Kenza eBookz

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 44

L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 44

L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 44: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 44. Har ya gama shiryawa cikin wata tattausar riga cotton…

3,365 words

Har ya gama shiryawa cikin wata tattausar riga cotton me kama da Moroccan thobe bata ko motsa ba. Idanunsa da hankalinsa gaba daya a kanta,ba wani minti da zai shude ba tare daya aza idanunsa a kanta ba. A cikin jinin jikinsa a yanzu yake jinta.....cikin kowanne bugawa ta zuciyarsa da fitar numfashinsa.

Wata madaukakiyar daraja....martaba da kima tata take ninkuwa cikin ransa. Wani matsanancin tausayi da qauna me narka zuciya.

A ransa yakejin zaiyi komai saboda ita....zai iya aikata saboda ita. A baya.....saboda SULTANE ne kawai......amma a yanzun........zaiyi komai SABODA ita.....zaiyi komai saboda ta cancanta,zai aikata komai saboda ita din tasa ce....mallakinsa ce.....kayansa ce ita!.

A baya saboda ETHIOPIA........amma a yanzun yana jin tilas mammina ta karbi hukunci a kurkusa. Saboda KHADEEJA.....saboda BIFTUU.......saboda AKHNAN......saboda matar SHIEKH MUHAMMAD HAUSAM ALSAAMIT (the silence one).

A nutse ya tako inda take kwance,yana qishirwar ganin fuskarta,wannan blue eyes din.....har wannan hawayen nata da suke qarawa eyelashes dinta wani mugun kyau. Amma ya sani duka a yanzun ba abu bane me yiwuwa. Zai taro match ne kawai.

"My princess" Ya furta haruffan sunan da wani irin girmamawa. Ta jishi....taji zamansa kuma dab da ita,taji yadda ya kiratan da wani yanayi na GIRMA,amma kunya ba zata barta ta motsa ba.

"Biftuu" Shuru.

"Akhnan" Shuru.

"Khadeeeeeejaaaah!" Wannan karon kasa daurewa tayi sai data runtse idanunta tana jin yadda tsigar jikinta ta yamutsa.

Yaga alamun saqon ya isa. Yaga reaction nata,saidai shi kansa yasan tayi qoqari da bata nuna ba. Sai ya sanya yatsunsa yana yaye bargon iya kanta,ya sunkuyo daidai fuskarta,abinda ya sanya sauran ruwan dake kansa ya diga mata d'is gefan fuskarta.

Ta runtse idonta,ya saka yatsansa yana dauke ruwan.

"Kaina bisa wuyana.....afuwa nake nema" Ya fada da wani irin laushi,kamar ba shine wannan jarumin ba.....zakin hukumar binciken manyan laifuka na sirri na farin kaya. Kamar ba shine wannan zakin ba......dake iya bibiyar laifi dame aikatashi komai girmansa ba komai tsanani da girman laifin.

"Zan baki guri idan kin zabi shiryawa da kanki,amma idan nakai qofa baki tashi ba.....na samu ticket na taimaka miki da kaina" Ya fadi yana miqewa,ya kuma ja da baya sannan ya fara takawa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 78* _________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee* __________________________

Firgigit tayi,ta miqe ta zauna,saidai tun a zaman ta gane shayi ruwa ne,amma sai ta kanne ta fara yunqurin sauka daga gadon.

"Wayyo bappi" Kalman ta subuce daga bakinta. Abinda ya sanya haisam tsaiwa cak kenan,sannan ya waiwayo a hankali,sai kuma ya juyo gaba daya yana dawowa cikin dakin.

Ba dama ta biyu....ba shawara.....ba kuma dogon tunani ya dauketa cak kamar jaririya,kai tsaye kuma ya wuce bandakin da ita ba tare daya kula da magiya da qananun koke kokenta ba,wanda ya tabbatar tanaso ya sauketa ne,bataso ya sake ganin jikinta a karo na biyu.

★★★Lallausar black slim fit shirt ce a jikinsa me dogon hannu wadda ya nannade hannunta ya barshi iya gwiwar hannun nasa,akwai dan rubutu kadan daga qasan rigar gefan dama da wani gold zare wanda ke dauke da sunan brand na rigar (zegna).

Three quarter ne a jikinsa shima baqi wanda duka kalolin suka cakude suka fidda wannan sassanyar farar kalar fatar tasa.

Yammaci ne.....wanda ya dauki awanni daga abinda ya faru tsakaninsu daga daren jiya zuwa yau. A wannan yammacin,tarin saqonnin da suke fitowa daga sassan nanay zuwa wannan sashen ko daya bai samu isowa garesu ba.

Hadimai da dukka 'yan aikin dake da alhakin kula da sashen a yau sun samu iyaka da sashen,iyakar dasu kansu basu san dalilinta ba.

Shi kadai.....daga shi sai ita ne cikin yinin gaba daya a sassan. Ya lullubeta da wata irin soyayya. Ta rikitashi gaba daya,saboda yinin da tayi tana share hawaye.

Yana ankare da ita,abinda ya hanashi dukkan wani sukuni kenan. Ya sani rigima ce daban takeji kuma,saboda taso ya qyaleta ta kula da kanta,wani abu da shi kuma sam bazai iya ba. Daidai da space da takeso ya bata ya hana mata,ya wuni sir da ita,koda sallolinsa na azahar da la'asar dukka a nan sukayi jam'i ita dashi.

Koda bata gaya masa ba yasan gurin a yanzu ya daina wannan zugin da zafin,don da kansa ya dinga hada mata wani ruwan zafi daya sanya wasu abubuwa da batasan meye ba,wadanda suka sanyaya mata gurin sosai. Har tayi bacci,baccin da ko sanda ta tashi ta sameshi zaune a gefanta riqe da littafi yana dubawa. Yinin ranar waya kawai yake dagawa,duk motsin da zatayi idaninsa akai.

So yake ta kalleshi,amma ya rasa dalilin daya sanya taqi kallonsa kwata kwata. Yayi dukkan qoqarinsa amma ko sau daya taqi yarda ta kalleshi.

Kaman yanzu da yake takowa dauke da wani irin baqar butar shayi,wadda ta dace da shigar jikinsa. Ta saci kallonsa tana ganin yana mata wani irin kyau a idanu da zuciyarta,ya koma mata tamkar BUZU tamkar dan qabilarta.

Cikin sa'a ya kamata,ya kamata da wadannan idanun nasa,ya kalli tsakiyar blue eyes dinnan nata da yaketa shauqin kalla.

Abinda ya gani a cikinsu kuma yaso birkita nutsuwar da yaketa qoqarin samu tun bayan da akayi sallar asuba. Bayan sallar asubar komai ya zame masa sabo. Bayan sallar asuba sai yaji duk duniya ba abinda yake buqata irin ya sake jinsa cikin jikinta. A wannan lokacin,ya yiwa zuciyarsa da gangar jikinsa wani irin qarfa qarfa,sai kawai ya buge da karatun da dole ya dakusar da abinda yakeji,don a sannan yana zaune a gabanta yana gadinta ne.

To amma a yanzun data kalleshi......a yanzun da take sanye da wata gown dark Olive color,silk material da yake shaking yake kuma kwanciya a jikinta,sai yakejin kamar haqurinsa zai iya gazawa.

Zama yayi sosai a gabanta da butar shayinsa. Ya tanqwashe qafafunsa kamar yadda qaramin yaro yakeyi a sanda ake koya masa ladabin zaman cin abinci.

Qoqarin lalubar qwayar idanunta yakeyi amma ta hanashi hakan. Ya narke fuska yana jin yadda take sake janye hankalinsa,yana kuma jin yadda take sake fusgar feelings dinsa xuwa gareta.

"Hey" Ya fadi a nutse da wani sassauqan sauti.

Yadda ya kiratan,tasan ta yiwa kanta qarya idan tace zata iya jurewa bata juya ta kalleshi ba. Batasan da wanne siddabaru yake amfani ba.....a qa'ida ya kamata ta tsaneshi......ya kamata taji haushinsa.....ya kamata ya fita daga ranta saboda ya keta haddi da iyakar da ba'a taba keta mata ba. Amma haka kawai sai takejin wata irin mahaukaciyar soyayyarsa tana hudata.

Ko na minti biyar ya matsa daga inda take,sai taji kaman ya mata nisa ne na shekara biyar. Yadda ya tsareta da idanu ya sanya hawaye taruwa mata a idanu.

Haisam ya lumshe idanunsa tare da budesu lokaci daya,wannan feelings din yana sake fadada cikin jikinsa.

"Shshshshsh.....it's okay" Ya fadi da muryar rada sosai wanda koda kana dab dasu ba lallai kaji ba.

"Look at me" Ya sake fadi yana lalubar qwayar idanunta bayan ya kamo tafukan hannayenta ya riqe cikin nasa. Kai ta girgiza,ta yaya zata iya kallonsa yadda yace?.

Qasa sosai yayi da muryarsa,still bai daina kallonta ba.

"I'm here my healer" Ya fadi da harshen faransanci. Da wannan accent din.....da wannan yanayin dake dimautata

"My healer?.....har ya warke kenan tunda ya mata mugunta jiya?" Ta tambayi kanta tana lumshe idanunta gami da budesu lokaci daya.

Sunan taji ya sauka a ranta da wani irin girman matsayi.

"Giiftii" Ya fada softly. Ta sani,yaudararta yakeso yayi ta juyo ta kalleshi,ita kuma ba zatayi ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Zaki dan qaramin.....don Allah" Ba tare data shirya ba ta waiwayo da hanzarinta. Murmushi me kama da dariya ya kubce masa. Sai a sannan ta fahimceshi yaudararta yakeso yayi,ya tsoratata kenan,don butar shayin gabansa ya nuna mata.

"Wannan.....shi zaki qaramin" Harararsa takeso tayi kaman yadda takewa su sheshnaz,saidai shi kuma ya mata girma da nauyi ta masa hakan,saita dauke kanta kawai.

"Giiftii" Ya sake kiranta da accent na Oromo.

"Zazzabi nake.....da gaske,amanar nanay tana hannunki,ya cancanci na kwanta....ki kula dani" Zuciyarta tadan motsa kadan,a dazu ta yarda tea din yake nufin ta dada masa,amma a yanzu sai taji cikin ma'anar zancansa kamar ba akan kulawa normal yake magana ba.

Kafin shi ko ita wani ya sake cewa komai wayarsa dake cikin jerin security na gidan tayi haske. A kasalance,kamar bazai daga ba ya latsa,muryar ta fito tar ta ciki.

"Mama oromo ta qaraso babban parlor na fuskar yamma".

"Okay" Ya fada a taqaice yana yanke saqon.

A nutse ya tattara idanunsa dukka akan fuskar akhnan yana kallonta.

"Nanay tazo.....tazo dubamu" Ya fadi da wani coolness. A dan tsorace ta daga idanunta tana dubansa,sai taba shi zaune yake hankalinsa kwance yana kallonta da wannan narkakkun idanun nasa dake razanata. Dukka idanunta ta fiddo waje tana dubansa,a hankali yaga yadda idanun nata suka fara tara hawaye.

"Nanay.......kaine?" Kai ya girgiza da sauri.

"Bani na kirata ba.....nasan dama zata shigo dole,zata dubani,zatabi ba'asin aiken da tayo". Sosai taji hankalinta ya tashi,ba nanay ba.....a yau dai ko noorah batajin zata iya kalla ballantana nanay da kanta. Kai koda birra ma,gani take duk wanda ya kalli qwayar idanunta zaiga komai,zaiga komai daya faru tsakaninta dashi a tsakiyar daren jiya.

Qasa tayi da kanta tana qoqarin boye hawayenta.

"Giiftii" Ya kirata a tausashe. Hannunsa ya miqa mata sanda ta daga kan nata,da idanunsa kuma ya mata alama data dora masa nata hannun. Bata musa ba,ta dora din.

"Kalleni" Ya sake fada yana dubanta sosai.

Sau uku tana attempting hakan tana kasawa,sai ana hudun ta samu ta iya tsaida dubanta a kan nasa.

"I'm here with you.....im not going anywhere"

"Tsoro nakeji.....kada nanay ta gane" Dariya yakeso yayi,dariya sosai na irin quruciyar akhnan din. Komai nata yana sake nuna masa irin qarancin shekarun da take dashi,komai nata yana sake nuna masa bata da wani experience na rayuwa,an karkata tunaninta ne kawai akan izzarta mulkinta sarauta da kamfaninta.

"You're safe" Ya fada a taqaice,saidai yadda take kallonsa ne kamar bata gamsu ba,har sai daya sake maimaitawa.

"......With me.....you're safe,ba wani abu da zan bari ya sameki..." Kanta ta gyada a hankali,ya miqe tare da ita yana fadin.

"Ki komai normal yadda kika saba....karki wani abu da nanay zata dauka naci amanarta ne...." Ya fadi da guntun murmushi.

Waiwayawa tayi idanu a narke tana kallonsa,kallon data masan wanda ya masa kyau ainun,ya danne dariyarsa,wasu hawayen suna taruwa.

"Kaine ka jawomin.....kuma saina gaya mata k......"

"......kin kwanta da mijinki a darenku na farko?" Ya qarashe mata maganan yana katse mata numfashi gami da dage mata dukka girarsa.

Wata irin kunya me bala'in nauyi ta taso ya danneta,ta rasa inda zata boye fuskarta taji dadi,sai kawai ta sake masa kuka,shi kuma ya bude mata dukka qirjinsa yana rungumeta,damar da yake jira kenan dama ya samu.

Tun asuba yake neman dalilin rungumeta amma bai samu ba,a yanzun daya samu damar sai ya mata kyakkyawan riqon da ya tayar masa da duk wani tsumi na jikinsa,ya dinga sauke boyayyen numfashi yana kuma lallashinta a hankali cikin dabara tare da sake mannata a jikinsa sosai idanunsa suna lumshewa tare da budewa duka lokaci guda.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 79* ________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX _________________________

"Tu es détendue?(“Are you feeling relaxed now?)" Ya fada yana hada sautinsa da qyar cikin maqoshinsa saboda yadda yaji komai yana son sake kwance masa,kamar ma baiyi komai ba,kamar yanzunne yake buqatar yayi komai.

Accent din nan nasa da yaren French ya shiga kunnenta da wani irin sanyi da laushi. Bata sani ba,ko Allah ne yake kamata?.....ko Allah ne yake mata hukunci akan gatsalinta?. Ta masa gorin yaren French,duk da cikin zuciyarta ne amma a yanzun bayan daya tabbata ko ya iya,da wata irin qwarewa da ko ita da yake yaren qasarta. Ko ita da yake yare na biyu a gurinta bata kaishi iyawa ba,sai ya zame mata wani irin jarrabi. A duk sanda zaiyi yaren,yana shigewa ta narke ta cikin kunnuwanta,ta kuma kwarara har cikin zuciyarta.

Janye jikinta baya tayi kadan,sai bai hanata ba,saidai kaman yadda taga ya koya,wani irin mayen kallo da yafi na baya,wani irin kallo da shanyayyu kuma narkakkun idanuwasa dinnan dake mata wani irin tsananin kwarjini.

Ba'a komai yake bude baki ya mata magana ba,yafi amfani da body language a komai nasa sama da magana,kamar tana masa wahala wani lokaci ko bakin nasa yana masa ciwo. Ko yanzu ma hannunsa kawai ya miqa mata bayan ya tabbatar ta lullube jikinta da wata lafiyayyar silk abaya me tsananin daraja,wadda daga gefenta a bayanta yake dauke da wasu qananun stone da aka rubuta haruffan sunanta cikakke dasu. Iya wannan dutsen.....iya shi kadai idan aka cire kudinsa dabanne,iya shi kadai idan aka kankare kudine ba abayar kawai ba. Yana cikin nau'ikan duwatsu masu daraja a duniya da kamfanin suka sarrafa suka fidda adon sunanta. Zasu yiwa sheikh muhammad haisam komai,saboda ya cancanta,yana da wata irin kima da daraha me yawa a gurinsu.

Lallausan tafin hannunta ta saka a nasa,ya runtsesu a hankali cikin zara zaran yatsunsa sannan suka fara takawa zuwa parlor din yana bude duk qofar da suka iso gareta.

Tana daga gefan nanay daga qasa,hannunta rungume da ledar turaren da tunda nanay ta miqa mata qamshinsa yake dukan hancinta. Turaren kamfanin shuwa ne,shuwa incense and more(turarukanta duniya ne,seriously jiya dana qona wani a parlour na......ya Allah🥰,irin qamshin nan da idan ka shiga daki ba zakaso ka fita ba,irin asalin qamshin turarukan wuta ba na yanzu gamje gamje ba,trust me akan kowanne turarukan wuta da zan recommending muku a novel dina +234 704 229 3387).

Banda kiran sunan Allah da take tsakanin jiya zuwa yau,ba abinda zai hanata kwanciya magashiyyan,saidai kuma tana gayawa kanta tana sake maimaitawa,qwarin gwiwa takeso......qwarin gwiwa take buqata,bata buqatar ta kwanta yanzu.

Abu mafi gigitata ta daga mata hankali shine.....wannan izzar da take gani tattare da ita......wannan izzar wadda take sanyawa bata sanin da zamanka a guri ballantana motsinka.....wannan izzar da motsinta ma kawai yake zame mata abun kallo. A jiya zuwa yau din wani sashe me girma na zuciyarta yana magana da ita......yana kuma gargadinta.

"Ki janye saamee.....zaki iya kuwa?,ba wata hanya......ba kuma wata fuska ko daya da zaki samu shimfida shirinki. Da mutum me shuru,da mutum me izza kowanne shiri wahalar isa ga manufa yakeyi" Take maimaita mata,amma ko sau daya taqi bawa wannan tunanin hadin kai.

Daga nesa ta hango nanay..... Kallo d'aya tal tayi mata amma sai takejin kamar nanay din na kallon komai a jikinta. Tadan so taja tunga amma ya matsa hannunta kadan.

"Relax please" Ya fadi yana motsa wadannan kyawawan labban nasa.

"Kowanne action naki yana determining abinda kika boye.....she's not the Allahn musuru......ba abinda zata fahimta" Ya sake fada softly yana qara yiwa hannunta kyakkyawan riqo.

Waya nanay din takeyi,kuma batakai ga ganin fitowarsu ba sai da suka iso tsakiyan parlor din. Tayi sallama da wanda take wayar tana ajeta gefe idanunta a kansu fuskarta dauke da murmushi.

Cikin yanayi na girmamawar nan tata,cikin yanayi na nuna zallar qaunarta ga wadannan halittu guda biyu ta miqe,idanunta a kansu,tana gaza gane wanda tafi qauna tsakanin ita ko shi?.

"Ina maraba da d'iyata" Nanay ta furta tana budewa Akhnan hannuwanta.

Wani irin kunya,wani irin nauyi suka taso suka lullubeta,ta yaya zata fara shiga jikin nanay bayan duk abinda suka aikata ita da dan nata?. Salon taji wani abu?,salon ta gane komai?,maimakon ta shige jikin nata bayan ta zame hannunta daga cikin na haisam din,saita tako a hankali ta iso gaban nanay din ta tsugunna tana gaidata cikin takatsantsan da ciwonta.

Durqusawa nanay din tayi tana murmushi ta dagota tana sanyata cikin jikin nata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Yaushe muka fara surukuta dake?" Ta tambayeta tana murmushi,saidai kuma hancinta ya jiyo mata sauyin wani qamshi cikin jikinta,kamar yadda taji dumin jikin Akhnan din ya qaru kadan,abinda ya d'arsa wani zargi kadan a ranta,saita janye Akhnan din baya kadan tana duban Fuskarta.

"Ina fatan kin tashi lafiya" Nanay ta sake fadi tana karantar wani haske da taga fuskar Akhnan din tayi. Ta washe da wani irin yanayi da yaso sake qarfafa zarginta a ranta,tana jin wani nauyi na duban haisam da take jinsa a tsaye a gefansu.

"Lafiya alhamdulillah nanay" Ta amsa mata tana jin duk duniya idan zasu hadu ba zata iya hada idanu da ita ba.

"Na yita aike......ba alamun samun amsa,har na dan tsorata na dauka yanayin jikin nasa ne.....nayita kiran wayoyinku duka ba wanda na samu" Ta qarashe maganan wannan karon kai tsaye tana aza dubanta akan haisam.

Karon farko da yaji wani nauyi na kallon idanun nanay.....a yau din sai yaji kallo dama idanuwan nanay din kamar daban suke da kallonta na baya. Tunda ta qarashe maganan idanun cikin nasa.....hakan yana gaya masa shi takeso ya amsa mata tambayar bawai diyartata ba.

Shidai wayarsa baisan inda ya jefata ba,tun daga sanda suke magana da omar maganar da har yanzu ba'a kammalata ba,har zuwa yanzu bazaice ga inda take ba. Tata wayar ma bai ganta ba ballantana ya fadi inda take.

Samun kansa ya kawai da aza hannunsa saman sumarsa yana shafawa,ya sake taku biyu yana qarasowa gaban nanay din,da wani yanayi daya sanya Akhnan satar kallonsa ta qasan idanu sanda yake gaida nanay din.

"Da gaske ne" Ta fadi a ranta,da gaske shi din shagwababben nanay dinne......da gaske ne shalelenta ne,kusanci qauna da shaquwar da take gani a tsakaninsu yana sanya mata wani shauqi.....yana sanya mata burin cewa Dama tata MAHAIFIYAR tana raye,yana saka mata jin dama haka rayuwa tsakanin uwa da d'a take?......me yasa wannan qaunar me zurfi......wannan yanayin gaba daya bata ganinsa tattare da MAMMINA?.

Ta nuna mata kulawa a komai nata.....amma wannan kallon....wannan shauqin da take gani cikin idanun nanay zuwa ga haisam ita bata taba ganinsa tattare da mammina ba.

Readers Also Read

More by Huguma