gurin.
Idanun ta bude a tsorace,saidai ta sameshi ya kafeta da wani irin kallo me tsananin kaifi.
"Kalleni" Ya fada da wani irin coolness ganin tana son janye qwayar idanunta.
"Cikin idanuna" Ya fada yana nuna nata qwayar idanun nasa da yatsarsa. Batasan me yasa ta gaza janyewa ba,batasan me yasa ta gaza masa musu ba,sai tayi yadda yace din.
Tayi yadda yace din.....tayi kuma yadda yaso ba tare da tasan SAKAMAKON da hakan zai haifar mata ba. Duban idanunsa kadai sai taji kaman yana zuqeta daga ainihin duniyar da take ciki......kamar yana zuqeta daga ainihin gangar jikinta zuwa wata gangar jikin ta daban.
Kamar yana zuqeta zuwa DUNIYARSA.....wasu irin magnet masu tsananin qarfi taji a hankali suna janta. Wani iri yanayi.....wani irin kallo.....wasu irin idanuwa data dinga ji kamar ana jifanta da wasu abubuwa masu sanyi dake sauka saman zuciyarta suna narkewa suna kuma bin sassan jikinta. Wani zuzzurfan kallo da bata taba yiwa wani d'a namiji irinsa ba.....wani zuzzurfan kallon da itama ba wani d'a namiji daya taba yi mata irinsa.
"An gama" Lafazin ya sauka a kunnenta yana kuma maidota duniyar ta daya saceta daga ciki zuwa wata daban.
Zare idanunta tayi a kansa duk da shi yaci gaba da kallonta ne. Takai dubanta ga qafartata. A hankali wani mamaki yake lullubeta. Yaushe yayi gyaran?,yaushe kuma ya gama shi duka bata sani ba?.
"Kiyi alwala.....lokacin magarib yana kusa da fita" Tana kallonsa yasa hannu ya share rairayin gurin ya Ciro ruwa daga jikin dokinsa ya soma alwala,
Hankalinta ya dauku sosai,yadda yake alwala da wata irin nutsuwa da kamewa,gami da cika dukkan sunnoninta da farillanta sai abun ya kasa wucewa a idanunta. Sai ya matso bayan ya gama,ya tsugunna a gabanta ya fara zuba mata ruwan a hankali ta fara alwalar. Idanunsa ya sauka akan fararen tafukan hannunta da sukayi kwanciyar jini saboda tsananin hasken fatarta. Samun kanta tayi da halarto kalar tasa alwalar tana bibiya itama daki daki,gabanta yana faduwa. Haka kawai takejin ya mata wani kwarjini,ga tsugunnonsa dab da ita dake sake yin kaca kaca da nutsuwarta.
Wai itace a yau take alwala da takatsantsan kada wani yaga kuskurenta?.
Dakatawa ta danyi sanda tazo shafar kai. Ya daga manyan idanunsa ya zube a kanta,kafin a hankali ya dauke dubansa yana maidashi wani gurin daban. Ya fahimci ne ta tsayawa.....itama ta fahimci ya bata space ne nayin shafar kan. Qafafunta ya zubawa ruwan tana wankewa,saidai tsigar jikinsa ce yaji tana zubawa lokacin da take wanke sambala sambalan fararen qafafun nata.
"Ina zuwa" Taji ya fadi bayan ta kammala. Narai narai tayi da idanu,ina zaije a wannan fili saharar da baka ganin kowa da komai?. Fitilar wayarsa dake kunne ce kawai take basu haske.
"Ba nisa zanyi ba" Ya fadi yana bata qwarin gwiwa da kuma tabbaci da idanunsa. Daga inda ta tsaya tana hangensa,mamaki ya kamata ganin ya sake sauya alwala bayan yanzu ya gama.
Dawowa yayi,ya tsaya daga gabanta kadan ya fara tayar da iqama,ya kabbara sallar yana daidaita tsaiwarsa sannan ya fara rera karatun nan nasa. Da wannan muryar.....wannan sautin me kama da qira'ar sheikh afif,cikin suratul furqaan da wani kwantaccen sauti daya soma sanya nutsuwa tana lullubeta.
A nutse ya kammala ba tare da jan dogayen ayoyi ba...ya zauna kadan sannan ya fara gabatar da nafilolin bayan sallar magariba din.
"Baya gajiya ne da sallah?" Ta tambayi kanta tana satar kallonsa sanda yake sake zaman tahiyar qarshe.
Itakam sai take ganin kamar sallarsa tana da banbaci da tasu,kamar akwai wasu abubuwa wata nutsuwa da wani tsantseni a sallarsa da suka rasa a tasu.
Kwarjinin da yayi mata ya sanyata yin qasa da kanta sanda ya waiwayo bayan ya kammala sallar. Kamar tsakanin fara sallar da kammalata ana qara haske fuskarsa ne.
"Zaki iya takawa?" Ya fada da kulawar da taji ta ratsa har tsakiyar zuciyarta. Kanta ta daga masa,sannan ta yunqura ta miqe a hankali. Ga mamakinta ba wani ciwo me zafi,ta dinga takawa a nutse a nutse har suka kai bakin dokinsa daya rage.
Tsayawa tayi ranta da zuciyarta fal saqe saqe. Saman doki daya zasu zauna?,tabbacin fa kenan zasuyi sharing muhalli daya?. Idan ma haka ne ta yaya zata iya dokin?,tsahonta baikai ba,ta riga ta saba duk sanda zata hau sai an saka mata abinda zata taka ko an samu wadda zata tallafeta.
Wani irin mamaki ne ya soma narkar da ita sanda taga ya tsugunna saman gwiwoyinsa yana daidaita gaban dokin. Ko baiyi magana ba,ko baice komai ba ta fahimci abinda yake nufi. Durquso ne da akewa sarakuna don su tattaka su samu hawa doki,duk da cewa a tasu masarautar sultane ya haramta hakan. Suna da abubuwan takawa masu kyau na musamman da aka ajiye don hawa doki bawai dan adam ba.
Ji tayi kamar tana narkewa sanda ya daga manyan idanun nan da koda ace da duhu a gurin bata iya ganinsu tarwai amma tana iya jin tasirin kwarjininsu a jikinta. Sanda yake fadi mata.
"Ki hau mu tafi" Sai takejin kamar ba zata iya ba. Ta yaya zata taka gadon bayansa don tahau doki?,gadon bayansa fa?,abun ya mata girma da nauyi.
"Taka ki hau mu tafi" Ya sake maimaitawa da wani sauti daya sanyata takowa a hankali kamar wadda ke tsoron taka qasa.
Takalmanta ta kalla,sai takejin ba zata iya taka gadon bayansa da takalmi ba. Tsugunnawa tayi a hankali ta zare takalman daga qafafunta. Sannan ta matso tana jin wani abu yarr yana tsirgawa a jikinta,ta sanya qafarta ta dama kafin ta dago ta hagun itama.
Cak ta jita tsaye saman bayan nasa,ba wani girgidi ko lagwai lagwai na nama ko fata. Kaman tana zaman wani abu dake shimfide saman doron qasa,sai curi curi na muscle da dumin jikinsa da yake ratsa tsakiyar fatar qafafunnata. Bismillah tayi tana hawa ta zauna sosai,bismillah din data sauka a kunnensa,karon farko da yaji tayi wani abu daya burgeshi.
Hagu da dama ya zagaya yana dubawa,kaman bai amince da iya zamanta saman dokin ba,tana jira taga yahau bayanta,sai taga kawai ya kama linzamin dokin sun fara tafiya a hankali.
*T A M I M*
Daga gurin da yayi kyakkyawan boyo tsakanin tent din akhnan dana maqotanta,daga nan din yana iya ganin kai kawo da motsin duk wanda zai shiga ciki ko kuma ya fita.
A irge yake da shudewar kowanne minti,a lissafe yake da shudewar kowacce daqiqa. Akan idanunsa komai yake faruwa,saidai a yanzu fatansa daya shine dawowar akhnan da kuma shigarta cikin tent dinta kamar kowa....
Baida yaqinin inda ta shiga daga sukuwar dokin daya kubcewa saitinta,duk da bai ganta a kasuwar bajakolin kayan al'adu dake ci a sansanin ba.....amma ya tabbatar duk inda take zata kwana ne dole a tent dinta.
Tsakiyar dare zuwa asuba sune awannin sa'arsa.......daga tsakiyar dare zuwa asuba mummunan labari zai tarwatsa taron festival de l'Aîr gaba daya.
Zabi biyu ya aje mata a ransa,idan ya samu nasarar tafiya da ita lafiya lau haka yakeso,idan hakan kuma zai zame masa kaya zai aikata abinda yakeso da ita a gurin,ko banza ya kashe wata wutar kafin ya samu sararin hada target na gaba.
★Wata irin tafiya data saukar mata da wani yanayi a zuciyarta....wata irin tafiya da take jinta kamar cikin litatattafai da finafinai. Hasken farin wata sai ya zame musu tamakar wata fitila tsakiyar duhun daren daya keto. Samun kanta tayi da zuba masa idanu. Yadda yake takawa cikin sahara da wani irin yanayi dake gwada jarumtarsa da rashin tsoronsa. A iya saninta baqo ne shi a yankinsu,a iya saninta baisan kan sahara da hanyoyinta ba,amma kuma sai gashi yana taka saharar da wani confidence da rashin DAMUWA.
A duk sanda ta tuna yadda ya bata gadon bayansa ta taka sai taji wani tashin tsigar jiki.....a duk sanda ta tuna da wannan sai mamaki ua mamayeta. Tana zaton yana da girman kai......amma kuma wannan abun ba wanda keda girman kai komai qanqantarsa da zai iya aiwatar dashi. Tana ganin wata kulawa a tare dashi.....kalar kulawar da sultane kadai take ganin makamanciyarta a gurinsa. Tun tana ganin NA GANIN IDO ne.....tun tana ji a zuciyarta na NEMAN SUNA ne gurin sultane,ya zuwa yanzu zuciyarta ta gama sallamawa DABI'A CE A CIKIN JINI.
Ya girmamata ta hanyoyin da bai girmamata din ba a gaban mutane.....ya girmamata da nau'in abubuwan da take jinsu sun tsaye mata sosai a zuciyarta. A inda ba kowa daga shi sai ita sai Allahnsu,.....a inda idan yaga dama zai iyayi mata komai,ba wanda zai hanashi.....bame qwatarta.....a irin wannan gurin sai ya zabi girmamata,sai ya zabi kare mutuncinta sama da komai.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Sanda suka fara hango haske sansanin festival din.....saita dinga ji kamar su rage saurin tafiyar da sukeyi. Duk da tafiya ce sannu sannu cikin nutsuwa......amma sai takejin kamar karsu iso gurin.
Ita dashi dukka sun hangi maleek da falaak zaune saman rairayin,da alama cikin wani yanayi suke na zallar shauqi da qauna.....har basaji basa ganin kowa dake daura dasu. Ga mamakinta sai taga ya dauke kansa,ya kuma ja akalar dokin sun dan sauka daga kan hanya kadan yadda ba zasu ji motsin tafiyarsu ba,ya yanke ta wani hannun daban can qasan ransa yana sakin murmushi. Ya aminta da gaske maleek yake,baida zaqewa haka.....baida rawar kai akan diya mace iya saninsa dashi,saidai zuwa yanzu ya gasgata da gaske yake yarinyar ta zautashi da yawa.
Ta sake binsa da idanu sanda yake miqawa birra akalar dokin yanayin gaba,bayan ya danyi magana da birra din da batasan me yace mata ba. Sai sake waiwayarta,bai sake juyowa ba ya taka yana shigewa cikin mutane har ya bacewa ganinta.
"Zamu iya tafiya ranki ya dade?" Taji birra tana fada cikin girmamawa
"Muje" Ta amsa mata a taqaice,saitayi gaba da dokin kai tsaye zuwa ga tent hanyar tent dinta.
Wani shu'umin murmushi tamim ya saki,yana jin wani dadi yana kamashi sanda ya hangi isowar akhnan da shigewarta tent dinta.
Akan idanunsa Madame minister......da sauran ministoci mata suka dinga shiga duba lafiyarta suna fita,kuma akan idanunsa aisa da shehnaz da suka zama fitar qarshe suka fita suma,bayan shehnaz ta gama cakar da ita da wannan kalar tsokanartata.
Yau bata da bakin cewa komai.....a yau bakinta da zuciyarta sun wani mutu murus. Komai game dashi ne yake dawo mata,idan tace komai tana nufin komai da komai din.
Nutsuwar nan data mamaye komai nasa......miskilancin nan data lura yana iya hanaka ganin murmushinsa.....kwarjinin nan da har yanzu take tambayar kanta INA YA SAMOSHI?,INA YA GAJESHI?.