L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 80
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 80: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 80. "Da alama kinaso kisha wahala" Ya fada yana sakin duvet…
3,356 words
"Da alama kinaso kisha wahala" Ya fada yana sakin duvet din,sannan ya fara ware tsummar hannunsa. Cikin wani dan qaramin hanyoyin kariya da aka koya musu kasancewar yana daya daga cikin abinda jinin sarauta ya kamata ya iya cikin masarautu irin nasu ta dauke numfashinta sanda yake karkade tsumman hannun nasa cikin mugunta yana dariya,kafin ya cillar da tsummar yana haurawa saman gadon da wani irin kuxari yana jin cewa lokaci yayi da zai dauketa su wuce.
Muguwar razanar da tayi ganin yana haurowa ya sanyata bude bakinta da nufin qwalla qara.....wannan abun yayi sanadin shaqar kadan daga cikin qurar hodar daya badeta da gurin don gusar da hankalinta.
Yadda yaga bayan tent din a fafaye a qasa tamkar an zubda tabarma ya sakashi mqewa cikin zafin nama. Baisan yadda akayi yakai kansa cikin tent din ba.....bai sani ba da qafa ne?,ko saman iska ne duka bazai tantance ba.......saidai kuma abinda ya gani ya zane masa wani abu mafi munin kallo a rayuwarsa gaba daya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tamim baqe baqe saman gadon da yabar Akhnan tana bacci cikin kwanciyar hankali?.
Bai gane komai a sannan......baya fahimtar komai a lokacin......lokacin da tamim hankalinsa ya karkata kan yadda xai jawo Akhnan daga saman gado zuwa qasa donsu fice daga tent din.....daidai lokacin yaji wata azaba tana ratsa tsintsiyar hannunsa,azabar data sanyashi buga wani irin gigitaccen ihu kafin ya kalli hannunsa dake lilo jikin tsoka da fatar jikinsa,saidai ko wanda ya aikata masa hakan bai samu daman daga kansa zuwa gareshi ba yaji an fincikoshi zuwa qasa an watsar duk da irin girma jiki nauyi da qarfinsa,kansa ya bugu da gefan qarfen tent din guda daya,ya runtse idanunsa yana jin wata sabuwar azabar.
A hautsine ya haura saman gadon yana yayubo dukka duvet din,duk da nauyinsa.....duk da girmansa da fadinsa turashi yake kawai a jikin Akhnan din yana lullube jikinta kanta dake a bude iskar data samu cikakkiyar hanyar shigowa tana kada gashin nata. Zuciyarsa ke wani irin bugu kamar ta shirya tarwatsewa tayi pieces a qirjinsa,baya gane komai sai yadda zai suturce duk wani abu tattare da ita da idanu ke iya gani,cikin wani rudewa da rawar jiki,duvet din yana zamewa saboda yayi kauri da yawa amma yana sake tattareshi a jikinta.
"Bai miki komai ba.......bai miki komai ba?" Ya samu kansa da maimaitawa.
Idanunta a kansa.......duk da nata kalar tashin hankalin da takeji sai taga salaama ne.....duk da rudewar da takeji da yadda taji numfashinta ya fara mata nauyi a qirjinta sai take ganin kamar cikin aminci take akan abinda take iya hanga daga qwayar idanunsa.
Sanda ya bude idanunsa......sanda ya sauke idanunsa akan haisam daya samu nasarar lulluba mata babban mayafi sai yaji ALQIYAMARSA TA TSAYA.......sai yake hangen wata irin jar wuta tana fita daga fuskarsa dama motsinsa gaba daya.
"Ko bazaka tsira ba.....ka gwada guduwa" Zuciyarsa ta raya masa,saiya miqe da hanzari saidai rudewar da yayi tasa ya manta da ragargajajjen hannunsa yayi nufin dafa qasa dashi. Azabar da yaji ya sakashi sakin wani nishin yana danne ihun daya taso masa. Yadda yaga hankalinsa ya raja'a a kanta,ya sani yana sakin ihu zai tuna dashi dake yashe a wajen wannan dalilin ya sakashi danne ihunsa,ya miqe ya soma takawa da wani irin gudu ta inda ya yage tent din,zuciyarsa tana yaudararsa da cewa tabbas yana haurawa nan ya tsira.
Yadda jikinta yayi week ya sanya ta aza kanta samam kafadarsa,tanason gaya masa ne numfashinta yana riqewa......tanason gaya masa tana jin kamar numfashinta zai kubce mata amma ta kasa bude bakinta.
Sosai ya riqeta cikin jikinsa yana zube idanunsa akan tamim dake kwasar gudu iya qarfinsa. Da hannunsa yakeson ya kamashi......da hannunsa yakeson ya damqeshi,.....kamar yadda da kansa yakeson duk wani abu da tamim ya kamata ya fuskanta ya zamana shi ya zaba masa. Sakinta yayi a hankali a hannun birra data dimauce,birran da ita kadai ta shigo tent din ita shehnaz da aisa,kowa yana daga wajen tent din saboda bin qa'ida da kiyaye haddi.
A rungume take a jikin aisa da shehnaz......saidai kuma duk yadda idanunta sukaso su lumshe su rufe kansu da kansu ta hanasu yin hakan. Shi take hange daga inda take kwance,kai tsaye shi kadai idanunta suke hange. Wani irin gudu yake kamar mayunwacin zaki......wani irin gudu yake cikin yashi duk da wahalar da hakan yake dashi ga dabbobo ababen hawa ballantana kuma dan adam......yana kuma dakatar da duk wanda yayi yunqurin biyoshi,har zuwa sanda ya saka hannu ya damqo tamim yana warwaro dashi da hannu daya daga tudun yashin da yahau,sannan ya jashi kamar kayan wanki yana adanashi zuwa duhuwar bayan yashin.
*_SHUD'EWAR MINTUNA BIYAR_*
"Ku adanashi beeno.....a raye nake nufi" Haisam ya fadi yana tsallake tamim da ya yiwa wani d'aurin butar malam,hanyar fitar numfashinsa kawai yabar masa,shima saboda da gaske yana buqatar tamim din a raye kaman yadda yace.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261 KO 08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 137*
★Gaba daya qwayar idanunta tana cikin nasa......kamar yadda nashi qwayar idanun dama fuskarsa suke dab da tata fuskar.
Yanayi ne da takejin ya kamata ta damu da wani abu daban.......yanayi ne da takejin ya kamata ta ace wani tsoro.....firgici da rudani ne yake mamaye da ita.......amma dukka sabanin wannan takeji a tattare da ita. Idanunsa kawai take kalla.....fuskarsa kawa take iya gani wadda inches kadanne suka rabata da tata fuskar. Tana iya gane wasu abubuwa......amma abubuwan dashi kadai suka shafa. Numfashinta yana barazanar dauke mata.....bata iya gane ko tantance komai........bata kuma iyajin sautin komai......amma tana iya jin nasa sautin......tana iya jin sautin muryarsa,tana kuma iya jin tattausan tafin hannunsa da yake cikin nata. Cikin harshen French yake mata magana.....cikin wannan yanayin karya harshen.....wannan accent din da tafison ji sama da sauran sautika tun wandancan satittikan. Tana iya jin dumin daya tafin hannun nasa dake kwance gefan fuskarta yana shafawa a hankali daga sama zuwa qasa,tana kuma iya ganin zallar tashin hankali saman fuskarsa. Fes take hangen yadda launin fuskarsa ya sauya,har wani jajajaja take......tana iya ganin kuma zallar madarar fushi dake yawo tsakanin idanuwansa guda biyu.
"Kija numfashi......karkiji tsoro......ina tare dake......ba abinda zai cutar dake......ba wanda ya isa ya sake cutar dake.....kijia numfashi......ja numfashi akhnaaann.......a hankali......kija saiki saukeshi ki sake jan wani......zaki iya,.......zaki iya......zaki iyaaaa" Ya fada yana matsa hannunta dake cikin nasa.
Wani qaimi maganganunsa suka bata,wani tabbaci maganganunsa suka bata,ta fusgi numfashin da wani irin qarfi ta sauke.
"Eheeen......sake ja.....sake maimaitawa" Ya fadi da confidence yana sake matsawa sosai dab da ita kamar yana bata support da nashi numfashin da kuma bugun zuciyarsa ta hanyar matso da hannunta cikin qirjinsa yana sake sarqafe yatsunsu.
Sake maimaitawa tayi yana kuma cewa ta sake. Sannu a hankali numfashin nata ya fara daidaita,abinda ya saukar da relief cikin zuciyar morsa safiyya sultane,nannie shehnaz aisa birra dama sultane dake tsaye a gurin cikin babban bedroom din haisam din dake bangarensa cikin masarautar agadez din.
"Kawomin ruwa kadan" Haisam din yace da birra cikin bada umarni,still hannunsa dama idonsa suna kan Akhnan din.
A gaggauce birra ta kawo,yakai cup din bakinsa ya tofa gajeriyar addu'a sannan ya saka mata a bakinta bayan ya tallafota. Kadan ya bata tasha ya janye,ya saka mata pillow yadda zai dago mata kanta sosai,ya sake jan kujerar gaban gadon sosai kaman zai haura yana duban yadda numfashinta ke sama da qasa.
"Astagfirullahal azeem.....astagfirullahal azeem" Ya fara maimaitawa can qasa da wani irin softness sosai cikin muryarsa. Lumshe ido tayi tana jin wani hawaye yana taruwa a idanunta. Wani irin abu me girma da tasiri take hanga cikin idanunsa......abunda yafi girma da nauyi a zuciyarta sama da abinda ya sameta.....domin kuwa tayi imani da yaqinin Allah bazai taba bawa tamim ikon keta mata haddi ba.
Istigfar din da yakeyi dab da kunnuwanta shike saukar mata da nutsuwa. A hankali taji ta soma motsa labbanta,a hankali taji ta fara maimaitawa itama.
Wani hawaye ne ya cika idanun sultane harma da morsa safiyya,wani yanayi sukeji su kansu me saukar da nutsuwa. Zuciyar sultane din ta karye sosai.......tabbas akwai wata nutsuwa da hangen nesa ga ma'abota addini,sai ya daga hannu yana yiwa kowa da kowa alamun ya fice ciki kuwa harda shi.
"Alhamdulillah......na gode,na gode da baki gaza ba.....na gode da bakiyi qasa a gwiwa ba,na gode da kika dage sai an jona rayuwar Akhnan da mijin da zai ma rayuwarta jagora duniya da lahira" Sultane yace da morsa sanda suke komawa sassansa yana damqe hannunta cikin nasa.
Hawaye ne ya sauko zuwa saman fuskar momma,tayi qasa da kanta tana duban sultane.
"Tsoro nakeji bappi.....me yasa tamim ya aikata haka?....tsoro nakeji kada ya sake dawowa ya sake cutar da ita,tunda ba tabbacin an kamashi". Murmushi ya sake me sanyi.....wani kalar murmushi dake nuna tsantsar kwanciyar hankalinsa.
" Be fada bane......kuma nasan bazai fadawa kowa ba......amma tabbas tamim yana hannunsa. Yadda be fada ba bazan nuna masa na gane na,bazan kuma matsa da tambayar ina ya kaishi ba?,ko kuma wanne hukunci zai masa ba.....abu daya zanyi......zan tabbatar sati be zagayo ya samesu a agadez ba......ya dauki matarsa sudan matsa daga nan.......idan sun tashi dawowa ina fatan ganin kusancin da yafi wannan.....na godewa Allah.....ko a yanzu na fadi na mutu zan kwanta a kabarina cikin salama......nasan inda nakai diyar safeena". Karyewa zuciyar morsa tayi,saita samu kanta da shigewa jikin sultane din tana hawaye sosai.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ka daina fada......bakai ba safeena ba KHADEEJA......me zan zauna kenan nayi a duniya" Murmushi ya saki yana riqe hannunta sosai a nashi.
"Wataqila ke zaki riqe jikokina....ke kadai zaki dauki jikokin safeena da hannunki" Kuka ne me nauyi ya balle mata,kukan da daga qarshe sultane ya fahimci daga zuciyarta yake,kuma da gaske ya taba zuciyarta da abinda ya fada din,tilas yaja hannunta ciki yana qoqarin lallashi.
*M A M M I N A*
Idan akace jikin mutum yana rawa kamar mazari a baya daukan abun takeyi da wasa. Saboda abu daya ta sani,rawar mazari da ba abu bane na wasa da jikin dan adam zai iya yinsa,amma kuma a yau ta tabbatar bisa yaqini da abinda taji nata jikin yanayi da gaske har sama da haka dan adam zai iyayi idan tashin hankali ya girmama.
Sanda ta miqe daga labarin da daya daga cikin hadimanta suka bata na abinda ya faru a gurin festival jiya......jiyan data zo mata da wani asararren bacci da batasan me yasa ta yishi ba.....baccin daba wanda ya tadata sai bayan sallar asuba data tashi da kanta.
Ba farmakar Akhnan bane damuwarta ba......ba yadda aka ceto Akhnan din da qyar ne damuwarta ba......damuwarta shine B'ATAN TAMIM.
Tana ji a jikinta ba guduwa tamim yayi ba kamar yadda kowa yake fada......tana jin cewa qirqirarren labari ne wannan......an shirya a fadi hakanne saboda akwai wani birnannen abu a qasa.
"Idan tamim ya bata......idan ba'a gama tamim ba ya tabbata daukeshi akayi kaman yadda aka dauke almaz.......ya tabbata wanda ya dauke almaz shine ya dauke tamim......inde kuma wanda ya dauke tamim shine wanda ya dauke almaz tabbas ba kowa bane wannan sai sheikh muhammad haisam!!!" Mammina ta furta a sarari dukkanin muryarta da jikinta suna rawa.
Qasa tafisu tayi da kanta,cikin nuna salo na girmamawa.
"Ranki ya dade......karki jefa zargi a inda zai iya jawo miki matsala......nutsuwa itace jigon komai.....ki nutsu tukunna".
"Bazan iya ba tafisu.....bazan boye miki ba.......a yanzu na fara jin tsoro......ya kamata na fara kammale jama'ata da dukkan wanda yasan sirrin ciki na........ina yalwa?" Qasa tafisu ta sakeyi da kanta,tana jin da wanne irin yare zata gayawa mammina?. Saidai tasan dole ta gaya mata,don nan bada jimawa ba zata sake neman yalwa din.
"Yalwa......ba'aga yalwa ba tun daren jiya". Maganar ta sauka saman kan mammina,ta kuma tilasta mata durqushewa tana zama dirshan a gurin.
"Ba'a ganta ba?,taje wani gurin ko itama ta bace?"
"Zargin dauketan yafi qarfi ranki ya dade.....don har gidanta nasa an duba don tazo ta kula dake jiya da naga kinyi nauyin bacci,amma har yanzu ba wanda ya bani tabbacin inda take"
"Innalillahi....innalillahi" Mammina ta fada tana dafe kanta.
"Kan dai?" Tafisu ta daga kanta a hargitse tana tambayar mammina.
"Shine tafisu.....maganina". Da sassarfa ta saketa ta kuma juya zuwa inda tasan an zube magungunan.
★Da wani irin naiyun qirji yake takowa zuwa sassan Akhnan din,da wani irin yanayi da duk wanda ya kalli fuskarsa yasan ba yanayinsa bane. Baida yawan fara'a,baida yawan sake fuska,amma kuma wannan hasken......wannan haibar tasa ya sanya zakaga fuskarsa da wani annuri koda yaushe.
Cikin girmamawa dukkan hadiman ke gaidashi.....cikin wani qarin girma da karamci bisa yadda labarin kariyar daya bawa diyar shugabansu mafi soyuwa a zukatansu kariya.
Har zuwa sanda ya isa qofar da zata sadashi da living room din da birra tace masa suna ciki.
Da nutsatsiyar sallama ya tura qofar dakin ya shiga,sallamar da taja hankalinta momma dake zaune tana shafa mata man zafi a qafarta,yanayin daya sanya Akhnan ta dinga satar kallonta.
Sallamar da still ta fusgi zuciya da hankalin Akhnan din wadda ke riqe da bowl tana shan farfesu a hankali.
A jiyan ta sani....har sanda bacci ya dauketa yana zaune a gabanta. Har sanda bacci ya dauketa hannunsa da Jikinsa yana manne da nata,abinda ya bata wani irin peace da bata taba sanin akwaishi ba a rayuwarta. Abubuwan dake faruwa da ita wadanda basu kai girma da hatsarin wannan ba sunsha gigitata,to amma batasan me yasa ba.....wannan din yakai girman da zata gigice.....amma wani peace take samu a ranta. Me yasa?,SHINE SILA.....SANADINSA NE. abinda zuciyarta ke gaya mata kenan. Sanda ta farka momma ta samu ta maye gurbinsa,ita ta kwana da ita.....ita ta zauna a gabanta,ta kwana a gabanta idanunta biyu. Taga zahirin maganar nan da ake cewa yadda naga rana haka naga dare......tsakanin momma da haisam din dukkaninsu tana iya ganin yadda suka raba daren a tsakaninsu suka raba baccinsu. Ko qarfe uku da rabi na dare ta jishi ya sake shigowa,ta jishi yana tambayar momma game da ita,saidai daga wannan lokacin bata sake ganinsa ba sai yanzu.
Da wani irin qauna da girma momma ta sauke man tana rufeshi,fuskarta fal da murmushi tana gyara zamanta,irin yadda kowacce uwa keji a sanda surukinta yake gurin.
"Sannu muhammad......sannu da qoqari" Momma ta amsa masa sanda yake gaidata da wani irin girma da martabawa. Ko meye zai mata yana jin kamar ya yiwa nanay dinsa ne. Kowacce girmamawa yana jin kamar ya girmama nanay dinsa ne,ya cancanci kalar kowanne girmamawa.
Miqewa tsam momma tayi,saidai ya dakatar da ita ta hanyar fadin.
"Ba jimawa zanyi ba......akwai inda zanje,wataqila na kwana biyu" Maganan ya tsaida momma. Tana jin meye dalilin da ya gaya mata zaije wani guri?,bata da hurumin tambayarsa......amma a ranta tana jin kamar ba lokacin da zaice zaije wani guri bane. Tafiyarsu duka duka ba zata haura kwana hudu ba,don sultane ya kammala shirin komai,to amma kuma hakan sai takejin kamar wata qarin dama ne da zata qarasa shirya Akhnan din.
"Allah ya bada sa'a.....yayi jagora yayi riqo da hannaye" Kai ya gyada a hankali,zuciyarsa tana masa nauyi. Tausayinsu ne dukka yake kamashi......ita nanay dinsa.....na Akhnan me sauqi ne don yana jin a yanzu a wannan lokacin,a kuma wannan qadamin ko mummunan quda baida ikon qarasowa gurinta,baida ikon sauka a jikinta ballantana wani dan adam. Sultane mutum ne na gaske.....me nuna qauna ta gaske.....ya cancani komai don kare gudan jininsa. SAFEENA wani ruhi ne da kadan Allah ya halitta a jikin mutane......dattakonta da sadaukarwarta da tata kalar qaunar ta gaske ta cancanci KARIYA da KAARA.
Shuru ya wanzu a dakin sanda momma ta fita zuwa daya parlor din,ta zabi ta basu guri ne saboda tana ganin abinda ya dace kenan.
Idanunsa kar a kanta,ba abinda yake dawomasa a duk sanda zai kalleta sai abinda ya faru. Har yanzu yanajin wani abu daya dunqule masa tsakanin wuyansa da qirjinsa me d'aci
"TAMIM FA?" Abinda yaketa maimaitawa kenan cikin ransa,saidai mamakinsa ya sassuta ya juye zuwa tsananin fushi a sanda omar ya fara turo masa wasu bayanai.
Ya kasa haquri omar din,ya kasa jurewa kaman yadda haisam ya buqata,bayanan kawai da haisam din ya gani daga omar ya sani.......za'a samu ninkinsu daga gurin tamim....muma qila sune cikamakin bayanan da yake jiran samu,don haka ya yanke kawo qarshen komai a kwana biyu kacal.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 138*
Tazara ce sosai a tsakaninsu,amma tana jinsa ne tamkar kusa da ita.......yana ci gaba da kallonta shima yana ganin wani irin sanyi a tattare da ita. Kwana daya kacal amma kuma fuskarta ta nuna wata irin rama ta fitar hankali a tattare da ita. Ya motsa bakinsa zai magana,na'ura ta nuna masa kira daga abeer. Abeer din yaketa jira.......jiran Aberdeen yafi zame masa wani mafi munin jira daya zauna yana lissafa wucewar kowanne second da mintuna da suka shude tsakani awanni sha biyun nan.
Ta qasan ido take satar kallonsa sanda ya danna wani button jikin agogon dake daure a hannunsa. Wani irin sassanyan kwarjini fuskarsa yake fitarwa,wani irin yanayi daya cakuda da daurewa da miskilancin da a yau ta fara ganinsa qarara tattare dashi. Fuskarsa a daren jiya......yanayin daya shiga wanda batajin akwai d'a namijin data taba ganin haka tattare dashi saboda ita.
"Sun kammala obbo......an gamasu gaba daya".
"Ma sha Allah.....on my way" Ya furta yana jin wani abu guda daya ya saki daga abubuwan dake danne da zuciyarsa. Idanunta ta lumshe a hankali,tana jin wani abu me kama da BURGEWA yana sauka saman zuciyarta. Yadda yayi maganar da wani irin nutsuwa da maturity sai takejin kaman a yau ne ta fara ganinsa yana magana.
Kujerar da momma ta tashi ya qarasa,ya zauna akai yana sake janta gaba kadan idanunsa a kanta. Ta motsa labbanta tana sarrafa tunaninta,zata gaidashi ne yadda take gaida sultane?,ko zataci gaba da shuru?,. Kamar ya karanci haka daga gareta saiya hutar da ita ta hanyar fadin.
"Kin tashi lafiya?,ya jikin naki?"
"Alhamdulillah" Ta samu kanta da fada tana danyin qasa da kanta. Kai ya jinjina,shuru yana sake ratsawa a tsakaninsu,kafin ya sake magana yana miqewa.
"Koda wani abu zai taso......ban aminta ki dorawa sultane nauyin komai ba.....kisa a kira miki abdii,yawan saurare da karanta qur'ani ya sanyawa zuciya nutsuwa,kiran sunan Allah da tunashi" Yayi maganan yana dosar qofar fita,
Samun kanta tayi da binsa da kallo,tana jin kamar tace masa ya dakata,tana jin kamar tace masa INA ZAKA?,tanajin kamar ta tsaidashi tayi masa tambayoyi masu yawa......amma tana jin wani nauyin hakan.
"Na gode" Bakinta ya subuce ta furta a hankali. Maganan ya bashi mamakin da yaji saukarsa har saman tsakiyar kansa,amma kuma bai juyo ba bai kuma tsaya ba,yadai amsa mata a taqaice da.
"Haqqina ne" Kawai yana qarasa ficewa,saitaja iska qamshin nan nasa yana ratsa kowacce kafa ta kwanyarta da zuciyarta yana hudawa da wani abu me sanyi.
★Ba zuciyarsa kadai ba.....hatta da gangar jikinsa sun qagauta su isa gidan,wannan dalilin ya sanya yau shi da kansa......prince muhammad haisam aba jifar ke driving motar da kansa,salaana yana zaune a gefe yana jin shugaban nasa kamar ya aza masa wani irin nauyi da tuqashi da yakeyi shi kuma yana zaune cikin motar.
Wani irin gudu yakeyi sosai daya basu daman isa gidan a qasa da awa daya,maimakon awa daya harda wasu mintina daya kamata su dauka a baya.
Sanda suke gifta gidan idanunshi akan tsarin tsaro da aka bawa gidan. Villa street data zama qarin wani matattarar sirri ga zeenatun zaitunaa. Gidan da a yau yakejin muddin bai sanya qafarsa a cikinsa yayi bajakolin komai dake cikinsa ba shi ba jinin aba jifar bane.
Ya dauke idanunsa daga kai yana qarawa motar gudu. Sanda idanunsa suka sauka akan tamim da ya wani kumbure sama da ainihin halittarsa sai yaji jininsa yana tafasa. Ya dauke idanunsa daga kansa yana bulla qaramin garden din dake manne da dakin da tamim din yake yashe.