Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 1

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 1

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 1: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 1. Bismillahir rahmanir raheem

3,354 words

💎 L U'U L U'U

(The diamond)💎

haisam&akhnan tales

H U G U M A

BOOK 03///PAGE 01

AGADEZ

VILLA STREET

Wani irin ginin gida ne wanda yasha banban da dukkanin gidajen dake jerarru kuma tsararrun layukan da anguwar ke dasu.

Daga waje ba zaka bashi wannan martabar da kwarjinin ba,kamar yadda koda wasa ba zaka taba kawowa zaka samu cikin anihin gidan dauke da wani irin gini da tarin tsaron daya daukesu lokaci me dan tsaho kafin su cimma cikin gidan dama target dinsu ba.

A hankali ya sauke babbar takardar daga idanunsa......takardar data kasance launin ruwan bawon lemo wadda ke dauke da wasu irin tarin rubuce rubuce da suka qunshi bayanai masu muhimmancin gaske.

Sanye da wasu irin baqaqen kaya da suka sake bayyanat da ainihin zatinsa......kamalarsa suka kuma cikashi da wani irin kwarjini. Duk da cewa bai bada dama ga duk wanda ke tsaye a gurin ba da zaiga fuskarsa kai tsaye ba.......amma wadannan idanun......wadannan idanun dake jiqe da tarin abubuwa masu yawa da nauyin gaske........suna juyawa ne tsakanin mutanen dake durqushe saman gwiwoyinsu a gabansa. Mutanen da bai taba tunanin sune zai samu cikin gidan ba,duk da ya sani......yana kuma ji a jikinsa tabbas BINNANNUN ABUBUWA ne da zasu iya zama da nauyin da ba kowacce zuciya ce zata iya dauka ba......ya kuma sake gasgata hakan........ya sake amanna lokacin da shiga cikin gidan yake neman zame musu barazana.

Daga faffadan parlor din daya zama ZUCIYAR GIDAN,kuma mahada me hatsarin gaske data game kowacce boyayyar shiyya ta gidan.....boyayyun sasannin da ba lallai ordinary mutum ya iya gani ko ya iya fahimtarsu ba.

Da wata irin nutsuwa ya sauke idanunsa akan mutumin da qirarsa halittarsa da kuma salon shigarsa yasha banban data kowanne mutum dake durqushe a parlor din.

"TAMIM" Sunan ya sake harbawa a kansa da wani irin tarin mamaki da kuma sake jinjina girman zaren dake daure da dukkan wata sarqaqiya. An haifa an kuma qirqirar tare da tabbatar da sunayen TAMIM har uku cikin masarautar agadez. Ba don komai ba,sai don a batar da hankalin masu hankali,a sauya nazari da hangen nesan dukkan wani me tunani a duk sanda za'a furta sunan TAMIM a masarautar agadez,ta inda dukka hankali bazai kai ba.

Da wani irin sanyi ya sake zare idanunsa daga kan mutumin.......mutumin daya dauki shekaru yana wahalar da K'ASARSA......mutumin daya sanya shugabanni masu yawan adadi da suka jagoranci Security Agency dinsu suka kammala wa'adinsu.....suka kuma sauka da tarin burin shigarsa hannunsu.....mutumin daya zama silar jefa tsoro cikin masarautar OROMO.....mutumin daya yanke nutsuwa da dukkan farinciki daga ahalin AJANI AHMED. Kallonsa kawai yana rura wata irin wuta daga zuciyarsa......kallonsa kad'ai yana sanyashi yaji kamar ya yanke dukkan hukuncin daya kamata ace ya fuskanta a lokacin.....saidai kuma akwai saura......akwai kuma lokaci.....ba kuma yanzu ba.....ba'a daidai nan ba.

Yanaso ya zama AIKE ga dukkan wani sassa da rassa sa sukayi tarayya wajen ginashi.....wajen gina laifukansa......wajen tabbatar da wanzuwarsa. Sau biyu yana bude baki da zummar masa magana sai ya maida bakinsa ya rufe. Baya da tabbacin komai da zaice masa.......saidai yayi imanin duk da girman jikinsa.....wannan gangar jikin da yake alfahari yake kuma taqama da ita tayi laushin da har tsakiyar zuciyarsa yasan yana ji. Artabu ne suka fara dasu beeno......daga qarshe dole muhammad haisam yayi taking over......yayi masa wata irin qofar rago ya sanyashi a corner ya shigo hannunsu.

Takun tafiyar dake kusanto gurin ya sakashi maida idanunsa hanyar da sautin yake fitowa. Omar salawii da abeer ne......sai idanunsa suka sauka kan matashin saurayin dake tafe a tsakiyar su.

Dukkan idanuwa haisam ya zuba masa.....kamar yadda shima matashin nasa idanun ke cikin na haisam tamkar yana neman wani abu daban.....wani abu daya banbantashi da sauran halittun dake gurin.

Wannan zuciyar dake kwance cikin qirjij haisam ce ta motsa.......yana jin wani rauni yana tsarga masa. MATASHIN AMSAR TAMBAYARSA NE......fuskarsa kawai AMSA ce ga tarin tambayoyin da basu qarasa warwarewa cikin kansa game da gidan ba.

AJANI qarami yake gani yana takawa da qafafunsa.......ta wani motsin nasa kuma SAFEENA ce. Shine wannan jinjirin......wannan jaririn da aka dauke tun daga ranar haihuwarsa......shine wannan yaron jini na farko.....kuma iri na farko daga jikin safeena.......

Ci gaba da kallonsa haisam yakeyi,sanda suke sake kusanto inda haisam din ke tsaye. Sai yaji kaman qafafunsa sunayin sanyi a sanda yake karantar sigar yaron,don haka ya dunqule dukkanin hannuwansa yana cusasu a aljihun wandonsa yana ci gaba da qarewa matashin kallo.

Idan dai har nazarinsa yana tafiya a yau a daidai......idan dai har abinda idanunsa suna iya gane masa daidai......nutsuwa da wani irin kamewa yake gani qarara tattare da matashin,abinda yasha banban sosai da AHMAD ALMAZ.

Kallon kallon dake Tsakaninsu bai yanke ba,har sai da suka iso dab dasu. Da idanu ya yiwa omar magana,sannan ya maida dubansa akan sauran dukkaninsu. Su dinma da ido kawai ya musu magana suka fahimci me yake nufi,ya juya a hankali ya fara takawa,saidai maganan da tamim babba yayi da yaren oromo ya sanyashi d'an dakatawa kadan.

"Ina kyautata zaton kai din jinin ABA JIFAR NE......IBRAHEEM din da qaddarar salwantar SALEEM magajinsa tazo a hannuna" Yayi maganar da qeqasashen lafazi,da kuma wannan qeqasashiyar zuciyar da a iya lafazinsa kawai ta nuna hakan.

Yaji saukar maganarsa har cikin ransa......yaji saukar dukka lafuzansa gaba daya.......saidai juyawa ya kalleshi a irin wannan yanayin zai iya haifar da komai,don haka sai ya zabi ci gaba da takawa a nutse,muryarsa da wannan haibar ya furta.

"Beeno.......inason a batar da gidan". Gajeriyar maganar data qunshi tarin ma'anonin da baida buqatar tsaiwa fassarawa su abdii din.

A K H N A N

Ba zata ce ga wani abu dake riqe da zuciyarta ba.......amma tabbas akwai wani baqon abu dake ragaita tsakanin zuciyartata zuwa qirjinta.

Wani fayau takeji tsakanin zuciyartata zuwa qirjin nata lokacin data tsinci kanta da sanya karatun qur'ani bayan shuru da kad'aicin da ita ta zabeshi ya mamayi dakin......zuciyarta tana mata tuni da kalamansa na qarshe

"yawan saurare da karanta alqur'ani yana sanya zuciya ta samu nutsuwa"

A hankali haqiqanin yarda da maganarsa yake ratsata,wani irin yanayi me cike da nutsuwar da bata zaton akwai yiwuwar samuwarta ba ga ruhi da gangar jiki bayan fuskantar wata mummunar baraza daga rayuwar dan adam ba itace take ratsata. Sassanyan sautin nan nasa daya samu nasarar shiga kamfanonin dake sarrafa na'urar MP3 na zamani masu zuwa da fitilar gado. Wannan kwantacciyar qira'ar......wannan muryar dake nuna zallar nutsuwar da mamallakinta ya mallaka tun kafinma kakai ga ganin anihin fuskar me muryar.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Kamar ita dai......a yanzun da sautin karatun ke shiga kunnenta da wani irin nutsuwa da sanyi,sai fuskarsa take dawo mata......sai fuskarsa take gilma mata da dukkan wannan motsin nasa dake nuna irin izza da qasaitarsa......tun daga ranar farko a hippodrome.......a hankali har zuwa awanni da lokutan da suka samar da kusanci me girma tsakaninsu....wato festival d'lAîr......ranar da taso zame mata wata mummunar rana da zata shafe tarihinta raga SARAUNIYAR QASAR AGADEZ zuwa wata halitta mafi qasqanci. Saidai taimakon Allah,da kuma wanzuwarsa.......jarumtarsa dama wata irin zarra daya mallaka ya sanya ta kubuta daga wannan mummunan harin.

A hankali ta bude idanunta da zuwansa qarshen suratul baqara wanda yayi daidai da tambayar data harba cikin kwanyarta.

"Akwai wani abu da wani zai sake bata a duniya da yakai darajar abinda yayi mata?" Tambayar ta sauko mata a hankali tana hadewa da wata tambayar data sake zuwa mata.

"Inda ace tamim ya samu nasarar abinda ya qudirta......inda ace abinda ya tsara ya tabbata......inda ace haisam baya tare dasu a wannan lokacin fa?.....me zai faru?. Tambayar data sake buga wani abu me girma a qirjinta,abinda ya tilasta mata lumshe idanunta a karo na biyu,saita samu labbanta ta furta.

"Astagfirullahal azeem" Da wani irin yanayi da ya bayyana cikin kunnuwanta......da wannan muryar tasa......da wannan taushin a sautinsa wanda ya zama tamkar dan jagora a gareta,har zuwa sanda taji yanayinta ya daidaita......yanayin kuma da yazo daidai da fara kiran salla cikin wayarta dake ajiye a gefanta.

Idanu ta zubawa wayar tana kallonts kamar me sauraren jiran wani abu,kiran sallar yana fita a nutse......irin kiran sallar da masjid haramain sukeyi kowanne lokaci na salloli guda biyar din,bata kuma dauke idanunta ba har sai da wayar ta gama kiran sallar.

A hankali ta miqa hannunta ta dauki wayar tana latsawa. Shine ya sanya mata kiran sallar tun a wancan ranar daya kaita wancan gidan......wancan gida dai da batasan har yanzu ina bane?,gidan waye kuma cikin agadez. Kiran sallan da a wancan lokacin takejin ya takura mata.......saboda duk wata sa'ar da lokacin sallah ya shiga zai dameta da bugawa har sai tabar komai taje tayi sallar. Tayi dukka shige shigenta cikin wayar amma kuma ta gaza ganin ta inda ya sauke manhajar,ta kasa gane komai......ta gaza fahimtar komai. A dole ta haqura,har kuma zuwa yanzu data fara sabawa da abin.

"Manzan Allah yayi jan kunne sosai game da sallah......ya gargademu mu kiyaye lokutanta,wata abace da duk kyan ayyukanka idan ka samu naqasu a kanta to bata yadda zaka wuce a gurin Allah.....komai naka.....dukkan ayyukanka sun baci......sallah kadai magani ce......tana gyaran zuciyar dan adam dama ayyukansa,idan ka kyautata sallarka to hatta da zunubai zasuyi qaura daga gareka.....amma idan har kana sallah.....kuma baka daina aikata munana ayyukan da Allah ya hana ba.....ta iya yuwuwa sallarka aslan bata karbuwa........ko batayi yadda Allah yake sonta ba,shi yasa bata tasirantu a kanka gurin hanaka miyagun laifuka ba". Ta tuna d'aya daga cikin maganganunsa da taji a wata rana da suke karatu dasu falaak.

Kafin tayi kowanne motsi birra ta nemi izinin shigowa,kamar kowanne lokaci cikin girmamawa da suka saba bata ta sadda kai.

"Lokacin sallah yayi ranki ya dade" Tayi maganan tana sunkuyar da kanta qasa. Idanu akhnan tadan zuba mata kadan. Karan farko da birra ta soma shigowa don tunasar da ita lokacin sallah?.......to me ya faru?......me ya kawo wannan sauyin?.

Bata tsananta wannan tunanin ba,saboda jikinta dake bata daga inda canjin yazo,sai kawai ta yunqura ta miqe sosai tana zama saman lallausan qaramin gadon hutawar.

"Tanti Aisa ta bayar da saqo......tace a shaida miki ta wuce......tace mu barki basai mun mata iso ba.....mu barki ki huta......amma zata dawo nan da kwanakin tafiyarku taga tashinku in sha Allah" . Ta danji mamaki kadan na tafiyar aisa din a wannan lokacin. Ba lokaci bane daya kamata ace ta tafi din ba,saboda ko kwanakik festival din basu kammala ba bare ayi shirin komawa......

"Akwai wani abun da kike buqata?" Birra ta sake fada a ladabce. Maganan yadan bawa akhnan din mamaki,har sai data waiwaya ta dubi birran. Ta sani......wani sabon abune yin kalar wannan tambayar ga akhnan din.

"Afwan........umarni ne daga abdii wanda ya sameshi daga sheikh muhammad........komai qanqantar buqatarki a sanar a kuma yi abinda ya dace". Ta dauki wasu lokuta kadan tana kallon birra,maganan kuma yana samun wani mazauni na daban yana zama cikin kanta.

Ba yau ne karo na farko da ake kula da buqatunta ba.....ba yau ne lokaci na farko da buqatunta suka zama abun riritawa da kulawa ba......amma a yau dinne takejin komai kaman yasha banban da yadda aka saba mata.

Batace da birra komai ba ta miqe a nutse.

"Ina buqatar zuwa dakin karatu na mai martaba" Ta fadi haka kurum. Haka kawai takejin tana buqatar duba wani littafi daya shafi tarihin manzan Allah. Tanason ta samu haske kan abinda ya shafi ma'aikin da yake yawan cewa yace ko yayi. A yau karo na farko a rayuwarta tana sha'awar duba tarihin rayuwar fiyayyen halitta da yadda yayi rayuwar tasa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261 KO 08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 02*

"An gama" Birra ta furta sannan ta miqe,saidai kuma tadan dakata kadan.

"Saidai morsa safiyya tabar saqo". Ido kawai akhnan ta lumshe kadan tana budesu sanda take qoqarin tura sumar kanta data cika mata kanta cikin siririn band.

"Tace inda zai yiwu,da kin daure kin qarasa karbar ragowar gyaran jikin na kwanakin da suka rage" Kaman ba zata amsa ba......da wannan kalar miskilancin daya zame mata halitta taci gaba da takawa,har takai qofar toilet din sannan ta bada amsa kafin ta shige.

"Zan shiga......bayan na kammala da library din". Haka kawai takejin nauyin a yau karon farko tace da morsa safiyya ba zata amsa tayinta ba......ba kuma zata amsa kiranta ba.

Sanda ta shige bandakin saida birra ta saki qaramin murmushi kadan sannan ta juya ta fice don sanar da fitarta daga sassan nata zuwa sashen da dakin karatu na me martaba yake don a gyara hanya. Doka ce.....kuma tsari ne nata ita kadai......bata tarayyan hanya da kowa a sanda zatayi tattaki cikin gida. Duk wani kai kawo zai dakata a hanyoyin da zata wuce din har sai takai inda tayi niyyar zuwa.

*_H A I S A M_*

D'aure da towel ya fito a qugunsa,towel din da duka duka tsahonsa iya qasan gwiwarsa ne da kadan.....qanqantar towel din ya sanya bai rufe duk wani ginannen jiki da surar qarfi me cike da zati da cikar halitta da Allah yayi masa baiwa da ita ba. Wani yanayi da ba wanda yake bari ya ganshi a haka.....koda kuwa su omar ne.

Sassalkar sumarsa dake d'igar ruwa kadai ta isa ta shaida maka wanka yayi,ya kuma kwarara ruwan daya ratsa cikin wannan sumar tasa ta anihin qabilar oromo da gasken gaske.

Tun daga takunsa zuwa yanayin fuskarsa zaka karanci qarancin kuzari da kuma walwala me tarin yawa dake tattare dashi. Haka yake.....don can cikin kansa yakejin kamar ana wasu qananun tsawawwaki tun daga sanda binciken farko ya kammala akan matashin da amsar daya bashi bayan ya tambayeshi sunansa.

"BANI DA SUNA" Shine kawai sunan daya sani nasa a matsayinsa na cikakken dan adam daya debi shekaru sama da ashirin yana rayuwa.

"JININ AJAANI NE......JININ SULTANE MUHAMMAD HAMMUD NE" Wadannan maganganu guda biyu bayajin akwai wani lokaci yanayi ko sa'a da zasu shafe daga cikin kanshi.

Ko a yanzun daya tsaya gaban qawataccen makeken madubin lafiyayyen master bedroom din nasa.......sai daya cusa yatsunsa dukka goma cikin jiqaqqiyar sumarsa. Yaja iska sosai cikin hunhunsa yana fesarwa bayan ya sauke hannuwansa a qasa.

Yayi cases kala kala na criminals iri iri......yaga tarin abubuwa da suka qara qarfafar imaninsa.......ya shiga cases masu hadarin gaske,ya kuma binciko sannan ya tabbatar da gaskiyar me gaskiya.......amma bai taba ganin zallar qwarewa gurin iya cutarwa.......daukan fansa akan wanda ba ma'abocin laifin ba.......da kuma tsananin bijirewa Allah irin na ZEENATUN ZAITUNA BA.

Manyan idanunsa masu wani irin kyau......irin kyan da ba abinda yake sauya sunansu na KYAWAWA ya lumshe yana sake cusa yatsunsa guda biyar cikin sumarsa gami da budesu fes saman kyakkyawar fuskar nan irin ta matasan oromo masu jini a jika.

Wani irin zafi yakeji daga can cikin zuciyarsa....zafin dake farawa tun daga saman fuskarsa har izuwa gangar jikinsa idan ya tuna AHMAD jini ga akhnan.......yayanta shaqiqinta da bata da kamarshi shi ZAITUNA taso aurawa a matsayin MIJINTA?.

"Ya salam" Ya fadi yana dunqule hannunsa a sanda zuciyarsa ke tambayarsa.

"Inda haka ya faru fa?,inda komai ya faru kaman yadda taso fa?,inda komai ya kasance kamar yadda ta tsara fa?". Wani irin rauni yaji qafafunsa sunyi da wani irin sanyi,kamar a yanzun abun ke shirin tabbata......wani irin rauni da babu kamarsa koda kuwa a runtsin aiki cikin kalolin ayyukansu masu tsananin hatsari da sarqaqiya,sai ya fara komawa da baya a hankali yanajin kamar nauyin dake cikin zuciyarsa shine yake qoqarin rinjayar gangar jikinsa gaba daya.

Yana shirin zama kiran wayarsa ya katse masa wannan hanzarin,ya sanya hannu ya dauki wayar yana duba sunan. Omar ne.......sai yanzu ya tuna ya barshi yana jiransa tsahon lokaci,don haka bai bata lokaci ba ya daga kiran yana fadi a taqaice

"dhiifama,dhufaa jira(afwa,gani nan zuwa)". Omar baice komai ba kamar yadda shima bai jira yaji abinda zaice din ba ya katse wayar,saidai kafin yayi wani yunquri green light ta bashi alama.

Green light ne na musamman daya qirqireshi ya kuma jonashi da duk inda yakeso yake kuma buqata cikin wasu sassa nata dama wasu sassanni na masarautar ba tare da sanin kowa ba. Cikin nutsuwa ya miqe,ya isa inda qaramar na'urar take,ya dauko wata qaramar system dinsa ya koma gefan mulmulallen gadon da yafi kama da qaramar duniya bawai gado ba ya zauna sosai sannan ya soma hada komai daidai da yadda yakeso.

Hannaunsa dafe da stool din daya dora system din yake kallon komai. Ta fito sosai ta cikin allon system din sanda take takawa a nutse birra na biye da ita. Wani irin taku da zaka dauka yauqi ne ko yanga bawai dabi'a na halittarta ba,takun da cikin kowanne yanayi yake iya nuna yadda qasaita kebin jininta. Idanunsa ya zare a hankali yana maidawa gefe inda wayarsa ke ajiye,siririyar ajiyar zuciya ta subuce masa. Wayar ya dauka ya bude da nufin aika saqo,wani abu yana kuncewa daga can qasan zuciyarsa,a yanzun daya sake ganinta sai yakejin rad'ad'in da yakeji a qirjinsa ya ninku......sai wani siririn abu me me kama da tausayi dake huda zuciyarsa a hankali,yanajin kamar ya rasa wani bangare na juriyar iya kallonta na tsahon lokaci,kamar yafi buqatar tsaronta a yanzu sama da kallon nata.

Bugu daya aka daga wayar,ya sakata a kunnensa. Idonsa ya lumshe ya kuma bude lokaci daya,yana jin yadda zuciyarsa har yanzu take ba dadi,cunkushe da wannan abun da yayi masa tsaye da har yanzu ya gaza fassara mene shi. Labbansa ya motsa yana amsa sallamar,wadannan kyawawan labban dake daukan hankali da burgewa.

"Ina zasu fita?".

"Dakin karatu obbo".

"Akwai cikakken tsaro?" Kaman haisam yana gabansa abdii ya gyada kai.

"Akwai obbo" Shuru ya gilma na sakanni kaman bazai amsa ba kafin yace.

"Zaituna ba......inaso a zareta daga cikin jerin sahun mutanen da suke da damar ganinta kai tsaye.....koda kuwa ta buqaci hakan"

"An gama obbo" Abdii ya fadi,amsawar ta abdii kuma ta kawo qarshen maganan tasu,ya maida wayar cikin nutsuwa ya ajiyeta.

Miqewa yayi yayi tattaki zuwa gaban mirror din,har yanzu yana jin kansa a cushe a kuma cunkushe da tarin abubuwa. A duk sanda zai tuna matasan guda biyu......a duk sanda zai tuna abubuwan da suka shude a wannin da suka gabata sai ya sakejin bacin ransa yana ninkuwa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Tsaf ya shirya cikin black trouser da dark olive green shirt. Kalolin da suka zauna da wani irin tsari da kuma dacewa a gangar jikinsa. Sun fidda tsahonsa dama murjewar murdadden jikinsa,kamar yadda suka haska farar fatarsa zuwa fuskarsa da a yau ya amsa cikakken sunansa na MISKILI ZAM.

Sassanyan turaren nasa dai shine abu na qarshe daya maida ya ajiye,sannan ya fara nufar qofa da 'yar sassarfa yana fita,kaman wanda ya tuna da mantuwar wani abu me muhimmanci da yayi.

Takunsa shi ya sanya Omar daga kansa daga tattaunawar kai tsaye da sukeyi da bobbo muhammad dawud ta hanyar kiran kai tsaye na ido da ido wato video call.

"Gashinan bobbo" Omar ya furta a nutse yana tashi ya zauna sosai saman kujerar.

Kai tsaye ya zabi daya daga cikin kujerun dake daura da omar,kuma tun kafin ya zauna ya miqa dogon hannunsa yana jawo fuskar system din zuwa saitin inda zai zauna din sannan ya koma ya zauna a dan gaggauce.

Abeer ya miqa wayoyinsa tare da sign na saka masa charge kafin ya dawo da hankalinsa kan allon system din. Kan bobbo muhammad dawud idanunsa suka sauka,wanda ya zubawa haisam din dukka idanunsa da irin kallon daya tabbatarwa da haisam din nazarinsa bobbo din yakeyi.

Janye idanunsa haisan yayi sanda bobbo Muhammad dawud ya saki qaramin murmushi,har yanzu idanunsa akan fuskar haisam din.

"Me yasa banga alamun farincikin nasara ba saman fuskar muhammadu ba?" Ya furta har qasan zuciyarsa yana mamakin daukewar walwala daga fuskar haisam.

Ba haka ya zata ba,bama shi kadai ba.....dukkan wanda yasan da aikin......dukkan wanda yasan da aikin yana hasashen farincikin nasarar haisam a ranar zai zama na dabanne.

Chapter notes and social links

Bismillahir rahmanir raheem

Readers Also Read

More by Huguma