L u'u l u'u book 3 complete by huguma - Chapter 88
L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 88: L u'u l u'u book 3 complete by huguma Chapter 88. *_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki…
2,713 words
*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*
*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*
*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen* __________________________
".....abbee"
"Don't.....karki musa" Ya fada yana daga hannuwansa sama duka biyun.
"....coz ni na yarda....saboda...." Sai yadan tsaya.
"......dama a mallake nazo wallahi" Dariya suka saki shi da ita,sai ya jata jikinsa a karo na biyu yana manna mata tattausan kiss.
"Khadeeja zaki haifo in sha Allah....da alama kuma rigimarki zatayi,so stay at home,banaso kiyi stressing kanki,zan saka a saka miki device,zakiga komai kamar kina gurin....after an gama,zan tattaro duk wanda kikeson gani na kawo miki shi nan......ko waye....." Kai kawai take girgizawa. Yana fasa mata kai da yawa. Tana jin kamar gatan ya mata yawa.
"Abbee" Ta kirashi sanda yakai bakin qofa tana qare masa kallo. Ya waiwayo yana dubanta da manyan fararen idanunsa.
"Kayi kyau......" Murmushi ya subuce masa.
"Kuma haka zasu gani su haqura su barwa khadeeja ni ba" Dariya sosai ya sanyata harda hawaye.
"Ka yafemin" Ta sake fada.
"Don Allah....bazan sake ba" Juyowa yayi gaba daya yana dubanta.
"Da laifin da kika taba yi duk da baki dashi ma.....da wanda kikayi yanzu....dama wanda zakiyi a gaba.....muddin bai sabawa fadar Allah ba,indai haqqina ne na yafe to na yafeshi....." Maganansa ta qarshe kenan ya juya yana fita ya barta da zuciya me nauyi,zuciya me cike da soyayya.
★★
Daukacin ilahirin unguwar bama masallacin kawai ba......ba abinda kakeji daga manyan sifikun da masallacin mafi kyau girma da daukan hankali ke fita sai lallausan sautin karatun qur'ani da muryar fitaccen malamin addinin nan.....kuma jinin sarauta yarima muhammad haisam aba jifar.
Daren ashirin da bakwai ne ga watan ramadan. Daren da duka musulmi suke bawa muhimmanci tare da qarfafa zaton samun daren lailatul qadr a cikinsa. Duk da ba wani nassi kai tsaye daya bada tabbacin cewa eh shine daren.
MASJID ASSAKEENA.....masallacin da kaf unguwar da kewayenta ba masallaci irinsa. Wani irin gini aka masa me daukan hankali qwarai,taswirar masallacin haram na madeena aka dauko aka tsara masa gini me kamanceceniya dashi. Ya dace da gurin dama unguwar ta masu hannu da shuni qwarai,saidai duk da yawan security da unguwar ke dashi saboda wanzuwar yarima haisam din a cikinta,hakan bai hana mutane daga nesa zuwa masallacin yin sallolin farilla guda biyar ba. Har ma da sallah juma'a ake gudanarwa.
A yanzun da aka cikin watan azumin ramadan kuwa. Wani irin cika masallacin yake ba masaka tsinke,masallacin dake da sassa biyu manya manya. Sashen maza dama sashen mata,wanda shima aka qawatashi sosai kamar sauran sasannin na masallacin.
Ba kyan masallacin kawai ba. Abu mafi jan hankali a masallacin bayan tsaro da yake dashi,kyau da tsari na shayar da masallata ruwa me kyau da lemuka harma da shayi......limaman masallacin.
Qananun matasan 'yan ukun masu abun burgewa. Jinin masarautar jimma....jinin masarautar gumma. 'Ya'ya ga yariman matashin nan sheikh muhammad haisam,wato muhammad muhammad haisam(ashraf). Da ibraheem muhammad haisam(aseef). Da kuma mahmud muhammad haisam (afeef).
Dukkaninsu shekarunsu na haihuwa tsakanin goma zuwa sha daya. Amma kowannensu mahadacci ne na alqur'ani me girma.
Ba iya haddar kawai ba,qira'o'i ne kala kala suka iya,ba wadda basa yi cikin qira'o'in nan guda bakwai sanannu. Hakanan kowannensu akwai launin sautinsa,yadda yake sarrafa qur'ani a harshensa da yasha banban dana dan uwansa.
Asharaf yana yin qira'ar sheikh badr al turki,kuma da yake yana da miskilanci sai qira'ar ta dace da yanayinsa sosai.
Asif ne yake qira'ar sheikh yasser aldosari. Yana qaunar malamin tun asali,wannan ya sanya ma haisam sai daya tafi dashi umra suka gaisa.
Afeef qira'ar sheikh sa'ud shuraim yakeyi,wadda kusan dukka cikinsu best qira'ar ammensu akhnan kenan idan ka cire asali ta mahaifinsu.
Wani dadi nutsuwa da kwanciyar hankali takeji a duk sanda take sauraron karatun yaran nata.
Kaman yanzun......bayan da haisam ya idar da raka'o'i biyun farko kaman yadda suka saba. Yakan fara budewa ne da nasa jagorancin,sai ya matsa baya ya bawa daya daga cikinsu.
A yau din afeef ya kalla,don ya fisu sauri sauri a karatu. Duba da yadda masallacin yake a cike da mutane,akwai buqatar sassauta tsahon tsaiwar sallar kamar yadda addini yakeso.
Suna jere ne a bayansa,dukkaninsu sanye da farar silk jubah da mayafin nan da larabawa ke dorawa saman kansu,wadda hasken fararen qwayayen da suke tarwai a masallacin suka fidda kyanta da sheqinta da tsadar da take dashi.
Kai yaron ya rusunar alamun girmamawa ga mahaifinsa,sannan ya taka a hankali yahau saman abun sallar inda haisam din ya sauka.
"Allahu akhbar" Muryarsa me cakude da yarinta kadan ta ratsa ta mic din ta raba wani irin nutsatsten sauti zuwa kowanne sashe na masallacin dama uguwar gaba daya.
"Alhamdulillahi rabbil Aalameeeeennn". Ya soma da suratul fatiha. Sautin daya ratsa da wata irin nutsuwa ya kaiwa akhnan dake tsaye itama cikin tarin kushu'i saman abun sallar ta. Cikin private musallah dake wani bangare dake manne da masallacin a cikin gidansu. Ita da sauran hadimanta ne duka da ma'aikatanta mata,wadanda suka kusa su ashirin. Aikinta ne wannan,bata sake dashi. Duk wanda ke qarqashinta sai ya tashi wannan ibadar indai ba uzurin al'ada irin na diya mace ba. Cikin taimakon Allah.....sai itama Allah ya hadata da masu son ibadar,ance kamanninka kamannin mutanen da kake rayuwa dasu,kuma zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai. Sun riga sun tasirantu da kyawawan dabi'u irin na iyayen gijin nasu sheikh haisam da akhnan.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Idanu ta lumshe a hankali,tana jin wani alfahari da yaran nata. Tana jin wani tarin godiya ga ubangiji bisa ni'imar da yayi mata. A duk sanda zata wuce ta dakinsu,kota garden na gidan taji suna musaffa sai taji hawaye ya cika idanunta. Ko iya irin wadannan yaran da haisam yasa ta haifa.....ta kawowa duniya kyakkyawan iri....kyakkyawan misali....me zai hana ba zata kirashi da suna ALMAZ BA?(lu'u lu'u). Wani lokaci takan jima tana kiranshi da LU'U LU'U din,idan kuma ya juyo ya kalleta sai ya sake mata murmushi.
"Ke kika cancanci wannan sunan da kika bani rassa masu kyau.....dukkan bishiya me kyau ita ke fidda 'ya'yan itace masu kyau".
A yanzun hatta dasu ahsan sun dauki hanya,sunyi nisa a tasu haddar,a sanda kuma su asif kowanne haisam ya fidda tsarin makomarsu da yake tunanin zasu zama a gaba.
"Kita musu addu'a,Allah ya hukunta musu alkhairi a abinda na zaba musu,addu'ar uwa nada kaifi sosai" Takanyi murmushi,abun ita kanta da take uwarsu yana burgeta sosai.
Sun samu fasihin uba,wanda gobensu da jibinsu yake kallo,ba jiya da yau ba.
Yakan ce
"Shi ashraf,shine babba,first born....ina masa sha'awar business Administration + Economics,shi ne babban magaji. Shi yasa nake tafiya dashi meetings. Yana kalla,yana koyon shugabanci,kuma yana fahimtar yadda ake tafiyar da kamfanoni. A nan gaba shi ne zai zama shugaban empire dina gaba daya. CEO na haisam group of company in sha Allah" Murmushi tayi a sannan tana jinjina kai.
"In sha Allah" Itama ta mainaita.
"Sai Afeef (Mahmud),The Innovator Computer Science + Artificial Intelligence. Afeef yana da basira sosai da naci akan duk abinda yakeso ya koya....nasan kema kin lura,inaso nan gaba ya zama me gina software. Yana son cybersecurity tun yanzu na lura,sannan yana son robotics. Kin gane hikimar zamanshi a haka?" Kai ta girgiza.
"Good.....Shi ne zai mayar da empire din ta zamani,kowanne zamani aka shiga zai sanyata ta dinga tafiya daidai dashi" Kai ta jinjina.
"Idan Ashraf ya gaji empire din, Afeef ne zai kai shi gaba." Murmushi ya sake balle mata,saboda yadda taji hikima a tsarinsa sosai.
"Sai Asif(Ibraheem),The Diplomat International Relations + Law,ya iya magana baba na sosai......ya iya sasanta qannensa tun yanzun" Dariya tayi sosai.
"Son kai ko?" Girarsa da kafadarsa gaba daya ya dage yana karyar da kai.
"Gaskiya ce....ke mamarsu ai kin fini sanin hakan" Kai ta gyada tana murmushi
"Haka yake"
"Bana fatan suyi siyasa.....amma idan Allah ya qaddara masa shigarta.....zan tabbatar ya zamana na daban a cikin su me kawo gyara,bame neman wani matsayi ko muqami ba. Dole a akwai hulda da sarakuna da shugabanni. Akwa wakilci duk zai iya shiga ciki,kinga zai taimaka sosai wajen tafiyar da ragamar gidan nan dana masarautar kakansa.....idan kuma likitanci ya zaba....nafi masa sha'awar cardiology ko surgery saboda ceton rayuka"
"Allah yayi musu zabi mafi alkhairi" Akhnan ta fadi zuciyarta na mata sanyi gami da qara alfahari da iyalin nata.
Sai kusan hudu aka kammala sallar,ta sanya ruqayya ta sauke mata su yumna da sukaqi yarda su kwanta a dakinsu. Yawanci idan zata fito sallar da ruqayya suke zama a dakinsu,amma idan fa suka farka to sai gurinta kuma.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 162* __________________________ *_Amintaccen gurin siyayya_*
*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*
*_BONONZA DA PROMO akai akai_*
*dukka sai a HUGUMA CLOSET*
*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*
*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*
*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*
*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX ___________________________
Ta sani,bazai shigo gidan ba sai bayan sallar asuba. Yawanci a can sukeyin sahur da abincin da yasa ake dafawa kuma a raba duk me sha'awa ya zauna yayi sahur a masallacin. Lafiyayyen abinci ne kamar a gidanka,don ko a gidanka abinda zakaci kenan,da shayi dai da ruwa da drink,saboda wasu nada dan nisa,kafin su isa gida suyi sahur lokaci ya qure musu.
Wannan tsarin masallacin daban yake,kusan ya ciri tuta kuma yayi suna. Hakanan tasirin albarka da addu'ar da haisam din ke samu ne na jama'a keta bibiyarsa shida iyalinsa.
Yakan gaya mata cewa.
"Ko bayan na mutu.... Ki riqe ciyarwa,ba abinda Allah keso sama da ciyarwa. Ciyarwa tana bude qofofin arziqi da alkhairi ga dan adam me tarin yawa,tana rufe qofofin tsiya dana azaba sosai" Murmushi take ta gyada kai,ta yarda da wannan tuntuni. Ciyarwar da takeyi duk juma'a tun tana akhnan dinta,me izza da jin sarautarsu tafi ta kowa......a kullum tana kyautata zaton qilan ita kadai Allah ya duba cikin ayyukanta ya karba ya mata kyautar haisam din. Banda haka batajin tana da wani aiki da zata samu wannan ladan.
Bayan sun gama sahur a Masjid As-Sakina, suka fito cikin sanyin iskar qarshen dare.
Yaran suna zagaye da Haisam suna masa hira.
Ashraf ne ya ja sallar Fajr a wannan asubahin.
Muryarsa ta cika masallacin da wata nutsuwa mai kama da ta mahaifinsa shekarun da suka gabata.
Da suka shigo cikin gidan,akhnan tana jiransu. Don bayan sahur bata kwanciya har sai taga shigowar haisam.
Fuskarta cike take da farin ciki da annuri wancan irin farin cikin da bai taba gushewa ba muddin zata ji sautin muryoyinsu suna karanta Al-Qur'ani a masallaci.
Tun daga nesa ta hangosu,haisam a gaba,yaransa shida a bayansa banda su yumna dake daki suna bacci.
Kamar wata qaramar rundunar sarakuna haka idanunta ke gane mata tattare dasu.
Sai ta jingina da bakin qofar parlour tana kallonsu. Ba tare da ta ce komai ba......haisam ne ya fara lura da ita. Murmushi ya bayyana a gefen bakinsa.
"Why are you standing there?" Ya fada da muryar nan da ko yaushe take taushi idan zai magana da ita. Kusan narkewa take idan taji muryar,akwai randa ta riqeshi gam suna cikin yara,Allah yasa sun juya suna ficewa.
"Haisammm manaaa" Ta fada a shagwabe,shi da ita duka idan suna abu kaman basu ajiye yara haka ba.
"Akhnaaaannn.....me kuma?"
"Kana sani ina narkewa......don Allah abbeee....wannan muryann....hmmmmnnnn". Murmushi ya saki,ya kamata a nutse ya zaunar da ita,sannan ya zauna kusa da ita.
" Bazan iya daga miki murya ba my princess....bazan iya ba,kada ma Allah ya kawo ranan....manzon Allah ne yace rifqaan bilqawarir,ma'ana kuyi hankali da abun qarau dinnan,kaman abu na glass....kinsan me yake nufi?" Saita girgiza kai tana murmushi. Ta karanta ta sani ta gani,amma a bakinsa kawai takeso taji. Kota karanta nassi ko tarihi,tafiso taji ta a bakinsa,yana wani irin shigarta ne da zauna mata a kai.
"Manzo S A W ya kwatanta zuciyar diya mace da tangaran ko glass saboda rauninku,yaya zan iya miki magana da irin muryar da nake magana da kowa?....kamar ke din bata musamman bace?" Wani lallausan murmushi ne ya subuce mata,ta boye fuskarta saman kafadarsa tana dariya.
"Kai kam ko....Allah ya maka baiwar iya koyarwa....kai din malami ne na haqiqa".
"Karatu kawai na iya na takarda....ko harda wancan daya karatun?" Ya tambayeta muryarsa can qasa da wani yanayi daya sanya duka tsigar jikinta zubawa.
Ruqunqumeshi tayi tana qyalqyala dariya,don da iya maganar kawai ya tsumata gaba daya. Dama haka yakeso.....irin cikin su ashraf ne.....kai tsaye ya dauketa suka wuce can matattarar sirrinsu.
Kama yatsunta da yayi ya dawo da ita daga tunanin,sai ta girgiza kai a hankali.
"Nothing." Ta amsa tambayarsa,amma murmushinta ya qara fadada.
Ashraf ne ya karaso kusa da ita.
"Ammiee."
"Hmm?"
"How was it?" Ta san abinda yake nufi,kowace rana idan ya ja sallah. Sai ya tambayeta.
Sai ta kamo fuskarsa da hannunta,kamar yadda take yi tun yana qarami.
"It was beautiful ashraf......barakallahu feek" Idanunsa suka yi haske da wani farincikin yabo daga mamar tasa. Uwar da sukewa wata irin tarin qauna tun suna qananunsu har zuwa yanzu da suka qara hankali.
"Every time I hear your voice..." Sai ta dan yi shiru
"...I remember the little boy who used to sleep on my chest." Su asif suka fara dariya.
"Not again." Ahsan ya fada.
"Mama always says that."ajmal yace shima.
"Because it's true." Ashraf ya fada yana gyada kai cike da qaunar ammiee din tasa
Tsaiwa kawai haisam yayi yana kallonsu,idanunsa cike da wani irin natsuwa.
Akhnan ta waigo ta hada ido da shi,na dan lokaci babu wanda ya yi magana. Sboda babu buqatar magana,magana ce yawancin lokuta sukeyi tsakanin zukatansu.
Shekaru da yawa sun shude. Sun sha gwagwarmaya. Sun sha hawaye. Sun sha farin ciki. Amma a wannan lokacin...da yaransu suna kewaye da su. Da sautin Al-Qur'ani har yanzu yana yawo a kunnuwansu. Da Ramadan ya sake hada su a teburin sahur. Akhnan ta ji kamar Allah Ya amsa addu'ar abinda ta fi so a rayuwa.
Sai ta matsa kusa da Haisam.....ta sauke kanta a kafadarsa.
"Alhamdulillah." Sai ya sumbaci goshinta a hankali.
"Alhamdulillah." Kuma a karon nan... ba ta fadeta ne saboda dukiya. Ko sarauta. Ko nasara.
Ta fada ne saboda tana kallon mijinta da yaranta.....ta san cewa wannan shi ne mafi kyawun arzikin da Allah ya taba ba ta.
*Alhamdulillah!*🎉🤍
🌹*SAƘON GODIYA*🌹
*_Assalamu Alaikum wa Rahmatullah_*
*Da farko* *_Alhamdulillah da yardar Allah da taimakonsa muka kawo qarshen Lu'u Lu'u._*
*_Kalaman godiya ba za su isa su bayyana irin farin cikina da jin daɗin da nake yi ba saboda qauna_* *_addu'o'i, sharhi, gyara, da goyon bayan da kuka nuna min tun daga farkon wannan tafiya har zuwa yau._*
*_Ga duk wanda ya karanta, ya yi comment,ya yi addu'a, ko ya kasance cikin masu jiran sabon page da doki, ina muku godiya daga zurfin zuciyata. Kun kasance wani babban bangare na nasarar wannan littafi._*
*_A wasu lokutan nakan gaji, nakan rasa qwarin gwiwa, amma kalamanku masu dadi da qarfafawa sukan sa ni ci gaba da rubutu. Wannan littafi ba nawa kadai ba ne, na ku ne tare da ni._*
*_Ina roqon Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya sanya abin da kuka karanta ya zama sanadin farin ciki da albarka a gare ku, Ya kuma hada mu a cikin alkhairi a ayyuka masu zuwa._*
*_Ku yafe min duk wani kuskure da kuka gani a cikin rubutun, domin kamala ta Allah ce kadai._*
*_Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da ni a dukkan tafitar rubuce rubuce na na gaba._*
*_Na gode. Na yaba. Ina Qaunar ku saboda Allah._* 🤍🌹
*FI AMANILLAH*🙌🏽🙌🏽
✍️ *Safiyya HUGUMA* 08187255862