L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 31
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 31: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 31. Idanunsa ya zame a hankali zuwa santala santalan…
3,373 words
Idanunsa ya zame a hankali zuwa santala santalan qafafunta,yayi sama da dubansa har zuwa qugunta daya fito sosai ya bayyana bajajjun mazaunanta da suka dace da shafaffen cikinta. Yadda ta zauna saman kujerar ba'a daidai ba ya sake fidda shape dinta sosai,ya kuma sake fidda fadi da tudun mazaunanta,don ta karkace bangaren damanta ne sosai,sai hakan ya zamana kakar da gayya ta turosu daga daya side din.
A hankali yaci gaba da bin sassan jikin nata da kallo,har zuwa sanda ya kawo kan mutanen nasa. Wannan gurin da kallo daya tak ya masa yaji kaman qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba......sai kawai ya zube hannuwansa cikin aljihun trouser dinsa ya jingina kafadarsa da jikin qofar,yayi crossing qafafunsa kawai yana ci gaba da narke idanunsa a kansu kamar an bashi aikin kallonta,ko kuma wanda ya shiga gasar iya kallo ta duniya.
"Ya salam.....ya salam sallim sallim" Ya furta yana jin yadda ake jona masa wani wiring na shocking cikin jikinsa gaba daya.
A cikin jikinta ta soma jin she's not comfortable ba kaman dazu ba,amma sanin cewa ita kadai ce cikin gidan ya sanyata jawo plate din farfesun,ta sanya spoon din,amma ta gaza kaiwa bakinta sai juyawa take a hankali. Ta kusa minti daya kafin takai na farko bakinta,yabi dan qaramin bakinnnata da kallo,yana tuna yanayin daya shiga wancan lokacin daya hade bakunansu guri daya......yana tuna abinda ya dinga ji da yadda kowacce wuta ta jikinsa ta dauke masa.
Tana zare spoon din daga bakinta idanunta suna sauka a kansa. Wani bugawa zuciyarta tayi da kyau,bugawar data haddasa mata qwarewa ta ajiye spoon din ta fara tari.
Da sauri ya zare hannunsa daga aljihun wandon ya fara takowa sa sassarfa. Kai tsaye ya isa gaban table din,ya dauki gorar ruwan data kasance ruwan kamfanin masarautar ne,ya bude ya tsiyaya mata a cup a gaggauce ya miqa mata. Ta miqa hannunta tana yin tarin a hankali,ga zatonta zai sakar mata cup dinne,amma sai taji ya hada harda hannunta ya riqe gam ya isar da cup din bakinta,sai data fara sha sannan ya zare hannunsa a hankali ya koma da baya a nutse ya zauna saman kujerar dake opposite din tata yana kallonta. Komai nata da jan aji,komai nata akwai isa a ciki,ko yadda takeshan ruwan kawai zakasan akwai ginshira cikin lamarinta.
Cire cup din tayi daga bakinta,sannan ta soma ajiyeshi a nutse tana sauke numfashi. Idanunta ta daga ta aza a kansa. Still kallonta yake kaman Allah ya aikoshi,fuskarta ta hade sosai tana jin bugun zuciyarta har yanzu bai daidaita ba. Batason wannan kallon......yana sanyata ta daburce gaba daya.....batason wannan kallon saboda yana karanta mata kai tsaye abinda yake cikin zuciyarta. Bataso ta nuna masa rauninta ko wani abu makamancin haka,don haka ba zata tashi ta bar masa gurin ba,hakanan batasan me zatace dashi ba tunda sai yau ya tuna da ita?,don haka ta sake jawo plate din ta maida spoon din da zummar ci gaba daci,amma kallonsa a kanta yayi yawan data kasa hakan,sai kawai ta zabi ci gaba da juya spoon din.
Ya fahimceta duk da batace komai ba,baijin zai iya hana kansa ci gaba da kallonta.....bayajin kuma zai cuci kansa ya janye idanunsa daga kanta,halal ce.....halal dinsa ce.....wannan kallon da yake mata na halal ne......wannan kallon da Allah zai bashi lada ne.....wannan kallon da Allah zai saka ya sake yarda dashi ne,don bai kalli d'iyar kowa ba......bai kalli halalin kowa ba sai nashi.
Spoon daya ya zaro shima cikin wani hadadden abu na silver dake gefe wanda aka adana spoons din a cikinsa. Kai tsaye ya zura cikin bata kwanon,ya kuma yi bismillah ya debo ya fara kaiwa cikinsa.
Yunwa yakeji.....yunwar da bata tashi ba sai a yanzu da yaga abincin gabanta. Yana lissafe kwanaki daya daya har kwana biyar bai zauna yaci abincin kirki ba,uwa uba kuma ga mura da yakejin alamu tana son kamashi. Duk wannan tunanin duk wannan zaman duk wannan cin naman da yake bai dauke idonsa a kanta ko na second daya ba.
Tako ta ina......ta kowanne bangare ya takurata. Kallonsa wani irin dafi yake sauke mata a jikinta wanda ba zata iya jura ba,duk iya yadda take zaton tana da zarrar da zata iya basar masa saita dinga jin kamar idanunsa suna yaye mata kowacce sutura dake jikinta,suturar da wata irin nadamar sakata tazo ta mamayeta,don daidai da bugawar da zuciyarta takeyi ta tabbatar yana iya gani ta d'amammen qirjinta.
Batayi qarya ba.....idanunsa suna kai.....idanunsa suna ankare da wajen yana irga adadin bugun zuciyarta daya tabbatar adadin ya zarta yadda ya kamata ya kasance. Can qasan ransa ya saki murmushin da bai nuna a saman fuskarsa ba. Ya sani fushi take,fushin da ya tabbatar koda ya gaya mata dalilin yinsa ba yarda zatayi ba.
Idanunta ta maida kan plate din da tun naman farko bata sake kai komai bakinta ba,amma yana dab da cinye naman gaba daya.
"To zaman me nake?" Ta tambayi kanta,sai kawai ta ture kujerarta baya da zummar miqewa,saidai kuma kawai taji tattausan tafin hannunsa saman bayan hannunta.
Wani irin abu ya tsarga mata yarrrr a jikinta,tana jin wata kewa me nauyi na wannan tattausan tafin hannun tana ratsata,amma a zahiri saita hade rai ta daga blue eyes dinta ta watsa masa.
"Zaifi kyau ki zauna mu sasanta a nan your royal highness" Ya fada softly yana sake kasheta da wadannan abubuwan dake cikin narkakkun idanunta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Idanma saqo ya aike mata da gaske ya isa har tsakiyar zuciyarta,taji kaman an ragewa qafafunta qwari,to amma ba zata taba yarda ba.
"Me ya faru?,me zamu sasanta?,ba abinda kayimin,kawai zamanka a nan ne banaso,ka tafi" Sune kalaman da takeson gaya masa,amma kamar daukewar ruwa suka dauke daga bakinta,sukaqi bata hadin kai ballantana ta furtasu. Abu daya tayi shine zame hannunta,ta kuma juya ta soma sauka daga gurin,abinda ya bashi full access na ganin komai da komai,da yadda suke juyawa da wani irin yanayi daya fusgi hankalinsa,ya kuma sanya naman tsaiwa saman bakinsa,kafin ya tattara qarfinsa ya hadiyeshi da qyar. Sai kawai ya daina jin duk wani taste na naman,wannan dadin da ya masa ya dauke daga kan harshensa gaba daya,sai ya miqe a nutse yana ture tasa kujerar baya,ya soma takawa da kuzari da burin cinmata sanda take shiga parlour din da daga shi sai bedroom dinta.
Tsaiwa tayi tana zare takalman qafarta don musanyasu da bedroom slippers,ta saka qafa daya,tana zura qafa dayar kawai taji an mata wata kyakkyawar runguma daga baya,rungumar data tabbatar duk iya qarfin halinta bata isa ta qwace ba,rungumar data sanyata taji tana narkewa cikin jikinsa gaba daya,shu'umin turarensa yana gaya mata MUHAMMAD HAISAM NE.
*NA BIYAKU BASHINKU NA JIYA DAI KO?*
*_Assalamu alaikum warahmatullah_*
*_Na gode sosai,na gode da jumurinku,duk da na dauka zamu fahimci juna ni daku sama da haka,shi yasa na yita dagewa ina baku pages sama da yadda nake bayarwa,ashe da saura_*
*_Ko nawa kake samu a komai ma.....dan adam ne kai akwai gajiya,kana buqatar hutu,ballantana rubutu da yake cinye awanni mafi rinjaye na rayuwarka_*
*_kin taba biki na tabbatar,kinsan yadda hidimarsa take,yaushe kika samu kanki sanda kuka fara naki bikin?,yaushe kika gama nutsuwa duka kika koma daidai?_*
*_wannan rubutun da kuke ganin muna muku shi,wallahil azeem ko baci ranki yayi a rana bakya iya rubutun,koda kin takura kanki kinyi kowa pages din zasu zowa me karantawa ba armashi,koda yara ne suke gida baka samun nutsuwar yinsa,har sai basa kusa dake,walwala kike buqata,nutsuwa kike buqata ta gaske kafin yin kowanne page_*
*_wannan ya sanya sau tari da zaku gane haka don marubuci yayi ALLAH YA ISA ga wanda ke fidda masa pages ba zaku zargeshi ba_*
*_shi kadai yasan takura da quncin da yake fuskanta kafin ya hada kowanne page,a haka me sata ya fitar yake zaton ZAICI BULUS A GABAN ALLAH?_*
*_Ina amfani da wannan damar na shaida ma masu fidda mana pages ta kowacce hanya cewa,zanta gayawa Allah inde ban taba satar miki komai ba....ban taba cutar miki da komai ba......to Allah ubangijin al'arshi yayi min sakayya Allah ya isana duk wadda ta fitarmin da pages ta kowacce fuska kuwa,Allah ya sakamin_*
*_Yadda muka killace haqqinmu kayanmu,kuka watsawa duniya UBANGIJI KA BANKADE SIRRINTA DA TAKE ALKINTAWA A IDANUN DUNIYA,ALLAH KARKA SUTURTATA HAR ABADA_*
*_Na gode da jumurin bina da kuke,kuma in sha Allah next time labarinmu zai zamana pages saba'in tamanin kamar yadda aka saba book a baya ayi a qarqareshi_*
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 56*
Ta bayanta daya rungumetan ta dinga jin wani abu yana ratsowa yana watsuwa zuwa ga sassan jikinta. Ko ina na jikinta ya dauki rawa saboda wannan rungumar ta daban ce.....wannan rungumar tasha banban da wadanda ya taba yi mata. Ya matseta sosai cikin jikinsa yana sauke mata numfashinsa cikin kunne. Dukkanin wata tsiga ta jikinta ta zuba,har batasan sanda ta riqe hannayensa dake riqe da qugunta ba tana jin zuciyarta kamar zata b'allo qirjinta ta fito.
Da wani irin zafin nama ya juyo da ita gaba dayansa yana hana kowacce tazara shiga tsakaninsu. Sukayi musayar numfashi lokaci guda kaman yadda qwayar idanuwansu ta hade guri guda.
Qirjinta ne kawai ke dagawa sama da qasa saboda wani irin tsoro daya shigeta,dukkanin idanunta cikin nasa tana duban qwayar idanuwan nan nasa da suka birkice gaba daya. Sosai take jin saukar numfashinsa akan saman fuskarta,da wani irin yanayi cikin qwayar idanunsa me zafi,yana yin daya sanya ta zabi rufe idanuwanta ruf tana sake jin yadda yake bada kusanci a tsakaninsu.
Ta rufe idanunta ne kawai don bata da qarfin jure abinda takeji,GARWASHI kawai take hanga cikin idanunsa,wani irin abu me kaifin gaske dake sukar zuciyarta da wani irin abu me tsananin kaifi,yana ajiye mata wasu ciwuka da batasan ranar warkewarsu ba.
Cikin kunnuwanta takejin cakuduwar numfashinsu guri daya da wani irin banbanci da yabar mata mamaki a tsakiyar rudanin da take ciki. Nasa numfashin me wani irin nauyi ne,ba kamar nata da yake fita da sauri ba.
Wani irin riqo ya sakeyi mata yana jawo qugunta ya manne da jikinsa. Numfashinta ya kusa qwacewa da wata irin shidewa da sai daya tallafota da kyau,yayi mata kyakkyawan riqon dake nuna bazai barta ba.
Hannunsa daya ya sanya ya daga habarta yana kallon qwayoyin idanunta da suke a rufe,saidai duk da haka ga tudunsu nan don Allah ya hore mata baiwar qwayar idanu.
"Regarde-moi dans les yeux(kalli cikin idanuna)" Yayi magana da harshen faransanci,muryarsa can qasa,kamar wanda yake gudun wani yaji abinda yake fada
"Ya salammm" Ta fada can qasan maqoshinta tana jin ta fara rikicewa. Ashe duk sanda zai magana da ita da faransanci a nesa take dashi?,shi yasa batajin yadda kowanne harafi yake fita da wani irin nauyi daga bakinsa......da wani irin qwarewa da wani irin accent da salo na sarrafa harshe?. Me yasa a daidai kunnenta haka zata faru?.
"Ki bude idanunki" Ya sake fadi yana sassauta riqon da yayi mata,saidai yana qaa tsananta kusancin da yake tsakaninsu da wani irin yanayi da yasa ta soma narke masa a jiki,qafafunta suka fara barazana qin daukarta. Kaman ya gane hakan,sai ya sake riqeta sosai cikin jikinsa yana mata kyakkyawan masauki.
"Ki kalleni biftuuu" Ya fada da wani irin taushi da sanyin daya karya mata zuciya,ya kuma sanya hawaye taruwa cikin idanunta.
Wai baya gani ne?,baya lura da yadda zuciyarta ta fara narkewa?. Tayi qanqanta da yawa......tayi qanqanta da daukan yadda yake mata magana haka. Bata saba ba.....ba'a taba mata magana da irin wannan yanayin ba..baya ga haka ma kuma sai ya shigo mata kanshi tsaye?. Baiga laifin da yayi ba yakeson lallai sai ya sanya ikonsa da qarfin qwanjinsa ya zagwanyar mata da zuciya?. Besan zuciyarta batayi wannan girman ba?,batayi wannan qwarin ba?.
"Bude idonki" Ya sake fada yana aza habarsa dake cike da tattausan sajen dake fidda wani kalan qamshi na daban yayi maganan da low tone sama dana dazu.
Ta fahimci da gaske saita bude idanun,ta fahimci rashin bude idanun nata daidai yake da ci gaba da sauke mata ruwan rokoki a jiki da zuciyarta daga sautinsa qamshinsa da yadda ya tilasta cakuduwar jikinsu guri daya.
Da ruwan hawaye a idanunta ta bude blue eyes dinta da launin ya cakuda,sai ya riqe fuskartata da kyau cikin hannuwansa yana dubanta da wani irin kusanci.
"Bance karki tafi ba?,bance ki jirani ba muyi magana ba?" Ya fada a narke kaman wanda ke shirin sakin kuka. Abubuwa da yawa......abubuwa masu nauyi yake gani cikin idanunta,fiye ma da yadda ya zata. Wasu irin alamu da suka sanya ya fara tantamar anya a yau karatun kai tsaye daga zuciya zuwa cikin idanu basuyi masa kuskure ba?.
"Why?....me yasa?" Ya sake fada idanunsa suna qanqancewa,dukkan jikinsa yana saki.
Girgiza masa kai kawai takeyi ta kasa cewa komai,duk da yadda taso ta dakatar da hawayen fuskarta abun yaci tura,sai kawai suka gangaro ta gefe da gefan idanunta.
Da kallo yabi hawayen har suka dige.....wani hawaye da suke qyalli a idanunsa kamar sunfi na kowa kyau da haske.
"Kuka?" Ya tambayeta da wata murya da tafi kama da muryar wanda yasha giya ya qoshi.
"No" Ya fada yana girgiza mata kai,sai ya sake riqe fuskarta sosai cikin hannunsa,ya sanya fuskarsa cikin nata,sai kawai ta tsinci harshensa saman fuskarta.
Lashe duk wata hanya da hawayen yabi yakeyi yana sauke mata wani irin rikitaccen numfashi. Cikin lokaci madan ta dimauce ta rikice,qoqarin magana take.....qoqarin roqarsa take amma kaman yasan hakan zatayi saiya hade bakunansu guri daya da wani irin zazzafan kiss. Wani irin kiss da yasha banban matuqa dana wancan ranar,tana jin sanda qafafunta suka saki gaba daya suka gagara daukarta saboda ba wani kuzari da karsashi daya rage musu. Tana jin sanda ya sanya ragowar qarfin daya rage masa ya tallafesu gaba daya shi da ita ya qara taku uku zuwa hudu shi da ita dake cikin jikinsa ya qarasa dakin dasu.
Shi bai iya wani dogon tsaiwa ba suka zube gaba dayansu saman gadon da baida nisa da bakin qofar. Wani kyakkyawan riqo yayi mata kamar wancan ranar,ya hana bakinta aiwatar da komai,sannan taji hannunsa yana laluben zip din da shine ya hade gaban rigar tun daga sama har qasa.
Tsoro ne ya kamata,wani irin tsoro daya sanya cikin rawar hannu ta cafki hannunsa ta niyyar janyewa,shi kuma kawai sai ya sakar mata nauyinsa gaba daya. Nauyin daya sanya qirjinta qara nauyi,numfashinta ya dinfa fita da wani irin yanayi. Hannunsa ya cusa ta tsakanin qirjinsu ya lalubi zip din,ya masa kyakkyawar zuga guda daya tak sai gashi yakai qarshe.
Qaramin hauka ya shiga sanda idanunsa suka kai masa kan albarkatunsa. A yau ma ya taki sa'a,ba bra saboda rigar me roba ce,ta hade mata jikinta sosai.
A wancan ranar ba wadataccen haske......a yau kuwa haske ne tarwai da zai baka daman ganin koda allurarka ce ta fadi. Wani guri wani muhalli da yake ganinsa a yau a bayyane lullube da farar fatar data sake qawatasu.
Tunda hannayensa suka isa gurin komai ya tsaya cak da aiki cikin qwaqwalwarsa,ya daina gane komai sai wani irin saqonni da yake aike mata masu zafi da gusar da hankali.
Karon farko ta fara qoqarin bore.....karan farko ta fara qoqarin tawaye,saidai cikin minti goma ya soma kaita wata duniya ta daban,duniyar da batasan da ita ba.
Wani hargitsatsen yanayi suka shiga shi da ita,sosai jikinta ke karbar saqonninn da suka sanya bugun zuciyarta zarta kima sama da kowanne lokaci da zata buga din.
Zuciyarta ce hautsine da wani irin tsoro sanda yake qoqarin rabata da skinny jeans din jikinta.....wani abu guda daya da yaji ya zame masa wani qatoton waigi.....ya zame masa wata babbar barazana me wahalar fuskanta......kamar dai yana shirin ture dutsen dala ko gauron dutse daga ainihin mazauninsa.
Ta samu bakinta a yanzu,don haka gam gam ta riqe hannunsa,saidai ba riqe hannunta ne kawai ba,don bata da wannan qarfin,sunan bappi data sake kira masa ya zare duk wata laka ta jikinsa. Bai matsa daga jikinta ba.....saidai ya sauke mata nauyinsa ta side daya kawai,kwanciyar rub da ciki yana daga sama,ya qanqameta sosai cikin jikinsa yana jin kukan da take rerawa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Bai shirya sakinta yanzu ba.....bai kuma saketan ba,har sai da dumin jikinta da laushin fatarta ya samar masa nutsuwar da yake qoqarin samu. Kaman an fusgeshi haka yayi,ya sake qanqameta kaman zai ballata,abinda ya sake bata tsoro kenan ta kuma fashewa da kuka. Wannan karon me sauti ne kukan,wannan lokacin ba iya hawaye kawai bane.
Tsoro yake bata sosai da gaske a duk sanda ya shiga irin wannan yanayin,sai ta dinga ganinsa kamar ba shine ba.....kamar ba shine ainihin sheikh din data sani ba.
Gumin da yake fita a goshinsa zuwa jikinsa ya soma nasarta,ta cikin t-shirt din suit din jikinsa data rage gumin yake ratsowa da gaurayen qamshin turarensa yana nashe mata jikin fatarta.
"Wanne irin ci amana ne wannan?,saina gayawa bappi,tunda ai yace amanata ya baka" Ta fada muryarta tana rawa sosai kukanta yana sake qaruwa.
Da farko maganan ya masa bambarakwai,sai ya saki wani kasalallen murmushi yana cusa fuskarsa cikin wuyanta yana zuqo qamshinta da kyau,amma yadda ta saki kukan da gaske ya sanya yace bari ya gwada. Qasa ya koma ya birkitota samansa yana qarewa fuskarta kallo wadda doguwar sumarta da aka gyara a dazun ta hargitse ta musu rumfa shi da ita. Tun a dazun tun farkon shigowarsu dakin ya zare siririn band din da aka daure gashin dashi,ya kuma cusa fuskarsa sosai cikin gashin yana shaqar daddadan qamshin hair mist na kamfanin SHUWA INCENSES AND MORE dake tashi da wani sassanyan qamshi me halaka nutsuwar zuciya(+234 704 229 3387).
Hannu ya sanya yana maida gashin zuwa gadon bayanta,ya taso da wani irin zafi zai soma sauke mata sabbin saqonnin daya tabbatar a wannan karon ba zata iya tabuka komai ba.....saidai tun kafin hakan ya faru manyan idanunta suka firfito waje,ta saki kuma sosai tana tokare tafin hannunta saman lallausar gargasar qirjinsa don tuni button na rigarshi ya zame yayi nasa guri.
"Kayi haquri" Ta fada cikin sigar ban tausayi. Maganan yazo masa a bazata.....wani irin ba zata da bai taba zato daga gurin ta ba. Ta cikin idanunta yaga tsoro qarara,tsoron daya sanya kokwanto da mamaki me dimbin yawa a ransa.
Sai ya zameta gefe,amma duk da haka bai saketa ba saboda rawar da jikinsa yakeyi bai gama daidaita ba,sai ya bude qirjinsa sosai ya sakata a ciki yana sauke numfashi. Sautin kukanta ke tashi kadan kadan,sakinta kawai takeso yayi ta matsa gefe. Wani irin rayuwa take gani daban da bata taba kawota a kanta ba.
"Kiyi shuru......" Ya fada a hankali,saidai hakan bai mata tasiri ba sam. Ya lumshe idonsa muryarsa can qasa ya sake fadin.
"Don Allah" Kalmar ta fito mata da wani sanyi daya sanya a hankali sautinta yayi qasa.
Bawai ya samu dukkanin nutsuwa bane.....amma yana qoqarin kame kansa ne kawai. Mamaki ne can qasan ransa. A shekarunta?,a wayewarta?,tana nufin bata da masaniya akan irin wannan abun?.
Kamar bazai gamsu da haka ba.....amma wani halint guda daya tal na fadi da yin abu kai tsaye ya sauya akalar tunaninsa. Ya tuna yadda ta sauyawa falaak bayan ta tabbatar da abinda ya faru,t juya kaman haushinta takeji......wannan duka yana cikin tarko da plan din mammina?,ko tsabar yadda ta killacw rayuwarta take sarrafata cikin tafukan hannayenta ya kawo mata wannan naqasun?.
Baida amsa sam,don haka ya mirgina da sauran kuzarinsa don sauka yayi wanka,don a lokacin yanayin duhun magariba ya tabbatar masa an riga an kammala sallar magariba din.
Miqewar da yayi yaji mararsa a qulle sosai. Zafin ya ratashi sosai,yasan hakan zata iya faruwa,don lokaci lokaci yana fuskantar irin wannan issue din.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862