L u'u l u'u book 2 complete by huguma - Chapter 81
L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 81: L u'u l u'u book 2 complete by huguma Chapter 81. Omar......beeno salawii dama sauran duka manyan team…
998 words
Omar......beeno salawii dama sauran duka manyan team dinsa na agadez ya samu zaune a gurin. Duk da kana ganinsu kasan kowa jininsa akan farce yake......amma hakan bai hanasu shan coffee ba,don ga cups da trays din duka a gurin. Shigowarsa ya sanya kowannensu miqewa......hatta da omar idan aka shiga irin wannan yanayin zare alaqar abota yake dake tsakaninsu. Yana jin haisam a matsayin OGANsa bawai aboki kuma amini ba.
Miqewa ce ta grimamawa......miqewa ce ta mutuntawa,dukansu sai yabisu daya bayan daya suna musabaha gami da tambayar kowa lafiyarsa cikin yaren oromo.
"Ku zauna" Ya fada yana miqa hannunsa ya kuma karbi takardun dake liqe da wani takarda me qarfi daga hannun abeer.
Bai iya minti biyu a tsaye ba ya koma ya zauna......ya koma ya zauna yana qara kallon takardun......ya koma ya zauna yana qara ganin girma istigafari da kiran ismullahil A'azam din daya dinga yi a sanda yake ganawa da mutanen da online direct video call.
Dukkanin takardun zaitunaa ne......dukkanin wani takarda da mammina ke taqama dashi......dukkan wata power da take ganin ta mallaka......power din data dauketa ta dauke asalinta da komai daya shafeta daga ETHIOPIA ya maidata NIGER. A yau komai nata ya canza......a yau gaskiyar asalinta ta canza a dukkan wata ma'aikata......dukkan wata hukumar shige da fice......a yau daga yanzu ba wani abu.....ba wata hujja data ragewa mammina da zatayi riqo da ita kota nunawa duniya da sunan ita din JININ QASAR NIGER CE. da kanta......da kanta zai sanyata ta gayawa duniya ITA MAQARYACIYA CE... Da kanta zai sanyata ta gayawa duniya TA HA'INCI AL'UMMAR NIGER ta musu cushe da qarfa qarfar shigo musu qasa,tare da mallakawa kanta shaidar zama tasu bayan ba haka bane.
Idanunsa ya lumshe yana gyada kai.......ko a iya nan nasararsa ta tsaya yana maraba.....ballantana komai ya gama hawa kan saitin da yakeso.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Waye zai iya?" Yayi tambayar a taqaice yana duban fuskokinsu.
"Zanyi obbo" Dukkaninsu sukayi maganar a kusan tare. Duk da bayajin wani yanayi na dariya ko murmushi,duk da bayajin wani yanayi na nishadi sam a tattare dashi,amma hakan da sukayi sai daya sanya murmushi me sanyi qwace masa. Wannan murmushin nasa da dukkaninsu yake burgesu,wannan murmushin nasa dake cike da kamewa da maturity.
Ya tambayesu ne bawai don yana shakka ko kokwanto ba,ya tambaya ne saboda yasan dukkaninsu zasu ce zauyi.
"A zabi mutum daya.....na bude wata sirrintacciyar hanya.....sirrintacciyar hanya takai tsaye zuwa dakin ajiyar mammina. Takardunta nake buqata gaba daya,sannan a maue gurbinsu da wadannan" Ya fada yana daga takardun dake hannunsa.
"Ni zan saka obbo....don Allah" Salawi ya fada yana riqe takardun da sauri. Ido ya bisu dashi,ba wanda yayi challenge nasa,abinda yake gaya masa sun barwa salawi din.
Ya dasa wannan a zukatansu,ya koya musu yadda zasu so junasu,ya koya musu fifita buqatar dan uwansu akan tasa buqatar......a yanzun shi kansa yana cin moriyar hakan.
"Ya sake cewa wani abu?". Ya kuma tambaya bayan shuru ya ratsa gurin
" Ya bayyana komai" Omar daya qagu ya gayawa haisam wannan amsar ya amsa masa. Idanu ya zubawa omar yana dubansa.
"Da sauri haka?,garin yaya?"
"Waccan hanyar yabi" Beeno ya amsawa haisam,maganan data sanya haisam juyawa ga beeno sannan ya sake maida hankalinsa ga omar.
Dukka girarsa biyu omar ya dagewa haisam din.
"Meye amfanin mazantakar tsinanne......kasan mata nawa ya yiwa fyade?,ka sani ko a musulunci hukuncinsa jefewa ko?" Shuru haisam yayi yana jin wani sanyi yana ratsashi. Samun amini na qwarai....aminin daya fahimci burinka da fatanka ya idar maka dashi tun bakace komai bama rahama ne. Sai ya kasa cewa Omar komai.....ya gama hukunci na farko daya kamata tamim ya karba.
"Omar.....beeno......zamu shiga gidan can,qarfe daya na rana daidai" Ya furta yana miqewa da takardun a hannunsa.
Wani murmushi omar ya saki,burinsa kenan....abun kuma ya masa dadi.
"Ko sha biyunnan kace mu shiga a shirye muke" Ya amsa masa yana murmushin jin dadin zabarsa da haisam din yayi.
Qaramin murmushi ya saki kawai,kafin yace komai kuma Aateeq dake kula da motsin komai na gidan ya shigo.
"Obbo.....me wada ya iso"
"Kaishi daya parlor din" Ya fadi yana miqewa a hankali. Sunan me wada ya sanya omar bin haisam da kallo,kallon da yake cike fal da tambaya da mamaki.
"Me ya kawo me wada kuma gidan nan?" Tambayar dake cizon omar kenan,amma bayan haisam ya kalleshi sai yayi kaman bai fahimta ba ya dauke kansa yana takawa zuwa gaba abinsa.
A nutse yayi sallama,me wada ya amsa yana rusunar da kai cikin girmamawa.
"Bismillah.....zauna" Haisam yace dashi yana zama. Zama shima yayi,yana tattara dubansa ga haisam din.
"Farko dai godiya zan miqa maka......kayi qoqari qwarai......ka kuma taka dukkan rawar daya dace" Haisam ya furta yana jinjina kai. Qasa da kansa me wada yayi yana amsa masa.
"Nine da godiya da wannan damar da aka bani,nine da godiya da akaban damar da zan samu 'yanci bayan shekarun dana kwashe ina bauta" Kai haisam ya gyada a hankali.
"Wannan aikin na wannan zangon ya qare......abinda ya rage yanzu kawai shine.....kasa hankalinka akan kitchen.....akan abincin sultane" Yayi maganan yana duban me wada. Kai ya jinjina yana kallon haisam shima.
"Abun nufi ungo wannan" Yayi maganan yana danna wani madanni daga gefan kujerar da yake kai,budewa gurin yayi,ya sanya hannunsa ya ciro wani abu.
Siriryar kwalba cw me dan tsaho kadan,saidai a cikinta akwai wani baqin abu da koda baka tsiyayoshi ba zaka fahimci yana da kauri. Kai tsaye haisam ya zube idanunsa akan me wada.
"Zaka iya shayar da sultane wannan a duk sanda na buqaci haka daga gareka?" Haisam ya jefa masa tambayar fuskarsa tana tsukewa daga sakewa da sukunin da take dashi a dazu zuwa wani yanayi na daban
*_TOFA!......MEYE HAKA HAISAM KE SHIRIN SHAYAR DA SULTANE?,......SULTANE FA?_*
*_WANNE GIDANNE?,MEYE NE WAI A CIKIN GIDANNAN NA VILLA STREET?.....MAMMINA?......ANYA KUWA ZAKIKAI LABARI?_*
*_AKWAI WANI QUDURI NE AKAN HAISAM DABAN BAYAN QUDURIN CAFKE MAMMINA?,KO KUMA AKWAI WANI ABU DABAN DAMU BAMUSAN DASHI BA?_*
*_A YAU IN SHA ALLAH NAKE SANYA RAN ZAMU SAUKE PART 2 NA LABARIN NAN_*
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)