L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 86
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 86: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 86. Yaran suna da watanni takwas ta aurar da nata 'yan…
3,368 words
Yaran suna da watanni takwas ta aurar da nata 'yan biyar din. Birra barratu buhaina bushira da baraka. Saidai kusan dukkaninsu sun aminta suci gaba da aiki da ita,don haka a cikin villa dinsu aka warewa kowa apartment daban shi da mijinsa,don masu gidan nasu ma duka 'yan gidan sarautar agadez ne,birra ce ta samu dan cikin masarautar jimma.
Tana tafi da kowanne company nata daga gida ta cikin system. Sau bibbiyu bayan haihuwar su ashraf taje dubai da Niamey tayi ziyarar gani da ido ta duba duka companies din nata. Meeting.....shawarwari da gudanarwar kamfanonin daga gida takeyi.
Bayan ta sallami haisam din,ta kuma sallami yaran,a kowacce rana awa uku ko biyu take warewa tana aiki saman saman system tana gudanar da komai,idan ta rufe kuma sai washegari,saidai idan wani abun ya taso su sanar mata tahau ta duba.
*_BAYAN SHEKARU_*
Safiyar Jimma ta kasance cikin nutsuwa.
Iskar sanyi daga tsaunukan Jimma na motsa farin curtains din balcony a hankali,yayin da hasken safiya yake shiga cikin bedroom dinsu mai fadi da wani irin tsari dake bada iska me dadi da wadataccen haske.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Itama don dai kawai ba'a manta asali.....kuma ba'a manta gida. Amma saura qiris a lokuta da danma ta zabu jimma sama da agadez. Garin yana da wata irin albarka,hakanan yana da wani irin weather dake sanyaya zuciya. Irin weather din da yawancin zukata da gangar jiki sukeso,irin yanayin nan me sanya nishadi a zukata.
Akhnan ce,tsaye bakin glass railing din tana riqe da cup din tea dinta. Ta zama wata irin mayyar tea har abbee(haisam) yana tsokanarta a gaban yara su kuma suna tayashi.
"Mun maidata 'yar jimma....cikakkiyar yar Ethiopia....mun mantar da ita agadez gaba daya"
Daga qasa...dariyar yara ta cika garden din. Ta sauke idanunta a kansu tana kallonsu daya bayan daya.
Ba ashraf bane.....ba asif bane....ba afeef bane. A yanzun....wasu yaranne na daban.....wasu saitin 'yan ukun daban......da wani set na 'yan biyun da suka zama haihuwarta na qarshe da tayi shekaru biyu baya.
Ahsan.....ahlaam......da ajmal.....sai 'yammatan da suka kasance twins su biyu masu tsananin kama da akhnan din kamar kakinsu tayi ta ajjiye. Safiyya da safeena.....wanda nanay tayi kawaici tace sunansu ya kamata ya saka ita ta yafe. (YUMNA DA YUSRA).
Yumna ce ke gudu tana qoqarin kaucewa kubuta daga hannun ahsan wanda yakeso lallai sai ya riqeta kada ta fadi,yayin da nannynsu ruqayya yarinyar da bata haura shekara sha uku ba ke binsu cikin dariya.
Murmushi ya bayyana a fuskar Akhnan ba tare da ta shirya ba. Years ago...... da wani ya gaya mata cewa zata taba samun irin wannan rayuwar,da bata yarda ba.
Ba wannan mutumin ba...yarima sheikh Muhammad hausam. Ba wannan gidan ba......ba wannan nutsuwar ba.
Mafarkinta yayi nisa akan ta rayu ita kadai kawai. Mafarkinta yayi nisa yana gaya mata lallai akwai rashin 'yanci da takura gurin rayuwa tare da d'a namiji. Ashe dai saidai ga wadda bata dace ba.
D'A NAMIJI.....KUMA MALAMIN data raina.....shi ya zame mata wani tsani na kaiwa wani mataki da bata taba mafarkin kaiwa ba kaf rayuwarta. Malamin dai.....shine ya kama hannunta ya sanyata ta san ma mene addininta haqiqanin sani. Ya sanyata ta sauke litattafan addini da dama. Ya sanyata ta gyara lahirarta ta hanyar yin karatun litattafan addini masu yawan gaske daga bango zuwa bango. Ta sauke hadisai masu yawa,litattafan fiqhu dana sira. Tasan rayuwa a haqiqanin zahirinta. Tasan mutuwa hisabi da kwaciyar kabari sanin da bata taba kaiwa koda gefansa ba. Ya sanyata da kudinta da abinda ta mallaka takewa kanta mahaifiyarta da morsa safiyya sadaqatul jariya. Harda wadanda ta manta. Yawan sadaqar ya sanyata take mafarkin mahaifiyarta cikin ni'ima a mabanbatan lokuta. Allah ya nuna mata a mafarki yadda sadaqatul jariya dinta ke isa ga mamminta. (Iyayenki sun mutu?,amma kina da dubu hamsin,dubu dari da zata isa gina rijiya......siyan qur'ani kikai masallaci......gyaran hanyoyin unguwarku ko yin cikon hanya amma ki kasa yi musu wannan kice ladan Allah yakai kabarinsu?).
Sharrin mammina bai hanata roqa mata yafiyar Allah ba....sharrinta bai hana mata yi mata sadaqatul jariya ba tunda bata da wanda zai mata. Tana fatan wannan ya sanya ta samu sassauci a gurin Allah.
(A duk sanda bawa ya maka sharri,kai kuma idan ka samu dama akansa gwada masa alkhairi. Yi masa alkhairi har sai ya kasa kallon idanunka,Allah kasa mufi qarfin zukatanmu....kasa mu shuka alkhairi don mu girbeshi ranar gobe qiyama).
Tayi nisa a tunaninta sai ta ji motsin qofa a bayanta.
Ba sai ta juya ba kafin ta san shi ne. Presence dinsa har yanzu yana nan quiet power. calm danger. the same man.......prince sheikh muhammad haisam.
Wannan kamannin.....wannan lallausan kyan....wannan charisma din.....haiba,kwarjini,kamala dukkansu suna nan tattare dashi,sai ya zamana kamar an ninkasu ne ma.
Da tarin nutsuwar nan tasa ya tsaya bayanta cikin dark suit dinsa,ya zube hannayensa a aljihun suit din,saidai hakan bai hana bayyanar agogon hannunsa dake kyalli qarqashin hasken safiyar ranar ba.
“Kika gudu kika barni da su.” ya fada a tausashe da wannan husky voice din tasa me zurfi,wadda idan yayi magana take kai mata kowanne sashe na jikinta.
Ta yi murmushi tana kallon garden,har yanzu anata artabu da yumna. Kuzari tafi kowa a gidan?,ko rashin ji?,itadai ba zata ce ba.
“They like you more.” ta amsa masa da muryarta dinnan da bata sauyawa
“A’a.” ya fada a tausashe,sannan a nutse ya tako ya qaraso kusa da ita yana aza hannunsa jikin makarin silver din.
“They fear me more.” Tayi qaramar dariya tana duban idanun nan nasa da kowacce rana yake sake narkar da ita.
"Abbee....yaran nan wani lokaci abinsu baya tashi ma sai sun ganka fa" Murmushi ya saki a hankali,ya miqa hannunsa yana dan ja hancinta da yaga ya bude kadan.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 158* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Akwai shaquwa da sabo da sakewa sosai tsakaninsu sama da yadda suka sake da mamansu..... Amma akwai wani tsoro da respect a tsakaninsu. Wani shakkarsa suke....musamman idan kasan kayi ba daidai ba. Amma kuma idan kaga yadda suke rayuwa dashi zaka dauka abokinsu ne ba uba ba.
"Hancina ko abbee" Ta fada taba dan tsuke fuska. Ido ya zuba mata sosai kaman bayason ya daina kallonta. Itama kallonsa take tana sake ganin yadda kyansa ke sake fitowa yana cakuda da shekaru wadanda ke sake qara masa kwarjini. Mutumin da duniya ke tsoro… ita ce kadai take jin yadda zuciyarsa take samun wata cikakkiyar nutsuwa idan yana gida.
"No" Yace yana danne murmushinsa. Rau rau tayi da idanu tana dubanshi.
"Kaji tsoron Allah ka fadi gaskiya" Ta fada muryarta tana raurawa kaman zata sake masa kuka,abinda ya tilasta dariyanshi fita gaba daya. Siririn kuka ta sake masa,amma kuma da gaske abun mamaki qwalla take fitarwa,ya dan zaro ido yana mamaki.....saidai kafin yace komai,sai qaramar muryar yusra ta taso daga qasa.
“abbeee!" Ya sauke idanunsa sanda take rugowa qofar da zata sadata da inda suke tsayen kafin ruqayya ta kai ga kama ta.
Idanunsa ya maida kan akhnan yana narke idanunsa shima.
"Ki rufan asiri ammee...(sunan da yaran ke Kiran ta?,kinga dai banyi miki komai ba...hasalima yau ni aka yiwa laifi,da asuba akaqi sanmin abun arziqi. Yanzun yusra zata shigo,idan taga qwalla a idonki tace me na yiwa ammeenta?" Banda bacin rai kadan da takeji wanda batasan asalinsa ba,tabbas data qyalqyale da dariya. Saboda haisam din wani irin mutum ne da sam bayaso yaranta suga alamun ya bata ran mamansu. Ya taba bata amsa da cewa.
"Inaso su taso da tausayin iyalansu suma a gaba,dole sai ina kwatantawa. Yaro kuma baya mantuwa,komai a kansa yake zama,inaso su samu memory me kyau....inaso su tashi da yiwa rayuwar aure kyakykyawan zato,adadin kulawa nutsuwa da kwanciyar hankali da kuma soyayyar da yaro ya samu,adadin yadda zai dinga mu'amala da kowa a waje. Da taushi,da nuna qauna da soyayya ga kowa,ba tare da musgunawa ba" .ta gamsu da hakan dari bisa dari,don tana ganin tasirinsa tattare da yaran.
"Ba kaine ba.....dariya kakewa hancina".
" Na tuba.....na tuba giiftii din jimma" Ya fada yana hade hannayensa guri daya. Daidai lokacin yusra ta iso.
Yusea me sleepy eyes ta bayyana bakin qofar gurin tana kallonsu duk sy biyun. Sai dukkaninsu suka bude mata hannayensu,da gudu ta rugo,amma sai ta zabi fadawa jikin haisam. Dan ihu ya saki yana dariya wa akhnan din. Murmushi kawai ta saki,don dama tasan hakan na iya faruwa,bata sanya rai da yawa tazo gurinta ba.
Dagata sama yayi yana zagaye gurin da ita yana mata wata waqar larabci da yakan rera musu tun suna jira jirai idan suna kuka.
Burgeta kallonsu yakeyi......haisam.....mutum na musamman a duniya. Bata gajiya da fadin hakan. Idan ka ganshi cikin iyalinsa ba zakace shine wanda kullum manyan attajirai da manyan shuwagabannin duniya ke jiransa ba.
Yadda yusra ta kwantar da kanta a kafadarsa kawai ya isa ya gaya maka ita kanta ta gamsu tana da amintaccen uba a duniya. Yadda hannun Haisam ya riqeta instinctively. Yadda cold din mutumin nan yake narkewa a gaban iyalinsa kawai,sai idanunsu suka hadu da nata.
Na wani second guda… duk memories suka dawo mata. hamadar agadez,tsoron da suka fuskanta a tare,jarrabawar rayuwarsu da mammina....soyayyar da ta firgita ta. Da kuma daren da ta taba tunanin bazata iya rayuwa cikin duniyarsa ba. Yanzu kuma…ita ce duniyar tasa.
Haisam ya kalleta cikin nutsuwa irin tasa muryarsa a qasa yadda yusra ba zata fahimta ba.
“Why are you looking at me like that?” Ta girgiza kai a hankali.
“Just thinking.”
“Dangerous.”Ta yi murmushi,still him. Amma taqi bashi amsa. Ta sani tsaf zai qarar da duka lokacinsa a gurin,bayan tun a jiya tasan fitar yau me muhimmanci ce.
"Zaka wuce ne?" Ta tambaya kaman me masa tuni.
Ya sani.....meeting dinsa na jiransa. Phones suna ta vibrating tun safe. Duniya tana jiransa kamar kullum. Amma sai ya kalli matarsa......'Ya'yansa.....gidansa sannan calmly yace
“No.”
Akhnan ta dan daga idonta a kansa.
“Your meeting?”
“It can wait.” ya furta yana rage tazarar nisan dake tsakaninsu. Sai ya qaraso gare ta,ya tsaya kusa da ita yusra na rungume a jikinsa.
A wajen balcony din… ,wata irin iska mai sanyi da dadi ke ratsasu. Garden din na cike da tsirrai dake bada iska me dadi har nan inda suke tsaye,shi yasa aka gina gurin daura da garden din. Rana mara haske da qarancin zafi tana haskaka gidan kamar wata sabywar rayuwa.
A nutse haisam ya sumbaci goshin akhnan din,sai yusa ta kalleshi,ta kuma tura masa tata fuskar. Dariya suka sanya dukansu ita dashi,yayi kissing nata itama,saita qanqame wuyansa tana murna,abinda ya sake basu dariya gaba daya.
"Kawota.....kaje ka dawo.....zaka samemu cikin aminci da yardar Allah". Girarsa dukka biyun ya dage.
" Are you sure?" Kai ta daga masa a tausashe. Ya miqa mata yusra,amma saita maqale kafada.
"Ba zata yarda ba...."
"...muje na rakaka sai na karbeta a bakin motar"
"Kina nufin da ba zaki rakani ba yau?" Ya tambaya yana bata fuska,ta saki murmushi kawai. Kasala take fada da ita kwanan nan duk safiya,batason gaya masa yanzun nan zai rasa nutsuwar sa,sannan uwa uba ma zarginta yafi qarfafarta akan ciki ne,don duka alamunsa sun nuna mata.
Tare suke takawa da wani irin yanayi me dadi inda jerin motocinsa ke jiransa. Dab da zasu fita yaran na shigowa. Dukkaninsu suna maqaleshi,hakanan ya sunkuya ya dauki yumna itama,su ahsan suka riqeshi ta gefe da gefe suna zuba masa surutu,duk da yadda akhnan ke fadin kada su bata masa kaya sam bai damu ba,don pyjamas ne duk a jikinsu,yau ba wanda yayi wankan safe,sannan duk yashin gefan pool na gurin ya bata hannuwansu da qafafunsu.
Akhnan na kallonsu tana girgiza kai. Wannan abu na yaran idan haisam zai fita bai taba canzawa ba.
Ko da yaushe sai sun yi masa rakiya,indai suna gidan,indai idanunsu biyu.
"Abbee,ka kalli kayanka." Akhnan ta fada sanda daya daga cikin amintattun guard dinsa ya bude masa qofar motar ya kuma zura jikinsa. Ta nuna farin shirt dinsa da yanzu yatsun yumna suka bar masa alamar yashi.
"Meeting zaka je fa." Sai ya kalli rigar. Sannan ya kalli yaran.
"So?" Ya furta yana dage mata dukka girarsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"So?" Ta maimaita tana dariya.
"Ba su ne suka bata min ba." Ya fada yana kade gurin da wani dan farin handkerchief me kyan gaske da guard dinsa ya miqa masa a girmame.
Ajiyeshi yayi,ya sake jawo yumna da yusra ya dan rungume su. Ya miqa musu kuncinsa,sai kowacce ta bashi kiss guda daya.
"Sun qara mata kyau ma rigar." Dariya ta kubce mata daidai sanda Yumna ta sa qananan hannayenta biyu ta riqe fuskarsa.
"Abbee..."
"Na'am, princess?" Ya amsa yana shafa sassalkar sumarta me tsaho da santsi data gada daga buzuwar babarta.
"Kar ka dade." Nan take zuciyar Akhnan ta yi wani irin laushi. Yarinyar nada wani irin wayo na daban,har yanzu idan zai tafi sai sun gaya masa hakan.
Sunkuyo da kansa yayi ya sumbaci goshinta.
"I won't."
"You said that yesterday." Ahsan ya fada,akhnan ta rufe bakinta tana dariya.
Da dariya a fuskar haisam ya juya ya kalli ahsan.
"Whose side are you on?"
"Mama's." Ya fada yana tsalle da dariya.
"Me too." Ajmal ma ya fada yana dariya.
"Me three." Yumna ma ta fadi tana daga yatsunta uku duk da bata gama fahimtar akan abinda ake maganar ba.
Sai kawai ya girgiza kai kamar wanda aka ci nasara a kansa a yaqi.
"Traitors." Yaran suka fashe da dariya.
Dariyar itama ta danyi,saidai kuma ta ji wani jiri sama sama ya ratsa ta.
Ta dafe gefen motar a hankali tana kiran sunan Allah. Ba wanda ya lura sai haisam. Nan take murmushinsa ya dusashe.
"Akhnan." Kirata da kulawa. Ta dago kanta a nutse.
"Hmm?" Idanunsa suka tsaya a kanta. Na dan lokaci kamar yana qoqarin karanta wani abu.
"Are you alright?"
"Of course." Ta amsa masa da confidence.
"You're tired." Yace yana zare seat belt dinsa da sauri.
"Just a little." Ta fadi tana daga masa hannu gami da dakatar dashi,saboda ta fuskanci fitowa yakeso yayi,kuma taga yadda hussam keta kiransa,da alama abune me muhimmanci. Dakatawar yayi amma sai ya ci gaba da kallonta kamar bai nutsu da yanayinta ba.
Wancan kallon dake mata nauyi,don idan ya fara yi mata shi.....yana ganin abubuwan da take son boyewa fes cikin idanunta.
"Kinci abinci?" Ya sake tambaya.
"Eh naci,ka shigo ka ganni da cup ba?"
"Properly?"
"Muhammad." Ta fada tana yarfe hannunta kamar yarinya irinsu yumna.
"Akhnan." Ya kirata shima don bazaije ko ina ba sai ya tabbatar lafiyarta qalau.
Yaran suka fara kallon iyayensu. Saboda sun san wannan yanayin. Tsananin kulawa da junansu da baya boyuwa ko a gaban waye.
Haisam ya ci gaba da kallonta,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya.
"Rest today." Ya fada daga qarshe.
"I will." Ta amsa masa.
"Banda shiga kitchen yau duka.....ba girki na auroki kiyimin ba" Qaramin murmushin da bata shirya ba ya qwace mata. Dole sunan NA MUSAMMAN batasan sanda zata sauke masa shi ba. Abubuwan da maza da yawa suka daukakesu,suka kuma daukesu da zafi shi basu dameshi ba. Kawai shi ta zamana cikin qoshin lafiya,ta kula da tarbiyyar yara,sannan ta kula da buqatunsa a shimfida,komai ba dole bane a wajensa idan ya wuce wadannan.
"Promise?" Ya tambayeta. Sai ta gyada kai.
"Take care of yourself......" Yayi maganan yana miqa mata hannunsa kaman yadda ya saba duk sadda zai fita suyi musabaha. Bashi tattausan tafin hannunta tayi,wanda take kula da taushinsa sosai tun daga sanda ta gane yana daya daga cikin abinda yakeso a jikinta. Baya rabo da riqe hannunta muddin suna tare.
"......For me." Ya qarasa maganan daya fada din dazu.
Akhnan ta ji wani irin murmushi ya subuce mata.
Sai ta kalli yaran da ke maqale da mahaifinsu. Ta kalli haisam.......tana tunanin yadda zai kasance idan ya gano abin da take zargi.
Ta san abu daya kawai..... Idan ya tabbata...mutumin nan ba zai sake samun nutsuwa ba kwata-kwata sai sanda ta haifa abinda ke cikinta din.
"Am....amma nace zamu samu jet?,nasan ka manta" Ta fada sanda take dab da rufe masa qofar motar. Kai ya daga yana dubanta ba tare da yayi magana ba.
"Zamuje agadez....duba sultane.....baya jin dadi,aisa ma ta sakeyin miscarriage tana gida".
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 159* __________________________ https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0
*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*
*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*
*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*
*_Assalamu alaikum my loyal people_*
*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*
*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*
*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*
*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*
*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*
*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen* ___________________________
"I know,ina sane,ta yaya zan manta da duk wanda ke rayuwa cikin gidan nan?.....zansa su shirya jet din,ko gobe da safe sai muje. Sahel couture new branch ma yana buqatar sanya idanunki.....kamar akwai gyararraki daya kamata kiyi".
" Yes sir" Ta fada tana saluting nasa. Abinda ya sanyashi sakin murmushi kenan,ta rufe masa qofar a hankali sannan taja baya,ya sauke window din kamar yadda ya saba ta tsaya sosai ta masa addu'a kamar kowacce rana idan ta rakoshi zai fita. Suka shafa addu'an tare.
"Allah yayi miki albarka" Ya fada sanda ya bawa driver umarnin tayar da motar,
"Ameen....."
"Fi amanillah" Ya furta lafazinsa na qarshe kaman yadda ya saba fada kowanne lokaci.
★★★
*_TSAKANIN HARSHE DA HAQORI_*
Gagarumin sauyi da sabbin tsare-tsare ne suka fara bayyana a tsakanin masarautar Agadez da ta Jimma qarqashin jagorancin Prince Sheikh Muhammad Haisam Aba Jifar.
A cikin yan shekarun da suka biyo bayan aurensa da Khadeeja Sultane Muhammad Hammud,an samu qulla manyan alaqoqin kasuwanci, ilimi da al'adu tsakanin masarautun guda biyu. Abubuwan da a baya suke daukar watanni kafin a cimma matsaya a kansu, yanzu cikin sauqu suke samun sahalewa da cikakken goyon baya daga bangarorin biyu.
Dangantakar da ta fara ne ta hanyar aure da haduwar jini, ta rikide zuwa wata gada mai qarfi da ta hada al'ummomi daban-daban, tare da qara kusantar da zukatan jama'ar qasashen biyu.