Labarina 1 to end complete 1 - Chapter 3
Labarina 1 to end complete 1 Chapter 3: Labarina 1 to end complete 1 Chapter 3. Muna zaune ni da umma tana aiki a system dinta ni kuma inai mata hirar…
4,457 words
Muna zaune ni da umma tana aiki a system dinta ni kuma inai mata hirar dunyi nace umma kinga su bakara (wadda muke uba daya dasu) Gani suke asirin da sukai min ne yai ta siri uhmm basu san Allah ya fisu ba,umma tace kaf din su ba suyi halin uwar su ba,har gwanda mazan,ni wllh umma har Maman ma haushin ta nake ji, Dan ita ce bata tsawatar musu, shiya sa sai na fi sati ban shiga bangaren su ba, to Allah ya sawwake ta kuma cigaba da kare mu Ameen,
Mu tara ne 'ya'yan umma aunty Jidda,aunty mas'uda,sai aunty Farida,aunty zainab sannan kuma ni mufeeda,sai kanina Abdul yayi candy Sadiq yana last year a secondary Muhd yana ss1 sai kuma fadila a jss1, ita kuma mama tana da mata hudu maza uku, Mayan 'ya'yan Abban mu su uku ne Maman su ta Haifa ta rasu maza biyu mace daya,da yake ummana ce amarya😜
Su fadila har yanxu basu taso dg ismaliyya ba,sarakan fada yanxu zaki Ji su dan lokacin ta shi yayi su har yanxu basu gama hankali ba, Kin ji ihun su kai Allah ya shirya, Ni dai umma bari na shiga daki na yanxu sai su sama mutane ciwon kai kyaji da shi Ke dai Kice zaki ki je ki sana'ar taki ta bacci kai umma na dade ban baccin rana ba,
A bangare muhseen kuwa yana zaune yana karanta jarida mukhtar abokin sa ya turo kofar tare da sallama, Ah abokina Kaine tafe haka ba dole na zo ba,kai da na nace ka jira ni gani nan sai zuwa nai na tarar ka katafi to ba dole na tafi ba, Ka shanya ni kamar kayan wani to afuwan aboki ya huce,yanxu ya akai uhmm abokina ban baka labari ba name kuma, Uhm ae tsayawar da nai jiran ka,ya zamar min alkhaeri ko me ya faru cikin sauri mukhtar ya tambaya, Na hadu da wata yarinya,me hankali,nutsuwa ga kuma kyau, kai Kace wannan tai sa'a,tai sa'a ko nai sa'a ae ba irin wannan emmatan bane wanda ka sani wannan ta hadu,to yaushe zamu na ganta ne,saurin me kake haka ne ae ko fada mata banyi ba,sai da nai dabara sannan na sami number dinta da address na ta,nan ya kwashe labarin abin da ya faru ya fada masa,to ya kuma za kai da Angelina tsaki yai sannan yace kaima Kasan wannan ba son ta nake ba ita kanta ta sani koda ina kasar su bana biye mata bare yanxu dana dawo,ta cigaba da shirmenta har ta hakura ta daina,to amma ya kamata ka fada ma madam din taka kar kaje wani ya riga ka bayan kai kuma ka afka,zan je har gidan na su muyi maganar,bari naje duk yanda kukai da ita ka fadan Allah ya bada sa'a Ameen in ma da iskanci ka fada,
Ko da yamma tai ina kitchen ina girki ina tunanin muhseen ni ba abin na kira ba nace masa me, Tuwon alkama miyar kubewa tare da busasshen kifi nake shirya mana,ina cikin dogon tunani na waya ta dake gefe ta soma kara ina dubawa na ga muhseen ne,cikin farin ciki na dauka amma sai da ta kusa katsawa sannan nai picking iri dan Jan ajin nan namu na mata😜,
Cikin muryar sa me dadi yai sallama na amsa masa, Kwana biyu kin buya murmushi nai sannan nace ina nan amma baki nema na, uhmm ya kake lapiya ya umma tana nan kalau, kina ina haka ne,me kaji kawai tambayar ki nai ina gida ina girki, Har da zance miki zan zo, uhmm tom in na gama ba sai ka zo ba, tom shikken me kike girka mana haka tuwon alkama miyar kubewa woow delicious asa dani tom sai kazo,
Ciki sauri na kammala girkin na zuba a flask sannan naje na cema umma zanyi bako,cikin mintinan da ba su fi 20 ba nai wanka na shirya cikin doguwar riga ta atamfa blue me adon pink,ina kan sallaya na idar da sallar magariba ya kira yace ya kara so, Na tashi na kuma gyara fuska ta sannan na feshe jiki na da turare,na kira fadila nace takai shi dakin baki sannan ta jera abinci a dakin, Sannan nace ma umma zan fita haka kawai na Ji gaba na yana faduwa,na daura na karasa bakin dakin nai sallama na shiga sai da ya katse wayar sannan ya amsa sallamar...... [2/15, 7:20 PM] +234 703 962 5239: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕
*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~
Page 130-135
*Ina godiya ga duk kan masoya na da masu Fatan alkhaeri, nagode da addu'ar ku Allah ya bar kauna*😍😍😍
Ina zaune akan sallaya ina kammala azkar ya kira ni,da kamar bazan dauka ba, na dauka dai,fatan kin tashi lapia na bashi amsa, ya rashin bacci kuma,ya akai Kasan ban yi bacci ba,ae daka jin muryar ki ansan bacci be ishe ki ba,to ni nayi bacci haka dai kika ce bayan da tunani na kika kwana,kamar yanda tunanin ki ya hanani bacci, Uhmm to ki samu ki kwanta kamin lokacin skul yayi kya dan rage kar kan ki yazo yana ciwo sai anjima zan kuma kira nace tom,
Tsawon Kwana uku kullum sai ya kira ni amma be samu wata gamsashshiyar amsa ba,a wannan lokacin kullum sai nayi istikara, tsawon Kwana uku wani son muhseen ne yake karuwa a zuciyata,
To ya zanyi gashi kullum son sa gaba yake, daga hannu na nae sama ina addu'a ya Allah kafini sanin komai na rayuwa ta Kaine masanin gaibu,ya Allah idan har muhseen ne alkhaeri a rayuwata to Allah ka tabbatar min dashi,wasu hawaye ne suka zubo min sbd tunawar da nai da abubuwan da suka faru dani, Allah na barma komai,
Koda muhseen ya kira cikin hikima da dabara ya samu amsar sa, tun daga wannan lokacin soyayya me karfi ta kullu a tsakanin mu,
A haka har muka fara exam,bayan mun fito shukrah tace kawata wai baki lura da mufeeda bane Kwana biyu ta fan canja kuma ga yawan wayar da take yi ko dai kin saukko da ka kan kujerar nakin da kika hau, Ku dai kun fiye sa ido a'a ae kece kamar wata me iskokai lamirin ki sai Ke, ni'ima tace wane ne yai sa'a haka ya janye ra'a yin ki bamu labari, Kudai kun fiye son jin gulma muka zauna, duk yadda suka so jin labarin muhseen ba su Ji ba, na dai fada musu su nan sa, To gashi anfara exam ya ake ciki, ae kayan da zamu sa kamar kala biyu ya isa ko,eh yayi daya Musa muzo dashi,da kuma in za'a partyn da aka hada to hakan yayi, ni'ima akan Mama ki zabo mana kizo dashi gobe sai mu gani,
Mun fitar da atamfa irin fashion din nan me kalan ja,sai kuma leshi yellow wanda akai masa adon fulawa blue, ni na karbi kayan na kaima mai yima na dinki nace yai mana iri daya a atamfa yayi doguwar riga a leshin riga da siket,gwajin shukrah na kai itace kawai ta dan fi mu kiba da kadan amma ni da ni'ima kai daya aka yima na, Ran e gobe mu gama exam gidan mu suka zo suka karbi kayan su kai amma dinki yayi kyau daman ae ya iya dinki sosai kace gobe zamu dau wanka, yawwa ga wannan kayan shukrah tana fito dashi daga jaka inji yaya Isma'il yace gudunmawar sace dogayen riguna ne dg Dubai ya tawo mana dasu jiya ya bani yace nabawa ko ta ta, Da sauri na zari wata blue me adon dutse pink, Allah yasa mara kyaun kika dauka, eh naji komecece na fison ta to da ma baki sauri ba ita yace a baki, sbd Nina ce ya siyo mana Ke ni'ima ga taki orange me adan lemon shukrah ta ta pink ce da adon purple, kai amma sunyi kyau, to yanxu kaya sun karu sai mun san ja tsari gaskiya, kyau wannan dogayen rigu nan Musa in za'a party gaskiya,wannan leshin koma gobe muzo dashi a jikin mu,haka muka gama tsare tsaren mu gwanin sha'awa. Haka na raka su titi kowacce ta tafi gidan,
Washe gari exam sai 2-4 ce sai da nagama shiri na tsafa ni'ima ta biyo min nasa leshin na daukko blue din mayafi da jaka blue takalmi ma blue haka itama ni'ima, kinga zo mu tafi kinga tun dazu waccen uwar azazalar take kira muje Kila ta kara so, Muna zuwa muka ganta a bakin gate tana jira haba kunsan ana jiran ku kun ki fito wa ina tsaye kowa sai tambayen lafiya to muje ayi haquri, duk inda muka huce sai an kalle mu masha Allah wanka mu yafita,wasu ma har magana suke, mufeeda ina nikaf din ki,tsaki tayi sannan tace gashi sbd kallo har tun tube nake yi, suka sa dariyar keta ku kunfiye tsokana muje kar a shiga muna nan, fatan kowaccen mu tayi karatu kunsan wannan malamin ba sauki y iya murda question, ae ni jiya ban yi wani bacci sosai ba to Allah ya bamu sa'a ameen, muka kara sa exam hall duk hadin kan mu amma in za'ae exam rabewa muke yi,
3:45 aka fara submitting ana fitowa muna fito duk wanda kagani maza da mata fuskar dauke da fara'a a haka aka fara pictures da sauran friends din mu, ku kuna nan kuna pictures gashi monitor yana raba invention card ga naku nan,OK next week ne ma,Allah ya kai mu, ya kamata kuzo mu tafi ga yamma yayi,haka aka yi exchanging number da en class sbd wasu baza su dawo party ba.................
Love u all my fans😘😘😘😘 [2/15, 7:20 PM] +234 703 962 5239: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕
*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~
Page 150-155
Cikin jin dadi suka gama hirar su san ya daukko wani karamin akwati ya mika ta ga gitf dina ta gama exam kai gaskiya ni bana san irin haka wllh ni ba zan karba, To in ban baki ba wa zan bawa,kawai ka barshi kin san dai ba kyau me da hannun kyauta to na gode,
******
*Wane muhseen*
Muhseen dane ga alhaji muhammad, haifaffen garin kano ne,su bakwai ne a wajen Hajiya Aisha Aunty Bilkisu ce Babba sai huda,sannan muhseen sai kanin sa Naseer, sai kanwar su me sunan hajiyar su Aisha suna ce mata mama itace sa'ar mufeeda,sai husna,sai autan su Ahmad, sun taso cikin kulawa da so,anyi bikin matan Bilkisu da huda, Muhseen a UK yai karatu inda ya karanci business administration, acan ya hadu da wata yarinya Angelina wadda ta Ke tsananin son sa amma shi koda wasa baya son ta sbd bata d hali ga shi Christer ce kuma duk wani gidan giya ta san shi, a haka har yai karatun sa ya gama farkon haduwar su ta dauka irin abokan harka ta ne,amma ina sai gashi shi kuma ba wanda ya tsana kamar ta,
Yau ma haka yana zaune ta kira Shi haba dear me yasa wai baka sona ne nace zan dain shaye shaye zan daina duk wani abun da baka so pls, yaushe zaka dawo UK sai da yai murmushin takaici sannan yace ba yanxu ba sai na aure zan zo kuka ta sama sa ta na ba shi haquri, Kashe wayar yai gaba daya ma dan karta dame shi,
Ranar partyn su mufeeda a gidan su na'ima suka hadu dagan suke wajen make-up duk anyi musu sunyi kyau amma mufeeda tace bata so basai anyi mata ba, Haba mufy kiyi haquri ko kaka ayi miki mana ni ki kyale ni bana so, Sai da kyar.sannan ta yarda akai mata light make up tayi kyau sosai ta yane kanta da mayafin doguwar rigar shukrah ta ja motar suka tafi,Fatan dai duk kun daukko kayan da zamu je photon ko,eh to yan uwa mufara zuwa muyi photon sannan mu karasa sbd in muka ce sai an tashi ba lallae mu sami damar zuwa ba, gaskiya kam ina zamu muje studio24 yafi kusa,am musu sunyi kyau kai kace labarawa ne sbd kyau daga nan suka karasa wajen da za'ae party suna shiga kallo ya dawo kan su, Kowa na fadin albarkacin bakin sa,muhseen ne yaje gida ya tarar bata nan ta tafi party,kai star shine me yasa kika tafi bayan kin san tare nace zamu,kiran wayar ta yai amma bata dauka,a lokacin suna can ana musu photos, Yawwa fadila zo nan ina aunty ki kamar zatai kuka tace ta tafi party kuma bayan tare tace zamu tafi,na dawo dg ismaliyya na tarar ta tafi, to yanxu zaki eh mana to sauri Kije Kice ma umma zamu tafi tare in Muhd yana nan shima ya shirya mu tafi tare da gudu ta shiga gida tana murna ta fadawa umma, umma tace su haqura kawai,kuka ta fara sannan umma ta yarda suka shirya suka fito da yake yaran suma suna da kyau, ba karamin haduwa suke ba,yawwa ku taho mu tafi suka ciga yaja suka tafi, Koda suka je tuni an fara party,suka nemi waje suka zauna,sam be gano mufeeda ba, ita kuwa samun waje tai taje ta zauna inda ba haya niya,sbd wajen a cike yake kuma tunda taje maza suka fara yi mata magana Can aka fara bata award wanda suka yi fice a shekarar, Duk wanda aka kira sai yaje ya karba tana zaune taji ana,yanxu zamu kira dalibar da tafi kowacce daliba a wannan shekarar shigar mutunci da kamun kai sunan ta Taji an kira gaban ta ne ya yanke ta fadi, Na shiga uku cikin wannan jama'ar zan fita, Shukrah ce tazo ja hannun ta suka je sai da suka karasa tsakiyar wajen sannan ta tafi take aka fara tafi,wasu na daukan ta a photo shikuwa muhseen wani farin ciki ne ya lullube shi,ganin yadda maza suka zagaye ta ana photo yasa fadila taje ta kirata, Ke yaushe kuka zo tun dazu Ke da wa nida ya muhseen da Muhd,to muje kamin ta karasa wajen aka kuma kiran kawayen da suka fi kowannen kawance mufeeda,na'ima da shukrah nan ta koma aka basu award din su, [2/15, 7:20 PM] +234 703 962 5239: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕
*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~
Page 140-145
Ina daki a kwance ni da fadila muna gani pictures din da muka yi,na gaji sosai fadila amma aunty gaskiya kunyi kyau, me yasa Ke baki jagira ba,tunda muke kin taba gani nayi wata jagira, kuma da kinyi kyau zakiyi wllh,aunty wai ina ya muhseen ne,ban sani ba tashi ki fita ki bani waje kin cikan kunne, ga gajiya ga surutun kin sai ki samin ciwon kai,to aunty bani wayar ki nayi game,bazan baki ba,Lah kin yi min alkawari fa,to gata amma Kije can parlor kiye ni bacci zanyi,kai umma fa ta hana baccin magariba wllh in baki fita zan kwade ki,miko min waya na, na fasa to yi haquri fadila ta fita tana dariya,
Koda ta fita gyara kwanciya nayi abinka ga wacce ta gaji tuni na fara bacci, Waya ta dake hannu fadila ce take ringin,kai wannan ya katsa min game dina ni Allah yasa kar ae min game over, ko ya muhseen ne bari na dauka,hello au kanwata ce ina aunty taki tana can dakin ta, Ni kuma ta bani wayar ta ina game to maza ki kaimata, to da gudu fadila ta shigo dakin jinai an fado kaina cikin bacci nake magana fadila mene haka kin san ban son hayaniya in ina bacci ko ya muhssen ne yace naka wo miki wayar,
Kabarba nai star shine na kira daya wayan naki baki dauka ba, eh tana silent ne kuma bacci nake Ayya sannu ya exam wllh alhamdullilah,yau an gama eh to Allah ya bada sa'a ameen, In anyi sallah isha'i zan kara so kai gaskiya ka bari sai gobe yau na gaji,cikin kwaikwayon murya ta yace ni a'a sai na zo, a shagwabe nace na fa gaji yace in kin ganni zaki daina jin gajiyar, kinga fa tunda kuka fara exam Sau daya kika barni na zo, sai na zo kan na kuma magana ya kashe wayar, Bin wayar nai da kallo na ma rasa me zanyi, can dai na tashi na shiga toilet din dake dakin nai wanka, Doguwar rigar da muka yi ta atamfa na sa, zan ta da sallah Ke nan ya kira yace ya kara so, dakin baki nace ya shiga,ni kuma nai sallah ba abinda na shafa a fuska ta turare kawai na fesa na fita
Sallama nai na shiga na hade rai, ni ala dole ya batan rai, tun da nashiga ya kafan ido,woooow natural beauty dan kar naxo naga kyakkyawar fuskar ki shine kika ce kin gaji,
Pls star kin fi kyau in kin hade rai bari na miki photo kamin nace wani abu ya fara,dan Allah ka bari bana so a hakan za kamin photo sai an gani an min dakunya
Tom shikken nan sai kinyi dariya zan daina uhmmmm, Ko gaisawa ba muyi ba fa to,ya gajiyar exam din wllh gata yanxu ma wani irin bacci nake Ji rabon da Nayi isashshen baccin tun kan mu soma exam,yayi kyau Ammm mufeeda kinga in nai miki maganar turo iyaye na bakya maida maganar serious yanxu gashi kin gama exam pls, Mufeeda na kagu naga kin zama mallaki na, tom ka bari na huta wane Hutu kuma cemiki akai wahala.zaki fara in anyi auren,
Komai fa yi miki zan dinga yi abinci ma abaki zan baki, Ko bacci zakiyi a baya zan Goya ki in ta jijjigaki har kiyi bacci, Da sauri na rufe fuska ta ina dariya dan ya bani kunya sosai au wai Ke kunya ta kike Ji tab ae tun yanxu ki kokarin ajiye ta dan in munyi aure ba zance kunya..
To naji yasu Hajiya tana nan kalau yaushe zaki ki gaishe ta,hmm ko baza ki ba, zani mana amma ni kunyar ta nake Ji,kuma kullum sai tai min zance ki, Bari na kira ta ku gaisa Hajiya ga mufeeda zata gani she ki, A kunya ce na gaishe ta ta amsa da fara'a ya mutan gidan suna nan kalau to ki gaishe su, Zasu Ji muhseen dai Yaki ta kawo ki,zan zo in Allah ya yarda, ko nai masa magana yace kuna exma ya exam din alhamdulillah ae mun ma gama to Allah ya bada sa'a ameen, sai anjima Hajiya a huta lapiya [2/15, 7:20 PM] +234 703 962 5239: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕
*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~
Page 160-165
Haka aka cigaba da bawa Saura daliban na sa award din sannan aka cigaba da party aka, sannan aka saki sauti kamin kace me fili ya cika da jama'a ana rawa ita kuwa mufeeda zuwa tai ta zauna, Ni'ima kuwa ta ja hannun su fadila suka shiga filin rawa,
muhseen ne ya kare mata kallo yace amma fa kinyi kyau nagode, Mun zo mun hanaki sakewa da samarin da kike so kiyi ko,uhm kawai nace,suna hk wani saurayi yazo mika masa hannu yai sukai musabiha sannan yace dan Allah Aron kanwar ka zaka bani minti biyu sai da ya kalleta yaga ta hade rai, sannan yace matata ce, ayya kayi haquri ban sani ba amma ina taya ka murna ka sami mace me kyau nagode ya amsa a takaice, Mai da kallon sa yai kanta sannan yace nazo ina kashe miki kasuwa ko,waya na na daukko na fara danne danne hakan ya bashi daman yimin pictures batare da na sani ba, Magariba naga yayi tashi nai naje na kira su na'ima to kannen Michael Jackson rawan ya isa haka ku tawo mu tafi, Muna fito wa dg wajen yana kirana a waya, naje masallaci ku jira ni, Be jira amsa na ba ya kashe muna tsaye har ya dawo sannan na gabatar wa dasu shukrah muhseen ah lallai kin iya zabi na'ima ta ce na yaba da wannan zabe👍
Muka yima su shukrah sallama muku ma muka shiga mota maka tafi,
A daidai wani supper market ya tsaya madam zaki shiga ne,adawo lapiya nace,ya ce Muhd da fadila su biyo shi duk da hararar Danake maka musu be sa sun fasa bin sa ba, zama nai a mota har su dawo da kaya a hannun su,
A kofar gida yai parking sannan ya mika musu kayan yace a gaida umma kokarin bude murfin motar nai naji har yasa mata key,wai Ke yau me Ke damun ki bakomai,
Uhm nagode ni zan shiga gida sai da safe Allah ta kai mu, Ina shiga na tarar sun baza kaya suna kasafi umma mun dawo sai yanxu a'a ba'a fara dawuri bane kiyi haquri kin san bana son ku dinga kaiwa dare ne to umma,
Aunty ga naki wani mugun kallo na watsa musu sannan na fita,ina shiga daki na kashe duk wayoyi na, sannan na shiga wanka
Ina fitowa naga fadila ta ajiye min wata Leda,
Sai da na gama rama sallolin da ake bina sannan na duba wani ket ne na chocolates da wasu turaruka, Bude durowa nai na saka sannan na kwanta, Ciki da haushin muhseen me ya maida ni angaya masa kowane mutun nake kulawa,dan yaga na kula shi shine zai fadan magana, uhmmm zan koya masa daya dga cikin karatuna
Da safe wajen 11 ina goge wa su fadila uniform na jiyo nace ma umma daman kince sai nagama exam zaki sa ghali ya koyan mota to yaushe zaki masa magana to a satin nan zan masa magana,
Umma ina so zanje gidan aunty zee anjima tom shikke nan akwai sakon ta da zaki tafi mata dashi to,
A gaggauce naga ma sannan nai wanka na na karbi sakon na tafi, Sai yau kika ga damar zuwa kinsan bamu dade da gama exam ba
Amma dai kwana zaki yi,nace aa yau zan ware haba dai,zan ma umma waya nace zaki Kwana tab karma kiyi mata dan ko kinyi sai na tafi,
Duk naci wata ran dole ki rabu da ita hhhhhhhhhhhhh Haka mukayi hira cikin jin dadi sannan na tafi
Yau ni kadai ce a gidan ina wanke wanke wani yaro sani ta shigo sani daman kana nan eh ina Maman ka tana gida aunty mufeeda wai ki zo inji muhseen,je kace masa bana nan kaji,ko ya karka sake kace ina nan, kadawo ka karbi wani abu maza je ka,
Yana fita yace bata nan ta tafi gidan yayarta da yake sani na da wayo nan da nan ya hada labari ya fada masa sai da yai jum sannan yace tom jeka, da gudu sani ya dawo aunty na tsara shi yawwa ungu wannan kai da baby sannan wannan gobe sai ka tafi da ita islamiyya ko na bashi 50N ya kuwa tafi yana murna, [2/15, 7:20 PM] +234 703 962 5239: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕
*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~
Page 170-175
Muhseen baza ka same ni a sauki ba wannan Karon nai murmushi, Amma fa duk wannan abun daurewa kawai nake sabida ina son ganin sa,
Tuki kawai yake amma sam hankalin sa baya tare da shi mufeeda meyasa zaki min haka in ma laifi nai miki be kamata ki min hukunci ta wannan hanyar ba,
Da kyar ya kai kansa gida, bangare sa ya nufa ya zauna kan kujera ya dafe kansa wani irin ciwo yake masa,
Tun ran da suka rabu da mufeeda be kuma samun kwanciyar hankali ba ya Allah,ka sassauta min haka yai ta sakawa da kwance wa tsawon lokaci, gashi lokaci bayan lokaci sai ya kira wayar ta amma amsar daya ce a kashe,
Nayi shirin bacci zan kwanta na kunna waya ta ya salam messages ne barkatai suke shigo wa ba kakkautawa sai ko kamin su gama shigowa kiran sa ya shigo har ya katse ban dauka ba sai da yai 5 missed called sannan na dauka murya a dakile ya akai komai ma anyi mufeeda, Ya kike so nayi kin san halin da na shiga kuwa me yasa zakimin haka, To wai me ya faru au duk abinda kike biki san me ya faru ba nagode mufeeda,
So Ke nan zuciyata naji ta karye, zanyi magana yace kiyi haquri akan laifin da nai miki wanda nima kaina ban san wane laifi bane,
To Bakai ne ba na fada ina shirin fara kuka,mufeeda Karki kuka kunne baza su jure jinki cikin bacin rai ba, In ne baki so ki fadan gaskiya,
Tuni na fara kuka mara dalili kaine fa kace ina kule kule sanyayyiyar ajiyar zuciya ya saki au daman akan haka kike fushi dani ae ni wasa nake miki kiyi haquri,
Ko sai na miki waka zaki haqura nai masa shiru to bari ae mata rawa tuni na saki dariya cikin kan kan nin lokaci ya shaho kai na daman ance fadan masoya Hutu ne a lokacin yace ba fada a gida iyayen sa zasu zo ranar Saturday nace to, Na fada ma umma ita ma ta fada ma wanda ya kamata a satin akai tsaida maganar auren mu ni da muhseen wani irin farin ciki yake har mamaki yake bani, Wata biyu aka sa da kyar ya bari a sa dan cewa yai yayi yawa,
Lokacin da naje gidan su,alkaki da dubulan umma tasa akayi na kaiwa Hajiyan su, naga so da kulawa haka Hajiyan su ta dinga nan nan dani, ko da zan tafi hk ta hadan sha tara ta arziki,
Lokaci na tafiya yau Saura wata daya bikin umma shirya ni take sosai kullum da sabon abinda za ae min har nagaji da san mangunguna wasu masu dadi wasu kuma bauri,ga turare iri iri,
Tun yanxu an fara min dilka ranar farko da aka faran har kuka nai sabida yanda ake dirjan fata, gaba daya na daina wanka da farin ruw,
Gashi umma ta hana ni fita daman gani ba gwanar fitan ba inma zan fita sai na sa nikaf,
Duk wani kayan da zansa umma tasa ayi mata odar su dg Dubai a dinken su,
Amarya ta sha gyara gashin nan tubarkalla shima ba'a barshi a baya ba,duk inda na huce sai kaji kamshi ko zama nai a waje har na bar wajen yana kamshi in na taba abu kuwa hk zaka Ji kamshi ya makale ajiki,
Su ni'im da shukrah ne Ke ta hada hada fito da ankon duk abinda suka ce min sai dai nace tom
Yan uwa kuzo kuga irin dukiyar da aka narka waje hada kayan lefe wayyo naira tai kuku har ta gaji,
Haka aka kawo kaya kowa na san barka, Ranar da akaje kafi aka dawo hmmmmm hk aka wuni ana santi gidan masoya na farin ciki makiya na bakin ciki😡
Da kamu aka fara ranar laraba a d apecent akayi amarya tasa wata gown fara ce Sol haka akai ma amarya kamu sannan ake lecture wanda tunda aka fara nasiha da kuma haqqin miji akan matar sa da haqqin mata akan miji mufeeda tayi kuka shukrah da ni'ima ne a gefe na rarrashin ta haka aka gama kowa ya watse amarya da yan tawagarta sukai yo gida,