Kenza eBookz

Labarina complete - Chapter 4

Labarina complete - Chapter 4

Labarina complete Chapter 4: Labarina complete Chapter 4. Washe gari party ne aka shirya shi a season saven a kawayen amarya ne da ango wata doguwar riga…

4,314 words

Washe gari party ne aka shirya shi a season saven a kawayen amarya ne da ango wata doguwar riga tasa me kalan blue da ratsin silver tasa head silver wayyo readers kuxo kuga kyau tab ango muhseen wata shadda yasa shima blue tunda suka je ake yayyafin kudin tunda ga kan nera har zuwa dala,💵,pictures kuwa sun sha shi, [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* ~*(Aunty)*~

Page 180-185

An sha hidima kowacce rana da abinda za ae rana da akai mothers night kuwa umma har Hajiyan su muhseen tace tazo anci an sha irin bayyana kyaun da amarya da ango bata yawun baki ne kudai kawai ku gano min ita,

Ranar Sunday muhseen har tsaguwa yai lokacin yayi gani yake kamar lokaci baya tafiya yarda ya kamata,

A hka suka kara so babban masallacin juma'a inda anan za'a daura auren,

Mufeeda tana zaune a tsakiyar gado ita da kawayenta maryam,Fatima shukrha da na'ima suka jiyo ana cewa an daura auren muhseen da mufeeda akan sadaki dubu dari lakadan ba ajalan ba,

Faduwar gaba hade da farin ciki suka lullube ta tuni wasu hawaye sun fara ambaliya a fuskar ta,

Da sauri Fatima ta fara goge mata hawaye haba mufeeda meya zaki kuka kin san yau ranar farin ciki ce,shukrah ta rike hannunta haba kawas kiyi shiru Karki bata kwalliyar ki,ko so kike in ango ya shigo yaga kina kuka shima yayi,

Dariya suka yi gaba daya sannan suka kuma gyara mata zaman daurin dankwalli, Nan aka fara kiran amarya ta fito ayi pictures da ango, Da kyar kawayenta suka fito da ita, Shikuwa muhseen baki har kunne yau mufeeda ta zama mallakin sa,

An sha pictures sosai da kyar abokan sa suka ja shi suka fita sauran abokan sa suna jira aje ayi walima a info stadium dake kofar mata,

Ci gaba da yini akai a gidan in da masu kidan kwarya suka baje kolin wakokin su,

Da misalin karfe hudu aka shirya amarya cikin wata koriyar lafaya me haske tayi kyau matuka, Tana dakin umma tana kuka wanda tunda aka fara shirin kaita ta soma, Yau zata Rabu da ummanta, Da kyar aka banbareta daga jikin ummanta tana kuka me ban tausayi,😭wata kwalla umma ta goge tana mata Fatan alkhari ta shige daki baza ki san lokacin d zaki fara kuka ba indai kina da saurin kuka,

Haka aka fice da ita zuwa gidan ta dake yahya guso road, iya kacin haduwa gidan ya hadu komai nasa irin na kasar larabawa ne,

En kai amarya suka fara watse wa daga ita sai kawayenta 5 ita ta shida sai hafsa da ameera 'ya'yan aunty sauda suma daya bayan daya suka watse aka barta ita kadai ba yanda batai dasu su zauna ba suka ki,

Wani sabon kuka ta saki yau gata ta shiga wata sabuwar rayuwa sabon dangi,tayi kuka me Isar ta idanu sunyi luhu luhu, Haka ta tashi tashiga toilet domin alwala ta kare masa kallo sannan tayi wani abun ma bata san amfanin sa ba

Magariba tayi sannan tai isha'a tana zaune tajiyo alamun tafiya da sauri ta jawo mayafin ta rufe fuskarta,

Iya kacin gate abokan sa suka rako shi koda sukace zasu shiga yace ya yafe, suka tafi suna masa dariyar farin shiga,

Da sallama ya shiga da muryarta da ta dashe sbd kuka ta amsa zama yai a kan carpet ya riko hannun ta wani shock Taji tunda ga kanta har ya tsun kafa, Da sauri ta janye hannun ta tai masa sannu da zuwa,lallaima mufeeda kuka ne yasa muryarki tayi hka,sai da ya bude fuskarta subhanallah yafa da da sauri haka kika yi kuka sai kace za'a kawo ki gidan presion,

Zafi yaji jikin ta ya dauka zai in kika sa masara tsab zata gasu😜,ya salam ya fada tashi Kije ki dauko plate nasan baki ci komai ba,tangal tangal tai kamar ,zata fadi da sauri ta riko ta kinga irinta ko,zaunar da ita yai ya dauko plate fork,sannan ya zuba musu kajin da fresh milk bude bakin ki Kice a koshe nake zaki ci ko sai ranki ya baci haka ta karba tana ci daman yinwa ce fal a cikin ta, cikin lokacin kadan suka gama ci rike ta yai suka tashi jeki alwala kizo muyi sallah ae nayi nasan kinyi ta godiya zamuyi,

Bayan sunyi alwala sunyi sallah ya jiyo ya Dora hannun sa akanta idon ta a rufe sai da yai kusa 15minutes sannan suka shafa,

Tashi Kije kiyi wanka bari naje daki,ko baza ki iya ba nazo nai miki da sauri na tashi nai toilet ina jin fitar sa sannan nai wanka na fito body freshener na feshe jiki na da ita da wasu humra masu dadin kamshi wata sleeping dress naga ni a gefen gadon,na shiga uku yanxu wannan Zn sa kai bazan iya ba,Tav tana jiyo shi tai saurin sawa ta koma gado ta kudunduna tare da rufe ido kamar tayi bacci,

Hawa yai ya yaye bargo wayyo Allah na fada a raina starshine nasan baki bacci ba ki tashi,shiru nai hakan ya bashi dar yaye bargon gaba daya shima ya kwanto, sum sum nai na fito tare da jawo musu kofar a wannan Daren me cike da tarihi sun faranta ma junan su musamman muhseen [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* *(Aunty)*

Page 190-195

Angelina ce zaune tana shan shisha,abin duniya yabi ya dame ta wai me yasa muhseen baya son ta ne,

yanxu in ta kira wayar sa bata shiga kawarta ce Mary ce ta dafa ta wai tunanin mekike ne haka tun dazu,

Cikin yaren su suke magana, muhseen kai wai Ke yaushe zaki dinga jin magana ne ki rabu da shi ga guys nan da yawa amma kin manne sai shi bakar fata ne fa,tsawa ta daka mata tare da fin ciko ta Ke da Kata Karki sake bakin ki ya fadi wata mummunar kalma akan sa ina son sa a haka ba ruwana da banbanci jinsi ko addini, Zan iya yin komai akan sa for sake of love,kuma duk wadda ta rabe shi zan iya illata ta,

Toni ne ya shigo abokin shaidan cin su, me ya kawo ka Kasan nace ma sai an kwana biyi zaka dawo, Na sani yanxu ma wani labari ne na kawo miki bana son jin komai indai bashafi muhseen ba, eh labarin sa nazo miko dashi da sauri ta tashi ta karasa wajen sa fada min ko hankalina zai kwanta,

Murmushi mnugunta ya sakar mata sannan yace duk da labarin ba me dadi bane sai kin siya, haba Toni kar muyi haka mana to Ke nan bakya son Ji bari na tafi yayi hanyar tafiya ta kamo shi da sauri pls fadan me kake so, Wank murmushin ya kuma saki sannan ya shafi gefen fuskarta yace Ke ma ae kin sani,zan dai baka wani abun banda wannan,indai bashi ba kin ga tafiya ta dakatar da shi tai sannan tace na yarda daman abinda yake son Ji kenan wata irin cafka ya kai mata, ka fara fadan mana haba sai kace banda wayo na fada miki kuma Kice baki son zencen ba,

Toni ya cire yaloluwar rigar jikin ta tun a falo suka fara shaidan cin su kamin ya tashi da kyar ya dauke ta sai gado sun shafe ya fi tsawon away uku suna abu daya sai sai da ya gaji dan kan sa sannan ya sake ta,baccin wahala ne yai gaba da ita,

Tana farkawa ta ganta a jikin sa shima baccin yake daka masa duka tayi,a firgice ya tashi yana kallonta ya saki wata mahaukaciyar dariya sannan yace ta same shi a falo,

Jakar da yazo da ita ya fito da system din sa yana danne danne haba Toni kai da zaka bani labari me ya hada ka da system kalli wannan invitation card na auren muhseen ya nuna mata cike ta shin hankali take karantawa tana gama wa ta saki kara,haba da sauri zaki karaya haka ki bari ki gama gani, Sauran pictures din na bikin ya shiga nuna mata,

Kara da tafi ta dazu tayi tare da cakumu shi tana iho kamar mahaukaciya hayaniyar da suke ce ta ankarar da Mary ta fito fa gudu ganin abinda Ke faruwa yasa tambaya nuna mata system din tai daya bayan daya ta fara dubawa tana gani tana jijjiga kai,

Freg ta nufa da sauri ta dauko mata kwalbar wine ta mika mata da sauri ta karba ta kafa kai sai da ta shanye sannan ta yada kwalba tana cikin maye Toni ya kuma kwasarta yai daki da ita da yake jarabbebe ne,

Sai da safe sannan ta dawo hankalin ta zama tai a kusa da Mary tace pls abinda ya faru jiya gaskiya ne,ta ce eh to menene mafita haquri,kin san abinda bazai taba yihuwa bane zanje har kasar tasu nayi abinda naga dama a'a ki bari jiya kina bacci naje na nemi information akan sa a inda ya fara aiki ance nan da wata daya zai zo,

Sun gama shirya abinda zasu yi in muhseen ya dawo UK sannan suka shiyara su ka nufi club dan aiwatar da abinda suka saba..

Love u all my fans😍😍 [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*Written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* *(Aunty)*

Page 200-205

Gidan yan uwa muka je sallama mun dawo a gajiye,yana zaune ta Dora kanta a ciyar sa yana wasa da gashin kanta starshine kin san kuwa yanda nake son ki kuwa,kullum sonki karuwa yake a zcuciyata wai mene sirrin,dariya tai tace kawo kunne ka kaji da sauri ya kawo, to na fasa fada pls baby tom zo kaji rada masa tai wani murmushi ya saki jin abinda ta fada masa ko me tace masa oho wannan sirrin nasu ne,

Yanxu next week zamu tafi ni gaskiya dear bana son barin garin nan in bar umma to ba gani ba ko ba ki son zama dani a'a, a can ma sai mun fi sake wa shekara daya ne fa kacal da sauri ta tashi daya kai amma gaskiya da yawa zamu dade,

Ta so muje mu karasa siyo abinda ba mu siya ba ko baza ki ba, Da hanzari ta tashi tace zani ma a shirye nake, Suna tafe suna hira ba ruwan sa a ko'ina nuna mata soyayya yake, ko kunya ba ya Ji in tai masa magana yace ni da matata sai a hanani abnd naga dama,

Sauran kwana daya su tafi suka je gidan su Hajiyan sa tai musu nasiha sosai sbd tashin dare zasuyi, Zasu tafi ta riko ta to 'yata mufeeda Allah ya ki yaye ya tsare ku Ameen ki kula da kanki da abinda ki jikin ki sam ban gane abinda take nufi ba, wasu hawaye ne ya zubo min a'a banda kuka kiyi haquri kamar yau zakuga kun dawo,

Haka muka taho gidan mu nan ma umma tai mana fada sosai sannan muhseen ta fita yace zashi gidan abokin sa koda ya fita umma sabuwar nasiha ta min sosai kamar yau za'a kaini gidan miji kuka nake sosai sannan ta daukko wata karamar jaka ta bani tace ga wannan in kin je sai ki duba ko wanne da yanda ake amfani da shi a jiki ki kula da tsafta gida da ta jikin ki, nasan kina da tsafta ki kara akan wadda nasani mufeeda kin san garin kar ki dinga barin sa da damuwa ko bacin rai,

Kar ki barshi ya dinga yawan fita ki zamana kece me daibe masa kewa Karki dunga barin sa da yunwa, Ki kula da irin abokan sa na can duk da nasan baze biyewa shashashae ba in yamiki wani abun kiyi haquri banda yawan complain ko kawo kara ki zama me rike sirrin ko dana mijin ki,

Na san ki da roko da addini ki kara akana wanda na sani nace to umma haka Muhd da fadila suka rike ni muna kuka bayan ya dawo muka tafi ina kuka, suna kuka har muka kule,

A hanya nace ya kaini gdn au shukrah daman munje gidan au na'ima da zamu xo da kyar ya yarda ina zuwa muka rungume juna sai kuka Momeen su ce tafi to da sauri lapiya, haba sai kace yara daka hadauwa sai kuka muka gaisa da mome itama tai min nasiha sosai wasu turare ta hado min tace kar nai wasa da su nai godia har mota shukrah ta rakoni,hk muka rabu ba dadi,

Dare nayi jirgin mu ya tashi sai united kingdom (UK), Muna isa driver na office din su yazo ya dauke mu wani flat din gida matsakaci muka shiga komai na gidan tsaf tun daga gate har ciki,

Zama nai ina karewa palon kallo driver ya gama shigo mana da kayan mu tsaf, Nunfashin sa naji akai na yace ya madam sannun da kokari kaji ka da wata magana ae tare mukai tafi yar kai ma sannun ka, Munyi wanka ina shirya wa ya kalli starshine ta mudubi na kalle shi Na'am ya akai yace bakomai riga nasa mara nauyi sannan nace ina jin yunwa fa sosai ciki na har kuka yake OK zo muje abincin yana Palo,hk muka ci yar da junan mu cikin kulawa

Duk wata damu da Ke tare dani sai da muhseen yasan yan da yai ya cire min ita watan mu daya a UK, Ashe ina da shigar cikin wata biyu ban sani ba, da yake ba abunda Ke damuna sai yawan cin abinci da kayan kwadayi ga kasala,

Muhseen na dawo dg waje. Aiki yake daukana mu tafi wajen shakatawa,hk weekend bama yi a gida,da ka kalle ni Kasan ina jin dadi ga wani kyau dana kara yi sosai,

Ina kawance ina kallon sa yana shirin fita office, ya akai irin wannan kallon ko da magana,yana fada yana karasowa inda nake da sauri na tashi nace a'a dan yanxu ba karamin aikin sa bane ya tsaya, Amma gaskiya kadawo da wuri tom shikke nan baby yana ga ka zauna ka tashi, Kamo hannu na yai yace baby ni fa gaba daya kin canja kinyi wani kyau ga haske murmushi nai nace kawai weather din garin ne ya karbe ni anyya kuwa, Eh mana kaima Kaga yanda kai kyau kuwa ina fada ina shafar sajen fuskar sa amma ae ban kai ki ba,anya kuwa shiru yai sannan ya Dora hannun sa akan cikina ya akai sai naji kamar akwai ajiya a ciki ba wani nai saurin fada tare da tashi,ina lura fa dake tunda mukai aure banga kina fashin sallah ba shiru nai ina tunani dan wata biyu ke nan bn ga mensis dina ba,kuma tunda muka xo kullum kike cikin lalaci Rannan fa cewa kika kina son zogale, To ka tafi karka makara amma fa ina dawo sai munje asibiti an yi check opp naki naga lpy baby na,

Har mota na rakashi sannan na dawo ina tunani nima naji sanji a jiki na sosai, bacci na koma sai 11 sannan na ta shi sai da nai wanka sannan na fito nashiga cikin raguwar kayan breakfast din da muhseen ya naci ina kwance a Palo duguwar riga ce a jikina dan na fi jin dadin ta wasu matan turawa suka shigo kallon kallo mukai da su a tura wan ma dg ganin su Kasan yan duniya ne taso zaune nai sannan nace lapiya,

Zama sukai suna taunar cingam suka Dora kafa daya kan daya

Wata me Jan gashi irin na yar tsana ce ta fara magana akan wannan muhseen yake wulakan tani,Mary ce ta magana ba laifi Ashe a bakake a kwai masu kyau kin haduwa fa wata harara Angelina ta watsawa Mary tare da cewa muyi abunda ya kawo mu............ [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* *(Aunty)*

Page 210-215

Tsaye suka tashi me gashin yar tsana ta matso dad da ita kece wadda ta dalilin ki ne muhseen yake wulakan tani ko to yau zanyi maganin ki ta kai hannu zata taba ta ta sauri damke hannun ta wllh kika tabani sai kin Ji ba dadi,

Hanka da mufeeda tai da karfi taga taga tai zata fadi tai sauri tsayawa,tana dagowa wasu tagwayen mari ta sakarwa Angelina wanda har sai da bakin ta ya fashe dambe ne sosai ya sarke a tsakanin su,ita kuwa Mary tana tsaye ta kasa ae watar da komai dan tunda ta ga mufeeda taji ta kwanta mata,

Duka suke kai wa junan su,wani naushi mufeeda ta kaiwa Angelina a fuska sa da ta ga duhu sai da ta dibi wasu seconds sannan ta fara gani take ta fara kai ma mufeeda duka a cikin ta baji ba gani ruwan lemon da yake kan center table ta watsa mata a fuska,amma a banza tun mufeeda na kokarin tashi har ta daina wani irin azaba take Ji ga marar ta kulle tana mata wani irin ciwon da bata taba yi ba kokarin tashi tayi amma Angelina ta danne ta ta cigaba da dukan ta,

Da sauri Mary ta karaso ganin Angelina tana kokarin yin kisan kai dan nunfashin ta da kyar yake fita,iya karfin ta tasa ta hankade ta sannan ta tashi,mahaukaciya Ke zaki kashe ta kallo fa yanda kike mata sai a sannan ta kalleta.wanda har jini ya fara zuba duk da ta tsorata amma ta dake tana zagin Mary ita ma rama wa ta fara tuni fada ya harke a tsakanin su Jakarta ta bude ta daukko wani abu tana shirin watsa mata Mary ta fisge tai j fa da kwalbar tun ta fadi ta fashe,

Wukar ta raruma tayo kanta ae karfin Mary da na Angelina ba daya bane tuni ta kwace ta fara dukan ta tana zagin ta tana duk masifar da ta daukko ta kare mata ita kadai,

A guje Angelina ta fita,Mary ta dawo wajen mufeeda ta jijjiga ta Ji shiru tini hankalin ta ya tashi dan Tasan muhseen in yaji labarin da ita aka zo masa gida to ita kanta sai ta shiga uku,

Da sauri ta nufi freg ta dauko ruwa ta yayyafa mata amma shiru,

Ganin haka yasa tai saurin tattara kayan ta ta fita tana sane ta ki daukan jakan Angelina tana fita ta labe a wani dan sakon inda baza a ganta ba, a gogon hannun ta ta kalla 2 o'clock ta san yanxu yana hanyar dawo wa, Wayar ta ta dauka ta kira shi sai da tai Sau uku sannan ya dauka wake magana cikin sauri yake yana tattara wasu takardu so ya ke ya tawo gida,dan ya tsagu ya zo ya ga starshine nasa, am daman yanxu Angelina taje gidan ka what yai fada da karfi har sai da wayar hannun ta ta kusa faduwa, eh taje ta daki matar ka,kamin yai magana tai saurin kashe wayar gaba dayan ta ko 15minutes ba tai ba sai ga motar sa ta danno cikin layin gaban tane ya fadi, ganin irin gudun da yake yi yana shiga ta fito a guje tai hanyar gidanda suke,

Shikuwa ko motar sa be gama parking ba ya fita da gudu kofar parlon a bude take da sauri ya karasa wajen ta inda take a kwance kamar matacciya, jijjaga ta yake da karfi amma ko alamun motsi batai ba wata kara ya saki Wllh Angelina kika kasheta saina kashe ki ko zan gama rayuwata a prison,

Kuka yake sosai yana jijjaga starshine dan Allah ki tashi Karki mutu gaba daya hankalin sa yabar jikin sa Yama rasa me zai mata sai can yai sauri ya tashi ya sure ta ya fita gudu yake na ganganci wanda ya jawo hankalin security masu kula da hanya suka dafo masa baya wasu suka sha gaban sa da sauri ya taka burki, tambaya suka fara masa kasa magana yai kawai yana nuna musu cikin motar koda suka leka suka ga mace aciki ga jini na xuba tuni suka fara tambyar meene alakarsa da ita da kyar ya budi baki yai musu jawabi,releasing motar sukai sannan ya tafi yana isa aka karbeta akai emergency da ita, sai da aka shafe wajen 3hrs sannan likita ya fito yace ya same shi a office [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* *(Aunty)*

Page 230-235

Suka kara sa wajen inda Naseer kanin sa yazo daukan su dagan nan sai gidan su,sai da suka fara zuwa gida sukai wanka sannan suka shirya suka je gidan Hajiyan sa daya Ke basu da nisa sosai,hajiya taji dadin ganin su gashi har mufeeda ta kusa haihuwa,bayan an gama gaisawa da hiran sannan suka bawa Hajiya tsarabarta ita da 'ya'yan ta sannan suka wuce gidan umma acan y barta shi kuma ya dawo wajen hajiyar sa sai dare sannan ya dawo ya dauke ta suka tafi haka yan uwa da abokan arxiki sukai ta zuwa suna yi Musu sannu da zuwa,na'ima da shukrah sun zo kowaccen su tayi aure,

Satin mu biyu da dawo wa da yamma ina zaune,na yi shiru dan tun safe nake jin ciwo amma na Ke daurewa, muhseen yana ya fita ya dawo can ciwo ya fara yawa wayata dage gefe na dauka nakira shi da kyar nake magana kana ina ne ina gate yanxu zan shigo naka she wayar sai gashin da hanzari ya shigo ganin halin da nake yasa yai sauri karaso ya ya kamani ya kaini mota ya dawo ya daukko akwatin kayan baby sai a sibiti muna zuwa a karbe ni akai labour room dani,

Tunda muka je ya kasa zaune ya kasa tsaye yana ta zirga zirga gashin tace kar a fadawa ko abari in ta haihu a fada musu dan kar a tashi hankalin su

kamin 30minutes na haifi santalelen yaro,

Nurse ce tafi to tace inai maka murna madam ta sauka lapiya,ta haifi baby boy cikin farin ciki yace alhamdulillah,da sauri yai hanyar dakin Yana kokarin shiga ta dakatar da shi tace yanxu za akai su dakin Hutu, sai sannan ya fara yiwa gida waya ana fito dasu ya karbi jajaririn yana kalla wasu hawaye farin ciki ya zubo masa mene kuma abun kuka yai saurin rike hannun ta ni na rasa dawacce kallama ma zan miki magana Allah ya baki lafiya,ya rungume su gaba daya cikin farin ciki da jin dadi asibiti ya koma kamar gidan biki sabida kowa so yake ya zo yaga babyn da aka Haifa dan ana fadar kyaunsa sosai likitane ya basu sallama aka wuce da ita gidan ta muhseen yai ma yaro huduba da sunan mahaifin sa kuma maifin ta ita ma wato Muhammad,wanda suke kiran sa da suna *noor* ranar suna anyi shagali sosai inda umma ta hada walima a meena restaurant har muhseen din ma sai da yaje.

***** Noor dan shekara biyar ne ya biyo Humaira yar shekara biyu da gudu zai kwace mata chocolate dinta kan mufeeda ta fada wadda take zaune tana gyara meeme gashin ta,Ke mene haka bakwa gani ne zaku danne mi 'ya ku matsa ku ban waje baku da aiki sai fada mome shine zai kwacen chocolate dina da aunty fadila ta kawo min ta fada cikin gwaran cin ta,bani ta kwace ta bata kuka yasa muhseen ne ya shigo lalala waya taban dady kai ma zomu fita na siyo ma taka,daukan sa yai zasu fita yayi ma Humaira gwalo itama kukan ta sa ajiye shi yai ya Dora ta a cinyar sa yace su shirya har Momeen nasu su fita shan ice cream,

Sun shirya sunyi kyausosai sannan suka fita domin yi siyyaya, cikin soyayya da jin dadi suke tafe bayan sun gama daga nan suka huce gidan photo vella akai musu falimy din alhaji muhseen da Hajiya mufeeda.

A nan na kawo karshen wannan littafin nawa me suna *LABARI NA* sani abu na cikin littafin ya faru a gaske bakomai ne kirkirarre ba idan akwai wanda be Ji dadi ba to ayi haquri in nai kuskure a yafe ni,nagode da kaunar ku wanda masoyana masu yimin Fatan alkhaeri sda addu'a nagode Allah ya kara zumunci sai mun hadu wani littafin na gaba,

Ta ku har kullum

*Salmah Ali Wada*

Love you all my fans miss you too😍😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘😘

Bye bye [2/15, 7:20 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 💕💕💕 *LABARI NA* 💕💕💕

*written by*✍✍✍ *Salmah Ali Wada* *(Aunty)*

Page 220-225

Doctor ka gayan halin da take ci,ka kwantar da hankalin ka an samu an ceto rayuwar ta da abun da Ke cikin ta wanda bincike ya nuna dan wata biyu da sati daya da da ba ae saurin kawo ta ba daga ita har babyn zasu iya rasa ransu,

Dan bugun da ta sha ya galabaitar da ita sosai wani gumi ya share to ductor yanxu ya jikin nata eh to mun dai mata alurori sannan an sami nasarar tsayar da jinin dake zuba,

Yaushe zata farka gaskiya jikin ta yana bukatar Hutu sosai zata iya kai wa dare ko ma fin hakan, Ga list na magunguna sai kai maza kaje pharmacy ka karbo,

Tunda ya shiga dakin ya kasa zaune ya kasa tsaye can ya zauna a gefen gado kuka yake kamar karamin yaro,ya rike hannun ta kam yana mufeeda ta dalilina akai miki hka ko,kiyi haquri magana yake kamar tana jin sa

Yana zaune ko da akai salla a dakin yai tasa sannan yai addu'ar Allah yaba ta lpy,

Yana zaune yana rike da hannun ta yana tunanin irin hukunci da zai yanke wa Angelina,

Gashin kanta ya gyara mata wanda ya zubo a fuskarta har ta rame ga wanj fari da ta kara,

Kwafa yayi Angelina zaki gane baki da wayo har dare bata farka ba,

Bacci barawo ne ya sace shi cikin baccin yaji kamar hannun sa na motsi yana tashi yaga ta farka amma idon ta a rufe hawaye na fita ta gefen idon ta,ko da ya duba a gogon dakin 2:45am

Starshine kin tashi sannu ya jikin shiru tai cikin ta wani irin ciwo yake ga yunwar da ta huni da ita duk da a cikin drip din Ansa ta abinci,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull