L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 85
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 85: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 85. Ta masa kyau ainun,fatarta glowing kawai takeyi,ta dan…
3,319 words
Ta masa kyau ainun,fatarta glowing kawai takeyi,ta dan cika kadan irin ta masu jego,saidai qiba tayi ba. Ta murmure sosai,qirjinta ya cika fam ya zauna daidai da shape din jikinta. Wannna cikin ya shafe ya koma cikin sati biyun,abun har mamaki ya dinga bashi,shape dintan nan ya fito. Fatar cikin ta batabar wani alamu me yawa ba,saboda wani hadi da nanay tayi mata traditionally daya batar da duk wani tattarewa da fatar cikin tayi ta kuma taimaka wajen fidda shape dinta sosai.
"Na zo in ga ko kina tuna cewa kina da miji." Ya fada da gajiyayyar muryarsa.
Kasa riqe murmushinta tayi sam.
"Ta yaya zan manta da rabin zuciyata?"
"Da kyau." Haisam ya fada yana lumshe idanunsa.
"Me ya hanaki nema na?" Ya fada da tuhuma sosai a muryarsa.
"Family dina ne fa suka zo."
"Na gani."
"Sun zo daga nesa."
"Na sani."
"To me na yi?" Ta fada a shagwabe tana dan buga qafarta kadan a qasa. Hakan da tayi kaman ta tsokanoshi ne,sai ya matso kadan.
"Kin yi yini baki zo inda nake ba."
"Haisam..." Ta kirashi a narke.
"Kin yi breakfast tare da su." Ya daga yatsa yana irga mata.
"Lunch tare da su." Ya daga wani.
"Dinner tare da su." Sai ya girgiza kai.
"Ni kuma?" Ya fada kaman zai sake mata kuka. Sosai ya bata dariya.
"Ka girma sosai fa da za ka yi wannan rigimar....yara uku captain obbo.....amma ba zaka daina rigima ba?."
"Ba ni da matsala da hakan......har abada a wajen matata......a wajen mamana ni yaro ne" Ta rufe baki tana dariya,don da alama da gaske yake.
"Me kake so yanzu?" Sai ya nuna parlour din da kansa.
"Ina so ki hada kayanki."
"Me?" Ta tambaya da mamaki don nufinta tazo kenan sai gobe a yadda ta tsara,har tasa birra ta kawo kayansu bedroom din.
"Ke da yaran."
"Haisam!" Ta sake kiransa,ba tare daya danu ba yaci gaba da magana.
"Zamu koma bangarenmu."
"Yanzu?"
"Eh....yanzu."
"Family dina fa?"
"Za su ganki gobe a suna." Ya fada yana sauke idanunsa akan lallenta,yadda ya zanu akan yatsunta da farar fatarta. Ya fidda kyawun siraran zara zaran yatsun hannunta. Ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya yana jin komai nata yana tafiya da zuciyarsa da nutsuwarsa.
"Amma yau..." Ya kalleta kai tsaye,abinda ya sanya ta kasa qarasa maganan.
"...ina son matata da yarana." Yadda ya fadi maganan ta sani daga qasan zuciyarsa ya fito,sai ta ji zuciyarta ta yi laushi.
"Ka yi missing dina ne?" Ta tambayeshi tana miqa masa hannayenta,bai bata lokaci ba ya bata nashi ta sarqesu tsakiyar nata,dumin yatsun nata suka ratsashi. Ya daga gira.
"A'a." Ya fadi ,ta yi dariya ganin zai mata gatse.
"Da gaske?"
"Akhnan." Ya kirata a tausashe,saboda ji yayi ba abinda yake buqata irin ya rungumeta a jikinsa..
"Na'am?"
"Five minutes."
"Ko?"
"Ko zan shigo parlour in sanar da kowa cewa kina sakaci da mijinki." Ya fada yana matsa hannuwanta da adon lallen keta burgeshi.
A wannan karon ta fashe da dariya gaba daya.
"An gama ranka ya dade" Ta fada tana zame hannunta da sauri tana fara shirya kayan yaran.
"Baki tambayi wanne suna aka basu ba har yau" Bata kalleshi ba ta amsa masa.
"Sun haifu daga uba me tarin ilimin addinu,ko wanne irin suna zaya basu....na tabbatar me ma'ana ne....kowanne irin suna zaya basu kuma.....na tabbatar zai zama mafi kyawun suna da zasuyi alfahari dashi" Alfaharin data furta shi ya mamayeshi game da ita,yaji bazai iya jurewa ba,ya taka a hankali ya isa bayanta ya mata wata kyakkyawar runguma.
"Madalla da mace ta gari....." Murmushi ta saki,sannan a hankali ya dora kansa saman kafadarta. Jego takeyi.....amma wani daddadan qamshi take fitarwa da ya sanyashi lumshe ido na shiri.
"Hassan......ibraheem muhammad haisam aba jifar......hussain......muhammad muhammad haisam aba jifar.......gambo.......mahmud,abun godiya kenan saboda qarin da muka samu akan abinda muka zata Allah ya bamu.....mahmud Muhammad haisam aba jifar"
"Madalla da uba na gari.....madalla da miji na gari.....sultane na godiy....."
".....shshsh" Ya dakatar da ita sanda ta juyo tana rungumeshi tsam a jikinta gami da riqeshi sosai ta baya ta hanyar shimfida tafukan hannayenta a bayan nasa.
"Ke.....kinsan abinda sultane yamin a rayuwa?.....kinsan me ya bani kuwa?" Ta girgiza kanta a hankali wanda yake kwance a qirjinsa tana murmushi idanunta a lumshe tana jin bugun zuciyarsa kai tsaye da kunnenta dake kwance a qirjin nasa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 156* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen* _____________________________
"Sabon ruhi ya bani.....sabuwar duniya,ya mallakamin ruhi daya.....yayi yabanya me albarka ya bani rassa uku,wa ya sani ko a gabama hudu zan samu?" Siririyar dariya ta saki tana boye fuskarta a qirjinsa.
Bayan mintuna kadan kuwa...Muhammad da Ahmad dasu shehnaz dake zaune sai ganin haisam sukayi da akhnan,yana tura stroller din yarantana biye dashi a bayansa.
"Ni na sani." Shehnaz ta fada qasa qasa cikin gulma.
"Ni ma." Aisa ta masa tana boye murmushinta
"Ya kwashe ta kenan?" Ahmad ya fada shima yana boye gulmarsa.
"An gama."muhammad ha fada yana laluben Aanani dinsa a waya. Yana jin kawai gwara tazo suma su wuce.
"Zan dawo da ita gobe."
"Ba mu yarda ba." Ahmad ya fada yana murmushi.
"Ba tambaya na yi ba." Haisam ya amsa masa yana dan jifansa da hararar wasa.
Dariya sukayi cikin nishadi,ya saki qaramin murmushi suna jerawa da akhnan din suka fice daga parlor din.
*WASHEGARI*
Tsaftatacciyar walima ce da aka yita har kashi biyu. Daya ta kowa da kowa,saita bayan la'asar data kasance iya jini da tsatson masarautun biyu ne.
Idan kaga yadda masarautar ta koma a ranar zaka dauka wani gagarumin biki akeyi na amare da angwaye goma. Ciyarwa kawai akeyi irin wadda ba'a taba irinta ba. Sadaka kawai ake fitarwa daga taskar haisam dama motii dinma gaba daya kamar zasu qarar da abinda suka mallaka.
Danyen abinci kuwa ba'asan adadin tirela nawa aka qarar ba. Tufafi da kudi kuwa ba'a maganarsu.
Duk da kasancewarsu masu tsananin kyauta sadaka da alheri wa talakawansu,amma wannan ranar wannan lokaci komai ya zama na daban.
Cikin dakin walimar data zama ta relatives kawai. Kyautuka ne akhnan ke karba har suka sanyata ta fara qwalla. Nanay....motii....sultane,morsa safiyya.....shehnaz aisa,rumaisa.....Anaani.....balqess.....khansaaa......Areef....ga uban 'ya'ya hussam da ta kasa daina mamakin yadda yake kyauta baya tsoron talauci sam. Wata irin kyauta dake nuna zallar soyyayar da yakewa yaran kamar shine ya haifesu. Ga wani account daya bude a take wanda zai dauki dawainiyar karatun yaran daga randa suia tsoma qafa a makaranta har randa zasu kammala. Daidai da noorah wadda ita ta zama photographer a gurin tata kyautar ta wankewa akhnan kai gaba daya. Ta dinga juyata tana mamakin inda ta samu kudi irin wannan ta siya abu me tsada da daraja na kudade masu nauyi ta bawa yaran
Ashraf.....asif da afeef,sune sunayen da iyayensu su shehnaz dasu rumaisa suka hadu suka zaba musu bayan sun tabbatar da ma'anar sunan me kyau ce. Ta sauke idanunta akan yaran dake kwance cikin wasu qananun royal bed dake nuna su din da gaske jini ne na sarauta.....gadon da akayi order dinsa direct daga italy,bayan yarjejeniya da kamfanin da haisam yayi dasu kan su kadai zasu siyarwa design din,aka qerashi da miliyoyin kudi kuma suka aiko dashi.
Inda gata yana yawa,ta tabbatar zaiwa yaranta yawa. Inda gata yana zarce misali zatace nasu ya wuce wannan. Sai a yanzu take gane lallai ba shakka.....a baya ba wani gata gareta ba data dage tana qafafafa dashi,ga inda asalin ainihin gatan yake nan.
Ta daga idanunta a hankali akan haisam daya miqe a nutse,yana takawa sanye da wasu tsaddadun jubah da cloak throbe qirar 2027 data kasance mallakarsa,kuma mutum na farko da kamfanin na al_imaraat suka saqa masa ita.
Abin mamaki,yau da kansa ya isa gurin jawabi,abinda sam ba kasafai yake son yin jawabi a tarurruka na family ba.
Nanay ma ta daga kai tana kallonsa. Sultane daya iso a ranar zai kuma koma zuwa dare yayi murmushi. Saboda ya san akwai wani abu. Yana iya karantar haisam daga yanayinsa kawai.
"Yau ba ranar yaranmu kawai ba ce." Shiru ya mamaye wajen.
"Yau kuma rana ce ta godiya." Sai ya juya ya kalli Akhnan.
"Na gode wa Allah da Ya bani su." Ya fada yana sauke idanunsa akan su ashraf.
"Kuma na gode wa matar da ta kawo su duniya." Akhnan ta sunkuyar da kanta cikin kunya.
"Amma kamar akwai buqatar godiyar tafi haka" Akhnan ta dago kai,sai idanunsa suka dawo kanta.Kai tsaye. Ba tare da ya kau da kai ba.
"Matata." Wajen ya yi shiru gaba daya. Akhnan taji wani sabon nauyin.
"Mutane da yawa suna taya uba murna." Ya girgiza kai.
"Amma ni na san wanda ya cancanci yabo."
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Na ga wahalar da ta sha."
"Na ga tsoron da ta boye."
"Na ga addu'o'in da take yi lokacin da babu kowa." Akhnan ta sunkuyar da kanta tana mamakin yadda ashe yake bibiye da dukka wani motsinta.
Sabbin hawaye suka fara taruwa a idanunta.
Da salon mulki da izzar nan ta jimma,wadda ta zama jinin jikinsa yayi alama da hannu kawai,nan take aka kawo wani velvet folder.
Karba yayi,sannan kai tsaye ya miqawa akhnan.
"Open it." Da mamaki ta karba da hannu biyu kaman yadda take karbar abu daga gurinsa yanzu. Ta budeta a nutse.
Da farko ba ta gane ba. Sai ta sake kallon rubutun. Sannan ta sake dubawa. A saman takardar an rubuta
*THE AKHNAN ESTATE* Sai hannunta ya yi sanyi. Maison akhnan ne ke dawo mata. Wannan dinma ba wata kyauta bace ta qaramin abu. Ba wani zobe bane......wani cikakken estate ne.
A cikin manyan kadarorin daular haisam. Me private gardens....library.....children's wing......amily courtyard... Artificial lake.....Private masjid.....underground royal gallery,komai an tsara shi da abubuwan da takeso kaman mafarkinta ne a gabanta.
"Haisam..."Ta kasa qarasawa saboda yadda jikinta yayi sanyi gaba daya. Kaman yana nuna over soyayya a kanta. Kamar wannan qaunar tayi yawa,me ta masa?,me ta bashi data cancanci wannan gaba daya?.
Duruqsawa yayi sosai kusa da ita. Abin da ya sa duk wajen ya yi shiru. Saboda sabon abu ne,haisam din ba qaramin abu ne yake sanyashi fallasa zuciyarsa haka ba.
"Kin bani gida." Ta kalle shi cikin mamaki.
"Na yi shekaru ina da gidaje."Sai ya girgiza kai.
"Amma ban taba samun home ba sai da ke." Nanay ta rufe bakinta,hawaye suka cika idanunta. Morsa Safiyya ma ta fara share hawaye a hankali. Su kansu abun wani burgesu yakeyi.....soyyayar da suka jima basuga irinta da gasken gaske a soyyayar zamanin nan ba.....a tattare da yaran zamani irinsu ba. So saboda Allah kawai,ba don ta bashi komai ba. So saboda Allah kawai.....saboda kyakykyawar mu'amalarsa ba don tasan wayeshi ba.
"Na gina wannan tun kafin a haife su." Ya nuna yaran.
"Saboda na san wata rana zan so in nuna miki cewa..." Sai ya dan yi shiru.
"...duk abin da na mallaka zai iya qarewa." Ya furta kalmar sanda I danunta suka hadu da nasa.
"Amma darajarki a wurina ba za ta taba raguwa ba."
A wannan lokacin Akhnan ta kasa magana gaba daya.Ta ji kamar zuciyarta ta yi nauyi saboda soyayyarsa daya sake cusa mata da kuma wani irin launin farin ciki.
"Karbi" Taji muryar nanay daga gefanta. Akhnan ta waigo a hankali tana duban uwar mijin nata. Uwar mijin da inda za'ace ta bada award na har abada ga best uwarmiji ba ko shakka nanay zata danqawa shi gaba daya.
"Wallahi kin cancanta." Ta sake fada tana kallon akhnan sosai tana gyada kanta.
"Fiye da haka ma." Muryar motii ta marawa ta nanay baya.
"Yayi yawa" Akhnan ta fada cikin karaya,tana ganin kamar batakai girman wannan kyauta ba.
"Not enough." Ya fada da dukka zuciyarsa. Akhnan ta girgiza kai itama tana duban abinda ke narkewa a idanunsa.
"Haisam..."
"Not enough."Ya sake maimaitawa idanunsa cikin nata.
"Da zan iya biyanki saboda duk abin da kika yi..." Ya girgiza kai.
"Da babu wani abu a duniya da zai isa biyanki wannan aikin.....wannan wahalar..." Nanay ta sake share hawaye tana jinjina kai gami da gamsuwa da maganganun haisam gaba daya.
A hankali morsa Safiyya ta juya gefe tana murmushi zuciyarta na mata wani irin sanyi. Irin mijin da safeena ta yiwa diyarta mafarki. Shi ta samu,sama da haka ma,itakam ko yanzu ta fadi ta mutu,tabbas tana da amsar bawa safeena,zata iya tsaiwa ta fuskanceta.
Matsawa yayi kusa sa ita,ya sunkuya qasa qasa ba tare da kowa yaji ba.
"You're crying giiftii"
"Saboda kai ne" Ta fada a shagwabe.
"Good" Ya fada yana murmushi. Da mamaki ta kalleshi.
"Yes" Yace yana dage girarsa.
"Because now everyone can see...."
"Can see what?"
"How much you love me" Ya fada da zolaya fal muryarsa. Ga mamakinsa tattausan murmushi ta saki,ta rausayar da kanta gefe.
"Ban fadi ba....duk irin son dana nuna maka ban fadi ba,koda a gaban waye" Ta masa surprise daya kasa magana,sai lumshe idanunsa kawai da yakeyi ya gaza daina kallonta.
A wannan ranar...ba estate din kawai bane ya sa mutane da yawa taya akhnan kukan murna ba......Ba girman kyautar ba ne.
Abin da ya taba zukatansu shi ne.....sheikh muhammad haisam......mutumin da ya shafe shekaru yana gina dauloli da kamfanoni....amma zabi ya sanya sunan mafi kyawun abin da ya gina da sunan Akhnan.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 157* __________________________ *_INGANTACCEN MAGANIN SANYI NE SADIDAN,WANDA BA'A CAKUDASHI DA KOMAI BA SAI ZALLAR SASSAQE DA ITATUWA MASU AMINCI_*
*_KAYAN GYARA MASU INGANCI DA WARWARE MATSALAR MATA TA FUSKAR CIWON SANYI WANDA YA KASA JIN MAGANI_*
*_GARZAYA A SIRRANCE KI WARWARE MATSALARKI,KI TUNTUBETA TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE_*
+234 810 914 9876 ___________________________
Idan da za'a tambayeta menene rayuwa?. Zata iya cewa HAISAM ne. Idan da za'a tambayeta mene RUHI ZUCIYA MAFARKI da BURI duka zata ce haisam ne.
Idan za'a tambayeta mececw SOYAYYA ko QAUNA?.....MENE FITAR NUMFASHI DA BUGAWAR ZUCIYA.. dukka zata iya cewa ASIF NE.....ASHRAF NE....AFEEF NE.
Idan aka tambayeta kinsan rayuwa?. Zata ce aah,....sai a yanzu. Sai bayan da Allah ya mallaka mata haisam. Sai bayan data haifi ashraf asif da afeef sannan tasan me duniya ke nufi da RAYUWA.
MUTUM HUDU dinnan.....mutane HUDU dinnan sun zama RUHINTA da batajin zata iya rayuwa ba tare dasu ba. Mutum HUDU dinnan da kullum take kwana take tashi da fargabar rasa daya daga cikin su. Mutane hudun nan da kullum take addu'a kada Allah ya jarabceta da rasa daya daga cikinsu.
Wata ingantacciyar rayuwa.....wadda take kwanciya da burin ganin kamar wanzuwar rayuwa me kyau wa ahalinta. Wara rayuwa da take farkawa da sautikansu su hudun. Haisam da yaransa......ta kwanta dasu dumin jikinsu yana gogar nata.
Wata rayuwa ta tsarawa kanta. Duk wata wahala ta raino ta koyawa kanta. Bata yarda da rainon hadimai ba.....bata yarda da rainon bayi ba.....bata yarda da rainon 'yan aiki ba. Tafi ganewa ta hidimta musu da kanta. Bata yarda da kowa akan yaranta ba indai ba jininsu bane.
Rayuwarta a hannun mammina wata irin izina ce.....wani irin karatu ne me zaman kansa da kansa. Karatun da wataqila mammina bata mata shi ba....ba lallai ta gane ta sauqi haka ba.
Silently ta dinga gyaran kanta....silently ta dinga Maida kanta macace ta hanyar koyin hanyoyin kula da miji da yara. Ta sanya dukkan hankalinta da qarfinta a kai. Yadda cikin lokaci kadan ta iya komai,....cikin qaramin lokaci ta zama cikakkiyar mace da zata iya kula da gidanta da mijinta,wannan ya gaya mata lallai komai idan mutum yaso zai iya gyara rayuwarsa. Idan mutum yaso zai iya gyara kansa...... Idan har mutum yaso zai iya gyaran kurakuransa.
Ta yarda komai soyayyarki da cikarki mace...akwai abubuwan da idan baki iyasu ba....komai kawaicin da namiji zai miki kina da naqasu. Har yanzu idan tayi wani abun mamaki kashe haisam yakeyi. Yaya akayi ta iya?.
(Karki saki baki waike ai ana sonki,ai shi baida damuwa don bakiyi kaza ko ba'ayi kaza ba. Komai kawaicin namiji indai baki iya wani abu da yake so ko yaya ba.....zai iya kawaicin,ya dauke kai.....amma acan cikin ran shi yanaso,yana kuma kewa,idan kuma kin iya din zaiji dadi,zaki gane hakan bayan kin iya din).
Taso ya barsu taci gaba da kula da yaran,shi kuma yayi focusing akan business dinsa da boyayyen aikinsa. Amma koda ya amsa mata da to......idan tafiya ta kama,koda ya fita saidai taga ya dawo da kanshi yahau hada kayansu asharaf,saidai ta tsaya cak tana dubanshi.
"Abbee" Sunan da takan kirashi yanzu kenan.
"Mm" Sai ya amsa amma bazai dubeta ba,don yasan qilan qorafi ne
"Amma fa....."
"I'm sorry,bazan iya tafiya na barku ba,Even if I force myself to go, aikin ba zai yi min dadi ba....aikin bazai yuwu ba....ko kinason ganin faduwar mijinki?" Tana ji tana gani dole haka take rabuwa dashi.
Sun zama kamar aljihunsa,duk inda ya zaije sai ya daukesu hankalinsa yake kwanciya.
Akhnan ta yi murmushin nan dake qara mata kyau.
"Drama prince."
"No." Ya amsa cikin sanyin murya.
"I'm very serious." Ta girgiza kai.
Tun da yaran suka zo duniya...ta fara ganin wani sabon haisam. Wani haisam da yake saurin komawa gida.
Wani Haisam da yake duba hotunan yaransa a tsakiyar meeting.
Wani Haisam da baya iya yin yini bai gan su ba.
"Ranan da suka shiga school,zanga yadda zamu dinga yawo dasu" Ta taba cewa dashi. Murmushi ya saki yana kallon tsakiyar qwayar idanunta.
"Ba abinda zai sauya....ba abinda za'a fasa. Su dama 'yan rakiya ne ai".
Akhnan ta qyalqyale da dariya.
"Yan rakiya?"
"Yes."
"For the rest of their lives?"Sai ya kalleta,wannan kallon da kullum ke sa zuciyarta ta narke.
"For the rest of mine." Na dan lokaci Akhnan ta kasa cewa komai. Saboda yadda ya fad'a. Ba wasa ba. Ba tsokana ba. Da gaske yake.
A wurin Haisam...dukiyarsa..... Sarautarsa.....Kamfanoninsa.......nasarorinsa. Duk suna da matsayinsu. Amma babu abin da yake so ya dauka tare da shi kamar matarsa da qananan sarakunansa uku.