Kenza eBookz

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 79

L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 79

L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 79: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 79. Uwa uba.....tana ganin wani good sign da wani good…

3,363 words

Uwa uba.....tana ganin wani good sign da wani good character da riqo da addini yake iya bawa d'a namiji ashe?. Wani kalar shiriya kusanci da Allah da Allah a dukka lamura. Komai zaiyi a iya tsahon awannin da suka taba yi tare sai taji ya kira sunan Allah.

"Bismillah....alhamdulillah.....a'uzu billah.....astagfirullah......subhanallah" Bata taba jin wata mummunar kalma ba......bata taba jin wata kalma mara kyau daga bakinsa ba.

Ta juya tana gyara kwanciyarta da kyau bayan birra ta taimaka mata tayi wanka,ta kuma canza kayan jikinta zuwa wani riga da wando masu taushi na bacci farare tas.

"Yace idan kinyi wanka ki rama sallolinki saikisha wannan" Ta tuna maganar birra a dazu data bata ruwan wani abu me dumi tasha. Wanda tana kammala sha da mintuna kadan taji gajiya tana warware mata gami da barin jikinta.

A hankali idanunta suka fara lumshewa,wani irin ni'imtacen bacci da ta jima bataji irinsa ya lallabo ya dauketa.

Sannu a hankali sawu ke daukewa.....sannu a hankali gurin yake qara cika da shuru saboda kwanciyar jikkuna izuwa makwancinsu don huce gajiyar ranar farko ta festival din,don samun cikakken baccin da zai basu daman tashi da karsashi me yawa a rana ta biyu.

A wannan lokacin burin tamim yake sake kusanta zuwa ga cikarsa.....a wannan lokacin kowacce daqiqa dake gotawa take sake cika zuciyar tamim da madaukakin farinciki.

A wannan Lokacin ne kuma haisam ke dawowa sansanin,bayan ya sake tabbatar da tsaro a kowacce fuska da nahiya na gurin,cikinsa da wajensa.

Wani irin gumi me dumi ya yankowa tamim ganin yadda haisam ke tunkaro gurin. Ba yau ba ba jiya ba ba kuma shekaran jiya ba. Tun a ranar farko daya fara ganin sa yakejin wani abu me qarfi da girman gaske a kansa. Tun daga wancan ranar yakejin wani kwarjini na bala'i yana dukansa a kansa. A duk sanda zasu hadu dashi,a hanya ko a wajen sultane,dukka wannan ranar yana yinta ne cikin rashin sakewa da kuma d'ari d'ari.

Numfashinsa gaba daya ya dauke ganin ya tako dab da inda yake yayi tsaye. Baibar gurin ba saida ya kusa rasa numfashinsa saboda riqeshin da yayi,ya zuqi iska yana riqe wuyansa da kyau ganin yadda tsaiwarsa ke shirin hallakashi,idanunsa a kansa har sanda ya shige tent din da Akhnan ke ciki.

Bai damu ba....koda ya rasa samunta a tsakiyar dare,ya shirya samunta lokacin sallar asuba.... Lokaci ne daya tabbatar haisam zai fita da sauran dukka maza don bada faralin sallar asuba din.....saidai daga yanzu zuwa kowanne lokaci inde dama ta bashi iko.....zai iya aiwatar da qudurinsa,don haka ya zauna sosai yana ci gaba da gadin komai gami da ci gaba da daidaita numfashinsa da har yanzu bai dawo daidai ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 135*

Sassauqan haske ne a dakin,wanda sam baiyi yawa ba,kusan ma za'a iya cewa hasken fitilun dake zagaye da tent din sune suke haske dakin,hasken da zai iya nuna maka komai ka ganshi fes.

A nutse ya dinga takawa zuwa cikin dakin,idanuwansa akan fuskarta,yana shaqar qamshin dake manne da d'akin. Sosai ya shaqi iska ya fesar,yana qarasawa saman kanta da wani irin taushi yana dubanta.

Bacci takeyi sosai,da alamun tarin gajiya a tattare da ita. Dazun zuciyarsa ke dawo masa da komai daya faru. Tana da jarumta can qasan zuciyarta......tana da tsaiwa da rashin tsoro akan abinda takeso da dukkanin abinda ta sanya a gabanta. Ya tuna yadda tayi da yumna,duk da irin qwarewa yumna din wajen sarrafa doki da babanta ke gaya masa,da yadda shima ya fahimta. Baisan meye mafarin abun ba,besan meye ya jawo hakan ba,amma abinda ya lura kawai FANSA take nema daga yumna din.

"Rigimammiya" Ya fadi sanda yake matsawa daga inda take,saidai idanunsa suka sauka kan yadda hannunta ya lanqwashe. Kamar zai gyara mata sai kuma ya fasa,bayason abinda zai kawo haduwar jikinsa da nata. Komawa yayi da baya ya soma rage jayan jikinsa a nutse,ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tsane jikinsa ya kuma shafeshi da lausasan lotion dinsa da kuma turaren daya saba amfani dasu.

Abun sallah ya shimfida,yayi shafa'i da wuturi da sauran addu'o'insa. Yayi zaune saman abun sallahr yana qarasa azkar na yammaci da bai samu yayisu ba a yau,jifa jifa yana tsintar idanunsa suna fadawa kanta. Baccinta take hankalinta kwance,baccin daya tabbatar qila inda tasan yana gurin ba zata sake har haka ba. Hular kanta ta zame tayi nata gurin,wannan ya bawa gashin kanta me santsi da sheqi daman bayyana.

"Alhamdulillah" Ya furta yana miqewa a nutse,ya ninke abun sallar. Fita yakeso yayi ya sake tabbatar da tsaron gurin,sannan ya qarasa gurinsu omar ya karbi coffee da yasa suka ajiye masa. Yayi missing coffee yau duka,wani abu da ba kasafai yake yinsa ba saboda tsananin amincin dake tsakaninsa da coffee din.

Har yayi taku uku zuwa bakin qofa,sai ya sake dawowa ya kalleta. Maimakon fita kamar yadda ya tsara,sai kawai yayi kwana yana dawowa inda take kwance.

Cikin wani irin taushi ya tsugunna a gabanta,qamshin nan nata daya mamaye dakin ya cakude da nasa qamshin yana bada wani yanayi na daban. Hannunsa ya miqa gareta,sai kuma ya janye. Idan ta farka fa ta ganshi haka dab da ita?,idan ta bude idanunta kuma ta ganshi a gabanta fa?. To amma kuma zai iya fita ya barta haka hannunta a lanqwashe?. Idan yayi hakan zai iya cutar da ita,xata iya tashi da ciwon hannu kuma bayan qafarta.

Koma yayi ya zauna sosai,wannan ya kashiginda kan hannunsa daya tamkar yadda uwa keyi idan zata lallaba yaronta yayi bacci ko zata gyara masa kwaciya.

Hannunsa ya miqa a hankali yana zare mata hannun,zuciyarsa na bugawa da wani irin sanyi,yana jin kusancin har cikin zuciyarsa.

Can cikin hancinta takejin qamshin,can cikin duniyar baccinta takejin qamshin sosai kamar yadda ta saba jinsa a duk wani.mafarki nasa da zatayi. A yau bayan qamshin tana jin wani abu tattare da mafarkin,wani abu da yake mata kama da wanzuwarsa dab da ita. Wani irin sanyi nutsuwa da sukuni takeji sosai tattare da qamshin a yau cikin baccinta fiye da wanda ta saba ji,fuskarsa tsaye a gabanta,da wannan kalar fusatar data faru a dazu bayan ta sauka daga saman dokin ba tare daya tsammaci haka ba,don haka tayi wani kyakkyawan juyi tana yamutsa fuska kadan,tana gyara kwanciyarta sosai muryarta can qasa take fadin.

"Kayi dariya mana......kafi kyau idan bakayi fushi ba,hai.....haismmmm". Idanunsa ya lumshe a hankali,wani murmushi da baisan daga inda ya taso masa ba ya subuce masa,wani murmushi da baisan daga inda ya taho ba ya subuce masa,duk da yadda ta danne masa dantsen hannusa ta kuma zagaye hannun nasa da kyau da dukka hannuwanta biyu kamar ta samu kyakkyawan pillow,kamar kuma wadda ta samu abun kamawar da take tsoron faduwa.

A hankali ya motsa bayan ya tabbatar tayi relax ta kuma sake komawa baccinta da nufin zaren hannun,saidai tuni ya fahimci ba abu bane me yuwuwa. Ta qanqameshi sosai,idan kuma ya matsanta yace sai ya cire hannun farkawa zatayi,idan kuma ta farka din bashi da kalmar da zai mata bayani da ita kan abinda ya kawoshi gurin har hakan ta faru.

Mintuna masu yawa suka shude,idanunsa suna sauka a kanta. Kyakkyawan fuskar da a yau tayi kusa dashi sama dako yaushe,kyakkyawan fuskar da wannan gashin ma'abocin tsahon santsi da silki ya rufe rabinta,saidai hakan bai hanashi ganin tattausan labbanta ba dake tsuke kadan,alamun kodai still tana cikin mafarkinne,ko kuma dai ranta ne ba dadi.

"Me ya kawo sunana mafarkin ta?" Ya tambayi kansa da kansa har yanxu yana jin mamaki cikin ransa. Ya lumshe idanunsa sannan ya budesu duka lokaci daya,yana jin yadda wata muguwar kasala ke lullubeshi. Sosai lips dinta ke jan hankalinsa,ya zuba musu idanu yana kuma lumshe idanun nasa a hankali. Kaman ta sani yana kallonta ne.....ta sake motsawa da wani irin yanayi daya sanya qirjinta shafar qaurin hannunsa tana sake qanqame hannun nasa da kyau.

"Ya salam" Ya fadi labbansa suna rawa kadan,wani irin zubawa tsigar jikinsa tayi.....wani abu yaji me girma da qarfi ya tsarga masa tun daga saman kansa zuwa kowanne sashe na jikinsa,yadda suka taba hannunsa wani abune da ba wani namiji da zai iya tsallakewa abinda yaji. Suna cikin silk rigar bacci,yadda yajin kuma ya tabbatar babu bra a jikinta.

Numfashi ya sauke me matuqar nauyi,yana ji a ransa tabbas yau yana cikin tarko. Don yana iya jin yadda jikinsa ya fara rawa kadan kada. Baida wani sauran mafita,illa kawai kwantar da kansa da yayi sosai a kafadarsa yana ambaton sunan Allah. Kwanciyar kuma ba kuma ta samar masa da sauqi bane,saima qara kusanci da tayi a tsakaninsu. Musayar numfashi suka fara yi a hankali shi da ita,musayar numfashin data sake masa nauyi ainun,iskarsa yaji ta fara canzawa da wata kalar iska dake shigar da saqo kowanne lungu da saqo na jikinsa.

Wanda ta fitar shi yake shaqa,wanda ya fitar itama shi take shaqa. Yatsansa ya daga a hankali yana ajewa saman dogon hancinta medan tudu kadan daya qawata fuskarta,sannan kuma a hankali ya janyeshi yana kaiwa saman tausasan lips dinta.

Komai nasa ya fara rikicewa,komai nasa ya fara neman fita daga saitinsa. Dumin jikinta.....kusancinsu musayar numfashin dake gauraye da tattausan qamshin jikinta. Ya lumshe idonsa da kyau yana kiran sunan Allah a jejjere can qasan ransa,yana jin yadda yanayin bugun zuciyarsa da fitar numfashinsa suke sauke hargitsewa.

"Ya Allah.....not now.....not yet" Ya fadi yana qoqarin controlling kansa.

Ya jima idanunsa a rufe,ya jima da zame kansa qasa kadan saboda rage musayar numfashin dake tsakaninsu kafin ya samu ya rage dan wani abu kadan cikin abinda yakeji.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Ya sake bude idanun da suka sauya launi suka kada sukayi jaa yana sake zubesu a kanta. Kamar wani annuri da nishadi ke fita daga kan fuskartata,kaman yanayin yayi mata dadi cikin baccinta sama da kowanne yanayi. Ya sani muddin ya bari sukaci gaba da kasancewa a haka,muddin ya qyaleta cikin jikinsa tayi kyakkyawan matashin kai da hannunsa to komai yana iya faruwa........ya qaryata dukkanin wata jarumatarsa a yanzu.....ya yadda bazai iya ci gaba da mallakar kansa ba........don haka ya tattara dukkan wata jarumatarsa ya zare hannunsa a hankali yana maye mata gurbinsa da pillow.

Ko a yanzun sai data turo baki fuskarta tana yamutsewa,kamar dai tasan canjin pillow yayi mata daga hannunsa xuwa pillow din fiber. Kamar dai tana qorafi akan wancan yanayin yafi mata dadi,sai ya miqe a hankali yana jinsa kamar iska zata daukeshi,still idanunsa a kanta. Matsawa yayi daya side din,ya dauki lallausan duvet din ya lullubata a hankali ganin yadda ta qanqame pillow din,yayi tsaye saman kanta yana kallon fuskarta.

Wato ba qaramin kariya da ni'ima Allah yayi masa ba daya sanyashi ya zamana cikin masu kame kansu,ba qaramin taimakonsa Allah yayi ba daya sanyashi cikin masu bin umarninsa na RUNTSE GANINSU......ya sani inda ace ya shigo a sahun 'yan duniya......inda ace ya shigo a sahun mutane banza ba qaramin b'arna zaiyiwa yaran mutane ba.

"Alhamdulillah" Ya fada yana shafa qirjinsa da tafin hannunsa har zuwa saman cikinsa.

Har ya juya sai yaji kamar kada ya fita kuma,amma yanason ya qarasa karya wannan feelings din da yakeji a jikinsa. Yana son yayi nisa da abinda yakeji.....uwa uba kuma bayason yaqi fita ya bawa su omar daman sakashi a gaba.

Ya lura.....dama ya lura da kallon da suketa masa tunda aka warewa kowa tent dinsa,nasa tent din ya zamana daya da Akhnan din. Sam bai shiga ba ko sau daya,baima bata daman da zata gane a tent daya zasu zauna ba.....amman ko dazun da yace zaije ya watsa ruwa yana kallon yadda idanunsa da fuskokinsu ke cike da gulma.

"Ku ajjiyemin nawa coffee din" Ya fadi da yaren oromo sanda yake takawa zai fice.

"Anya kuwa?,kaidai kawai idan ka dawo shikenan.....idan baka dawo bama shikenan.....bazai kayi alaye ba" Omar ya fada yana wani mazewa. Harara kawai ya jefawa omar din sannan ya fice,yana jinsa kuma yana masa dariya qasa qasa,to tabbas idan bai fita ba yanzun ya bawa omar dasu khadeema abun fadin da zasu addabeshi dashi gobe.

Tunda yaga shigar haisam din hankalinsa yake a tashe,wani irin gumi yake yana lissafa lokacin fitowarsa. A iya saninsa bata zama tasa ba ta hanyar damqa masa ita officially bare su fara kwana tare guri daya,amma yanayin dadewarsa yanzu a ciki ya fara saka masa shakkar anya ba kwana zaiyi ba?.

Fitowarsa ta sauke masa wani gingimemen abu me nauyi daga saman zuciyarsa,ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin fuskarsa. Gwara kawai yayi me yiwuwa a yanzu,don a yanzunne kawai zai samu bugar da ita ta kwanciyar hankali tunda bacci take,xai masa sauqin tafiya da ita kuma.

Haka kawai yaji ya kamata a qara haske gurin,yana takawa zuwa gurinsu omar yana fidda wayarsa,ya kuma kira daya daga cikin security na gurin ya bada wannan umarnin yana isa bakin tent din su omar din.

Taku uku yayi haske ya gilma a gurin,taku uku yayi haske ya ninka na dazun,wani irin haske da yasa gabansa faduwa,wani irin haske daya haska can nesa da inda sansanin yake bama sansanin kansa ba,

"Akwai matsala tamim ka gaggauta" Abinda zuciyarsa ta gaya masa kenan,don haka da sassarfa a dudduqe ya durfafi tent din.

Tsaiwa yayi kamar wani sakarai yana dubanta yana sakin qaramar dariya sanda ya hangeta nade cikin duvet din. Duk wata tsohuwar qwalamarsa dama sabuwar zalamarsa yaji sun motsa gaba daya. Burinsa da karsashinsa ya qaru sanda zuciyarsa ke gaya masa,wanna halittar dake kwance tana zuba qamshi dab take da zama mallakinsa......wannan halittar dake kwance awanni kadan suka rage masa ya mallaketa dama komai daya shafeta. Sai yaci gaba da takawa cikin zafin nama kamar wani mahaukacin kare,har zuwa sanda ya isa gaban gadon.

Har zai fara hura mata abinda ya ruqo saboda gusar mata da hankali sai kuma ya fasa. Ko yaya yanason ya fara kallonta sosai don ya sake samun karsashi da qwarin jiki,don haka ya saka hannu ya fara zame qaton duvet din da haisam ya rufeta kafin ya fita

Daidai lokacin da haisam din ya saka hannu don bude labulen tent din.....daidai lokacin yaji zuciyarsa tayi wani mummuna dokawa......wani irin bugu da yasa yaji kamar zuciyar tasa tana shirin tsinkewa ne daga qirjinsa.

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ya fada yana lumshe idanunsa cikin tsananin mamakin nau'in faduwar gaba da mummunan bugun zuciyar da yakeji lokaci daya.

Sanyin da taji ya fara ratsata,da yadda takejin wani abu yana zamewa daga jikinta shine abinda ya sanya ta bude idanunta a hankali.

"Gimbiya" Taji an kira sunanta da muryar rada saidai kuma sam muryar bame dadi bace.

"Gimbiya Akhnan" Taji an sake maimaitawa da muryar da bata da dadin amo.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 136*

Wani irin tsoro ya kamata,tayi wani irin juyi ta miqe tana zama,saidai kuma da wani irin zafin nama ta kama duvet din dake barin jikinta ta qanqameshi zuwa qirjinta. Dukkanin idanunta ta fiddo waje da wani irin mahaukacin mamaki. TAMIM take gani zaune gefan gadonta......tamim wannan dadadden amintaccen bawan gidan nasu?. Duk yadda zuciyarta taso kawo mata uzuri a kansa a sannan amma taqi karba,abu daya tafijin zata aminta dashi shine.

"Me kakeyi a nan tamim?.....kasan girman laifin dake tattare da qetare iyakokin iyalin sultane?,a cikin dakin da nake bacci,?har kana saka hannunka kana janye abun lullubata tamim?,a hayyacinka kake?" Dariya ya saki wadda bame qarfi ba.

"Wallahi bana cikin hayyacina......saboda tun kina shekara bakwai a duniya nake kwana da sha'awarki nake tashi......karamcin mahaifinki yasa bazan iya keta miki haddi ba......ko a yanzunma sai idan ke kika zabi hakan.......na sani,ba zaki bini mu tafi salin alin ba,saboda nasan girman taurin kanki da kafiyarki.......zan tilasta miki mu tafi tare saboda na samu nasarar mallakarki ta hanyar aure,shine kawai halaccin da zanwa sultane daga tarin karamcinsa......amma inda ace ke din diyar MAMMINA CE da ba shakka a nan zan kaca kaca dake nabar mata jinyarki........wannan kuma kadai bazai isa na rama abinda tayimim ba.....zan dan huce ne kadan kafin na sake waiwayarta.......ki tashi mu tafi" Ya fadi yana zaro kakkaifar wuqarsa,ya kuma yage bangon tent din ya zube gefe daya,abinda ya sanya take iya hango duhuwar cikin sahara me nisan gaske daga inda take.

Wani irin tsoro da firgitar da bata taba shiga irinta ba ta saukar mata. Ba kowa a bayan tent dinsu tabbas ta gani tunda rana.....amma a lokacin akwai tarin guards da security,saidai a yanzu bataga kowa ba.....wanne irin kaifi takobinsa ke dashi haka?,ta tsaga tent din cikin sauqi ba tare da qara ba. Tabbas zargin farko na amfani da sihiri da aka taba yiwa tamim shekarun baya can mammina ta wankeshi a yau cikin wannan rudadden yanayin ta aminta da haka.

"Tashi mu tafi gimbiya" Tamim ya fadi yana mata murmushi,murmushin da yayi mata kama sak da hammar kare. Kai ta gara girgizawa tana sake tamke duvet din da taga yana sake kamowa da nufin zameshi,zameshin kuma da yake daidai da ganin surar jikinta ta kayan baccin da suke jikinta,duk da cewa masu kauri ne.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya qara fada yana jin kansa ya wani sara masa kamar an lafta masa itace.

"Man.....yadai?.....ka qaraso" Muryar omar ta sauka a kunnuwansa. Saidai bayan kallon omar da yayi baice komai ba,sai ya samu kansa ya sake bude wayarsa da wani irin sauri yana jin yadda zuciyarsa keci gaba da bugawa a jajjere kamar zata tarwatse. Red light daya gani a sashen security na tent din Akhnan ya sanya yaji hannuwansa sun fara rawa.

"Me yasa baka da juriya akan komai daya shafeta?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar duk da rudanin daya samu kansa a ciki.

Haka kawai yaji tsaiwa duba na'urar ma akwai bata lokacine. Kai tsaye ya soma takawa zuwa ga tent din,saidai bawai kai tsaye irin na wanda baisan kan tsaro ba.....ba kai tsaye irin na ordinary mutane ba. Tun daga nesa idanunsa suna kan tent din,ba wani alamun rikici ko hargitsi ko hayaniya daga qofar da dukkanin idanu suke iya kalla. Ji yakeyi kamar na tunzurashi.....ji yakeyi kamar ana jansa zuwa cikin tent din,amma wannan kalmar.....wannan kalmar daya dade yana horas da na qasa dashi cikin aikinsu ta taso ga danneshi

*"WANDA YASAN YAQI.....BAYA SHIGA TA QOFAR DA YASAN ANA JIRA"* Wannan wata babbar magana ce cikin aikinsu.....wata babbar qofar nasara ce ga aikinsu. Abu daya kacal ya danna a wayarsa duk wai security dake gurin ya koma bakin iyakarsa da shirin kota kwana. Cikin qasa da minti daya gurin ya zama kewaye dasu da wani yanayin da ba lallai yasan gurin ya samu tsaro da kewayewarsu ba.

Sawu ya fara dubawa......yana daya daga cikin dalilin da ba wanda ya sanshi saishi. Shi ya sanya aka yiwa dukkan wani wanda zai aikin bada tsaro a gurin takalminsa na daban......sawu yana daya daga cikin abu me amfani a aikinsu. Kuma ko a yanzun ya gane,ya iya tsame sawayen security din duk da suka wuce,saidai kafcecen sawu guda daya daya gani ya sake harba wani abu a zuciyarsa. Kama me laifi a guri irin wannan dake da tent ba gine gine ba,abune da yake buqatar qwarewa. Motsi ko gilmawarka tana iya bada inuwa da haske ga wanda ke giftaku ta waje,don haka yayi plate a gurin,da wani salon tafiya kamar me ninqaya ya soma zagayawa zuwa bayan tent din.

Readers Also Read

More by Huguma